Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
ina Marwah? Sannan kuma karatun ta fa su da suke kan gab'ar zana WAEC bayan haka Matsayin nasu ba d'aya ba. Baya son ya tura yaran sa inda za'a wulaƙanta saboda basu dashi. Kaman Ya Aliyu yasan tunanin da yake yace "Don Allah Baffa kar kace A'a. Ni nasan waye Deen ciki da waje. Dukiyar sa da matsayin sa ba komai bane . In har a kan karatune bashi da matsala zata iya zana jarabawar ta kuma ta cigaba da makaranta. Tunda har ya furta yana son Marwah da Aure kasan Baffa bawai wasa ne ya kowa saba. Yanzu haka zancen da nake auren iyayen nasa suke so ya yi ido rufe duk matan dake bibiyar sa babu wacce ta samu matsayi har ya furta yana son ta da aure sai Marwah. A ganina wannan abun alfahari ne a garemu domin tarbiyar da kuka bamu ce tayi tasiri a kansa har yake neman had'a zuri'a damu" Murmushi Mamee ta k'arayi na farin ciki. alhamdulillah burinta nason ganin aure yaranta ya fara cika Allah ya kawowa Sanaah itama miji na gari ta aura. Burin kowane iyaye kenan su aurawa y'ay'an su mazaje na gari da zasu kulasu dan haka tace "Inhar izini yake nema Aliyu kace mun bashi ya turo magabatan sa don na yaba da hankalin sa bawai ganin idon kaba. Allah ya yi Albarka " Wani irin dad'i ya kama Aliyu ya saki murmushi shima Baffa murmushin ya yi tunda har sanyin idaniyarsa ta amince bashi data cewa. "Amin Fulani. Allah ya nuna mana da rai da lafiya. Sai kuma Sanaah itama Allah ya fito mata da miji na gari" Gaba d'aya suka amsa da 'amin' WAI MENENE ASALIN BAFFA DA AYSHA FULANI? MAMEE? BAFFA malam Abbakar Siddiq SHAZALI cikakken bahaushene kuma nan D'an kano. BAFFA ya taso cikin gidan nan na mutan yawa wanda za kaga kaf familyn ne a cikin sa tun daga kakanni har jikoki. Alhamdulillahi ubangiji ya azurta familyn na SHAZALI da y'ay'an maza da mata don mata hudu ne a gidan ciff. Kuma ko wacce cikin su ta ajiye ya'ya bakwai zuwa goma . Sannu a hankali suma yaran suka taso sukayi aure suka hayayyafa . Alhaji SHAZALI irin tsohon attarijin nan ne. Bayan mutawar sa aka raba musu gado. Matan kowace ta tashi da fili da d'an kuɗi da zasu ja jari ya yinda maza suka tashi da gidaje da kuma gonaki. Baffa na daga cikin wanda ya mallaki gida da gonaki har biyu. Cikin ikon Allah kuwa Allah ya sawa gonar tashi Albarka ta shinkafa da masara. Buhu-buhu ake kaita k'asashen mu na Nigeria. Wata rana yakai Niger inda anan ne ya had'u da Aisha da mutanen Niger ke Kira