Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fita, janna ta manna takaddan a jikin kujeran sannan tace "ji mana" dawowa yayi ya kalleta, tauna cingum take tana kallon Ibtee da jaad wanda har sunyi gaba, saida ta tabbar gum ɗin ya kama riganshi kafin tace "it's okay" buɗe motan tayi ta fita, taku take kamar batason taka kasa, kawarta ta school suka haɗu a kofa tazo da sauri ta rungumeta tace "classy janna kinyi bala'in kyau" murmushi tayi cikin sanyin muryanta da babu hayaniya sai tsantsan raini tace "thanks" hira sukayi kaɗan kafin tace "zan wuce rauda sai mun haɗu" tace "to classy janna bye" tace "bye" wucewa tayi suka shiga, Ibtee da jaad suka fara zaɓen abinda suke so jaad yana rike da basket Ibtee na zubawa yana tura musu, janna ma zaɓa ta fara tana sawa a basket ɗin, nawal ya tsaya a gefe yana jira su gama, nunashi aka fara, bai damu ba ya zaci ko dan suit na jikinshi daya nuna shi guard ne yasa ake kallonshi, ɗan matsawa yayi daga inda sukafi kallonshi zai koma gefe, ji yayi wani yace "GAY?" kallonshi yayi yaga shi yake kallo, ya maimaita kalman "gay kuma?" zuwa yayi zai yiwa mutumin magana yaga mutumin ya matsa da sauri, yace "karka zo kusa dani" da mamaki yake kallon mutanen da suka taru suna kallonshi, wata mata ta tofa mishi yawu tace "abinda Allah ya haramta shine zai zama abin ado a wajenka? abinda ya hallakar da mutanen Annabi lud shine zakazo kana tallanshi? lalle bakayi albarka ba kaiba ɗan halak bane" da mamaki ya nuna kanshi alaman dashi take? ta kara cewa "tirr da haihuwan ɗa irinka" bai gane me suke nufi bafa, zuwa zaiyi wajensu domin gane me yayi, gani yayi kowa yana gudunshi. _Jiddah Ce....✍️_ 08144818849 [17/08, 11:13 pm] +234 814 481 8849: 🌸🌸🌸🌸🌸 *SHIMA ƊA NE* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 22* ~Kallon jikinshi ya fara, so yake yaga me suke kallo suke mishi wannan maganan, idonshi ya cika da hawaye Ibtee duk abinda ya faru akan idonta, ma'aikatan wajen suka kira security sukazo inda yake rikeshi sukayi ta karfi suka fara fitar dashi waje "bama son ɗan luwaɗi a cikin shagonmu sabida zaka iya zabar mana da darajan ShopRite" gani yayi an fara ɗaukanshi hoto mutane sun kewayeshi, fizge jikinshi yayi da ihu yace "wai me nayi? me nayi muku kuke kirana ɗan luwaɗi? sabida an haifeni babu aure? shine kowa yake min abinda yaga dama? laifi nane dan an haifeni babu aure? laifi na ne....?" kuka ya fara, Ibtee jakanta ne ya faɗi ganin kukan da nawal yake yi, sam ya kasa rike zuciyanshi yau, yana jin ya tsani duniya da abinda ke cikinta, yaji bayason kowa a kusa dashi, Ibtee ta karaso a hankali jikinta kamar an zare laka, ya haɗa kai da gwiwa yana kuka me taɓa zuciya, wani saurayi yace "haka dama suke ai masu aikata irin wannan zunubin sai su rinƙa taɓawa mutane zuciya da acting nasu a fitar dashi kuma bakayi kasuwa ba dan babu ɗan luwaɗi anan" tashi yayi a fusace zai kama saurayin da duka rikeshi Ibtee tayi, kallonta yayi idanunshi sun jiƙa da hawaye, girgiza mishi kai tayi tana jin har numfashinta yana ɗaukewa, a hankali ya motsa bakinshi cikin baƙin ciki yace "me nayi? mena musu suke jifana da waɗannan munanan maganganun? sabida Ammina ta haifeni babu aure? itama bada sonta hakan ya faru ba..." a hankali ta jashi