Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Daga gefe Baba ta zuba mata ido cike da tausayi har wasu hawaye suka biyo gefen fuskarta tayi saurin gogewa kafin ta lura. Ko menene ya sameta haka yarinya k'arama ta shiga tasku na rayuwa? Ina iyayenta ? Saida na cinye tuwon nan tas na ajiye kwanon ina sauke ajiyar zuciya. Yanzu na fara jin wata irin nutsuwa na ratsani gaskiya yunwa masifa ce. "Yauwa tunda kinci abinci ga ruwa can na zuba miki cikin bokiti kije kiyi wanka kiji dad'in jikin ,idan kin fito ga magani na kwana ki shafa a ciwukan dake jikin ki" Kallonta nayi ina tunanin me yasa ta taimake ni? Ganin na kasa tashi ta miƙe ta kamani mukayi waje. Saida na shiga band'akin ta mik'omin ruwan sannan ta juya d'aki. Na jima a tsaye ban motsa ba ina tunani kafin na yunk'ura jiki babu k'arfi na cire kayan jikina sa ni kaina tsami da suke duk ya isheni. Kai ruwa rahama ne. Cuda jikina nayi kaman zan chanza fata har gashin kaina da duk ya yamutse. Wata irin iska kuwa ta dinga ratsani tabbas ance tsabta na daga cikin imani. "Na manta ga zani ki d'aura idan kin fito" Muryar Baba naji bakin k'ofa tana ratayo zanin kan gini. Janyo zanin nayi na d'aura na fito ban shiga d'akin ba na matsa bakin buta da nagani da ruwa a cike nayi alwala. Sallah kwana biyu ce a kaina bashi Allah bazai yafemin ba domin nina d'urawa kaina ciwo naki nayi ibadah. Maa . Tunanin ta ya fad'omin ko wane hali ta shiga jin b'ata na? Did she even care ko ya ne? Kai anya? Ita ta jefani cikin wannan yanayin but still she's my mother. D'akin na koma na samu Baba na k'ok'arin kunna tv. Da mamaki take kallona kafin naji tayi tasbihi cikin ranta. "Tabbas babu abun bauta da godiya sai Allah. Baiwar Allah wacece ke? Menene sunanki?" Kai na sunkuyar gashin kaina ya sakko yar ya rufemin fuska. A hankali nace "BAHIYYA " ina ji ta jinjina kai tana maimaita sunan kafin tace "Ga riga da zani na fito miki dasu kisa kafin muga abunda hali zaiyi. Idan naje gidan da nake aiki zan duba ko Allah zaisa na samo miki abun sawa" A hankali na d'ago na kalleta idona cike tab da hawaye. Wacece wannan matar me yasa take taimakona? Me yasa bata kyamata kaman kowa? Saboda bata san wacece ke bane? Wata kila data san wace ke bazama ta kalle ko ba bare ta taimaka miki. Jiki babu kuzari na k'arasa shigowa na kwashi kayan zansa ta fice daga d'akin. Saida na gama sawa ta dawo ta nunamin gabas da bani hijabi don ta lura ina sonyin Sallah. Tunda na tayar saida na idar da duka sallolin da ake bani tuni lokacin tayi sallah isha ta kwanta harta fara barci. Juyowa nayi na kalleta ganin yanda takw barci hankali kwance kaman ba tare da mutumin da bata sani take tare ba. A irin wannan zamanin tsab mutum zai cuceka wanda mafi akasari gudun hakan yasa taimako ya yi karanci, amma ita sam bata tunanin na cutar da ita. D'an murmushi nayi na kalli abincin data ajiyemin cikin kwano hawaye ya taru cikin idona. Ina ma ace ana sake haihuwar mutum ya zabi inda yake so i will be gladly na dawo koda matsayin jikar tane. ➺➺➺➺➺➺➺➺ The president palace Wani irin kid'a ne ke tashi daga nan b'angaren nashi kaman zai tashi gidan. Mata ne na bugawa a jarida da maza masu ji kansu keta