Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
cikin wani irin d'acin rai da fargaban abunda zan tarar kuma a gida... ๐“‰๐’ฝโ„ฏ ๐’ป๐’พ๐“‡๐“‡โ„ฏ & ๐’พ๐’ธโ„ฏ. เผ„ZUBAR HAWAYEเผ„ ๐’œษฑฮฑศฅฮนษณษ  โ˜…'โ˜… ษฏษพฮนฦšาฝษพส‚ ฯฯƒษพฯ…ษฑ ( ๐’œ, โ˜… ส‚ฦšฮฑษพ'ส‚ ,ษฏ โ˜… ฯ) ๐—”๐˜€๐—ต๐—ฎ๐—ป๐˜๐˜† ๐—น๐—ผ๐˜ƒ๐—ฒ. "--๐‘ค๐‘’ ๐‘‘๐‘œ ๐‘›๐‘œ๐‘ก ๐‘โ„Ž๐‘œ๐‘œ๐‘ ๐‘’ ๐‘คโ„Ž๐‘œ ๐‘ค๐‘’ ๐‘™๐‘œ๐‘ฃ๐‘’,๐‘๐‘ข๐‘ก ๐‘Ÿ๐‘Ž๐‘กโ„Ž๐‘’๐‘Ÿ ๐‘œ๐‘ข๐‘Ÿ ๐‘ ๐‘œ๐‘ข๐‘™๐‘  ๐‘โ„Ž๐‘œ๐‘œ๐‘ ๐‘’ ๐‘“๐‘œ๐‘Ÿ ๐‘ข๐‘ ." VOL/36-40 Ban k'ara shiga tashin hankali ba saida naga mun shiga layin mu na hango Baffa da ya Khamis zaune k'ofar gida kan tabarma suna karatu. Wani irin birki ya Aliyu yaja ya fice daga motar da wani irin zafin rai ya zagayo inda nake nayi saurin matsawa na k'ank'ame jiki ina wani irin kuka mai Ban tausayi. Da mamaki sosai Baffa da ya Khamis ke kallon ya Aliyu daya fito daga cikin motar ya fisgo ni da karfi ya yi waje dani na fad'o k'asa tim. A hanzarce suka miฦ™e gaba d'ayan su Baffa ya tawo cikin sauri yana "Subhanallahi, Aliyu lafiyar ka lau kuwa ka ke janta haka a k'asa kaman mara hankali?" Kota kan Baffa bai biba ya yi cikin gida dani Baffa na k'ok'arin riฦ™e ni amma da yake k'arfin ba d'aya ba fuu ya yi ciki dani ya wurgar nan tsakar gida .Mamee da Marwah na zaune kan tabarma suna gyara Zogale. Ban iya tashi ba na kudundune jiki guri d'aya ina kuka sosai kaman raina zai fita. Ina jin Baffa ya daka matsawa cikin b'acin rai "Kar ka kuskura ka tab'ata da wannan belt din. Kana hauka ne?" Wani irin huci ya Aliyu ya yi ya kaiwa bango naushi .ya fara magana da matsanancin b'acin rai. Ya Aliyu na daga cikin irin mazajen nan da idan ransu ya yi koluwar b'aci za kaga jikinsu na rawa suna magana kaman masu in'ina. " Baff...Baff. k..k.." Ya Khamis ya yi saurin matsowa inda yake ya dafa k'afad'ar sa yana d'an buga bayan sa. Ajiyar zuciya Baffa yaja yana k'arewa Sanaah dake kwance kallo . Sai yanzu ya fara gane dalilin fushin Aliyu. Salati kawai yake cikin ransa Allah karya tabbatar masa da abunda yake zargi. Maida hankali kan Mamee ya yi da itama ta zubawa Sanaah d'in ido bata ko kiftawa Marwah dake gefe sai matsar kwalla take. Wani Numfashin ya k'ara ja ya maida hankali kan Aliyu da jikin sa ke rawa kaman mazari "Kwantar da hankalin ka Aliyu ka gayamin mene ya faru. Ja numfashi in and out " Kaman yanda Baffa yace yaja numfashi mai k'arfi ya fesar da Jan ido ya kwashe duk abunda ya faru ya gaya musu. Bai Ida zancen ba naji sheshshek'ar kukan Mamee hankalina ya yi masifar tashi da rawar jiki na rarrafa inda take ina k'ok'arin kama kafuwanta ta wani hankad'ani na zube k'asa ina gunjin kuka sosai nace "Don Allah Mamee kiyi hak'uri wlh banyi abunda ku ke zargi ba. Tsautsayine ya kaini amma wlh tunda aka rabamu bamu sake had'uwa da ita sai yau da ranan nan don Allah kuyi hak'uri " Na juya gurin Baffa dake tsaye ya kasa