obviously doesn’t deserve you, abu dayane bazanyi supporting naki ba shine kisamakanki damuwan Ni’ima, Hawwa don’t kill yourself akanta, Ni’ima don’t deserve you Allah use this chance ya nunamiki waye ita, so is time kifita daga rayuwansu both ita da mijinta and move on, toxic people ne dukansu biyun, kiji sauki kidena tunanin komi, I didn’t train you to be weak or to be crying for any girl, Hawwa you are a strong girl wacce guguwan iskan mountain baiyi putting baki down ba saida kikai destination naki, shit happens in this life, friends comes and goes, relationship ends that doesn’t mean bazamu cigaba da rayuwa ba, close chapter Ni’ima and move on learn from your mistakes, no more room for wacce wishes you death, your secrets should be for your stomach idan ba ni ko mahaifin ki ba babu wanda ya isa yaji sirrin ki, move on and be a better person kinji, kihakura da Ni’ima, tace taja miki layi kema kijamata layin kinjini” gyadama Ammi kai tayi ahankali tana kuka har lokacin, Ammi ta matso ta manna mata kiss a goshi sannan tadauki tray na abinci cikin masifa tace “nayi tir da dabi’un Ni’ima ayahya taje zata gani indai duniya ne fadi gareta, Allah zai saka miki” tashiga bata oats tana sha, masu massage sukazo akama bayanta massage dataji kaman an mikar da ita an ciremata duk wani bending da ciwon jiki, no wonder massage keda tsada ashe haka akeji, duk wani tsamin jiki saida suka fitar bacci yayi awon gaba da ita haka nurse’s sukazo suka kara mata fixing drip din tana bacci mai nauyi.
Tun asuba Allah sanya alkhairi akema Baba, kafinma yasamu yabar masallacin was around 8:20 sai farin ciki yake nanma wasu suka sake tsareshi anan waje anamai Allah sanya alheri wani kara son Baba ma akayi a unguwan Baba tsabagen murmushi kumatunsa har ciwo yake sai wajajen 9 yawuce gidansa da sallama ya shiga cikin gidan Maman Ni’ima daya gani a tsakar gidan kan kujera yasa yaci tura ya tsaya, Mama ta washe baki tace “ahhh Malam ka shigo barkanmu da safiya ai tundazu nazo nake jiranka” dan jim Baba yayi saikuma yakaraso ciki yace “Malama Maimuna ya kwana biyu ya yara ince dai kinaji daga garesu”? Murmushi Mama tayi tace “kowa na nan lpy, satin daya gabata ma Usaina ta haihu an samu Abdulwahabu” anatse Baba yace “Masha Allah, Allah ya raya” ya kwalama Ramla kira data fito daga dakin Hawwa tace “gani Baba” Mama yanuna mata yace “kaita ciki bari na zaga nazo” Mama ta mike tabi Ramla ciki tanabin dakin Hawwa dakenan tsaftsaf da kallo shikuma Baba yawuce makewaya.
