Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mana,dan ya ƙi jinin yayi tambaya a kuma jifansa da wata tambayar. "Amman Mommy ba ta kyauta mana ba,ta barmu da juyi a gado,to idan nufinta ma raba auran za ta yi,wlh tun da na san da shi a yau ɗin nan zan tabbatar da shi." "A'a Ibrahim ka da ka haɗa ni da Hasiyya,ka jira muga iya gudun ruwanta." Ɗif ya ji alamun ya kashe kiran,ya girgiɗa kai haɗe da faɗin Allah ya shirya mini kai Ibrahim,a tunaninsa balarabiyar matarsa ba za ta bar shi ganin wata mace ba,ta yuhu abin da yasa Hasiyya ba ta sanar musu da auran ba har yanzu amman da dukkan alamu Najwa ta ciri tuta. Takwas daidai tayi masa a tsakiyar falonsa,Allah Allah yake yayi tozali da Ammi ya ganta tana tafiya ido da ido,ya kuma ji ɗumin Naajjj,shiyasa ashe yake jin be aikata wani zunubiba,ashe halalinsa ce matarsa ce duk tsayin watannin nan,Momy ta barsu suna shan azaba da begen juna. Ɗakinsa ya wuce direct yayi wanka,ya zura kayan baccinsa me matuƙar kyau da tsada,kana ya nufi ɗakin Naajj ɗin yana zuba fitinannan ƙamshi. Ina tsaye gaban mudubi cikin shirin bacci Ina ɗaure kaina da reborm na ji ƙarar turo ƙofa,a hanzarce na waigo saboda na san ba Zuwaire ba ce,mun riga munyi sallama tun ɗazu ta shige ɗaki yau ba ta jin daɗi,a kansa idona ya sauka,nayi saurin kautar da idon duk tsananin kyan da yayi mini kuwa,zuciyata na bugawa na haye gado haɗe da shigewa bargo saboda rigar da ke jikina me fito da shape ɗin komai ce. Gadon Ammi yaje ya gama shashshafa ta saboda tayi bacci,amman baccin nata ba wani nisa yayi ba,sai kwa gashi ta buɗe ido a kansa,tuni ta wartsake daga baccin,ya sunkuce ta suka fice zuwa nasa ɗakin ya baje mata tsarabar sweet sweet ɗin da ya yo mata da chaculate,kafin ya ɗauketa ya kaiwa Zuwaire ita haɗe da faɗin cewar ta kwana a gurinta,kana ya juyo zuwa ɗakin Najj. A tunanina Ammi ya dawo da ita,shiyasa nayi bakan ina jiran ya fita na tashi na rufe ƙofata,sai dai kawai naga ɗaki yayi dumɗin ma'ana ya kashe swich ɗin ɗakin,wayata na fara laluban nema dan na haska na ga abin da ke faruwa kawai na ji mutum ya dabaibaye ni,daga ƙamshinsa na fahimci shi ne,na fara ƙoƙarin fisgewa ina faɗin. "Meye haka wai?" "Idan ba ki yi kewata ba ni nayi kewar ki Naajjj." Ya faɗa haɗe da ƙarfin ƙara riƙon da yayi mini ya fara ƙoƙarin birkita mini lissafi. Tun ina turjiya har na miƙa wuya yana fitinar jikina da salonsa me tsayawa a rai cikin matuƙar gwanancewa,ban taɓa tunanin zai shiga jikina ba,amman ya shammace ni sai kawai ji nayi yana ratsa jikina,jina cikin gajimare da maɗaukakin daɗin da ya wuce tunanina yasa na kasa yin wani bori,sai bayan mun gama luluƙawa duniyar daɗi mun dawo na hau yin kuka cikin jin na tsani kaina. Tun yana tsokana ta har ya dawo lallashina na, ganin na ƙi yin shiru ya fara ƙoƙarin komawa ruwa da ni na ƙi bashi ha ɗin kai. Kwana nayi ina kuka har su Momy suka zo,wannan Karna har da Baffa da Kawu,ya lanƙaya mini cewar tunanin result ɗin Ammi ne yasa ni kuka,haka na karɓa dan ba yadda zan yi,ban kuma san me zan ce musu yana damuna ba. Washe gari aka shiga da Ammi gwaji aka barmu cikin taraddadi,sai gashi mun samu magana me matuƙar daɗi cewar ba sai an yi mata aikin ba ciwon ya bar jininta,amman sai mun cigaba da ta'ammali da magunguna har zuwa nan da shekara biyar. A ranar Zareena ta dawo,Momy tayi amfani da hakan ta gurin haɗa mu baki ɗaya. "Zareenah zan fara da baki haƙuri na ƙin sanar miki sai yanzu,shekara guda kenan da ɗaura auran Najwa da Mu'azz,ban yi hakan dan wulaƙanta ki ba sai dan basu damar kula da rayuwar Ammi ba tare da samun wata matsala ba,dan kam Mu'azz shi ya cancanta da auran Najwa ba kowa ba. Wani ƙarfaffan kuka na saki wan da zance bansan ummul abaisin yinsa ba,wan da kukan nawa yasa Momy faɗin. "A'a Najjwa idan ba kya son auran,an shiga rayuwarki yanzu