Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
maƙasudin kiran,shima da ta miƙo masan Dad ɗin nasu ya kawo a ransa dan yasan shine kawai zai kira ta miƙo masa yana ɗagawa Dad ya hau faɗa kamar zai ari baki. "Wani irin wulaƙanci ne wannan?na aiko driver tun huɗu da rabi tararka yanzu ya dawo mun da wani zance, to wallahi sam ban yadda ba yanzu ka dawo gidanku tun kafin ranka ya ɓaci don ban yadda da raina da lafiyata 'ya'yana sui zaman agolanci ba ko Nasrin dan bana nan ne akai bikin shiyasa amman yanzu na dawo ka gaya mata ta dawo mun da 'yata tun kafin rayuka su ɓaci." "Ayi haƙuri Allah ya huci zuciya, a turo mini drivern in sha Allah zan biyo shi mu taho." "Ok ba komai Allah ya yi maka albarka, a turo address yanzu zan turo shi." "Amin, tom in sha Allah." Kana suka ajiye wayar,fuskar Momy ya Kala tana nan a yadda take bai ga alamun ɓacin rai a kanta ba ko kaɗan a fuskarta duk da yana da tabbacin taji duk abin da Daddyn ya faɗa. "Na haɗe maka abincin ka tafi da su can?" Ai kwa Momy da kin kyauta abincin yamun daɗi sosai." Ya kai ƙarshen maganar idonsa na sauka akan hoton Najwa window siz tayi masifar kyau a jikin hoton, kamar wan da aka kafe idonsa a kai haka ya dinga kallon hoton, Momy ta nufi kicthen dama ɗauko kwandon da zata jere masa abincin shiyasa ba ta lura da Son ɗin nata ba, sai da ta dawo yace. "Momy wace wannan?". Ya faɗa yana nuna hoton." "Najwa ce 'yar me gidan ce,itace ma tayi maka girkin nan." Wani murmushi ya saki cikin ransa ya furta. "Alhmdlillah na samu matar aure." Nasrin ce ta shigo da gudunta tana ƙwalla kiran "Yaaya" shiyasa ta katse musu maganar da suke da murnarta ta ɗane jikinsa shima kwa cike da ɗoki ya rungume 'yar ƙanwar tasa." "Ina Yaa El,yace mini tare zaku zo?" "Ki rabu da ni da zancen baturen yayan nan naki kamar ba a ƙasar larabawa yake zaune ba, ga tsarabar ki can jeki ki ɗauka." Ya nuna mata jerin akwatunan da aka shigo da su, ai kwa da gudu ta nufi gurin akwatinan dan hakan kawai zai mata ta rabu da shi da zancen EL mutumin da tun da ya kuma jin momy tayi aure ya kuma ɗaura gaba da nigeria, tun da da har ya fara saukowa daga fushin rabuwar Momy da Dad shiyasa ya fara zancen zuwan nasu tare. Har drivern da Daddy ya turu ɗaukar Sulaiman yazo Abba bai dawo ba,dan haka yace in sha Allah da safe zaizo su gaisa anan ma zai yi break fast, tsokanar Nasrin ya yi akan tazo su tafi tare ta maƙale kafaɗa sai kawai yaji tausayinta ya kama shi da ya tuna Daddyn yace zai karɓe ta sai yaji yana addu'a cikin ransa Allah kar ya bawa Daddyn ikon karɓar nasrin ɗin,ba don komai ba sai don ba'asan wata irin kalar rayuwa zatai a cikin gidan ba, babu Momy babu su tunda su dama ba mazauna bane. Motarsu na shiga harabar gidan nasu Daddy ya fito tare da Safiyya a gefen shi ta ɗau wanka tana taku ɗaiɗai ita ga wacce duniya ke garawa yadda take so, cike da so da ƙauna Daddy ya tari babban ɗan nasa suka rungume juna, bayan sun saki juna da Daddyn Safiya ta taho zata rungume shi yayi saurin jaa baya haɗe da jifanta da wani kallon baki da hankali? Murmushin yaƙe Dad ya yi kana yace. "Ga sabuwar momynku " yana nuna in da Safiyya ke tsaye tana