sha'anin su saboda d'an party da suke. Daga can gefe cikin wani haddedden garden yake zaune da bata bak'ar leather jacket da wando gabansa kwalabe ne na giya masu matuƙar tsada da manya-manyan taba cikin wani dan bowl. Kwalbace a hannunsa ya d'aga yana sha dimples nashi gaba d'aya sun motsa. Mata ne gefen sa kyakwawa da kallo d'aya zakayi musu k'asan ruwa biyune saboda kalar fatansu. D'aya kana ganin ta kasan yar Morocco ca d'aya kuma Ethiopian. Kyawawane da zance kusan kaf matan wajen kad'an suka kama k'afarsu. Daga gefe Aisar ce da Susu cikin nasu kwalliyar ta k'ananan kaya sunyi kyau babu laifi. Tunda ta shigo take neman hankalin sa amma inda take bai kalla ba kusan su kansu matan dake gefensa babu wacce ya cewa uffan amma bai hanasu tab'ashi ba suna shashshafashi. Zuciyar Aisar kaman zatayi hauka saboda Enzo yaki kulata bare ya nuna yasan da Allah ya yi wanzuwarta a wajen. Kasa jurewa tayi ta mik'e tana kwarkwasa da kwalba hannun ta nufeshi da tata kissar. Duk da k'irjinta na dukan uku-uku batayi k'asa a gwiwa ba ta zauna kan cinyarsa hakan kuwa ya bata reaction don wani irin buɗe idansa ya yi kanta da saida taji kaman ta saki fitsari a wajen amma ta danne tana masa murmushi. A hankali ya karkata kai gefe yana tunanin inda yasan wannan yarinyar? Ahh, yes itace yarinyar da tayi sanadin da ya yi raping wata useless girl da har yanzu ta k'asa barin kwanyar kansa. Hannun ta data d'ura kan k'irjinsa yabi da kallo yana jin wani irin disgust. Shifa baya son mace desperate na attention d'in sa. Gaba d'aya matan dake gefen sa suma tsayawa sukayi suna kallonta dan sunsan halin sa idan bashi ya baka ikon tab'ashi ba to akwai hukunci. Yanda ya zuba mata tsumammun idanuwansa babu wani emotion kan fuskarsa saida ya saka kowa on edge. Aikuwa ya wani mik'e da ita kan cinyarsa ya juya ya makata kan kurejar. Badai she wanted his body ba? To zai bata abunda take so. Gaban kowa abokai da y'an mata Enzo ya farke wandon Aisar babu tausayi ko imani ya ratsata da k'arfi saida ta zuba uban ihu. Ita d'in ba budurwace bace amma yanda ya shigeta saida ta raina kanta. Da wulakanci yake bugunta idansa na kallon gabansa don baison ma ganin mummunan fuskarta. Wajen gaba d'aya ya d'auki wani irin shiru sai ihunta kawai dake tashi na tsananin azaba. Saida ya mata cin wulakanci sannan ya janye yana jan tsaki ya mik'e yana gyara wando ya wuce mata rii suka bishi kaman zasu cinye. Duk irin wannan wulakanci da tozarci daya mata baisa taji haushi ba saima wani irin farin ciki da soyayyar sa data k'ara mata katutu a rai. Ji take yau babu wanda ya kaita farin ciki ta samu abunda Bahiyya ta kwace mata. Jiki babu k'arfi ta yunƙara ta miƙe zaune babu kunya mutanen dake kallonga ta gyara kanta Susu ta taimaka mata suka bar wajen party gaba d'aya don sosai ya mata kaca-kaca. Hmmm to Allah ya kyauta ya shirya mana zuru'a. Daga bakin k'ofar ya juyo ya watsawa matan dake biye dashi kallo gaba d'aya sukaci birki suna kallonsa har ya shige. Cikin rashin sani bayan shigarsa b'angaren nashi daga bakin stairs yaci karo da wata maid nashi dake sakkowa rike da kaya zata kai laundry. Saboda yanda kayan suka rufe mata gaba bata kula dashi