kafa ɗaya akan ɗaya, suna haɗa ido tayi baya zata koma yace "shigo"
jikinta yana rawa tace "Abba ka yafeni dan Allah wallahi tsautsayi ne"
tashi yayi yace "tsautsayi? meyasa be faru akan ibtisam ba itada ta zauna a gida?"
girgiza kai take ganin yana nufota, ta haɗa hanu biyu tana rokonshi, buɗe kofan tayi zata fita a guje ya cafko hanunta, ball ya fara da ita yana huci yace "ke kin san matsayina a garinnan kike kokarin zubar min da mutunci janna? kin san neman takaran senator nake yi amma kike zuwa party kina rawa da maza janna?"
ihu take yi tana neman taimako, kiran mami da ibtee ta fara tana neman taimako, daga karshe ta fara "jaad jaad kazo ka taimakeni zai kasheni"
a tare suka fito, ibtisam ganin janna kwance tana ihun azaba Abba yana takata taje da gudu tana jan janna daga kasan, tace "Abba dan girman Allah ka kyaleta haka Abba kada ta mutu"
yace "gara ta mutu da wannan abinda take yi, party zataje da dare su haɗa tana cikin maza? janna ashe wuyanki ya isa yanka?"
rungumeta ibtee tayi yana huci ya bar wajen, mami kallonta tayi har ta rame sabida yunwa da wannan dukan taja tsakin takaici kawai ta juya ta koma ɗakinta, ibtee da jaad ne suka ɗagata suka kaita ɗaki, akan gado suka kwantar da ita kamar batada rai ibtee ta shiga bathroom ta haɗa mata ruwan wanka me zafi, fitowa tayi suka kara ɗagata bataso a taɓa jikinta duk ciwo yake mata, Ibtee tace "kiyi wanka bari na kawo miki abinci"
fita tayi jaad yace "gaskiya unty Ibtee sai an kira dr kinga yadda jikinta ya farfashe kuwa? gashi bataso a taɓata sabida ciwo"
tace "eh zan kira dr a bata magani ko zata warke"
abinci ta kawo mata da shayi me zafi sannan ta kira aka faɗi maganin da zata bata, ta fito daga wankan ko towel ɗin bata iya cirewa ba ta faɗa gadon bacci takeji kamar me, ibtee tace "ba bacci zaki fara ba tashi ki daure kici abinci sai kisha magani ki kwanta"
tace "ba zan iya ba ki barni nayi bacci jikina ciwo"
tace "a,a tashi"
tashi tayi badan taso ba tasha shayin taci abincin kaɗan sannan tasha magani da towel ɗin ta kwanta bacci me nauyi ya ɗauketa.
ido Ibtee ta zuba mata tana cewa "meyasa yake haka? babu wanda yasan kamanninshi amma ni na sani, saide ba zan iya taimakawa ƴan sanda domin su kamashi ba, meyasa? meyasa nake jin ba zan iya tona mishi asiri ba bayan har janna yayi kidnapping? shin meyasa koda yaushe idan na zauna sai tunaninshi nake? me haɗina dashi ko bacci idan inayi fuskanshi nake gani cikin mafarkina, me zaisa na so ɓarawo? wanda yazo ya firgita mahaifiyata? wanda mahaifina yake nemanshi ruwa a jallo"
a wajen ta kwanta tana kallon saman ɗakin ta kasa daina tunaninshi.