zan saka ya sawaƙe miki shiyasa na ƙi bari kusan da auran sai yanzu." "Ai ba zancan saki tsakaninmu don tuni na riga na tabbatar da auran namu." Ya faɗi hakan kansa tsaye da alamu ya manta da wanzuwar Zareenah a falon,ita ko baiwar Allah tun fara maganar Momy zuciyarta ta fara wani irin gudu fiye da yadda take harbawa,jin abin da Mu'azz yace kuwa nan take yasa zuciyarta tsayawa da aiki gaba ɗaya ta zube a gurin a sume,don kuwa ta san waye Mu'azz tun da ya haɗa shimfiɗa da Najwa to tabbas tana da gurbi a zuciyarsa ta yuhu fiye da wanda take da shi. Sai da tayi awa ashirin da huɗu ba tare da ta san wanda yake kanta ba,tun bayan farfaɗowarta kuwa take wani irin kuka me taɓa zuciya,duk wani lallashi da Abii yake mata sam ta ƙi bashi haɗin kai,Mu'azz kuwa tun da ya zo sau ɗaya ta nuna sam ba ta son ganinshi,Abii yace ya taimaka ya daina zuwa asibitin. Da ta ƙular da Ammi kuwa ta hau kanta da faɗa,dama ai ta taɓa gaya mata Mu'azz ba daga sama ya faɗo ba,ga shinan kuwa iyayansa sunyi hoɓɓasa a kansa,sun kwa burgeta yanzu ne za ta san muguwar wautar da ta yiwa rayuwarta,itama kuwa Abii ya hau kanta da faɗa ta barsu da abin da ya dame su ba sai ta ƙara musu damuwa akan wacce suke ciki ba. Kafin Mommy su tafi sai da tayi tsayin daka na ganin komai ya gyaru tsakanin Zareenah da Mu'azz,ta bawa kowa kuskuransa ta kuma yi musu faɗa sosai ko nan gaba su san ba'a yiwa rayuwa shishshigi,tun da sitiyarin tuƙa rayuwar ba a hannuwamu yake ba,komai kake yi NAKA KAKE ALLAH YANA NASA,NASAN KUMA SHI NE GASKIYA dan haka ba mu isa mu yankewa rayuwarmu komai ba sai abin da Allah ya yanke mana. Bayan daidaituwar komai suka juya tare da Ammi,suka bar ni cikin kewarta,ban san shaƙuwa da ƙaunar da nake mata tayi ƙarfin haka ba sai da na laluba ba ita a kusa da ni,ga kewa da kaɗai ci ni kaɗai a gida,Zuwaire ta bi su Momy,su kuma mutan gidan ficewa aiki suke yi duk da dai nima wasan ɓuya nake da su,dukkaninsu nauyinsu nake ji da kunya musamman Zareenah. Yau dai yamun titsiye a kicin,ya bi ya kanainaye ni,ganin na ƙi ba shi haɗin kai yasa ya ɗaga ni cak ya fito da ni daga kicin ɗin wanda yayi daidai da fitowar Zareena daga nata ɗakin,ina ganinta na fara mutsu mutsun sauka ya ƙara ƙarfin riƙon da yayi mini tun da shi be ganta ba ya bata baya,ina ganin yadda tayi fasta ta bi bayan nasa da kallo (Namiji ne fa zaiyi fiye ma da haka Hajiya Zareenah. ) A hankali tun ina ɗari-ɗari da Zareenah har na saki rayuwar ta miƙa mana cikin kwanciyar hankali,babu fitina bare tashin hankali a tsakaninmu,sai matsalolin yau da gobe da ba'a rasasu tsakaninka da duk wanda zama ya haɗa ku,tun tafiyar su Momy da wata biyu na fara laulayin ciki,to sai na samu rangwame wannan karon bansha wahala kamar cikin Ammi ba. Cikina na da wata tara da kwana goma,Allah ya ƙara bani kyautar wata ɗiya macen,wacce ta ci suna Khadija nake kiranta Nihad. Nauwwa sai da ta zo ita da Najib,bayan sunyi umara ya barta a nan sai da ta mun sati guda ta juya. Tun a ranar da na haihu na yiwa Zareenah al ƙawarin ina yayeta zan bata ita halak malak,aiko Abii da Ammi har gida suka zo yimun godiya tun kafin na cika alƙawarin suka kuma ɗauki gata da soyayya suka ɗorawa Nihad. Shi ko gogan tsare ni yayi wai sai na samo mana namu Babyn,tun da rabon 'ya'yan har yau ba su ishe ni ba,haka kawai na ɗauke masa Prity na bawa su Momyy,duk da suma su Daddy sunje sun roƙi arziƙin a bar musu ita tun da su Mommyn suna da twince,to shi ne Abba ya basu,tun da a musulumce Daddyn ma ya fi su ƙarfi a kanta,amman duk da hakan 'yar gida biyu ta zama cikin gata da soyayya,ga Miqdad kullum yana tafe gurin zuwa ganinta da hidimarsa da ba ya gajiya. Ga wannan na ɗauka zan bawa Zareena." Nace. "To ai ta gurin Zareenah ko yaushe zata kasance tare da kai,har zuwa lokacin da za ta bar gidan ƙarƙashin inuwar aure." Yace. "Shi