ba ta karɓi maganar da akai ba bare har ta tan tance muryar wacce na ji.
NAWWATA haka na gani kamar yadda na yi saving number ɗinta.
"Kina kwa da hankali,wani Yaa Muhd ɗin kike faɗin ya mutu?"
Shirun da na ji shi ya bani amsar cewar ta kashe kiran, dan haka na yi saurin bin bayan kiran nata dukkanin ilahirin jikina na rawa kamar wacce ake bugawa ganga, kira nake ba ƙauƙautawa tana nuna mini busy amman ko lura da hakan ba na yi nake kuma danna kiran gaba ɗaya na fita daga hayyacina.
Salatin da na jiyo gaba ɗaya mutan gida sun ɗauka yasa jikina ya ƙara ɗaukar kyarma kamar wacce aka jonawa batir,motsi ƙwaƙƙwara na kasa yi a haka Aunty Hafsa ta shigo ɗakin ta same ni, ni dai naga ta saka hannu ta kamoni ko kaɗan taƙi bani damar da zanga fuskarta.
Idan nace ga ta yadda akai muka zo gidansu Nauwa nayi ƙarya kawai na tsince kaina ne a ƙofar gidan naga jama'a damƙam ba masaka tsinke a take jikina ya kuma ɗaukan kyarma a haka har muka shiga cikin gidan Nauwa ce ta kwaso da gudu ta yo jikina tana gursheƙan kuka tsabar jikina babu ƙarfi kuma babu nutsuwa ko ta kwabo a jikinsa sai muka tafi ƙasa gaba ɗaya muka zube wan da da ace a cikin hayyacina nake da yadda hannuna ya daki ƙasan simintin nan sai naji muguwar azaba ta ratsa kwanyata.
"Najj Yaa Muhd ya mutu,wannan ciwon cikin sai da ya kashe shi ya huta sai da ya rabamu da shi sai da yaga bayansa, me yasa me yasa me yasa zai mana haka?". Tana kawowa nan ta kuma kecewa da wani kukan, wallahi har lokacin ƙwaƙwalwata taƙi karɓar wannan saƙon sai tambayar kaina nake waye Yaa Muhd meye mutuwa? Wata naga tazo ta ɗaga Nauwa daga jikina ni kuma Aunty Hafsa ta kama ni muka ƙarasa ciki, kowa na gani hawaye yake musamman idan muka haɗa ido nakai hannuna kan fuskata na ji ƙamas to me yake faruwa kowa na hawaye ni ban da ni? Shine tambayar da nake taiwa kaina amma babu amsa.
Ina nan zaune kamar mutum mutumi ina bin kowa da idanuwa bayan wani ɗan lokaci na ji ana ina matar tasa tazo ta masa addu'a za'a fita da shi? Aunty Hafsa ce ta kama ni zuwa wani ɗaki ina ganin makara a gabana ɗauke da gawa ƙafafuwana suka kasa ɗaukata na zube a gurin jikina yana ɗaukar rawa.
Ni dai na farka na ganni ana ta mun fifita, sai kaina da na ji ya sara lokaci ɗaya, ji nayi daga tsakar gida ana ya haƙuri? Na ɗaga kai na kalli Aunty Hafsa haɗe da faɗin waye ya rasu?
Dass! Gaban Aunty Hafsa ya faɗi. "Wa takan duk wainar da aka toya ba ta san ma me ya faru ba ?" Ta shiga tattaunawa da zuciyarta Nauwwa ce ta shigo tana faɗin. "Har yau ba ta farka ba?" Idon da muka haɗa yasa hawayen da ke maƙale a idonta zubowa.
"Nauwwa waye ya rasu na ji ana ya haƙuri,suma na yi ko kuwa bacci na yi kike tambayar na farka?"
"Sai haƙuri mun rasa Yaa Muhd."
"Kina nufin gawarsa na gani ɗazu?" Na faɗa haɗe da zaburowa zanyi waje suka yi saurin riɗƙo ni ita da Aunty Hafsa.
"Ba ɗazu bane tun jiya ne, yau ya riga da ya kwana a makwancinsa na gaskiya wan da ni dake duka zaman jiran wannan ranar muke Najwa,duk wan da lokacinsa ya yi bai isa ya ƙara ko second a kai ba dan haka addu'a ya kamata kiyi masa domin kuwa bai samu addu'a daga bakinki ba har yau da ya kwan ɗaya a makwancinsa."
