Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuba santi suna mamakin 'yar k'arama da ni haka na iya girki,Gwaggo na k'ara kuzanta musu yadda nake da himma a komai ba ma a girki ba don tun dawowa ta gidan na hana ta aikin komai,komai ni nake sai dai wani zubin ta kama mini ko kuma in ina makaranta sai ita ta yi. Da naga har bayan la'asar Nauwa ba ta dawo ba sai na zuba mata dambun na cewa Gwaggo. "Bara na kai mata." A lokacin su kuma sun d'an kwanta su huta. Na zo daidai da zan shiga gidan nasu muka yi kacib'is da Yaa Muhd na tsuguna har k'asa na gaishe shi ya amsa kafin yace. "Har kinzo? Gashi yau ban jin zamu samu damar yin lesson,sai dai zuwa gobe in Allah yasa zamu gani.". Nace. "Allah ya nuna mana goben" Yace. "Amin." Na shiga ciki,sai dai ban sameta ba Umma ke cemin ta tafi Islamiya,ta gaya mata 'yan uwan mahaifiyata sun zo ni bazan samu zuwa ba,a raina nace. "Nauwa mayyar islamiya." Na bawa Umma dambun na juyo gida muka zauna da su muna ta hira,sai a lokacin suka ce "Ba ki tambayemu sunayenmu ba." Nace "To ai kune ba ku gayan ba." Gwaggo tace. "To ke ba sai ki tambaya ba banda sokanci irin na 'yar fari." Na k'arashe mata da. "Kuma auta ba." Dariya muka saka gaba d'ayanmu kafin su fara gayan sunansu, d'aya tace sunanta Maryam,d'ayar Halima,sai Hafsa,Hafsan itace k'anwar mahaifiyata,su kuma 'ya'yan yar mahaifin mahaifiyata. Nan dai muka cigaba da hira har suke cemun an kusa bikin autar su mahaifiyata nace. "Aikam zan zo,dama saura wata biyu mu yi juniour candy in nazo sai na yi kusan wata biyu ko uku duk na zaga dangi." Suka ce. "Da kwa Inna da Kawu sunfi kowa farin-ciki." Nace. "Wai su waye Inna da kawun ne?" Aunty Hafsa ce tace. "Babarmu da Babanmu." Nace. "Kakannina kenan?" Tace. "Eh" Aikam na saki wani ihun murna zanje naga kakannina ashe suna raye wayyo,ji nake tamkar mahaifiyata aka cemun tana raye tun da ita na riga na d'ebe tsammanin ganinta sai a aljanna idan Allah ya had'a fuskokinmu. Nace. "Aunty Hafsa Abba yace ba a k'asar nan kuke ba,ya akai kuka iya hausa?" Tace. "Ai Innarmu bahaushiya ce ita ke yi mana hausa shiyasa muka iya." Nace. "Ku yi mini yaren naku na ji." Aikwa suka hau yi mini ina kwasar dariya ina auna suma da ace ba su iya hausa ba haka zasu ji nawa harshen,Allah buwayi kenan gagara misali.Allah mai gari bam-bam. Sai da su Aunty Hafsa suka kwanan mana biyu kana suka tafi,d'an kwana biyun da mukai munyi sabo sosai,Abba yazo sun gaisa sun gaya masa sak'on su Inna yace dai su nema masa afuwar su ina yin juniour candy shi da kansa zai kawo ni in sha Allah,shi ya biya musu kud'in jirgi da sha tara ta arzik'i suka koma suka barni da kewa. Na gayawa Nauwa muna yin juniour candy sai sierealoan,duk da jikina ya yi sanyi da Abba yace shi zai kai ni kar abun ya kuma shiri ricewa, duk da na k'udiri aniyar saka Mallam ya matsa masa. Nauwa tace. "Dama Baba ya barni sai mu tafi tare." "Eh wallahi,ki tambayesa Allah yasa ya barki." "Amin to,zan gwada,anman kinsan halinsa." "To ga wata shawara" "Ta me fa?". "Ki gayawa Yaa Muhd sai ya tambaya miki." "Cib'b'in ina naga fuskar tunkararsa Naj? Ba fa ya sakar mana fuska ko kad'an,ko lesson d'in da yake mana albarkacin ki na ci." "Ki jimin sharri,ga abu a sarari kowa