janna saida tayi kwana uku tana jinya kafin ta samu sauki, yau zasuje school da ita da ibtisam sunyi shiri cikin uniform nasu green and white, janna tana rungume da jakanta na baya wanda ta goyashi a gaba, tafiya suke ibtisam ta zama shiru bata magana sai yawan tunani, janna wacce tun ɗazu take mata magana bata jita ba da karfi tace "unty ibtee magana fa nake miki wai me yake damunki ne? me kike tunani ne? kiga fa har kin rame"
murmushi tayi tace "ba komai janna"
tace "to shikenan ba zan takuraki ki fadamin ba"
jaad da jakanshi shima a rataye ya fito yana sanye da uniform irin nasu, yace "unty ibtee rikemin jakana na ɗauko wani abu na manta"
karɓan jakan tayi suka fita shi kuma ya koma da gudu ya ɗauko abinda ya manta kafin ya dawo ya shiga, Ahlam shi yake kaisu ko ina sabida Abba ya yadda dashi sosai, duk wani sirrin inda zasuje p.b Ahlam ya sani, shiba ɗan uwa bane amma yaddan da Abba yayi dashi yafi na ƴan uwa sabida Ahlam baya taɓa saɓa magananshi, driving yake a hankali sabida ibtisam bata fiyeson ana gudu da mota ba, shi kuma yana girmama ra'ayin kowa a gidan, Ibtee ta ɗauke kanta tana kallon gefen titi innocent face nata ya kara zama very innocent sabida tunanin daya dagula lissafinta ya hana ƙwaƙwalwanta samun sukuni harma yana taɓa gangar jikinta, lumshe ido tayi tunawa da murmushin daya mata a lokacin daya ɗaga mask ɗin, janna da kallo ta bita a ranta tace "koma me yake damun unty ibtee Allah ka saukaka mata kasa ya zamo me sauki a gareta"
har suka isa makaranta basuyi wani hira ba kamar yadda suka saba, jakanta ta rike da flask na abinci suka shiga cikin babban makarantarsu me masifan kyau da tsada, jaad ya wuce ɓangaren yara janna ta shiga class nasu ibtisam ma ta wuce class nasu, akan benci ta ajiye jaka da flask sannan ta zauna ta kwantar da kanta tayi shiru, kawarta yusra taga shigowanta amma ita da alama batasan yusra tazo bama, a gefenta ta zauna tace "Ibtee meya sameki?"
ɗago kai tayi tace "yusra kin fito?"
tace "eh na fito naga shigowanki amma meya sameki kin zama wani kala"
ta girgiza kai tace "ba komai kawai bana ɗan jin daɗi ne"
tace "Ayya sorry Allah ya baki lafiya"
amsawa kawai tayi da ameen.
labarin manya manyan satan da akeyi yanzu shi yake karaɗe gari, yayinda aka addabi manya da masu kuɗi a garin sata cikin salo akeyi, Abba ne yake safa da marwa yana goye da hanunshi a baya, zufa duk sa wanke mishi fuska cire babban riganshi yayi, sam ya kasa zama ga abokanshi da suke zaune akan kujeran meeting kowanne da abin magana a gabanshi, da alama meeting na gaggawa ne sabida kowa hankalinshi a tashe yake, gomna dake zaune a high table ya kalli Abba yace "ka zauna mana mu samu mafita"
a fusace yaje inda yake buga kujeran gabanshi yayi kamar zai ɓalla yace "mafita? muna garinnan har mu bari wannan satan yayi yawa haka? kasan meyamin ne?"
waya ya ciro a aljihu ya nunawa gomna alhaji sammani sannan ya nunawa kowa yace "kunga fa babban company ɗina ya kona sabida naki bada kuɗin fansan yaran makaranta daya kwashe, kasan yadda na tara kuɗin wannan company kasan nawa na kashe? talakawa suna can babu ruwa a wurare da dama babu magani a asibiti duk na kwashe kuɗin a lokacin da nake mulki na siya babban company ɗin kera motoci masu tsadan da babu a nigeria ni kaɗai na mallaka shine zai ƙona? ina jami'an tsaro? ina sojoji? ina masu kula da rayukan mutane da dukiyoyinsu? a addabi talaka sannan a addabemu to miye banbancinmu da talakan a yanzu tunda muna ɗar-ɗar kowa yana tsoron fita muna gudun kada ayi kidnapping namu, abin ma ba iya hanya ba har gida, har cikin gidana nida nake former governor ya shiga yayi sata, mataimakinka shima ya shiga har gidanshi yayi sata, mutum ɗaya ya gagaremu?"
shiru sukayi kowa yana zaune ya rasa abin faɗa, Abba ya fesar da iskan bakinshi sannan yace "idan ku ba zaku iya ba, ni zan cire a cikin dukiyana na siyawa jami'an tsaro da sojoji kayan yaki domin su yaki wannan addababben ɓarawon, sabida ba zan iya jure asaran da yake sani ba, na gama magana"
fita yayi da babban rigan a hanunshi, gomna yayi shiru shima abin da yana damunshi ace ɓarawo ɗaya ya rinƙa sace ƴaƴansu yana karɓan manyan kuɗaɗe haka?"