Aunty Hafsa ke wannan bayanin domin kuwa Nauwa kuka ya kasa barinta magana, ja da baya na yi na zauna daɓas a ƙasa ina mai maita kalmar "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un."A cikin raina kafin na fara jero masa adduoin da duk wan da ya ji yasan ba a hayyacina nake ba. Aunty Fati ce ta rungumoni jikinta tana shafan bayana haɗe da faɗin "Yi kuka Najwa, yi kuka" Kamar umarni kukan yake jira aikwa na kece da wani irin kuka me ban tausayi ban sani ba ko zaku tausayan ko kuma sai iya wan da ya tsinci kansa a irin halin da nake ciki ne zai tausayan har ya fahimci halin da zuciyata ke ciki?
Yaa Muhd ya tafi ya barni cikin duniya me cike da hargitsi kala-Kala a daidai sanda burinmu ya cika, muka fara hango kanmu cikin inuwar aure haɗe da shimfiɗa rayuwar farin ciki da buɗe page page na shafukan soyayya mai tsuma rai, ashe namu muke Allah yana na shi, ya cika mana burinmu na auren juna amman kuma bai bamu damar fara gudanar da rayuwa tare ba. Amman har ga Allah na so sai da aka kaini gidansa ya rasu ta yuhu na samu rabon da zai dishashe mini wani miki na rashinsa amman babu komai duk yadda Allah ya yi daidai ne domin kuwa ba yadda muke so komai yake faruwa ba.
"Najj ko yanzu Allah ya ɗauki raina ya cika mini burina, domin kuwa ya mallaka mini ke zan kuma mutu cikin ƙarƙashin inuwar aure."
Maganarsa ta jiya bayan an ɗaura aure sun shigo gidanmu har ɗakina ya biyo ni ya rungumeni yake gaya mini wannan maganar cikin kunnuwana wan da tun a sannan zuciyata ta fara rawa. A lokacin da na biye mishi tsaf zamu tafka abun kunya dan yadda ya birkice mini har tsoro ya bani , cikin ƙasa ƙasa da murya ya furta. "Kar fa na mutu da Muradinki Najj" Yakai ƙarshen maganar a wahale.
Wallahi da na san mutuwa zai yi da sai na rabu da shi mun daɗe ba mu tafka abun kunyar ba duk surutun mutane sun daɗe suna yi tun da dai ba zina muka aikata ba, sai dai kuma baka tara sani da Ubangiji.
Amman zan killace masa kaina har zuwa san da nima nawa lokacin zai yi muje can aljanna in da babu hargitsin rayuwa,babu mutuwa babu ciwo babu tsufa, babu tashin hankali musha romon damakwarad'iyar soyayyarmu.
(Anya kuwa Naj? Bari dai to mu cigaba da bibiyarki)
Aunty Fati ta haɗa mini ruwan wanka naje na yo,sai a lokacin na ji hannuna na zafi da alamu ko na bugu ko gocewar ƙashi amman ban bi ta kansa to ana ta kai wa yake ta kaya? Miji fa na rasa wan da nake matuƙar so da ƙauna a ranar da aka ɗaura mana aure, na ma yi ƙoƙari wallahi dan ko kaɗan ban yi tunanin zan iya tsaiwa akan ƙafafuna idan hakan ta kasance ba.
"To ai ba ke kike da ikon kanki ba, Allah ne yasa miki dangana da tawakkali."
Maganar da Aunty Hafsa tayi ce tasa na fahimci a sarari na yi tawa maganar kenan.
Sallolin da ban samu na yi ba na rama kafin Momy Hasiya ta kawo mun shayi yana tururi da Bread har da wainar ƙwai kallo ɗaya nai musu na kautar da kaina.
" Yi haƙuri ki sha ko tea ɗin ne, zai ɗan taimaka miki musamman da kinsan kina da ulcer."
Ban musa mata ba na karɓi tea ɗin domin kuwa ƙirjina zafi yake mun dan nasan bai rasa nasaba da ulcer, a haka nai ta kurɓa kamar mai shan magani har na samu na sha rabin cup ɗin kafin mu miƙe mu dawo tsakar gida muka ci gaba da karɓar gaisuwa.
