Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ki da aikata abunda ake tunanin kinayi" Sosai nake kuka k'irjin na wani irin ciwo. Ban tab'a jin zafin zargin da akemin ba saida hakan ya fito daga bakin uwar data haifeni. Waini shin waye ubana? Idan har tsananin kiyaryar da takemin ya kai haka, mai zai hana ta maidani wajen mahaifina? To amma shin ina mada uban kaman yanda kowa yake zargi ni shegiya ce? Ko daini ni shegiyar ce? Innalillahi wa innalillahi da wanne zanji ne a rayuwa ta?. "Kinsan Allah idan baki rufemin baki ba ki ka bari Lee ya shigo ya sameki kina kuka saina ci ubanki, ba ciwo ba ko mutuwa zakiyi sai ranki ya b'aci " Da kyar na had'iye kukan ina ajiyar zuciya da goge hawaye. Ban dade ba kuwa dayin shiru ya shigo still har yanzu rike da wasu ledojin. Ganina a zaune ya washe fuska ya nufo gadon yana murmushi tare da yimin sannu. Saboda mugun kallon da take watsamin na amsa da kyar kaina a k'asa. Ita ta fita ta kira likita yana shigowa ya yi d'an dube-dube da min y'an tambayoyi ko akwai inda yakemin ciwo nace aa. Magani ya rubuta ya mik'awa Maa tare da cewa ya sallame mu tunda banajin wani ciwo amma a dinga bani magani kan lokaci. Sosai Lee ya masa godiya ya k'arbi takarda muka fito daga asibitin ina takawa da kyar. Allah kad'ai yasan irin ciwo da jikina da zuciyata take. Saida muka tsaya hanya ya siyi maganin da k'arin wasu snacks d'in muka wuce gida. Tsawon kwana biyu na d'auka a gida ina jinya Nabila tazo ta dubani bayan an sallameni. Datazo nake tambayar ta abunda ya faru tace min itama batasan yanda akayi ba bayan zuwan Enzo da sukaje wajensa ta dawo taga bana nan inda ta barni. Tayi ta nemana bata ganni ba gashi dare nayi shine ta koma gida ta sanar da Maa suka dawo lokacin kuma ruwa ya tsuge sosai wajen kowa ya watse. Jikina ya sake yin sanyi jin itama bata da tabbacin abunda ya sameni. Idan har ban samu sheda ba taya zan iya kai wanda ya lalatamin rayuwa kuto domin ta kwatarmin hakki na? Yau dana kwana biyu a gida na wayi gari babu Lee . Hankalina yafi kwanciya da rashin sa a gidan saboda tunda na dawo wata irin kulawa yake bani bai damuwa da harara da kallon gardin da nake jefa masa saboda mugun kallon da Maa ke jifana dashi duk lokacin daya suka shigo d'akina. Shi zai tursasa nasha magani naci abinci badan ina so. Tun safe daya tafi Maa bata lek'o inda nake ba dama sai yana nan ne take shigowa saboda tana gudun b'acin ransa. Yunwa sosai take nurkusata dole haka na d'aure jiki babu kuzari na fito don neman abinci. Nan falo na sameta tayi shame-shame kan kujerar da y'ar singlet da dogon wando gabanta kwalbace da shisha tana zuka hankali kwance. Hannu nakai da sauri na toshe hanci ina d'an tari saboda warin daya daki fuskata. Harara ta watsa mun da jajayen idanuwanta tare da mugun jan tsaki tace "Y'ar iska, munafuka" Da sauri na wuce kitchen na d'ora yar indomie a gurguje na juye a flat na dawo falon zan wuce naji tana cewa da kaushin murya "Anjima zanyi bako ina so ki shirya shiga mai kyau kafin yazo. Idan naji wani kat daga bakinki sai kinci ubanki. Domin zan fara nuna miki ainihin kalata" Ban amsana na wuce da sauri k'irjina na harbawa. Wane