ba saida sukaci karo dashi ta koma baya da k'arfi ta zauna dabas a k'asa. Tsawa ya dakata da harsshen na korean yace "Mahaukaciyar ina ce ke baki ganin gaban ki ne?" Duk da batasan me yace ba jiki na rawa ta gurfana a gabansa tana bashi hakuri kaman zai kasheta. Da tsawa yace da turanci "You stupid slave da zaki tab'ani da wannan kazamin jikin naki. You're fired" Aikuwa ta sake sakin kuruwa kaman zatayi hauka. Idan ta rabu da wannan aikin yanda suke samun kud'i tsububu uwa ,uba suna karkashin sa da kowa yake mafarkin ko ganin gilmawarsa ne ai ta fad'o k'asa warwas. Duk irin ihu da kuruwar da take baisa yaji tausayin ta ba saima tsaki dayaja daya zame masa kaman ibada ya haura sama. Yana shiga d'aki ya fara cire kayan sa yana wurgi dasu don jinsa yake wani so dirty saboda ya yi wulda da waccan kazamar yarinyar. Yana shiga haddedden band'akin nasa ya sakarwa kansa shawa ruwa mai dumi na zuba kansa. Unexpected saiga wannan innocent face na yarinyar nan ya dawo cikin kwanyar kansa lokacin da take ta kokawar kwatar kanta. Hannu ya dunkule ya kaiwa bango naushi yana cewa "Ahh, f*ck" Wai wacece wannan yarinyar ta kasa barinsa ? He doe's not feel guilt kan abunda ya mata saima zafinta da yake ji tasa ya yi abunda bai tab'a aikatawa ba. Ya jima band'akin kafin ya fito d'aure da tawul. Babban mutum ne zaune kan makemen gadon nasa cikin manyan kaya. Kallo d'aya zakayi masa kaga tsananin kaman dasuke kaman ya yi kaki ne ya tofar. Murmushi ya saki cike da kauna da so ganin ya kalleshi ya d'auke kai yace "Wane ya tab'amin mai Handsome Baby?Hmm, AIZAK?" AIZAK shine ainihin sunansa sa Alhaji MUNEER ya yanka masa rago dashi kuma yake buri yaga ya k'arbi wannan sunan. A fusace kuwa yana huci yace yana kallon mahaifin nashi "That stupid b*tch slave nake so a kora. How dare she zata bugeni?" D'an murmushi Daddy ya taso inda yake tsaye ya tsaya gabansa rike da tawul. Zaunan dashi ya yi kan stool ya fara goge masa gashin da lallami yace "Shine abunda ya b'ata mata kai? To an sallameta sai kuma me ka ke so?" Wani kwakkwaba fuska ya yi da shagwaba yace "Find another one" "An gama" Ya cigaba da goge masa gashin ya gyara masa shi. In kaga yanda yake tarairayarsa kaman zai maidashi ciki ,sai abun ya masifar baka mamaki. Dole ya tashi a kangarerren yaro ya dinga yin abunda yaga dama tunda babu wanda yazai nuna masa illar hakan bare munin abunda yake. [01/07, 6:54 pm] Ashantyluv: https://chat.whatsapp.com/C0AOCxdDgofFmvJWw4ulrH 𝐁𝐀𝐇𝐈𝐘𝐘𝐀 𝓓͟𝓮͟𝓼͟𝓽͟𝓲͟𝓷͟𝔂͟ 𝓸͟𝓻͟ 𝓯͟𝓪͟𝓽͟𝓮͟? ©𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂𝓵𝓾𝓿 Not edit! 【ch6】 Kiraye-kirayen farko da aka fara na asuba da sanyin iska dake kaduwa mai sanyaya jiki, ya yi sanadin farkawa na daga barcin da bansan sanda ya d'auke ni ba. A hankali na buɗe ido da dake d'auke da barci kan Baba dana hango tana sallah. Sosai zuciya ta ya sake samun nutsuwa da matar naji babu wani shakka ko tsoron zata cutar dani. Maida idona nayi na sake lumshewa barci mai nauyi ya sakeyin gaba dani saboda gajiya dake tattare dani. D'an tab'ani da naji anayi tare da kira a karo na biyu na sake buɗe idon kan Baba dake tsaye bakin kaina. Murmushi ne kwance kan fuskarta dake sanye