aka bani makami tsab zan shek'a shi lahira saboda yanda raina yi yi kololowar b'aci. Wata y'ar dariya ya sake saki da gaba d'aya saida fararen hak'oran sa suka bayyana dimples nashi na lotsawa ya sake cewa
"You know? Ina karantar ki like an open book. I know that look. You wish to kill me ko?"
Wani irin deadly sneer na sake bashi ya sake wata dariya cike da nishadi.
"Oo I'm so loving this. Take her to work"
Kawai yace ya juya ya shige motar ya mata wani uan key da wani irin gwanancewa ya fisgi motar ya barni da Bodyguards nashi. Da ido nabi motar harya koma side nashi ina kallo ya fito ya shige ciki. Ajiyar zuciya na sauke na kasa motsi naji an rike habata da y'ar murya ance
"Muje ciki a nuna miki aikin ki"
Dattijuwa matace amma bata kai Baba ba shekaru da alama. Wani b'angaren muka yi ta gefen ido na hango Hassa'u da First Lady tsaye bakin balcony nata na kasa taba kallona cikin matsananci b'acin rai, Hassa'u kuwa kaman zatayi kuka. Nan ma babban wajene mai kyan gaske an kwatashi tako wace kusurwa. Babban falon da muka shiga muka iska babbar mace zaune cikin kujeru tana karatun littafin hisnul-muslim falon babu kowa si ita da wasu manyan mata biyu zaune kan kafet wajen kafarta da alama masu kula da ita ne. Tsohuwace kyakwawar gaske duk da cewa ta tsufa gashine da ita har gadon baya ga hancin nan har yanzu yana das kaman an zana mata shi. Shigar mu duk suka juyo suna kallonmu har muka k'arasa. Da girmamawa naga matar da muka shigo ta zauna nima na bita kaina a k'asa.
"Wacece wannan Zulai?"
"Allah yaja da ranki ya k'ara nisan kwana sabuwar mai aikin da jikan ki ya kawoce."
"Au,au to to. Kece yarinyar da aka ce yanzu Fulani ta saka a kai cell? BAHIYYA ko?"
Ikon Allah har labarin ya bazu kenan? Kai kawai na iya d'agawa naji tayi murmushi tace
"Matso nan kinji. Kar ki damu da Fulani haka take dasan iko kan bayinta. Ina so ki sani a yanzu kin tara makiya da yawa cikin gidan nan tunda har labari ya bazu cewa Aizak da kansa ya kawo ki cikin gidanna. Saboda shiya kawo ki nima na yarda na aminci dake domin kinfi duk dubbunnan matan dake gidannan. Tun yanzu zan baki amana Bahiyya akwai abubuwa da yawa da suke faruwa b'oye ina so ki dinga barci da ido d'aya, kunnen ki kuma ya kasance koda yaushe a bud'e. Kisa ido sosai kan dukkanin wani abu dake shige da fice b'angaren Aizak. Zan baki wannan ragamar ina fatan zaki kula ki kuma bashi kariya a matsayin ki na personal Maid nashi?"
Eh? Me wannan tsohuwar ke cewa ne? Na tara makiya saboda me? Don me kuma zan d'urawa kaina nauyin abunda bazanyi ba?. Shi waye nawa da zan bashi kariya?.abune da bazai sabu ba domin na karan kaina da tasan abunda ke cikin zuciyata kansa bazata gayamin wannan maganan ba. A fili na amsa da kyar da InshaAllahu. Hakan kuwa ya sake mata dad'i tace maza a kaini a nunamin abunda zanyi. Muna fitowa Zulai ta faramin lissafi.
*Kula da abincin sa
*kula da mai kai masa abinci
*fara duba abincin nayi testing nashi kafin a kai masa d'aki wanda tace yanzu nike da wannan nauyin a kaina
*kula da yi masa wankin na bedshet.
*kula da d'akin sa. Shara ,gyaran gado, band'aki da sauran su.
