Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a samo twince ɗin 'yan maka." Harara na galla Mata Kafin nace. "KO an gamun zan roƙa Allah ya inganta mana ya kuma saka twince ne." "To idan kin tashi ki roƙa mana duka." Ban tsaya bata amsa ba sakamakon Yaa Sulaiman da ya jaa hannuna ashe ana ta kiran sunan passingers, sai hannu kawai na ɗago musu muka nufi in da jirgin yake. Takwas na dare daidai jirginmu ya sauka a filin hawa da sauka na jiragen Madinah. Mota muka hau ta sauke mu a Hotel mafi kusa da masallacin Annabi Muhammad (S.A.W). Rashin sa'ar da aka samu ɗaki ɗaya ya rage kuma falle ɗaya ba kamar yadda yaso samun falle ɗaiɗai ko ciki da falo ba. Abinci ya fara zama ci,nikam toilet na shiga nayo shirin baccina na gabatar da sallar isha'i a ciki,har Yau dai ban fara gabatar da sallar shafa'i da wutiri ba, da na fara sai na daina nazo nace kuma sai nayi aure zan fara, amman in sha Allah ina nan zan tsayar da ita domin dacewa da gwaggaban lada, na dai samu na tsayar da yin walaha, Ina idar da sallar nazo na haye gado idanuwana cike da bacci. "Babu abin da zaki ci ne?" "Uhmmm ban jin yunwa." Na faɗi hakan idanuwana a lumshe. "A'a ki dai daure kisa wa cikin naki wani abun." "Allah da gaske nake ba na jin yunwa." "OK" Yace,ya na tashi ya shiga toilet, wanka ya yo ya shirya a ciki shima kana ya fito Cikin tunani da taraddadin ta yadda yau zai iya bacci a ɗaki ɗaya da wani. Sallaya ya shimfiɗa ya tayar da sallar isha'i kafin ya ɗora da shafa'i da wutiri. Cikin dare sau kusan biyu ina farkawa Ina ganinshi a zaune,a farkawa na u kun ne na tambaye shi me yasa bai yi bacci ba yace da ni ya kasa nace. "To saboda me?" Yace. "Tun ina yaro ba na iya bacci idan da wani a ɗakin da nake,da baccin ya ɗauke ni nake farkawa." "Allah buwayi, bara na ɗauro auwala muyi sallah nima baccin ya sake ni." DA na ganni a tsakiyar Rauda kuka na fashe da shi,ina shafa kabarin Manzo (S.A.W)(Madinah garin manzo Allah kA kiramu wannan gari Naka dan darajar manzon Allah SAW dan kaunar DA ke tsakaninku Amin ya Rabbi. ) Mun zaga garin madinah sosai,mun kuma yi ibada yadda ya kamata,tun washe garin da muka kwana a garin ya sama mana wani ɗakin ciki da falo ya bar mini cikin shi yake kwana a falon,zamu yini mukai dare tare idan anzo bacci kuma kowa ya kama tasharsa. Satinmu guda a madina muka nufi mikati domin ɗaukar haramar yin Umara,kowa ya fito cikin haraminsa kana muka nufi garin makkah adduo'i dauke a bakunanmu. Yaa Sulaiman dama ya riga ya kama mana ɗaki ta online,a hotel mafi kusa da masjidul Haram,falo ne ƙaton gaske da two bed rooms a ciki,kayanmu kawai muka a jiye muka juya masjidul haram. Da addu'a a bakunanmu muka shiga gurin da yake da matuƙar haske da ni'ima,gurin da yake sanyaya rai da zuciya. Sai da na zubar da ƙwalla tsabar farin cikin yau gani ga ka'aba.Muka hau ɗawafi kowa yana kai kukansa gurin da za'a share masa a biya masa bukataun da ya roƙa har da ƙari.Bayan mun gama muka gabatar da nafila raka'a biyu a bayan muƙamu Ibrahim Sannan muka wuce