Abba motarshi ya shiga da kanshi yake driving yana huci, gowslow daya haɗu yasa ya tsaya yana jira motocin gabanshi su wuce, jarida aka bashi, ya karɓa ya biya kuɗi sabida shi ma'abocin karanta jarida ne, yana buɗewa yaga hoton mask man wannan babban ɓarawon da ko ina yanzu magananshi ake, yaga jaridan yayi cikin tsana ya watsar a waje.
bayan an tashi daga makaranta suna hanyan dawowa suma gowslow ya tsayar dasu, jarida kamar kullum da aka saba basu aka mika musu, janna ce ta siya ibtisam kuma tayi shiru, buɗewa tayi a lokacin aka basu hanya suka wuce, karantawa ta fara, tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un"
Ibtee tace "menene janna?"
tace "wannan ɓarawon ya ƙona babban company ɗin Abba"
dafa kirji Ibtee tayi ta karɓi jaridan tana dubawa, tace "Innalillahi mun shiga uku"
janna ta dafa kai tace "dan Allah waye wannan? me mukayi mishi?"
ibtisam shiru tayi tana kallon hotonshi da aka ɗauka fuska da mask, babu wanda yasan wannan fuskan sai ita, janna tace "Allah ko sau ɗaya ka nunamin fuskan wannan ɓarawon dako saina kasheshi mugu azzalumi me hana mutane kwanciyar hankali"
Ibtee idonta har yanzu akan hoton, har suka isa gida hanunta rike da jaridan ta kasa yagawa, Abba ne a falo yana zaune ya dafa kanshi idonshi a rufe, tare suka shigo, duk suka kalleshi basu taɓa ganin Abba cikin damuwa kamar na yau ba, a hankali suka wuceshi sabida suna tsoron mishi magana, suna shiga ɗaki janna tace "kiga yanda Abba ya shiga damuwa, ɓarawon yaji daɗi kenan daya sashi cikin damuwa?"
shiru ibtee tayi, salla sukayi kafin suka canja uniform sukaci abinci, ibtee ce ta fara shigowa ɗaki ta zauna a bakin gado ta rike jaridan da hotonshi yake kai, maimakon taji tsanarshi sai taji hawaye yana zuba daga idonta yana sauka kan jaridan, a hankali ta shafa hotonshi tace "meyasa banajin tsanarka duk cutan mutane da kake? meyasa ka kasa barin zuciyata ta huta? meyasa ne? ko sunanka ban sani ba amma ka tsaya a zuciyata"
rungume hoton tayi ta fashe da kuka, knocking akayi da sauri ta wurgar da jaridan ta juya ta share hawayen, janna ce ta shigo tace "unty ibtee mami tace muje tana neman...."
shiru tayi ganin kamar ibtee tana share hawaye, da mamaki ta karaso tace "unty ibtee meya faru kike kuka?"
tace "ba kuka nake ba kwari ne ya faɗamin a ido da kyar na cireshi"
tayi maganan tana murmushi, tace "okay na zaci kuka kike muje mami na nemanmu"
tace "okay"
tashi tayi ta tura jaridan a karkashin gadon da kafa sannan suka fita.
nawal ɗakin da yake aje kuɗin yanada nisa da unguwan da yake duk abinda ya samu a wannan ɗakin yake ajewa, baya taɓa komai sai idan yaji ana neman taimako a wani waje to anan ne zai taɓa kuɗin ya kai inda ake bukata, yana siyan magunguna ya kai asibiti, sannan a ɓoye yake biyan masu aiki suyi aikin ruwa a kowane unguwan da yaga sunada buƙatan ruwa, naira biyar bai taɓa ci ba koda zai mutu bashida lafiya baya taɓa wannan kuɗin domin kullum maganan Ammi shine kada kaci haram duk kankancin halal yafi haram, shaƙuwa sukayi da kamal wanda shima iyayenshi ba masu karfi bane, saide duk yadda suka shaku kamal bai san komai akan satan da yake ba.