jikinta, kankameta yayi yana kuka, dama jira yake ya samu inda zaiyi kuka da kyau, abinda ke zuciyarshi yayi yawa, patting bayanshi take yi a hankali alaman yayi hakuri ya daina kuka, ji tayi tana taɓa abu a bayanshi, da sauri ta kalli bayan taga abinda aka rubuta "I'M GAY" ma'ana "NI ƊAN LUWAƊI NE" zaro ido tayi a razane take kallon rubutun dake manne a bayanshi, tace "nawal meka rubuta a bayanka?" girgiza kai yayi ya kasa magana sai cusa kanshi da yake a jikinta yana ji baida inda zai samu yayi kuka sai jikinta, a hankali ta cire paper sannan ta ɗago kanshi ta kalli fuskanshi daya koma jajur sabida kuka, takaddan ta nuna mishi, karɓa yayi yana karantawa, ya kalleta tace "ya akayi haka?" girgiza kai yayi ya saki takaddan kawai ya fita waje, ɗauka tayi ta yayyaga sannan ta bishi, jaad ya kalli janna dake harɗe da hannu a kirji tana kallonshi ta taɓe baki alaman ko oho, ganin kallon da jaad yake mata ta watsa mishi harara sannan ta mishi alaman idan ya faɗa saita yankashi, gama shopping ɗinta tayi duk abinda takeso ta ɗauka taje ta biya kuɗin ta fito rike da manyan leda. Ibtee tana fita taga ya shiga mota ya haɗa kanshi da stairy yana kuka mara sauti, a hankali ta buɗe ta shiga, kallonshi take tana jin zafin kukan a ranta, a hankali tasa hanu akan suman kanshi cikin sanyi take shafa gashinshi da jijiyan kanshi ya tashi tsaban kuka, tana ji har shesheƙan kuka yake yi, a hankali ta buɗe baki cikin lallashi tace "nawal..? kayi hakuri ka daina kuka...." rungumeta yayi yace "ya zanyi? kullum ina cikin damuwa bana samun kwanciyar hankali a duk inda naje kyamata ake, sabida me? sabida babu aure aka haifeni tun ina yaro nake fuskantar kalubale tun ina yaro babu me zuwa wajena, banada aboki babu me sona sabida ni shege ne" a hankali tace "ba haka bane nawal Allah ne ya kaddara maka haka" janna ce tayi knocking kana ta buɗe ta shigo, kafa ɗaya ta ɗaura akan ɗaya, jaad ya shigo jikinshi a mace, a hankali ya saki Ibtee ya share hawayen sannan yayi murmushi yace "na gode" shiru tayi tana wasa da yatsanta, itama kamar tayi kukan take ji. cikin sanyin jiki yaja motan ya fara tafiya, janna taunan cingum take, har suka isa gida batace musu komai ba, fitowa tayi ta kwashe kayanta ta shiga ciki, jaad da ibtisam suka shiga jikinsu a mace, Abba yana falo yana safa da marwa ya kasa zama, suna shigowa janna taga Abba tsaye jikinta ya fara rawa, Abba ya kalli jaad yace "jeka kiramin nawal" yace "to" fita yayi yaje yace "yaya p.b Abba yana kiranka" saida gaban nawal ya faɗi, yace "to kace ina zuwa" shiga ɗaki yayi ya cire uniform ɗin yasa personal, bindigan da Abba ya mallaka mishi ya ɗaura akan kayan sannan ya kama hanyan falon, sallama yayi duk suna falon harda mami wacce take aika mishi wani kallo da saida ya sunkuyar da kai, a hankali ya karaso gaban Abba ya durkusa yace "Abba gani" Abba yace "nawal dama kai ɗan luwaɗi ne?" girgiza kai yayi, cikin tsawa Abba yace "ka buɗe baki kamin magana" yace "A,ah" Abba yace "to meyasa kace kai gay ne?" hawaye ya fara ranshi yana ƙuna, Abba yace "ba kuka nace kamin ba amsa zaka bani ka buɗe baki ka bani amsa" shiru yayi, mami tace "shirun da kayi ya nuna kenan da gaske ne?" girgiza kai yayi, Abba ya dafa kai yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un