yasan albarka cinki nake ci zaki wani ce haka,to ni a suwa kare da gudun layya? Ni abinda na fuskanta Yaa Muhd ba ya son raini, don kinje kin rok'eshi babu abinda zai miki." "Ke duk fa abin ki bazan tunkari Yaa Muhd ba gara na gayawa Umma ta rok'a mini Baban." "Mtssss! ga hanya mafi sauk'i muka tsaya bawa kanmu wahala." Dariya muka saka tare da adduar Allah ya nuna mana lokacin..... #Bebee'arth #Rashuna #09037093702 [3/9, 23:28] FaShuNa: BEBEE'ARTH Watpad@Rashuna KANA NAKA2024 [Allah kuma na yin nasa] (5) Kwanci tashi asarar mai rai;idan bai aikata abin kirki ba,abin da zai d'ibi ladansa a lahira ba. Har mun gama juniour candy,dama tun da muka fara zana jarabawa nake gayawa Malam ya tunawa Abbana muna gama jarabawa zai kaini sierealeon,kuma ya siya mana waya ni da Nauwara,tun da tafiyar ma tare da ita zamui dan ta gayawa Ummansu tun tuni ta tambayar mata Baban nasu kuma ya barta yace. "Ai Najwa ce ba a hana Nauwara bin ta ba,k'awancensu ya zarta k'awance sai dai a kira shi 'yan uwan taka." Sai gashi kuwa muna gama zana jarabawar Abba ya fara mana shirin tafiyar,da yake yanzu naga yana d'an shiga lamarina dan ba kuga d'inkin da ya mana ba ni da Nauwa,ga kuma sababbin wayoyinmu masu kyau,duk da sai da muka sha fad'a da takara gurin kowa kafin a bamu wayar musamman Yaya Muhd don cewa yayi muddun ya samu d'aya daga cikinmu da kula samari sai ya yi mana hukuncin da ba mu tab'a tunani ba,shiyasa muka k'udiri niyar kiyayewa duk dama Allah bai yimu masu rawar kan kula samari ba dan ko mazan ajinmu bama shige musu sabanin wasu da har soyayya suke a tsakaninsu. Ranar lahadi mun gama shirinmu,mun had'a komai namu sai zumud'i muke da zirgillo da yake washe gari litinin zamu tafi.Baban su Nauwara shima yayi mana sababbin d'inkuna,Yaa Muhd ma ya siya mana dogayen riguna masu kyau,Gwaggo ma ba a barta a baya ba tayi mana dambun nama mai yawa da miyar kaji tace mu tafi da su Baffa kwa addu a ya bi mu da ita dan babu abin da kuma muke nema. Washe gari jirginmu ya d'aga sai sierealeon,ba mu sha wata wahala ba da yake da Abba a tare da mu tun da ya riga da yasan ainiyin garin da suke a cikin sierea d'in sai gamu har k'ofar gidansu mahaifiyata,sai da k'walla ta ciko idanuna na d'auketa da hannuna ba tare da ko Nauwa ta farga ba,abin da kuma ban sani ba Abba yana ankare da ni shi kanshi jikinsa wani mugun sanyi yayi yana jin tamkar ya aikata mugun zunubi,ya tabbata ya yiwa Kadija babban laifi ace tun mutuwarta sai yau da take da shekaru goma sha uku zuwa sha hud'u sai yau ya tako mahaifarta,bai dubi mahaifanta da ya shaida cewar tafi k'aunarsu akan karan kanta ba.Yana da tabbacin da zab'i aka bata ya tabbata baza ta tafi ba tare da ta wadata su ba yadda ko bayan ranta baza su yi kukan rashi ba,sai dai kuma da yake tsarin tafiyar rayuwar gaba d'aya ba a tafukan hannunmu yake ba tsarin na Allah ne,yadda yaso hakane yake kasancewa baka isa ka canja komai ba. Ji ya yi yana mugun kunyar had'a ido da mahaifanta,lura da ya yi ya barmu a tsaye yasa shi kallona yace. "Ku shiga Najwa nan ne gidansu mahaifiyar ki,sai ku shaida musu ina k'ofar gida." Da sallama muka shiga cikin gidan,da wata fara sol d'in dattijiwa muka fara cin karo zaune a tsakar gida itace