yin sa'ayi,bayan an gama mazanmu da matanmu muka cike ibadarmu da yanke gwargwadon abin da shari'a ta lamunce mana. Washe gari ya Kira Mu'azz yazo ya ɗauke mu zuwa gidan da suke zaune,kallo ɗaya nayi masa ban ƙara kallonsa ba sabo da yadda zuciyata ta dinga bugawa saboda tsananin kyaun da naga ya ƙara fatarsa ta ƙAra gogewaa,zuciyata ta dinga buga tsalle a kirjina saboda kasancewarmu guri guda nidai ina ta ta'awwizu har muka ƙarasa gidan. Plart ne guda biyu,kowa da nasa,ya anshi key a hannun Mu'azz din ya bude nasa plart din muka shiga,ina ji yana tambayarsa Zareenah yace tana india yin wani course. Falo ne ƙato sai two bed rooms a ciki,ko ina fes fes da shi da alamu a kwai masu gyaransa a ko da yaushe. Ina ganin ya buɗe ɗaya ɗakin ya shiga ciki nima na buɗe ɗayan na shiga idanuwana cike da bacci,da ƙyar na samu na sauya kaya zuwa sasasauƙar doguwar riga ta bacci na kwanta. Baccina yayi nisa na ji kwanciyar mutum a jikina a ɗan razane na wara idanuwana suka sauka akan Yaa Sulaiman,gira ya ɗage mini haɗe da sakin murmushi Kafin yace. "Ai kin gama cin bashin naki yarinya,biya kawai ya rage miki." Gabana ne ya faɗi cikin in inar da ta same ni a yanzu nace. "Ban ga ne ba." "Zaki gane ne." Ya faɗa yana shinshinar wuyana,kafin ya cirani cak ya nufi ɗakinsa da ni,sai da ya sauke ni kan tattausan faffaɗan gadonsa kana yace. "Na ci burin karɓar budurcin matata a wannan gadon,na kuma roƙi Allah yasa zuwan farko na zira ƙwallona a raga." Sunkui da kaina nayi cike da kunya,har lokacin ƙirjina na dakan lugude cike da tsoro da taraddadin yadda wannan al'amari zai kasance. "Ki fa daina tsoro dan yau babu abin da zai tsayar da ni,dan hakurina ya riga ya kare." Ya faɗa yana shinshinar wuyana tare da shafa dukkan wani sassa na jikina,nikam ban da kyarma babu abin da jikina yake. Bakinsa ya tsayar akan nawa kamar zai yi kissing ɗina sai kuma ya dakata ya ɗago ya kalle ni idanuwanmu suka gauraya guri guda,ban da tsoro babu abin da ya gano cikin nawa idon,shikam fitina ce kala kala na hanga cikin nasa idanuwan. "Kema kina son wannan abun ne?" Da sauri na girgiza masa kaina saboda tsabar yadda nake a tsorace ina jinsa ya sauke ajiyar zuciya da alamu bai ma san yana riƙe da ita ba kafin yace. "Na jima ina roƙon Allah ya bani matar da wannan abin bai dame ta ba, dan nikam a ƙazanta na ɗauke shi,da kuma al'adun turawa da muka ɗauka muka aza bisa kawunanmu, dan nidai in kika cire wannan kiss ɗin." Ya manna min kiss akan laɓɓana da kumatuna da goshina kafin yaci gaba. "Babu wani kiss da zan yi bayan shi,wai naga ashe kiss ɗinma kala kala ne ko wanne da sunansa ko?" Ƙasa na kuma yi da kaina ba tare da na ba shi amsa ba,to nace masa me? Ya barni ma da tsoron da ke ƙara shigata a ko wani second. A hankula ya bi da ni cikin lallashi da lallamawa kafin akai in da notinan kansa suka kwance gaba ɗaya,ya manta kansa bare ma ya tuna da cewa farin shiga ce ni a yau yau ɗin nan zan san wannan al'amari me girma. Na jigatu babu ƙarya bayan ya gama sauke mini buƙatunsa na