Fitowa yayi ko kallon Umma dake kitchen baiyiba itama haka yawuce dakin Hawwa inda Mama take, kujera yaja yazauna yakalli Ramla yace “jeki hadamana kari Ramla” gyadamai kai tayi shikuma yakalli Mama kai tsaye yace “ya akayi Maimuna wannan dakike nemana”murmushi sosai tayi tace “na farko dai Malam naji labarin dakebin gari sai shigowa makota suke sunamin Allah sanya alheri diyata Hawwa an daura aurefa shine nake kiran Ni’ima dan abankinta yakamata naji wannan labari amman saiba abakinta nakeji ba, nan fa Ni’ima tafara koro zance aiko saida namata tatas dan har mari na yanka mata, akan namiji zatai kalan haukan nan shine fa na zuro hijabi da sassafen nan nazo nabaka hakurin abinda Ni’ima tayi kuyafe mata Baba bakaga yanda ta damuba dan Allah ayakuri kaga tsakanin harshe da hakori ma ana samun sabani balle kawaye” Baba yace “wannan haka yake” Mama tace “Baba toh dan Allah kuyakuri mune iyayensu karmu zuba musu ido su lalata mana zumunta mu daidaitasu Baba, Ni’ima tayi nadama kwarai kawai shakkan ku take dakuma tana tsoro kar Hawwa taki yafemata amman dazaran kasa baki kowa yasan Hawwa zata hakura Malam”Mama tai shiru tana jiran amsan Baba, dan murmushi Baba yayi yace “Masha Allah naji duk bayanin dakikayi Maimuna” yasakeyin shiru yace “dan yafiya wlh na yafema Ni’ima, ni uba ne akan mene zan riketa azuciya bayan nima yarana zasu iya kuskure da shirme kaman nata, idan zancen yafiya ne nayafema Ni’ima har ranan gobe kiyama” dasauri Mama tace “Alhamdulillah,Alhamdulilah Alhamdulillah, shikenan yaranmu sun shirya” ta washe baki, Baba yayi shiru saikuma yakalli Mama yace “Maimuna dubeni nan, ni ubane kaman yanda kike mahaifiya, hakkine akanmu idan mukaga abinda zai cutar da yaranmu mu kauda abubuwan daga hanya” Baba yayi shiru yana lumshe idanu yana tuna yanda Ni’ima take ikirarin kashe Hawwa yace “idan Hawwa zata yafema Ni’ima bazan taba hanata ba amman idan Hawwa zata dawo da Ni’ima rayuwanta saina hanata!”Faduwa gaban Mama yayi dasauri takalli Baba bakinta tafara rawa, Baba yadan kada kafa yace “wato Maimuna jiya na karanci abubuwa da dama akan idanun Ni’ima, tundaga kissan data dinga ikirari zatama Hawwa, da fatan mutuwa data dinga mata, da yanda dudda mijin natane mai laifi ina shiyabi Hawwa? Shi yake sonta Hawwa bata sonshi amman batai kan mijinta ba kan Hawwa tayi, ga diyata agadon asibiti rai hannun Allah Ni’ima bataji tausayin ta ba karasata takeso tayi” yayi jimm yace “Maimuna ansan mata da kishi amman naga ko kishiyan ka ce take gadon asibiti zakadan tausaya karage wani abun” Dasauri Mama tace “Malam kishi kala kala ne, akwai masu zafin kishi kafahimta” adan zafafe Baba yace “Maimuna fahimtan danayi yasa nike miki bayanin nan, koda yaran nan sun shirya madaman Aliyu na kaunar Hawwa Ni’ima bazata taba kaunar Hawwa ba duk karyace! Ni’ima tariga ta tsani Hawwa! Naga kiyayya a idanunta kibar maganan nan kawai!”.
Mshakur🥰
[9/28, 8:18 AM] +234 806 486 0007: EPISODE 4️⃣2️⃣
Rasa tacewa Mama tayi amman taki giving up ina sai inda karfinta yakare kawancen nan saisun dawo dashi, ijiyan zuciya Mama ta sauke tace “Malam duk naji bayaninka kuma banki ba hujjujinka masu karfi ne, konine naga wacce ke shirin cutar da yarana zan dakatar, amman kuma ka kalli abin ta wannan fuskan mana, ina duk ba Aliyu ne sanadi, dalili, da haddasanan fadan ba? Malam ai komi yakare yanzu, Hawwa tayi aure, babu sauran fada kuma” Baba yayi murmushi irin na manya yace “ke mace ce Maimuna bazaki taba gane yanda zuciyan maza yakeba, idan namiji ya daurama kansa soyayyan wata har abada soyayyan nan baya fita daga ransa, daukeni a misali har gobe ina matukar kaunar marigayiya mahaifiyar Hawwa, shi son gaskiya baya mutuwa, inhar Ni’ima natare da Hawwa dole zata dinga ganin dabi’u wajen mijin nata dazai dinga konamata rai daganan kishi ya motsa afara tunanin illata wani ko kisan kai, maganin kar ayi karma afara naga Ni’ima, Ni’ima taganni, ayayyafe amman adawo tare ban aminta ba, kawai ahakura Aliyu yariga yabata komi, Hawwa takamu da hawan jini hakkinane na kareta gwara ta nisanci mutanen da zasu bata matsala arayuwanta wato Ni’ima da Aliyu dan haka kiyakuri kawai Maimuna, ahakura da kawancen tunda yazo irin gabar nan, zanje nayi kari daganan naje asibiti” yayi maganan yana mikewa bayason zancen bakaramin daurewa yayi yamata maganan hankaliba amman ya tsani Ni’ima da dabi’un datayi, yarinyar ta basa tsoro baitaba sanın haka Ni’ima take ba, tashi Mama tayi dasauri tace “dan Allah Malam ayakuri, Malam kabar yaran nan sudawo tare sunason junansu Malam” dakin Umma Baba yafada Umma ta watsama Mama harara dan basa shiri sabida uwar kawar Hawwa ce rai ba dadi Mama tawuce tabar gidan.