*yana shan coffe bayan magriba k'arfe bakwai daidai kafin ya kwanta zaki had'a ki masa
Saurin kallonta nayi cikin rashin fahimta nace
"Ban gane magriba ba? Aikin har sai ankai magriba? Na d'auka da zarar na gama abunda nake zan tafi gida?"
Y'ar dariya Zulai tayi tana girgiza kai tace
"Baki san komai ba shi yasa. Aa dole bazaki tafi ba sai ya kwanta barci duk wasu personal maid nashi idan suka zo sunzo kenan basa tafiya amma ke yace a barki ki dinga tafiya har ya bada direbe da zai dinga kaifi gida kuma yana d'auko ki da safe"
Kaina ya sake daurewa wane irin aikine wannan? Saboda me zai bani direba? Ce masa nayi ina bukata?Cigaba tayi da lissafi daidai muna shiga side nashi da uban kid'a ke tashi kaman zai fasa kunne.
*idan yana d'aki kar ki bari kowa ya shiga sai ya bada izni
*kullum da safe ana kai masa coffe kafin yaci kumi
*kafin ya gama shan coffee zaki had'a masa ruwan wanka
*kafin ya fito zaki chanza masa bedsheets zuwa sabo.
*duk ranan da zaiyi party ya kasance kece mai jagorartar sa. Ki kula da zuba ido kan abunda zaici tun daga naci dana sha
Wannan aikin bana Bodyguards nashi bane saboda me suke ta d'uramin abunda baya daga cikin tsarin aikina? Wannan aikine ko kuwa baiwa aka kai masa?. Daga bakin wata hadaddiyar k'ofa ta tsaya ta juyo tana kallona tace
"Ki shiga ki fara chanza masa bedsheets yanzu za'a kawo masa breakfast ki k'arba ki ajiye masa"
Bakina na motsa zance wani abu ta juya abunta ta barni tsaye bakin k'ofar. Kidan ba daga nan ke tashi ba na sauke ajiyar zuciya alamun baya ciki kenan. A hankali na bud'e d'akin na tura kai bakina d'auke da y'ar sallama. Wani irin sanyi kamshi ya daki fuskata saida na lumshe ido kafin na sanya jiki gaba. Ya Rabbi d'akina kaman ba duniya ba saboda tsananin had'uwar sa. Komai na d'akin white and golden ne ga d'aki tafkeken gaske kaman k'aramin flat house. Komai yana cikin d'akin har toilet da aka keway da wani shegen glass amma na waje baya iya gani cikinsa sai in ya danna wani abu dake jiki da zai bawa na d'akin ganin band'akin. Allah mai iko. Tsabar kallo baki na saki galala ina k'ara girmama ikon Allah. Tabbas Allah shine gagara misali mai arziki da bashi da iyaka kuma bashi da karshe.
Saida naji yawu ya fara bin gefen bakina tsabar kallo na dawo daga duniyar shagala dana lula na matsa wajen makeken gadon dake kewaye da wani rumfa kaman labule. Shi kansa abun kallona bare gadon. Makeken gadone dake dauke da filo wajen biyar masu laushi zanin gadon me shegen kyau sai kamshina yake gashi fes-fes. In banda kud'i ace kullum sai an canza zanin gado. Saboda girman sa da kyar na iya cirewa na ninnike kafin na buɗe wata kofa ashe kwanace irin mai kaman dakin nan. Ya Rabbi komai da drawers. Agogo, takalmi, kaya, belt, sarka, cambus. Kai abubuwa ne gasu nan birjik bazasu fad'u ba. Da kyar na sam drawers bedsheets wanda sunfi dubu a ciki. Sosai na duba na zabo wani mara nauyi da bai cika hayaniya ba na fito na shimfid'a. Ban gama ba naji an kwankwasa k'ofar nayi saurin gamawa na k'arasa bakin k'ofar na buɗe. Wata budurwace tsaye da kayanta gajeren sket da t-shirt.
