har na rasa mema zanci. Da dare ya yi Angel sao gata cikin pajamas nata ta haye gadona ta kwanta nayi y'ar dariya ina shafa kanta na tofa mata Addu'a kafin na shige banɗaki na watsa ruwa na fito.
Jakata na d'auko na fito da kayana na barci na saka na haura gadon na zaune riƙe da laptop d'ina. Buɗe ta nayi bayan na saka glasses dina na turawa Louis Vuitton sako kafin na rufe na ajiye gefen dirowa. Ina k'ok'arin kwanciya saiga Marwah data tafi wanka ta dawo sanye da kayan barci gashin kanta a jike sosai har d'iga yake.
Da mamaki na ke kallon ta tana k'ok'arin hawa gadon ta kwanta yanda take yin komai a sanyaye kaman wadda jikin ta babu karfi kona miskala zarratan. Yasa naji wani abu mai nauyi ya tokareni a k'irji nayi saurin kawar dashi nace
"Ya na ganki a nan kuma?"
A kasalance tace "ki barni na kwanta a nan pls. Na gaji wlh"
"Kin gaji da ki ka yi me?"
Batace min komai ba ta yi kwanciyar ta gefen Angel. Numfashi naja mai k'arfi na koma na kwanta ina Addu'a cikin raina. Allah ya bani ikon jure dukkanin wani kalubale da zan fuskanta a gidan nan.
ADX FLORENCE PRISON .
Is the most dangerous prison in the US. Cikin sa da wajen sa matakan tsaro ne na Innalilllahi saboda irin dangerous criminals da suke cikin wannan prison. Daga can k'arkashin prison da aka yi confine na RUSSO the COSTA RICA Mafia Boss. Gaba d'aya entire floor din shida yaran sa ne. Saboda hatsabin cinsa da kuma kuɗi sai yanda ya juya mutanen dake cikin prison d'in. Duk da cewa an kamashi amma hakan bai hanashi cigaba da harkalla da yake ba da ko wane b'angare yana da mutane. Yasan dukkanin wani abundake faruwa a waje ko cikin prison.
Kaman yanzu dai da d'aya daga cikin mutanen sa da wasu security suka shigo cell d'in nashi suka riske shi yana push up.
"Boss"
Miƙewa ya yi daga kwancen da yake ya juyo yana kallonsu. Gaba d'aya jikinsa wasu shegun tattoo ne. Zama ya yi kan gadon yana k'ok'arin kunna walkstick tashi (taba) da sauri d'aya daga cikin securityn ya matso ya kunna masa lighter.
Saida ya zuka ya fesar da hayak'in sannan yace da turanci
"You get some news ?"
"Yes, Boss "
Ya matso da sauri ya mika masa envelop d'in. Russo ya karb'a yana zaro hutunan da suka d'auka d'aya bayan d'aya yana bina yaron Mitchell yana masa bayani kaman haka da turanci
"Boss, we have been tracking him just like you ask us to. This is the picture we take some a hours back. It's seems like whoever she was, she's an important guest to him. He picks her up by him self which is very unexpected of him knowing his reputation."
Wani irin deadly smirk Russo ya saki ya cire tabar dake gefen bakinsa ya na kara kallon hoton da kyau. Perfect.
"And how it's going with our allied? Did she accept my offer?"
Ya yi maganan yana kallin Mitchell. D'an gyara murya ya yi
"She's still hesitant to accepts .but I will keep on trying ,Sir"
"Good"
Har shi MIGUEL zai kama?. Wannan shine big mistake daya tafka a rayuwar sa. He will make him pay just how yanda yasa ya yi loosing dignity nashi.
He is the Boss and will always be the Boss. Sai yasa shi paying back tenfold abunda ya yi masa.