cewa komai. Kai ya girgiza jiki a matuฦ™ar sanyaye yace "Kin tabbata Sanaah? Idan har nayi bincike na gane abunda ki ke cewa K'arya ne zaki fuskanci hukunci mai tsanani gurina .za kiga b'acin raina da baki tab'a gani ba" A hanzarce na d'aga kai na ina sharar hawaye. Kai ya k'ara jinjinawa ya juya kan Mamee dake kuka mara sauti. "Kiyi hak'uri Fulani mu cigaba da yi mata Addu'a. Kukan ki a gurinta yanzu masifa ne . Marwah " "Na'am Baffa " Ta amsa da shak'akk'iyar murya. "Tashi kije ki deb'omin dukkanin kananan kaya da take sawa ki kawomin" Da sauri ta tashi ta shige d'akin tsakar gidan ya d'auki shiru sai gunjin kuka na dake tashi. Him guda ta fito da kayan nawa cikin jaka ta ajiye gaban Baffa. "Sannu Marwa. Khamisu d'auki kayan nan kaje kayi sadaka dasu." "To Baffa " Ya d'auki kayan ya fice. Baffa ya juya kan Ya Aliyu dake zuba huci. "Kai kuma Aliyu kaje kasuwa ka sami mata yadi na hijabai a dinka kaman uku ko hudu ka had'u mata da riguna dogaye da zata dinga sawa kafin Allah ya hore ayi na musu d'inki na mutunci" Saida ya fesar da numfashi mai zafi ya amsa da " to Baffa " ya juya ya fice. Shima Baffa d'aki ya yi yana cewa "Fulani Bismillah" Farantin ta ajiye ta miฦ™e tayi d'akin bata k'ara kallona ba na bita da kallo harta b'ace. Majina naja ina k'ok'arin sauke idona k'asa ya fad'a cikin na Marwah dake tsaye gefena cikin damuwa. Wani irin abu naji ya daki k'irjina. Matsanancin haushin ta ya rufeni kaman wadda tayimin laifi nayi saurin d'auke kai ina k'ok'arin tashi amma na kasa don gaba d'aya jikina ke azabar ciwo na dukan da ya Aliyu ya yi min ga Jana a k'asa daya dinga yi. Wani yunฦ™urin na kara na koma d'abar na zauna na runtse ido. Ji kawai nayi Marwah na k'ok'arin kamani na hankad'eta da zafin rai tayi baya tagaga zata fad'i tayi saurin dafe bango tana kallona cikin matsanancin mamaki. Duk da ciwon da nake ji bai hanani Jan mugun tsaki ba na rarrafa na shige d'aki kai tsaye na haye gado na kwanta na rufe jiki saboda zazzabi da naji yana k'ok'arin rufeni. โ™ก๏ธŽโ™ก๏ธŽโ™ก๏ธŽ Kallon ta yake zaune gefen sa tana share hawaye lokaci zuwa lokaci .murmushi ya yi cike da damuwa yaja ta ya rungume yana cewa "Haba Fulani kukan na mene? Sanaah bata buฦ™atar kuka ko duka bare zagi. Addu'a shine take buฦ™ata. Dama shi ubangiji ta ko wace hanya yana jarraba bayinsa. Wani zai jarabesa da dukiya, talauci,y'a y'a. Ko kuma iyaye har ma da makoci. Ki cigaba dayi mata Addu'a bana son naga kina kuka kan wannan abun inshaAllahu komai yazo k'arshe mu cigaba da sa ido sosai kan tarbiyar su ." Da wannan kalamai ya tausheshe ta har tayi shiru. โ™ก๏ธŽโ™ก๏ธŽโ™ก๏ธŽ Duk yanda naso nayi barci kasawa nayi don sosai nake jin jiki sai juyi kawai da nake kan gado. "Ko na had'a miki ruwa kiyi wanka?" Banza nayi mata kaman da dutse take magana ina ji taja ajiyar zuciya tana k'ok'arin ficewa wayar