Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hakan sosai ya sake bawa uniform namu armashi. Yawanci sunfi saka hula ko bandana mata kan uniform d'in daidaiku ne suka saka d'an k'aramin hijabi kaman ni. Mamakine ya kamani sanda na fito naga Lee k'ofar d'akin cikin k'ananan kaya kaman jirana yake. Ina bud'ewa ya d'an ja baya yana murmushi "Good morning " Da ace yasan irin muguwar tsana dana masa da sam bazaiso ya dinga min shishshigi ba cikin lamurana. Jin ban bashi amsa ba ya sake cewa "Muje ki k'arya sai na sauke ki a school d'in ko?, Maa d'inki ta gama had'a miki breakfast da lunch." Dariyace ta kwacemin don sai naji abun kaman tatsununiya wai Maa tayi min girki. Saida nayi mai isata sanna na wuce bance masa komai ba ina jinsa ya biyoni. Ga mamakina kuwa abincin ne zaune kan d'an dinning dake falon da wani zube a sabon flask k'arami. Muna had'a ido nayi saurin durkusawa ina gaisheta ta amsa fuska babu wani annuri sosai tana kallon Lee kaman wacce bata b'acin ransa. "Zoki zauna ki karya" Baki na bud'e zance na koshi muna had'a ido na shanye maganan badan naso ba na zauna na tura abincin kad'an na mik'e da sauri nayi waje rike da flask d'in . Ina jin Lee ya biyoni babu irin naci da lallashi da baimin ba na shiga mota ya kaini nayi banza dashi na wuce duk da kuwa har yanzu akwai ciwon kafata don nasha rub ne na d'an samu sauki, shima na fuskata sosai na shafa masa hoda da concealer. Bakwai da kwata na isa bakin gate namu na school dake cike da manya-manyan motoci na kece raini ana sauke yara. Kai a k'asa na wuce da sauri na shige cikin school gabana na fad'uwa ina addu'a Allah kar ya had'ani dasu Aisar. Wato idan kaga school namu zakayi tunanin daga waje aka d'auko ta aka dasa. Ni kaina ina mamakin ina Maa take samun irin wannan mak'udan kudi na makaranta tana biyanin don abunda take samu wajen samarinta ba bazaikai rabin kaso na makaranta ba. Gab da zanshiga aji naji an kwalamin kira gabana ya yanke ya fad'i jin muryar Aisar. Chak na tsaya na kasa motsi jikina sai rawa yake na juyo a hankali inda naji kiran. Tana tafe kaman yanda ta saba the princess of the school da yaranta dake biye da ita suna taku kaman zasu gasa ko nace basa kashi. Gaba d'aya su mini sket ne a jikinsu ita kanta rigar bata kai cibi ba banda uban takarmi mai shegen tsini dake k'afarsu kan nan yasha gashin doki sai reto yake haka farcen hannun su yasha gyara yana ta shek'i da walwal an sakashi ya yi zako-zako. Dankareriyar jakar prada ce k'afad'arta hannun ta rike da galaxy data kai 2m da mukulli mota. Yanzu dana sake ganin yanda take takowa cikin takama da iko yara suna binta maza da mata sai jikina ya sake mutawa na fara tunanin menene ya kaini kai AISAR police station. Me nake dashi? Ido na kyeftawa na sake bud'ewa kan domin sai nake ganin kaman ba daidai ba don murmushi ne kwance kan kyakwawar fuskarta. Anya kuwa ban samu matsala a idona ba?. Tun kafin ta iso kamshinta ya cike farfajiyar makaranta dake nan kaman wani hamshakin garden. Yawu na had'iye saida suka kusa isowa dabdani sannan na iya ganin Nabila dake gefen Susu da tashin hankali sam baisa na kula da ita. Gabana duk suka tsaya na matse jaka