irin bako kuma? Menene ya had'ani da samarinta da har take son na shirya?ban bari tunanin bakonta ya dameni ba naci abincin da kyar babu dad'i na sha magani na kwanta. Wasu hawaye ne suka biyo kuncina saboda tausayin kaina da guilt na abunda ya sameni. Koma waye ya lalatamin rayuwa i will never forgive him ,kuma babu dare babu rana da ban kai goshina k'asa ina neman taimakon mahalillici daya gaggauta hukunta wanda suke da saka hannu wajen jefani cikin kangin rayuwa. ➺➺➺➺➺➺➺➺ Wani irin falone mai tsananin girma da tsab ya isa a gina manya-manya flat house cikinsa. Tun daga kan haddedden stairs dake chan gefensa daya kaman glass komai na falon blue ne da white. Hadaddun kujeru da cushion da swing chairs. Saman falon wata katuwar Fitilace data sauko kaman daimons makale jikin wani katon ruwa da wasu irin kifaye keta yawo cikinsa. Hasken ruwan da fitalar sai ya bawa falon wani irin blue light kaman sararin samanyi. Yana zaune kan wata hadaddiyar cushion ya jingina kansa da hannun sa yana kallon saman gefen bakinsa wata katuwar tab'a ce yana zuga. Farar rigace a jikin sa mai botira da gaba d'aya an balle botirin sai sarkar wuyansa dake kwance k'irjinsa tana shining. Yarinyar ce gurfane gabansa tayi goho taba bashi head wanda take ji kaman zata mutu sabo yanda yake can bayan makogaronta . Hannusa guda d'aya dake baje kan kujerar ya d'aga ya kai kan tabar ya cire daga bakinsa ya fesar da wani hayaki cike da gwanancewa. A hankali ya sunkuyo ya watsa mata manyan grey eyes nashi fuskar nan a mugun hade. Kallonsa itama take da hopefully eyes idonta tab cike da hawaye. Samada da minti talatin kenan tanayi masa abu guda amma still yaki bata wani reaction. Gashin dokin dake kanta ya kama yana fidda sound na tsk daga bakinsa ya wani wurgar da kanta gefe. Aikuwa ta koma gefe tana jan uban numfashi da tari kaman zata shide. "Mtsw. Useless " Yace ransa a bace. "Get out" bata jira ya sake cewa ba karo na biyu ta kwasa a guje ta fice rike da rigarta da bata tsaya sawa ba. Dariya abokinsa kuma aminin sa FADEEL dake fita a shake saboda yanda yake can cikin duniyar, ya juya a mugun hankali ya watsa masa kallo kafin ya d'auke ya koma lazy ya wani kwanta kansa a sama yana kallon kifaye dake yawo cikin akwariyon din. "Da gaske yau kaine yarinya tana baka Head ka kasa bata reaction? What happen to....you" Ya k'arasa yana jan fasali da sake rike kugun yarinyar dake sukuwa a jikinsa sai wani nishi da sumbatu take. Baki ya cije yana zuba wani uban moan saboda yaji release nashi na kusa. Bai iya bashi amsa ba domin shi kansa bashi da amsar Abunda ke faruwa dashi kwana biyu. Yanda yake mayen sex but tun ranan da ya yi raping yarinyar nan he can't seems to enjoy the sex anymore. D'an tsaki ya yi saboda har yanzu ransa na mugun suya idan ya tuna marin da tofa masa yawun da tayi. Gani yake just raping nata is not enough dole ya yi punishing nata ko ya daina tuna abunda tayi masa. Tasa ya yi loosing dignity nashi wajen forcing kansa kanta abunda bai tab'a yiba a rayuwar sa. Dole she most pay for this. Wani irin zukar tabar ya sake lokaci guda ya shanye ta ya fesar da wani uban hayaki idansa ya