rarraba ido. "Oh sannu Aunty mun yini lafiya?" Ya faɗa yana murmushin da bai kai zuci ba. itama yaƙe tayi kafin tace. "Lafiya lau, ya hanya." "Alhamdlillah" ya faɗa a taƙai ce kafin ya kalli Dad yace. "Daddy zan huta, an jima zan shigo muyi hira." Daga haka ya nufi phart ɗinsa kai tsaye. "Abinci fa?" yaji muryar Safiya ta faɗa. "A'a kar ki damu naci abinci." Yaci gaba da tafiyarsa ba tare da ya juyo ba. Taɓe baki tayi, to ita wata damuwa za tayi dan bai ci abinci ba? Dama tayi ne don ta burge mijinta dan ta fuskanci son 'ya'yansa a ƙahon zuciyarsa yake abin da ya gagara zarewa daga cikin zuciyarsa kenan dan haka sai ta tayasa sonsu ko na ganin ido ne tunda ta samu ta fitar da mahaifiyarsu daga cikin gidan. NAJWA Goma saura shiyasa muke a tsure gaba ɗaya daga ni har Gwaggon dan ganin Baffa har lokacin bai dawo ba,tuni zumuɗin cin tsire ya sake ni dan ganin Baffan shiru dan kuwa da wuya yakai bayan isha a waje, ganin goma ta gota yasa ni ɗaukan waya na kira Abba na gaya masa, yace bari to yaje can mandawarin da yace zai je ya duba ya gani. Wasa-wasa ƙaramar magana na nema ta zama babba, har ɗayan dare babu Baffa babu labarinshi duk mun ɗaga hankulanmu ranar kwa bacci tsakaninmu sai ɓarawo da ƙyar muka ga wayewar washe gari aka ɗora nemansa daga in da aka tsaya amman babu wani labari, duk an bada sanarwar cigiyarsa ko ina, amman har akai kwana uku shiru kike ji babu wani labari, duk na fita hayyacina nayi zuru zuru ba ƙaramin tashin hankali nake ciki ba na ɓatan Baffa kuka kuwa na yishi ba iyaka."Ni kenan kullum daga wannan sai wannan, na buɗi ido ba tare da ko sanin fuskar mahaifiyata nayi ba,nazo na rasa kakata a lokacin ina tsaka da jin dadinta na kuma sha azabar matar uba, ranar da aka ɗaura mini aure ranar mijina ya rasu gashi yanzu Baffa ba'a san inda yake ba har gara ace mini mutuwa yayi hankalina zai fi kwanciya." Na cewa Momy da take ta bani bakin naci abinci amman yaƙi tafiyuwa." Ba kuka da cin abinci ne zai tabbatar da soyayyar da kike musu ba addu'arki suka fi buƙata sama da komai,shi kuma Baffa in sha Allah Allah zai bayyana shi.". Haka ta dinga lallaɓa ni har sai da na ɗan ci abincin. Kwanan Baffa biyar da ɓata ulcer ta rafke ni aka ɗauke ni ranga ranga aka nufi asibiti da ni ba tare da nasan in da kaina yake ba. #Rashuna #Bebe'arth #090 37093702 Free novel ne.masu bukatar paid novel dina su same ni a layina. Katanga Cin amana Cikin Duniyarmu Halittar Zuciya [9/25, 10:49] RASHUNA: BEBEE'ARTH Wattpad@Rashuna KANA NAKA (Allah na nasa ) 14 "Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun. "Lafiya dai ko na ci muku bashi?" " Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba." "Hmm shine matsalarku?" "Eh" "To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi." "Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?" "Eh mana ɗan hannu ne." Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu. https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1 Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita. ****""""" Sai da na kwana biyu ba tare da nasan in da kaina yake ba kana na farka da daddaɗan labarin cewa an gano in da Baffa yake,ashe mota ce ta bigeshi sai da ya kwana shida ba tare da yasan in da kansa yake ba,kafin ya farfaɗo shine ya gayawa mutumin in da zai samu Abbana yazo ya gaya masa dan yasan duk in da muke muna nan hankulanmu a tashe,to shine Abbana yaje asibitin da aka kwantar da shi a take ya nemi terensfer ya dawo da shi asibitin da aka kwantar da ni. Ina farkawa Momy ke bani wannan daddaɗan labarin, ai kuwa na tashi da kuzarina tare da cewar ta rakani ɗakin da Baffan yake na ganshi, ta son samunta ne sai nayi wanka na samu ƙarfin jiki na sha ko tea ne sai muje naga Baffan,amman tasan idan ta hanani zuwa yanzun ba lallai na hanu ba,dan haka ta kamo hannuna muka fito zuwa ɗakin da Baffan yake. Ba wani ciwo yaji ba,kansa ne ya bugu sosai shiyasa ya wahala sosai,amman yanzu an shawo kan matsalar dan gashi har magana yana samu ya yi.Ina ganinsa na faɗa jikinsa sai kuka yasa hannusa yana shafa kaina haɗe da cewa. "Haba Amaryata ke da na sanki jaruma meye kuma na kukan?Ko so kike na janye Gwaggonki ta samu abun yi?" Ɗagowa na yi ina share hawayena kafin nace. "Baffa kukan murnane, ya jikin naka?" "Da sauƙi ya naki jikin?" "Alhmdlillah." "To masha Allah,ciwo dai ya ƙare tun da ga Baffa ya dawo da ransa ko." Dariya nayi kafin nace."Sosai ma,daman ciwon na rashin ganinka ne,ni dama zasu taimaka su sallame ni yanzu wallahi naje gida na ɗumamo maka tuwonka dan yana nan a fridge na saka maka dan dama jikina ya bani zaka dawo gare mu." "Ai idan suka bincika komai naki lafiya lau zasu iya sallamarki a yau ɗin.amman tuwo Gwaggonki ta rigaki kawo mini,tun da aka bada umarnin na fara cin abinci nace tuwo nake so shine tace aikuwa akwai wan da kika ajiye min dan haka saura nawa biyan bashin na tsire da Rufaidah." Da saurina nace. "A'a Baffa na yafe wannan tsiren." "Kwantar da hankalinki ba ni zanje ba har nan asibitin za'a kawo mana shi da daddare." Murmushi nayi tare da tsallaen murna Kafin naji muryar Gwaggo na cewa. "Daina murna babu wani tsire da zaki ci ke da ke fama da ulcer."Kwakkwaɓe fuska nayi kamar zan kuka Baffa yace."Kada ki ɓata hawayenki a banza tsire dai kam sai kin ci shi, haka kawai a dunga lanƙayawa mutane ciwo ace kar su ci abu, me ya koro ɗan ƙauye birni?ina to ba zaƙi da maiƙo bane haka kawai wani likita ba Allah ba ya hana amaryata ci." Murmushi nayi jin furucin Baffa, Gwaggo kuwa bakinta ta ja tayi shiru dan wannan rigimamman tsohon ba ta da ƙarfin jaa da shi in dai akan Najwa ne,domin kuwa ko ta jaa dole ta saki amman idan ciwon Najwan ya tashi yafi kowa tayar da hankalinsa. Momy kuwa cewa tayi na taso naje nai wanka na samu na ci wani abun,kafin likita yazo ya duba ni, muna shirin fita Abba ya shigo dan haka sai da na tsaya muka gaisa kafin mu tafi zuwa nawa ɗakin da aka kwantar da ni. """""" Da daddare muna ɗakin da Baffa yake gaba ɗayanmu har Abbana, tsiren da aka kawo da zafinsa muke ci ni da Baffa muna korawa da Rufaidah,nikam gurin kitse kitsen nake zaƙulowa na ci,idan ma ban gani ba Baffa sai ya sako mini a gabana,shiyasa dama na gudo nan dan muci tare,dan nasan a can wa'yannan nurses ɗin baza su barni naci ba. Ƙofar ɗakin aka buɗe aka shigo