ta tahau ring ta dawo ta dauka kan mudubi . Yunฦ™urawa nayi da sauri na miฦ™e zaune ina kallonta ta kara wayar a kunne tayi sallama da y'ar k'aramar murya. Murmushi ta saki a kunya ta sauke kanta kasa wani matsanancin kishi ya rufeni na zuba mata ido k'irjina na harbawa da gudu. Kallonta na cigaba da yi harta gama wayan ta mayar kan mudubi ta ajiye ta fice . Saboda bak'in ciki da kishi hawayen dana samu suka d'an tsagaita suka cigaba da zubowa da gudu kaman an buษ—e fanfo. Anya kuwa zan iya bari Marwah ta Auri Deen? .idan nayi haka nayiwa kaina Adalci. Bansan sanda na kamu da soyayyar sa haka ba da nake ji idan ban mallake Shiba zan iya mutuwa . Why? Why zuciyata ta kamu da son masu wani , Kuma y'ar uwata, Why?. Shar hawaye suka k'ara biyo fuskata hak'ika shid'in ya zama silah ta ZUBAR HAWAYE na da bana jin zan daina sai ranan dana koma ga mahaliccina don tabbas nasan mutuwa zanyi matsawar ya Auri Marwah ba niba. ๐“‰๐’ฝโ„ฏ ๐’ป๐’พ๐“‡๐“‡โ„ฏ & ๐’พ๐’ธโ„ฏ. เผ„ZUBAR HAWAYEเผ„ ๐’œษฑฮฑศฅฮนษณษ  โ˜…'โ˜… ษฏษพฮนฦšาฝษพส‚ ฯฯƒษพฯ…ษฑ ( ๐’œ, โ˜… ส‚ฦšฮฑษพ'ส‚ ,ษฏ โ˜… ฯ) ๐—”๐˜€๐—ต๐—ฎ๐—ป๐˜๐˜† ๐—น๐—ผ๐˜ƒ๐—ฒ. "-- ๐‘†๐‘œ๐‘š๐‘’ times ๐‘– ๐‘ค๐‘–๐‘ โ„Ž ๐‘– โ„Ž๐‘Ž๐‘‘ ๐‘›๐‘’๐‘ฃ๐‘’๐‘Ÿ ๐‘š๐‘’๐‘ก ๐‘ฆ๐‘œ๐‘ข. ๐‘‡โ„Ž๐‘’๐‘› ๐‘กโ„Ž๐‘’๐‘Ÿ๐‘’ ๐‘ค๐‘–๐‘™๐‘™ ๐‘๐‘’ ๐‘›๐‘œ ๐‘›๐‘’๐‘’๐‘‘ ๐‘ก๐‘œ ๐‘–๐‘š๐‘๐‘Ÿ๐‘’๐‘ ๐‘  ๐‘ฆ๐‘œ๐‘ข. - ๐‘๐‘œ ๐‘›๐‘’๐‘’๐‘‘ ๐‘ก๐‘œ ๐‘ค๐‘Ž๐‘›๐‘ก ๐‘ฆ๐‘œ๐‘ข. - ๐‘๐‘œ ๐‘›๐‘’๐‘’๐‘‘ ๐‘ก๐‘œ ๐‘™๐‘œ๐‘ฃ๐‘’ ๐‘ฆ๐‘œ๐‘ข. - ๐‘๐‘œ ๐‘›๐‘’๐‘’๐‘‘ ๐‘ก๐‘œ ๐‘๐‘Ÿ๐‘ฆ ๐‘œ๐‘ฃ๐‘’๐‘Ÿ ๐‘ฆ๐‘œ๐‘ข." VOL/41-45 Saida naci kuka na2 koshi sannan barcinl b'arawo ya d'auke ni. Ban farka ba sai wajejen magriba da shima Marwah ne ta tashe ni nayi sallah. Da kyar na miฦ™e jikina duk ya yi tsami da d'an dingishi na fito na shege banษ—aki don na d'an watsa. Saida na shiga ne naga ashe tashin hankalin dana shiga yasa bak'ona zuwa da wuri shida nake tsammanin sa nan da kwana biyar gaba. Wanka kawai nayi na fito kafin na shiga d'aki Mamee ta fito daga kitchen riฦ™e da kula zata shiga d'akin Baffa. Da sauri na matsa zan kama mata ta jefeni da wani mugun kallo ta wuce ta barni nan a tsaye cikin mutuwar jiki hawaye tab cikin idona. D'aki na shige ina tunanin har yanzu Mamee bata sauka ba. Marwah na samu bakin mudubi tana shafa hoda ta shirya cikin less d'inkin doguwar riga ta d'auka mayafi ta nad'a a kanta. Sosai tayi kyau duk da ba wata kwalliya tayi ba hoda ce kawai da man leb'e tasa. Kasa jurewa nayi ina k'ok'arin zama kan gado nace "Ina zaki?" Saida ta gama nad'a mayafin sannan tace min "Deen.. yace yana hanya" Wani dum k'irjina ya buga duk wani ciwo da nake ji na nemeshi na rasa na zuba mata ido tana fesa turare harta gama ta sunkuya ta jawo flat takarmi ta saka. Kwala mata kira Mamee tayi ta amsa da sauri ta fice na bita da kallo cikin matsanancin kishi. Dafe k'irjina nayi da naji yana barazanar tarwatsewa na tashi da sauri na dauko