cikin hijabi a hankali da kulawa tace "Ki daure ki tashi haka kiyi sallah rana ta fito saboda naga bakya jindadi da irin gajiyar da ki ke tattare da ita yasa ban tashe ki ba da asuba" A hankali na yunƙura na mik'e zaune tare da sakkowa daga kan katifar da nake da ladabi nace "Ina kwana?" "Lafiya lau ya jikin naki? " Kai a k'asa na amsa da sauk'i duk sai nake jin abun wani iri domin ban saba ganin irin wannan kulawar ba. Ajiye tunanin nayi na mik'e a hankali na fice jin tana sake nanatamin naje nayi sallah kafin rana ta buɗe sosai. Ruwa na fara kamawa na kuskure baki sannan na d'auro alwala na dawo d'akin na samu harta shimfid'a min dadduma da hijabi a kai. Saida nayi sallah nayi addu'oi sannan na sake juyo murya a k'asa na sake gaisheta . Fuska a sake ta sake amsawa kafin d'akin ya d'auki shiru na d'an wani lokaci sai k'arar fanka dake kaɗawa. Har yanzu ina fargaba idan ta tambayeni labarina da asalina wanda nasan muddin taji itama zata koreni daga gidanta. Ficewa tayi naji motsin ta kaman tana fama da kwanuka bata jima ba ta dawo da y'ar kula da kwanan ruwa. "Daure kici abinci ga magani na sake jikawa kisha saboda jikin ki, ni zan fita wajen aikine ina fatan babu wata matsala idan na bar ki ke kad'ai a gidan ko?" Ni mamakin yardar ta a kaina nake daga had'uwar mu daga jiya zuwa yau? Ina da tarin tambayoyi a kanta amma yanzu bani da ikon yi mata wannan tambayar .shin ita kad'aice a gidan nan bata da y'ay'a ko jikoki? Abincin naja a hankali kwasai ne da kunu sai tururi yake da alama kafin na tashi ta siyoshi. Yawuna har wani tsinkewa ya yi na kama kosan ina masa cin hauka. Saida nayi kat sannan na d'auki maganin data kawomin a kofi na daga shima na shanye duk d'acin sa. Naji dad'i maganin kuwa tun jiya dana sha duk wasu ciwon jikina sun sassauta. Cikin atamfa da gyale ta fito da y'ar jaka a hannun ta. "Yauwa Bahiyya bari naje sai na dawo yau na makara sosai. Akwai ragowar tuwa na dumama na juye miki a flask saboda anjima koda bazan dawo da wuri ba. InshaAllahu zanyi k'ok'ari na dawo na kuma tawo mana da cefane " Ji nayi kaman nayi kuka saboda yanda take bani kulawa. Na d'aga mata kai a hankali ina kallo harta fice daga d'akin. Waishin dama akwai mutane masu irin wannan zuciyar yanzu cikin wannan duniyar? Daga jiya zuwa yau kaman wacce mukayi shekaru muna tare da ita? Ko kad'an babu zargi ko kokwanto a kaina ta d'auki yarda da aminci tun yanzu ta bani?. Na jima nan zaune ina sake-sake da tuni kafin na tashi naje na watsa ruwa na dawo na maida kayan jikina. Ban zauna ba na fito na d'auki tsinya na sake share gidan duk da cewa ko ina tsab yake gwanin sha'awa kafin na fita na had'a yan kwanukan da aka b'ata na wanke. D'aki na koma don har yanzu da wuta na sake bin katifa na kwanta ban jima ba barci mai nauyi ya yi awon gaba dani. Alhamdulillah tsawon kwana biyu bani da bakin da zan godewa Baba saidai nace Allah ya saka mata da alheri. Har yanzu bata tab'a tambayana dalilin da yasa na baro gida ba kuma na d'urawa kaina ciwon hauka. Ta kyaleni duk sanda na shirya gaya mata na gaya mata, wannan kuma ba k'aramin kara kimanta darajarta yake gurina ba. Na sake yanzu sosai da ita hakan kuma ya