Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zan iya aurenshi ba wallahi zan kashe kaina mami na gwammaci na mutu dana aureshi" mami tayi shiru, tashi tayi ta rungume mami ta baya tace "mami ki taimakeni kisa baki dan Allah ki hana wannan auren wallahi zan mutu" mami tace "Abbanku yace idan na hana wannan auren akan aurena" sakinta tayi tace "sai me? sai me dan ya sakeki kina tsoron saki meyasa mami? meyasa kika zaɓi zaman aurenki akan farin cikin ƴaƴanki? meyasa kike tsoron saki mami....?" cikin tsawa tace "ya isa janna, ya isa haka, dan nayi shiru bashi zai baki daman ki rinƙa gayamin maganganu son ranki ba" sanyi tayi da murya sakamakon hawayen da suke zuba tace "ba saki nake tsoro ba wajen zama nake tsoro, na fiki tsanan nawal na fiki tsanan auren mara asali da zakiyi, na fiki tsanan wannan haɗin tun akan ibtisam to amma ya zanyi? babu yadda zanyi" ta tsaya a gabanta tana kallon yadda take kuka tace "idan har kin tsani wannan auren me zaisa ki yafe aurenki ki hana faruwanshi?" tace "sabida babu inda zanje, yau zan faɗa miki dalilin tsanan auren mara asali da nakeyi, na rasa iyayena da kanina da ƴar uwata ta jini sabida cikin shege guda ɗaya, kin san wacece wannan ƴar uwar tawa? ban taɓa baku labarinta ba sabida abin yana min ciwo, yana ciwo sosai a raina jannah, yayata wacce take talla sabida kada ta barmu da yunwa, yayata wacce take da nutsuwa da kamun kai duk garinmu babu wanda ya kaita, yayata da take dagiya kullum a kaina sabida nayi karatu, itace kullum take siyamin takadda ta siyamin uniform kuma ta biyamin kuɗin makaranta ita batayi karatu ba amma ta dage ni nayi, rana ɗaya yayata tayi cikin shege wanda ƙaddara ne ya sameta amma ba halinta bane, nan take sabida wannan cikin kowa ya tsaneta ciki harda mahaifiyarmu, baba ya mutu saboda haka, mama sabida bataso ace ƴarta ce tayi ciki ta koreta a gidanmu, wannan shine sanadin lalacewan komai, tunda tasa kafa ta bar gidanmu yunwa da talauci ya samu a gaba, babu abincin ci, kanina sun koreshi a wajen aiki wai sabida yayarshi tayi cikin shege, muna kwana da yunwa babu me taimaka mana, idan na tuna magananta kullum shine Nana A'isha kiyi karatu duk wuya duk rintsi, da yunwa nake tafiya makaranta, mama ta mutu sabida yunwa yasir ya gudu sabida baya iya shiga cikin abokanshi, na rage ni ɗaya a gidan kamar zan mutu kamar zan rayu har na gama secondary zaman kauyen yamin wahala na fito birni ina neman aiki, da kyar na samu nayi karatu a lokacin na tsani duk wani abinda ya shafi cikin da babu aure sabida shine ya rusa mana farin cikinmu, shiyasa rabani da yayata wacce bansan yanzu ko ta mutu ko tana raye ba, kota haihu da rai ko ɗan ya mutu, har yau babu ita babu labarinta, kwatsam na haɗu da mahaifinku wato Alhaji usman makama muka fara soyayya a makaranta na haɗu dashi a lokacin ina hanun wata tsohuwa da nake kiranta inna, sautin kukanta ya karu, tace "ashe shima bada aure aka haifeshi ba ya aureni ya ɓoyemin, saida na aureshi na fara ganin wulaƙanci daga ƴan uwanshi babu me sona tsanar da suka mishi ya shafeni har saida aiki ya kawoshi garinnan kafin na samu na ɗan huta, har yau bana shiga family ɗinsu shima baya shiga, me zaisa naso wanda baida uba ya auri ƴata? kada hakkin zinar da akayi yabi yaranshi suma suyi cikin shege ƴata tazo ta shiga tashin hankalin dana shiga wanda ko makiyina banaso ya shiga, jannah ina zanje idan na rabu da Abbanku banada kowa, shiyasa kikaga ina danne kaina na zauna ko Inaso ko banaso, nasan bakyason nawal amma kiyi hakuri ki aureshi daga baya zamu san me zamuyi jannah" shiru tayi tana share hawaye jikinta yayi bala'in sanyi, a hankali ta hau gadon ta kwanta, mami ta fita daga ɗakin, tana fita jannah ta tashi, tace "akwai babban matsala wallahi akwai matsala matukar na auri nawal banyi nasara ba" da gudu ta sauka a gadon ta buɗe side drower da makulli fara neman karamin wayanta tayi, bata samu ba ta birkice tana nema, daga baya ta samu jikinta yana rawa ta kunna sannan ta toshe akan gadon sabida kara, saida ya kunnu ta fara neman number, tana samu ta sannan kira, ba'a ɗauka ba tace "please please please ɗauka mana akwai damuwa ka ɗauka akwai matsala babba" har ya katse ta kara kira ɗauka akayi tace "hello...hello..hello kana jina? ina kake? ya zama dole yau mu haɗu da dare a bayan