cikin k'irjina dake bugawa kaman zai tarwatse . Saida suka k'aremin kallo sai kuma naga sunyi dariya gaba daya Aisar ta dawo gefena ta sakalo kafad'ata da hannunta tana cewa "Ya naga duk kinyi wani iri kaman wacce taga wani dodo?" Had'iyar zuciya na sake ina kallonta da idona kaman zasu fad'o. Duk abunda zasuyi min babu wanda zai tsawatar musu ko ya hukuntasu dole naji tsoron abunda zai faru dani. Ganin na kasa cewa komai ta sake murmushi dana kasa gane masa ta janye tana laluben jakarta ta fito da wani k'aramin hadadden card ta mik'omin. Ido na zuba mata na kasa kabarba don gani bake koya na motsa akwai wani gagarumin abu da take shirya min. Hannu na ta kama ta sakamin card d'in tana murmushi tace tana kallona "Ki saki jikinki komai ya wuce kinji. Ina so daga yau mukulla abota mai k'arfi. I'm sorry a kan abunda ya faru jiya saboda nuna miki nadamata yau ina gayyatarki Birthday party nawa .Nabila zata zo ku tawo tare ga invitation " Saurin kallon Nabila nayi da tayimin murmushi tana d'an d'aga min kai. Bakina na rawa na bud'e amma maganan ta kasa fitowa. Anya kuwa ba mafarki nake ba?. Bazan manta yanda jiya suka rufeni d'akin hutu ba suka zaneni da gayamin bakaken magunguna da irin muguwar tsana da sukemin. Anya kuwa wannan ba wani mugun tuggun suke had'amin ba? . Kaman tasan me nake tunani ta sake cewa "Bahii I'm serious fa, kar ki bari abunda ya faru jiya yasa kiyi tunanin akwai wani abu, i just wanted to be your friend da fatan zaki bani chance please?" Bansan ya akayi ba na d'aga kai is like kaman gangar jikina da zuciya ta suna having different thoughts. Finally for the first time a rayuwa I'm having some friends. Ance mutum rahama ne don haka I'm willing na basu another chance tunda har sun yarda suyi abota dani duk da sanin su wacece ni. Zaman kad'aicin ya isheni. Ihu da hayaniyar wasu yan mata dake wucewa yaja hankalin mu gaba d'aya kansu a guje d'aya tazo inda muke jiki na rawa tace "Aisar the president son, ENZO ya yi accept na invitation na birthday party naki. His coming to your birthday " Wani irin ihu sukayi gaba d'ayan hardasu Nabila kafin su kwasa a guje suka fice gaba d'aya daga makaranta na bisu da kallo babu wanda ya dakatar dasu har suke fice a motar Aisar a guje. A hankali na sauke numfashi na zubawa katin ido ina sauke ajiyar zuciya da tunanin waye wannan ENZO da naji ana kira kaman ba musulmi ba da har Aisar ta ajiye isa da jida kanta haka tana rawar jiki saboda ance zaizo birthday d'in ta?. [20/06, 9:14โ€ฏam] Ashantyluv: ๐๐€๐‡๐ˆ๐˜๐˜๐€ ๐““อŸ๐“ฎอŸ๐“ผอŸ๐“ฝอŸ๐“ฒอŸ๐“ทอŸ๐”‚อŸ ๐“ธอŸ๐“ปอŸ ๐“ฏอŸ๐“ชอŸ๐“ฝอŸ๐“ฎอŸ? ยฉ๐“๐“ผ๐“ฑ๐“ช๐“ท๐“ฝ๐”‚๐“ต๐“พ๐“ฟ ๐™ฐ๐šœ๐š‘๐šŠ๐š—๐š๐šข๐š•๐š˜๐šŸ๐šŽ@๐™ฐ๐š›๐šŽ๐š ๐šŠ๐š‹๐š˜๐š˜๐š”๐šœ.