meyasa nake ɗaukan wrong mutane nake basu aiki a gidana? meyasa ka bari na yadda da kai? meyasa ka zama innocent a fuska amma a zuciya ba haka abin yake ba?" shiru yayi hanunshi rike da kayan kanshi kasa hawaye yana jiƙa kayan, Abba yace "meyasa duk da abinda kayi amma bana jin tsanarka a raina nawal? meyasa kayi haka bayan kasan ba zan iya bari kayi nesa dani ba? ka ceci rayuwata shiyasa ka kwantamin a rai" juya baya yayi dan bayason kallon nawal ɗin hawaye yake sashi, yace "tashi kaje na sallameka" a hankali ya aje kayan a kasa sannan yace "na gode Abba, amma inaso ka sani niba ɗan luwaɗi bane, Abba na taso cikin wahala sabida rashin mahaifi Ammina ta haifeni ba aure, ni ɗin shege ne kuma Alhaji Alhasan medara ya auri Ammina, tana shan wahala ba kaɗan ba shiyasa naso aikin da nakeyi tare da kai sabida ina taimakawa Ammina, na faɗa maka hakane sabida banaso na ɓoye maka komai kamar yadda kaima ka ɗaukeni ɗa baka ɓoyemin komai" tashi yayi yace "na tafi kuma na gode Abba koba komai kaine ka fara jana jiki ka nuna min nima ɗa ne" buɗe kofa yayi zai fita jaad wanda ya saba dashi sosai bayason rabuwa dashi yace "Abba dan Allah kada ka barshi ya tafi wallahi yanada hankali kuma da dagaske ne zaka gane Abba" ibtisam ta juya baya batason ganinshi zai tafi, kuka takeyi, jaad ganin da gaske zai tafi yace "Abba wallahi unty janna ce ta manna abin a bayanshi" ledan hanun janna ya faɗi, jikinta ya fara ɓari, kallon jaad take kamar idanunta zasu zubo, abba yace "wait nawal" tsayawa nawal yayi, Abba ya kalli janna da jikinta yake rawa yace "me kace jaad?" yace "wallahi ina ganin lokacin da take shafa gum a jikin takaddan dana kalleta tace idan na faɗa saita yankani" Abba ya kalli janna da take komawa baya tana girgiza kai, jakan ya fizge ya buɗe, gum ya gani, matsota yayi zata gudu ya damke hanunta ya fara duba gum ɗin, shinshina hanunta yayi yaji warin gum, jikinta kamar mazari bakinta yana rawa tace "Ab..ab..Abba na tuba wallahi na tuba ka yafeni" da wani irin mari Abba ya ɗauketa saida ta faɗi a jikin mami, tsaban ɓacin rai Abba ya kasa cewa komai, juya baya yayi yace "janna ki bar falon nan kafin na kasheki" da gudu ta saki mami zata gudu yace "tsaya" tsayawa tayi, yace "ki bashi hakuri" a hankali taje gaban nawal tace "kayi hakuri" kafa Abba yasa mata ta baya sai gata a kasa gaban nawal, rufe ido tayi a azabce tace "wayyo Allah na mutu" taka ta Abba yayi a gaban nawal ɗin yace "haka ake bada hakuri?" cikin azaba tace "kayi hakuri nawal ka yafemin" nawal da sauri yace "na hakura Abba ka barta" cire kafa Abba yayi a bayanta, tashi tayi cikin azaba tace "na gode" jan kafa ta fara domin ta tafi Abba yace "ibtisam" da karfi yayi maganan jijiyoyin kanshi sun tashi, idanunshi sunyi jajur, a tsorace Ibtee tace "na'am Abba" yace "kina son nawal?" gyaɗa kai tayi tace "eh Abba" yace "zaki aureshi nan da sati ɗaya" murmushi jin daɗi tayi, ya kalli nawal yace "juma'a aurenka da ibtisam ka sanar da Amminka" kanshi kasa yana hawaye ya durkusa kasa gaban Abba yace "na gode Abba" hanunshi Abba ya rike ya ɗagoshi sannan ya rungumeshi yace "daga yau kada ka kara kiran kanka mara uba, kaima ɗa ne" murmushin farin ciki yayi, Abba yace "zan baka aikin da yafi wannan zaka zama