Bansan me yasa ba sai naga kaman tana hararata na nuna ban kula ba na k'arbi katon tiren dake hannun ta dake shake da wasu uban flask masu shegen kyau.
Bata cemin komai ba ta wuce kaman tana fushi na bita da kallo kafin na tab'e baki na koma na ajiye abincin kan glass tebir dake d'akin mai kujeru uku. Abincin na zubawa ido wani tunani yazomin nayi murmushi mugunta. Band'aki na shiga kyansa bai saka na manta abunda nazo yiba na kwashi shampoo da conditioner na fito ina murmushi raina tas. Kular farko na buɗe dake d'auke da wani irin abinci ba irin namu ba. Shampoo da conditioner na zuba cikin cokali saboda kamshin su na diga kad'an yanda zai gauraye da abincin na juya. Haka duk nayiwa abincin kafin na koma kan drinks na d'auka nayi band'aki dashi. Bakina na wanke kumfar da yawun na mayar na juye masa cikin drinks din mai shegen hawa kai kamshin sa kaman zallan inibi na girgiza cikin kwalbar na maida murfin na rufe. Habawa jin raina nake tas ina ma nazo da yaji da gishiri amma zan fara yin guzurin su. Mu zuba nida shi shege ka fasa.
Harna gama abunda zanyi na fito bai shigo ba hakan yafi komai yimin dad'i. Turus naja na tsaya ina kallon corridor d'in da tunanin menene abinyi kuma yanzu?tunani nayi ko nahi tafiya ta kawai tunda na gama gobe na dawo wata zuciyar tace ki dai bari zuwa anjima kiga abunda hali zaiyi. Da wannan na taho ina d'an dube-dube don na sake gane ko ina sosai. Ina shan wata y'ar kwana gabana ya yanke ya yi wani mummunan fad'uwa nayi saurin komawa da baya na mak'ure jikin banga. AISAR ce ta shigo taci uwar kwalliya cikin k'ananan kaya abun har ya yi mata yawa. Idan har na tsaya anan tsab datasha kwana zata ganni na juyo da sauri zan koma daidai tana kwaryo kwana . Aikuwa naji muryar ta cikin yauki tana kira
"Ke wacece ke? Bakiji ina magana ba?"
Ras gabana ya sake fad'uwa na tsaya chak ban juya ba jikina na rawa. Me zanyi? Me zanyi. Babu zato wannan muryar ta ratso daga gabana da wannan deepness nata
"What are you doing in my house?"
Da azama na d'aga kai na kalleshi tsaye jikin k'ofar sa hannu duka rungume a k'irji. Sautin takarminta naji kaman ta k'ara sauri tayo inda nake gadan gadan tsabar tsoro na k'asa motsawa naci gaba da tafiya.
A zafafe naji yace
"Kar ki sake tako kafarki nan. Get out from my house"
Tana gab dani ko nace bayana naji ta tsaya chak rai itama a d'an b'ace tace
"A gaban maid naka ka ke cewa na fita Babe? Ka manta muhimmanci abunda ke tsakanin mu?"