kad'a ya yi jazur. ➺➺➺➺➺➺➺➺ Wajen magriba ina zaune ina tilawa Maa ta shigo fuska a murtuke. Gabana ya yanke ya fad'i nayi saurin ajiye qur'anin na mik'e ina kallonta bakina na rawa zan gaida ita ta rigani magana "Ungo wannan kayan kisa ki hanzarta ki fito baki na jiranki falo" Leda ta mik'o min na kai hannu na k'arba ina kallonta ta watsamin harara kafin ta juya tana cewa karna bari ta dawo d'akin ban shirya ba. Numfashi na sauke a hankali na maida idona kan ledan na buɗe. K'ananan kayane a ciki riga da wando rigar mai shara-shara dake dauke da gidan bra sai y'ar top da zan d'ura a kai. Baki na cije raina in ya yi dubu ya b'aci. Me Maa take nufi danine?. Da dai nasa wannan kayan na fita gwanda ta kasheni. Jefar da ledar nayi kan gado k'irjina na zafi. Wajen minti biyar da fitarta sai gata ta dawo d'akin. Aikuwa ganin ban shirya ba ranta in ya yi duba ya b'aci da tsawa tace "Wasa nake dake ne? Bazaki tashi ki shirya ba?" "Kiyi hak'uri Maa amma kayan sun nuna tsiraici da yawa bazan iya sa su ba" Dariya ta d'anyi mai tattare da b'acin rai tace " to bari kiji idan har ni ce uwar ki sai kin saka kayan nan don ubanki. Shegiya munafuka kinje kin kaiwa wani shegiya kan ki zaki zo kina nuna min ke mai tsoron Allah ce? Waye baya tsoron Allah ? Eh nace waye jahili?" Kai na sunkuyar kaina hawaye na sauka kan fuskata. Bazan iya jure irin wannan mugayen kalaman da take fad'i kaina ba "Wlhi ma kiji tsoron Allah, Allah baya barci ina sane dukkanin wani abu dake faruwa a fili kuma a b'oye. Ban tab'a aikata zunaba kuma bana fatan Allah ya jarrabeni da wannan kaddara na zubda mutunci na da kimata a idan duniya. Allah shine abun tsoro ba mutum ba kuma gareshi na dogara nasan abunda ya sameni yana daga cikin kaddarata ne ina kuma fatan cinyewa. Ubangiji baya durawa bawansa abunda bazai iya d'auka ba. Idan duniya ta zargeni da aikata abunda ki ke aikatawa zan jure domin Allah shine masani, amma bazan jure zargin dake fitowa daga bakin mahaifiyar data haifeni...." Tas. Ta d'auke ne da marin da saida naga wuta. Bata jira na dawo daga jimamin zafin marin ba ta sake d'auke ni da wani saida na zube a wajen dafe da kunci ina gursheken kuka Da ihu take cewa " dan ubanki ni zaki zaga? Harni zaki gayawa akwai Allah? To don k*tmar ubanki kar ki saka kayan nan da minti biyu kiga yanda zanyi dake. Shegiya bakin hali da bak'ar zuciya wadda haihuwar ta bai amfani da komai bai sai nadama da dana sani , banda kunci da takaici da haihuwar ki ya jefa rayuwata" Sosai nake kuka ina jin kalamanta kaman mashi take sawa tana sukamin a kahon zuci. Ji nayi gaba d'aya rayuwar ta fita daga kaina a zafafe na tashi tana tsaye na saka kayan zuciyata ta gama karyewa. Tana tsaye harna gama ina kuka sosai sai zuba huci take kafin tayi kwafa tayi waje na bita jikina na rawa ga wani irin zazzabi da nakeji yana neman rufeni. [27/06, 10:16 am] Ashantyluv: 𝐁𝐀𝐇𝐈𝐘𝐘𝐀 𝓓͟𝓮͟𝓼͟𝓽͟𝓲͟𝓷͟𝔂͟ 𝓸͟𝓻͟ 𝓯͟𝓪͟𝓽͟𝓮͟? ©𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂𝓵𝓾𝓿 𝙰𝚜𝚑𝚊𝚗𝚝𝚢𝚕𝚘𝚟𝚎@𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜.𝚌𝚘𝚖 【ch5】 Wasu manyan alhaza ne su biyu zaune falon cikin manyan kaya. Suna ganin mun fito suka mik'e suna washe baki idansu kyam a kaina. Babu tsoro ko tunanin wani abu zai faru dani naji tana cewa "Gata nan Alhaji kuje sai kun dawo, Allah ya kiyaye hanya " Da sauri na d'ago ina kallonta jikina na rawa saboda kukan da nake amma na kasa furta komai sai lebena dake ta motsi. Mugun kallo ta watsamin mai tattare da gargadi kafin ta mayar kan Alhajin da sukayi hanyar waje. Sai yanzu naji ina ma Lee yana gidan ,tabbas kasancewar sa a gidan babbar rahama ce a gareni. "Walahi, kinji rantsuwa da nayi ki ka kuskura ki ka basu wata matsala a hanya sai kin kwammace baki zo duniyar nan ba. Karma kiyi gigin dawowa gidan nan don sai dai a haifi wata bake ba" Yanda tayi maganan sosai na hango tsantsan gaskiyar ta zuciyata gaba d'aya ta k'arasa karyewa kukan da nake a take na nemeshi na rasa. A hankali na juya kaman wacce aka zarewa ruhi na fice ina kallon k'asa mind d'in gaba d'aya baya tare dani. Hannuna naji an kama an sakani cikin mota dana kasa kwacewa maganan Maa shine kawai kemin yawo cikin kunne. Dama uwa na tsanan abunda ta haifa haka a duniya har tana masa fatan mutuwa ko bada kashedi ita zata kasheshi da kanta? Bansan minti nawa muka d'auka muna tafiya ba saida naji hannu kan cinyata sannan hankalina ya dawo jikina na d'ago kaina kaman an jani da lantarki. Gaba ɗaya n su suna zaune bayan motar ashe direbane yake ja. D'aya sosai yake gab dani kaman zai shigemin ciki shine ya d'ura hannun kan cinyata. Yanda hankalina baya jikina shiya hanani jin motsowarsa saida ya tab'ani. Bansan me yazo kaina ba sai tsintsar kaina nayi dajin wani irin k'arfi na d'aga hannu da iya k'arfi na na d'auke shi da mari saida gaba d'aya motar ta amsa. Wani irin shiru motar ta d'auka na yan sakanni shi kansa direban saida ya juyo motar ta kwace masa ya yi saurin maida hankali kan sitiyarin motar. "Ke ashe baki da hankali baki da kunya? Kinsan wa ki ka mara kuwa?" D'aya Alhajin ne ya yi magana ransa a b'ace cikin natsawa kafin wanda na maran ya k'arbe da ƙaraji yace "Dan ubanki zan ladabtar dake kud'i dana biya a kanki bazai tashi a banza ba. Har zaki d'aga hannu ki mareni y'ar iska mara tarbiya ko da yake waye zai baki tarbiya kina tare da tsinanniyar uwa ,jahila, karuwa..." Ban bari ya k'arasa ba na sake d'auke shi da wani marin jikina na rawa.zsn iya jure komai amma banda zagarmin uwa. Uwa, uwa ce komai lalacewar ta. Bani da kowa duniyar nan sai ita dole na sota duk irin bak'in halinta. Gurnani naji ya yi yaja kutuntuma min ashar gaba d'aya sukayo kaina banji wani abu ba na buɗe murfin motar a guje na wuntsula kan titi. Allah ya taimake ni babu wasu motoci dake wucewa ko suke tawowa amma da hakan zai kasance wata kila da hakan yafi na mutu da zama cikin wannan duniyar. A kwance na mirgina gafen titin sosai kuwa na kurje gwiwa da hannu saboda yanda na fad'o kan titin ga motar ba k'aramin sharara gudu take ba. Kyee naji motar taci burki daga nesa dani kad'an na hangosu sun fito a guje sunyo inda nake sai ihu suke da danna uban ashar. Ganin sun nufoni na yunƙura da sauri na mik'e na kwasa a guje na shige jeje da sai yanzu na lura mun d'auki hanyar barin gari ne shi yasa babu wasu motoci sai dana shiga