๐šŒ๐š˜๐š– ใ€ch2ใ€‘ Kusan zan iya cewa yau saboda murmushi dake fuskata saida kumatuna ya fara ciwo. Duk wanda ya kalleni sai ya hango farin ciki da nake ciki. Karatu kam yau nayi sa cikin salama da nutsuwar zuciya duk da cewa wani sashen na zuciyata sosai yake fargaba da kuma kokwanto na wannan chanji nasu Aisar lokaci guda, amma ance idan zuciya nasan sauyi naki bari wannan sashen ya yi tasiri a kaina ina hango irin chanjin rayuwa da da zan samu idan nashiga cikin click na Aisar. Duk wannan uฦ™ubar da nake ciki da Bully da nake fuskanta zai zama tarihi zan kasance daga cikin wanda ake shekka da kuma tsoron tabawa. Haka za'a dinga bani girma nima saboda ina cikin su Aisar.Tuni duk wani abu da Aisar sukemin na yafe musu kuma na manta domin wannan babban cigaba ne a rayuwa ta. Wata kila itama Maa na samu dan chanji wani b'angare da zai dinga nuna ni matsayin y'ar ta ba mikiyarta ba tunda dama burinta kenan.Har aka tashi ina cikin farin ciki da kissima abubuwa da yawa ciki harda tunanin zuwana party d'in anjima. Bana jin Maa domin nasan ko bance zanje da ba idan har tasan an gayyace ni saita turani dole. Murmushi dake fuskata ne ya d'auke bayan na fito gate na makaranta saboda ganin Lee da nayi cikin jerin motoci na d'aukan yara. Da sassafar na nufeshi don bana son a ganshi Allah ya taimake ni su Aisar basa school. Tabbas da ace suja school dole zasubi diddigi sunan koshi waye waje na. Kaman yanda kowa yasan halin ma abun kunya ne a wajena ace d'aya daga cikin samarinta da take bad'alarta dashi an ganmu tare. Chance d'in da nake tunani zan samu wajen su Aisar zai rushemin shi domin kowa yana min kallon ina aikata abunda Maa take yi wannan shi yasa tsanan tawa tayi tsamari wajen al'umma. Islamiyar ma da nake zuwa gani suke kaman munafurci ne yake kaini ba don neman ilimi ba saboda duniya karta zargeni. Bansan sai yaushe ne zan fita daga cikin wannan zargi ba da tun abun yana damuna ya zama kaman abune daga rayuwata dana tashi dashi domin nayi rayuwa dashi. Ya zama normal kaman daily routine nawa na kullum. Fuska a b'ace na tsaya gabansa ina dan waige-waige nayi magana da d'acin rai "Me ka ke a nan?" Da murmushi kan fuskarsa yace "Nazo d'aukan ki ne, Maman ki ta gayamin makarantar da ki ke da lokacin da ku ke tashi. I most say Bahiiii, this is a very prestigious school kaman yanda mamanki tace, I'm so proud of you da ki ke zaune saboda kaifin ilimin ki da basirar ki ba don kin kasance wacce ta fito daga wani tsatso ba na masu hannu da shuni. " Mugun kallona watsa masa tare da jan dogon tsaki na wuce da sauri ban tanka masa ba. Har waye shi da zaice yana alfahari dani? Shi a matsayin sa nawa?. Gabana yasha da motar ya leko ta windo cike da lallashi naji yana cewa "Kiyi hak'uri nasan ina takura ki duk abunda nake ina yine saboda ke d'in kaman y'a ce a wajena duk da nasan wajen ki bakya kallo na matsayin Uba, amma don Allah ina so ki bani dama bazakayi dana sani Bahii. Kiyi hak'uri tunda nazo ki daure ki shigo na kai ki gida Maman ki bazataji dad'i ba idan taga ban dawo dake tunda ita ta turoni" Chak na tsaya da tafiyar da nake ina juya kalaman sa cikin raina. Nasan ko mutuwa zanyi Maa bazata tab'a cewa yazo ya d'auke ni ba amma duk da haka ina gujewa b'acin ranta. Numfashi na sauke tare da cize lebe na juya na bud'e gidan baya na zauna. Ina ji ya yi murmushi ya tashi motar muka tafi. Har muka je gida ban yarda na kalle shi gaba d'aya hankalina na waje. Yau naji d'an dama-dama samarin unguwar duk basa nan da sauri na fice na fad'a gida. Kad'an ya rage bamuyi karo da Maa ba dake neman fitowa da alama taji k'arar tsayuwar motar. A hanzarce na koma