da nayi alkawari bazan shiga ba. Kai a k'asa na shiga ban yarda na d'aga kai ba bare naga haramci nayi wajen dj da sauri duk da jikina na bani kaman ana kallona. Kai tsaye na kashe kid'a wajen ya d'auki shiru da ko allurace ta fad'i sai kaji k'arar ta. Yawu na had'iye da kyar saboda ni kaina naga k'arfin halina. A hankali na d'aga kai hall d'in ila kuwa idan kowa yana kaina cike da mamaki musamman ganina da sukayi da katon hijabi.
Murya na d'an gyara dake rawa da d'an d'agata nace
"Ayi haฦuri ana kiran sallah ne idan an idar da sallah za'a mayar. Ina fatan masu yin sallah zasu daure suje su gana da Mahaliccinsu"
Wai. Ni kaina nasan girman abunda na aikata wani gumi ya karyomin lokacin da idona ya fad'a cikin nasa daga can karshen wajen zaune kan wata kureja da mata gefen sa duk suna kwance kan k'afad'arsa sai k'ok'arin jan hankali sa suke kansu. Kin shiga uku ke Bahiyya. Yanda ya kafeni da kaifin idanuwansa ji nayi kaman mashi na fitowa daga cikinsu yana shiga nawa na sake had'iye makogaro amma ya yi kamas don gaba d'aya shi kansa yawun bakina ya kafe gashi na kasa dauke idona daga kansa kaman wacce ya sawa mayen k'arfe. Da wani irin slow naga gefen bakinsa na d'agawa zuwa smirk ya d'aga wani cup dake hannun sa ya kurba kafin ya kama wuyan d'aya dake gefensa ya jawo kanta wajen nashi a haukace ta buษe baki kaman mayya. Kunsan me abunda ke bakinsa ya tofa mata cikin bakinta, Tofawa fa kaman ya kaman yana zubar da yawu ita kuwa ta had'iye a guje kaman wata kare .
Wayyo ni kaina nasan yanayin da fuskata ya yi na tsananin kyankyami sai ya bani dariya da ina kallon mirror tsigar jikina ta wani tashi yam gashi kaman mayya na kasa d'auke ido daga kansa. Tashi yarinyar tayi ta wani durkusa a gabansa tana kokawa da wandonsa na hangame baki nayi imanin har makogarona ana gani tsabar yanda na buษe shi. Ina kallo ya wani koma ya jingina da kurejar gaba d'aya ya wara hannun sa kai yana kallona. Tana zare belt d'in wando ya wani kashemin ido tare da huramin d'an k'aramin kiss ta iska. Wannan shiya farkar dani daga suman tsayen da nayi na shock na dire daga wajen a guje na fice ban damu da kallon da mutane kemin ba kaman mahaukaciya.
Tana ficewa ya saki wani mugun smirk ya kurbe ragowar drink d'in dake hannun sa kafin ya mik'e ya wani ture yarinyar dake ta kokawa da wandon sa harta fara zuge masa zif. Hankalin kowa yanzu ya dawo kansa ganin bai d'auki mataki kan waccan yar kauyen ba wacece ma ita?. Fadeel dake ta shek'a dariya tun dazu da Bahiyya ta kashe kid'an ya kalla ya watsawa harara shima yana d'an murmushi. Maganan da tayi shima baisan sanda y'ar dariya ta kwace masa ba. Maganace tayi mai harshen damo wato a fakaice ta kare musu zagi. Hannu ya kai cikin gashin kansa ya shafa kafin ya sauke kan mutanen dake kallonsa kowa na jiran yaga action da zai d'auka. Ga mamakin su sai sukaji yace
"The party is over. Get out of my house"
Babu wanda ya sake tambayar ba'asi kafin kyeftawar ido kowa ya watse a wajen daga shi sai Fadeel da har yanzu keta shek'a dariya harda hawaye. Kai ya girgiza ya fice daga wajen ya barshi.