daji na hango hasken fitila na tunkaro su. Wata katuwar bishiya na samu da kyar na haye ina sauke ajiyar zuciya ga zafin ciwo da jikinta yake saboda buguwa da nayi a k'asa. Ina kalli suka gama dube-duben su kafin su koma mota suna hayani har abun yaso ya zama fad'a tsakaninsu ina jin suja cewa dole su koma su k'arbi kud'in su don bazasuyi asarar mak'udan kud'i da suka bayar ba. Ido na lumshe tare da cije leb'e hawaye suna gudu kan fuskata. Yanzu kudi yafi mata rayuwata da halin da zan shiga? Tun ina kuka a fili har ya koma na zuci tsananin azaba da gajiya ban san me ya sake faruwa ba daga lokacin, suma nayi ko kuma barci nayi ?Allah masani. Iska naji mai k'arfi na kaɗawa da d'an haske da nakeji kaman yana dukan fuskata yana kuma d'aukewa. A hankali na buɗe ido na ashe rana tayi sosai garin ko ina ya d'auki hayaniyar mutane da motoci da nake ji suna ta kai komo kam titi. Ganyen bishiyar da nake kai shi yake kare tsananin hasken rana dake dukan fuskata idan iska ta kad'a shine yake yin mitso a she. Yunk'urin mik'ewa nayi daga yanda nake kwance kan reshen bishiyar na rungume ta saboda karna fad'o. Banji motsin abu dake kwance wuyana zuwa gashin kaina ba saida na motsa sannan naji hiss tssss na miji yana motsi wuyana a hankali. Mugun firgita nayi na kame na daina motsi k'irjina na harbawa kaman zai fito waje. Ya Rabbi shikenan rayuwata tazo karshe? Hawaye ne suka biyo kuncina idan har rayuwata tazo karshe ina farin cikin komawa ta ga mahalillici na amma bazanso na mutu cikin wannan shigar ba, babu wanda yasan na mutu bare ayi min wunka a suturtani, tabbas bana wasa da ikon Allah domin yana kallo abunda ke b'oye kuma yake a fili. Nasan da ikonsa zai kawo hanya da koba yauba wata rana za'a ga gangar jikina. Numfashi na sauke na maida idona na lumshe ina kiran sunan Allah. Banyi zato ba naji micijin ya sauka daga jikina gaba d'aya ya wuce ta gefeb wuyana. Yanda ya dade yaba wucewa ya tabbatar min da bak'arimin miciji bane. Sama da minti biyu da wucewar sa sannan na iya motsi ina sauke numfashi a guje tare da yunƙurin buɗe ido. A firgice naja baya ina kiran sunan Allah ganin sa gabana ya nannade ya fasa kai yana kallona sai fito da harshe yake. Innalillahi wa innalillahi raji'un. Firgice da tsoro yasa yanda na wuntsula kaman zan fad'o na kasa wani motsi na rike reshen jikina babu inda baya rawa. Tsawon sakanni na d'auka a haka sai kuma naga ya sauke kansa a hankali ya biyo wajen kafata kaman yana shafa ni kafin ya wuce gaba d'aya ya barni kan bishiyar. Bansan sanda na fashe da matsananci kuka ba domin na gama fidda rai ga rayuwa. Da kyar na iya lallashin kaina nayi shiru sannan na fara yunƙurin sakkowa daga kan bishiyar ina tunanin banyi sallah isha ba bare asuba gashi alamu ya nuna azahar na gabda gabatowa saboda tsananin takewa da rana tayi. A hankali nake jan kafata da sukayi tsami kai gaba d'aya jikina ya yi tsami ciwo ko ina duk ya bushe da jini. Titin na sake fitowa hannu rungume a k'irjina saboda babu mayafi ko hula tare dani sai gashin kaina daya bazu kaman mahaukaciya. Tafiya kawai nake ni kaina bansan inda nasa gaba ba ina jin yanda mutane na k'afa dana mota