Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuwa bakin k'ofa taja tunga na buɗe a hankali na shiga da y'ar sallama. Daga bakin k'ofar na tsaya ina kallonsa kwance kan k'irjin wani da bama sai amin bayani ba his excellency ne saboda tsananin kamar harta b'aci saida shi bakine mai haske ba kaman Aizak ba dake fari tas. Yanda yake lallabashi kaman wani jariri abun har mamaki ya bani, dole kuwa ya kangare ace kaman wannan katon mutum ake lallabawa haka kaman zaisha nono? . Kallona ya yi da murmushi kan fuskarsa nayi saurin tsugunnawa na gaisheshi "Lafiya lau Bahiyya ko? Naji dad'i da ki ka zo. Daure kije ki had'a masa Latte mai zafi ya kasa shan komai" Da to na amsa na fice da sauri Allah ya taimake ni har yanzu Zulai na tsaye. Ita ta kaini kitchen d'in ta musu bayani abunda zanyi. Nunamin komai sukayi na had'a masa na zuba cikin mug mai kyau na d'ura kan tire na ajiye gefe. Gani nayi iya shi kad'ai shayin bazai masa ba na kwaba masa d'an cake dayaji butter da madara na gasa masa nayi topping nasa da chocolate da strawberries. Gaba d'aya kitchen d'in ya kaure da kamshi ni kaina cake d'in ya burgeni na juya na zuba kan plate na d'auka da Latte na wuce ban lura da yanda kowa ke kallona ba cike da mamaki. Ina gabda fitowa naci karo da wannan yarinyar har abincin ya kusa zubewa nayi saurin matsawa ina kallonta. Harara ta zubamin daga bayana naji an kira "Kausar bata hanya ta wuce " Kaman bazata matsa ba tazo ta wuceni har tana dukan kafad'ata. Banza wahalalliya tana ta wahalar da kanta kan wanda baisan tanayi ba. Ni menene nawa da take sauke kishinta a kaina? Mahaukaciya kawai. Ficewa nayi na koma d'akin har yanzu his excellency yana ciki na ajiye kayan na juya na zan fice naji yace "Zonan Bahiyya " Ban musa ba na dawo na tsaya daga d'an nesa kad'an. "Waye ya yi wannan?" Gabana ya fad'i kar suce nayi musu katsalandan fa. Murya na rawa nace "Nice Sir" Sai a lokacin naga ya wani d'ago daga k'irjin mahaifin nasa ya kalleni nayi saurin d'auke kaina daga kallonsa. Murmushi his excellency ya yi yace "Thank You Bahiyya " Da haka bai sake cewa komai ba na fice da sauri saboda k'irjina dake dukan uku-uku. Ban sake dawowa d'akin ba saida nayi sallah na koma saboda abincin rana. Bakin k'ofar na tsaya ina jiran naga bullowa Kausar amma shiru har wajen minti goma dole na nufi kitchen d'in da kaina. Ga mamakina suna zaune suna ta hira ina shigowa suka d'ago kai gaba d'aya suka kalleni suka wani watsar gefe. "Ina abincin da za'a kai na rana?" Nayi tambayar ina kallonsu. Babu wanda ya amsa na tsawan sakanni kafin naji wata tace "Ke aka bada sako zaki dinga dafawa daga yau saboda haka kije ki dafa ki kai masa da kan ki" Yanda tayi maganan kasan ranta a b'ace yake. Kai kawiq na jinjina na shiga katon kitchen nabi dukkanin inda ake ajiye komai na fidda wanda zanyi amfani dashi na koma kan gas. Abinci mara nauyi nayi masa da zobo dayasha kayan fruits sai tsire danayi da soyayyar agada. Ina gamawa na juye komai cikin kula na dura kan tire na juya na fice daga kitchen d'in. Shi kad'ai ne yanzu d'akin har ya yi wanka ma ya sake