Wani kallo ya mata na baki da hankali na had'iye yawu saboda hucin numfashin ta dake sauka gefen keyata. Sauke hannu ya yi tare damin wani kallo da naji kafafuwana na neman kadani. Murya ya d'an sassauta yace
"Get in and finish your work"
K'ofar ya bud'e yana kallona kaman an hankadani na daga k'afata da mugun sauri na wuce d'akin. Tana shiga ya maida k'ofar ya rufe ya juya kan Aisar dake kallonsa baki a sake. Wacece wannan yarinyar da har take da ikon shigar masa daki haka kai tsaye kuma yake wulakanta ta a gabanta. Gabanta ya tako da wata irin tafiya da taji kaman ta juya ta zura a guje. Rumfa ya mata da katon jikinsa murya da tsananin kaushi yace
"Wannan shine last warning naki. Duk sanda ki ka sake tako kafarki gidannan ba tare da invite ba sai kin raina kanki. Blame yourself kan abunda zanyi miki. I will have punish you yanzu but your not worth it. Saboda haka idan kina da sauran dignity daya rage miki leave my house"
Kaman ta had'iye zuciya ta juya fuu harda had'awa da gudu. Da mugun kallo ya bita tare da jan tsaki yace
"Clingy B*tch"
Yana maida k'ofar na kona jiki na jikina hannuna dafe da k'irjina. Akwai babbar matsala aikina cikin gidannan bama kad'an ba. Tabbas wata rana wani zai ganni duk sanda suka ganni kuma shikenan cover nawa zaiyi blow. Tsakani da Allah yanzu nafi jindadin rayuwata bana son abunda zaiyi sanadin Maa tasan inda nake bare hartazo nemana. Zamana da Baba ya fiye min komai. Motsin tab'a k'ofar da naji yanayi nayi saurin matsawa na bashi hanya ya shigo. Da gefeb ido ya kalleni da wani smirk kan fuskarsa direct ya wuce kan tebir. Wani kululu cikina ya yi tunawa da muguntar da nayi masa. Da hanzari na kama k'ofar zan fice naji ya yi y'ar tsawa
"Kar ki kuskura ki fita a d'akin nan."
Juyawa nayi na kalleshi da straight face ya wani yi murmushi kafij ya sake takowa inda nake tsaye bakin k'ofa. Ganin bai daina matsowa ba na faraja da baya harna jingina da k'ofar ya k'araso kaman zai shige min jiki ya dafe k'ofar da duka hannun sa gefe da gefen kaina. Kara danna jiki nayi jikin k'ofar ina zabga masa harara cike da tsana. Shifa bashi da tarbiya gani yake hakan ba komai bane a wajen sa tunda rayuwar turawa yake. Don ya sake kunna min wani haushin ya wani rankwafo da fuskarsa wajen tawa nayi saurin kauda tawa gefe bakina na rawa amma ina tsoron kalman da zata fito daga bakina.
"Do you think I'm stupid?"
Wani abu dake makale makogaro na ya wuce da kyar nayi saurin juyowa na kalleshi. Gira ya d'aga da wannan shegen smirk yace
"Ina ce an sanar dake sai kin fara tasting abincin kafin naci ko?. Well go and eat it"
Kaman ya dokamin guduma a kai haka naji na zuba masa ido yana wannan smirk nashi. Da gaske yake so yake naci abincin? Ko yasan na zuba masa wani abu a cikine?
Baku tunanin anan kaman ya yi saving nata ne?
Mheeee i don't know how I'm feeling about this chap, hmmm, anyway enjoy . The story is a slow burn dake moving slowly saboda akwai different twists. Next chap will be better. Comment and like 🤌
[10/07, 9:28 am] Ashantyluv: 𝐁𝐀𝐇𝐈𝐘𝐘𝐀
𝓓͟𝓮͟𝓼͟𝓽͟𝓲͟𝓷͟𝔂͟ 𝓸͟𝓻͟ 𝓯͟𝓪͟𝓽͟𝓮͟?
Not edit!
【ch10】
Yanda zuciyata ke bugawa nasan babu tantama yaji don wani d'aga gira ya yi da shegen murmushi dana tsana yanzu sama da komai yace
"What? Are you scared to taste it? Does that mean baki da gaskiya kenan? What did you do with my food?"
Wani mugun yawu na had'iye daya tokare ni a makoshi ina kyefta ido kaman kyanwa. Gira ya d'aga fuskarsa cike da amusement ya sake cewa
"I take that as a yes. Me ki ka yi min da abinci ?"
Kar kiyi saurin bada kan ki zuciyata tamin gargadi da dakiya nace
"Ban gane me nayi maka da abinci ba me zanyi maka da abinci? Ka d'auka kowa irin kane da bashi da abunyi ?"
