buɗemin gate yanzu zan fita sannan ka janye hankalin security's kada su gane"
ta ɗan russuna kamar yana gabanta tace "na gode baba"
katse wayan tayi ta juya baya tace "zaka iya fita"
kallon bayanta yayi, a hankali yazo gabanta ya tsaya, mask na fuskanshi ya cire ta yadda zata kalleshi da kyau, murmushi yayi mata, kallonshi tayi taga asalin fuskanshi, tun daga idonshi data gani jikinta yayi sanyi yanzu kuma da taga fuskanshi taji jikinta ya gama yin sanyi, wani irin wutan kyau yake dashi kamar balarabe, badan yayi hausa ba daya shigo zata rantse ba daga nigeria yake ba, maida mask ɗin yayi ya rufe fuskanshi baice komai ba kawai ya kara gyara jakan daya goya a baya ya buɗe kofan ya fita sanye da hijabinta.
Allah ya taimakeshi itama ta taimakeshi ya fita ya bar gidan ba tareda an kamashi ba, cikin ruwan saman da bai gama tsayawa ba yake tafiya, duk lokacin daya taɓa jakan ya tuna abinda ya faru sai yayi murmushi, a inda yake ɓoye duk abinda ya sace yaje ya ɓoye sannan ya koma gida, momy wacce batayi bacci ba sabida Dady da take bashi magani akai akai tana tsaye a stair tana kallon cikin gidan dake ɗauke da haske kamar rana, idanunta ya sauka akan nawal daya shigo yanzu, da sauri tace "daga ina yake?"
kasa kwanciya hankalinta yayi saida ta fita taje ɗakinshi, babu sallama ta tura kofan, da sauri yasa bindigan a kasan katifa, ta tsaya a kanshi tace "daga ina kake?"
yace "daga asibiti ina wajen Ammi"
tsaki taja sannan ta fita daga ɗakin, ta manta da kazamar gurguwan Amminshi tana asibiti, kwanciya yayi akan katifan ya rufe ido kamar me bacci, deep down yana tunanin abinda ya faru, bai taɓa zaton akwai masu taimako har yanzu a rayuwa ba sai gashi yau ta taimaka mishi, yana tunanin har bacci ya ɗaukeshi.
_Jiddah Ce...✍️_
08144818849
[17/08, 11:13 pm] +234 814 481 8849: 🌸🌸🌸🌸🌸
*SHIMA ƊA NE*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 13*
~Ibtisam yana fita ta sauke ajiyan zuciya ta kwanta akan gadon ta rufe ido, a ranta tace "thank god ya fita ba'a kamashi ba"
tashi tayi da sauri tace "amma meyasa na rufa mishi asiri? ɓarawo nefa meya...."
kiran sunanta da akayi yasa tayi shiru "Unty Ibtee? waya rufe bathroom?"
da sauri ta tashi taje ta buɗe bathroom ɗin, juya baya tayi sabida gani take kamar za'a gane abinda tayi, subhanallah tsarki ya tabbata ga ubangijin da yayi kowane halitta, tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci Annabi yusuf Annabi me kyawun halitta, hakika Allah shi yake kowane halitta idan yaga dama yayi mummuna idan yaga dama yayi kyakkyawa, suna tsananin kama da ibtisam amma wannan siririya ce bata kai ibtisam cika ba, karan hancinta yafi na ibtisam tsayi da tsini, ga wani gashin daya rufe saman idonta zara-zara baƙi wuluƙ, babu lokacin bayanin kyawun wannan yarinyar wacce a shekaru ba zata wuce 18 ba itako ibtisam 21 take, baƙin sleeping dress ne a jikinta silk yard da less a hanu da wuyan, ya mugun fito da kyawun fatarta, this is the real definition of beauty, tace "unty ibtee nace miki mu ɓuya a toilet ɓarawon ba zai ganmu ba kinki yadda tsaban tsoro kika ɓuya a bayan gado amma be shigo ba ai ko? kinsan ni bacci nayi banma sani ba"
hamdala tayi a ranta da bataji abinda ya faru ba, juyowa tayi tace "JANNAH meyasa idan bacci ya ɗaukeki a ko ina yinshi kike? jan kullum ina cewa ki daina bacci a duk inda kike amma bakya ji"
turo karamin bakinta tayi sannan tace "am sorry na daina"
tsaki taja tace "ke kika sani"
hawa gado ibtisam tayi taja duvet ta rufe har kanta, so take tayi bacci, janna dake shafa night face cream nata tace "unty ibtee amma fa cikin bacci kamar naji kina magana da wani kuma kamar shima naji yana miki reply"
da sauri ta janye duvet ɗin tana kallon janna, ta cikin madubin ta jinjina kai tace "yes ko dai mafarki nayi ne?"