Oh Gidan biki dai ya juye gidan mutuwa ni dai ɓarin wata zuciyar tawa ji nake kamar wasa ne kamar Yaa Muhd ɗina zai dawo gareni.
"A aljanna ba in sha Allah, domin kuwa babu in da kika taɓa ganin an mutu an dawo sai dai in dama can ba'a mutum ba." Maganar Aunty Fati tasa na fahimci a sarari na yi maganar, to dai ina to mutuwar Yaa Muhd ta taɓan kwanya to in ba haka ba maganar zuci sai ta dinga fitowa fili?
[9/25, 10:49] RASHUNA: BEBEE'ARTH
Wattpad@Rashuna
KANA NAKA
(Allah na nasa )
12
Ranar da Yaa Muhd ya kwan bakwai da rasuwa Babansu yace Nauwwa ta shirya a kaita gidanta, tana kuka wiwi take roƙonsa akan ya bari sai anyi arb'ain tukunna yace "Shekara arba'in zan bari ayi ba arba'in ba,bana son shashanci idan kin zauna za ki dawo da shi ne? Ai gwara kije ɗakinki ki ta bin bayansa da addu'a shima zai fi son hakan, in kuma ba so kike iyayen yaron nan su maidamu mutanen banza ba."
Ganin za'a kai Nauwwara gidanta nacewa Gwaggo ta gayawa su Abba nima a kaini gidana nai masa takaba a can, suka kwa ce hakan yana da kyau amman sai an samo wacce zata taya ni zama sai Umman su Yaa Muhd tace ga 'yar uwarta nan Baba Gaje zata taya ni zama tun da kamar yaune kwana arba'in ɗin zata cika.
Da na ganni akan gadona na sha kuka kamar ba gobe mutuwar Yaa Muhd ta dawo mini sabuwa fil.
"Ina son kafin Allah ya ɗauki raina na samu naje saudiya naje madina garin manzo na kuma gina sadaƙatuj jariya wa ni da iyayena."
Na tuno san da muna hira ya gayan wannan maganar, aikwa da Abba yace zai biya mini Hajji nace ya bari idan anyi bikinmu sai ya biya mana tare da Yaa Muhd mu tafi, Allah sarki ashe ba shi da rabo, to wa ya sani ko nima bani da rabon zuwan shiyasa banje a wancan karan ba? Allah shine masani ban isa na bawa kaina wannan amsar ba amman in sha Allah zan gina masa sadaƙatuj jariya.
A haka kwanaki sukai ta tafiya kullum ni kenan ina d'aki ina jan carbi da mik'a addu'ata ga Yaa Muhd, da ba dan Baba Gaje a tsaye take a kaina ba da Abinci ma bazan dinga samu na ci ba duk da Gwaggo na leƙo ni haka Ummansu Nauwa da Momy Hasiya,Nauwwa ma sai da Najib ya kawota ta yinan mini kafin ranar arba'in ɗin ta cika ranar da na fita daga takaba kenan, anan gidan nasa aka taru akai saukar qur'ani mai girma akai sadaka da fatan Allah ya kai ladan kabarinsa Amin.
Sannan akai rabon gadon abin da ya bari nidai abin da na tashi da shi wani ƙaton fili ne wan da na ƙudurta a raina in sha Allah masallaci zan gina masa da sunan Allah yakai ladan kabarinsa.
Hmmm in ji me ciwon haƙori,kamar jira ake na fita takaba maza su fara mun cincirundo ake, amman nikam babu wani wan da na bawa fuska abin haushi da takaici ma har da wani abokin Yaa Muhd Yasir wai shi nan duniya ni yakanar da Yaa Muhd ya kwan bakwai da rasuwa Babansu yace Nauwwa ta shirya a kaita gidanta, tana kuka wiwi take roƙonsa akan ya bari sai anyi arb'ain tukunna yace "Shekara arba'in zan bari ayi ba arba'in ba,bana son shashanci idan kin zauna za ki dawo da shi ne? Ai gwara kije ɗakinki ki ta bin bayansa da addu'a shima zai fi son hakan, in kuma ba so kike iyayen yaron nan su maidamu mutanen banza ba."