Ina rufe baki ya saki wata sexy dariya kansa na komawa baya kad'an. Da yaransa na uwa wato korea yace
"Ahh ,neomu johayo" (너무 좋아요) (i like this very much)
Me kuma yace? Badai zagina ya yi ba? To walahi kuwa idan zagina ya yi nima banza kawai. Ai bakai kad'ai ka iya zagin ba. Maganan da nake tunanin a zuci nayi ashe a fili nayi bansan harda murguda baki da zabga masa harara ba saida naji sosai yana dariya daya sashi komawa baya yana neman fad'uwa. Ido kawai na zuba masa ance makiyi yasan abu mai kyau. Yanda yake dariya sai ta k'ara masa wani mugun kyau naji idona kaman an dalleni da torch. Ki saita nutsuwa ki mana kar kiyi saurin bada mu. Saurin d'auke kaina nayi daga kallon nayi saurin juyawa da sassafar na buɗe k'ofar na fice kafin ya hanani. A hankali ya mik'e tsaye da kyau daga dariya da yake shekawa harda d'an guntun hawaye. Kofar ya zubawa ido yana d'an murmushi tare da lashe lebensa. Yarinyar is very interesting and funny. Matsawa ya yi jikin wata hadaddiyar drawer ya bud'e ya d'auko wata katuwar tab'a ya kunna tare da komawa kan cushion ya kwanta yana kallon silin ga tabar a bakinsa yana fesar da hayakin da wani irin gwanancewa. Hannu ya d'an daga kad'an ya yi waving sai gaba d'aya fitilar d'akin ta d'auke wata blue light mara haske ta maye waccan. Daga nan inda yake zaune yana fuskarta wata drawer saiga dankareriyar plasma bango guda ta sakko daga sama kaman an boyeta cikin silin. Da wani kasala ya d'auki remote ya danna saiga Bahiyya radau jikin tv kaman kace mata ke ta amsa. D'an murmushi ya yi ya zubawa tv idon yana kallo tun shigowar ta d'akin da muguntar data had'a masa na zuba masa shampoo da conditioner cikin abinci. Harda wanke baki ta juye masa ruwan cikin lemo da tofa masa yawu. Maimakon yaji b'acin rai like how dare she zata masa wannan rashin mutuncin, no sai abun ya bashi dariya ya yi ta dariya shi kad'ai kaman mahaukaci. Hakan kawai yake jinsa cikin wani irin farin ciki da shi kansa ya rasa na menene.
Ban tsaya ba saida na fito daga b'angaren nashi gana d'aya sannan na samu wani d'an kebantaccen waje kaman irin tsohun garden d'in nan dake d'auke da irin kujerun nan na seminti. Yanayin wajen ya nuna kaman ba'a cike zama ba gashi cike yake da furanni amma duk mutu saboda rashin kulawa. Guri na samu na zauna sai a lokacin na iya sauke numfashi da nake rik'ewa. Wai Allah ya soni nasha da kyar yanzu daya sani cin abincin nan ai dana kwana yau ina amai inma ban kwanta ciwo ba. Ance idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi gajere. To Allah yamin lidifi amma walahi idan ya sake kawon wargi nima sai na rama ya yi duk abunda zaiyi. Nan wajen na zauna iska mai dad'i na kaɗawa ina ta tunani kala-kala har wajen azahar. To ni na manta ma ban tambayi inda zan dinga karban abinci ba domin ba zuwa nayi aikin da zan hura kaina da yunwa ba.
Jin an fara kiran sallah na mik'e neman wajen alwala. Nan cikin wajen na samu fanfo nayi alwala na dawo inda nake zaune na cire ɗankwalin kaina cire na shimfiɗa nayi sallah. Bayan na idar na mik'e na koma ciki tunanin yanzu me zanyi?. Nan bakin k'ofa d'akin sa na iske yarinyar data kawo masa abinci dazu yanzu ma rike da wani sabon tiren an shek'a uban kayan abinci kana gani kasan ya mata nauyi. Da sauri na k'arasa ina mamakin abunda ya hanata shiga. To dama can inba personal maid nashi ba babu wanda yake shiga d'akin ne. Tna hango ni kuwa ta wani saka san magani ni abunma sai ya bani dariya. Da y'ar faraa na k'araso kafin nayi magana ta rigani rai a b'ace
"Tun dazu ina ki ka tafi ina tsaye a nan ina bugu baki buɗe ba?"