daga daƙin ya fito ya rufe sannan ya kama hanyan tafiya gida, sanye yake da jampa yayi bala'in kyau, a nitse yake tafiya sabida baida hayaniya daga tafiyanshi zaka gane, gidan da kullum idan zai zo sai gabanshi ya faɗi sabida tashin hankali da yake cikin gidan ya nufa, kullum cikin faɗa suke da junansu kuma idan yasa baki zasu mishi taron dangi suci mishi mutumci shiyasa bayasa baki, yana shiga ɗakinsu da Ammi ya wuce direct, tun daga bakin kofa yaji tana sheƙa amai baisan time ɗin daya karasa da gudu ba, ta galabaita da alama ba tun yanzu ta fara aman ba, kwanciya tayi a kasa tana rike da cikinta sai nishi take a hankali tana kiran nawal, riketa yayi ya ɗagota yace "ammi bakida lafiya baki faɗamin ba ammi meyasa?"
tace "nawal ka kaini asibiti zan mutu"
karamin wayanshi ya ɗaga ya kira kamal yace "ina kake? please kazo yanzu da mota ammi babu lafiya"
kamal yace yana hanya zaizo yanzu, sannu yake mata har kamal yazo suka riketa suka sata a motan, tafiya sukayi zuwa asibiti, text aka fara mata domin gano me yake damunta, gado suka bata sannan kamal ya zauna kusa da ita shi kuma nawal dr tace ya sameta a office, wajen zama ta nuna mishi tace "zauna mana"
zama yayi yana kallonta, takaddan text ta bashi tace "mamanka na ɗauke da cikin wata huɗu"
a razane ya kalleta, ta jinjina kai tace "tabbas gwajinmu ya tabbatar mana haka"
ya kasa ɗauke idonshi akanta, tace "a rinka kiyaye ɓacin ranta, sannan a rinƙa sanin me zataci a kiyaye abincinta ta rinƙa cin na masu ciki"
abinda ya fito daga bakinshi shine "a zubar da cikin"
da mamaki ta kalleshi tace "batada aure ne? me zaisa a zubar da cikin?"
yace "tanada aure banason cikin a zubar dan Allah"
girgiza kai tayi tace "cikin ya kai wata huɗu zata iya rasa ranta idan akayi yunkurin zubarwa, saide kasa hanu koda an zubar idan ta mutu ba zakayi magana ba"
ido kawai ya zuba mata, jikinshi yana rawa, tace "ka amince?"
girgiza kai yayi yace "ba zan iya risk na rayuwar Ammi ba"
tashi yayi kawai ya fita, ɗakin da take ya shiga, kamal ganin ya tsaya a jikin kofa yayi shiru yana kallon Ammi yace "nawal menene? me yake damunta?"
a hankali yace "ciki take dashi"
kamal yace "ciki kuma? amma sunyi gwaji me kyau?"
gyaɗa kai yayi ya karaso a hankali ya zauna, ya kalli kamal sannan yace "kamal banason wannan cikin"
kamal ya rasa abin cewa, nawal yace "so nake a zubar da cikin"
kamal yace "bakada hankali ne nawal? bakada hankali ne zakace a zubar da ciki kayi hauka ne? ina maka kallon me hankali ashe baka dashi"
ya girgiza kai hawaye yana sauka yace "kamal AKWAI DALILI shiyasa banason cikin, nasan bakasan komai a kaina ba, kamal yau zan faɗa maka waye ni"
hawayen ya share amma sun kasa tsayawa, yace "sunana Nawal Alhasan medara"
da mamaki kamal yace "what? kenan kai ɗan Alhaji Alhasan ne?"
gyaɗa kai yayi yace "eh amma ni ba asalin ɗa bane kamar kowa, ni shege ne bada aure aka haifeni ba"
ya fara faɗa mishi komai saida yazo karshe ya fashe da wani irin kuka me taɓa zuciya, a hankali kamal ya share hawaye yace "dan Allah ka daina kuka nawal"
yace "ta yaya zan daina kuka ammi nada ciki zata maimaita kuskuren da tayi a baya, ko makiyina bana fata Allah ya jarrabeshi da irin jarabawata, tanaso ta kara haifan wanda babu uba su fuskanci kalubalen rayuwa?"
yace "kayi hakuri nawal..."