ajiyan zuciya ta sauke tace "yes dear mafarki kikayi banyi magana da kowa ba"
zatayi magana tace "shii please kiyi shiru kada Abba yaji muryanmu"
tace "gaskiya saina faɗi abinda yake raina..."
tace "haba jan meyasa bakya ji ne? kinfi kowa sani ko tari akayi na kirki idan Abba yaji sai ran kowa ya ɓaci, kinfi kowa sanin idan yana gida babu me yin magana me tsayi har sai ya fita, meyasa kike son janyo mana matsala ne?"
shiru tayi tana kallonta har ta gama taja duvet ta kara rufuwa rufe ido tayi.
janna gama shafawa tayi sannan ta hau gadon, kallon bayan ibtisam tayi batason ranta yana ɓaci sabida tana bala'in sonta, a hankali ta rungumeta ta kanƙameta sosai, haka ta saba bacci tun ibtisam tana jin haushin yadda take kankame mutum idan zata kwanta har ta kyaleta sabida hakan ɗabi'anta ne, cikin sanyin murya tace "am sorry unty ibtee ba zan kara tsallake dokan Abba ba"
kullum haka take faɗa amma babu wanda ya kaita tsallake dokan, sam janna batajin magana duk abinda Abba ya hana yana fita zatayi, idan taga dama yana gida zatabi ta baya ta tsallaka katanga ta tafi yawon daya hanasu zuwa ta dawo babu wanda ya sani sai ibtisam, har ta fita har ta dawo ibtisam bata iya zama da taji muryan Abba gabanta zai fara faɗuwa, mutanen gari da mutanen gida babu wanda baya tsoron Abba sai janna wacce take tsallake dokan daya sanya a duk lokacin da taga dama, kawayenta yaran masu faɗa aji ne domin bata ƙawance da ƴaƴan talakawa, bata ɗaukan raini indai class ne babu me nuna mata domin har kawayenta kiranta suke da suna CLASSY JAAN indai dressing ne an barwa janna domin babu wacce take gaya mata dressing a school nasu, matukar tasa kaya kuma biyayya yake a jikinta, ita kuma ibtisam sauƙin kai gareta batada hayaniya batason rigima gata da bala'in tsoro batason faɗa, tanada tarin kawaye sabida sauƙin kanta harda yaran talaka tana mu'amala dasu, kawarta da tafi so sukafi shaƙuwa itace YUSURA ƴar senator ce, shi kanshi Abba yasan ibtisam tafi hakuri a cikinsu.
washe gari weekend ne babu school yau shiyasa duk suke gida, kuku sun gama girki an jera a dinning table, babu wanda Abba yake jira idan lokacin cin abinci yayi duk abinda kakeyi ya zama dole ka bari kazo kaci abinci saɓanin haka zaka fuskanci fushin shi, ibtisam da janna sun fito rike da hanun juna, duk sunyi kyau cikin simple dress ɗinsu, zama sukayi jaad da bai jima a tashi daga bacci ba shima ya fito kyakkyawa ne karamin yaro kamarsu sosai dasu, yace "good morning"
Ibtisam tace "morning jaad ya ka tashi?"
yace "lafiya ƙalau"
ya kalli janna wacce bata amsa ba yace "unty janna?"
harara ta watsa mishi sannan tace "karka sake ka kara kiran sunana idan ba haka ba saina fasa maka baki"
ibtisam tace "A,a me ya miki?"
tace "shi ya sani ai"
kallon jaad tayi tace "me kayi mata?"