shekaru da dama tun daga ranar da ya fara balaga,ƙirjina,cinyoyina da gurin gaba ɗaya raɗaɗi suke mini,yadda Nauwwa ta bani labari ba haka na ji ba,tace wlh ita duk yadda ake zuzuta azabar daren farko ba haka ta ji ba, kawai ya danganta da yadda namiji ya jewa mace,wasu mazan sukan yiwa mace zuwa ɗaya ne,wasu kuma sukan yi kwanaki ana buɗa gurin a hankula wananna kam sune baza su ɗorar da wahalarsa ba tun da an raba musu zafin ba na lokaci guda aka musu ba amman fa wannan sai maza masu haƙuri irin Najib ɗin Nauwwa,Amman yadda ake faɗarsa a novel ban taɓa ji ko ganin haka a gaske ba,dan nikam har yau ban taɓa ganin wacce ta suma ba a daren farkonta sai a novel. Shi ya haɗa mini ruwa me zafi ya taimaka mini na tsarkake jikina,na gasa shi sosai yadda ya kamata,bayan na gama tsane jikina na saka wata sassauƙar rigar baccin ina ƙoƙarin kwanciya ya shi go riƙe da mug sai tiriri yake. Shayi ne haɗin kauri,ya san ni da son murtuk ɗin shayi shiyasa yamin irin haɗin ba musu na ansa na fara sha a hankula,yana zaune yana ta kallona har na gama sha,ya bani magani na sha wan da zan ji sauƙin jikina kana na kwanta ya sauke mini pick a kumatu. "Allah yayi miki albarka, Allah kuma yasa na yi babban dashe me albarka a mahaifarki, tabbas da ace mata da yawa sun san kima da mutumcin da martabar da suke in sun kawo wa mazansu budurcinsu da da yawansu ba su wasarere da shi ba,ba su bayar da shi a banza ba,gurin da ba'a san daraja da mutumcinsa ba.Ke dai kam babu abin da zance da ke,sai dai Allah ya jiƙan Ummanmu ya kai lada kabarinta,ya ƙarawa Abbanmu da Baffanmu lafiya da tsayin rai me amfani yayi musu sakamako da gidan aljanna." "Amin." Nace ina matuƙar jin daɗin addu'arsa har cikin raina. To ban da abin wasu matan ma, ni banga abin daɗi a wannan abun ba ban da wahala da har zan bayar da kaina a banza ba,Allah na gode maka da ka tsare mini mutumcina ka nufe ni da kawowa mijina shi har na samu tukuicin add u'a wa iyayena. Sati biyu muka ƙara ya na gwangwaje amarcinsa kafin mu nufi sieria can dangin Mamana. A sati biyun da muka yi tun ranar da Mu'azz ya sauke mu ban ƙara sanya shi a idanuwana ba,ba ya shigowa idan ma magana zasu yi sai dai su haɗu a waje,lokacin kuma da zamu fita baya nan yana asibiti har mu dawo,wani zubin ma a can asibitin yake kwana,sai a ranar da jirginmu zai tashi zuwa sieria ya kaimu airport. Ya na tsaye jikin motarsa muka fito,idanuwanmu suka sarƙe guri guda,yayin da ya lumshe nasa idanuwan ya kuma warasu cikin nawa idon,nikam kamar wani magnent na kasa cire nawa idon daga cikin nasa duk da yadda zuciyata ke buga tsalle a ƙirjina,sai da ƙyar na yakice su daga kansa saboda yadda muke ƙara kusanto gaban motar. Yayin da nake ta faɗin. "Astagfirillah Allah ka yafe mini,ba laifina ba ne laifin zuciyata ne,Allah kar ka bata ikon sarrafa ni a ko da yaushe,ka ɗorani a kanta kasa kuma na fi ƙarfinta Amin." Sai da muka ɗauki hanya muna tafiya ya dubi Yaa Sulaiman yace. "Na rasa me na yiwa matarka Bro ba ta kula ni." Kallona Yaa Sulaiman yayi cike