Kai tsaye daga nan ban sake tsayawa ba saida na ganni bakin titi na sauke ajiyar zuciya. Gwanda nayiwa kaina lidifi na bar gidan don nasan babu wani batun aiki kuma ya k'are. Gabda magriba na shiga gida a gajiya na samu Baba na k'ok'arin daura sanwa. Saida nayi mata sannu da gida na shige d'aki na chanza kaya zuwa karamar riga da zani. Fitowa nayi na kamawa Baba dake ta hanani tana cewa naje na huta nace mata aa. Ban gaya mata yanda mukayi da Hassa'u ba don bana son zumunci ta dana Baba ya lalace domin tare nazo na gansu.
Munayin sallah isha na shige d'aki na kwanta sai yanzu naji gajiyar gaba d'aya ta riskeni. Koya na rufe ido ina hango shi da yarinyar nan abun har ya fara bani haushi. Da kyar na iya yin barci babu wani tunanin gobe zan sake komawa don nasan ya gama sallamata idan ma Allah baisa ya aiko a kamani ba kenan.
2pm
Yauma kaman jiya wajen biyu na farka
saboda mummunan mafarkin dana sakeyi. Abun mamaki mafarkin babu banbanci da wancan saidai wannan na kusa cimma hasken naji an fisgoni da mugun k'arfi murya mai amo tana cewa
"Har duniya ta nade in har ina raye bazaki taba samo shi ba"
A firgice na farka ina salati wanda ya tada Baba ta miฦe tana kallona da tambayar lafiya?. Numfashi kawai na sauke don na kwantar mata da hankali nace babu komai mafarkine kawai nayi. Bayan ta koma kasa komawa nayi na mik'e na fito waje na sake d'aura alwala na koma d'aki na tada nafila wacca na dinga jerawa har saida akayi sallah asuba sannan barci mai nauyi ya d'auke ni. Wajen bakwai Baba ta tashi ta gama shiryawa ta tashi Bahiyya dake barci kaman kasa. A hankali na mik'e ina salati na kalli Baba data gama shirinta na gaisheta.
"Ki daure ki tashi ki hanzarta ki tafi wajen aiki nima zan wuce nawa tunda na d'anji dama-dama"
Wane aiki kuma ni Baba ai an koreni nace a zuci a fili nace
"To "
Tana k'ok'arin mik'ewa yaro ya rafka sallam tsakar gida
"Salamu'alaikum wai ana sallama da Bahiyya?"
Eh? Daga ni har Baba muka kalli juna cikina ya bada wani k'ara kululu. Shikenan nasan inba shiba ya aiko a tafi dani ba babu wanda zaizo nemana yanzu da sassafenan nida ba kowa ya sanni ba unguwar tunda ba fita nake ba sai in an shigo gidan.
"Ikon Allah waye haka yanzu da sassafe nan. Kace masa gata na....
"Kai kaje kace bata nan"
Nayi saurin katse Baba da yar siririyar murya dana shake ni kaina bansan na canza muryar ba saida nayi maganan. Ido Baba ta zubamin can kuma sai ta saki dariya sosai da ban tab'a gani tayi ba
"Duk tsoron kinyi saurayine yasa harda chanza murya haka? To in bakiyi saurayi yanzu ba sai yaushe bare har kema ki tafi d'akin ki?"
Hmm kawai nace kaina a k'asa gumi na karyo min. Yaron ne ya sake dawowa
"Wai sako za'a bata don Allah tazo yanzu zata dawo"
Baba tana dariya tace "gata nan zuwa"
Wayyo Allah Baba mai yasa ta kwafsa min. "Tashi maza kije kiga waye"
Sai naji ma tausayin ta ya rufeni wata kila idan na fita shikenan bazata sake ganina ba zaisa a baddani can wata duniyar. Da kyar na mik'e a hankali jiki babu kuzari na ja hijiba na saka nayi waje ina waigen Baba daketa dariya har zuwa lokacin ina ganin kaman shikenan kallon karshe nake mata.