cute eye's nashi ya zuba mata, tace "me kayi mata?"
yace "just because dan naga tana haura katanga zata fita shine...."
gyaran murya Abba yayi, tsit wajen ya zama babu wanda ya kara ko tari, fuska ba walwala ya zauna duk suka gaisheshi a tare, a tsanake yace "lafiya"
babu wanda ya kara ko numfashi me karfi, breakfast suka fara bai tambaya ina mami ba, sam baya tambaya ina wane, a cewarshi duk wanda yaci abinci dan cikinshi yayi wanda baici bama dan kanshi baya lallashin mutum.
jaad ne ya kalli ibtisam itama ta kalleshi, alama yayi mata ina mami?
itama tayi mishi alaman bata sani ba, zai kara mata wani alaman Abba ya ɗago kai zai ɗau ruwa ibtisam a tsorace ta maida hankali kan abincin kamar batayi komai ba.
janna ta kalli agogo karfe tara da rabi yayi kuma yau dole saita fita ko me zai faru sai taje birthday party ɗin classmate ɗinta saarah satan kallon Abba tayi taga baya kallonta, karamar wayarta ta ciro daga inda ta ɓoye a aljihun wandon jikinta me faɗi, numbern da yake dialing call ta shiga ta tura text, kara ɓoye wayan tayi ganin time yana tafiya tayi breakfast da sauri sauri, tissue ta zara ta goge bakinta sannan ta tashi zata tafi, cikin rashin sa'a karamar wayar ta faɗi ashe be zauna da kyau a cikin aljihun ba, dafa kirji ibtisam tayi ta waro ido ganin Abba yaga wayan, jaad dafa kai yayi ya rufe ido sabida yasan yau akwai tashin hankali a gidannan, jikinta yana rawa tasa kafa zata taka wayar cikin wani irin tsawa Abba yace "idan kika sake kika taka saina kasheki da duka"
cak ta tsaya da kafarta jikinta yana rawa tana kallon abban da har jijiyan kanshi ya tashi, cikin tsananin ɓacin rai yace "AISHA? AISHA? AISHA?"
mami dake kwance akan gado cikin zazzaɓin tsoron da jiya ta shiga da daddare sanadin ɓarawon daya shigo taji muryan Abba yana mata kiran da idan yayi to fa babu lafiya, ta dafa kirji tace "na shiga ni Aisha me kuma ya faru?"
sauka tayi a gadon bata cire bargo a jikinta ba sabida zazzaɓi ta fita, ganin janna a tsaye gaban Abba shima yana tsaye tace "me kuma janna ta kara yi yau? janna zata kara min hawan jini"
durkusawa tayi tace "gani"
kallon janna yayi yace "kinga uwarki ai ta durkusa ke kuma kina tsaye kina nema ki haɗa kirji dani"
a hankali ta durkusa kusa da mami, ya ɗauki wayan sannan yace "me wannan?"
mami tace "waya ne"
cikin tsawa yace "kenan za'a iya tsallaka dokan dana aje a gidana? sau nawa nake cewa kada wani ya rike waya a cikinsu? kina sane suke rike waya?"
ta girgiza kai, cikin zazzaɓi tace "wallahi ban sani ba ban san janna tana rike waya ba"
ya kalli janna sannan yace "ke tun yaushe kika fara rike waya a gidannan?"
tace "ji..ji.ji"
marin daya sauka a gefen kumatunta yasa taga taurari a idanunta, yace "zaki faɗamin ko saina taka wuyanki?"
tana rike da kunci tace "jiya ne..."
duka ya fara mata cikin zafin rai yace "karya zaki min? karya zakimin janna?"