Ammi dake kwance tace "nawal ka bani ruwa"
a hankali ya tashi ya siyo mata ruwa, bata yayi tasha, sannan tace "ɗagani zan zauna"
ɗagata yayi yana ɗauke kanshi bai son su haɗa ido, tace "nawal kalleni"
kin kallonta yayi, ta riko hanunshi tace "nawal ka kalli Amminka"
a hankali ya ɗago manyan idonshi ya kalleta sannan ya kara sunkuyar da kai, tace "nawal na cutar da kai tunda na haifeka babu aure, amma inaso ka sani wannan cikin dake jikina da aure, Alhaji Alhasan kullum idan ka fita yana zuwa yamin fyaɗe a cewarshi ni matarshi ce, nawal fyaɗe yake min amma ina kunyar faɗa maka sabida ban san ta yadda zan fara ba, nawal kullum sai yazo yamin fyaɗe har yau saida ya shigo ɗakin ba tareda kowa ya sani ba a gidan, yana tura matarshi unguwa sabida ya samu daman zuwa wajena, nawal banason wannan cikin a zubar nawal sannan zan kai kotu a rana aurena da Alhaji Alhasan"
sauka zatayi a gadon ya riketa durkusawa kasa yayi yace "dan girman Allah Ammi kada kiyi yunkurin zubar da wannan cikin, Ammi dr ta tabbatar min zaki iya rasa ranki kuma kin san nawal ba zai iya rayuwa babu Amminshi ba, Ammi kimin rai kada ki kashe kanki ta hanyar zubar da wannan cikin"
tace "nawal ka tashi banaso kana rokona abu, nawal zan iya maka komai a rayuwa sabida na cutar da kai tun kana ciki, nawal ban san irin wahalan da zansha a gidannan da cikinnan bane ba zai taɓa kula dani ba"
yace "ammi zan yiwa lawyer magana zamujw gidan tare saiya kula da cikin kamar yadda yake kula da cikin matarshi sabida cikin dake cikinki ɗanshi ne kamar sauran ƴaƴan gara ni ba kamar su nake ba"
kukan da suke yasa kamal kuka sabida tausayi.
_Jiddah Ce....✍️_
08144818849
[17/08, 11:13 pm] +234 814 481 8849: 🌸🌸🌸🌸🌸
*SHIMA ƊA NE*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 17*
~Bayan an sallamesu suka fito yana rike da hanun ammi suka wuce direct cikin gidan a tsakiyan falon ya shiga da ita zai wuce momy tace "ina zaka kai mana shara?"
yace "ɗakinta zan kaita sabida tanada ciki kuma cikin mijinki ne a jikinta"
glass dady ya cire yace "wani maganan banza kakeyi?"
tace "ba maganan banza bane ciki ne dani kuma kafi kowa sanin naka ne"
momy tace "tanan kuka ɓullo?"
dady yace "ka fitar da ita kafin nasa a fitar da ita"
"babu inda zasuce"
cewar lawyer ɗin daya shigo yanzu, da ido suka bishi harda su naseer ɗin da suka fito, lawyer yazo gabanshi ya tsaya, sannan ya danƙa mishi takaddan text a hanunshi yace "matarka tanada ɗauke da cikin wata huɗu kuma cikin kasan naka ne, sannan wannan shine dokan da kotu ta gindaya maka gashi nan duk wanda ka tsalleki a cikin wannan zaka fuskanci hukuncin kotu, duk abinda zaka yiwa matarka itama dole ne kayi mata sabida itama matarka ce, sannan da ita da ɗanta anan zasu zauna babu zancen bakin kofa zasu zauna ne sabida suma family ɗinka ne"
kallon nawal yayi yace "idan ya koreku ka kirani a waya zan faɗawa alkali komai sannan za'a mishi hukunci"
tafiya yayi ya barsu, hanun Ammi ya rike yace "muje Ammi"
ɗakin da suka zauna farko ya kaita akan gado ta kwanta ya zauna a gefenta, kayan marmarin daya siya mata a hanya ya bata, ta fara ci, tace "nawal duk abinda zakayi kada ka cutar da mutane kaji?"