Kwanana biyu yau a UK. Washegarin ranan dana sauka wuni muka yi muna yawo cikin garin. Sosai ya burge ni zama a UK yana da matuƙar dad'i. Yau da shiri na fito zance company na Louis vuitton don naga yanda aikin ke tafiya don tunda nazo ban zauna ba muna ta kai koma wajen ganin mun shirya rigar yanda ya dace. Marwah nasa itama ta bani wasu ideas d'in muka hada. Doguwar riga ce a jikina y'ar kanti da aka yiwa ado da folawowi. Saman rigar na d'ora y'ar jacket ta jeans data tsaya iya kuguna sai d'an mayafi dana d'aura a kai jelar ta koma bayana da gashin kaina dake reto.
Dana fito falon sama naji alamun motsin Marwah da Angel a kitchen don haka na nufi kitchen d'in ina duba wayata da sakon Wizad ya shigomin. Kaman koda yaushe dai kalamai ne bege masu tab'a zuciya. Murmushi nayi na k'ara kitchen d'in na same su daga ita sau wata y'ar shimi da short wando kad'an ya wuce Mazaunan ta Angel ma haka. Sunyi budu-budu da fulawa.
Y'ar dariya nayi na tsaya ina kallon yanda suke wasa da fulawa a kitchen wai za suyi crossaint. Kai na girgiza nace
"Marwah bari naje naga yanda aikin ke tafiya"
Da sauri ta juyo da fulawan a hannu suka had'a ido da Angel.
"No, No .Don't you there"
Nace ina ja da baya . Ai kaman zugasu nayi a guje suka biyo hannu cike da fulawa na juyo da mugin gudu ina ihu suka rufamin baya. Babu zato naci karo da mutum muka tafi gaba d'aya zamu zube a k'asa amma da yake mutum ne made of steel tuni ya dage kafansa na bugu da wannan faffaɗan k'irjin nasa na koma baya da k'arfi na zauna d'abar a kasa.
"Ouch"
Nace ina sosa duwaisiya na da kae zuban zugi. A hankali na fara dago da idona ina bin k'afawunsa dake sanye da Black jeans zuwa farar shirt dake jikinsa sai leather jacket daya dora akai hannu sa sanye da safa da helmet rike a hannun sa. Cikin silver eyes nashi nawa idon ya fad'a. Heart d'ina ya yi skipping nayi saurin kauda kai na miƙe da sauri zan raba ta gefen sa na wuce daidai su Marwah suka cimmin gaba d'aya suka juyamin fulawan nan a tsaye suka barni cikin shock.
Dariya suka sosai harda tafawa ganin na sandare a tsaye .dad'i ya rufe su .banyi zato ba naji dariya sa mai tsananin gard'i. Ya rabbi me nake ji ko imagination d'ina ne? .juyowar da zanyi naga sunyi kansa ya juya a guje yana dariya suna binshi sai zagaye falon suke. Hawaye naji sun cika min ido ina kallon su da murmushi kan fuskata. They deserve to be a very happy and loving family. Suddenly naji dukkanin wani weight dake k'irjina ya kau. I will forever be happy for them.
Murmushi nayi na juya zan koma d'aki Angel ta zo da sauri ta wuce ni ta shige d'akin a guje ta banko k'ofar. Sakato na tsaya ina kallon k'ofar kafin nayi y'ar dariya na kai hannu na buga ina cewa
"Angel buɗe mana na gyara kin san fita zanyi"
Daga ciki"Uh-uhm babu inda zakije. Yau a gida zamu zauna"
Dariya nayi na juya zan cewa Marwah tayi mata magana. Nayi mummunan gani da ko a mafarki bazan so ganin hakan ba.
Tsaye suke tsakiyar falon ya matseta cikin k'irjin sa, duk da tana d'an kici-kicin kwacewa amma irin zazzafan French kissing da yake bata yasa jikin ta ya yi la'asar. Gaba d'aya jikinta ya saki shi ke riƙe da ita yana bata wani irin zazzafan romance mai zautar da mutum. Wani irin gumi ne ya karyo min saboda ,all the while da yake rikata mata lissafi da zafafan kisses. His eyes suna tsaye ne cak cikin nawa saboda ta juyamin baya shi dake rungume da ita, shike fuskanta ta.