kuma ta amsa mana sallamar mu,ina ganinta a jikina naji itace kakata saboda kama da suke da mahaifiyata,nima kuma mahaifiyar tawa nayo sak sai dai na d'ebo zubin Abba kad'an. Da fara'arta tace mu shigo dan daga ganinmu tasan ba 'yan garin ba ne bak'i ne,sai dai kuma ta k'ureni da ido tana ta kallona,murmushi na saki kafin nace. "Abin kunya kaka ta kasa gane jikarta." "Ta ya za'ai na kasa gane jinin Khadijata?A tun shigowarku sai da jikina ya bani Khadijata ce ta dawo." Janyo ni jikinta ta yi ta rungume had'e da fashewa da kuka tana kiran sunan Kawu. Gyaran muryarsa muka fara ji yana fitowa daga makewayi a gabanta ya shiga anman ta mance ta ma yi tunanin yana d'aki,shima fari ne anman ba can ba yana da jiki duk da tsufan da ya cimmasa. Hannu ya d'aga sama yana wa Allah kirari da godiya da ya bashi aron rai da numfashi har sai da yayi tozali da jinin Khadija,kafin ya k'araso in da muke shima ya rungume ni cikin jikinsa,muryar Nauwa naji tana. "Naj munfa bar Abba a waje." Kafin na yi magana Kawu yace taje tace ya shigo. An gaggaisa an tambayi bayan saduwa tare da neman afuwarsu na nemansu da bai yi ba suka nuna babu komai,komai nufi ne na Ubangiji idan bai nufeka da yi ba komai damun da abin zai maka a zuciya ba ka isa ka aiwatar da shi ba. Abba bai wani jima ba yayi musu sallama ya tafi anman yace su bani Accaunt number na tura masa zai sako musu sak'o,wata bak'ar jaka da na yi tunanin tasa ce itama yace na bawa su Innan sak'onsu ne a ciki,sosai suka dunga masa godiya. Bayan tafiyarsa ne nake cewa Inna. "Ina su Aunty Hafsa?" "Ai duk suna gida jansu,bara Fatima ta dawo sai ta raka ku ko gidan Hafsan ne kawai zuwa gobe in kun huta sai ku fara zaga dangi. Tun d'azu na aiketa kin jita shiru tamkar maye yaci shirwa,ta yuhu tana can gidan Hafsan,da ta sama muku wani abun kun ci." "Da yake ma ba yunwa muke ji ba mun ci cake da coffe a jirgi." Ina rufe bakina sai ga sallamar Fatiman. "Inna na jima ko?Wallahi..." "Wallahi me?" Inna ta yi saurin katse ta.kinje kin yi zamanki gidan Hafsa zaki zo kimin dad'in baki,ga baki nafi awa hud'u da aiken ki sai yanzu zaki kwaso k'ananun k'afafuwanki ki taho mini kina Inna wallahi." Fad'a sosai Inna ta dinga mata duk da yarensu mudai sai saurare ba ji muke ba.sai can Fatin ta kallo in da muke zaune baki ta saki tana kallona kafin tace. "Inna na canka" Innan ba ta dai ce mata komai ba sai ta kalle ni tace. " 'Yar Aunty Khadija hakane?" Gyad'a mata kai na yi aikwa ta yi wata sufa ta rungume ni tana murna kafin tace. "Ashe dai da gaske su Aunty Hafsa suke da suka ce zaki zo? Ba yadda ban yi ba su taho da ni da zasu zo anman suka k'i wai kud'in jirgi nace su saka ni a maleji ko boot Aunty Maryam tace Uban wa yace miki akwai maleji a jirgi?" Dariya muka saki gaba d'aya dama tunda tace meleji muke rik'e dariyarmu ni da Nauwa,nace. "Aunty Fati ga 'yar uwata Nauwara." Tace. " 'Yar uwarmu zaki ce,nima ta zama 'yar uwata daga yau.'Yar uwarmu kunzo lafiya,ya hanya?" "Lafiya Alhdlillah Auntynmu." Cewar Nauwa. Inna ce tacewa Aunty Fati ta tashi ta raka mu gidan Aunty Hafsa ta sama mana abin da zamu ci dan in tace Aunty Fati ta mana shiririta zata tsaya har mu jigata da yunwa dan tasan hali. Sai da Aunty Fati ta fara