Ganin za'a kai Nauwwara gidanta nacewa Gwaggo ta gayawa su Abba nima a kaini gidana nai masa takaba a can, suka kwa ce hakan yana da kyau amman sai an samo wacce zata taya ni zama sai Umman su Yaa Muhd tace ga 'yar uwarta nan Baba Gaje zata taya ni zama tun da kamar yaune kwana arba'in ɗin zata cika.
Da na ganni akan gadona na sha kuka kamar ba gobe mutuwar Yaa Muhd ta dawo mini sabuwa fil.
"Ina son kafin Allah ya ɗauki raina na samu naje saudiya naje madina garin manzo na kuma gina sadaƙatuj jariya wa ni da iyayena."
Na tuno san da muna hira ya gayan wannan maganar, aikwa da Abba yace zai biya mini Hajji nace ya bari idan anyi bikinmu sai ya biya mana tare da Yaa Muhd mu tafi, Allah sarki ashe ba shi da rabo, to wa ya sani ko nima bani da rabon zuwan shiyasa banje a wancan karan ba? Allah shine masani ban isa na bawa kaina wannan amsar ba amman in sha Allah zan gina masa sadaƙatuj jariya.
A haka kwanaki sukai ta tafiya kullum ni kenan ina d'aki ina jan carbi da mik'a addu'ata ga Yaa Muhd, da ba dan Baba Gaje a tsaye take a kaina ba da Abinci ma bazan dinga samu na ci ba duk da Gwaggo na leƙo ni haka Ummansu Nauwa da Momy Hasiya,Nauwwa ma sai da Najib ya kawota ta yinan mini kafin ranar arba'in ɗin ta cika ranar da na fita daga takaba kenan, anan gidan nasa aka taru akai saukar qur'ani mai girma akai sadaka da fatan Allah ya kai ladan kabarinsa Amin.
Sannan akai rabon gadon abin da ya bari nidai abin da na tashi da shi wani ƙaton fili ne wan da na ƙudurta a raina in sha Allah masallaci zan gina masa da sunan Allah yakai ladan kabarinsa.
Hmmm in ji me ciwon haƙori,kamar jira ake na fita takaba maza su fara mun cincirundo ake, amman nikam babu wani wan da na bawa fuska abin haushi da takaici ma har da wani abokin Yaa Muhd Yasir wai shi nan duniya ni yake so,dama can ya fiya shegen kallo nikam bana son namiji me shegen kallon tsiya, ido na rufe na tata masa rashin mutumcin da ko gobe a hanya ya ganni bazai nuna ya sanni ba amman da yake maye ne haka yaci gaba da naci ya dinga sunturin zuwa gidanmu kuma ya samu fada gurun Gwaggo har ta fara yi masa campyn nikam da na gaji kuka na saka mata akan ni babu wani namiji da zan so bare har na aureshi.
"Da yake mu kuma zuba miki ido zamui muna kallonki ba."
Amsar da ta bani kenan.
Ai da na gaji da matsawar Yasir da 'yar koransa Gwaggo ban shawara da kowa ba na haɗa kayana na gudu gidanmu, ranar farin ciki gurin Momy Hasiya kamar tayi me yadda kuka san ta ɗauki zani ta goyani haka ta ji haka kawai Allah ya saka mata so da ƙaunata sai dai kuma murnarta ta koma ciki don da daddare sai ga Baffa yazo maza maza na haɗo kayana mu tafi babu me ƙara matsa mini kan Yasir har sai san da na samu wan da ya kwantan a rai na kawo musu da kaina.
"Anya kuwa akwai wannan ranar ?"
"Lokaci ne zai nuna mana hakan Najwa"
Cewar Momy Hasiya,ashe a fili nayi maganar.
Da ƙyar Malam ya barni dan yana jin nauyin Momy Hasiya shima a zuwan zan kwanan mata biyu.
Na ji daɗin kwana biyun da nayi a gidanmu daga Momy har Abba lelena suke kamar ƙwai Allah sarki sai na tuno zamanin Hajiya Kubrah ana can dai walakiri yana jibga dan nikam dai bani yafe azabtarwar da matarnan tayi mini duk da dai ga 'yarta can na girbar abin da ta shuka tana cin gashin azaba gurin matan uba sun hana ta aure duk wan da ya fito yana santa sai sun san yadda sukai maganar ta rushe.