da tuhuma,na numfasa nace. "Allah Man." Sunan da nake kiransa kenan yanzu da ya titsiyeni da sai na daina kiransa da Yaa Sulaiman, nace zan dinga kiransa da MAN yayi masa? yace "Eh to ba laifi." Nace."Be yi ba kenan a sauya?" "A'a yayi mana matar Man" Ya faɗa haɗe da jan karan hancina. "Idan aka gaishe shi ba ya amsawa." Na ƙarasa maganata,kallonsa Yaa Sulaiman yayi kana yace. "To ka ji laifinka." "To shikenan mutum idan yayi abu sau ɗaya ko da yaushe hakann ne zata kasance?" Saboda kawai na tsagaita maganar nace da shi. "Ina yini?" Saboda ni kaɗai nasan yadda Accenrt din muryarsa ke ragargaza zuciyata,bacin haka sau nawa zanga su Zuwaire na gaishe shi sai dai ya ɗauke kai kawai idan ni yayi mini sau ɗaya? "Ki bar gaisuwar ki yanzu saboda ni na roƙa ki barta sai haɗuwarmu ta gaba." Daga haka babu wan ya sake cewa komai har muka isa airport ɗin,sai muryar Man da ke ta shi a cikin motar yana amsa wayar Miqdad abokin aikinsa. Su Inna da Kawu sun yi matuƙar farin cikin ganinmu,har suka rasa in da zasu sakamu tsabar murna da farin ciki,kwananmu uku,duk gurin da ya kamata muje munje Man yayi musu alkhairi me girma.A ranar da muka sauka hotel ya so kama mana,Inna tace sam ba wannan zancan ga wadataccen muhalli babu wani hotel da zamu tafi. Ɗaki ne guda me kyau da tsari aka bawa Man,duk da Inna ta so korani gurinsa a ranar nace mata ai ba ya iya bacci da wani a kusa da shi,tace. "Ikon Allah,Allah buwayi kenan, me halittar bayinsa kala-kala." Tun daga ranar muke kwana tare da ita,mu raba dare muna hira tana bani labarin mahaifiyata,ƙuruciyarta da komai nata da yadda take matuƙar son iyayanta da 'yan uwanta,har zuwa yau da muka yi sallama da su zamu tafi cike da kewa. Man yayi musu alkhairi sosai,haka nima na basu abin da ke hannuna,suma suka haɗo mu da tsaraba rigijib muka rabu cike da kewar juna. A abuja muka sauka,ya koma bakin aikinsa,watanmu uku a can na matsa masa da ni gida nake son zuwa,gashi a lokacin shi kuma yana tsaka da aiki dan yana da marasa lafiya sosai,da ya gaji da nacina haka ya sako ni a jirgi,kafin ya samu sauƙin abubuwa ya biyo bayana,duk da yadda yake jin zai yi mugun kewata musamman ta fannin abinci,dan shi kam ba me yawan buƙata ba ne,nima kuma a lokacin ba sanin kan abun nayi ba,duk tsayin lokacin da zai ɗauka kafin ya nemi ni ba damuwata ba ce,dan a wahala na ɗauki abun da takurawa. Idan kuka ga Yaa Sulaiman a yanzu ba za ku gane shi ba,ya canja sosai yayi ƙiba jikinsa ya buɗe tun a wata rana da muna kallo nace mishi ina son namiji me buɗaɗɗan jiki,ma'ana namiji me ƙarfaffan jiki,irin aftawan indiya da zakuga jikinsu ya buɗe sosai,duk da shi ba me ra'ayin ɗaga ƙarfe ba ne amman da jin wannan magana tawa sai gani na yi ana shigo da kayan motsa jiki cikin gida,ɗaki guda ya ware aka danƙaresu kala kala masu kyau da tsari na zamani,sai gashi lokaci guda jikinsa ya fara wani irin buɗewa ya ƙAra fito da cikar zatinsa da ilhama. A zaman wata huɗun nan da muka yi da Man,bazan iya cewa ga wani abu da yayi mini na bacin rai