canza Ash singlet da gajeren wando mai tazuge. Ikon Allah wati duk kud'in mutum,isar da da ikona sa bai isa ya bawa kansa lafiya ba haka bai isa ya hana zuwa ranan mutuwar saba. Yanzu duba yanda yake kwance babu wannan izzar da ikon. Da sauri na ajiye ganin ya yunk'ura ya mik'e zaune ya zubamin ido. Ban kalleshi ba na zuba masa komai na tura gabansa banyi tunanin zaici ba naga ya d'auka a hankali yana ci abincin kafin ya faraci kaman zai cinye da kwanon. Tas ya cinye abincin ya sake mokimin kwanon da ban fahimta ba saida ya kalli kula na gane. Sake zuba masa nayi ya sake cinyewa tas zobon kuwa tunda ya kafa kai saida ya shanyeshi tas sannan ya jiye jug d'in. Na hangame baki ina kallonsa duk ina ya zuba abincin shi kansa abincin kad'an ya rage. Yana gamawa kuwa ya tashi ya shige band'aki na bishi da kallo jna girgiza kai. Wajen tv nashi nayi da speaker da kid'a ke tashi kad'an kad'an na juya shi zuwa karatu Qur'ani da ban taɓa tunanin za'a samu cikin Mp ba. D'an murya na k'ara kad'an na kwashi kwanukan na fice dasu zuwa kitchen. To dai ranan fisha zance ta wuce saboda rashin lafiyar da yake bai wani takura ni kaman yanda ya saba ba. For 2 days nothing special ya faru zanje nayi aiki kaman yanda na saba na dafa masa abinci duk inda yamma tayi zan saci hanya na dawo gida kafin yasa dibera ya kawoni, amma kullum da safe shike kawoni sai na sauka bakin gate na k'araso da k'afata. Tunda Lee yazo bai sake zuwa ba hankali na ya kwanta. Yau ya kama week end Baba tana gida na barta nima ban fito ba sai wajen takwas. Kaman koda yaushe yana jirana k'ofar gida na shiga mota muka tafi. Muna zuwa bakin gate na sauka na k'arasa. Bansan me yasa ba ina saka kafata ciki gabana ya yanke ya fad'i saida na kai hannu na dafe kaman wani abu na shirin faruwa. Salati na fara da Addu'a na k'arasa duk inda nayi sai kaga sunbar abinda suke sun bini da kallo. Kitchen na fara wucewa na had'a masa Tea da simple abinci daya sha kayan kamshi na koma d'akin sa. Samu nayi yana wanka na ajiye tiren d'in na gyara masa gadon da d'akin a gurguje na fito kar ya fito daga wankan ina ciki. Kai tsaye nayi garden da nake hutawa Ina saka k'afata naci wani uban birki ganin Aisar da Susu harda Fadila dasu First lady da Hajja kaman suna jiran wani ga su Kausar gaba d'aya sun hadu sai magana suke harda misali. Ina shiga kuwa suka juyo kaina gaba d'aya cikin matsananci mamaki baki a sake kafin Aisar ta saki wata irin mahaukaciyar dariya tana tafa hannu. Cikina ya hautsina tsoro da tsananin fargaba ya riskeni na zuba musu ido zuciyata na cewa ki juya ki nemi ta kan ki. "Allah mai iko mai yanda yaso da bayin sa. Dama kece yarinyar da labarin ki duk ya karade gari? Kin d'auka zaki gujemin ne Bahiyya? Kin d'auka kin gudu daga kaddarar ki? Kinsan waye wannan ki ke tare dashi? Ko kin manta abunda ya faru dake ne to idan kin manta ni bari na tuna miki. Kun ganta nan munafukar yarinyar ce tana yawo da hijabi kaman ta Allah bayan kowa ya sheda shegiya ce bata da asali. Mahaifiyar ta banda yawon karuwanci babu abunda ta iya kullum tana bi kwararo kwararo gindin alhazai