Ikon Allah nace a zuci amma a fili na sake yin yake nace
"Yi hak'uri na dan zagaye ne nayi sallah"
"Eh dole kije kiyi sallah tunda ke kad'ai ki ka damu da addini. Kar dai ki bari tunanin ko ke wata special aba ce yasa ke kad'ai ke iya shiga d'akinsa har kiyi amfani da wannan kice zaki kai kanki inda Allah bai kai kiba"
Baki na hangame cike da mamakin kalaman ta. Duk menene ya yi zafi haka data tsaneni haka nan kawai. Ban gane babu wanda yake shiga d'akin saba? Bata jira na nace wanu abu ba ta ajiye farantin ta juya fuu ta barni nan tsaye da sakakken baki. Allah ance iska taba wahalar da mai kayan kara. To Allah ya kyauta. Kaman kuwa yanda nayi tunani yanzu tiren yafi n dazu nauyi da kyar na d'aga bayan na buɗe k'ofar da najita a bud'e na shiga. Turus na tsaya bakin k'ofar bayan na juyo. Yana fa kwance kan wata katuwar farar kujera dake ta swinging a hankali k'afarsa d'aya nata reto da kujerar saboda ya sakko da ita ya zubawa k'ofar ido da lumshashshun idanuwansa da gashi ya kusan rufewa alamun bai jima da yin wanka ba. Har ila yau dai farar rigace a jikinsa da bai balle botiran ba da wani gajeren wando mai tazuge.
Shi wanna shegen k'irjin baa rufeshi ne kodan yaga Allah ya bashi body? Banga sarkar ba wuyansa yanzu da alama ya cirene ya huta. Haushi ya kamani dama yana ciki yana ji ana bugu amma yak'i buɗewa. Kai kawai na jinjina na wuce wajen tebir na ajiye masa abincin banga na dazu ba Allah yasa ya cinye. Dariyar mugunta nayi a raina na juya zan sake ficewa naji ya kirana sunana very gently da saida tsigar jikina ta tashi kafafuwana sukayi sanyi kalau. Dama yasan sunana?
" Bahiyya "
Yanda ya kira sunan da hausarsa da bata fita sosai sai ka rantse shi kad'ai ya iya fad'an sunan nawa. A hankali na juyo jiki a mace na kalleshi. Muna had'a ido ya kai taba bakinsa a hankali ya zuga tare da fesar da hayakin sama nayi saurin yatsina fuska.
"Come and eat"
Ya sake cewa yana kallona. Ido na zuba masa ina jira naji yace wasa yake amma shiru. Kaman yasan tunanin da nake yace
"It's your job to eat first no?. D'auki plate ki zuba abinci ki faraci "
Baki na bud'e zanyi magana na fasa. Abincin na nufa na buɗe hadaddun coolers d'in. Nayi tunanin zanga irin abincin dazu sai naga hadaddiyar fried rice da taji kayan alatu da kwai harda kaji. Gefe ga miyar hanta sai turi take ga kuma haddedden coslow da soyayyar agada a gefe.
Cokali na d'auka zan dibe kawai naji mutum bayana ya zuri hannu ta wajwn kuguna ya k'arbi cokalin dake hannun.