Da Aishwarya saboda kyau da Allah ya bata. Aisha irin fulanin nan ne da ake kira da SADAKA YALLA. Kyakkyawar mace ce ta bugawa a jarida. Had'uwar farko ta tafi da zuciyar Baffa. Soyyayya mai karfi ta shiga tsakanin su Cikin ikon Allah Iyayen ta suka aminci masa bayan mak'udan kuɗi daya bayar na sadaki. Baiji komai ba acewar sa Fulani ta kai ka saida dukkanin wata dukiya taka a kanta. Yana can Niger y'an uwa suka zo aka nema masa aurenta bai bar Niger ba saida Fulani. Shekarar su d'aya a nan kano Fulani ta sankaco Kyakkyawan yaron ta Aliyu kaman balarabe. Baki kuwa ya yi caa a kansa shi yasa a koda yaushe cikin Addu'a iyaye yake. Allah da ikon sa sai arziƙin Baffa ya fara habb'aka ganin haka ne kuma aka fara tsegumi da gulmace-gulmace a unguwa. Tun bata tasiri cikin dangi na SHAZALI har tazo ta fara aiki kunsan ance zuciya bata da kashi. Daga nan Baffa da Mamee suka fara fuskantar canzi daga cikin family. Hassada ,bak'in ciki ya fara tsananin k'arara.Kullum cikin hab'aici ake mata ta shanye Baffa ta hanashi taimakon y'an uwa saboda taga Allah ya fifitashi kan su ta kuma hanashi aure. Abun har yakai Aliyu baya iya shiga cikin yara na dangi da yashiga za kaji an buge shi an koroshi ana kira da shege. Tun abun baya damun Mamee har ta fara maidawa idan suka tab'a mata yaro saboda haka gaba d'aya suka had'e mata kai. Data gaji ta kwashi kayanta zata koma Niger tace da Baffa in har yana son zama da ita dole ya nema mata wani gida baza ta zauna ana cin zarafin taba da yaron ta ana shegan ta mata shi saboda ya fita daban. Da kyar ya lallabata tayi hak'uri da baki da rarrashi. Kaf zuri'ar su babu wanda ya tab'a barin gida yaje waje ya zauna don haka baza a fara a kansa ba. Shekarar Aliyu Biyu Mamee ta haifi Khamis a kuma lokacin ne zamuce jarbawa ta sami Baffa ya tara Albarkar gona za'a kai masa border dan fita da ita waje . Y'an garkuwa suka kame motar da mutanen ciki saida ya biya diyya ta y'an kudadden sa ya bayar aka sake su. Kaman jira ake karayar arziƙin tazo abun ya k'ara tsamari cikin dangi yanzu sai haibicin ya koma nacin mutunci da dariyar mugunta. Wato su abunda ya samesu sunfi kowa farin ciki da hakan. Sosai abun ya dami Baffa ganin yanda y'an uwan nasa maza suka juya masa baya. Cikin gida babu dad'i waje babu dad'i saboda haka ya saida b'angaren sa ya nemi gida nan Adamawa ya zauna shida iyalen sa. Hikimar Ubangiji kuwa yana zuwa nan ya samu aikin zaman shago a wata