Yau na ke shirin tafiya gida, tun safe na gama shirina kamar wacce zata wani gari, Momy ce ta tsaida ni akan na bari sai yamma na tafi saboda Son ɗinta ya kira ta in sha Allah jirgin k'arfe biyar da zai sauka yau a nigeria har da shi a ciki kuma bata jin daɗi shiyasa tace na tsaya na ɗan yi masa abin tarɓa Nasrin sai ta taya ni da wani abun.
Har na nufi kitchen sai kuma na dawo gurin da Momyn take nace.
"Momy to me kike ganin za'a masa?"
"Ai shi wannan ɗan gargajiya ne ba kamar wancan baturen ba,ki masa tuwon shinkafa miyar kuka, a kwai nama ƙaramar dabba a fridg ki zuba a ciki ya wadatu sosai, sai ki masa farfesun naman kaza,idan na tashi ni kuma zan haɗa masa lemon."
Har na juya kuma naji tace.
"Au manta akwai awara a fridge ki soyata sannan ki soya masa ita da ƙwai."
"Au Momy shima yana son awara?"
"Sosai ma kuwa, ai ni ban taɓa ganin mai son awara irin Son ba, saboda shi dukkanmu muka koyi cinta, gashi nan har yanzu da baya nan na saba bana zama babu ita a fridge tana ƙarewa nake dafa wata."
Ankarewa ta yi da hawayen dake tsere akan kuncina tace.
"Lafiya kuma kike kuka?"
"Na tuno Yaa Muhd ne Momy,yana mutuwar son awara."
"Allah sarki,to ai addu'a zaki masa ba kuka ba, kuma zamu dunga bayarwa ana dafawa a soya ayi masa sadaka Allah yakai ladan kabarinsa, ana so idan mutum ya mutu a dunga masa sadaka da abin da yake mutuwar so (Nikam in na mutu wake da shinkafa za'amun sadaka ko kuma awarar.Allah kasa mu cika da kyau da imani amin.)"
"Na gode Momy."
Na faɗi haka haɗe da juyawa na nufi kichen ɗin ta bi bayana da kallon tausayi.
Nan da nan na gama aikin komai Nasrin ta jere masa su akan dining,sai da na ɗibarwa Baffa tuwon dan mutuminsa ne in ya mutu abin da zan dinga masa sadaka da shi kenan to kuma wa yasan gawar fari? ƙila ma na rigasa sheƙawa. Duk yadda Momy ta so na tsaya sai Son ya iso amman na ƙi Allah Allah nake naje na kaiwa Baffa tuwon nan dan nasan sai ya buga santi.
Ɗan halak kwa a ƙofar gida muka ci karo da shi ya fito da ɗan kekensa mai masifar kyau da yake zazzagawa a kai.
"A'a Baffan shagali ina kuma zuwa?"
"A'a Najwan sha'ani ni ai har na haƙura na barwa Bashir da Hasiya ke."
"To ko na koma?"
"Yaushe zance ki koma? Da dai ba ki riga kin taho bane, me na samu ne?"
"Canki mutuminka ne."
"In dai mutumina ne bazai huce tuwo ba."
"Aikam dai shine na shinkafa miyar kuka."
"Allah yai miki albarka ya tsunduma ki a aljanna ɗazun nan nake kewarki Gwaggon nan naki ba wani iya tuwon shinkafa tayi ba."
"Au haka kace? Najwan zatai aure ne ta barni da kai ne ?"
Cewar Gwaggo da ba mu san sanda ta fito ba,dariya mukai daga ni har Baffan kafin nace.
"Idanma na yi auren na dinga kawo masa daga gidana."
"Yawwa gaya mata shalelen Baffa, tukuicinki yau dole na biya mandawari."
Yakai ƙarshen maganar yana hayewa kan kekensa.
"Yauwwa Baffa a haɗo da Rufaida."
"In sha Allah shalele,ki kula mini da tuwona ina dawowa ta kansa zan fara, ko gutsire kar ki bari Gwaggonki ta taɓa."
"Ni kam me zan yi da tuwon zamani ga tun na iyaye da kakanni?"
Bai jiyo ta ba da sai ya bata amsa ya riga da ya miƙa a dawo lafiyar ma da nake masa hannu ya ɗago mini, muka shige ciki ni da Gwaggo ina murnar yau zan ci tsiren mandawari.....