keta jefamin kalli cike da tuhuma. Kallo na Allah wadai saboda shigar da suka ga a jikina wasu kuma kallo sukemin kaman mahaukaciya. Bansan tsawon lokacin dana d'auka ina tafiya ba saida na isa bakin wani katon shago dake cike da mutane ana ta siyaya sannan naji yunwa da ishi sunmin rubdugu. Waje na samu bakin shagon na zauna ina bin mutane dake fitowa da kallo da dasun ganni zakaga sun buga tsalle na firgici, a guje suke wucewa hakan ya yi sanadin mai shagon ya fito rai a b'ace da sanda a hannun sa yana korani . Kukan ma sai naji ya kasayin don makogaro na gaba d'aya ya bushe. Kora yamin ta wulakanci harda had'awa da yara suna bina da jifa da ihun mahaukaciya. Ina jin yanda mutane keta jefana da zagi wasu har suna cewa Allah ya k'ara yanzu gashi nan ai ina girbar abunda na shuka daga yawon karuwanci na k'are a mahaukaciya. Zuciyata kawai nake had'iye ina ji ina ma Allah ya d'auki raina yanzu na huta koda bazan samu masu tsayawa a kaina ba bare a suturtani, nasan akwai Allah. But abun is to much for me, wata kila idan na maida kaina mahaukaciyar zanfi samun sassauci cikin zuciyata. Saida na share wasu hawaye da suka biyo kuncina sannan na juya a hankali na kalli yaran da suke bina suna ihun mahaukaciya. Baki na cije saboda gursheken kuka daya zomin nayi saurin shanyewa kafin na yunk'ura na kwasa nabi yaran a guje suka juya suna ihu da dariya dad'i duk ya ishesu. Haka nayi ta binsu suna jifana da kirana mahaukaciya duk sun jimin ciwo kafin na juya ina jan jiki na bar wajen gaba d'aya. Tsawon kwana biyu na d'auka cikin wannan yanayin duk na fita hayyaci na duk inda na wuce na zama abun gudu da ihu. Yunwa da ishi ji nake kaman zan had'iye makogaro . Ina kwance gindin wani tsohon shago na langa-langa wanda alama ya nuna da akwai mai shayi dake siyarwa kafin ya tashi. Tsananin yunwa da kukan da cikina yake yasa na kasa tashi ina kallon mutane dishi-dishi da suke kallona ana wucewa da sauri. Daga can nesa dani naji ana kiran sallah la'asar cikin masallaci dake nan cikin layin. '𝘵𝘢𝘣𝘣𝘢𝘴 𝘉𝘢𝘩𝘪𝘺𝘺𝘢, 𝘪𝘥𝘢𝘯 𝘩𝘢𝘳 𝘢𝘫𝘢𝘭𝘪 𝘺𝘢 𝘳𝘪𝘴𝘬𝘦 𝘢 𝘩𝘢𝘬𝘢?, 𝘸𝘢𝘯𝘦 𝘩𝘶𝘫𝘫𝘢 𝘬𝘪 𝘬𝘦 𝘥𝘢 𝘪𝘵𝘢 𝘢 𝘬𝘢𝘯 𝘬𝘪 𝘸𝘢𝘫𝘦 𝘮𝘢𝘩𝘢𝘭𝘪𝘭𝘭𝘪𝘤𝘪𝘯 𝘬𝘪?' Zuciyata ta ce dani hawaye suka biyo kuncina masu zafi na fashe da kuka a fili nace "Na tabba asararriya tunda na d'urawa kaina abunda Allah bai d'uramin ba, na yaudari kaina da Mahalillici na, na durawa kaina cutar da nasan ba ita gareni ba, shin idan Allah ya jarrabeni da ciwon hakan ya ya zanyi kenan?, nasan wannan babban laifine na aikata but zuciyata bazata iya cigaba da d'aukan halin da nake ciki bane. Na d'auka hakan zai rangwanta halin kunci da tsananin da rayuwata ke ciki ,amma babu wani hutu saima tsanani da rayuwata ta sake wanda ni na jawowa kaina domin Allah baya durawa bawa abunda bai iya d'auka kuma dukkanin wani tsanani yana tare da sauk'i" K'irjin na dafe dake tsananin ciwo na fara kiran "Astagfirullahi wa'atubu ilaihi" Ban sauke hannu ba cikina ya wani mugun murd'awa bugun zuciyata ya tsananta kaman mai shirin samun heart attack. Babu zato naji a kaina murya na d'aga da sauri ina kallon dattijuwa dake tsaye a kaina tana min sallama. Ganin ban motsa daga inda nake ba saboda