da masu hannu da shuni. Abuja Mahaifiyar take shima ita takeyi har ta iya samu ta shigo gidannan da sunan mai Aiki. Walahi na rantse muku da Allah Enzo ya kusance ta saboda sanadi hakan ta iya shigowa gidannan don ta cika burinta. Saboda munafurci da gudun idon duniya ta gudu daga wajen uwarta saboda duniya karta zarge ta dan tana ta k'ok'ari taga ta nuna cewa ita da mahaifiyar ta ba d'aya suke ba to walahi munafukace" Ta k'arasa maganan tana huci da shegen murmushi. Hawaye masu tsananin zafi suka wanke min fuska na rushe da matsananci kuka. Hajjo naji tace "kash amma Allah wadaran naka ya lalace. Da ina miki kallon yarinya mai hankali da nutsuwa ashe duk kwanwar jaa ce har ina bada amana a hannun ki. Me ki ka zo nema gidannan? Kina da cikin sane? ,idan kina da cikin sa nawa za'a baki diyya ki kula da abunda ke cikin ki har ki haihu amma kar ki kuskura ki sake tako kafarki gidannan. " "Aini dama Hajja tunda ta shigo gidannan bata kwanta min a raina ba. Ni nayi imanin akwai abunda tayiwa Aizak da yasa saka ya damu da ita haka kuma dole saita warware shi" First Lady ta k'arbe zancen.Wane iko suke dashi da har zasu ga laifina? Basa ganin abunda dansu ke aikatawa wato mu mata mune banza, tabbas ance duk abunda namiji ya yi ado ne amma donme zasu jefani da abunda ban taɓa aikatawa ba? Zina fa? Su rasa kagen da zasumin sai aikata zina da dansu wato inma nayi shi ado ne wajen sa?. Kafin Hajja ta sake cewa wani abu Zulai tazo a guje tana kira waiga Aizak can ya fito daga d'akin sa ya fad'i yana aman jini. Gaba d'aya suka kwasa a guje banda Aisar dasu Susu dake kallona suna murmushi mugunta. Sosai nake kuka zuciyata na zafi sai lokacin na lura da Hassa'u dake jijjiga kai cike da kyama ta wuce da sauri tabi su Hajja. How dare them zasuyi judging d'ina kan abunda su suke aikatawa?. "Tunda har kin nace sai kin shiga rayuwata to yau ba gobe ba zan canza miki halitta ta yanda ko a hanya aka ganki zaki zama abun gudu. Har kin isa ki shigo gidannan Enzo ya wulakantani saboda ke? Bastard child? To in baki sani ba barina tuna miki Enzo shine wanda ya yi raping naki ranan a birthday party d'ina ina kuma da proof" Fuskar wayarta ta hasko min wajen idona daidai yana yagamin riga. Kaman an kwadamin gudu a kai haka naji a take komai ya fara dowawin kai yana rushing kwakwalwata. Wannan idon da nake gani cikin mafarki nashi ne. Wayyo Allah zuciyata wani irin ciwo ta fara na dafeta ina jan numfashi kaman mai shirin tada Asma. Ihuna sanda ya ketamin haddi ya ratsa kwanyar kai na zube wajen ina kuka mai hade da ihu da gunji. Dariyar suka fashe da ita Aisar tace "Mahaukaciya mara hankali da is so easy to manipulates. Bari na gaya miki wata gaskiyar ni ko nace your dear friend Nabila ita ta shirya wannan plan na ayi gan raping naki at my party. Kin d'auka kawar kice ko? She is not your friend ni na sata shiga jikin ki saboda ta samu trust naki incase in abu makamacin haka ya faru. That stupid girl nima tayi backstabbing d'ina wajen yad'a video nawa da Enzo yana having sex dani. Na zama abun dariya da zunde wajen mutane saboda kowa yaga cin