doguwar riga cikin kayanta da mayafi na saka nima na fito daidai Ya Aliyu na shigowa cikin k'ananan kaya. Mugun kallo ya watsamin nayi saurin rabewa gefe ya wuce d'akin Mamee. Yana shiga Marwah ta fito d'auke da Teri da kayan abinci. tana ganina tace "Yauwa zoki kamamin don Allah " Ban musa ba na shiga d'akin Mamee da y'ar sallama. Kan dadduma na sami Mamee da charbi a hannu Ya Aliyu na zaune kan durowa ta gado . Ya Aliyu ne ya amsa min sallaman Ciki-ciki fuska a tamke Mamee kuwa kurar data d'eboni bata kallaba. Jikina ya kara sanyi na sunkya nan bakin kofa na d'auko jug dana gani da lemo kan faranti nayi waje dashi. K'ofar falon namu na tsaya riฦ™e da farantin k'irjina na cigaba da bugawa kaman zai tarwatse. Inda nake nan tsaye ina jin daddadan Kamshin turaren sa dake ta ratsowa ta cikin falon hakan ya tabbatar min ya shigo ta can k'ofar relar dake waje. Jiki na rawa na d'aga labule na shiga da y'ar siririyar sallama. Bugun da k'irjina ya yi sanda nayi arba dashi abun bazai kwantuba. Manya kaya ne ajiki sa, Shadda dakakkiya fara kal da ita d'inki tazarce kanshi bak'ar hula ce data zauna kan dogon gashin sa dake tufke tsakiyar kansa. Hannun sa d'aure da wani dankareran agogo silver sai shek'i yake. Jiri ne ya kwasheni na nemi fad'uwa sanda ya d'ago wanna silver eyes nashi suka fad'a cikin nawa. Da hanzari Marwah ta taso ta kama kwanan tana cewa. "Yi hankali kar ki fad'i " Ajiye tiren tayi wajen kafafun sa ta riฦ™e hannuna dake rawa. "Sanaah ga Deen, Deen ,Sanaah my sister " Kallon tsana daya watsamin yasa jikina ya yi wani irin sanyi kaman an watsamin k'ank'ara na sunkuyar da kai k'asa. Magana ya yi babu wani annuri kan fuskarsa "Yes ,we have meet" Kaman zatayi Magana sai kuma ta fasa ina ga ta tuna abunda ya faru d'azu. Murmushi tayi ta kalleni kome ta tuna sai cewa tayi "Yauwa ina zuwa." Kafin nace wani abu ta juya ta fice da sauri ta barni nan tsaye. Jiki babu kwari na matsa na zauna kan kujera dake fuskantarsa. Shiru dakin ya d'auka sai bugun zuciyata dake harbawa kaman zata fito fili. Yawu na had'iye na d'ago a hankali don na k'ara ganin kyakkyawar fuskarsa. Karaf idona ya fad'a cikin nasa dakemin kallo na tsantsan kiyayya amma duk da haka na kasa jin haushin sa saina wani irin farin ciki dana tsinci kaina a ciki yau gani ga muradin zuciyata. Wani irin 'Tsk" sound ne ya fito daga bakinsa kafin naji yace da boring voice. "You are so pathetic" Kar kusu kuga zuciyata lokacin na zuba masa manyan brown eyes d'ina da hawaye suka fara taruwa a ciki. Bai damu da hakan ba ya d'an yunฦ™uro daga jikin kujerar da yake jingine ya had'e kyawawan yatsun sa guri d'aya ya d'an karkata kai gefe yana kallona kaman mai karantar abu. Sai naga ya saki wani mugun smirk daya nunamin dimples nashi. Wayyo Allah na fad'ar kyawun sa abun b'ata bakine. "You know ,i can read you like an open