Kari Baba yayi tareda Ramla sannan ta shirya suka fito tare wajajen 11 daidai motar Baban Yaseer na parking Baba ya tsaya turus yace “je gida Ramla natashi tafiya saina kiraki” komawa ciki tayi, Baban Yaseer yafito yazo wajen Baba cikeda mutunci suka gaisa Baba ya zauna kan kujera shikuma ya zauna a tabarma yadan sosa kai yace “Baba zan fara da baka hakuri bisa ga abinda yafaru jiya, Baba kayakuri yawancin maganganun da Ni’ima tayi na tabbatar cewa karya tama Hawwa, kowa yasan hakan ba halin Hawwa bane, Baba dan Allah kayakuri” murmushi Baba yayi yace “bakomi nahakura komi yawuce” ijiyan zuciya yasauke yace “saikuma ahhhhhmmm” yadanyi shiru yana sosa kai Baba yace “ina jinka” kanshi ya sauke kasa yace “Baba inaso kabani daman auren Hawwa! Baba ina matukar son Hawwa, namaka alkawari Baba zan kula da ita nakuma riketa amana Baba, Baba dan Allah dabi’un Niima kada su sa ka ki bani wlh Baba zan kula da Hawwa namaka alkawari babu abinda Ni’ima zata iya mata”
Ijiyan zuciya Babayasauke anatse yace “Aliyu” dagokai Aliyu yayi yakalli Baba yace “Na’am Baba” Baba yayi murmushi yace “Aliyu kai d’a nagari ne da babu iyayen dabazasuyi alfaharin samunka amatsayin d’a ba, Kanada hankali natsuwa da kirki babu wanda bazaiso yahada zumunci dakaiba” yayi shiru chan yace “Allah yana jarabtanmu da abubuwa da dama, wani zubin yana nunamana duk yanda mukakai ga son abu bamu samuba sabida banamu bane” faduwa kawai gaban Aliyu keyi Baba yace “ina sonka Aliyu sosai amman y’ata Hawwa bataka bace, jiya nadaurama Hawwa aure da Ibrahima, Hawwa tariga tazama matar wani!” Faduwa gaban Aliyu yayi dasauri yakalli Bab idanunshi har twitching suke sabida bugawan kirji yama kasa magana Baba ya lumshe idanu yabude, Baba yace “kayakuri Hawwa tayi aure, inaso kaima kaje ka gyara rayuwanku da Ni’ima, ku daidaita kanku, ku shirya ku kula da yaranku, yanzu Hawwa tafita daga tsakiya, babu wani abu dazai kara jawo muku fada, inaso naga ka koma yanda kake d’a da Ni’ima gwanin ban sha’awa, ku manta da komi acigaba da rayuwa anama juna fatan alkhairi kaji Aliyu”baki Aliyu yabude zaiyi magana saiga hawaye mai zafi sun sauko daga idanunshi dasauri yakai hannu ya share yajuyar da kai yana huci zuciyanshi na kuna yanason Hawwa sama da tunanin kanshi, waye Ibrahima? Yaushe Hawwa ta sansa? Ko sanarwan da Baba yayi sanarwa a masallaci ne yasa aka samo Ibrahima? Zafi yaji ranshi namai hawaye suka kara zubowa ya share da sauri still yakasa magana, ba karamin tausayi yabama Baba ba, kana gani kasan Aliyu na son Hawwa sosai, ahankali yace “kayakuri Aliyu, nasan yanda so yake, baya neman shawara idan zai kamaka, amman kayakuri, ka rungumi kaddara, ka gyara aurenku da Ni’ima ka rungumi iyalinka kaji” gyadama Baba kai yayi yakasa motsi Baba yayi shiru yana kallonshi yakai kusan 20min ahaka sannan yatashi muryanahi narawa sosai kaman zai fashe da kuka yace “natafi Baba” Baba ya gyadamai kai duk jikinshi yayi sanyi but this is the right thing, yawuce yatafi Baba shima yayi shiru, saida yaga barinshi unguwan ya kwalama Ramla kira suka tafi abinsu.