mata dad'i. Dan aiki ko wani girki zata kirani na taimaka mata, yanzu idan zata fita ma ganin ina yi mata aiki batayin komai kuma zata barmin cefane na d'ura mana abinci idan rana tayi. Yau ya kama weekend kaman yanda tace bata zuwa asabar da lahadi. Tunda mukayi sallah asuba muka koma barci daganu bar ita bamu tashi ba sai wajen takwas na safe nama rigata tashi har na gama aiki na dumama mana abinci sannan ta tashi. Yanayin ta na lura kaman batajin dad'i na kasa jurewa na tambayeta take cemin k'afarta ce take d'an damunta dama kuma tanayin ciwon kafa lokaci zuwa lokaci. Gaba d'aya duk sai na damu da ciwon ko dan naga mutum na farko a rayuwata da take nuna damuwa da lamurana batajin dad'i ne?. Ita kanta data fahimci na damu taita kwantar min da hankali harta bani maganin da take shafawa na shafa mata a k'afar bata jima ba kuwa ta sake komawa barci. Gefen katifar na zauna na zuba mata ido cike da tausayi. Tabbas Baba dattijuwa ce sosai amma saboda kyan jiki garau take. Ance ko wane bawa da irin tashi kaddarar ban sani ba da ko akwai wani dalili itama daya saka ta bari nata y'an uwa da ahli tazo nan taba fafutukar rayuwa ita kad'ai. "Salamu'alaikum" Da hanzari na mik'e nayi nayi tsakar gidan da nake jin ana sallama. Kaman Baba babbar mata ce itama ta shigo amma bata kai Baba shekaru ba. Da mamaki take kallona kaman yanda nake kallonta don tunda nazo gidan sai yau wani ya shigo saidai yara dake shigowa lokaci zuwa lokaci kallo. "Aa ikon Allah bakuwa Baba tayi ne?" "Ina kwana?" Nace ina d'an rankwafa. "Lafiya lau y'an mata. Ina Baban tana ciki" "Eh" "To yimin iso sauri nake. Ya sunan ki?" Ina k'ok'arin juyawa d'aki nace "BAHIYYA " Zaune na samu Baba dake yunk'urin tashi da alama sallaman bakuwar ya tashe ta. Da sauri na k'arasa na taimaka mata ta miƙe zaune da kai daidai matar ta shigo tana cewa "Wai hala mo barci ki ke ne?" Saida tayi y'ar dariya tace "wlhi kuwa kinga nan Hassa'u yau tashi nayi da ciwon k'afar nan" "Ayya Subhanallahi, ai shi yasa nace ki daure kije asibiti kinki ke sai maganin hausa. To Allah ya sake afuwa yanzu zan wuce nace bari na lek'o kwana biyu bamu samu had'uwa ba" "To ya za'ayi tunda aiki ya hanamu zumunci. Hala gurin aikin zaki yanzu?" Zama Hassa'u gyara na tana cewa hmm na mik'e da sauri na fice na kawo mata ruwa cikin kwano na ajiye gabanta cike da ladabi. Godiya tamin tana murmushi tace "Kai wannan jikar taki akwai hankali wlhi Ai bansan kinyi bakuwa ba da tuni nazo mun gaisa." Murmushi Baba tayi bata ce komai ba Hassa'u ta cigaba da cewa " wlhi yau bagatatan fa aka min waya dazu da safe wai maza nazo akwai aiki duk da sunsan yau ranan hutunace. Wacceb kangarerren yaro ne kuma wai haka kawai ya sake tsiran party amma naji ance yau ko na watan haihuwar sa. Kedai wannan rayuwar Allah ya shirya mana zuri'a amma banda lalace ka bar yaro shi ba musulmi ba ,ba kafiri ba yana yin abunda yaga dama kuma babu mai kwabarsa. Kwanaki fa kinsan daga cikin yara da suke b'angaren nashi naji wai saboda ta bugeshi bata lura ba ance bakiga irin korar karen daya mata ba shima kuma uban ya d'aure masa gindi. Yanzu haka wai an kawo sababbin masu aiki amma duk ya koresu tun ranan ana