mutuncin da yamin wanda na juya sa na yad'a cewa munyi having passionate sex har muna dating. Yar iskar yarinya nan munafuka bata san ba'a shiga hurumina so kinsan me nasa aka mata? Nasa itama anyi gang rape nata na kuma durashi live social media kowa ya gani. Yanzu haka sunbar gari ita da iyayenta. Duk wanda yace zai shiga hurumina zan gama dashi musamman ma ke? Kinsan waye enzo a wajena and how I'm madly inlove with him?" Gaba d'aya kaina ya juyo duniyar tamin wani irin zafi sai juyawa take dani kaman ana kwatantanwa dani. Sama-sama naji tace "Bani kwalban nan Susu" A hankali na d'aga jajayen idanuwa daidai Susu na mik'o mata wata kwalba mai d'an girma ta miƙe tsaye tana mugun murmushi tana kwance murfin. Bansan me yasa ba wani k'arfi yazomin daidai tana k'ok'arin zubamin koma menene cikin kwalbar na murde hannun da k'arfi na fisge kwalbar na sheka mata ita tun daga tsakiyar kanta zuwa kafarta. Wani irin kururuwa ta saki ta zube k'asan wajen tana ihu jikinta gaba d'aya ya fara fidda wani irin hayaki. Tsananin storo da dimaucewa naja baya ina kallon ta suma su Susu sai ihu suke sun kasa tab'ata. Acid ne Bahiyya meya kai ki? A guje na juya da wani bala'in gudu nayi hanyar waje daidai naji muryar Hajja na cewa "Ku kamota kar ku bari ta fita ta zubawa Aizak guba cikin abinci " Wai yau meke faruwa danine? Tabbas na tashi cikin rashin sa'ar da ban taɓa shiga ba cikin rayuwata. Guduna na karawa tsanani ni kaina bansan inda nake saka kaiba . Sosai nake sheka gudu ban damu da yanda ake kallo na titi ba ban tsaya ba saida na ganni k'ofar Baba. A guje na shiga ina kiranta gaba d'aya suka d'ago ita da bakuwar ta suka zubamin ido. Tsananin rudu da firgici ganin wacce ke zaune tana murmushi na zube wajen a sume. 🙆‍♂️Bahiyya na ganin tasku. Who is this mata datazo? 𝐁𝐀𝐇𝐈𝐘𝐘𝐀 𝓓͟𝓮͟𝓼͟𝓽͟𝓲͟𝓷͟𝔂͟ 𝓸͟𝓻͟ 𝓯͟𝓪͟𝓽͟𝓮͟? 𝙼𝙰𝚁𝚄𝙱𝚄𝙲𝙸𝚈𝙰𝚁 𝚃𝙰𝚄𝚁𝙰 𝙱𝙸𝚈𝚄 𝚂𝚄𝙻𝚃𝙰𝙽𝙰𝙰𝙷 𝙶𝚄𝙳𝚄𝙽𝙰 𝙰𝙺𝙴 𝚂𝙰𝚄𝚈𝙸𝙽 𝙻𝙰𝙼𝙰𝚁𝙸 𝙺𝙰𝙸𝙳𝙸𝙽 𝙼𝙰𝙲𝙴 𝙼𝚄𝙻𝙺𝙸 𝚉𝚄𝙱𝙰𝚁 𝙷𝙰𝚆𝙰𝚈𝙴 𝚉𝚄𝙲𝙸𝚈𝙰𝚁 𝙼𝚄𝚃𝚄𝙼 𝙽𝙾𝙾𝚁 𝙳𝙰 𝚂𝙰𝚄𝚁𝙰𝙽 𝚂𝚄. Not edit! 【ch12】 𝐿𝑎𝑠𝑡 𝑓𝑟𝑒𝑒 𝑝𝑎𝑔𝑒 Kafin zuwa azahar labari ya baza gari ana neman Bahiyya ruwa a jallo da hutanan da aka kafe ko wace kusurwa y'an sanda na yawon nemanta. Hassa'u aka saka a gaba har gidan Baba amma sai akayi rashin sa'a sun iske gidan garkame da kwado. Mutanen unguwa kuma babu wanda ya lura da ficewar su sai daidaiku da suka ce sunga sun shiga wata jar mota tare da wata mata sun fita. Jin wanna labari nan da nan kuwa matakan tsaro suka bazu hanya ana tare dukkanin wani abun hawa dake wucewa ko Allah zaisa a samu sa'ar ganin su amma har magriba babu alamun wannan motar da kuma ita wacce ake neman. Aisar kam tana cikin wani mayunwaci hali domin da gaggawa aka shiga da ita emergency amma Sanet na zuwa yaga halin da y'ar sa ke ciki da yanda ta chanza kamani sukayi waje da ita bayan yaci alwashi sai ya d'auki mataki kan wacce ta aikawata y'ar wannan aika-aika. Mahaifiyar ta kuwa tayi kuka harda suma, Susu da Fadila suma duk sun firgice an rasa wanda zai fad'i abunda ya faru koda y'an sanda suka zo. Da fari sun yanke shawarar zasu fad'i k'arya da gaskiya kar asirin su ya tuno amma ga mamakisu