kwashe mana kayanmu ta shigar mana da shi d'akinta kana muka nufi gidan Aunty Hafsa babu nisa,zo kuga murna gurin Aunty Hafsa da ta ganni ai abun bazai fad'u ba, wannan zuwa ba zato ba tsammani dan ba su tab'a tunanin Abban zai kawo ni ba. ' #Bebee'arth #Rashuna #09037093702 [3/9, 23:28] FaShuNa: BEBEE'ARTH Watpad@Rashuna KANA NAKA2024 [Allah kuma na yin nasa] (6) Ashe bayan tafiyarmu Mama sai ta nufi gurin bokanta saboda ganin yadda Abbana ya kashe mana kud'i ni da dangin mahaifiyata,ya kuma tafi kai ni da kanshi,alamu ne na farrak'un da aka mana ya fara sakinsa shiyasa taje a sabunta shi,wanda da ta san abin da zai faru da ko da kud'i ba taje ba sai dai kuma idan ajali yayi kira babu abin da ya isa ya dakatar da kiran dole ka amsa ba ma kasan sanda zaka amsa kiran ba. Da murnarta da farin-ciki ta baro gurin bokan da ya sanar mata muddun ta yi turaran da ya bata Abbana ya shak'a to an mana farrak'un da ba wanda ya isa ya warwareshi ko shi karan kansa ne.Wannan farin-cikin shi yabi ya isheta take tuk'inta cikin kwanciyar hankali ba tasan ajalinta yana k'ara kusantota ba domin kuwa nata shirin take Allah kuma yana nasa rayuwa da mutuwa tafiyarsu gaba d'aya a hannunsa yake anman wani zubin sai tunani da hankulanmu su gushe. Hatsari suka tafka mai muni babu kyan gani wanda ya yi sanadiyar mutuwar Mama a nan take gashi nan ta tafi ta bar mana duniyar tana k'ok'arin raba tsakaninmu ita sai Allah ya rabata da nata numfashin kuma babu yadda za ta yi babu yadda zata iya komai sai da amincewarsa sai da yardarsa yake faruwa baka isa ka canja faruwar komai ba. (Me yafi wannan asara cikin rayuwa Ka mutu kana aikata shirka, bayan baro warka gurin mushirikin?Allah da kansa yace ba ya yafe laifin shirka idan har baka tuba ba,idan kaje gurin boka sai kayi kwana arbain sallar ka ba ta karb'u ba,kana da tabbacin zaka mayar da asarar wannan sallar da kayi?ko kwa kana da tabbacin zaka wuce kwanaki arbain din ba tare da ka amsa kiran mahaliccinka ba? Wannan tambayoyin ya kamata ka fara yiwa kanka yayin da shaid'aniyar zuciyarka ta kwadaita maka zuwa gurin boka,ka kuma nemo amsoshinsu wanda bai wuce baka da tabbacin domin kuwa ba ka san me gobe ta tanadar maka ba,Allah ne kawai ya barwa kansa sani to sai ka sakawa ranka babu wani k'ato ko gardi da zai iya yi maka abin da Allah bai maka ba domin kuwa shima yadda aka baka aron numfashi da rayuwa haka aka bashi,yadda ake sarrafa taka rayuwar shima haka ake sarrafa tasa,duk wani abu da zai faru to dama can haka yake a rubuce "An d'auke alk'aluma kuma takaddun sun bushe." Allah ka kiyashemu kasa mu dace Amin. ) Abba sai fasa tafiyar da yayi niya ya yi ya dawo a ranar akaiwa Mama sutura aka kaita aka barota daga ita sai halinta domin kuwa shine kad'ai zai kunceta ya bata salamar kwanciya cikin aminci idan ta aikata daidai(Innalillahi wa inna ilaihir raji'un wallahi ina tunanin wannan ranar.Abun damuwar kuwa baka san ranar da zata riskeka ba sai dai ka bud'i ido ka ganka cikin kabari,halinka na gari shine zai ceceka,Allah ka bamu ikon aikata daidai Amin.) Sai da daddare da muka yi waya da Abbana yake gayan mutuwar nace."Allah ya jik'anta. Satinmu d'aya a sierea mun gama zaga dangi gaba d'aya duk in da muka yi