Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
numfashi. Akan so babu abunda baza ki iya aikatawa ba. Yana kai mutum halaka ga wanda ya kasacin jarabawar sa kenan. Ya kasa hak'uri da juriya. Yanzu da ace kin yad'a wannan hoton na gaibu kina tunanin Allah zai barki da sharrin da ki ka kulla?" Duk cikin maganganun ta babu abunda na ji sai 'Allah zai iya jarrabaki da son maso wani'. Hannun Marwah dana gani kan fuskata tana sharemin hawaye yasa na farga ashe kuka nake mai ciwo. Gaba d'aya kalaman ta sai suka sa nake jin kaman tasan halin da nake ciki. Rungume ni tayi itama tana kuka sosai babu mai rarrashin wani. Tsawon minti biyu muka dauƙa a haka kafin na janye a hankali ina share hawaye. Jakata na buɗe na d'auko kuɗin nan da Deen ya jefeni dashi na miƙa mata da jan ido. Da mamaki take kallona kafin nayi magana da shak'akk'iyar murya nace "Deen, Deen ne mutumin da muka had'u ya jefeni da kuɗi ranan daya fara zuwa. Ki mayar masa da kuɗin sa" Da mamaki sosai kan fuskarta take juya kuɗin dake hannun ta bakin ta na motsi amma ta kasa cewa komai. Nima ban jira tace wani abu ba na haye gado na juya mata baya. Ta jima a tsaye kafin naji motsin ta ta fice daga d'akin na runtse ido ina sauraran bugun da zuciyata take da k'arfi. Ina nan kwance wajen minti biyar naji motsinta ta dawo d'akin ta gama abunda za tayi ta hayo gadon ta kwanta tana Addu'a. Bata jima ba da kwanciya barci ya kwashe ta ni kuwa ina nan na kasa barcin sai aikin tunani da nake wanda ya k'aramin ciwon kai. Na jima ido na biyu na kasa runtsa har wajejen biyu na dare kafin da kyar barcin ya kwashe ni da matsanancin zazzabi a jikina da ciwon kai. To washe gari saboda barcin da ban samu ba ina yin sallan Asuba na fara k'ok'arin komawa na kwanta Mamee ta shigo d'akin namu sanye da hijabi da carbi a hannun ta tana ja. Da sauri na miƙe zaune muka had'a baki nida Marwah muna gaishe ta. Ido ta zuba mana na d'an lokaci tana kallon mu ta hasken fitila daya haske d'akin tamu ta sola saboda rashin wuta. Da kulawa kan fuskar ta amsa da "Lfy lau alhamdulillah. Kun tashi lfy?" "Sanaah meke damun ki naga idon ki a kumbure sunyi jaa haka?" Gabana ya yanke ya faɗi nayi saurin cewa "Wlh Mamee jiya ne kawai na kwanta da ciwon kai" "To garin ya kin kwana da ciwo bakiyi magana an samo miki magani ba?" Da sauri nace "ai naji sauki yanzu Mamee" Kai ta jinjina alamun gamsuwa da magana ta amma duk da haka tace "Zansa Khamis ya samo miki panadol idan garin ya waye .yanzu idan kun gama ku fito ku taya ni aiki don yau muna da bak'i " Fad'an wannan kalman ta Mamee sai naga Marwah ta sunkuyar da kai katsa alamun kunya. Mamee bata k'ara cewa komai ba ta juya ta fice daga d'akin na bita da kallo ina wasi-wasi cikin raina. Wane bak'i ne haka zamuyi kuma?. Da saurin na juya kan Marwah na tambaye ta su waye zasu zo. k'afin na kaiga tambayar tata ta ajiye qur'anin dake hannun ta ta miƙe da sauri ta fice daga d'akin. Ajiyar zuciya na sauke nima na miƙe na fito ina d'aura d'an kwali kan doguwar rigar dake jikina ta barci. Kayan miya ne baje a tsakar gidan namu Marwah har ta fara gyarawa. Matsawa nayi nima na zauna na saka hannu muka gyara kayan miyar nan tsab muka wanke muka zuba cikin bokiti . Mamee ta fito daga kitchen riƙe da kullin shinkafa