ana biyan sa dubu bakwai. A guje Baffa ya karb'a babu girman kai shi dama neman halak ba'a girman kai da dukkanin abunda aka samu. Allah kuwa ya sanya masa Albarka dukkanin wani abun buƙata yana ajiyewa Mamee a gida basu rasaci ba basu rasa sutura ba. Shekarar Aliyu biyar ya shiga makaranta shi kuma Khamis yana Shekara hudu. Tun tasowar Aliyu yake da burin aikin Soja kuma Allah ya cika masa burin sa. Khamis shikam har yanzu bashi da zabi kaman Baffa duk abunda ya samu yi yake indai za'a biya shi. Khamis nada Shekara shida Mamee ta samu cikin Su Marwah. Tayi mamaki matuƙa don ta fidda ran k'ara haihuwa sai kuma Allah ya bata lokacin da batayi zato ba. Wata tara ciff ta haife Sanaah da Marwah. Duk yaran Mamee hasken ta suke yowa da gashin ta Sanaah ce kad'ai ta sirka da bak'in Baffa .hakan yasa fatar ta take kaman ta Black Americans mai shek'i da maik'o sannan ita kwayar idon ta ta fita daban dana sauran nata Brown ne sosai asalin hakan nada nasaba da mahaifin Mamee don irin kwayar idon sace saboda mahaifin ta baturene. Wannan shine Asalin SU. 𝓉𝒽ℯ 𝒻𝒾𝓇𝓇ℯ & 𝒾𝒸ℯ. ༄ZUBAR HAWAYE༄ 𝒜ɱαȥιɳɠ ★'★ ɯɾιƚҽɾʂ ϝσɾυɱ ( 𝒜, ★ ʂƚαɾ'ʂ ,ɯ ★ ϝ) *ZINARIYAR MACE⚡* *Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.* Na gyaran nono. Na sanyi. Dilka tare da hadin sabulu. Duk Wani nau'in maganin mata. Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani. *08089965176* *07084653262* 𝗔𝘀𝗵𝗮𝗻𝘁𝘆 𝗹𝗼𝘃𝗲. " -- 𝑌𝑜𝑢 𝑤𝑖𝑙𝑙 𝑘𝑛𝑜𝑤 𝑦𝑜𝑢'𝑟𝑒 𝑖𝑛 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑤ℎ𝑒𝑛 𝑦𝑜𝑢 𝑐𝑎𝑛'𝑡 𝑓𝑎𝑙𝑙 𝑎𝑠𝑙𝑒𝑒𝑝 𝑏𝑒𝑐𝑎𝑢𝑠𝑒 𝑟𝑒𝑎𝑙𝑖𝑡𝑦 𝑖𝑠 𝑓𝑖𝑛𝑎𝑙𝑙𝑦 𝑏𝑒𝑡𝑡𝑒𝑟 𝑡ℎ𝑎𝑛 𝑦𝑜𝑢𝑟 𝑑𝑟𝑒𝑎𝑚𝑠.." VOL/21-25. "Sanaah, Sanaah ki tashi lokacin islamiya ya yi" Juyi nayi ina k'ara k'ank'ame filon da nake kwance a kai saboda mafarki da nake da bana son ya katse. Jijjigani ta k'ara yi "Kinsan fa ya Aliyu na nan" Kalman ya Aliyu data furta yasa na buɗe ido da sauri na zuba mata su cike da haushi ina cikin mafarkina mai dad'i tasa na katse. Harara na zuba mata na yunƙura na miƙe ina mita. Shikenan mutum bashi da hutu. Ka dawo daga ta boko k'arfe d'aya ,karfe uku kuma ka tafi islamiya sai shida haba. ( Nace yaushe ki ka je makaranta?). Kallon ta nayi harta shirya na miƙe na zura nawa uniform d'in ina tunanin mafarkin da nayi na wannan mutumin mai kyau. Murmushi nayi na gama shiryawa muka fito muka iske Mamee nan tsakar gida kan tabarma tana shan iska gefen ta radio nata aiki. Zafin garin ne ya yi yawa gashi bamu cika samun wuta ba. Har k'asa muka