Aunty Fati na tare da mu,ita ke fassara mana abin da wasu ke fad'a dan ba iya yaren nasu muka yi ba.Muna da sati biyu da zuwa aka fara gudanar da bikin Aunty Fati,al'adar bikinsu gwanin birgewa.Anyi biki lafiya an gama lafiya gidan Aunty Fati babu nisa da na Aunty Hafsa,kuma da alama mijin Aunty Fati yana da farcen susa. Kwanci tashi ciki k'udirar Ubangiji har mun cinye wata uku a sierea,daga ni har Nauwa har mun fara koyan yarensu.Gobe muke saka ran tafiya sai shiri muke da yake jirgin da zai tashi da asuba zamu bi,yadda kasan kar na rabu da kakannina suma haka suke ji kamar nayi ta zamana a tare da su haka muka yi sallama da tunanin ko zamu k'ara ganin juna?Domin kuwa Allah shi ya barwa kansa sani bamu da tabbaci,ta cewar Kawu. "Wai shi yasan rayuwarsa tazo gangara,yamma ta cimmasa daren kawai yake jira." Nace."Babu wanda yasan gawar fari sai Allah k'ila na rigasu yin gaba,k'ila muna da sauran rayuwar mai tsayi gaba d'aya wannan kuma du Allah ne ya barwa kansa sani sai dai muyi fatan Allah k'addara saduwarmu." Cikin k'oshi lafiya muka sauka k'asarmu,cikin garinmu,mun baro su Inna da kewa.Muna sauka direban da Abba ya aiko ya d'ebemu sai gida muna shiga na d'afe Gwaggo ina murna tace. "Najwa kar ki k'arasa ni mana dama k'ashi ba k'wari ba duk ya takwar kwashe." "Kai Gwaggo wata uku cur ba ki kewata ba?" "Na yi kewarki mana,anman lafiya ai tafi kewar." Baki na turo gaba,na shige ciki ina k'walla kiran Baffa sai naji Gwaggo tana. "Bai jima da fita ba." "Allah sarki Habibina Allah ya dawo mun da shi lafiya amin,nasan ya yi kewata ba kad'an ba." "Nauwara shigo ta barki tsaye sai zance take." "Wallahi kuwa Gwaggo." Sai da muka shiga d'aki kana muka gaisa da Gwaggo tana tambayarmu yadda muka baro su. "Naj nifa na matsu naga Baba da Ummana." "To muje na rakaki,anman ke zaki d'au kayanki dan na gaji bazan iya d'auka ba." "To cewa na yi ki d'aukar mun 'yar rainin hankali." "Oho dai,kinga ni muje." Tafiya muke har muka je gidansu ba wanda yace da d'an uwansa uffan,muna shiga da sallama Ummansu da ke tsakar gida ta amsa mana,Nauwa ta fad'a jikinta cike da murna da kewa. "Ummana sannu da gida,mun sameku lafiya?" "Lafiya lau Nauwara,ya kuka baro su?" "Lafiya lau." Na tsuguna har k'asa na gaisar da Umma na k'ara da. "Umma su Gwaggo sunce a muku godiya Allah ya bar zumunci." "Ai babu komai Najwa,ke da Nauwara d'aya nake d'aukar ku saboda k'aunar dake tsakaninku kullum addu'ata kada Allah ya bawa shaid'an damar shiga tsakaninku." Mukace"Amin"Gaba d'ayanmu. "Baba baya nan ne?" Cewar Nauwa,Umma tace. "Yana ciki ku shiga ku gaisa." BEBEE'ARTH Watpad@Rashuna KANA NAKA2024 [Allah kuma na yin nasa] (7) Mun same shi a kishin gid'e da alamun bacci ke d'an fisgarsa,sallamar da muka yi ce ta saka shi bud'e idanunsa tare da amsa mana. Guri muka samu muka zauna,a tare muka had'a baki gurin gaishe shi ya amsa mana cike da farin-cikin ganinmu yace. "Kun baro kakannin naku lafiya?" Nace. "Lafiya lau,kuma,sunce a gaishe ku ai muku godiya,Bafffa da Gwaggo ma sunce a k'ara musu godiya Allah yabar zumunci." "Amin,kice musu ai ba wani abu duk an riga an zama d'aya." "Tom in sha Allah zan fad'a musu." Daga haka na mik'e na fito na bar Nauwa na hira da mahaifinta,na