ihu take yi tana neman taimako, jaad da ibtisam jikinsu ya fara rawa sun kasa zuwa su karɓi janna sabida Abba baida sauki, mami kuma ihun da janna take yi yana kara ɗaga mata hawan jininta saima jiri da take ƙara ji fiyeda na jiya da dare, saida ya tabbatar ta daku kafin ya buga wayan da kasa, ya cire sim ɗin ya kakkarya sannan ya wurgar da wayan bayan yayi raga-raga, tsallakata yayi ya barta kwance a wajen tama kasa kuka sai rike hanunta da take ji kamar ya karye tayi, sai a lokacin ibtisam tazo da gudu itada jaad suna ɗaga ta, bakinta ya fashe yana jini, ibtisam tace "mami bakinta jini yake"
mami tace "ibtee me zan faɗawa janna? ta maida duka ba komai ba a wajenta kullum tana cikin shan duka a wajen Abbanku amma ba zata nutsu ta daina yin abinda ze sa ya dake ta ba? yaushe rabon da Abbanku ya dake ki ibtee? keba mutum bane? bakya son rayuwar ƴanci ne kema? kin hakura amma ita batada hakuri kullum tana cikin aikata laifi bayan tasan koni tsoronshi nake, nida ba ƴarshi bama ji nake kamar na gudu na bar gidan bale ita daya haifa a cikinshi"
gwada ɗaga hanun da janna take rike dashi tayi, ihu tayi da alama hanun ya karye, tace "innalillahi janna meyasa kike nemawa kanki ciwo ne?"
ta kalli jaad tace "jeka kira Ahlam yazo mu kaita asibiti"
da gudu ya tashi yaje ya kira Ahlam, cikin dressing na bodyguard yazo tsaye yayi a kansu yace "meya sameta?"
tace "dukanta Abba yayi kuma ina ganin hanunta ya karye mu tafi asibiti kawai"
yace "okay"
ibtisam tace "mami ki kawo kuɗi mu kaita dole zasu nemi kuɗi"
girgiza kai tayi tace "wallahi banada kuɗi ibtisam a hanuna, kuma nasan Abbanku ba zai bada ba, bari na ɗauko gold ɗina Ahlam ya siyar saiku kaita dashi"
tashi tayi har amai amai take ji dauriya kawai take yi, ɗakinta taje ta buɗe drower ɗin da take aje gwala-gwalanta waro ido tayi ta dafa kirji, batasan lokacin data saki ihu ba, tare suka shigo Ahlam ne a gaba sukaga tana shirin faɗuwa, ibtisam ce ta riketa tace "mami what happened to you?"
tace "ibtee babu sarƙana na gold ko ɗaya kuma sune kaɗai abinda na mallaka a a duniya na dukiya ibtee ɓarawon jiya ya kwashe"
ibtee tayi shiru, kwantar da ita tayi akan gadon sannan tace "insha Allah zaki samu wanda ya fisu mami"
tace "ya zanyi Ibtee? yanzu dame za'a kai janna asibiti?"
tayi shiru, mami tace "ki ɗau gold naku ki kaita dashi"
tsayawa tayi sabida babu ko ɗaya ta tattara ta baiwa ɓarawon da a yanzu gani take yayi mata asirine yasa ta bashi komai sannan ta rufa mishi asiri, mami tace "lafiya? meyasa kikayi shiru?"
tace "ba komai bara naje na duba"
tafiya tayi zuwa ɗakinsu, tana shiga ta jingina bayanta da kofan tayi shiru, a ranta tace "anya ba aikin asiri bane yasa na tattara komai na bashi?"
shiru tayi, tunawa tayi da akwai kuɗi a jakan janna domin bata rabo da manyan kuɗi, buɗe jakan da janna take ajiya tayi sannan, waro ido tayi ganin daloli ne kwance dal a cikin jakan masu yawan gaske, da mamaki tace "aina janna ta samu daloli haka? Abba baya bamu kuɗi hasalima cewa yayi kuɗi yana lalata yara janna ina ta samu kuɗi haka?"