gefe bakina na rawa na durkusa ina mata sannu da gida. Wani mugun kallo ta watsamin ta bud'e baki zatayi min magana Lee ya shigo nan da nan naga yanayin fuskarta ya chanza. Mamaki ne ya kamani ganin ta sakemin murmushi tace na shiga na watsa ruwa nazo naci abinci. Kallonta nake na kasa gasgata abunda nake gani ina k'ara jimanta yanda take gudun b'acin ransa. Da gaske dai so take ta auri yaron da ko auren fari baiyi ba wanda a kalla bazai bani wasu shekaru masu yawa ba?. Jiki babu kwari na wuce ina waigenta har na shige d'aki da murmushi kan fuskarta tana kallon Lee kaman wani zarah. Jakata na fara cirewa na ajiye na cire kayan makaranta na d'aura tawul na shige band'aki don watsa ruwa. Ban jima da shiga ba naji alamun an shigo d'akin na kasa kunne tare da zubawa k'ofar ido haka kawai gabana na fad'uwa. Kar naje ko Lee ne ya sake shigomin d'aki kar ya shigomin band'aki don naga baida hankali . Wani irin mummunan fad'uwa gabana ya yi na k'ank'ame jiki tare da sakin k'ara ganin an bud'e k'ofar band'akin za'a shigo "Lafiyar ki ke wannan ihun kaman mahaukaciya?" Da azama na ware idona kan Maa ina kare k'irjina da gabana. Tana tsaye rike da murfin k'ofar tana bin jikina da wani kallo dana kasa ganewa. Ido ta zubawa k'irjina kafin naga ta sauke ido kan fatar cikina zuwa kuguna dake a baje. Wani irin flash abu ne ya wuce idonta kaman kyiftawar ido kafin naji tace murya a cunkushe "Idan kin fito ga abincin nan na ajiye miki. " Kai kawai na iya dagawa don ji kaman an shakeni. K'irjina ta sake kallo kafin ta sake sauke kanta kan gashin kaina dake jiki har kuguna ta jinjina kai ta juya ta fice. Numfashin da nake rik'ewa na sauke hawaye masu zafi suka biyo kuncina. Wace irin rayuwa ce wannan fisabillahi? Da kyar iya yin wanka can k'asan zuciyata na gayamin kallon da Maa takemin kallone mai tattare da ayar tambaya da kuma kishi amma nayi gaggawa kauda wannan tunanin. Hadaddiyar wainar masa na tarar da miyar taushe tasha nama da ganda. Sosai kuwa yawuna ya tsinki cikina ya bada k'ara alamun yunwa. Tabbas Maa karshe ce wajen iya girki amma saboda rayuwar data d'auka ta watsar da dukkani wasu dabi'u namu na sunna ta kaman na yahudawa. A gurguje na saka kaya nayi sallah na ja abinci naci nayi kat na koma gado na kwanta ina tunanin yanda zan sanar mata da fitar zuwa party d'in Aisar anjima. Ban sake lek'owa falon ba saboda nasan Lee yana nan kuma na lura Maa bata son maganan da yakemin. Bayan magriba ina zaune na idar da sallah ina lazumi ta kwalamin kira na mik'e a hankali na fito sanye da dogon hijabi na. Falon sai kamshin turaren wuta yake sanda nafito sai abun ya zamamin wani banbarakwai. Lallai na yarda Maa tana son kasancewa da Lee daga jiya zuwa yau babu wani namiji daya sake shigowa ,haka tun jiya banji alamun tasha tabarta ko shisharta kaman yanda ta saba ba kullum. Bayan haka tun jiya cikin chaba kwalliya take da yin girki gashi yanzu gidan harda turaren wuta. Tunanina ne ya katse bayan na fiti ganin Nabila zaune falon ta chaba ado kaman zata gasa. Turus na tsaya ina kallonta kaman yanda take kallona da murmushi kwance kan fuskarta. "Dama kinsan kina da gayyata na Birthday party na Aisar