manager ɗin company ɗina sannan kaine zaka rinƙa kula da dukiyana, daga yau ka zama ɗana" hawaye masu zafi suna wanke mishi fuska yace "na gode Ab..." kuka yaci karfinshi ya kasa karasa maganan, jaad share hawaye yayi yana jin dadi ya fara murmushi, janna kunnuwanta sun jiye mata munanan maganganu, ji take kamar ana zuba mata ruwan dalma me zafi a kirjinta, idanunta suna rufewa tsaban tashin hankalin maganan da taji daga bakin Abba, dukan da yayi mata bataji zafinshi kamar maganan da take ji ba a halin yanzu, taka kafa tayi zata haura stair case, faɗuwa tayi kasa a sume, da gudu Ibtee tazo ta riketa tana kiran sunanta, mami ta kalli nawal ta kara mishi wani kallon me kama da kallon tsana, sunkuyar da kai yayi, abba tsallakata yayi ya wuce, ɗagata sukayi tareda mami da jaad suka kaita ɗakinsu, ruwa suka sa mata ta buɗe ido a hankali tana kallon Ibtee, hanunta ta rike tace "kin yadda zaki auri wanda baida uba? kin yadda zaki auri wanda aka haifa ba ta hanyar aure ba? kin yadda zaki auri wulaƙantacce?" a hankali ta zame hanunta ta juya baya, mami tace "tambaya fa ake miki Ibtee ki bada amsa mana, kin yadda zaki auri shege?" gyaɗa kai tayi tace "na yadda" salati mami ta fara tace "na shiga uku ibtee, zaki zubar mana da mutunci Ibtee, ki rasa wanda zaki aura Ibtee sai mara uba? basu haifeshi ta hanyan aure ba ina zai san darajan aure?" juyo da ita tayi tace "ki kalleni da kyau Ibtee baki isa ki aureshi ba, na baku tarbiyya me kyau baki isa ki auri wanda aka haifa kafin aure ba kinyi kaɗan" hawaye ta fara wallahi ba zata iya rabuwa dashi ba, Allah saita aureshi ko anki ko anso, kwace hanunta tayi ta bar wajen, mami tace "la'ilaha illallah Ibtee ta kwace hanunta daga nawa janna, janna Ibtee ta nuna ba zata ki aurenshi ba janna" kuka mami ta fara janna ce ta dawo tana bata hakuri, jaad yace "wai mami me aciki dan ta aureshi? shi yayi laifin..." a fusace zata kai mishi duka ya fita da gudu. Mami da janna duk yadda sukaso su hana auren Ibtee taki, tuggu suke yi ta yadda Abba da kanshi zai kori nawal a gidan Abu ya gagara, ramewa mami ta fara tana neman hanyan da zata raba mara zuri'a da ƴarta, amma sam Ibtee taki, duka zagi faɗa mami babu wanda batayi mata ba, harma ta dawo yi mata nasiha taki, Abba ya bata karamin waya yace su rinka waya da nawal, duk wani abu na abba ya ɗaura nawal akai yanzu nawal shine manager ɗin company ɗin Abba, shaƙuwa sosai yayi da ibtisam sabida soyayya da take nuna mishi, masha Allah yau saura kwana uku aure, tana zaune a garden tana kallon tsuntsaye tayi shiru, jiran nawal take domin anan yake zuwa suna hira idan batason damuwa, ganin bai zo ba har yanzu ta kira wayarshi a kashe, cikin damuwa tace "meyasa bai zo ba?" numbern kamal ta kira tace meyasa yau nawal baizo ba? kamal yace Amminshi ce babu lafiya, tayi godiya ta kashe wayan, tashi tayi ta tafi, ɗakinsu ta shiga tasa dogon hijabi tasa flat shoe zata fita janna tace "ina zaki unty Ibtee?" tana gyara fuskanta tace "gidansu nawal" tashi tayi tazo inda take tace "unty Ibtee dole ne na hakura nabi zaɓinki sabida ina sanki ba zan iya fushi dake ba, amma ki sani wallahi ba zan taɓa son ko girmama nawal ba har duniya ta tashi" murmushi tayi tace "soyayyan da kikemin kaɗai ya isa janna kuma