๐คฃBahiyya is so funny fa. Kun yarda da magana sa yace she's Fun to have. Shin aikin nata ya kare kenan da wannan katobarar data aikata? Shima zai kyaleta kuwa zai d'auki mataki?
[11/07, 3:30โฏpm] Ashantyluv: ๐๐๐๐๐๐๐
๐อ๐ฎอ๐ผอ๐ฝอ๐ฒอ๐ทอ๐อ ๐ธอ๐ปอ ๐ฏอ๐ชอ๐ฝอ๐ฎอ?
Not edit!
ใch11ใ
Daga d'an nesa da gidan kad'an bayan na fito naga mota k'irar Camry ja fake da bakin tint. Gabana ya sake fad'uwa na tsaya daga bakin k'ofa ina kallon motar zuciyata na harbawa da sauri-sauri. Motar aka buษe da sauri wanda ya fito daga cikin motar saida ya saka cikina hautsinawa na zare ido ina kallonsa cikin matsananci mamaki kaman yanda shima yake kallona fuskarsa dauke da relief na tabbatar da nice. A hanzarce ya nufo ni yana kira
"Bahiyya, Alhamdulillah banyi b'atan kai ba"
Baki na rawa na kira sunan sa
"Lee"
"Alhamdulillah na d'auka tsawon lokaci ina nemanki kafin Allah yasa na sameki"
Da sauri na juya zan koma kafin ya k'araso ya yi saurin tare da murya cike da desperation
"Tsaya don Allah nayi miki alkwari Maa batasan na samu ki ba"
Kiran sunan Maa da ya yi sosai ya sake jefani cikin fargaba na juya da sauri na kalleshi. Taya akayi ya san inda nake?
"Don Allah don Allah na rokeke kar ka sake zuwa inda nake don girman Allah "
Nayi maganan idona cike tab da hawaye da kuma tsananin fargaba. A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya sake d'an sassauta murya kafin nace
"Nasan zuwana wajen ki ya tsorota ki ki yarda dani wlhi banzo don Mahaifiyarki ko dan na nemoki saboda ita ba. Tun ranan dana zo gari naji abunda ya faru nake nemanki kafin ita ta fara nemo ki kaman yanda naji tayi alwashi shi yasa na dage wajen nemanki domin nayi miki gargadi kuma ina so na baki taimako da kulawa kaman yanda na d'auki nauyi da yiwa kaina alkawari. Bazan iya daina zuwa ganin ki da halin da ki ke ciki ba kiyi hak'uri BAHIYYA, amma bazan iya daina zuwa ganin ki ba"
Hawayen bakin ciki suka wanke min fuska da muryar kuka nace
"Inhar taimakona ka ke so kayi shine ka fita daga rayuwata don girman Allah. Rayuwata ta yanzu tafi mun nutsuwa da kwanciyar hankali dawowar ka cikin ta kaman ka buษe wani sabon gibine dana riga na binne shi daga cikin rayuwata. Bana fata da kuma wani burin shigowar wani abu daya shafi waccan rayuwa ya sake shigowa cikin wannan sabuwar dana gina wacce da ace ana bada zabi ita zan zaba na goge shafin wancan rayuwar daga duniyar nan gaba d'aya. Zuwanka nan kaman hanyace ka nunawa Maa ta samoni cikin sauk'i don haka ina rokon ka don Allah ka rufamin asiri ka fice daga cikin wannan duniyar tawa. Nan babu wanda ya sanni bare ya kyamace ni ko ya zargeni bisa laifin da ban taษa aikatawa ba. Ka tafi don Allah kar ka sake dawowa na rokeka"
Da sauri na juya harda d'an gudu na koma ciki. Ban shiga ba na tsaya daga soro na rufe da matsananci kuka hannu toshe a baki. Ya Rabbi kar ka saka dawowar Lee cikin rayuwata ya sakw zana nakasu a gare bisa wannan sabuwar dana gina. Samoni yanzu da ya yi hakan na nufin asirina na gab da tunawa wajen Baba kenan? Har yau da muke zaune tsawon sattittika Baba bata tab'a tambayana dalili ko wane abu ne yasa na baro gida bare ta tambayeni waye mahaifana har taji ba'asi da yasa bana maganan su ko son komawa garesu. Saboda wannan nake sake girmama mutuncin ta a gareni da kuma ganin darajarta mai girma a idona. Tana zaune dani bata tab'a nunamin kyama ko kuskuren abunda nay aikata ba. Saida naji kukana sosai na koshi na share idona na shiga gidan na wuce band'aki domin nasan tabbas na shiga Baba zata san nayi kuka.