shine baki fad'amin ba?" Kallon Maa nayi k'irjina na bugawa da tsananin fargaba saboda ganin Nabila yau cikin gidanmu, ban taษ“a tunanin zata shigo ba ko zatazo na d'auka duk fad'ane kawai shi yasa har cikin raina ban d'auki abun da gaske ba. "Ki maza kije ki hanzarta ki shirya ki fito tana jiranki" Bance komai ba na juya da sauri na koma d'aki. Doguwar riga nasa maroon kirar Dubai nayi rolling mayafin ta. Hoda kawai na shafa da d'an man lebe na saka flat takarmin sai y'ar pose dana jefa k'aramar wayata ciki kirar tecno. Sanda na dawo falon suna ta hira da Maa kaman wasu abokai harda Lee dakw zaunw gefe yana murmushi cikin k'ananan kaya. Gaba d'aya suka kalleni fuskar ba ba yabo ba fallasa tace "Har kin shirya kenan?" A hankali nace eh ina kallon Nabila dake kallona tun daga sama har k'asa tana murmushi. Itama doguwar abaya ce a jikin ta dark blue wanda kana gani kasan zatayi masifar tsada. Mik'ewa tayi a hankali tana cewa "Bari muje sai mun dawo Maa" "To Allah ya kiyaye hanya sai kun dawo" Wucewa nayi domin sosai naji wani banbarakwai jin Maa tana addu'a . Har munkai k'ofa naji Lee na cewa "K'arfe nawa zaku gama sai nazo na d'auke ta?" Saida ta juya ta kalleshi kafin tayi murmushi tace "Zan dawo da ita ai idan mun tashi ba dare za'ayi ba" Ban jira naji abunda zaice ba na fice saboda idanma da nake ji keyata kaman zai fasa kokan kaina. K'aramin CAMRY ce fake k'ofar gida bayan ta Lee da direba. Ita ta bud'e mana gidan baya muka shiga zuciyata har yanzu cike da kokwanto da fargaba. Tunda muka d'auki hanya shiru babu wanda yace komai cikin motar sai k'arar Ac da tafsir dake tashi kad'an kad'an cikin motar da kuma bugu da zuciyata take da tsananin k'arfi. "Kin kasa sakin jikin Bahii kaman kina tare da bakuwa" Yak'e na danyi bance komai ta sake yin murmushi tace "Ki saki jikin ki don Allah wani idan ya ganmu ai sai yace sato ki nayi" Yanzu kam dariya na saki ina d'an jan numfashi. Bata sake cewa komai ba amma nayi k'ok'ari wajen ganin na d'an saki jikin kaman yanda tace. K'arfe takwas daidai muka isa bakin katon gate d'in da aka birthday d'in. Tangamemen waje ne dake cike da furanni da fitilu kaman a k'asar waje. Tun daga bakin layin manya manya motocine na kece raini y'ay'an manya sunata safa da marwa duk inda ka wurga ido. Yanzu danaga inda mukazo sai jikina ya sake sanyi zuciyata na sake jaddamin nan ba irin waje daya kamace ni bane sai naji kaman na koma gida gashi bakin alkalami ya bushe. Da sauri Nabila ta fice na bita jiki a sanya ina rarrabewa bayanta har muka shiga wajen. Ashe abun kallo na ciki domin waje ne an kashe masa dukiya ta kece raini. Babban Hall ne da ya yi guri guda tsakiyar da harda wani uban swimming full ga y'an mata da samari a ciki sunata badala. Gabana ya tsananta fad'uwa saboda irin suturar dake jikinsu wasu daga su sai pant da breziya . Hankalina ya yi mummunan yashi domin abune da ban saba gani ba. Duk rashin mutuncin Maa bata zama cikin tsiraici haka a gida matukar ina nan. Badai zaka rasata da saka k'ananan kaya ba amma kaman wannan ba. Daga can gefe kuma wasu ne kan wani mambari sai tikar rawa suke ta rashin mutunci abun babu kyan gani. Haka dama