durkusa muka yi mata sallama ta bimu da Addu'a muka fito. D'an nesa damu kad'an na hango ya Aliyu da ya Khamis cikin y'ar majilisa da samarin unguwar ke zama. Na tab'e baki aikin kenan dai kullum a zauna ana hirar y'an mata. Wlh ni makarantar nan in badan zanje shagon Talle ba babu abunda zai sani zuwa makaranta. Yauma dai damuwa ce kwance kan fuskar Harira karatun ma Sam bata yi sai in Malama Zainab tayi magan kaga ta firgita.Dole kuwa na d'auki mataki kan Khadija .muna tashi na riga Marwah ficewa da sauri nayi shagon Talle. A cike naga shagon mata suna ta hotona alamun wani abune za suyi ko biki ko party. Yana ganina ya washe hak'ora .fuska na b'ata a dake nace "An gama had'a hutunan?" Dariya ya yi ta irin y'an iska ya miƙomin hutunan da aka yi editing babu ta yanda za'ayi kace had'asu aka yi. Shegen kwaro kenan. Murmushi nayi ina kallon hutunan. "Ya kiga gansu? Sunyi yanda ki ke so?" Murmushi na k'ara yi ina jinjina kai. "Sunyi Sosai Talle Nagode kwarai" "Ta hanya d'aya ne zan karb'i godiyar ki" Kallon sa nayi ina jiran me zaice "Ki bani number d'inki da ki ke tamin rowar ta" Wani irin murmushi ne ya sub'uce min banyi tunanin komai ba na bashi number Khadija yanda plan dina zai tafi daidai. Bakin sa kuwa har kunne kallon sa nayi nace "Amma fa da sharad'i yanzu ka kirani don na bar waya a gida zanyi save nata. Tana shiga sai ka kashe sai na kiraka tunda kasan bana waya a gida. Amma ka dinga min flash kullum idan na fito zan kira ka sai ka kirani" Aikuwa ya kara washe baki na fice zuciyata fes nayi gida. Karo mukaci da ya Aliyu dake k'ok'arin fitowa nayi saurin rabewa gefe ina zare ido? Murtake fuska ya yi yana kallona cikin tuhuma "Daga ina ki ke?" Da sauri nace " yau bamu tashi da wuri bane mun tsaya bada hadda" "Karya ki ke wuce muje ciki" A guje na shige ya biyo ni nayi saurin b'oyewa bayan Baffa dake fitowa daga d'aki riƙe da carbi Mamee biye dashi. "A'a Subhanallahi lfy Hassana? Kai Aliyu lfy ka biyo ta cikin gida haka da gudu" "Baffa tun d'azu Marwah ta dawo ita gidan ubanwa taje sai yanzu ta shigo ana gab da kiran magriba? " Rau-rau nayi da ido ina kallon Baffa nace "Baffa hadda fa muka tsaya bayarwa shine yasa bamu dawo da wuri ba" Ajiyar zuciya Baffa yaja yana kallon Ya Aliyu "To kaji Aliyu don Allah a dinga tsayawa anaji basi a daina yanke hukunci kai tsaye" "Baffa kasan Karyar Sanaah. Marwah fito nan " Cikin nutsuwa ta fito daga d'akin muna had'a ido da ita