"Har kin dawo Bahiyya? Hala kinsan wanda yazo wajen naki? Bari na wuce dama ke nake jira ki hanzarta kema ki fito ki wuce wajen naki aikin sai na dawo."
Daga band'akin naji tayi magana a tsakar gida na gyara murya data shake na amsa da sai kin dawo. Ina jin motsin ficewar na fito daga band'akin na samu waje nan bakin k'ofa na zauna na had'a kai da gwiwa na cigaba da rera kuka. Ina tsoro da fargabar ranan da Baba zata san asalina da nake gujewa ashe farin cikin da nake tunanin na samu ba mai d'urewa bane. Bana fatan ranan da zatazo Baba tasan irin mummunan kaddara data sameni ,kaddarar da ko a cikin mafarki bana fatan ganinsa bare tunanin sa. Banji motsin shigowar mutum ba saida naji an tsuguna kusa dani na d'ago a firgice idona ya fad'a cikin wannan manyan grey eyes d'in. Zabura nayi zan mike a guje na zube k'asa tim ina kallonsa da jajayen ido cikin matsananci firgici da rudu musamman yanda naga fuskarsa a mugun hade babu wani emotion. Ba abun mamaki bane idan ya shigo gidan tunda bashi tsoron duk abunda zai faru. D'an tsk k'ara ne ya fito daga bakinsa kaman ya yi tsaki yana sake gyara tsugunnunsa . Saboda firgicewa kasa tashi nayi daga nan inda nake kwance sai hawayen idona da suka tsananta zubowa.
Harshen ya irin turashi cikin kumatu ta ciki baki wajen ya d'an kumburo kafin ya kai hannu gashin kansa daya zubo goshinsa sai shek'i yake gashi baki sidik. Yanayin yanda yake yin komai kaman yana cikin b'acin rai ya sake d'aga min hankali matuฦa. A hankali naga ya juya yana bin gidan da kallo kafin ya juyo da tsumammun idanuwansa kaina ya yi magana
"Who is that guy?"
Bansan me yasa ba gabana ya sake fad'uwa da k'arfi. Ban gane me yake nufi ba? Yana nufin ya ganni da Lee kenan? Idan ya ganni Lee tun yaushe yake k'ofar gidan kuma daga ina da har yasa ban ganshi ba kona lura dashi?. Shikenan my perfect life tazo karshe kenan?
"Nace waye wancan guy d'in?"
Ya sake tambayana da d'an kaushin murya. Firgicewa nayi na sake rushewa da matsananci kuka nace
"Nima ban sanshi ba. Don Allah ka fita daga gidannan"
Ido kawai ya zubamin Allah kad'ai yasan tunanin me yake. Wani irin rankwafowa ya yi inda nake nayi saurin komawa jikin seminti kaman zan shige ciki.
"Kar ki manta who you're talking to. Ki gayamin ko kar ki gayamin i will still find out who is he and believes me . If he there's mess with what's m......"