birthday party na y'ay'an manyan yake ko kuwa ita nata ne haka daban? Idan har haka dabi'un Aisar yake menene marabarta da Maa? Wane iko take dashi ko nace dama da har takemin abunda taga dama saboda mahaifiyata bayan itama ba tana da wannan mugayen dabi'un a b'oye?. Itama Nabila haka take? Da sauri na kalli Nabila dake gabana na had'iye wani kululun abu daya tokare min makogaro. Allah kar kasa zargin da nake a kanta ya tabbata. Tabbas ance mutum abin tsorone baka san wani ba sai ya nuna maka ainihin kalarsa. Wata y'ar rumfa muka nufa da aka kawata kaman gadin ga wasu irin fitilu masu bada kala da suka haske wajen marasa haske sosai. Daga tsakiyar sa katon tebir ne na glass da kujera sun kewaye shi. Su Aisar na hango zaune cikin kujerun da kwalabai kala-kala gabansu tare da wasu maza suna magana kaman basu san aji mu suke cewa. Muna saka kai wajen duk suka d'ago gaba d'aya suka zuba mana ido sai naji kaman ni kad'ai suke kallo. Bayan Nabila na sake rabewa gabana ya sake bugawa da k'arfi. Kallon juna sukayi gaba d'aya sukayi murmushi a guje Aisar ta taso kai tsaye wajena tayi ta rungume. "Ahh my babbar bakuwa welcom. Da ai nayi fushi na d'auka ko bazaki zo ba" Da kyar na kakari murmushi nayi ina k'ok'arin sauke idona k'asa saboda shigar dake jikinta. Wata irin riga ce mai gida-gida kaman abun tata sai walwali take saboda da zallan duwatsu akayi ta. Rigar ki cinya bata k'arasa ba sosai hakan ya bawa jan pant nata fitowa koya tayi wani dan motsi dama kuma babu abunda ta kare don ga bra nata nan kana gani itama jaa. K'afarta shima wani dogon takarmi ne mai madauri har gwiwar k'afa kanta kuwa yasha uban gashi sai shek'i yake. Tabbas babu karya Aisar kyakwawar yarinyar ce maiji da kyau ,kudi da kuma gata. Hannuna taja muka k'arasa bakin tebir d'in da Nabila tuni ta samu waje ta zauna bayan ta cire abyar dake jikinta. "Friend ga babbar bakuwarmu ta yau Bahii. Ina so a bata special treatment koda bana nan please " Gaba d'aya suka had'a baki wajen amsawa " with pleasure " mazan harda dariya suna tafawa. Bansan me yasa ba amma sai hankali ya kasa kwanciya da yanda suka bata amsa. Kujerar data tashi ta zaunan dani Susu ta mik'o min lemo data tsiya a cup tana murmushi tace "Sannu da zuwa " Kallonta nayi na mayar kan mutanen da duk suka zuba mana ido kowa yana jiran yaga zan amsa ko bazan amsa ba. Hannu na rawa na k'arbi glass cup d'in amma na kasa kaiwa baki. Hira suka cigaba dayi ganin hankali su ya d'auke daga kaina na samu damar sakin numfashi da nake rik'ewa na d'an d'ago kad'an ina k'ara musu kallo. Gaba d'ayan su abun babu wanda zakace gwanda har Nabila data cire nata doguwar rigar ya rage daga ita sai wata y'ar top da dogon wando. Wannan wane irin wajene na kawo kaina. Ban sake shiga tashin hankali ba saida na fara jin ihun mata da dariya su kaman wanda suke wata duniyat daban. Saboda tsoro ban iya juyawa daga inda nake jin yawan ihun da gurnani ba zuciyata na harbawa bana so na zargin dake cikin zuciyata ya tabbata. Har wani gumu yake karyo min na tsananin fargaba. Kaman d'aukewar wutar nepa komai ya tsaya cak na y'an sakanni kafin naji wani irin kuruwar da ihu na mata harma da mazan