ɗauke da sallama wacce ta saka ni ɗaga ido naga me wannan sallamar caraf kuwa sai idona cikin nasa, ganin ban san shi ba sai na ɗauke nawa idon daga kansa,ganin yadda kowa ke sakan masa murmushi,shi kuma yana binsu ɗaya bayan ɗaya yana gaisarwa,haka ma suka gaisa da Baffa cike da ƙauna yana tambayarsa jikinsa, Baffan kuma ke ce masa baya gajiya ganin ledojin da wani ya shigo da su ya ajiyesu hakan sai naji yana ƙaryata tunanin da nai akan ko likitan da ke duba Baffa ne? Baffa ne ya fitar da ni daga tunanin nawa ta hanyar cewa. "Najwa ga Yayanki nan Sulaiman ɗan wajen Momynki Hasiya." Kallonsa na kuma yi a gain dai idanuwanmu suka kuma gaurayewa guri ɗaya, alamu ke nan idonsa a kaina yake.Naiver shiyasa naga yana ɗibar mini kamanni da Yaa Muhd mai makon na gaishe shi sai na mayar da idanuwana kan Momy nace. "Momy to ina EL MU'AZZ?" Ganin yadda idanuwa suka yo kaina gaba ɗaya yasa na gane aikin da na ɗebowa kaina to me ya kaini wannan tambayar? Na rasa me yasa tun da Nauwwa ta bani labarinsu sunan ya tsaya mini a zuciyata na kuma zaƙu da son ganin mamallakin sunan. "Dama kin san shi ne?" Momy ta jefo mini tambayar. "Um um Nauwwa ce dai ta bani labarinsu ta kuma ce EL MU'AZZ suna ɗiban kamanni da Yaa Muhd sosai." na faɗi hakan dan wanke zargi kawai ba wai dan hakan Nauwwan ta gaya mini ba." "Ai kuwa Nauwra ba ta san kamanni ba, Son shi ke kama da Muhd sosai ba MU'AZZ da ko hanyar kama ba su haɗa ba." Mayar da idanuwana nayi kan fuskarsa har lokacin idanuwansa suna kaina nima kuwa na hau ƙare masa kallo duk da yadda naji yanayin jikina na sauyawa saboda irin kallon da yake mini,ga gabana da ke ta faduwa bazai wuce nasaba da fuskar Yaa Muhd da nake gani cikin tasa ba. Tabbas suna kama da Yaa Muhd, wani ma zai iya rantsuwar uwa ɗaya ce ta haife su." Cikin rawar harshen da na tsinci kaina a ciki na furta masa. "Ina yini?" Ko zan samu tsagaitawar wannan kallon da yake mini. "Lafiya lau,ya jikin naki?" Ya faɗa da wani karyayyan harshe. "Alhmdlillah" Nace ina kautar da kaina gefe dan wannan kallon nasa kuma ya ishan. Muryarsa na tsinkaya yana cewa Momy zai huce cikin raina nace."Ai gara ka wuce ɗin ko na huta da wannan kallon naka." Sai kuma naga sun fita tare da Mom ɗin bayan yaiwa su Abba sallama da neman karin lafiya ga Baffa. SULAIMAN Ganin da ya yi mata a sarari sai yaga ta fi kyau akan a hoton, har cikin zuciyarsa yake jin cewa tabbas ya samu matar aure, domin kuwa sonta da ƙaunarta ba su shigesa da sauƙi ba a tun san da ya fara sauke idanuwansa akan hotonta. "Momy nikam na samu matar aure." "To Alhmdlillah,a ina ɗiyar tawa take?" "Najjwa ce Mom ina sonta sosai." Ya faɗa haɗe da danne saitin da zuciyarsa take, sororo Mom tayi tana kallonsa,tabbas tana matuƙar sha'awar Najwa ta zamo sirikarta, amman ba Sulaiman take wa sha'awarta ba MU'AZZ ne dan ta yankewa ranta duk ranar da ya sako ƙafarsa garin nan bazai koma ba sai da auran Najwa,zata roƙi Abba alfarmar ya ɗaura aurensu tasan bazai ƙi yi mata ba,Najwan ce tarkon da take ƙoƙarin jefawa MU'AZZ ko zata ƙwato shi daga hannun yahudawan mutanan can da ya jefa kansa a ciki,sai kuma gashi Sulaiman yazo da batun son