Sai kuma ya yi shiru bai k'arasa ba ya zubamin ido kawai yana jinjina kai kafin ya mik'e gaba d'aya bayan ya ajiye wani d'an k'aramin kwali gabana da sam banma lura dashi ba hannun sa ba. Yana mik'ewa ya zuba hannu cikin aljihun wandonsa ya wani kalloni daga tsayen da yake yace
"Get ready and come to work na baki nan da 20mnts. Someone is will be waiting for you to take you"
Yana gama fad'a ya juya nayi saurin rarumar kwalin daya ajiye nayi jefa dashi wajen k'afarsa da ฦaraji nace
"Bana son abinka bana son abunda zaisa ka sake shiga rayuwata. Bazanzo aikin ba banayi ai ba'a dole don haka bazan zoba"
Chak ya tsaya daga inda yake bai jiyoba yace
"I know who you're Bahii and the life da ki ke so desperate ki b'oyewa this pity woman data d'auke ki tamkar granddaughter nata. Kin tab'a tunani abunda zai sameta saboda ke? I'm the man of my words bana going back. How do you think she will feel the betrayal idan tasan cewa saboda ke ta shiga halin da zata shiga soon? Kin d'auka zata cigaba da zama dakene?"
Kalaman sa sosai suka karyamin zuciyata na sauke fuskata k'asa hawaye na cigaba da gudu kuncina. Tabbas gaskiya ya fad'a bazan tab'a son abunda zai cutar da Baba ba. Yanzu fatana shine Lee kar ya sake dawowa. Kaina na d'aga inda yake tsaye tuni ya fice ashe na sauke k'aramar ajiyar zuciya na mik'e na koma band'aki nayi wanka na fito. Riga da sket na saka na less da Baba ta siyon na d'ura hijabi tare da shafa d'an mai da hoda fuskata saboda nasan ta kode kukan da nayi. A gurguje naci abincin bakina babu dad'i saboda damuwar da nake ciki na fito nayi waje bayan na rufe d'akin da kwado na sakashi saman window. Karo naci da abu ina k'ok'arin ficewa ashe kwalin nan ne. Bai d'auka ba kenan?. D'auka nayi naga ashe wayace k'irar Iphone daga gani kuma latest ce mai tsada. To ni mai zanyi da waya daya kawomin waya mai tsada haka? Dama haka yakewa duk sauran masu aikin nasa. Daga jikin kwalin naga takarda da aka lika anyi rubutu ajiki kaman wancan ranan
' ๐ค๐๐๐๐๐ ๐ค๐๐ฆ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐ ๐ง๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐ง๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐ข ๐ค๐๐ก๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐ข๐ ๐. ๐ท๐๐'๐ก ๐ก๐๐๐๐ ๐ฆ๐๐ข'๐๐ ๐ ๐๐๐๐ก๐๐๐๐ ๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐ฆ๐ ๐ก๐ข๐๐๐๐๐ ๐๐๐ง๐๐๐ ๐'๐๐๐๐ ๐๐. ๐ก๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ก ๐๐ ๐ฆ๐๐ข๐ ๐ค๐๐๐ '
Hmm nace ina tabe baki a fili nace
"Dama ai bance ni wata special bace wajenka. Kuma bazan k'arba ba" . Fitowa nayi k'irjina na bugawa saboda tsoron kar ko mutane sunga shigowar sa. Dole na taka masa birki yanda yake shigowa gida babu tsoro ko shakkar abunda zaije ya dawo. Daga bakin k'ofa na tsaya na dafe k'irjina ina addu'a kafin nayi k'arfin hali na fito . Kowa harkar gabansa yake danma unguwar bata cika yawan mutane ba kuma nan babu ruwansu da saka ido ba kaman can layinmu ba da dukkanin wani motsi da shige da ficen ka kan idon mutane ka ke. Tsirarrun mutane ne a layin da alama fitowar su kenan kowa yana neman wucewa wajen aikinsa. A hankali na sauke numfashi saidai ban gama jin relief ba na hango hadaddiyar motar Mercedes baka fake daga gefe ga wani tsaye jikinta da suit irin nasu na masu tsaro. Idona na sauka kansa ya bud'emin gidan baya na shiga. Maganan sace ta dawomin na cewa akwai wanda zai jirani.