duk sun kwasa a guje sunyi bakin gate. K'arar wasu motoci da wani machine me ya dumfaro wajen a guje kaman walkiya katon mashin d'in ya wuce baki wuluk dashi wasu dankarara dankara motoci kirar BMW sport suia rufa masa baya wajen guda shida. Wani keybantaccen waje machine d'in ya wuce ya yi bakin na mutane duk suka yanyame bakin wajen hardasu Aisar. Daga cikin motocin wasu shegeun Bodyguards ne suka fito sanye da suit bakake suka rufe wajen don bada kariya. A hankali na mik'e daga nan inda nake zaune rike da cup d'in ina d'an d'aga wuya don nima naga waye wannan haka da kowa ya rude zuwansa. Bakaken kayane a jikisan irin dai na masu Motorbike da hular machine a kansa data hana ganin fuskarsa. Tunda ya faka machine d'in ya wani koma lazily ya zauna yana k'arewa mutane da suka yanyame wajen kallo na tsawon minti biyu kafin ya sakko da isa kaman baya so. Hannu naga ya kai ya zuge jacket d'in dake jikinsa hakan ya bawa dankareriyar sarkar dake wuyansa zuwa k'irjinsa fitowa mai d'auke da wani katon daimon daga tsakiya an kawata shi kaman cross. Kugunsa ya rike yana d'an dube-dube da ihu naji matan suna faman kira "Enzo" Kai na girgiza ina sake maimaita sunansa cikin raina da Allah wadai dasu da suke fifita wani katon kafiri kaman sunga Annabi. Daga nan inda nake ina iya hango yanda yake jibgegen kato domin kusan kaf ya kere mazan dake wajen tsayi duk da cewa b'oye yake cikin bakaken kaya bai hana kasan ingarman namiji ne. Batare da ya cire hular kwanon ba ya wani tako da yanga ya wuce zuwa wani k'ofa da aka rubuta VIP ENZO a jiki Bodyguards nashi suka rufa masa baya wasu suka shiga tare dashi wasu suka tsaya bakin k'ofa. Ina kallo su Aisar suka shiga tare dasu Susu banda Nablia data juyo ta nufo inda nake. Ido na zuba mata harta k'araso taja kureja ta zauna bakinta yaki rufuwa kace anyi mata albishir da Aljanna. Baki na tabe na sauke kai kasa don nikam banga abun burgewa wajen kafiri ba. "Au wai har yanzu baki sha lemon ba?" Na hannuna na ta k'arba ta sake zubamin wani ta mik'o min. Yanzu kam banji komai ba na kai bakina saboda ishin ruwa da nake ji. Ina saka lemon a baki wani irin zafi kaman an zubamin yaji naji nayi saurin ajiyewa ina tare. Dariya tana cewa "Easy. Haka lemon yake shi yasa ake kiransa PARADISE. Da farko zakiji kaman anyi burn d'inki amma da zarar ya wuce za kuga abunda yasa ake ce masa paradise " Kafin na bata masa kaina ya wani irin sarawa yan fara juyawa kaman wacce ke maye. Hannu na kai na dafe ina jin wajen namin hajijiya dariya da ihun mutane duk ya had'armin kaman cikin kwanyar kaina yake yinsu. Yanda kasan kaman irin novels d'in nan ko movies na werewolves dake jin duk wata magana ta mutane komai nisan da suke. Ita Nabila dake kusa dani sai naji maganan ta yamin nisa ba kaman na kowa da nake ni kaman cikin kaina suke ba. Fad'uwa na kus yi daga kan kurejar tayi saurin taro ni tana dariya tace "Kinji abunda nake fad'a ko?, kaman duniyar danke kawai aka yita, saima kin k'ara" Wani cup d'in ta sake kowawa bakina nayi k'ok'arin bugeshi amma saboda jikina babu k'arfi na daki iska . Bakina ta sake bud'ewa ta zubamin lemon ina k'ok'arin dawo dashi naji

Chapter 2 of 11