tsananin ciwo ta sake motsawa babu digon tsoro kan fuskarta tare da k'ok'arin kawo hannu ta tab'ani. Inda dane da nake ciwon karya dana kaiwa hannun nata mugun cizo. "Ya Rabbi" Tace da sauri tana k'ok'arin kamani akuwa sai sha na dinga kelaya uban amai tsabar yunwa wani yellow mai wari. "Subhanallahi, sannu, sannu baiwar Allah. Tun daga nesa na hango ki hankalina ya bani hak'ik'a ke ba mahaukaciya bace kaman yanda kowa ke tunani. " Jin maganan ta ya sake karyamin zuciya na fashe da kuka mai tsananin ban tausayi. Babu kyama ko tsoro ta kamani da sauri ta mik'ar muka hau tafiya sai kallon mu ake daga cikin samarin dake layin harda masu taremu suna cewa "Baba Mahaukaciya cefa karta cutar dake" Kai kawai take girgiza musu tana murmushi bata tanka ba muka fito daga layin zuwa bakin titi. Taxi ta tare wanda da da fari yace bazai d'auke mu ba saida ta kwance kulli dake kugunta ta k'ara masa kud'i sannan ya amince ya d'auke mu. Jikinta ya kwantar dani tana d'an buga kaina da yimin sannu sai nishi nake da kyar idona nata lumshewa. Sama-sama naji suna magana da mai taxi tana masa bayani ba mahaukaciya nace kaman yanda yake tambaya mutanene da basu fuskanci hakan ba. Shi kansa ya yi mamaki daya juya ya k'are mata kallo kuma ya tabbatar Tabbas yarinya ce k'arama kuma babu alamun ciwon hauka tattare da ita . Cikin d'an kullin dake hannun Baba ta warware ta fiddo zani ta rufamin tana cigaba da jeramin sannu. K'aramin gida mai taxi ya yi parking ginin irin na k'asa ne. Layin duk gidajene na gargajiya amma ko ina layin fess suna da tsabta wajen gyara kwata da kuma kula da wajen zuba shara. Baba ita ta sake kamani muka fito yanzu ina ji kaman zan mutu saboda yanda cikina ke tsananin ciwo. Nayi mamaki da naji mai taxi nayimin sunna da fatan samun sauki. Dazu da kyar ya d'auke mu a motar kome ya chanza masa tunani kuma? Allah masani. Cikin gidan muka shiga dake d'auke da d'an tsakar gida an shareshi tas ga band'aki da aka rufe da buhu gefen sa akwai y'ar rijiya sai murhu. D'aki biyune da suke a rufe ta bud'e guda d'aya muka shiga. Falo ne matsakaici dake d'auke da d'an kafet da gujera guda d'aya dage gefe akwai y'ar tv irin mai kaman akwatin nan da receiver . Ko ina d'akin fes ga fanka da wutar nefa harda d'an firij. Kan kurejar ta kwantar dani kafin ta miƙe ta da sauri ta bud'e firij ta d'auko wura a kwanan sha mai kyau ta mik'omin. Ban musa ba na kafa kai saboda mugun ishin da nakeji ina gama sha kuwa na sake kelaya uban amai. Bataji haushin b'ata mata d'aki da nayi ba saima sannu da take ta jeramin da mike da sauri ta fice ta dawo da tsumma ta goge wajen. Ficewa ta sakeyi ta dawo da k'aramin kofi ta mik'omin tana cewa "K'arbi wannan kanwace data zargade kisha domin harda Ulcer da yunwa ke damunki. " Badan naso ba na k'arba jikina na rawa na kafa baki na d'an sha kad'an. Tabbas kuwa ban jima ba na fara jin dan dama-dama. Ganin ciwon ya d'an sarara ta fita da kawomin kunu cikin kwano da tuwon dawa miyar karkashi data dumama sai tururi da kamshin man shanu yake. Take kuwa yawuna ya tsinke na k'arbi abinci ina ci hannu baka hannu kwarya kaman zan had'a da kwanon na cinye.

Chapter 4 of 11