na watsa mata manyan ido na ta sauke ajiyar zuciya ta maida hankali kan Ya Aliyu dake jefa mata tambaya. "Da gaske ne abunda tace?" A sanyaye tace "Eh ya Aliyu na biya ta ajin nasu naga ba'a tashe suba shi yasa ni na tawo" Wata b'oyayyiyar ajiyar zuciya na sauke ina hamdala cikin raina. Kwafa ya Aliyu ya yi yana kallo "Wlh da K'arya ki ka yi sai na bab'b'alla cikin gidan nan" Murmushi Baffa ya yi yana girgiza kai "Ash-ash Gadanga kusar yaki, ayi mata hak'uri. Hassana bawa yayan naki hak'uri " Ciki-ciki nace "kayi hak'uri " cikin raina ina tunanin abunda zanyi na rama nima. Kwafa ya yi ya fice daga gidan saboda kiran sallan magriba da aka fara Baffa shima yabi bayan sa. Numfashi na sauke bayan sun fice na juyo ina kallon Mamee dake kallona kaman tana karantar wani abu nayi saurin wucewa na shige d'aki na iske Marwah zaune kan gado ta zubawa k'ofar ido. Ina shiga muka had'a ido nayi saurin d'auke kai na cire uniform d'ina na saka doguwar riga data d'an kamani daga sama. Duk abunda nake ina jin idonta a kaina naki kuma bata fuska tayi magana har na gama shiryawa na fice na had'a uniform d'ina da pant da bra d'ina ina wanke wa. Ina cikin shanya pant dina da breziya ta ya Aliyu da ya Khamis suka shigo Baffa biye dasu. A murtuke ya Khamis yace "Mene wannan ki ke shanya mana a tsakar gida saboda bakida kunya" Turus na tsaya riƙe da kayan a hannuna ina kallon su kaman wata wawiya. To ina suke so na shanya tunda igiyar kwaya d'aya ce . Baffa wucewa ya yi baice komai ba ya shige d'aki ,Mamee dake k'ofar kitchen ta miƙe ta bishi d'aki. Tsawa ya Aliyu ya k'ara dakamin "Ba magana ake miki ba? Haka ki ga Marwah nayi?, ko tsakar kiga ki ka ga Marwah na shanya nata sai kece mara kunya ?" Their is the famous haka kiga Marwah Nayi? Hawaye ne suka cika min ido na juya da kayan na shige d'aki fuu y'ar ventilation namu dake bayan d'akin mu na shige na shanya su bayan window inda take shanya nata. Ina k'ok'arin tada sallah ta miƙe ta fice daga d'akin. Dana idar zama nayi ban fito ba ina jin sunata hira cike da nishaɗi babu wanda ya nemi. Ni dama nasan duk sun tsaneni. Jakata ta islamiya na buɗe na d'auko kuɗin nan da mutumin nan ya bani na hau tunanin yanda zanyi dasu ba tare da an zargeni ba. K'arar wayar Marwah ya katsemin tunani na zubawa wayar tata dake kan gado ido sai vibration take na neman a gaji. Ina ji wayar harta tsinke banyi yunƙurin kiranta tazo ta d'auka ba wani kiran ya k'ara