da aka zo tambayar su kansu basu yanda akayi ba suka dinga fad'o komai tiryan-tiryan kaman lokaci komai ke faruwa. Tun daga ranan da suka shiryawa ayi gang rape d'in Bahiyya da tun a ranan Aisar taso zuba mata acid da yanda suka sami sabani da Nabila da sanadin barin su garin Jordan har yau da yanda komai ya faru. Abun sosai ya d'urewa jami'an tsaro kai duk da wannan sheda da aka bayar Sanet da mahaifiyar Aisar sunce san basu yarda ba sharri akewa y'arau dole a nemo Bahiyya a hukuntata kwatankwacin abunda ta aikawata y'arsu, yanzu gashi ta jawo mata mummunan rauni da duk mak'udan kud'i da zasu zuba bazai dawo mata da halittar taba. To ai dama ance Allah bai gama yiwa bawansa halitta ba sai ya koma gareshi. Allah yasa mu dace. B'angaren Aizak shima dai abun babu kyau dom hankula suk tashi sosai musamman yanda yake aman jini kaman zai mayar da hanjin cikinsa. Mr. President yana can Uk taron shuwagabanin k'asa labari ya riskeshi. Hankali ya tashi ko sakan d'aya bai k'ara cikin taron ba ya fito hankali tashi saidai yana shiga jirgi kiran Mahaifiyar Aizak ya shigo wayarsa. Tashin hankalin da ita take ciki ma yafi nashi ta rikice sai an kawo mata d'an ta. Da kyar ya lallasheta yace yanzu zaisa a tawo dashi nan shima direct daga nan South Korean ya wuce bayan ya yi waya wajen su Hajja maza a sakashi jirgi a tawo dashi. Haka aka sakashi jirgi da manya-manyan likitoci tare da Hajja banda First Lady data tsaya saboda ayi bincike sosai a gano yanda akayi poison ya shiga abincin sa abunda bai tab'a faruwa ba shekara da shekaru sai bayan zuwan Bahiyya. Jigga da naji jikina nayi kaman ina cikin abu yana tafiya yasa na buɗe idona a hankali ina jan numfashi kafin na sake maida idon na rufe na sake buɗewa. Kaina ya sake buguwa da abu kaman glass na yunƙura da sauri don naga menene. Cikin mota muke dake sharara gudu dokar daji saboda yawon bishiyu da kuma ciyayi da muke ta wucewa kaman iska. A razane na juyo gabana ya yanke ya fad'i ganin Baba zaune gefena a d'aure idonta ya yi ja alamun tasha kuka ta koshi. Innalillahi wa innalillahi raji'un na fara furta a zuci tare da k'ok'arin motsa bakina amma sai najisa gam a rufe. "Oo kin tashi?" Wannan muryar. Wani mugun fad'uwa gabana ya sake yi sanda na d'aga ido jikin mirror da aka saito wajen fuskata. Muna had'a ido ta sakarmin murmushi tare da d'an juyowa ta kalleni kafin ta mayar da hankali kan tukin da take. MAA. Na furta da k'arfi cikin raina na fara kici-kicin kwance hannuna da naji an d'aure ta baya. BABA na kalla da tayi shiru alamun gajiya tattare da ita. Wani irin kuka ne yazomin mai cin rai na fara yunƙurin kai hannu na kamata amma na kasa tsananin tausayin ta duk ya rufeni. Abunda nake gudu gashi ya faru. Baiwar Allah da bataji bata gani ba ta shiga wani hali saboda ni. "Aui so cute. Tausayin ta ki ke ji? Well saida na bata zabi amma tace bazata iya barinki ba saboda tana son ki saboda da Allah. Kinsan me ta fara cewa bayan na gabatar da kaina wajenta? 