ba,duk abin da na nuna ina so ko ba ya so zai yi mi ni,zai takura kansa ni ya faranta mi ni,duk da ance sai zama yayi zama ake gane halin juna amman ina da yaƙinin Man a ko da yaushe zai yi kokawa da ɓacin raina,mutum ne simple ga daɗin zama kamar yadda Momy ta taɓa faɗa mi ni. Kamar laulayi jirana yake na sauka kano ya sako ni a gaba,na fara wani irin azababban laulayi,in da Allah ya taimake ni a gidanmu na sauka,nan Gwaggo da Momy suka shiga kula da ni,tamkar su cire mini ciwon su mayar jikkunan su,musamman da result ya fito na asibiti cewar ina ɗauke da juna biyu har na tsayin wata uku,murna da farin ciki gurin su ba'a magana.Man sai da ya zo yayi kwana ɗaya ya koma saboda ayyuka sun haɗar masa,farin ciki kuwa ba sai an tona zuciyarsa ba kamar ya ɗauke ni ya haɗiye ni tare da abin da ke cikina ya ke ji,Allah ya cika mishi burinsa ya dasa mishi ƙwansa a mahaifar Najjwa za ta haifa masa jininsa shima zai ga jininsa kamar yadda yake tsananin buri da fata. Yau da lafiya gobe babu,na yi sati a asibiti na yi sati a gida,duk na bi na ƙare ba na ce na lalace ba,saboda fatata a murje take,tayi wani irin kyau ta na sheƙi a haka dai aka gurgura har cikina yayi wata bakwai kana na samu lafiya,ko da yaushe Man ya na hanya,idan yazo ya ganni sai ya koma,wani zubin ya kwana wani zubin kuma a ranar yake juyawa,har sai da Abba ya hau shi da faɗan sintirin da yake ya yi yawa ya je ya mayar da hankalinsa kan aikinsa tun da anan ɗin ga su dukkaninsu a kaina ana samun laulayin nawa yayi sauƙi zan komo Abujar amman duk da haka Man ya kasa jurewa kullum cikin kiran waya amman sai ya mayar da zuwan nasa duk sati. Ga Daddynsu shima a tsaye yake a kaina,duk wani faɗi tashi na laulayin cikin da nake da shi ake yi,duk wani abu na kwaɗayi da sha'awa na masu ciki ya na kan hanyar kawo mi ni,wani zubin sai dai kawai na ji ya kira wayata akan na aiko a karɓo mi ni abu kaza gashi a ƙofar gida,idan jikina da ƙwari na taka da kaina naje na anso,idan kuma ba ƙwari sai na tura a karɓo mi ni. Kamar yau da ya kirani cewar ga shi a bakin gate na turo a amsar mi ni saƙona,kasancewar jikin nawa da ƙwari yasa na saka hijabi na fita da kaina,don mu gaisa,dan nasan shi kansa zai fi son na fito da kaina dan yaga yanayin jikin nawa ko hankalinsa ya nutsu guri guda,ba shi da wani buri da fata da ya wuce ganin fitowar jikan nan nasa lafiya,jikan da yake jin babu wani wan da zai zo daga baya da zai kai shi ko ya kamo shi ko kuma ya zarta shi a zuciyarsa. Shi ko Daddy tare su ke da Safiyya sun je dubo mahaifinta ba shi da lafiya,shine ya biyo da su nan domin ya bawa Najwa saƙon gashin kazar da ya san ta na matuƙar so da ƙauna a fara wannan laulayin nata,haɗe da tatacciyar madara me sanyi da garɗi. Tun tsaiwarsu a bakin gate ɗin gidan Safi ya ke bin gidan da kallo,a kyau da tsari da girman gidan sai dai su zo ɗaya da wan da take ciki ba dai wani ya fi wani ba,tana cikin ƙarewa gidan kallo Najjwa ta fito tinƙis tinƙis cikin tafiyar masu ciki,gabanta ne ya yanke ya faɗi kafin wani irin