yace "to Ammi"
kula da ita yake sosai cikin yana bata wahala amma kulawan da take samu yana rage wahalan.
baya shiga harkan kowa Amminshi kawai yake dubawa, yau kamar kullum ya gama bata abinci ya fito zai tafi samha ta shigo, a bige take domin layi take yi idanunta suna buɗewa suna rufewa, tsayawa yayi yana kallonta yana jin zafin ganinta haka, zai wuce ta faɗa jikinshi tace "ya nawal ina zakaje?"
cikin sanyin muryanshi yace "zanje kasuwa"
tace "to ya nawal ka kaini ɗakina kada na fadi"
yace "to"
riketa yayi suka fara tafiya idan zata faɗi ya tarota, tace "ya nawal kasan me?"
yace "A,ah"
tace "dady kullum suna magana da wani mutum a waya naji yana cewa Ahlam kuma inada tabbacin mugunta yake yi dan jiya naji yace a sawa wani guba a gidan, wai kasan me?"
yace "A,ah"
tace "wai mutumin shine tsohon gomna shine yake neman senator basa shiri da dady tsofin abokan gaba ne, dady ya tsaneshi shima ya tsani dady so suke ma kowanne su kashe junansu, shi yana harin dady shima dady yana harinshi, har dady ya aika wani gidan yaje a matsayin p.b ɗinshi wato personal bodyguard Ahlam, shi mutumin be san dady bane ya turashi kullum yana waya da dady yana faɗa mishi sirrin gidan, yanzu shirin kasheshi suke gadan-gadan wai shine yasa aka tuge dady a party ɗin da yake ciki ya bawa Alhaji sammani gomna"
shiru yayi yana jinta, a fili yace "kisa kuma?"
ashe taji, tace "wallahi dady yace ya bashi kwana uku idan be kashe mutumin ba zai tona mishi asiri"
akan gadonta ya kwantar da ita, rufata yayi da blanket sabida sanyi, zai tafi ta rike hanunshi, yace "me kuma?"
tace "yaya kayi hakuri nasan momy batada imani zata iya yin komai domin kada ka raɓi jikin dady ka dage da addu'a domin momy tana bin boka batada aiki sai hayake hayake da bin bokaye suna bata magani shiyasa ko dady be isa ya kara aure ba kuma be isa ya tsallake magananta ba, kaji?"
a hankali ya gyaɗa kai sannan ya zame hanunshi ya fita daga ɗakin, zai fita naseer ya shigo rike da hanun mata santaleliyar budurwa tana sanye da kayan da suka matse ta, harara naseer ya aika mishi, yarinyar tace "wannan shine shegen gidanku?"
yace "shine"
tace "wow amma wallahi he's handsome yanada bala'in kyau"
hararanta yayi yaja hanunta suka wuce tana juya baya tana kallon nawal daya buɗe kofa ya fita, maganganun samha suna yawo a kanshi, kenan dady yanada mummunan gaba tsakaninshi da Alhaji usman makama? har yana nema ya kashe shi?
Ahlam wanda yake gidan harma yayi zaton yayan yarinyar da ranan yaje sata gidansu ce shine maci amana? shine yake can sabida yayi kisa?"
da wannan maganan ya wuni, yana gidansu kamal bai dawo gida da wuri ba yau saida dare ya fara nisa kamal ya kawoshi har kofa ya saukeshi, sallama sukayi ya shiga gida, saiya duba Ammi kafin yayi bacci hakan yasa ya fara tafiya zuwa ɗakinta, har zai wuce ɗakin dady yaji yana waya, tsayawa yayi yana jin maganan da yake faɗa, yace "Ahlam na yadda da kai ka tabbatar kamin wannan aikin sabida kai ɗana ne, Ahlam daga ni sai momynka da kuma kannenka muka san kaine babban ɗana Ahlam bayanmu babu wanda ya sani sabida a kasar waje kayi karatu tun kana yaro karami, inaso ka cikamin wannan burin nawa ka kashe Alhaji Usman makama a gobe, sunada meeting a gidan gomna na tabbata zai faɗa maka yau zaku fita gobe kusa da gidan gomna akwai wani kwalta daya rabu gida biyu, ɗaya idan kabi senta shine zai kaika gidan gomna ɗayan kuma ɓarawon hanya ne, Inaso kabi ɓarawon hanya Ahlam zanje wajen a lokacin zai san kai ɗana ne na cikina sannan zaka kasheshi da hanunka"
yace "gobe idan zaku fita ka faɗamin domin na zauna a shirye"
dariya yayi sosai sannan yace "zasu san sunyi da ɗan halak"
katse wayan yayi, nawal rufe baki yayi yana kallon kofan, jin ya yanke kiran ya taka cikin sanɗa ya shige ɗakin Ammi bai bari kowa yasan yaji ba, tunda ya shiga Ammi tace "nawal me yake damunka kake tunani?"