Da kyar cikin ikon Allah Baban Yaseer yakai gida gateman dinsu na gaidashi ko iya amsawa baiyiba yawuce yabude flat nasu yashiga yashiga bedroom nasu yazauna yafara fuzar da iska da baki sosai, hawaye masu dumi suka shiga zubomai yasan da Ni’ima duk batai haukan nan ba wlh Baba zai iya bashi Hawwa, yanzu ga shi Baba yaki, yasan rigiman Ni’ima yasa Baba yaji gwara ya aurar da Hawwa ga kowama ko wutan da Ni’ima ta kunna tamutu, iska yakara fuzarwa hawaye masu zafi suka zubomai baitaba sani rana zaizo dazaiji yanajin tsanan Ni’ima ba sai yau jiyayi ya tsaneta completely, bazaima so yaganta ba ko ya kalleta sai iya shaketa, yana ahaka wayanshi yahau ringing share fuskanshi yayi ya daga wayan Ni’ima yagani na kiranshi harta katse wayan bai daukaba tanamai kira na biyar ya daga yakai kunne baiyi magana ba, murya chan kasa tace “Baban Yaseer dama nakira nacemaka kayakuri ne da duk abubuwan dana maka natuba dan Allah let’s forget the past and move on for the sake of yaranmu” Wani kaluluwan abu Baban Yaseer yaji yana tasomai yana zuwa wuya Ni’ima tace “Babyna kaji nasan bazaka iya fushi dani for long ba please kayakuri” kasa rike abun dake wuyan nashi yayi cikin tsantsan tsana yace “bazan taba dawo dake ba, and for yarana ko da ke ko bake zasu rayu, na tsaneki Ni’ima na tsaneki da ko muryanki banso na sake ji, I hate you with everything in me, na tsaneki” yazare wayan ya katse ya jefar yazauna akasa yana dafe kanshi yashiga kurma ihu sosai kaman mahaukaci he’s so heartbroken, gateman yazo yana buga kofansu yana “Alhaji lafiya, Alhaji Alhaji”.
[9/28, 8:18 AM] +234 806 486 0007: EPISODE 4️⃣3️⃣
Ammi na zaune wuraren 11 tana duba wani littafin azkar while Hawwa na bacci sosai mai nauyin gaske taji kamshi ya daki hancinta mai dadi har saida tadago kanta ta kallo kofa Khaleel ta hango jikin kofan dago kan datayi yasa ya matsa da sauri gefe, shiru Ammi tayi saikuma ta kalli Hawwa dake bacci mai nauyi massage din yamata dadi ga drip ana samata ta lullube mata tundaga ciki har kafafu da bargo daga cikinta zuwa kai abude kanta babu dankwali tayi kyau sosai, she’s sure shine yaron jiya shine mijin Hawwa kunya yakeji ne kome? Lallai yaron kam akwai kunya yana abu saikace barawo, Ammi tayi murmushi tana tashi ta taho wajen kofan tabude tafito, Khaleel na tsaye jikin kofan yana sanye da riga da wando masu kyau milk adan hankali yace “good good morning Mom” saikuma yajuya zai tafi dasauri batare daya jira amsan Ammi ba, ahankali Ammi tace “Ibrahim” chak ya tsaya yadan juyo kanshi akasa, dan murmushi kadan tayi tace “bazaka duba matar taka ba? Dan zauna da ita nima kafafuna sunyi tsami bari nadanyi tafiya cikin asibitin kadan” kafin yayi magana ta wuce yabi Ammi da kallo saida yaga tafice sannan yajuyo ya kalli dakin kafin ahankali yabude kofan ya shiga maida kofan yayi yarufe ya tsaya jikin kofan yana kallon Hawwa dake bacci mai nauyi hakanan kawai yaji kirjinshi na bugawa sosai dum dum dum! Gently yadaga kafanshi yataka zuwa gaban gadon ya tsaya tareda folding hannu a kirji yana kallonta, she looks very sick and beautiful a hospital gown din, har lokacin akwai bandage a goshinta but an cire na hannuwanta ga ciwuka a hannu, ahankali yadaga hannunshi yakai gently yadaura kan left hand dinta wani kalan shock yaji baisan sanda yarike hannun gam ba