shigowa. Miƙewa nayi a hankali na nufi kan gadon saboda zuciya ta da take ta ingizani na d'auka naji dawa ne take yawan waya haka daga jiya zuwa yau. Babu suna kan number sai EMOJI kawai na zuciya. Hannu na kai na d'auka na k'ara ta a kunne kafin nace komai wata irin ajiyar zuciya ta sauka cikin kunnena k'irjina ya wani irin harbawa kaman an soka mashi ya wuce ta tsakiyar ta kafin naji wata irin murya mai tsananin dad'i ta da kaushi tace "Baby" Da wani irin gudu zuciyata ta fara harbawa kaman wadda ke tseren gudu, nayi saurin kai hannu na dafe k'irjina meke shirin faruwa ne?. Rawa jikina ya fara na k'ank'ame wayar cikin kunne ina sauran muryasa mai tsananin gard'i da taushi yana kira "Baby are your there?, say something pls? Ya rabbi meke shirin faruwa da nine? Wani irin nutsuwa muryar ke saukar min sai takemin shige da wannan mutumin na jiya. Ko kad'an bana so ya daina magan dan gaba d'aya sassan jikina ke amsawa. "Sanaah " Babu zato naji muryar Marwah bayana nayi saurin cire wayar a kunne na juyo kaina a k'atsa na miƙa mata wayar jikina na rawa nace "Ana kiran ki" A hankali ta tako ta karb'i wayan na wuce da sauri na fice daga d'akin .kusa da Mamee na zauna jikina gaba d'aya a mace babu kuzari. Muryar Baffa naji yana cewa "To Alhamdulillanhi d'azu Aliyu ke sanar dani cewa magabatan Kamaludeen na nan zuwa cikin satin nan inshaAllahu don neman auren Marwah ,don haka Fulani ki zuba tsanmami daga nan har k'arshe sati a ko wace rana zasu iya zuwa tunda ba mutanen nan bane na " Dum naji k'irjina ya buga da tsananin k'arfi saida na kai hannu na dafe. Wai meke shirin faruwa da nine meke damuna?. D'agowa nayi ina kallon Mamee dake murmushi najin dad'i babu wanda ya kula da yanayin dana shiga na maida kaina katsa cikin zurfin tunani. Banji sanda Baffa ya juyo kaina yana magana ba saida Mamee ta zungureni na d'ago a firgice ina kallonta tace "Tunanin me ki ke ana miki magana?" Bance komai ba na mayar da kaina kan Baffa dake kallona cike da kulawa. "Nace Hassana ko kema kina da wani da ki ke so?" Kai na girgiza na kasa cewa komai. Murmushi ya yi yana cewa "To ubangiji kema ya fito miki da miji na gari ." Ya juya kan su ya Aliyu "kuma ya kamata ku fara shirin ajiye iyali a gida Allah ya bada mata na gari masu tarbiya don Y'ar Uwar ku tayi dace sai dai muce Alhamdulillahi " Saida na had'iye wani abu daya tokare min makogaron na da kyar na amsa da 'Amin' tare dasu Mamee. Har Marwah ta fito