'Bazan tab'a baki Bahiyya ki koma da ita duk da cewa ko baki fad'a ba naga tsananin kama da ku ke da ita kuma lashakka ke ki ka haifeta, amma kiyi hak'uri da Bahiyya tayi niyar koma miki da bazata b'oye asalinta ba bare har musan cewa kina da rai'. Ita wacece da har zata yanke hukunci kan y'ata? Nike da ikon naga yanda naga dama dake kaman yanda naci alwashi. Zuwanki duniya baisa na mallaki abunda nake so saboda haka baki da amfani. Idan har sanadin ki baisa na samu soyayyar sa ba to zan kuntata masa ta hanyar ganin kin bar duniya gaba d'aya kaman yanda nayiwa y'ar uwata" Duk da cewa bakina a rufe yake sosai gunji ke fitowa daha bakina. Idan na fahimci maganan Maa ina da uba kenan? Wace y'ar uwa take magana a kai? Me ya yi zafi haka da har take som taga na mutu na bar mata duniyar?Hannun Baba naji kan nawa ta rike wanda hakan sosai ya sake karyamin zuciya na cigaba da kuka sosai mai tab'a zuciya itama Baba hawaye na sauka kan fuskata. Baki ta tabe babu digon imani tace "Ai baku fara kuka ba tukun, ku d'auka kaman ceton ku nayi daga wancan kangin rayuwar da ki ke shirin fad'awa. Ko kinsan duk an yad'a hoton ki kafafen labarai dama na duniya ana nemanki ruwa a jallo? Bayan zubawa y'ar Sanet acid a jiki bai ishe kiba saida ki ka zubawa the only president son Guba cikin abinci?. Hahhaha wow Bahiyya after all kin debo wani abu daga cikin halina. So ku godemin na fito daku daga waccar ukubar amma wanda zaku shiga tafi wannan tsanani " Sam babu tsoro, fargaba ko digon imani cikin maganan ta bare wani abu wai mai kaman soyayyar uwa ga d'an ta ya ratsa zuciyar ta taji tausayin mu. Hannun Baba na sake rikewa tsabar yanda hawaye ke gudu fuskata bana ganin fuskarta sosai. Ni banajin kaina sai ita? Menene laifinta saboda ta taimake ni? D'an murmushi Baba tamin daya sake saka zuciyata cikin wani irin ciwo ina ji kaman zata buga. Dajine sosai muke ciki don ko kukan tsintsu bakaji sai na wasu irin ababan boye mai ban tsoro daya karade gashi dare ya yi sosai danma garin akwai hasken farin wata. Daga nesa aka hasko fitila mai tsananin haske kaman ta mota kafin ayi horn a kashe ma ta mayar da Horn d'in. Wajen haske tayi kai tsaye muka tsaya gaban wata bak'ar civic mai duhu da wasu manyan maza kaman iyamurai ke tsaye. Tanayin fakin ta fice da sauri ta nufeso na sake rike hannun Baba ina kiran sunan Allah ya kawo mana d'auki. Basu wani jima suna magana ba suka nufo motar suka fito damu daga ciki da k'arfin tsiya. K'ok'arin samu suke cikin tasu motat na fara tirjewa ina kallon ma cike da tsananin tsana da kiyayyar ta. Alamu taga kaman ina son magana ta matso ta cire tiff data d'auren baki dashi aikuwa na tari yawun bakina na tofa mata a fuska. Tsananin mamaki ya kamata ta zubamin ido rai a b'ace. Da tsananin tsana nace "Na tsane ki, tsane ki Allah ya miki abunda ki ka min . InshaAllahu bazaki gama da duniya lafiya ba. InshaAllahu sai kin wukakanta kin muzunta kafin Allah ya d'auki ranki. In Allah ya yarda sai kinyi mutuwar wulakanci da kaskanci kuma bazaki zama abun tausayi ba sai Allah wada..... " tasa ta d'auke ni da mari da saida hancina ya fashe da karaji dajin na amsawa tace "Don kutumar ubanki kin d'auka kalaman ki zasu karyamin zuciya ko