ta kawo masa yara tun daga waje har uwarsa dake can wata duniyar tana ta aiko masa da masu aiki amma yana korarsu tsabar jin dad'i. Nikam Alhamdulillah da Allah yasa ba b'angaren yaron nake ba dama kuma sai k'ananan yara ake kai masa y'an mata banda maza. Wato idan akwai kud'i babu abunda baya yiwu wannan duniyar. Shi gata ne ya masa yawa shi yasa iskancin nasa ko a film bazakiga wanda ya takashi gashi naji ance yaron mugun kyau ne dashi kaman aljan" Kai Baba ya girgiza a zuciyata ina ta tunanin waye wannan kuma haka? Me yasa yanayin sa yake min kama dana wannan kafirin ENZO? "To ina amfani aiki cikin irin wannan gida? Mai zai hana ki daina zuwa kawai ki huta kema da aiki irin wannan gidan ai gwanda babu" Wani irin rike haba Hassa'u tayi tare da zaro ido tace " in bari fa ki ka ce Baba. Tab. Kinsan irin dumbin alherin da nake samu kuwa a gidan nan. Kullum sai munci munyi nak da irin nauyin abinci ma da babu su a nan saboda ba tabawa yake ba idan anyi. Sai a masa abinci kala goma na safe daban na rana daban haka na dare amma kar kiji mamaki idan nace ko guda d'aya baya tabawa idan baiga dama ba haka za'a dawo dashi kuma a sake kai masa wani rashin yin abincin a kai masa babban tashin hankaline. Ga uban kud'i da uwar d'akin nasa ke sakar mana idan yau bamu samu dubu goma ba alalace to gobe zamu samu ashirin, kuma bawai cikin albashi bane. Kawai kiyi mata kirari kina zuzuta yaron daba nata ba yanzu zakiga uban alheri. Kedai kibar gidan gwammatin nan ai idan ka shiga kaddara ce kawai zaisa ka fita" "To Allah ya kyauta ya kuma shirya mana zuri'a" Amin Hassa'u tace tana k'ok'arin mik'ewa "kinga ni da nake sauri nazo na buge da hira. Baba taimaka ki bani aron jikar nan taki mana ta rakani don nasan yau akwai babu sauk'i duk da nasan akwai mu munfi d'ari amma duk ranan da yake irin wannan fatin nashi jikin mu sosai yake gaya mana" D'an shiru Baba tayi tama tuni nayi wuff nace " zanje Baba" ni kaina bansan me yasa nace zanje baa amma haka kawai zuciyata naji ina son zuwa. Ido ta zubamin tana nazari Hassa'u tayi maza tace "Yauwa y'ar albarka tashi maza d'auko gyalenki mu tafi rana nayi" A hankali na mik'e na d'auko hijabin da Baba ta kawomin na saka wanda ya sakko har k'asa. Sosai naga rashin son fitana fuskar Baba amma bata hanani ba tace Allah ya kiyaye sai mun dawo. D'an sahu Hassa'u ta tare tare da cewa gidan Gwamnati. Kud'i sosai kuwa ya chaja bata musu ba ta bashi da alama ta rigada tasan kud'in. Tunda muka d'auki hanya kuwa sai zuba uban surutu take da jefomin tambayoyin da bana bata masa. Hassa'u irin mutanen nance masu shegen magana kaman aku sam basu da sirri. Bansan me yasa ba muna yanka wani katon titi da tun daga bakinsa matakan tsaro ne gabana ya fara fad'uwa. Tun daga nesa ka ke hango tangamemen rufin gidan saboda tsinin sa ta saman bishiyu da suka rufe gidan gaba d'aya tako ina ga uban matakan tsaro. Ganin mun tunkari katon gate d'in bugun k'irjina ya tsananta saida na kai hannu na dafe. Kafin mu k'arasa kuwa an tsaidamu yafi sau goma ana checking d'inmu da tambayar dalilin zuwanmu. Wani d'an kati Hassa'u take nunawa da sun ganshi zasuce mu wuce. Daga bakin katon gate d'in mai nafe