Najwan wan da tasan tun da ya furta to hakanne a zuciyarsa don sam bashi da zurfin ciki ko nuƙu nuƙu irin na MU'AZZ shi ɗan kai tsaye ne baya barin abu ya cuceshi idan har yana so a cikin ransa. Maganar Sulaiman ɗince ta katseta daga tunanin da take. "Mom ko wani ya riga ni ne?" "A'a sai dai kuma itace Muhd ya aura wan da ranar auran nasu ne ya rasu." "Ayya ai jiya munje da Nasrin nai musu ta'aziya. Yauwa maganar Nasrin ɗin kwa nake so muyi Daddy ke ƙoƙarin shigar da ƙara kan sai kin bashi 'yarsa da ƙyar na samu dai ya haƙura akan nan da wata uku in sha Allah zata komo na yi hakanne don kafin lokacin in sha Allah naje haɗo komai nawa na dawo don so nake na dawo ƙasata itama na hidimta mata ina kuma saka ran kafin lokacin kema in sha Allah kin sauka." Maganarsa ta ƙarshe ce ta rufe bakin Momy ruf dan magana take shirin yi,ashe duk ɓoyen da takewa cikin nan sai da yaron nan ya gano shi? kenan kowa ma yasan da ciki a jikinta abin da take ta ɓoyewa da tsoron a sani goɗai goɗai da ita tsakani da Allah a wani ce tana da ciki? abin da har suruka ne da ita banda sun ƙi haihuwa ta tabbata da tuni tana da jikoki, shi kuwa Abba ba ruwansa murna ya dunga yi da kyautar da Allah yayi masa bayan ya cire rai da samun wasu 'ya'yan tun daga kan su Najwa sai gashi kuma Allah zai nufe shi da samun wani ba dole yayi murna da farin ciki ba? Juyawa Momy kawai tayi ta tafi ta barshi a gurin a tsayen yayin da ya saki murmushi dan yasan abin da yasa Momyn tafiya ta barsa,to ya zasuyi da hukuncin Ubangiji?Babu babu yadda za su yi da shi domin kuwa ya tabbata rabon wannan cikin ne ya fito da Momyn tasu daga gidansu,shiyasa har Safiya ma ta samu dama akan Daddyn nasu..... [9/25, 10:49] RASHUNA: BEBEE'ARTH Wattpad@Rashuna KANA NAKA (Allah na nasa ) 15 "Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun. "Lafiya dai ko na ci muku bashi?" " Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba." "Hmm shine matsalarku?" "Eh" "To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi." "Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?" "Eh mana ɗan hannu ne." Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu. https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1 Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita. ****""""" Ba shiri likita ya sallamemu don ganin yadda muka mayar masa da asibiti dandalin party,tun safe idan nai wanka nake gudowa ɗakin Baffa anan za'a haɗu gaba ɗaya ai ta shan shafta da dirama kala-kala da daddare kuma ayi phartyn tsire da youghurt na Rufaida ko L nd Z, ɗaki ɗaki haka zamu bi mu raba musu duk da suma ba su fi ƙarfinsu ba haka zasui ta murna da farin ciki,wan da hakan ya janyo mana shaƙuwa da wasu sukan zo ɗakin Baffan suma ai ta shan diramar da su ana kwasar dariya ganin haka yasa ya tattara mu gaba ɗaya ya sallame mu tun da dukkaninmu babu wata matsala da tai saura, har gara Baffa ma tun da yace zai cigaba da zuwa gida yana dubasa. Ba ƙaramin kai ruwa rana akai ba kafin Baffa ya amunce mu koma gidan Abbana da zama, domin kuwa phart biyu ne a cikin gidan wan da ya gina shi da burin iyayansa su zauna a ciki amman Baffa ya kafe