na gode, saide shima soyayyan da nake mishi kaɗai ya isheshi ba sai kin kara da naki ba" a hankali ta buɗe mata hanu tace "come here" zuwa tayi ta rungumeta, murmushi tayi tana shafa bayanta tace "kiyi hakuri da fushin da nake dake" tace "ba komai ya wuce janna bari naje kada dare yayi" sakinta tayi ta fita, janna tace "ya zanyi? dole na hakura amma zaiga asalin munafurci" Ibtee taga mami a falo, cikin respect ta gaisheta ɗauke kai tayi bata amsa ba, a hankali ta tashi ta fita. mota ta shiga direct sai gidansu nawal, sallama tayi aka buɗe mata gata ta shiga, a hankali take tafiya tana kallon katon gidan daya girmi nasu, da tambaya ta isa main parlour, tsayawa tayi tana sallama, amsawa akayi samha tace "wasalam waye da yamma nan yake rafkawa mutane sallama kamar gidan ubanshi?" a bige tayi maganan tana saukowa kamar zata faɗi a stair, sanye da riga guntu da wani banzan takalmi me uban gashi, ganin zata faɗi Ibtee taje da gudu ta riketa ta faɗo a jikinta, taɓe baki tayi ta yatsine fuska tace "wacece ke?" tace "sunana ibtisam" tsaki taja ta janye jikinta tace "meya dameni da sunanki?" shiru Ibtee tayi tana kallonta, nasir ne ya shigo da wata budurwa suka zauna akan sofa, gaisheshi Ibtee tayi ko kallonta baiyi ba, magani ya ɓare sannan ya ɗauko ruwa yace "gashi drink it cikin zai zube yanzu, wannan medicine ɗin asalinshi anyi ne for abortion so relax and drink nothin will happen" karɓa tayi da alama tasha kuka domin idonta a kumbure, shan maganin tayi sannan yace "sleep" kwanciya tayi ibtisam tana tsaye tana kallon ikon Allah, a ranta tace "ko dai ba nan bane gidan da akamin kwatance? anya kamal baiyi mistake ba?" jim kaɗan taga yarinyar ta fara birgima tana rike ciki, kuka ta fara tana cewa "cikina" yace "sorry abortion yayi yaron zai sauka yanzu ki daure" ihu takeyi kuma da mamakin Ibtee babu wanda ya fito, ta fara tsorata zuwa yanzu dama tanada saurin jin tsoro, wayan nawal ta kara kira yanzu ya shiga amma bai ɗauka ba, juyawa tayi zata fita nabil ya shigo yana waya tsayawa tayi ya gama ta tambayeshi ko zai bata amsa, ji tayi yace "eh koda bakada gaskiya nasan kai kayi kisan faruk amma na maka alƙawari zan kareka a kotu" dariya ya kwashe dashi sannan yace "karka damu ka kawomin kuɗin anjima dan bana karɓan transfer, zan bawa alkali nashi cin hancin babu wanda zai kamaka bakaga case ɗin fyaɗen daka yiwa wancan yarinyar na rufe ba?" dariya yayi yace "to faruk sai kazo" katse wayan yayi, Ibtee tayi shiru ta kasa tambayanshi, yace "who are you?" tace "tambaya nazo yi" harara yayi mata yace "for what?" tace "dan Allah nawal nake nema ance nan gidansu ne" wani kallo yayi mata sannan yace "point of correction nan ba gidansu bane nan gidanmu ne" shiru tayi, nuna mata hanya yayi yace "fita" da sauri ya kama hanya zata fita taji muryan nawal muryanshi me sanyi da yake sanyaya zuciyarta yace "Ibtee" a hankali ta juyo, wani murmushin farin ciki tayi da sauri taje ta sameshi, yace "kinzo?" tace "kamal yace min Ammi batada lafiya shine nace zanzo na dubata" yace "anyi mata allura tayi bacci" tace "Allah sarki ya jikin nata?" yace "da sauki kanta ke ciwo kuma tun jiya ne amma yanzu da sauki karki damu" tace "to Allah ya kara mata lafiya" yace "muje ki ganta" ta kalli lokaci