tareda sauke ijiyan zuciya sannan ahankali yakai yatsanshi yana shafa ciwon hannun wanda yasan Ni’ima ne tamata cus yana mota data tattake mata hannu haka murya chan kasa yace “why will you love a girl this much?” Yabi hannun da kallo that felts super soft kaman hannun little Noor ga nails nata so long and white and clean looks so sexy, mirginowa Hawwa tayi kanta zai fadi daga filo dasauri yakai hannunshi yatare fuskanta yafado cikin palm dinshi tana sauke ijiyan zuciya daya huro a hand nashi cikin muryan bacci tace “Ammiiii” wani irin lankwasa kai Khaleel yayi yana kallon fuskanta dake cikin hannunshi
Her face is so damn soft, baitabajin wani excitement dan mace ta shiga jikinshi ba but right now he’s feeling so good, tsareta da idanu yayi yana kallonta ya duko a tsaye fuskanta na cikin hannunshi, kaman mai whispering yace “Hawwah!” Kar Hawwa tabude idanunta saida gabanshi yayi wani mummunan faduwa yanda take kallonshi da very very bright eyes saikuma tamaida idanun tashiga kullewa suna juyawa, muryan Baba yaji awaje dawani kalan sauri yazare hannunshi fuskan Hawwa ya kife anan kasan filo daidai Baba na bugo sallama yana shigowa tareda Ammi da Ramla dakuma wasu mata guda uku, biyu daga cikinsu goye da yara abaya daya babu yaro abayanta somehow somehow they look like Baba, Ammi ta wuce tana gyara fuskanta, Baba yace “Ibrahima kana nan? Ka kannin matarka Hawwa ku gaisa Khadija” Babban wacce ita kebin Aminu Khadija tace “ina yini Yaya Ibrahim” akunyace Khaleel ya gyadamata kai, Hafsa tace “ina yini Ya Ibrahim yamai jiki” Maryam tace “ina yini ya Ibrahim” Ramla itama tace “Ya Ibrahim ya jikin Ya Hawwa” kaman bai iya magana baisaba da mutane haka ba ana kiranshi Yaya Yaya yace “da…da sauki” yakalli Baba akunyace yace “Baba zan tafi zan dawo anjima” Baba yace “muje na takamaka” shida Baba suka wuce suka fita suna fita Khadija da Hafsat da Maryam da Ramla suka shiga tafi saikuma sukahau rawa, Hafsa tace “wlh mijin Ya Hawwa yahadu Wayyoo Allah na I’m so happy for Yaya Hawwa” Ammi tace “kunga karku tadamin yarinya da surutu” duk dariya sukayi sukahau hira.
Around 4 DIG yazo hospital din tareda Abraham da Hayatu Baba yamusu iso suka gaisa sosai, suka ijiye kudi da basket na so many goodies sannan sukama Baba sallama suka tafi.
Shima Aminu around 4 yashigo asibitin Baba yadingamai fada akanme zaibar school yazo….
Wuraren 7 Khaleel yashigo asibitin Salman na binshi da shopping na kayan kwadayi daban daban yarike hannun Noor data isheshi da maganan Hawwa ga teddy a hannunta looking so pretty sukai ciki, tundaga glass na kofan ya hango Hawwa zaune kan gado an ijiyemata table da abinci daban daban kekai Ammi na kaimata abinci abaki tana kaudakai tana yatsine fuska idanunta sun kumbura na kuka da bacci, ga Baba shima tsaye kansu suna fama dataci abinci murya chan kasa Khaleel yace “she’s such a child” dasauri Noor tace “Daddy mekace?” Kallon Noor yayi baiyi magana ba tace “Daddy let’s go inside I want to see FAA” dan ijiyan zuciya ya sauke yasa hannu yayi knocking tareda bude kofan Noor tasaki hannunshi tai ciki da gudu tace “My Fairy Angel Anty” Hawwa tadan bude idanu tana kallonta kawai Noor tahau gadon ta gefen Ammi ta tattaka tafada jikin Hawwa ta rungumeta tsamtsam da karfi Hawwa itama ta rungumeta yarinyar is freaking cute and adorable.