koma gurin Umma na zauna muna tab'a hira da ita kafin na mik'e na yiwa Umma sallama zan tafi,sai ga Nauwa ta fito. "Tsaya na rakaki ba dan halinki ba." "Ki bash shi ba na so,ai ba rok'a na yi ba bare amini ba don halin nawa ba." Daga haka na doshi hanyar fita,tayi saurin janyo mayafina. "Umma jiye mini wannan maganar;ita fa ta fara tsokanata shine har zata fini fushi." "Kinga malama babu ruwan Umma a wannan maganar." "Aikwa ita ke da ruwa,ruwan ma na maliya." Umma ce tace."Wai me ke faruwa?yanzu na gama yi muku nasihar kar ku bawa shaid'an damar shiga tsakaninku,ku dinga hak'uri da juna." Nauwa ce tace. "Umma ba fa wani abu ne ya faru ba." Ta zayyana mata abin da ke tsakaninmu,Umma tace. "To me ye abun fushi anan?"Sai a sannan nai magana nace. "Umma kinga fa tun da muka taho ta had'e fuska ta sha kunu shi ne nima nasha kunun da yafi nata yawa.Ai a tsakaninmu Ummq babu zancen fushi ko?" "Eh hakane Najwa.To dai yanzu abu ya huce kar na kuma ji kar na kuma gani." Nace. "In sha Allah Umma" Na kalli Nauwa na sakar mata murmushi nace. "Afuwa 'yar uwa,bazan kuma ba." Martanin murmishina ta maida min tace. "'Yar uwa dama ke kika d'au abin da zafi.Muje na raka ki." "Ba ki gaji ba?" "Kar ki damu ai mun saba rakiyar kura in ba muyi ba ba ma jin dad'i." Dariya muka yi a tare na yiwa Umma sallama muka fito.Sai da Nauwa ta rakani har k'ofar gida kana ta juyo,ina shiga na tarar Baffa ya dawo na shige d'akinsa muka gaisa muka d'an tab'a hira kana na shiga d'akin Gwaggo. "Idan kin yi sallah ga abincinku nan,naga Nauwara ta matsu taje gida shi yasa ban tsaida ta ba." "Toh Gwaggo idan nayi sallar na kirata a waya tazo mu ci." Wanka na fara yi nai sallah kana na kira Nauwa a waya tazo mu ci abincin sai cewa ta yi itama yanzu abincin zata ci,bara ta taho da shi sai mu had'u mu ci gaba d'aya. Satinmu guda da dawowa muka soma zuwa makaranta,dama Abba ya gama mana shirin komai,nan da nan muka fara d'aukar karatu musamman da yake ajin sience muke sosai muka daga da karatu Yaa Muhd yana taimaka mana ta b'angaren lesson d'in da yake mana.Muna sss2 Abba ya tashi yin aure shima saboda matsawar Baffa,sam ba ya son ganinsa babu aure domin kuwa shine cikar mutumtakar mutum. Ina gidansu Nauwa muna hira,sai muka shiga hirar auren da Abba zai yi,domin jiya Gwaggo ke fad'a mini 'yar uwar su Nauwa Abba zai aura. "Nauwa ashe 'yar uwarku Abba zai aura?" "Eh wallahi nima jiya nake ji a bakin Umma wai Mommy Hasiya zai aura." "Mommy Hasiya dai k'anwar Baba?" "Eh wallahi ita,kinga zumuncinmu zai k'ara k'arfi,dan nasan gidanku zaki koma nima sai na tattara na biki dama Mommy Hasiya ta gurina ce." "Sai dai in ke zaki koma,nikam ina gaban Baffa da Gwaggo babu abi da zai saka ni matsawa." "Kin san dai Mommy Hasiya ba irin Kubrah ba ce,tana da kirki da hak'uri ga son mutane,ba wai ina fad'a miki haka ba ne don tana k'anwar mahaifina." "Na sani Nauwa,nima ba wai ina gudun kar ta cutar da ni ba ne, kinsan irin k'uncin da takurar da na shiga lokacin Mama,haka ta saka Abba ya kore ni har da cewa ya tsane ni kar ya k'ara ganina a gidansa shine Baffa yace ni da gidan nasa kuwa sai dai bayan ranshi.Kinga kuwa babu ni ba saka ran komawa." "Gaskiya kam,ai Mama ba ta kyautawa kanta ba,gashi