suyi tasiri a kaina? Naji wanda suka fi wannan kuma gani har yanzu ina raye garau babu abunda ya sameni. Ba kune Allah ba baku kuma isa ku yanke hukunci ba. Kin d'auka ke wata aba ce. Y'ar uwata da muka fito ciki d'aya naga bayanta bare ke banza wawuya da haihuwar ki babu abunda ya kareni da ita sai bakin ciki? Kin d'auka zan so ki ni duk da cewa ni na dauki cikin ki wata tara na haifa? In banda kina da shegen taurin rai ai nima da tun a ciki zanga bayanki domin babu hanyar da banbi ba don naga bakizo duniya ba amma gaki. Ki godewa Allah bayan kiyayyar dana miki na barki kin rayuwa har kin kai yanzu kin kuma shaki iskar duniya. Yar iskar yarinya kawai a curse to humanity. Ku wuce da ita daga yau kuma sai a lahira" Tana gama fad'i taja mugun tsaki ta wuce ta koma motar ta ta barni tsaye da iyamurai nan d Baba da suka rike. Gana d'aya zuciyata ta gama karyewa tabbas ba yarda idan Allah ya cire wannan imanin ya tafi kenan har abada bazai dawo ba sai wanda Allah yaso da rahamar sa. Maa tana manta cewa komai lokaci kuma tabbas Allah baya barci. Babu kokawa na shiga motar da suka buga mana tsawa mu shiga Baba ma tayi saurin shiga kaman yanda nayi. Kasa kallonta nayi saboda ina ganin komai laifina ne. Tabbas Maa batayi k'arya ba da tace I'm a curse. Wata kila dana ban gudu ba daga wajen Mama da dukkanin wad'annan abubuwan basu faru ba musamman ga Baba. Sam banyi nadamar abunda nayiwa Aisar ba domin hakkina na kwata amma Aizak fa? Duk cewa bani na zuba masa gubar ba I'm selfish to say I'm happy da abunda ya sameshi saboda he ruined my life. I hate him so much da nake ji just sa masa poison da akayi is nor enough. A hankali na maida kaina jikin glass d'in motar na kwantar ina jin yanda marata ta wani murda lokaci d'aya amma tsananin tashin hankali da nake ciki baisa naji ciwon ba sai sha abu ya kwance marar tawa kaman na saki fitsari a zaune. Kafin wani lokaci na farajin jiri sosai na d'iba na na fara lumshe ido a hankali ina bud'ewa tare da kiran sunan Allah k'asa-k'asa. Ina ji Baba ta dafani tana d'an jijjigani da kiran sunana kafin komai ya sake d'aukewa kaman an d'auke wutar nepa. 🤧kai this chap ya yi touching nawa sosai. Tabbas Maa tayi nisan da bata jin kira saidai muce Allah itama ya mata abunda ta aikata. Waishin wacece Maa? Menene alakar ta da yar uwarta da take ta kirari? Wane Hali Bahiyya da Baba zasu shiga wajen wad'annan mutane da Maa ta kaisu? Su waye su inyamuran? Shin Aizak zai samu nasarar gano Bahiyya bayan ya farfado duk cewa an bar gari dashi? Wane mataki zai d'auka idan yaji abunda ya faru? Wane hali Maa zata shiga nan gaba? Waye asalin mahaifin Bahiyya ? Shin Maa itace kuwa ta haifeta? Menene sanadin barin Maa gida da asalin ta? Yaya soyayyar Bahiyya da Aizak zata kasance bayan sanin gaskiyar Lamari? Duk wad'annan amsoshi suna cikin book 2 da zamu fara babu jimawa. Come and make your @500 kad'ai cikin wannan asusun bankin 👇 8140754777 Aisha sani hassan Opay A turo shedar biya 08140754777 domin neman karin bayani. Ashantyluv💜 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da

Chapter 10 of 11