sannan tace "no tunda tana bacci idan ta tashi kawai ka faɗa mata nazo, amma yamma yayi Abba baisan na fito ba" yace "to muje na raka ki" tafiya sukayi har zuwa wajen motarta suna hira, sai murmushi take domin yana sakewa da ita suyi hira, yace "kiyi hakuri" tace "dame fa?" yace "da abinda suka miki" tace "babu komai ai ba wajensu nazo ba kai da Ammi nazo dubawa" yace "to na gode" shiga mota tayi yana ɗaga mata hanu har ta tafi, a kofan masallaci ya zauna har akayi mangarib. rana bata karya kamar yadda Abba ya faɗa hakan ya faru yau aka ɗaura auren nawal da ibtisam akan sadaki dubu ɗari biyu, Abba ne ya zama waliyin ango, mami da janna babu wanda suka gayyato, janna kam ɓoye auren ma take yi sabida bataso kowa yasan Ibtee bodyguard ɗinsu ta aura, mami sam taki yadda ta faɗawa kawayenta wannan abin kunyan wai wanda baida asali za'a bawa auren ibtisam, wannan abin yana ci mata rai, Ibtee tana zaune a bakin gado tayi kyau sosai cikin farin leshi tana waya da nawal, janna ma tayi kyau amma fuska babu walwala tunda safe rabon da tayi koda murmushi Ibtee bata gani ba, jaad ne kawai ya tayata murna yana mata congrats bayan shi babu wanda yayi mata, taji a ranta koda me zasuyi mata ba zai rage soyayyan nawal a ranta ba. _Jiddah Ce...✍️_ 08144818849 [17/08, 11:13 pm] +234 814 481 8849: 🌸🌸🌸🌸🌸 *SHIMA ƊA NE* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 23* ~Yusra ce tazo ai ko ibtsam ta rinƙa murnan ganinta suka zauna suna hira daga nan ta daina damuwa, har lokacin da Abba ya kirata yayi mata nasiha, motan ɗaukan amarya guda biyu ne na kamal da wani abokinshi, janna kin shiga ko ɗaya a ciki tayi motar gidansu ta shiga tana sanye da bakin glasses tana taunan cingum cikin raini har suka isa gidan Alhaji medara, shiga da Ibtee akayi har zuwa ɗakinta da nawal, kanta kasa tana rufe da farin mayafi babu abinda ke sata kuka kamar mami da har yau taki mata magana, tana zaune a bakin gado janna ta shigo, rungumeta tayi sukayi kuka me isansu yusra ma tana tayasu tana basu hakuri, da kyar sukayi mata sallama suka tafi, sai kuka take ita kaɗai ce a ɗakin har yanzu bataga nawal ba kuma baya ɗaukan kiranta, kamal ta kira yace "amarya kiyi hakuri jikin ammi ne ya tashi shiyasa nawal yace muje kawai zaizo daga baya kiyi hakuri dan Allah" tace "ba komai kamal na gode" shiru ta zauna a wajen har dare ya fara nisa. momy cikin tsananin damuwa tace "boka kana gani fa har an ɗaura auren wannan shegen, boka yanzu idan ta haife wannan cikin na ƴan biyun da yake jikinta ta zama daidai dani fa a gidan, gashi wannan shegen yayi aure ƴaƴana suna nan babu me hankali, daga me zubar da ciki sai me neman mata da danne hakkin mutane sai mashayiya? kenan haka zan kare a gidan Alhaji yana ruɗewa a kanta? kullum fa yana satan zuwa ɗakinta, taya hankalina zai kwanta boka?" shiru yayi yana wasu abu a cikin kwarya, cikin tsawa yace "shiru hajiya naja, yanzu haka aiki ya kama shi wannan yaron babu abinda muka isa muyi mishi amma ita yanzu haka ta haukace ki koma gida ki gani da idonki, karki kuskura ki cutar da yaron domin yafi karfinmu yanada ibada lokacin salla baya wuceshi sannan yana yawaita karatun Kur'ani koda yaushe cikin tsarki yake da alwala ba zamu iya dashi ba, amma ita tunda ta samu wannan