book " Yawu na had'iye ido waje ina kallon sa a tsorace. Nashiga uku me yake nufi da yana iya karantata badai ya san abunda zuciyata ke ciki game dashi ba? Kaman jira yake kuwa ya bani amsa da wani irin voice kaman wanda aka durawa kashi a baki. "I can see you have feelings for me. I can see how your so inlove with me, because your not very good at hiding it. So na baki shawara tun wuri throw this feelings da ki ke min a shara. Saboda nan sukafi dacewa. A garbage .their is no way in he'll i will love the likes of you bare ke kan ki. So do your self a favour and stop this nonsense. I hate you and everything about you saboda ke d'in selfish mutum ce dake son kan ki. Kinsan ina son sister naki but you dare to fall in love with me? " Tunda ya fara maganan hawaye kebin kuncina kaman an buษ—e fanfo zuciyata na wani iri ciwo. Duk kalma d'aya idan ya furta kaman dagger yasa yake stabbing d'ina a kahon zuci. Maganganun sa sun mun tsauri. Mene laifina? Bani na d'orawa kaina sanshi ba Allah ya jarrabeni da soyayyar sa, amma yana cemin selfish saboda ina son shi?. Mene aibuna? Don Allah ku gayamin mene laifina? . Yunฦ™urawa nayi don na tashi, jiri ya kwashe ni na koma na zauna ,kukan dake neman kwacemin nayi saurin toshe baki da sauri na miฦ™e da ragowar k'arfin daya ragemin nayi waje ina jin idonsa dake d'auke da tsantsan kiyayya a kaina har na fice. Allah ya taimake ni babu kowa tsakar gida nayi d'aki cikin azama. A guje na fad'a kan gado na rushe da matsanancin kuka mara gunji dafe da k'irjina da nake ji kaman zai tarwatse. 'Me yasa Allah ya jarrabeni da son mutumin daya tsaneni yak'i jinina? wane gagarumin laifi na aikata haka? 'Kul Sanaah ki ka kara furta haka ki kasance mutum mai tawakali da neman gafarar Ubangiji. Hak'ika Allah baya d'orawa bayansi abunda bazai iya d'auka ba. Ki dage da Addu'a Allah ya kawo miki mafita cikin gaggawa. ' Numfashi naja ina jin wani iri ciwo da k'irjin na yake. Zuciyata ta k'ara cewa 'Tabbas a yanzu babu abunda zakiyi da zai saukar miki da nutsuwa daya wuce karatun Qur'ani. Ina mai baki shawara ki karanta ko aya biyu ne . Da yardar Allah zaki samu nutsuwar zuciya.' Kai na jinjina na share hawayen dake gudu kan fuskata na miฦ™e da sauri na fito dan d'aura alwala. Takalmin Marwah dana hango k'ofar Falon naji wani abu ya k'ara tasomin nayi saurin wucewa banษ—aki. Ruwa na kama na fito ina idar da Alwala Mamee ta fito daga d'aki za tayi kitchen riฦ™e da flask. Da sauri na tashi na karb'a banyi tunanin zata bani ba ta miฦ™omin na wuce na ajiye ta juya ta koma d'aki nima nayi d'akin da nauyin k'irji. Guri na samu na zauna na fara tilawa karatunda ka a hankali cikin kira'a ta mai masifar dad'i kaman mai rera wak'a. Nida Marwah Allah ya bamu murya mai masifar dad'i idan muna karatu kace wasu larabawa ne dan ma ni ban cika yiba saboda shirita dana