ya faka muka fito. Tabbas maganan Hassa'u gaskiya ne. Idan akwai kud'i babu abunda bazai yiwu ba wannan duniyar. Gate d'in kad'ai abun kallo. Saida suka gama duba mu a karo na babu adadi sannan aka bamu daman shiga. Ina saka kafata ciki kuwa k'irjina ya wani buga dum saida zuciyata ta d'an tsaya da aiki na y'an sakanni. Wai meke damuna ne? Wata doguwar hanya mika mika dake d'auke da wani irin titi gwanin sha'awa ko ina fitilu da bishiyu sun zagaya shi daya sake fito da hanyar. Tafiya mukayi mai nisa kafin na fara hango wani tangamemen glass mansion daga tsakiyar wajen. MashaAllah nace a raina amma bugun da k'irjina yake ya hanani tsayawa jimanta irin had'uwar gidan. Tun daga nan na hango mutane suna ta kai koma ta ko wace kusurwa cikin sauri dukkanin su sanye da dogayen riguna baki da fari kaman dai kayan masu aiki. Ikon Allah harda wani dress code a gidan kenan? Muna k'arasa kuwa wata babbar mace ta tunkaro cikin sauri fuskarta babu wani annuri da d'an fad'a tace "Hassa'u sai yanzu ki ka zo? Tun yaushe nace a sanar dake kinsan yanda aikin ya kacame mana kuwa" Da sauri Hassa'u tace tana d'an rankwafa "kiyi hak'uri wlhi a hanya ne motar dana shiga ta d'an samu matsala" D'an tsaki taja ta juyo tana kallona gabana ya fad'i " wannan kuma fa?" "Bakuwa ce nayi tazo jiya shine naga babu dad'i na barta a gida ita kad'ai bata san gari ba na tawo da ita ko Allah zaisa zata taimaka da wani abu" Da mamaki nake kallon Hassa'u saboda jin irin karya da take ta zubawa babu ko kunya. Yanzu dana sake k'arewa matar kallo na lura da yanda uniform nata ya fita daban dana sauran harda wani tag a jiki da aka rubuta HEADSLAVE. wato ita ce babbar masu aikin gaba d'aya. Ga yanda take wani takama da sunan kaman wacce aka bawa Aljanna sai wani d'aga kai take. Wani irin sansanyan kamshi ne ya ratso wajen gaba d'aya naga duk sun juya da girmamawa harda had'a baki wajen gaisar da matar dake fitowa cikin wani hban leshi da gwalagwalai har baka ganinta da kyau tsabar yanda kayan suka haska. Bakace sosai amma saboda hutu da jindadi ta d'an washe kayan ga fuskar nan tasha uban mai daya sake banbanta tata da wuyanta. Wani irin taku take kace bata so tana wani yatsina. Ni kamshin turaren nata ma data sake matsowa sai naji yana hawarmin kai. Dagaji kasan shi kansa turaren anyi masa barin kud'i banda ita kanta daga samanta har k'asanta kukan kud'i take. Kaman yanda Hassa'u tace kuwa suka hau zuba mata kirari kaman a film daga cikin masu tsaro dake binta ta hau kwaso kud'i daga jaka tana watso musu kaman wasu kaji sukayiwa kud'in rubdugu harda Hassa'u da bansan sanda ta motsa ba sai ganinta nayi cikin su suna kokawa. Allah mai iko. Idan ka cireni da Matar da matakan tsaronta da kuma Headslave d'in, gaba d'ayan su sun dukufa wajen su hamsin sai kuruwar kowa yana so ya kwashi rabonsa. Yanzu wannan rayuwa ce?a maida mutum d'an adam kaman wani dabba?. Ina abun so anan da har Hassa'u take ganin bazata iya barin wannan aikin ba ta kwammace a barta Allah ya darajata matsayin baiwarsa, ta bar wasu da sudin ba komai bane wajen mahalillici suna kaskantata saboda abin duniya?. Yanzu na sake dana sanin zuwa wlhi in har

Chapter 5 of 11