Lebena na d'an cije tare da fesar da huci mai zafi na nufi motar ina tunanin me yasa ne yake so yaga yana controlling rayuwata ne?. Dana shiga saida na sauke ajiyar zuciya saboda kamshi da sanyi da motar take. Yaushe rabon da nashiga mota haka mai tsada na manta. Bamu wani d'auki lokaci ba muka isa presidential house. Yau gidan sosai yake cike da masu tsaro da ma'aikata suna ta kai kawo duk inda ka wurga ido. B'angaren sa kai tsaye direban ya yi ya faka motar hadaddiyar farfajiyar sa dake cike da motocin sa da bikes nashi. Ji nayi gabana ya fad'i saboda hango wannan masu aikin da nayi sun fito su uku suna y'ar hira da kaya hannun su. Kaman karna fito na dai daure na fito zuciyata na harbawa bana so suyu tunanin wani abu ganina cikin motarsa. Aikuwa ina fitowa gaba d'aya hankalin su ya yo kaina cikin matsananci mamaki ido waje baki a hangame. Da kyar na iya yin yake na wucesu da sauri na shige ciki ina ji suka bini da kallo.
D'akinsa nayi kai tsaye na buga ba'a amsa ba na buษe k'ofar na shiga a hankali bakina d'auke da y'ar sallama. Yana kwance kan kujera kansa kan hannun kujerar k'afars d'aya a k'asa daya kan kurejar ya rufe fuska da hannun sa guda d'aya d'ayan ya yi matashi dashi. Singlet ce a jikinsa fara da dogon farin wando ba kayan dazu ba ash d'in riga da blue jeans. Kallo d'aya na masa na wuce wajen gadon da sauri don na gyarashi. Kaman ba'a kwanta kainsa ba yana nan fes dashi don haka karkadeshi kawai nayi ban cire zanin gadon ba saboda ina ganin hakan almubazzarancine. Band'aki na shiga shima dai yana nan tas banda walainiya da yake kaman zai kashe ido duk da haka na sake wanke shi na fasa masa turarruka masu sanyin kamshi na fito. Har yanzu yana nan yanda yake a kwance bai motsa ba na tab'e baki na nufi wajen da ake ajiye irin cleaner d'in nan ta turawa nabi dakin na share na goge inda zan goge saida na gana tas na dawo inda yake kwance na ajiye wayar kar tebir nace
" Ga wayarka nagode amma bazan k'arba ba"
Sai a lokacin na sauke hannun sa daga kan fuskarsa ya juyo ya zubamin manyan idanunsa da suka saka gabana fad'uwa saboda yanda suka kad'a sukayi jazur. Yanayin sa gaba d'aya kaman mara lafiya saida ya had'iye makogaro sannan naji yace a hankali
"Take it Bahii is not an option nor did i ask you. It's an order, so take it and leave my site"
Inye wato ma ordering d'ina yake kenan yana nufin ban isa nace aa ba?. Mugun kallo na watsa masa amma na kasa furta komai saboda kaifin idansa. Y'ar kwafa nayi na fisge kwalin na juya nayi waje na barshi nan kwance yanda yake. Ina fitowa naci karo da yarinyar nan d'auke da tire a hannun ta. Tsayawa nayi harta karaso naki kallon fuskarta saboda kallon tuhuma da naji tana bina dashi kiyayyar ta ta ma yanzu naji tafi tsanani. K'arba nayi na juya da sauri na koma d'akin na ajiye kan tebir. Gaba d'aya kulolin na buษe na dandana abincin da basu da wani taste bare armashi na mayar na rufe kafin na juya zan fice na sake kallonsa banga alamun yana shirin tashi ba. Jim na tsaya ina kallonsa da tunanin ko baida lafiya ne?zuciyata tace ke ina ruwanki yai ta ciwon mana.
Kai na jinjina nayi ficewara zuwa d'an garden d'in nan dan na huta. Tunda na zauna nake ta tunanin yanda zanyu da wayar.