yace "ba komai ammi"
kwanciya yayi ya ɗaura kanshi a kafarta yayi shiru, hanu tasa a sumanshi me yawa tace "gashinka ya kara taruwa kamata ka rage ai duk da yanada kyau"
murmushi yayi ya gyara kwanciyan yace "Ammi na ina sanki"
tace "nima ina sanka nawal amma kasan me?"
girgiza kai yayi tace "inaso kayi aure"
shiru yayi, tace "nawal dan Allah ka nemi mata kayi aure wannan shine burina"
ya rike hanunta yace "tunda shine burinki ammi zan cika miki"
tace "yawwa nawal wacece zaka aura to?"
yace "ina zuwa"
waya ya ciro a aljihu ya kira layin kamal, yana ɗauka yace "ya akayi?"
yace "kamal wannan yarinyar da kace tana sona inaso ka faɗa mata ammina tanaso nayi aure gobe da safe zamu zo gidansu neman aurenta"
kamal da mamaki yace "nawal da gaske ka yadda zaka aureta? ai ɗazu ma ta kiraka a waya take fadamin maganan aure kawai take jira kayi"
yace "ba komai gobe da safe zamu zo da Ammi na gidansu"
yarinyar makociyar su kamal ce batada matsala ko kaɗan, da fari nawal ne ya fara ganinta amma baiyi magana ba saida yarinyar tace tana sanshi kamal ya mishi magana, sunanta fatima tanada hakuri sannan kullum tana kiran nawal a waya shine baya damuwa da ita, kamal cikin murna ya faɗa mata ta sanar da gida gobe da safe nawal zasu zo domin maganan aure, ai kuwa tayi farin ciki kuma ta faɗawa babanta da mamanta duk sunyi farin ciki, sun san nawal yana zuwa unguwan wajen kamal kuma kamal mutumin kirki ne.
Ammi tace "nawal na gode sosai kana matukar girmama duk abinda nake so, na gode nawal"
yace "Ammi idan ban miki biyayya ba wa zanwa? ke kaɗai fa nake dashi sai kanina ko kanwata da zaki haifa"
murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, tashi yayi yace "zanje na kwanta saida safe"
tace "Allah ya tashemu"
tace "Ameen"
fita yayi, samha wacce ta shigo cikin sanɗa takalminta a hanu bataso kowa yasan sai yanzu ta shigo, ta juyo daga rufe kofan sukayi ido huɗu, ajiyan zuciya ta sauke tace "ya nawal kaine? na zaci wannan mugun nabil ɗinne ashe kaine"
yace "eh nine"
tafiya ta fara tace "ya nawal saida safe"
ganin ta haura sama da gudu yace "Allah ka shiryeta"
ɗakinshi ya tafi ya kwanta yana tunani har bacci ya ɗaukeshi.
Asuba ta gari, bayan sunyi salla ya haɗawa ammi dashi karyawa suka shirya domin zuwa gidansu fatima wacce yayi waya da ita akan zuwansu, kamal ne yazo ya ɗaukesu har kofa, suna tafe suna hira harda Ammi kamar ƴan uwa, har suka isa kofan gidan, kamal ne ya buɗewa Ammi ta fito sukayi sallama kafin aka musu iso suka shiga, akan babban tabarma suka zauna tareda iyayen fatima suka gaisa harda kanin babanta, Ammi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 17