sa a gaba ba. Cikin ikon Allah kuwa na fara samun nutsuwar zuciya. Hak'ika babu abunda yafi k'aratun Qur'ani dad'i. โ™ก๏ธŽโ™ก๏ธŽโ™ก๏ธŽ Kofin dake hannun sa data zuba masa zubo mai shegen dad'i ya k'ara d'agawa ya kurba kafin ya ajiye kan tiren dake gefensa idon sa kur a kanta baya ko kyiftawa. Tunda ta zauna kanta ke katsa tana wasa da gefen mayafin ta. Murmushi ya yi mai k'ayatarwa yana jin wani irin sonta da bazai iya misaltuwa ba cikin ransa. Wannan kunyar tata na d'aya daga ciki abunda ya sashi fad'awa kogin santa bai farga ba. Dukkanin wani abu da yake so tattare da mace ta had'a. Kyau, ilimi, kunya, addini, uwa ,uba tana da body da yake so gurin mace gata kuma yarinya d'anya sharaf. Shi yasa ya yi mamaki da yaga y'ar uwarta ba haka take ba. Ita d'in ta kasance albasa da batayi ruwa ba. Halayen ta abun kyama ne a gurin sa tun daga ranan da ya fara ganinta baiyi tunanin kuma zai fad'a soyayya da Marwah ba . Ganin farko da ya yi mata yasan cewa ya fad'a tsamo-tsamo kogin sonta. kalman nan da ake cewa LOVE AT FIRST SIGHT shi yasa yana fitowa bai b'ata lokaci ba ya gayama Aliyu shi ya samu matar aure kuma alhamdulillah baiyi zaton zata karb'i soyayyar sa ba nan take ashe itama dai kaman shi ta kamu da son shi LOVE AT FIRST SIGHT . Abunda baiyi zato ba shine itama y'ar Uwarta ta fad'a soyayyar sa da baima san tana yiba sai yau daya karance ta tsab. Numfashi yaja a hankali ya kirata da wata irin murya mai kashe jiki "Baby " Cikin matsanancin kunya ta d'ago da jan kumatu ta watsa masa manyan idonta. Wani Numfashin ya k'araja suna kallon juna a hankali yace "Say something mana. Nace Dad d'ina zaizo jibi .Are you happy zaki zama tawa nan da d'an wani lokaci?" Maimakon ta bashi amsa sai ta tashi a guje ta fice ya bita da wani irin kallo yana ji kaman ya tashi ya kamato ya rungume. All his life ya yi rayuwa da mata iri-iri . Mata suna throwing kansu gurin shi don samun soyayyar sa bai tab'a tunanin zaiyi soyayya da yarinya k'arama kaman Marwah ba ,to top it all yarinya y'ar Nigeria daya raina do da cewa mahaifin sa cikakken Bahaushene amma shi Sam matan hausawa basa cikin agenda nashi. Kai bama su kad'ai ba shi soyayya a gurin sa yana ganin shirme ne da b'ata lokaci. Bashi da time d'in ta sai kuma tayi masa shigar sauri, dalilin da yasa ya iya karantar Sanaah. Don yaga wannan fire works kwayar idonta kaman yanda ya tsinci kansa lokacin daya fara arba da Marwah. Zobon ya d'aga ya kurbe ragowar kafin ya tashi ya fito. ๐“‰๐’ฝโ„ฏ ๐’ป๐’พ๐“‡๐“‡โ„ฏ & ๐’พ๐’ธโ„ฏ. เผ„ZUBAR HAWAYEเผ„ ๐’œษฑฮฑศฅฮนษณษ  โ˜…'โ˜… ษฏษพฮนฦšาฝษพส‚ ฯฯƒษพฯ…ษฑ ( ๐’œ, โ˜… ส‚ฦšฮฑษพ'ส‚ ,ษฏ โ˜… ฯ) ๐—”๐˜€๐—ต๐—ฎ๐—ป๐˜๐˜† ๐—น๐—ผ๐˜ƒ๐—ฒ. "--๐ฟ๐‘œ๐‘ฃ๐‘’ ๐‘–๐‘  ๐‘กโ„Ž๐‘Ž๐‘ก ๐‘๐‘œ๐‘›๐‘‘๐‘–๐‘ก๐‘–๐‘œ๐‘› ๐‘–๐‘› ๐‘คโ„Ž๐‘–๐‘โ„Ž ๐‘กโ„Ž๐‘’ โ„Ž๐‘Ž๐‘๐‘๐‘–๐‘›๐‘’๐‘ ๐‘  ๐‘œ๐‘“ ๐‘Ž๐‘›๐‘œ๐‘กโ„Ž๐‘’๐‘Ÿ ๐‘๐‘’๐‘Ÿ๐‘ ๐‘œ๐‘› ๐‘–๐‘  ๐‘’๐‘ ๐‘ ๐‘’๐‘›๐‘ก๐‘–๐‘Ž๐‘™ ๐‘ก๐‘œ ๐‘ฆ๐‘œ๐‘ข๐‘Ÿ ๐‘œ๐‘ค๐‘› ." VOL/46-50. Washegari haka na tashi babu wani kuzari. Duk lokacin dana kalli Marwah sai naji wani abu mai nauyi ya tokareni a k'irji. Wunin ranan haka nayi sa babu k'arfi kalaman Deen namin yawo a kunne duk lokacin dana kebe ni d'aya. Bayan haka kuma ga fushin da Mamee take dani dan koda muka je gaisheta da safe bata amsa gaisuwa ta ba sai Baffa ne ya amsa cikin rashin jindaษ—in abunda Mamee tayi. Muna fitowa naji yana mata magana k'asa-k'asa nasan kuma saboda abunda tayi ne yake mata nasiha. Ko a makaranta bana iya fuskantar komai tun daga ta bokon harta islamiya. Marwah da Harira babu irin tambaya da basuyi min ba amma na kasa cewa komai. Ji nake da zarar na buษ—e bakina zan iya fashewa da kuka hakan kuma zaisa tabbas su gane ina cikin damuwa. Nasan halin Marwah tsab zata sani a gaba sai na gaya mata abunda ya sani cikin damuwa idan nak'i kuma taje ta gayawa Mamee dole sai na furta abunda nake b'oyewa. Da dai suka ga bazance komai ba dole suka hak'ura suka kyaleni . Da muka dawo gida babu laifi Mamee ta d'an sakemin ba kaman da safe ba nasan kuma maganan Baffa ne yasa hakan. Ya Aliyu dai har yanzu fushi yake dani sosai. Koda dare ya yi muna gama cin abinci na miฦ™e na shige banษ—aki na tsabtace jikina na fito nayi d'aki. Kan gado na samu Marwah riฦ™e da hutunan da nake ta b'oyewa. Ina shiga ta d'ago ta zubamin ido alamun tambaya da mamaki k'arara kwance kan fuskatar. Da sauri na k'arasa na warce su daga hannun ta bance komai ba na fara maida su cikin jaka raina a mugun b'ace. Bana san irin wannan bincike da takemin. Jaka na tura bance komai ba fuskata a had'e. Batace komai ba saida na gama sasu cikin jaka taja numfashi tana magana a hankali. "Yanzu Sanaah menene wannan da ki ke shirin aikatawa? Yanzu na fuskanci maganan da Harira tayi take cewa ko kece sanadin da yasa Zubair fasa auren Khadija?. Ki gayamin gaskiya kina da hannu a ciki?" Ban bata amsa ba na juya zanyi wajen kwaba ta taso da sauri ta riฦ™e hab'a ta juyo ni ina fuskantar ta. Da d'an ihu tace "Ki gayamin dasa hannun ki a ciki?" Wani irin red nagani na turata da k'arfi tayi taga taga zata fad'i tayi saurin dafe gafen gado ta tsaya da kyau. Da wani irin fad'a nace "Idan ma da saka hannun nawa ina ruwan ki bare kuma nace bansan komai ba. Ban kai ga aikata ba asirin nata ya karye. Kuma koda ace nice sanadin rushewar alak'ar tasu bazanyi dana sani abunda na aikata ba domin ta cancanci haka" Na k'arasa maganan ina wani irin huci. Haushin ta da kishin ta ya rufeni lokaci d'aya. Ido ta zubamin muka zubawa juna ido kafin ta k'ara jan ajiyar zuciya ta matso kusa dani muna fuskantar juna. "Sanaah me yasa bakya tunanin kema wata rana Allah zai iya jarrabaki da son maso wani?. Kin manta shifa so halitta ne jikin d'an Adam. Raine dashi kaman yanda ki ke

Chapter 5 of 9