yanayi ya dabaibayeta muryar bokan da taje gurinsa ne ya faɗo mata a rai,ko kuma tace matsafi don da haka ya dace ba boka ba. "Zai aureki,za kuma ki mallakeshi har ki samu nasarar fitar da uwar gidansa daga gidan,ta hanyar abu guda ɗaya da muke buƙata daga gareki ba tare da ko sisin ki ba." A lokacin idonta ya rufe,zuciya da ruhinta sun cika da so da ƙaunar ɗan mutan Fanda,ba ta da wani buri da ya wuce na auransa ko ta halin ƙaƙa,sonsa take ƙaunarsa ta ke dan haka ba ta damu da abin da za ta rasa ba muddun zai aureta ta kuma rayu da shi muddun rai. Dan haka ta matuƙar ƙagauta ta ji me wannan matsafin ke buƙata a gareta,duk girman abun duk kuma illar da zai yi mata daga baya zata bayar muddun dai zata rayu inuwa guda da ɗan mutan Fanda. "Mahaifarki muke buƙata,bi ma'ana babu haihuwa tsakaninku da Aliyu Fanda." Matsafin ya gaya mata haka bayan ta uzzura masa da son jin abin da su ke buƙata a gurinta. Ajiyar zuciya ta sauke wacce ba ma ta san tana riƙe da ita ba,bayan jin a bin da suke buƙata a gurinta,ashe abinma me sauƙi ne,ita ba haihuwa ko tarin dukiya zai kaita gidan Aliyu Fanda ba sai zallar so da ƙauna,ƙaunar da ba ta taɓa tsintar kanta cikin yiwa wani ba sai a kansa,ba ma ta san cewar akwai buƙatar ɗa namiji a wani sassa na jikinta ba sai ranar da ta fara ɗora idonta akan Aliyu Fanda,duk wani boyayyen feiling da emotion suka bayyana kansu,don haka ko me za ta rasa muddun rayuwarsu zata gauraya guri guda da Aliyu Fanda ko me zai biyo baya me sauƙi ne,don haka babu tunanin komai ta mallaka musu mahaifarta ba tare da tunanin akwai zuwan rana makamancin ta yau ba da wani emotion zai bayyana kansa a gareta akan haihuwa. Ba ta taɓa tunanin akwai zuwan wannan ranar ba bare har ta bayyana a gareta a kurkusa,ashe za ta so haihuwa,a she itama zata so ganin jininta? Tun da duk in da akaje aka dawo shi Aliyu yana da nasa 'ya'yan tun da gashi yanzu ma jika yake shirin fara ɗauka. Ganin na samu lafiya Abbana yace Man yazo mu tafi,duk da Momy ta so a barni sai bayan na haihu Baffa da Abbana suka kafe akan babu wannan zancen,ai yaron yayi matuƙar ƙoƙari,idan cikin nawa ya isa haihuwa in yana ra'ayi ya dawo da ni gida na haihu a gabansu, da ƙyar suka barni ganin sunan Nauwwa da ta haifi ɗanta namiji Najif ya yiwa Yaa Muhd takwara,irin farin cikin da na tsinci kaina bazai musaltu ba,wannan yaro kuwa ya ga so da ƙauna da bajinta iri-iri ta ko wani ɓangare. Bayan sunan da kwana biyu Man ya zo washe gari muka juya Abuja muka gina sabuwar rayuwa me kyau da inganci,na wani irin maƙale masa kamar cingam,ko be neme ni ba zan kai kaina,kuma ko ba ya ra'ayi haka zai biye mini mu lula duniyar masoya,wani zubin ko ya rigani samun nutsuwa ba ya barina sai ya nema mini nutsuwar nima,kuma ba na shiru da bakina bare na cuci kaina,mijina ne babu kunya a tsakaninmu,idan ba shi ba babu me biya mun buƙatata idan kuma ba a halaka zan jefa kaina ba,Allah ma ya kiyaye amin. Ban taɓa sanin haka abun yake da daɗi da nishaɗi ba sai a 'yan kwanakin nan,don ni a wahala na