kam sam be yadda ba sai na samo mana namu Babyyn." Da ƙyar na ƙwace daga hannunsa ganin daga wasa yana neman jiƙa mana aiki duk ya bi ya hautsinamu ga halin kuma da nake ciki. TAMMAT BI HAMDILLAH Kuskuran da ke ciki Allah ka yafe mana ka hadamu cikin ladan gaba daya. Kuyi hakuri da yadda ya zo a gurguje abubuwa ne sunyi yawa. Idan mutuwata ta riskeku ina bukatar add u'arku,Allah ka saka mu cika da kyau da imani. Sai Allah ya hadamu a sabon littafina. WADJDA SHINFIƊA "SHEGIYA" Zan iya cewa wannan kalma da ita kunnuwana suka fara buɗewa,tun ana faɗa ban san ma'anarta ba har nazo na fahimci abin da take nufi. Hmmmm! Abun babu sauƙi sam Aunty Bebee'arth,iya wa'yan da aka haifa ta hanyar da aka haifeni ne kawai zasu fahimci abin da nake ji a ƙirjina, domin duk yan da zan kwatanta miki baza ki fahimta ba, ba kuma zaki gane ba sai dai kawai ki tausaya mini, Amman abun ya wuce yadda kike tunani, babu sauƙi sam sai gurin Rabbus samawati wan da shi ya ƙaddara samuwata a haka. Wannan kalma ta dafa rayuwata fiye da yadda wuta ke dafa bushasshiyar ganda,duk wani gata da soyayya da ake bani bai hana ni kamuwa da ciwon zuciya ba,kar kiga laifina Aunty Bebee'arth ba ko wacce zuciya zata iya jurewa,ba ko wacce zuciya zata iya karɓa ba,ba kuma ko wacce zuciya zata iya ɗauka ba,domin kuwa tabo ne wan da ba wani wan da ya isa ya kankare shi daga jikina duk kwa shekarun da za'a ɗiba ana dirjeni, ke ko cikin inji aka sakani aka wanke na fito wannan tabon dai yana zaune raɗam a jikina a haka dai zamu lallaɓa rayuwar har zuwa lokacin da wan da ya bamu aron rayuwar zai karɓi abarsa. Fatana da burina bai wuce zuri'ata su rayu cikin farin-ciki ba tare da nawa tabon ya taɓa musu tasu rayuwar ba. Labarina Sadaukarwa ne ga duk yaran da aka haifa ba ta hanyar aure ba watakam SHEGU kamar yadda ake kiranmu.Sai dai muma ba zaɓinmu ba ne ba kuma son ranmu ba ne ,Allahn da yayi kowa shi ya zaɓa mana rayuwar ya kuma yo mu a haka ba don ba ya sonmu ba,ba kuma don yafi sonku ba sai dan haka yaso ya ganmu ya kuma jarabci imaninmu. Mu mata mun fi shiga taskun rayuwa fiye da namiji wan da in ba tsananin rabo ba ba lallai wasunmu su auru ba, nima da ba don DARA TACI GIDA BA bai zama lallai na auru ba,sai gashi na samu mijin da ban yi tunanin zai karɓe ni ba har yayi kokawa da duk wani tarnaƙin da yaci gaba da bibiyar RAYUWATA. Dan Allah a rage tsan gwamarmu muma ba yin kanmu ba ne,a haka rayuwar tazo mana kamar yadda kuka gani. Kuma sadaukarwa ne ga duk macen da Allah bai bawa HAIHUWA ba,domin kuwa abin da ya taɓa rayuwar Oummuna shi ya taɓa tawa rayuwar, zan iya cewa ƙaddararta ta fara ne gurin ganin ta inganta mana rayuwa,Allah yasa wannan ƙaddarar taki itace silar shigarki aljanna Oummuna tare da dukkan wasu mata da suka ɗanɗani ɗacin RASHIN HAIHUWA. Idan 'ya'ya ɗari zan haifa duk mata bazan gaji da sanya musu WAHIDA ba idan har ni aka bawa zaɓin sunan,ba kuma zan gaji da baki su ba halak malak domin kuwa cikin rayuwar WAHIDA aka fitar da rayuwar WADJDA. Ya na nan zuwa da yardar Ubangiji kuzo ku nuna mun kara da so yay ya. 31/12/2024. Rabee'ah Shu'ayb Nababa "Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun. "Lafiya dai ko na ci muku bashi?" " Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba." "Hmm shine matsalarku?" "Eh" "To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi." "Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?" "Eh mana ɗan hannu ne." Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu. https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1 Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita. Ga masu bukatar a tallata musu hajarsu kofa a bude take cikin farashi mai sauki. #Najjwa #Sulaiman #Mu'azz #BR #09037093702/08082007142 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 17 of 17