gidanmu ya zama dole mu haɗu akwai babban matsala" amsawa yayi da "to" daga nan bai kara cewa komai ba, har dare bata fito daga ɗakin ba, abinci ma jaad ne ya kawo mata, tana zaune a kasa tayi shiru abincin yadda ya aje haka ta barshi ko taɓawa batayi ba, tana wajen har dare yayi nisa ta kalli agogo taga karfe ɗaya yayi, da sauri ta tashi ganin kira a wayarta tasan shine zai iya kira a wannan lokacin, babu takalmi hijabi kawai tasa sannan ta fita cikin sanɗa, ta kashe wutan gidan duka ya koma duhu, cikin sanɗa take tafiya har ta isa bayan gidan da yake da duhu sosai sabida bishiyoyin dake wajen, tana zuwa ta haska tocin wayar, yana gani ya nufo inda take, sanye yake da bakin dressing har hanunshi yasa safan hanu baki da rigan sanyi da mask baki, tace "kaine?" yace "nine wani matsala ne ya taso?" tace "ya zama dole ka saki unty Ibtisam ka kyaleta ta dawo idan yaso asirin ma ya tonu amma tabbas ta dawo domin Abba yana shirin auramin nawal gobe, kuma kasan ko sama da kasa zasu haɗu ba zan iya koda zaman aure na minti ɗaya dashi ba bale na tsawon rayuwa" dariya ya kwashe dashi dariya sosai, tace "dariyan me kake yi?" yace "kece kikace a saceta sabida a rabata da nawal bayan an saceta kuma kice a saketa? ni banma san inda kika kaita ba, kece ai zaki saketa sabida ni ban sace kowa ba" a razane ta mishi wani kallo ta cikin duhun, tace "ka san me kake faɗa kuwa? kaine ka saceta ina sane kuma har video ka turamin sannan kace ba kai bane me kake nufi?" ya taɓe baki kana yace "kinga ki daina sani a maganarki sabida ni bansan komai ba" dariya ya kumayi sosai sannan yace "eh nine na saceta dama me kike zato? zan miki aiki a banza ne ban samu rabona ba? ke ai ban taɓa sanin ke wawiya ce mara wayo ba sai ranan da kika nemi taimakona akan gidanku, kin manta nine naci amanan babanki? kin manta an bani amana naci kuka kika kara yadda dani? to ai abinda baki sani ba tsohon gaban dake tsakanina da wannan shegen da aka haifa wato nawal ya shafi yayarki ibtisam tunda tana sanshi, ke bari na fito miki a mutum bansan inda yayarki take ba kije ki nemeta sannan idan kikayi yunkurin faɗan wannan abun wa wani wallahi zan juye miki komai sabida inada evidence, daga ranan da muka fara haɗa wannan plan ɗin ranan da kikaje gidanmu kika samu Amminshi ta haukace daga ranan muka haɗa hanu da sunan zamu cutar da nawal kuma ya rabu da yayarki ibtisam, na cika miki burinki shine zaki zo kika min wani zancen banza?" nunata yayi da yatsa yace "mind your f*cking business ƴammata" juyawa yayi zai tafi ta damko hanunshi, zuciyanta kamar zai fashe tana wani irin huci tace "Ahlam ni kaci amanata? Ai ni wawiya ce dana yadda da kai bakayi karya ba, amma ka sani idan bakayi gaggawan fitomin da yayata ba zakaga aikin wawiya, na rantse sai nayi wasa da rayuwarka" dariya yayi sosai kana ya kwace hanunshi yace "shege ka fasa" barinta yayi a wajen, rasa abinyi tayi tana tsaye kawai, hanu ta ɗaga ta saukewa fuskanta wani lafiyayyen mari, maruka masu zafi take yiwa fuskanta tace "meyasa? meyasa nace ya sace ta? meyasa na cutar da ita? gashi Abba zai haɗani da wanda nafi tsana akan komai, ina unty Ibtee? ina take? ina kike?" zama tayi daram a kasa cikin duhun ta fara wani irin gunjin kuka. nawal yana zuwa gida yaga twins sunyi bacci da hawaye bushe a fuskokinsu, itama Ammi tayi bacci, a hankali ya kwanta ya ɗaura kanshi a kafarta, kuka ya fara me sauti domin ya kasa rike kukan, a hankali ta buɗe ido jin sautin kuka, hanu tasa a kanshi kamar yadda ta saba mishi lokacin da yake yaro, cikin muryanta me rauni tace "yau zanje gidanmu Ammi zaki zauna ke kaɗai" wannan kalman kullum saita maimaita yafi sau a irga, tun baya fahimta har ya fahimci idan tana son ibtisam ne take wannan maganan, idan tayi maganan saiya nuna mata hoton ibtee sai yaga tana murmushi daga nan ba zata kara magana ba. kuka yake yi sosai babu me lallashinshi. Abba ya sanarwa mutane gobe za'a ɗaura auren jannah da nawal da safe kamar karfe 9 kuma Abba baya magana biyu baya taɓa canja abinda ya faɗa. *Anan na kawo karshen free pages, ga mai buƙatan complete naira 400 ne ta account 8144818849 hauwa shuaibu mapi moniepoint, sai a turo katin shaidan biya ta nan 08144818849* _Jiddah Ce....✍️_ 08144818849 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 17 of 17