na kasa gane kaina haka suka cigaba da hira ana raha duk irin yunwa da nake ji kasa cin abinci nayi na d'an chakala na miƙe na shige d'aki na kwanta ko na samu nayi barci. Amma haka naita juyi kan gado barcin yaki zuwa koya ya na juya muryar sa nake ji cikin kunne na tana furta 'BABY.' Me yasa ne dashi da wannan mutumin suke neman hanani sukuni daga jiya zuwa yau? Meke shirin faruwa da nine ? Ina jin sanda ta shigo d'akin nayi saurin rintse ido kaman mai barci ta gama shirin ta ta kwanta gefena bata jima ba naji saukar numfashin ta a hankali alamun ta samu barci. Ni kuwa haka nayi ta juyi cike da damuwa na kasa barci duk irin shirin dana kulla na raba Zubair da Khadija da zan fara aiwatarwa yau kasawa nayi. Bansan awa nawa nayi ido biyu ba har barci b'arawo ya kwashe ni. 𝐁𝐄𝐇𝐈𝐍𝐃 𝐓𝐇𝐄 𝐒𝐂𝐄𝐍𝐄😂 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐀𝐇---- '𝐖𝐀𝐈 𝐒𝐇𝐈𝐍 𝐊𝐔𝐍𝐀 𝐓𝐀𝐑𝐄 𝐃𝐀𝐍𝐈 𝐊𝐔𝐖𝐀 𝐀 𝐖𝐀𝐍𝐍𝐀𝐍 𝐆𝐋𝐀𝐌𝐎𝐑𝐎𝐔𝐒 𝐀𝐃𝐕𝐄𝐍𝐓𝐔𝐑𝐄 𝐍𝐀𝐖𝐀? MENE 𝐊𝐔 𝐊𝐄 𝐓𝐔𝐍𝐀𝐍𝐈𝐍 𝐘𝐀𝐍𝐀 𝐒𝐇𝐈𝐑𝐈𝐍 𝐅𝐀𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐃𝐀𝐍𝐈? 𝐖𝐀𝐈 𝐒𝐇𝐈𝐍 𝐙𝐔𝐂𝐈𝐘𝐀 𝐍𝐀 𝐈𝐘𝐀 𝐊𝐀𝐌𝐔𝐖𝐀 𝐃𝐀 𝐒𝐎𝐍 𝐌𝐔𝐓𝐔𝐌 𝐁𝐈𝐘𝐔 𝐋𝐎𝐊𝐀𝐂𝐈 𝐃'𝐀𝐘𝐀 ? --'𝐊𝐔 𝐁𝐀𝐍𝐈 𝐀𝐌𝐒𝐀 𝐏𝐋𝐒 𝐀 𝐘𝐀𝐍𝐙𝐔 𝐊𝐀𝐌 𝐍𝐀 𝐒𝐇𝐈𝐆𝐀 𝐖𝐀𝐍𝐈 𝐘𝐀𝐍𝐀𝐘𝐈 𝐃𝐀 𝐍𝐀𝐊𝐄 𝐁𝐔𝐊𝐀𝐓𝐀𝐑 𝐒𝐇𝐀𝐖𝐀𝐑𝐀𝐑 𝐊𝐔. --'𝐊𝐔 𝐌𝐀𝐙𝐀 𝐊𝐔 𝐆𝐀𝐘𝐀𝐖𝐀 𝐌𝐈𝐒𝐒 𝐀𝐒𝐇𝐀𝐍𝐓𝐘 𝐋𝐎𝐕𝐄 𝐒𝐇𝐀𝐖𝐀𝐑𝐀𝐑 𝐃𝐀 𝐊𝐔 𝐊𝐄 𝐓𝐔𝐍𝐀𝐍𝐈𝐍 𝐙𝐀𝐊𝐔 𝐁𝐀𝐍𝐈 𝐒𝐇𝐄 𝐖𝐈𝐋𝐋 𝐒𝐄𝐍𝐃 𝐓𝐇𝐄𝐌 𝐑𝐈𝐆𝐇𝐓 𝐁𝐀𝐂𝐊 𝐓𝐎 𝐌𝐄😉. :--𝐌𝐈𝐒𝐒 𝐀𝐒𝐇𝐀𝐍𝐓𝐘 𝐋𝐎𝐕𝐄 𝐓𝐇𝐀𝐍𝐊 𝐘𝐎𝐔 𝐅𝐎𝐑 𝐆𝐈𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐄 𝐓𝐇𝐈𝐒 𝐏𝐋𝐄𝐀𝐒𝐔𝐑𝐄 𝐎𝐅 𝐓𝐄𝐋𝐋𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐘 𝐒𝐓𝐎𝐑𝐘. 𝐀𝐒𝐇𝐀𝐍𝐓𝐘 𝐋𝐎𝐕𝐄 :-- '𝐎𝐇𝐇 𝐇𝐎𝐍𝐄𝐘 𝐘𝐎𝐔𝐑 𝐒𝐎 𝐖𝐄𝐋𝐂𝐎𝐌𝐄. 𝐈 𝐂𝐀𝐍 𝐍𝐎𝐓 𝐖𝐀𝐈𝐓 𝐓𝐎 𝐇𝐄𝐑𝐄 𝐓𝐇𝐄 𝐄𝐍𝐃 𝐎𝐅 𝐓𝐇𝐈𝐒 𝐋𝐎𝐕𝐄𝐋𝐘 𝐒𝐓𝐎𝐑𝐘 ,𝐀𝐌 𝐒𝐔𝐑𝐄 𝐈𝐓'𝐒 𝐀 𝐑𝐎𝐋𝐋𝐄𝐑 𝐂𝐎𝐒𝐓𝐄𝐑 𝐎𝐅 𝐄𝐌𝐎𝐓𝐈𝐎𝐍🤧 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐀𝐇 :--- '𝐎𝐇 𝐈 𝐁𝐄𝐓 𝐘𝐎𝐔, 𝐈𝐓 𝐈𝐒☹️ 𝐀𝐒𝐇𝐀𝐍𝐓𝐘 𝐋𝐎𝐕𝐄---' 𝐎𝐇𝐇𝐇🤧🤧. 𝐆𝐎𝐃. 𝐀𝐋𝐑𝐈𝐆𝐇𝐓 𝐖𝐄 𝐀𝐑𝐄 𝐒𝐎 𝐑𝐄𝐀𝐃𝐘 .𝐈 𝐖𝐄𝐋𝐋 𝐒𝐄𝐄 𝐘𝐎𝐔 TOMORROW 𝐋𝐎𝐕𝐄. 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐀𝐇--- '𝐁𝐀𝐂𝐊 𝐀𝐓 𝐘𝐎𝐔, 𝐓𝐇𝐀𝐍𝐊 𝐘𝐎𝐔 ♥︎. 𝓉𝒽ℯ 𝒻𝒾𝓇𝓇ℯ & 𝒾𝒸ℯ. ༄ZUBAR HAWAYE༄ 𝒜ɱαȥιɳɠ ★'★ ɯɾιƚҽɾʂ ϝσɾυɱ ( 𝒜, ★ ʂƚαɾ'ʂ ,ɯ ★ ϝ) 𝗔𝘀𝗵𝗮𝗻𝘁𝘆 𝗹𝗼𝘃𝗲. VOL/26-30. Saboda barci da ban samu ba daren jiya yau na tashi da wani azababben ciwon kai irin na b'ari d'ayan nan. Da kyar na iya yin sallah na koma na kwanta na kudundune. Ina jin Marwah na tulawar karatu kaman yanda ta saba wani lokacin ta takura sai munyi tare .Da alama itama ta fuskanci bana jindaɗi dan tana gama tilawar ta fice ta hau shara da nake yi tayi har wanke-wanke da wanke toilet. Ina jin motsin ta a kitchen tana k'ok'arin d'ura abinci Mamee ta