Kaman da gayya ya wani d'agata gaba d'aya ya kwantar kan lafiyar cushions dake nan tsakiyar falon, ya koma ya yi mata runfa gaba daya da katon jikin nan nasa. Still idon sa na cikin nawa. Harshen ta yaja da wani irin dirty trick cikin bakin sa . Kaman mayya nabi yanda yaja harshen nata da kallo kafin na mayar da idona cikin nasa . Muna k'ara had'a ido zan iya cewa wani mugun smirk naga ya saki ta gefen baki kafin ya k'ashemin ido.
My heart. Kaman wadda akayi snap wani abu a jikinta na juya da wani fanfalakin gudu ni kaina bana ce ina na dosa ba. A guje nayi k'ofar dana fara cin karo da ita na buɗe da wani irin k'arfi kaman zan ballata daidai naji Marwah ta saki wani irin nishi da k'arfi. Bam na maida k'ofar na rufe saida tayi jijjiga.
Y'ar dariya ya yi ya suri Marwah data fara ficewa hayyacin ta ya yi master bedroom d'insa da ita in case koda Angel zata fito.
K'irjina na dafe da naji yana barazanar tarwatsewa. Saboda yanda nake a firgice ban ma lura da had'uwar d'akin dana shiga ba na koma jikin k'ofar na durkushe a takure. Hawayen dake k'ok'arin biyo kuncina na riƙe ina cewa kaina
'Don't cry, don't cry. His not worth your tears anymore '
𝓉𝒽ℯ 𝒻𝒾𝓇𝓇ℯ & 𝒾𝒸ℯ.
༄ZUBAR HAWAYE༄
𝒜ɱαȥιɳɠ ★'★ ɯɾιƚҽɾʂ ϝσɾυɱ
( 𝒜, ★ ʂƚαɾ'ʂ ,ɯ ★ ϝ)
𝗔𝘀𝗵𝗮𝗻𝘁𝘆 𝗹𝗼𝘃𝗲.
-Mom Sani bata da lfy sosai tana buƙatar Addu'ar ku.
VOL/71-75.
Nafi k'arfi awa d'aya zaune jikin k'ofa ina k'ara nana tawa kaina. 'Na daina ZUBDA HAWAYE saboda shi.' Duk abunda yake yanayi don yaga zuciyata ta buga ko? Zaisha mamaki na inshaAllahu emotions d'in da yake gani cikin kwayar idona saboda shi har yake hukunta saboda su zai dena ganin shi. Zan koyawa kaina tsanar sa kaman yanda nake jin zafin sa yanzu k'asan zuciyata. Enough is enough. I will show him i can leave my life with happiness ko da ban samu wanda zai maye gurbin sa cikin raina ba.
I'm so proud of myself da ko d'igo ban bari hawayen dake cikin ido na ya d'iga ba. Wani irin courage ya zomin, na tashi da k'arfi na, na buɗe k'ofar na fito. Kai tsaye nayi dakina da naci sa'a Angel ta buɗe. Wanka nayi na chanza kayana zuwa wando da riga jeans da shirt da suka kamani sosai na dora jacket kansu na fito sanye da hula . Ina k'ok'arin sauka Angel ta fito a guje sanye da pink gown kaman ta princess da tayi mata kyau sosai a jiki. Hannun ta na riƙe muka fito tare.
Saida na zabi mota lafiyar cikin jeron motocin gidan . Dankareriyar Buggati Chiron driver dake jan ta na karb'i mukullin da kaina na tuka muka bar gidan. Awa biyu muka yi chur a company na LOUIS VUITTON, aikin yana tafiya sosai yanda nake so kafin mu fito maimakon mu koma gida muka hau yawo sosai cikin gari, muna ta nishaɗi nida Angel .
Na kira su ya Aliyu zoom call a mota munfi awa ana hira gaba d'aya da mutan gida ina gaya musu irin ci gaba da aikin nawa ke samu. Gabda magriba bayan mun kwashi snacks, su ice creama da chocolate na juya kan motar muka koma gida. Muna shiga gidan na hango Marwa a tsaye ta cika tayi fam. Baki na tab'e muka fito ribe-ribe da ledoji. A kumbure ta k'araso inda muke tana fad'an mun fita bamu gaya mata ba kuma ta kirani naki d'auka.