daya tashi sosai ta ajiye gefe tana cewa na d'auko mata kirifoti a soro . Muna k'ok'arin doro wainar shinkafa saiga Baffa da ya Aliyu da da kayan nama da lemoka. Haka muka hada gaba daya sukayi. Kafin shadaya na safe mun gama komai mun zuba cikin flask mun kai falo mun jera su. Muna gamawa Marwah tayi d'aki a hanzarce kaman mai tsoron wani zai shigo ya kamata. Nima binta nayi d'akin na sameta tana k'ok'arin kwanciya. Gaba d'aya kaina ya d'aure na rasa me zan fassara yanayin ta. Sai abu take kaman mara gaskiya da take tsoron asirin ta ya tono. Guri nima na samu na zauna muka cigaba da zama kaman kurame . Ni ina aikin tunani ita kuma tana danna waya daga bisani ma ta ajiye wayar ta kwanta kaman mai barci. Duk sakan d'aya idan ya haura bugun k'irjina na karuwa. Haka na dafe k'irjin nawa ina jin yanda yake matsanancin bugawa kaman zuciyata zata fito fili. Wajejen k'arfe biyu saiga hayaniyar mutane sun fara sakkowa daga masallaci na juma'a da yake yau ranan juma'a ne. Abunda yafi d'aure min kai kaman k'ofar gidan mu suke yada zango Maimakon kowa ya wuce gidansa. Hayaniyar tayi yawa sosai da tasa na kasa jurewa na fito tsakar gida na kasa kunne ko Allah zaisa naji abunda ke faruwa k'ofar gidan namu. Duk yanda na kasa kunne na kasa istar komai. Don bakuna ne sunyi yawa da sam baza ka gane me suke cewa ba. Shigowar Baffa da Ya Aliyu cikin manyan kaya yasamin wani matsanancin fad'uwar gaba duk da ba yau ne na fara ganin su cikin manya kaya ba. Duk ranan juma'a Baffa na saka manyan kaya idan zaije masallaci. Kwalin dake hannun ya Aliyu na alwala da goro shine abunda ya ja hankali na. Fuskar Baffa nake kallo dake data cika da annuri sai murmushi yake. Yana ganina ya k'ara girman murmushin sa ya matso ya kama hannuna mukayi falo yana kiran Mamee da Marwah. Kusa da kafafuwan sa na zauna ina kallon ya Aliyu data ajiye kwalin alawa da dabino ya fice daga falon. Yana fita Mamee da Marwah suna sawo kai. Kusa da Baffa Mamee ta zauna Marwah kuma ta samu guri kusa dani ta zauna. Saida ya bimu da kallo d'aya bayan d'aya sannan ya yu murmushin mai k'ayatarwa ya fara da Salatin Annabi (S.A.W). Kafin yace " to Alhamdulillahi nasan dukkanin ku kuna neman k'arin bayani. Abunda ya faru shine Fulani " A sanyaye Mamee tace "Na'am " Murmushi Baffa ya k'ara yi " yau burin ki na son ganin ya'yan ki d'akin mazajen su ya fara cika. A yau d'innan bayan sakkowa daga masallaci an d'aura Auren Marwah da Kamaludeen. Kinsan ance kana naka ne Alla na nashi. Koda wasa ban tab'a tunanin cewa da hannuna yau zan karb'i auren Marwah ba. Domin munyi ne kan cewa zai turo magabatan sa sai a tsaida rana. To Allah bai nufin hakan ba saboda hukunci irin nashi. Mahaifin Kamaludeen dattijon kirki, dattijon arziƙi ya nemi Alfarma idan har na amince a yau d'innan, wannan rana mai Albarka a d'aura auren kaman yanda shi Kamalun ke buri. Yace koma mene daga baya sai ayi. Duba da irin kima da mutunci irin na wannan mutumin mai tsananin girma da mukami yana neman Alfarma saboda haka na amince. An d'aura Auren Marwah da Deen. Idan da akwai wani abuda za kuyi sai ku fara shiri" Khamis ya shigo da y'ar jaka ya miƙawa Baffa. Kuɗi ya fito dasu rafa biyu y'an dubu daidai guda biyu . "Wannan shine sadakin ta. Wannan kuma" Ya k'ara fito da