ɗauke shi sai ga shi yanzu na zama wata irin fitinanniya ko nace jarababbiya,dan ban taɓa tunanin ina cikin jerin mata masu buƙata ba sai yanzu,ko kuma ciki ne ya saka mini ban sani ba dai. Duk da dai Nauwwa ta taɓa ce mini ko wace mace da irin halittarta,wasu matan a zuwan namiji farko garesu ma suke sanin kan abun,wasu kuma sai sun ɗebi watanni kafin su gane shi,wasu sai sun haihu,wasu sai suyi haihuwa nawa ma kuma suce miki babu wani abu da zasu ɗorar a wannan harkar dan haka abin dai ya danganta da halittar da Allah (SWA)ya yiwa mutum babu wata magana ƙwaƙƙwara sai yadda kika samu kanki. EDD na na gab da cika Momy ta uzzurawa Man sai ya maido ni gida,ni kaina ba son tafiyar nake ba,don duk da cikina ya tsufa sosai kamar ƙara mini jaraba a ke,amman tun da Momy ta matsa babu yadda muka iya haka muka ɗunguma muka nufi kano tare da ɗumbin siyayyar Baby,duk da a scaining ance mana mace ce,komai unisex ya siya,dan yace bai yadda da abin da suka ce ba sai ranar da Babyn ya diro duniya yayi tozali da shi ko ita. Mu na zuwa mu ka tarar da wani jibgin siyayyar Babyn,ba ga Momy ba ba ga Abba ba,dan nikam na rasa tsakaninsu wa ya fi zumuɗin ganin jikan nan? Duk da Momy tun akan Mu'azz ta so samun jika,dan ko yau ma sai da ta kuma tambayar Man cewa. "Wai nikam har yau Zareenah da Mu'azz ba za su yi karatun ta nutsu ba,su haƙura da bokon nan su fara tunanin ajiye iyali ba?" Yau dai kam Sulaiman ya ji bari ya warwarewa Momy komai,ko an samu ta daina saka rai da samun jika ta gurin Zareenah,duk da alƙawarin da ya yiwa Mu'azz cewar maganar za ta tsaya tsakaninsu amma dai kam yau sai ya warwarewa Momy gaskiyar magana ko ta cire rai zuciyarta ta huta. "Zareenah fa tun kwanaki ta cire mahaifarta Momy,ina ganin tunanin samun jika daga garesu ya tsaya daga yau." Momy da ke zaune sai da ta miƙe tsaye ta na salati da sallallami. "Amman wannan yarinya ta cuci kanta,dan bazan ce ta cucemu ba,dan wallahi summa tallahi aure zanwa Mu'azz,Allah ya sauki Najjwa lafiya don muddun ya sake ya tako ƙafarsa ƙasar nan,bazai koma ba sai da mace wallahi." "Momy kina ganin hakan masalaha ce? Dan ina ganin hakan kamar zai karya zuciyar Zareenah, dan yayi Mata alƙawarin bazai mata kishiya ba,wa kuma kike ganin za ki aurawa Mu'azz har da za ta iya zama da shi?" "Idan Zuciyar Zareenah mutuwa za ta yi ba karyewa ba ta daɗe ba ta mutu ba,don wallahi sai na yiwa Mu'azz aure da duk macen da ta kwanta mini a rai,dan wannan ne zai saka Zareenah ta gane kuskuranta da kuma dukkan wata mace me ƙaramar ƙwaƙwalwa irin tata da zasu yadda da maganar namiji,basa duba cewar ba ka isa ka tsarawa kanka rayuwa ba yadda Allah ya so hakan ke kasancewa ko yayi mana daɗi ko akasin hakan.Abu Ɗaya da mace za ta riƙe a rayuwa shine;Kishiya ƙaddara ce,idan tana cikin ƙaddararki ko ba ta ciki allƙawarin namiji babu abin da ya isa ya hana ko ya saka,ki sakawa ranki bai zama lallai ki rayu ke kaɗai da mijinki ba,duk kwa tsayin shekarun da zaku ɗiba,tun da gashi nan ana yi muna gani sai

Chapter 14 of 17