Baki na taɓe cikin ko in kula nace
"Taya ki ke so na gaya miki kina wajen Aliya?"
Ido ta zaro matsanancin kunya ya rufeta ,fuskarnan tayi jajur. Na k'ara tabe baki na wuce abuna. Kaman ance na d'aga kai na hango shi tsaye jikin balcony sanye da kananan kaya da suka kamashi sosai ,hannun sa zube cikin aljihun wando. Gashin kansa dame tufke Iska tsakiyar kai iska na kad'a shi.
Bansan sanda na furta d'an rainin hankali ba a zuci a fili naja mugun tsaki na shige ciki. Muna shiga Marwah ta biyo mu da sauri ido rau-rau tace
"Kiyi haƙuri "
Juyowa nayi na kalle ta nace "au me ka ki yimin? Ki rufamin asiri kar ace nazo na hanaki karb'an Aliya. After all Ibadan kenan"
Bata ce komai ba sai kumatun ta data dafe in embarrassment. Huffing nayi na wuce abuna na barta nan tsaye da Angel dake ta munching ice cream. Tunda na shiga d'aki itama bata nemi ba nayi kwanciya ta hankali kwance ina midawa Wizad text messages da yakemin. Abunda ban taɓa yi masa ba tunda yake kirana a waya.
Mun jima muna chat yana ta sani dariya duk wata damuwa ta ta yaye kafin muyi sallama na kwanta zuciyata tar babu kuncin dana saba kwancita dashi.
Washegari hayaniyar dana ji shi ya yi sanadin tashi na na fito sanye da doguwar rigata da barci ina mik'a da hamma. Wata kyakkyawar yarinya ce tsaye da wata babbar mace da zatayi shekarun Mamee. Dukkanin su sunci kwalliya kaman masu zuwa gaba. Turus na tsaya ina kallon su kaman yanda suke kallona sun jera kaf masu aikin gidan da masu tsaron su sai fad'a suke musu kaman zasu ari baki.
Ikon Allah su waye wad'annan kuma?. Budurwar ce ta tako tana tafiya daidai da wata irin shiga breziya da mini jeans sai uban daimon necklace da takarmi mai shegen tsini dake jikinta. Tsayawa tayi gabana tana min wani irin kallo na kyama kafin tace
"And who are you?"
"Who are you?"
Na mayar mata da tambayar ta. Makan tayi bindiga ta fara kira
"Gaurds, take this Maid away right now "
"What?"
Jikina na kalla nayi y'ar dariya nace
"I did not know dressing decently not like some prostitute, will make some crazy ass people think am a maida. "
Da wani k'araji tace "what did you call me?"
Hannu ta d'aga da k'arfin ta zata mareni, nabi hannun da kallo ina jira ta tab'a ni yanzun na karya wannan shegen hannun mai kama da falanki.
"Mikelah"
Muryar sa ta ratso falon a kausasashe. Baki ta cije ta juya inda yake tsaye sanye cikin kakin sa na sojoji. Kayan sun masifar yi masa kyau ko dan ban taɓa ganin sa ciki su bane.
"My son "
Nayi saurin kallon matar dake tsaye tun fitowa ta bata ce komai ba. Wannan ce mahaifiyar sa? Tabbas ga kama nan kuwa. Ga inda ya samo kyau nashi duk da shina Mahaifin sa Alhaji Muhammad Siddiq kyakkyawan mutm ne. Ya tabbata kenan mahaifiyar tashi ba musulma bace. Saboda mutunci da girman Uwa nace
"Good Morning Ma'am "
Maimakon ta amsa ,sai ta watsamin kallo mai cike da tsantsan tsana kafin ta juya kan Deen da har zuwa lokacin yana tsaye cikin matsanancin b'acin rai.
"Miguel, please we need to talk?"
Miguel? Na maimaita sunan cikin raina. Numfashi ya fesar mai zafi ya tako har inda take tsaye
"How did you get in without my knowledge?,and who ask you to bring her into my house?"