wasu rafar guda uku "Wannan kuma yace a ba ku saboda ko zakuyi wani abu. Ina mai shawartar ku idan akwai abunda zakuyi sai ku hanzarta yinsa. InshaAllahu nan da sati zaki bisa ku tafi can gurin aikin sa" Tun sanda ya furta an d'aura auren komai ya kwance min bana jin komai sai shuuu cikin kunne na. Wani irin bugu k'irjina yake kaman zuciyata zata tarwatse. Har Baffa ya gama bayani bana iya fuskantar komai saida Marwah ta miƙe ta fice na yunƙura da kyar na miƙe kafafuwana na rawa na bita. Ina shiga d'akin jiri ya kwashe ni zan zube a k'asa nayi saurin dafa bango. Da kyar na iya k'arasawa ciki na haye gado na kwanta ina jin wani irn zazzabi da ciwon k'irji. Wunin ranan haka nayi sa a kwance kafin la'asar gidan ya cika da y'an uwa da abokan arziƙi. A daren Hajja da yayan Mamee suka sauka. Washegari aka tashi da biki ganga saboda yanda abun yazo babu shiri. Da kyar nake iya danne zuciyata nake yin abubuwan da ake. Gidan su Harira muka tafi gaba d'aya y'an matan da mai kunshi da suka zo tare dasu Hajja. Zuwansu suka fara gyara ta . Kafin kace me ta fara chanzawa ta k'ara wani haske da shek'i. Washegari Lahadi gidan ya cika da baki da suka zo daga dangin ango. Kusan rabin su turawa ne. Kalilan ne suke hausawa cikin su suma kuma inka gansu jajur dasu. Ni kad'ai nasan halin da nake ciki don duk abunda nake dauriya ce kawai. Zuwan dangin ango suka zo da lafiyayyun akwatina wajen ashirin na lafe shake da kaya na gani na fad'a harda kyautar gida da mota. Satin gaba d'aya anyi shi ana sabga ta biki. A d'an wannan tsakanin akayi y'an Al'adu irin namu na buzaye. Abun ya yi armashi matuƙa. Kowa ya ji dad'in wannan bikin idan ka cire ni. Kowa ka gani yana cike da walwala da farin ciki. Ana i gobe zasu tafi dangin ango suka sanar don haka a ranan muka je islamiya akayi mata sallama. Nan ma dai wani d'an k'aramin walima ce aka yi malamai da daliɓai suka bata kyaututtuka na taya ta murna da kuma sheda irin hazaka ta ta. A daren mun kulle a d'aki nida ita da Harira da kuma Janaah y'ar gidan kanwar Mamee. Kaya muke taimakawa Marwah muna shirya mata cikin jaka. Wayar ta ,tayi ringing ta koma can kuryar gado ta amsa. Zuwa wannan lokacin dauriyar da nake ta fara gazawa numfashi ya faramin wahalar fita, amma duk da haka ban bari sun gane ba har muka gama na samu guri na kwanta na runtse ido ina tunanin wata k'ila bazan k'ara buɗewa ba. A hankali na buɗe na kalli Marwah dake can kuryar sa tana murmushi kafin na maida kan Harira da Janaah dake hira katsa-katsa saboda dare. D'an murmushi nay ina jin a jikina kallon k'arshe ne nake musu daga haka na maida ido na lumshe ina fisgar numfashi da kyar. Ban d'auki lokaci ba na fad'a cikin deep peaceful slumber da bana fatan na barka. 𝓉𝒽ℯ 𝒻𝒾𝓇𝓇ℯ & 𝒾𝒸ℯ. ༄ZUBAR HAWAYE༄ 𝒜ɱαȥιɳɠ ★'★ ɯɾιƚҽɾ7ʂ ϝσɾυɱ ( 𝒜, ★ ʂƚαɾ'ʂ ,ɯ ★ ϝ) 𝗔𝘀𝗵𝗮𝗻𝘁𝘆 𝗹𝗼𝘃𝗲. Vol/51-55. 