Baba yace “Ibrahima shigo ga wuri” yabashi plastic chair shi Baba yakoma kan dogon kujera ya sauna su Salman suna shigo suna ijiye jakunkuna suka fice ahankali Khaleel yace “ina yini Mom” murmushi Ammi tamai tace lafiya lau Ibrahim, aran Hawwa tace “Ammi na ne Mom” da sick eyes tadan kalleshi tana rungume da Noor tana mamakin meya kawo dan iskan yaron nan asibitin nan taki gaidashi, tasowa daga jikinta Noor tayi tace “FAA ya jiki? That day of accident my Dady was taking me to school I saw wat you were doing” Noor tashiga gwadama Hawwa, tace “I told my Dady, Dady yafita yadinga bin car naki da gudu he removed you from the car you were biting my Dady hand” tanuna hannun Khaleel dake zaune da sauri yajuyar da hannunshi Baba yace “aiko naga ciwon dama Hawwa ce ta jimaka?” Kin magana Khaleel yayi, Noor tace “we brought you here FAA are you fine now? U will not fall sick again ko?” Gyadamata kai Hawwa tayi ahankali tace “yes” dasauri Noor ta rungumeta tace “I love you FAA” tashi Baba yayi cikeda hikima yace “bari na karbi sako wajen mai keke” Dasauri Ammi ta tashi tace “muje na bika nafadamai abinda zai fadama Ramla” kawai suka fice.
Itama Noor dasauri tasaki Hawwa ta sauko daga gadon tai wajen Khaleel dake kallonta tace “Dady I forgot my second teddy in car I brought it for FAA” ahankali yace “meet Salman to take you” dasauri tai wajen kofa tajuyo takalli Hawwa dake binta da kallo tace “FAA I’m coming” Gyadamata kai Hawwa tayi tawuce tafita dakin yarage daga Hawwa sai shi, kafa daya yadaga yadaura kan daya yayi shiru yana kallonta, yanda Hawwa taji ajikinta ana kallonta yasa tadan juyo ta kalleshi hada ido sukayi zata ballamai harara komi daya mata nadawo mata arai, da yanda yayi attempting tabata but yanda taji shiya ceceta, plus dazu Baba nata cewa Ibrahima yakawota asibiti yabiya kudin komi da motocin data bata yasa softly da dan kyar tace “thanks” tadanyi shiru ta dai daure tasaki muryanta tace “thank you for saving my life” tasakeyin shiru ahankali tace “once nakoma aiki i will find a way to pay you back every penny daka kashe” tasakeyin shiru chan tace “all this daka kawo kasa atafi dasu banso, i hate favors barinma na mutane like you! So I will pay back everything” Murmushi kadan yayi batare dayayi magana ba wato tana sick bed still masifa take, Noor tadawo dakin ta tafi wajenta da sauri tabata teddy tace “FAA take, Dady said you will soon move to our house kikazo i will give you more and more teddy kinji” dan murmushi kadan Hawwa tamata tace “thank you beautiful Noor” tana mamaki uban me zai sake kaita gidansu dayake gayama yarsa zata” kusan 10mins yayi sannan yakalli Noor daketa zuba yace “let’s go” kiss ta manna ma Hawea tace “bye FAA” murmushi sosai Hawwa tayi tace “bye Noori” wucewa tayi wajen Khaleel yarike mata hannu sukai wajen kofa hakanan Hawwa samin kanta da kallonshi tayi, the way he walks, he way he held Noor’s hand, everything looks soo….ta tsaida tunanin, saida yakai daidai kofa ya tsaya Noor ta fita dan juyo da kanshi yayi karaf suka hada ido dasauri Hawwa ta dauke kanta, cikin dan iskan murya Khaleel yace “see you soon cry cry Kulu” dawani irin sauri Hawwa tajuyo ta kalleshi kaman zakanya, gira daya yadaga mata yace “see you very very soon Kululu” kawai yasa kai yafice daga dakin Hawwa tawani yunkuro tace “sunana Hawwa not Kulu or kulul whatever” Khaleel na jinta yayi murmushi yawuce abinsa.