fito tana mata magana Da sauri Marwah ta durkusa har k'asa cike da ladabi tace "Barka da Asuba Mamee an tashi lfy?" "Lfy lau Marwah ina gimbiyar take ita bata tashi ba ta barki ki ke aikin ke kaɗai? " "Mamee wlh yau bata da lfy ne don jiya da zazzabi ta kwana" Nan da nan yanayin ta ya canza tayi d'akin tana cewa "Subhanallahi me yasa meta haka?" Ina jin ta nufo d'akin na k'ara kudundunewa ina runtse ido. Da sallama ta shigo ta nufi gadon da nake kwance da sauri tana zuwa ta dora hannu kan goshina da nake jinsa kaman an kunna masa wuta. A hanzarce ta janye hannun tana kiran Subhanallahi ta fara k'ok'arin d'aga ni tana kiran sunana. Jin yanda duk ta rikice na saki kuka da ni kaina na rasa na mene. D'agani tayi gaba d'aya ta rungume kan kirjinta tana min sannu saiga Baffa shima ya shigo d'akin ya Khamis da Ya Aliyu biye dashi. "Fulani me nake ji Marwah na cewa? Hassana babu lfy?" "Wlh ka ganta nan Baffa jikin nata ya yi zafi sosai " "To ko asibiti zamu kaita ne" Ina jin sunce asibiti na rushe da kuka don na tsani asibiti. Ya Aliyu ya k'araso ya janye ni daga jikin Mamee ya mayar nashi ya kwantar yana rarrashi. Damuwar da nagani kwance kan fuskar su sai naji wani irin dad'i ya rufeni rabon da naga kulawa irin haka harna manta. Aikuwa na lafe k'irjinsa ina maida ajiyar zuciya sai lallabani suke. Ya Khamis ya fice da sauri sai gashi ya dawo da plate shak'e da Indomie taji kayan lambu Marwah biye dashi da flask na shayi. Baffa ya karba da sauri ya zauna kusa dani yana bani da lallami sai shagwaɓa nake ina gamawa Ya Khamis ya bani panadol nasha ban jimaba barci ya kwashe ni jikin ya Aliyu. Bani na farka ba sai wajen azahar na farka garau dani amma saboda lallabata da ake yi na narke komai sai anyi min. Kwana biyu ina ciwon karya in ance za'a je asibiti na saka kuka dole sai magani Baffa yasa suke karb'owa daga chemist shima sai ya Aliyu ya yi da gaske nake sha. Yau Juma’a wajen la'asar ina kwance a d'aki tunani yamin yawa saiga Harira kaman wadda aka wullo. Naji dad'i zuwantan kuwa don ina ta burin naga na cika mata burin ta. Yanda ta shigo cikin farin ciki ta fad'o kan gadon da nake tana dariya. Miƙewa nayi zaune na jingina da filo ina kallonta nace "Wai farin cikin me ki ke haka ne?" Y'ar dariya tayi tana gyara zama Marwah ta shigo d'auke da jug da kofi ta ajiye gefen ta kafin ta samu guri kusa dani ta zauna suna gaisawa da Harira. Ruwan data ajiye ta d'auka tasha

Chapter 3 of 9