nan Zainab na girbar abin da uwarta ta shuka mata,gashin k'uma matan babanta suke mata ba kad'an ba,ko makaranta ba ta zuwa tun da muka yi juniour candy tana nan tana musu bauta." "Hmmmm! Nauwa kayi mai kyau ma ya ka k'are bare ka shuka tsiya? Ai kad'an ma ta gani,ba itace me muni gwalo ba sun samu duniya to gashinan itama uwar tata ta tafi in da tawa taje ta barta da shan azaba." "Wallahi kuwa,ai na rasa ina tunanin mutane ke tafiya?su dinga azabtar da 'ya'yan mijinsu ko tunanin had'uwarsu da Ubangiji ba sa yi,kowa yasan rik'on d'an wani da wani akwai wahala da wuyar sha'ani,anman idan ka kau da kai kayi hak'uri ka tafiyar da shi kamar yadda zaka tafiyar da d'an cikinka sai wannan d'an ya yi maka abin da ba lallai d'an da ka tsuguna ka haifa yai maka ba.Mu saka a ranmu ba lallai sai 'ya'yan da muka tsuguna muka haifane kawai 'ya'ya ba akwai wan da zai zame maka d'a ba tare da ko alak'ar jini kun had'a ba." "Maganarki gaskiya ce Nauwa ,Allah ka ganar da mu baki d'aya." "Amin ya Allah.Ai Naj yanzu Abbanmu zai san yayi aure Momy Hasiya mace ce me kirki da hak'uri lafiya suke zaune da mijinta kafin wata shegiya ta shiga tsakaninsu kai wasu matan dai a kallesu kawai zuciyarsu babu Allah a ciki." "Wallahi kuwa Nauwwa ,to me yasa Annabi yace mata sunfi yawa a wuta? Muna da rauni da tausayi anman sai ki rasa ina na wasu matan ke tafiya?" "Shaid'an ne ya zare shi mana,mudai fatanmu Allah yasa mu fi k'arfin zuciyarmu." "Amin.Ina jinki ki bani labarin Mommy Hasiyan." "Tom shikenan bud'e kunnuwanki ki sha labari.." #Bebee'arth #Rashuna #09037093702 #Bebee'arth #Rashuna #09037093702 [3/9, 23:28] FaShuNa: BEBEE'ARTH Watpad@Rashuna KANA NAKA2024 [Allah kuma na yin nasa] (8) Kamar yadda kika sani Mommy Hasiya k'anwar Babanmu ce,uwarsu d'aya ubansu d'aya sun taso cikin kulawar mahaifansu da kuma k'aunar junansu wanda rana d'aya aka yi bikin Babanmu da Momy Hasiya a yadda muka samu labari. Mijin da ta aura Aliyu Hassan Fanda shahararran mai kud'i wan da suka ga jiya suka ga yau cikin dukiya suke fantamawa,yana matuk'ar son Mommy itama kuma tana son kayanta. Mommy Hasiya ta riga Ummanmu haihuwa sai a haihuwa ta biyu suka yi tare da Ummanmu,Mommy Hasiya ta haifi EL MU'AZ Ummanmu ta haifi Yaa MUHD, d'anta na fari kuma da ta haifa SULAIMAN. Ummanmu tun daga haihuwar Yaa Muhd haihuwa ta bud'e mata ita kuma Momy Hasiya ba ta k'ara haihuwa ba sai da suka jera haihuwarmu ni da Nabila,sai dai kuma kafin suna Nabila ta koma. Daga nan ba ta sake haihuwa ba sai akan Nasrin a lokacin su Yaa Sulaiman sun gama juniour school har da El Mu'az da yake gab'b'an girma gare shi sai suka tashi kusan tare da Yaa Sulaiman duk da tsiran shekaru kusan uku dake tsakaninsu,tun gama school nasu Daddynsu yake musu shirye shiryen tafiya Jiddah domin yin seneour school d'insu a can,bayan sun kammala su d'ora ba tare da sun waiwayi gida ba sai da shaidar kwalinsu na kammala karatu gaba d'aya,in yaso su Mommyn zasu dinga ziyartarsu akai akai. Wata d'aya kafin tafiyarsu suka je Fanda zaga dangi,wanda nima na samu zuwa a lokacin nazo hutu gidan,Fanda akwai dad'i sosai domin kuwa mun yawata mun zaga sosai da Yaa Sulaiman dan yafi Yaa El kirki shi halinsu d'aya da

Chapter 2 of 17