[9/25, 10:49] RASHUNA: BEBEE'ARTH
Wattpad@Rashuna
KANA NAKA
(Allah na nasa )
13
"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmmm! shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL SPARKLES VEILS daga yanzu wahalar neman mayafai ta ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"
"Eh mana ɗan hannu ne."
Amma ta iya mayafai maza-maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.
https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1
Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL SPARKLES VEILS daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.
****"""""
Naj na fita Isah driver ya sauke SULAIMAN ALI FANDA Farin bafulatanin da ya juye ya koma tamkar balaraben da ya samu hutu da kwanciyar hankalin rayuwa, cike da zumuɗi ya buɗe murfin motar ya fito ganin Momy ta nufo gurin da akai parking motar tasu, rungumeta yayi cike da shaƙi kafin yace "I miss you Momy." Cikin harshen da ya saba yaruka kala-kala wan da ya juye yake bada wani sauti na da ban.
Murmushi kawai Momy tayi tana ɗan kaucewa daga rungumar da yayi mata, saboda kasancewarsa ɗan fari tana ɗan kawaici a kansa shiyasa ko sunansa bata kira sai dai tace. "Son" Amman itama tayi missed ɗin yaron nata yadda bakwa zato musamman da yake akwai shi da ƙulafuci shiyasa duk a yaranta ta fi ƙaunarsa duk da tana kawaici a kansa.
Hannunsa ta ruƙo suka nufi cikin gidan tana tambayarsa ya hanya yana bata amsa, har suka shiga ciki, direct dining area ta nufa da shi saboda tasan halin son ɗin nata baya wasa da cikinsa, komai zai biyo daga baya to bayan ya cika tumbinsa ne, kuma tasan ba mamaki tea ne kawai a cikinsa tun daga wayewar garin yau saboda yasan girkinta na nan na jiransa.
Flass ɗin farko da Momy ta fara buɗewa zata yi serving nasa idonsa ya sauka akan mutuniyar tasa tayi nashar nashar da ƙwai hannu na rawa yakai ya ɗauki guda ɗaya yakai baki yana lumshe kyawawan idanuwansa.
"Allah ya tsunduma ki a aljanna Momy."
"Gaba ki ɗayanmu Amin."
Sai da yaci awarar sosai kana ya saka mulmulallen tuwon shinkafa fari sol da shi malmala biyu a plate suka haɗa ido da Momy yayi murmushin da ya fito da zallar kyawunsa.
"Wallahi yau mom babu abin da naci sai tea ne kawai a cikina."
Murmushi Momy tayi kafin tace ai nasan za'a rina. Zareenah har yau ba ta gama bokon bane bare su fara tunanin aje iyali?"
"Hmmm! Momy ki rabu da sabgar wa'yannan yahudawan mutanen, kuma babban mai laifinma EL ne saboda yasan wa ya auro kuma kafin su bashi aurenta sai da sukai yarje jeniya saboda shima yaran ba damunsa sukai ba."
"To Allah ya kyauta musu wannan lamarin, ni ita nafi ji,shi namiji duk sanda ya tashi buƙatar yara aurensa zai ƙara."
"Wai nan yayi mata alƙawarin bazai mata kishiya ba."
"To ai zamu gani tun da shi ke da ikon tsarawa kansa rayuwa, gaba ɗaya shima ya koma kamar baturen da aka haifa a turai."
"To ai Mom zama da maɗaukin kanwa....kuma zani ce ta tadda muje ni."
"To Allah ya rufa asiri, zan yi maganinsu gaba ɗaya duk randa MU'AZZ yazo bazai koma ba sai da mata in basa son yaran ni ina son jikoki, kaima dai da fatan da shirin aure ka iso."
"Ban dai zo da shiri ba,saboda har yau ban samu macen da ta kwantan a rai ba,amman a jikina nake jin lokacin aurena ya matso kinsan komai kana naka ne Allah kuma na nasa shirin kuma nasa ne gaskiya namu duk shirme ne."
"Gaskiya ne,Allah ya shige mana gaba Amin."
Wayar Momy aka kira, tana ganin number ta gane waye ya kira dan haka ta miƙawa Sulaiman dan ta san shine
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 17