ɗaukan uku tayi sannan ta rufe sauran ta aje a inda ta gani, fita tayi ta samu mami tace "mami wallahi har namu an sace banga komai ba"
mami tace "ya Allah ka tsinewa ɓarawon daya shigo ya rabani da gold ɗina, Allah ka tona asirinshi ko a wani wajene wallahi idan na ganshi saina wulaƙanta rayuwarshi, saina sa anyi mishi hukunci daidai da abinda ya aikata"
shiru ibtisam tayi, saida mami ta gama sannan tace "zamu tafi da ita Ahlam yace akwai kuɗi a wajenshi"
tace "to ibtee ba sai na faɗa ba nasan zaki kula da ita"
fita ibtee tayi ta samu janna ta gama galabaita har ta gaji da kukan tayi shiru, taimaka mata tayi ta tashi sannan tasa mata guntun hijabin itama tasa nata, jaad ne ya riketa shima suka fita ahlam yana gaba, mota ya buɗe musu janna sai ɗingishi take har suka shiga motar Ahlam yaja suka fita a gidan, asibiti aka kaita Dr yana gani yace ta samu karaya a hanu, fara ɗaure karayan akayi banda ihu babu abinda janna take yi, Ibtee sai sannu take mata tana jin kamar tayi kuka itama, da haka har aka gama aka bata magani tasha sannan ya wanke ciwon da taji a baki, duk inda taji ciwo saida yasa spirit ya wanke sannan ta fara jin sauki banda kanta dake ciwo, a hankali suka sata a motan duk suka shiga Ahlam ya fara tada motan amma yaki tashi, ya fito domin duba meya samu motan baiga komai ba ya koma yana tadawa bai tashi ba, tsaki yaja yace "me matsalan motar nan?"
Ibtisam tace "yaki tashi ko zamu kira me gyara?"
dafa kai yayi yace "wallahi bansan meyasa motar nan taki tashi ba lafiya ƙalau kuma take"
fitowa zaiyi domin kara dubawa yaji an fara turasu, ta cikin madubi ya kalli wanda yake turawan, nawal ne sanye da kananan kaya riga fari da wando blue jinx, yasa picap a kanshi fuska babu walwala kamar kullum, motan ya tashi sakamakon turasu da yayi, murmushi ibtisam tayi tace "kaga wani ɗan albarka ya tura motar kuma ta tashi"
Ahlam yace "gaskiya mutumin kirki ne bamu rokeshi ba yayi abinda ya dace"
sauke glass tayi sannan tasa kanta tana lekawa domin zataso taga wannan me taimakon da ba'a rokeshi ba, ido huɗu sukayi da nawal da sauri ya kauda kanshi, da gudu yaja motar zai fita tace "wait Ahlam wait"
yace "saide kiyi hakuri idan na tsaya motan zaiki tashi"
duk yadda taso ya tsaya bai tsaya ba tafiya sukayi, nawal ajiyan zuciya ya sauke sannan ya tafi, Ammi an kwantar da ita a ɗakin da ake kwantar da wanda aka yiwa surgery, office na dr ya shiga bayan anyi mishi iso, ya samu dr zaune akan kujera ya zauna sannan yace "dr ina Ammina?"
dr yace "tana nan lafiya aiki ya kammala saide har yanzu ba zata iya tafiya kamar yadda mutane suke yi normal ba, dole saita rinƙa rike sanda komai yayi yadda akeso, amma ba zamu baka ita ba hasalima ba zakasan inda take ba har sai ka biya kuɗin aiki"
jakan bayanshi ya sauke ya aje a gaban dr yace "ga kuɗin aiki"
da mamaki ya kalleshi sai kuma ya kalli jakan, buɗewa yayi yaga kuɗi ne cike nak da jakan, ya kara kallon nawal kallon ina ya samu kuɗi haka?
nawal yace "ina Ammi na?"
dr ya kira waya, babu jimawa wata nurse ta shigo, yace "kaishi ɗakin new patient ɗinmu da akayi surgery"
tace "okay sir"
tashi nawal yayi tana gaba yana baya.