Tsananin firgita na kasa motsawa tare da rike numfashi gani nake ko numfashi jikina ya motsa zai taba nashi saboda yanda yake very close da bayana har ina nin hucin numfashin sa gefen wuya. Da zarrarrun ido nake kallon dogayen yatsun hannun sa daya d'auki plate yana zuba abincin. Saida ya shake plate din da abincin har ya yi tsini sannan ya kama hannuna sai lokacin na sauke numfashi dana rike nayi azamar buge hannun sa da k'arfi tare da buga matsa tsawa
"Kar ka kuskura ka tab'ani "
Bai bada wani reaction ba sai murmushi da naji ya yi ya ajiye abincin gabana ya matsa daga bayana. Saida ya juya naji yace
"Eat while I'm still being nice"
Numfashi na sauke na kai hannu na dafe k'irjina dake matsananci bugawa. Badan yunwa da nake ji Allah bazanci abincin nan ba tunda bansan wane irin hannu ya dafa ba. Da sauri na d'auka nayi waje da plate din ina jin idansa a kaina baice uffan ba saida na buɗe k'ofa naji ya yi magana k'asa-k'asa da banji ba da kyau nayi saurin ficewa da bugu masa k'ofar. Can garden d'in na koma na zauna naci abincina nayi nak tare da yiwa Allah godiya na kora da ruwan fanfo.
"Me ki ka a nan?"
Muryar Zulai ya katse min peaceful thought d'ina. Da sauri na mik'e ina kallonta tana shigowa wajen fuska dauke da tuhuma.
"Kin gama abunda zakiyi ne ki ka zo nan ku ka zauna?"
Da sauri na d'aga mata kai. D'an shiru tayi tana kallo na kaman bata yarda ba nayi yak'e ta girgiza kai ta mik'omin takarda
"Karbi wanna list ne na abokai da zasu zo anjima party da Aizak zaiyi. Ina so yanzu kije kitchen ki kula da dukkanin abunda za'a girka na girkin har zuwa abun sha da za'a had'a masa. Kaman yanda nace ki kula da abunda zaisha a wajen da ci hakkin hakan na kan ki. "
Party,party shi baya gajiya da party ne kaman muna k'asar turai?. Allah ya kyauta ace mutum sam baya tsoron ranan komawar sa ga mahalillici. Tare muka fito ta nunamin katon kitchen d'in dake shake da masu girki namu na gargajiya da kuma turawa kowa yana yin abunda ya kawoshi. Nan naga wannan yarinyar da har yanzu bansan sunanta ba dama wasu yan mata da muna shiga suka hau harare-harare ganin Zulai na numain komai da kuma gabatar dani wajen manyan chef's d'in dake da ragamar komai a hannun su. Duk saida nabi ko wanne naga irin abincin da ake had'awa kafin na fito nayi wajen party da Zulai ta min bayani sa. Wancan hall d'in dana fara zuwa. Shima ana ta decorating nashi ina na shiga ina dubawa da nuna inda ya kamata a chanza masa tsari. Kafin hud'u komai ya gama hallara guri ya d'auki harami kaman a k'asar waje.
Nina fito da list na tsaya bakin k'ofa lokacin da bakinsa suka fara zuwa. Kai Allah wadaran naka ya lalace dukkanin su babu wanda yake da shiga ta arziki duk y'ay'an manya ne masu ji da kansu. Daga mazan har matan. Tunda na tsaya a wajen ina bada iznin shiga duk da cewa akwai matsu tsaro gabana na fad'uwa kar Aisar ko wani daya sanni yazo wajen. Duk wanda yazo sai ya fad'i sunan sa na duba sannan ya shiga har suka k'are na sauke ajiyar zuciya cike da gajiya. Suna gama shiga kuwa guri ya d'auki hayaniya da shewarsu ga k'arar kid'a na tashi kaman zai fasa dodon kai. Can gefe na matsa daga bakin k'ofar ina Allah wadai da irin wannan rayuwa. Basufi minti talatin da fara tashewa ba aka fara kiran sallah. Ji nayi bazan iya bari ana kiran sallah wannan uban kid'a na tashi ba kaman ba y'ay'an musulmi ba. Da kwarin gwiwa na danna kaina cikin wajen da