cikin ta fara samun rauni a ibada shiyasa mukayi galaba a kanta" sai yanzu tayi dariya tace "na gode boka, amma dame zan biyaka?" yace "yanzu zaki biyamin buƙatata" tace "me kake so boka?" dariya yayi sosai sannan yace "saina kwanta dake aikin zai tabbata" tace "kwanciya kuma boka?" a tsawace yace "ba zaki yadda bane? na lalata aikin yanzu?" girgiza kai tayi tace "ranan biyan buƙata rai ba'a bakin komai yake ba" yace "kin yi wayo yarinya" fara cire kayan jikinta yayi boka yana zaune yana kallonta har ta kwaɓe duka kayan ta tsaya a gabanshi, wani tabarma ya nuna mata yace "kwanta anan" kallon kasa tayi ga datti ga wasu kayan bokanci harma da allurai akai, tace "amma fa da allura..." yace "kwanta" rufe ido tayi ta kwanta akan alluran duk jikinta alluran ya soke, shi kanshi bokan wani irin datti ya tara me yawa ga gashin kanshi ƙura ga hakoranshi baƙi ƙirin da kasumban daya cika mishi fuska, rufe ido tayi sabida ko ganinshi batason yi. Nawal yana kusa da Ammi sanye da babban rigan ɗaurin aurenshi, tun a wajen ɗaurin auren gabanshi yake faɗuwa hakan yasa ya dawo gida immediately bayan an gama, ya faɗawa kamal ya gaisa da mutane shi zaije ya duba Ammi, yana shiga yaga ta faɗo daga kan gado tana birgima a kasa, da gudu ya ɗagata ya maidata kan gadon tana rike kanta tace "nawal kaina" ya rungumeta yace "Ammi zai daina kiyi hakuri" tace "nawal kaina" yace "ammi kiyi hakuri dan Allah zan kaiki asibiti yanzu" fizge fizge ta fara, yana danneta ta fara tureshi tace "ka sakeni, nawal ka sakeni, zan mutu nawal kaina" kanƙameta yayi yaki sakinta, shiru tayi kamar wacce tayi bacci, shima yayi shiru yana sauke ajiyan zuciya ganin ta daina fizge fizgen, da wani irin murya tayi maganan daya firgita nawal, tace "zan gudu dodo zai kamani" addu'a ya fara mata yana tofa mata a kanta, tace "dodo zai kamani, dodo ka sakeni na gudu" ihun data fara saida duk gidan sukaji, Ibtee data kwanta har bacci ya fara ɗaukanta tana jiran nawal, ihun da ammi takeyi yasa ta tashi da sauri tasa flat shoe ɗin dake kusa da gadon ta fita, ɗakin da takejin ihun ta nufa, tana tura kofan taga nawal yana danne Ammi tana bugunshi da karfi tana cewa ya barta ta gudu, garin kokawan da sukeyi yana shirin ɗaureta ta ɗaga kafarta ta buga mishi a ciki, rike ciki yayi cikin azaba yace "wayyo cikina" dira tayi a gadon ta nufi waje zata gudu, kafarta ɗaya ya fita, ɗaura hanu aka Ibtee tayi ta kwala ihu tace "na shiga uku kafarta ya fita nawal" Ammi kokarin buɗe kofan take ta gudu ibtee ta riketa, kokawa suka fara tana kwace kanta ibtee tana riketa, ƙafan ya ɗauka ya fara sa mata, Ibtee sai kallonshi take cikin mamakin yadda yake maida kafan, dama ƙafan roba ne? saida ya gama ya rike ammi duk ihun da takeyi saida ya ɗaureta akan gadon, tana jujjuya kanta tana cewa "ku sakeni zan tafi wajen mamana ku sakeni zan tafi, kuna dukana kuna zagina kullum, bakwa sona zan tafi wajen mamana" kwanciya yayi a gadon ya rungumeta ya fashe da kuka me taɓa zuciya, jingina da kofa ibtee tayi tana jin tausayin Ammi a ranta, ji take kamar ta karɓa mata katon cikin dake gabanta wanda haihuwa yau ko gobe, hawaye ta share tana jin kukan nawal har cikin ranta, tana maganan haka har tayi bacci, shiru yayi a jikinta, saida tayi

Chapter 14 of 17