_Jiddah Ce...✍️_
08144818849
[17/08, 11:13 pm] +234 814 481 8849: 🌸🌸🌸🌸🌸
*SHIMA ƊA NE*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 14*
~Ɗakin da ammi take kwance suka shiga, da mamaki yaga wani saurayi a kusa da ita yana kula da ita tamkar mahaifiyarshi, jikinshi a sanyaye ya karasa tana zaune yana bata ayaba da kanshi, murmushi tayi ganin nawal yazo, tace "nawal kazo?"
idonshi ya cika da hawaye a hankali ya sunkuyar da kai yace "eh"
tace "kada kayi kuka nawal gashi na samu lafiya, wannan shine yake kula dani tun safe yazo duba ƴan uwanshi ne anan asibitin amma an sallamesu a lokacin ake fita dani daga ɗakin tiyata yace ba zai iya tafiya ba ganin babu kowa a kaina"
kallonshi yayi kyakkyawa ne kuma yanada kwarjini jikinshi me kyau, ya karaso ya mika mishi hanu suka gaisa, cikin sanyin muryanshi da rashin hayaniya yace "na gode"
Ammi tace "sunanshi KAMAL"
a hankali yace "na gode kamal"
murmushi yayi yace "ba komai nawal tunda kazo bari na tafi dama ana kirana insha Allah gobe da safe kafin a sallameku zanzo na kara dubata"
a hankali yace "to na gode"
sallama kamal ya yiwa ammi sannan ya tafi, zama nawal yayi a inda ya tashi yace "ammi ya jikin?"
tace "jikina da sauki nawal, na tashi na ganni da kafafun roba nawal dr yace kaine ka kawoni kuma kace zaka je ka nemo kuɗin aiki shiyasa baka zo lokacin da aka gama aikin ba"
yace "eh naje neman kuɗin ne kuma na samu harma na biya"
tace "nawane kuɗin nawal?"
yace "dubu hamsin ne na basu dubu arba'in saura goma"
tace "Allah sarki nawal aina ka sami kuɗi har dubu arba'in?"
"aikin karfi nayi Ammi kuma Allah ya rufamin asiri na samu"
tace "nawal duk halin da zaka shiga kada ka saci abin mutum, nawal kada ka ɗauki hakƙin wani ka zama mutumin kirki me neman halak"
jinjina kai yayi alaman to, murmushi tayi tace "ga ayaban da kamal ya siya kaci ga ruwan gora da lemu nasan bakaci komai ba"
be musa ba dan rabonshi da abinci tun ranan daya kawota asibitin, a hankali yake ci tana kallonshi kamar tayi kuka sabida tausayin da yake bata, a wajen ya kwana yana zaune akan kujera ita kuma akan gadon tayi bacci, washe gari yayi salla ya taimaka mata tayi salla itama, dr yazo ya dubata yace anjima ze sallamesu, da mamaki saiga kamal kamar yadda yace zai zo ya dubasu ya shigo da abinci a kula da flask na shayi, nawal ne ya karɓa mishi suka karasa suka zauna akan tabarma, gaishe da ammi yayi ta amsa cikin fara'a sannan suka gaisa da nawal, shiru nawal yayi a gefe domin bai saba sakewa a wajen mutum ba, sai wajen ammi kawai yake iya sakewa, kamal tun jiya ya lura da hakan shiyasa ma bai damu ba shi da Ammi kawai suke hira nawal saide ya bisu da ido kawai baya cewa komai.
har zuwa lokacin da dr yazo ya basu takaddan sallama, kamal yanada karamin mota a ciki suka shiga yace zai kaisu gida, sun hau titi yace "saide ammi baki faɗamin ina unguwan ku ba wani gida kuma zan kaiku"
kallon nawal tayi shima ya kalleta, murmushi tayi tace "low-cost"
yace "okay"
nawal yana gefenshi yayi shiru yana tunanin duniya, har suka isa unguwan nawal be sani ba, kamal ne yace "mun shigo unguwan Ammi wani gida ne?"
tace "gidan Alhaji Alhasan medara"
da mamaki yace "Alhaji Alhasan daya nemi takaran gomna?"
cikin sanyi tace "eh"
kara kallon Ammi yayi sannan ya kalli nawal yace "kai ɗanshi ne?"