Ya k'arasa yana watsawa Mikelah wani kallo na tsantsan bacin rai.
"How could you say that?, she's your cousin. More closer to you than your gold digging, scum bag of a wife"
Gasp ne ya fito daga bakina hannu dafe da k'irjina. Marwah take kira da wannan sunan? . Gaba d'aya suka kalleni na. Na k'ara harde hannu a k'irji ina kallon su .a shirye nake na kare y'ar uwara ,ba uwa ba ko wace ita zan gyara mata zama.
"Sanaah, koma d'akin ki"
Saida na tsayar da ido na cikin nasa don yasan cewa bawai dan ya yi min magana zan koma ba, ra'ayin kaina ne. Naga dalilin da yasa Marwah bata fito ba tunda suka shigo. Kallo na watsa musu gaba d'aya na juya na shige d'aki.
Tana shiga ya maida hankali kan Georgia dake kallon k'ofar da wani irin expression kan fuskarta .
"What do you want ?"
Numfashi taja tace " Your Father "
Wani iri taran numfashin ta ya yi "No. Your Husband. Kar ki kara kiransa da uba na"
Baki ta cije. Ta cigaba da cewa rai a b'ace " kasan irin rayuwar da muke da mijina. Mikelah nan " ta janyo Mikelah dake gefe tana kallon sa kaman ta had'iye.
"Kasan tuntuni take son ka?, mistake ne muka samu Mijina Micheal ya yi tarayya da ita ,and know she's pregnant da cikin sa. Idan abun ya fita zai bata sunan family namu the VALANTINO'S and you included. Abunda nake so da kai ina so ka auri Mikelah sai ka raini cikin a matsayin naka.."
"Get out, get out of my house and dont ever contact me again. Kisa a ranki baki d'a wani da mai suna Deen"
Da sauri ta matso zata tab'a shi tana cewa "Miguel, ina yin haka saboda repetition na family namu saboda me zaka ce ha.."
Da wani irin murya mai matsanin kaushi a d'ai-d'aice yace "G.e.t.o.u.t" ido ta zuba masa sai huci yake kamam zaki ,kai ta gyad'a ta juya da zafin rai zata fice, Mikelah dake sharar hawaye burinta bai cika ba son kasancewa dashi ta rufa mata baya tana waiwayen sa. Har sun kai bakin k'ofa ta juya tana kallon sa da wani irin tsana ganin blackmailing d'inta baici ba tace
"You will regret this"
Fuu taja hannun Mikelah suka fice. Numfashi yaja mai zafi ya fesar, ya yi saurin zama kan kujera dake gefen sa jikinsa na wani irin shaking, ya d'auko tabar sa mai tsananin kauri ya kunna ya sata cikin bakinsa yana zuk'a idon nan nasa jajur kaman garwashin wuta.
Shirun da falon ya d'auka Marwah dake mak'ale bakin kofa tuntuni ta buɗe k'ofar ta fito. Ido suka had'a daidai sanda ya kai tabar bakinsa yana mata wani irin zuk'a. Ta san waye Deen ciki da waje duk lokacin da yake cikin irin wannan b'acin rai ba'a iya tunkarar sa. Don haka taja ta tsaya tana kallon sa ciki matsanancin tausayi. Ace uwa ta haife ka amma duniya bata da mak'iyi irin d'an data haifa saboda ya tashi da addinin daba nata ba.
Mutum d'aya ne tasan yanzu idan ta kira zauyi calming wannan fushin nashi. Don haka ta juya ta koma d'aki ta d'auko wayarta tana kiran Mahaifin Deen. Bugu biyu ya d'aga cikin tsantsan kulawa yace
"Ya'ta, tunda naga kiran ki yanzu nasan kwanan zancen. Ki kwantar da hankalin ki zan kira shi."
"To Daddy "
A b'angaren sa kuwa zuk'ar tabar sa yake kaman babu gobe. Wayar sa dake gefe ta fara k'ara sunan Pops yana yawo a kai. Ajiyar zuciya ya sauke ya d'aga wayar ya kara a kunne baice komai ba yana sauraran Mahaifin nasa dake bashi baki har ya samu ya d'an sauka.