"Bahiyya "
Da azama na d'aga kaina jin an kira sunan gabana ya buga ganin first lady da mukarrabanta. A hanzarce na mik'e tsaye na d'an rankwafa da girmamawa na gaisheta. Fuska ta yatsina datasha uban makeup sai kyalli take. Ita wanna uban sutura da take sawa basa damunta ne?. Saida ta karemin kallo sannan ta tako inda nake tsaye Basamudiya ta k'araso da sauri ta shimfiษa abu kan kujerar dana tashi First Lady ta zauna tana wani yauk'i da yatsina. A hankali naji tace
"Da gaskene Aizak ya bada mota an d'auko daga gidanku?"
Cikina ya bada wani k'ara kululu na lashe lebena don har yanzu ban manta abunda tasa akamin ba jiya. Murya na rawa nace
"Eh "
Shiru tayi tana kallona Allah kad'ai yasan abunda ke cikin ranta kafin can ta sake jefana da wata tambayar
"Saboda me?"
Ni kaina bani da wannan amsar na sake sauke kaina a k'asa.
"To ina so naja miki kunne ki karkadeshi da kyau ki saurareni. Nan ke ba komai bace face y'ar aiki ina nufin Baiwa. Idan har kin shigo gidannan ne domin cimma wata manufa taki ina so tun wuri ki san inda dare ya miki. Mu bana had'a kai da talakawa marasa galihu musamman masu aikin mu bare wani abu daya shafi so ya shiga tsakani. Ina so tun wuri kijawa kan ki linzami kar ki kuskura na sakeji abu irin wannan ya sake faruwa gidannan domin daga ranan kin bar aiki cikin sa. Ba Aizak ya d'auko ki ba ko ubansa ne bai isa ya hanani kofar ki ko hukun taki ba. Ki tsaya iya matsayin ki daga yau ki ka sake bari abu makamacin haka ya sakw faruwa akwai mummunan mataki a kanki. Dake da sauran masu aikin gidannan d'aya kuke baku da banbanci da za'a wareki ana baki special treatment saboda kawai kina kula da Aizak. Tun farko da ki ka shigo gidannan baki kwanta min a rai ba saboda haka zan cigaba da saka ido a kanki"
Kai wani da wanne zanji ne? Da ikon dashi yake nunawa kan rayuwata ko da wanda ita mahaifiyar kemin ? Me yasa kowa ya kasa gane zamana gidan nan bason raina bane dole ya tursani. Hak'uri na bata kai a k'asa ina tunanin shi nan yana zarani da halin da Baba zata shiga idan naki masa aiki, ita kuma nan tana cewa na jawa kaina linzami a kansa kona fuskanci mummunan mataki. To da wanne zanji kenan, wanne zan d'auka wanne zan bari?. K'irjina na suya nace tayi hak'uri InshaAllahu hakan bazai sake faruwa ba. Saida tamin kallon wulakanci sannta mike ta suka barni wajen tsaye na fesar da huci mai zafi.
Yaraf na koma kujerar na zauna yanzu menene abunyi? Kaman daga sama naji an sake kira na sake jan numfashi na fesar. Nikam bani da wani sa'a na hutu a rayuwata. A Hankali na d'aga na kalli Zulai dake shigowa wajen ta tsaya kaina.
"Da gaske ne maganan daya bazu wai an kawoki cikin motarsa?"
Oo Allah. Lumshe ido kawai nayi ban bata amsa ba bana bukatar wata lecture daga wajenta itama. Inaji ta zubamin ido kafin naji tace
"Kifa kula sosai Bahiyya domin kin sake tarawa kan ki makiya cikin gidannan idan kowa yanzu yana kan ki ne bare kuma a kai ga y'an matansa dake bibiyarsa da suke da ido da kunne cikin gidan suna bada dukkanin wani information a kansa. Ki iya takun ki kaman yabda Hajja tace miki ki dinga barci da ido d'aya. Allah dai ya kyauta yanzu ki tashi kije yana nemanki yau tunda ya fita ya dawo dazu da safe ya kwanta baya jindadin "
Ya tabbata bashi da lafiyar kenan. Mik'ewa nayi muka jera tana sake jamin kunne na juya idona ban d'auki maganan da muhimmanci ba saboda ina ganin menene abunda zaisa na tara makiya?. Muna