yaƙi yadda sai yanzu aka samu aka shawo kansa ya amunce muka koma, Momy sai murna take da farin ciki, a zaman asibitin da nayi na ƙara gasgata so da ƙaunar da matar nan ke mini, haka ta tattaro tazo tayi ta ɗawainiya da ni har aka sallame mu. Duk ɓoyen cikin da take sai da na gano na dunga murna da farin-cikin nima zan samu 'yan uwa wan da har na kasa shiru sai da na fesawa Baffa da Gwaggo suka ce tun kan na gani suka gani sun barta ne taci gaba da ɓoyenta san da ta haife cikin ai ba ta isa ta ɓoye mana ba, duk da sun san nauyi da kunya ne yake saka Momyn ɓoyen cikin ban da abinta mutum ai bai isa ya ja da ikon Allah ba,wannan rabon shine ya kawota cikin zuri'armu. """""" Muna zaune a perllow ni da mommy ina dan danna mata ƙafarta data kunbura saboda cikinta da ya tsufa ina tai mata sannu sai ga Yaa Sulaiman ya shigo sai ƙamshi yake sanye yake da jus baƙi da farar riga fuskar nan tashi tai fresh ya ƙaraso ya tsugunna ya gaida mommy nima na gaidashi da murmushi a fuskarsa ya amsa yana bina da wannan kallon nasa da a yanzu na fara sabawa da shi, nace "Ina Nasrin?" Da yake bayan komowarmu gidan nan Mommy tace Yaa Sulaman ɗin ya mayar da Nasrin gidan mahaifin nata,Allah yana tare da ita addu'arta kuma za ta yi ta bibiyarta. Yace "Tana makaranta" Waya tace tai ringing na ɗaukota sai naga nauwara ce na ɗaga haɗe da sallama tace "Ki maza ki shigo makaranta Gadanya zai yi test." Nace "To ganinan" " Mommy nauwara ce Gadanya ne zai mana test tace na shigo makaranta."Tace "To maza tashi ki tafi mana tunda a shiryenki kike."Na miƙe na shiga ɗakina na sashen na ɗaukko mayafi da takalmi da jaka na fesa turaruka na ɗaukko key ɗin motata na futa nace "Mommy na tafi"Tace "To Allah ya kiyaye sai kin dawo" Na amsa da "Amin" Sai da na fara shiga gurin su Gwaggo nai musu sallama Baffa ya bani sautin rogo da gyaɗa kana na fito, har na shiga Mota zan tayar Yaa Sulaiman ya dakatar da ni ranƙwafowa yayi ta saitin da nake da murmushi a fuskarsa yana bin fuskata da wannan mayen kallon nasa yace "Za'a iya ragemin hanya?" Nai murmushi kafin nace. "Me zai hana kuwa?" Bai ce komai ba ya zaga ɗaya ɓarin ya buɗe motar ya shigo na jata muka ɗau hanya muna tafiya shiru ba wanda yayi magana na juyo na kalleshi idanunshi a lumshe nace. "Yaa ina zan saukeka?" " Nima makarantar zani" Ganin ina kallonsa da neman ƙarin bayana sai ya lumshe idanuwansa ya buɗe cikin karyayyar muryashi yace. "Aran motar zaki bani kan ku gama test ɗin" na dawo na ɗaukeki." Ban magana ba har muka isa nai parking a in da ɗalibai ke ajiye abin hawansu daidai Nauwara ita ma ta ƙa raso muka futo a tare ta ƙaraso gurinmu tana dariya tace "Sai gashi kuma munzo tare" Nace "Ehh ke da kika sanar dani ba, ni na zata ma kina makarantar." Tace "Ina fa a group na gani, na sanki chart ba damun ki ya yi ba shiyasa na sanar miki." Yaya Sulaiman ne ya fito daga motar yace "Su Nauwara manya." tace "Ashe tare kuke?"Yace "Ehh tare muke da gimbiya ta." tace "Ai ni fa fushi nake da kai tunda kazo bakazo gidana ba." yace "Ai ba ni zaki tuhuma ba ƙawarki zaki tuhuma tunda laifinta ne itace ba ta rakoni ba." tace "Kai ai bana

Chapter 5 of 17