Kashe wayar ya yi bayan ya gama sauraran Mahaifin nashi ya miƙe tsaye. Kallo d'aya ya watsawa Marwah dake tsaye tana kallonsa ya juya ya fice babu sallama. Da idon ta dake cike da hawaye ta bishi da kallo har ya fice kafin ta koma d'aki da gudu kuka mai k'arfi ya kwace mata.
Waya ga gahoo. Bansan meke faruwa ba don tunda na koma d'akin , na koma nayi kwanciya ta hankali kwance ban fito ba sai wajen biyu shima saboda yunwa. Da kaina na had'a y'ar Indomie data ji kayan lambu na soya plantain. Sannan na shake cup d'ina da fresh milk na zauna nan falon ina cin abinci hankali kwance. Shiru-shiru banji motsin Marwah da Angel ba na miƙe na nufi k'ofar d'akin nata na d'an buga kafin na tura na shi ga da y'ar sallama.
Can kuryar gado na hango cikin bargo. Da sauri na k'arasa ina kiranta ta dago da jajayen idonta da suke a kumbure.
"Subhanallahi, Marwah lfy? Meya same ki?"
Da kyar tacemin bata jindaɗi ne bayi saurin koma kitchen na had'a mata shayi mai kyauri na kawo mata .saidai na tabbatar ta shanye shayin sannan na koma na karasa nawa. Ban koma d'aki ba saida nayi can inda Angel ke wasa gurin Nanny d'in ta Atina dake kulawa da ita sosai.
Lokacin dana dawo na d'auki ragowar fresh milk d'ina na kurbe kafin na koma d'aki saboda kiran la'asar da ake. Wanka nayi na fito d'aure da alwa. Rigata kawai nasa na tada sallah. Dana idar sai kawai nake jin wata irin kasala ga wani irin barci da nake ji kaman ban wuni ina barci ba.
Nan kan daddumar na b'ingire sai barci.
Ihun Angel dana ji tana kiran "Mummy " shi ya yi sanadin farkawa ta daga barcin daya d'auke ni mai nauyin gaske. Ikon Allah kome yasa ni barci kuma da yamman nan Allah masani. A hankali nayi yunƙurin miƙewa zaune kaina ya sara nayi saurin kai hannu na dafe ina kiran wash.
Ido na da ya yimin nauyi sosai na ware kan Angel data juya a guje tana ihu. Mamaki ya kamani na dafa gadon ina k'ok'arin miƙewa wani irin santsi ya kwasheni na koma kasa tim na zube. Dif naji abu ya d'igo kan fuskata. Na kai hannu na shafo ina kallon ko mene.
Wani irin harbawa k'irjina ya yi ganin jini. Da sauri na ware ido ina bin ta inda jinjin ke d'iga. Daga kan gado na. Wait. Dakin nabi da kallo nan ba d'akina bane. Dakin Marwah ne. Da wani irin sauri na miƙe zaune.
Gigitacciyar k'ara na saki ina kiran Marwah dake kwance kan gado babu wani motsi tattare da ita. Tayi jina-jina kaman wadda tayi wanka cikin jini. A firgice na haye gadon na d'ago ta ina ihun neman taimako ban lura da wuk'ar dake soke cikin taba saida na rungume ta ina ihu da kuka kaman mahaukaciya sannan naji alamun ta.
Cikin matsanancin rud'u da tashin hankali na kai hannu wajen ina k'ok'arin zareta daga jikin ta, aka bugo k'ofar da k'arfin gaske.
"Stop. Do not move. Your under arrest . You have the right to remain silent. Everything da ki ce za'ayi amfani dashi wajen bada hujja a kan ki. Don haka kiyi shiru har sai munje Station "
Firgice da rudu yasa na saki baki cikin matsanancin mamaki ina kallon FBI da sojojin Deen da suka shigo d'akin da makamai. Daya daga cikin su ya matso da sauri ya kamani ya juya jikin bango ya sarke ni da ankwa.
Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Alhumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan min ha..
BOOK 1 END.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those