[9/28, 8:18 AM] +234 806 486 0007: EPISODE 4️⃣4️⃣
Yau Hawwa ta tashi da karfinta sosai tun asuba Dr yazo yace “za’a sallameta yau but sai Ogansu Mai asibitin yazo” aka ciremata bandage na goshi da hannuwa ciwukan sun warke tanada jiki mai kyau sosai, wanka tayi tasa wani simple gown da aka kawo mata na atampa red dayamata kyau sosai, ta rame idanunta kana gani zai nuna maka tayi ciwo but takara kyau skin nata sai glowing yake na drip datasha, tun wajajen 7 Aminu yazo dan daga masallaci yazo basai Baba yazo ba daya shigo dakin Ammi bata ciki taje karbo magunguna daga pharmacy sai Hawwa dake zaune ta kishingida hannunta rikeda wayanta tana dannawa tana replying messages na DIG dasu Hayatu, ganinshi yasa ta dago kanta dasauri yayi wajen gadon yana murmushi yace “ya karfin jiki Ya Hawwa?” Murmushi kadan tamai tace “Alhamdulillah I’m fine yaushe zaka koma school why did you even come back”? Zama yayi gefenta yace “yayata that is the strongest person I know a duniyan nan tana rashin lafiya why won’t I come?” Shiru Hawwa tayi tana kallonshi tadan harareshi kadan tace “mutum sai dadin baki” dan dariya yayi yace “Ya Hawwa nasha fruits dinnan”? Gyadamai kai tayi yadauka da sauri yana sha Ammi tashigo tace “Aminu jinya kazo ko cin dadi jiyafa haka komi kuka raba naka yamafi na su Khadija” murmushi yayi yace “Ammi to nine babba” hararanshi Ammi tayi ta ijiye magungunan tace “maza gamaci mu hada komi Dr na zuwa za’a sallamemu wai” tai maganan tana mikawa Hawwa red veil nata Hawwa tasa hannu ta karba tayafa saman kanta daba dankwali, duk suna zaune har wajajen 9 wayan Hawwa dake hannun Aminu yana connecting hotspot nata danashi yahau ringing dasauri yabata wayan yace “Abraham office” hannu tasa ta karba tana kwanciya ta danna wayan tana sawa a speaker daidai lokacin ana knocking tareda turo kofan Abraham yace “Hello Miss Hawwa how are you feeling” magana kasa fita yayi daga bakin Hawwa sabida Khaleel data gani ya shigo yana sanye da labcoat ajikinshi an rubuta Dr Khaleel Mangal, ga stethoscope a wuyanshi hannunshi rike da file na Hawwa dakuma office pad da pen idanunshi kyar akanta ga Dr daya saba duba Hawwan tareda shi sai Nurses guda uku daidai Abraham yasake cewa “Hello Hawwa are you there?” Firgigit Hawwa tadan farga daga kallon Khaleel, adan rude tace “uhn” Aminu yasauka dagakan gadon cikeda murmushi yace “sannunku ina kwnan ku” gyadamai kai Khaleel yayi kanshi akasa yace “good morning Mom” kafin ta amsa yayi wajen gadon daidai lokacin Abraham yace “huhh wat a relief! I’m so glad you’re okay I’ve been so worri……” wayan Khaleel yasa hannu ya dauka tareda katsewa Aminu yadaura hannu a bakinshi yana makale dariya Ammi tadanyi murmushi kadan tace “muje waje Aminu” suka wuce suka fita, wani kalan kallo Hawwa tama Khaleel irin who gave you the authority to end my call amman mutanen data gani wajen yasa tadaure tadauke kai batai magana ba, professionally Khaleel yace “can I have your hand Mrs Lee?” Wani kallo Hawwa tamai shekeke irin is something wrong with this guys head, dayan Dr yace “Dr Khaleel she’s the patient I consulted you for kace nakara mata dosage na wannan medication din nan and BP ya sauka sosai” “hand” Khaleel yafadi fuska ahade har wani
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 35