ammi zatayi magana nawal ya girgiza kai yace "A,a ni megadinsu ne aiki nake a gidan"
yace "okay okay na gane"
shiru Ammi tayi jikinta yayi sanyi, har kofan gidan ya tsaya dasu, fitowa sukayi Ammi bata saba tafiya da kafan ba tana ɗingishi sosai har suka shiga kamal yana rike da kayan, a kofan megadi suka tsaya inda nawal yake zama ya karɓi kayan yace "mun gode Allah ya saka da alheri"
yace "ameen zan koma amma zamu iya zama abokai? sabida ɗabi'unka sun birgeni"
shiru yayi sabida bayason aboki sam gashi kamal ɗin ya mika mishi hanu alaman su gaisa, sai kallon hanun yake ya kasa gaisawa dashi a matsayin aboki, Ammi ta katse shirun tace "me aciki? kun ma zama abokai"
kallon Ammi yayi ta mishi alama da eh, a hankali yasa hanu ana kamal ɗin suka gaisa, kamal yace "na gode"
murmushi kawai yayi, numbernshi ya karɓa sannan ya musu sallama ya tafi, Ammi tace "muje ka kaini ciki nawal tsoron shiga ciki nake"
hanunta ya rike a hankali take tafiya shima yana janta a hankali sabida ɗingishin da takeyi, har suka isa main parlour na gidan, ganin dady a falon saida jikin nawal ya fara rawa tsaban tsoro, ga momy dasu naseer zaune suna kallo, samha ce ta kallesu tace "dady dama waɗannan basu bar gidannan ba?"
shiru yayi, momy kuma ta zabga musu wani mugun kallon da yasa nawal damƙe hanun Ammi, naseer dake rike da remote yace "what the hell think you are doing here?"
cikin tsawa yayi maganan, Ammi tace "ka kaini ɗaki nawal"
jan hanunta yayi zasu wuce dady ya daka musu tsawa yace "wait"
tsayawa sukayi, Ammi ta ɓuya a bayan nawal sabida wallahi tsoro take ji, yace "ina kuke tunanin zaku shiga min da wannan dattin jikin naku? tukunna aina ta samu kafa?"
momy cikin mugun kishin ganin Ammi da kafafu tana tafiya hakan yasa diri da kyawunta ya kara bayyana sosai dama ashe dan a zaune take baduga wutan kyau da take dashi ba, saida ta tashi taga asalin diri da kyau, idonta rufe dan kishi tace "Alhaji ya zama dole ka saki wannan miskinyar matar"
girgiza kai yayi yace "no naja ba zan iya sakinta ba sabida zai taɓamin takaran da zanyi zuwa gaba sannan idan na saketa na tabbata akwai abokin gabana da zai iya lallaɓawa ya aureta sabida su ɓatamin rayuwata na gaba, zan zauna da ita amma saita gwammace bata sanni ba"
juya baya tayi batason ko ganin Ammi domin wani harbawa zuciyanta yake yi, ji take zata iya kashe Ammi, dady ya nuna musu hanyan waje yace "ku koma bakin kofa ɗakin megadi acan zaku rinƙa zama da kai da ita, ba zan saketa ba idan kunga zata iya yawo da aurena ku tafi idan ba zata iya ba ku zauna a ɗakin megadi"
nawal zaiyi magana Ammi ta damƙe hanunshi tace "A,a nawal shi ɗin mahaifinka ne, ba zan bari yana faɗa kana faɗa ba, nan shine asalinka kuma ba zan cuceka na rabaka da asalinka ba koba komai a gaba zai maka amfani"
shiru yayi sabida ko karen hauka ya cijeshi ba zai iya musu da Ammi ba, hanunshi taja suka fita, ɗakin megadin ya share sannan ya shimfiɗa bargo a kasa ya bar mata katifan, ya raba musu tsakani da zanin gado sabida ita macece shi kuma namiji duk da itace ta haifeshi akwai privacy da dole zata nema watarana, kallonshi take yana aikin, a hankali ya ɗago suka haɗa ido murmushin karfin hali daya saba yayi mata sannan yaci gaba da gyaran har ya gama ya kwanta a kasa ya ɗaura kanshi akan kafarta ya rufe ido babu irin tunanin da baya yi, itama Ammi tunanin take.
Janna bacci take yi na wahala ibtisam tana gefenta tayi tagumi, sam zuciyanta ya kasa walwala tunanin wannan ɓarawon data ganshi take yi, tunawa take da lokacin daya ɗaga mask na fuskanshi sabida ta ganshi,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 17