2 days later. K'arar abu da nake ni dif-dif kusa da kaina kaman monitor na bugun zuciya shiya sa na fara k'ok'arin buɗe ido. A hankali na buɗe idon nawa saidai ban kaiga buɗewa duka ba wani irin gaske dal ya dalle min ido nayi saurin maida su na rufe. Wani shuu kunnena ya fara kafin naji hayaniya sama-sama kaman ana ihu da kiran sunana. K'ara buɗe idon nawa nayi da haske ya cigaba da haskewa bayan kaman yan sakanni na fara gani tar-tar. Da farin silin na fara cin karo da fanka dake juyawa. "Sanaah. Sanaah. Doctor ,doctor, Mamee, Baffa..." Na gane muryar Marwah dake ihu kaman wata zararriya. Ihun ta ya janyo hankali mutane suka fara fad'uwa d'akin a guje. Mamee na fara ganewa da Baffa dake k'ok'arin kamani doctor ya shigo da sauri yana ce musu kowa yaja baya. Da ido nake kallon su d'aya bayan d'aya da mamakin abunda yake faruwa. Yanda naga fuskokinsu cikin tashin hankali wasu ma sai kuka suke musamman Marwah dake rungume jikin Ya Aliyu rungume da it da jajayen ido. Hajja ta face majina tana kuka ta d'aga hannu sama tana cewa "Alhamdulillahi. Allah mun gode maka daka tashi k'afadun ta lokacin da muka shirin fidda rai. Allah mun gode ma" Gaba d'aya d'akin suka amsa da Amin. Cigaba nayi da binsu da kallo ina mamakin dalilin da yasa Marwah bata tafi ba. Sai da doctor ya gama dubani sannan ya juya wajen su Baffa. "Alhamdulillahi Alhaji. Yanzu zuciyar ta na functioning . Coma data shiga na kwana biyu brain nata na buƙatar hutu. Zamanku kusa da ita yanzu zai iya jawowa a fad'i abunda zai kara triggering nata da har zaisa heart nata ya k'ara Malfunction . Wato zai iya kara tsayawa kaman yanda ya yi kwana biyu da suka wuce. Idan hakan ta faru, abu ne da bama fata saboda haka ina so ku barta tasamu barci dan brain nata ya yi functioning yanda ya dace" Babu wanda ya musa suka juya suna ficewa d'aya bayan d'aya. Bama su gama fita ba idona ya rufe ruf saboda allura da doctor ya yimin. Kwana biyu da farkawa ta yau. Ina ganin kauna da kulawa ta ko ina duk da oxygen kan fuskata bai hana suna bani abinci ba . Sosai ake taka tsantsan wajen bani kulawa. Tambayoyi da yawa ke cina amma na kasa samun daman tambaya sai yau da Marwah ke bani abinci idanuwan nan nata a kumbure . Da kyar nace "wai meya faru?, me yasa baki tafi ba?" D'an jim tayi da abinci a hannu sai shar ga hawaye sun wanke mata fuska. "Did you know? You die. Lafiya muka kwanta dake amma muka wayi gari kin ki farkawa daga barci. Kinsan irin tashin hankalin da muka shiga? Duk abunda akayi kin ki tashi. Mamee... Sai kuma tayi shiru tana wani irin kuka mara sauti. "Mamee da Ya Khamis kad'an ne zuciyoyin su basuga ba. Mun shiga tashin hankali da bamu tab'a shiga ba. Baffa was crying so miserably duk irin dauriyar sa ranan Baffa kuka ya yi sosai bai damu gaban ko waye ba. Ya Aliyu a take ya sume but bai jima ba ya farfado. We are so devastated mun d'auka mun rasa ki. Gida ya kacame da kuke-kuke ana shirin yi miki wanka sai ga Deen . Ya shigo fitar da ya Aliyu da Khamis da ni da muka hana a d'auke ki. Miraculously yana shigowa ya fara k'ok'arin janye ni daga jikin ki bansan me yaga ni ba ya saki da sauri ya janye ya Aliyu ya durkusa gaban ki. Hannun ki muka ga ya kama sai kuma ya d'ora kunnen sa kan kirjin ki. A guje muka ga ya sure ki ya yi waje dake muka rufa masa baya da gudu. Mutanen dake tsakar gida duk suka fito ganin yanda muka fito aguje Deen d'auke dake. Muna fitowa k'ofar gida mukaci karo dasu Baffa dake alwala har zuwa lokacin yana goge kwalla. Ganinmu yasa hankali duk ya yo kanmu Baffa da Mahaifin Deen suka taso da sauri suna tambaya meya faru damu kanmu bamu sani ba muna dai binsa ne kawai. Saida ya saki mota sannan ya juyo yana ya kalleni kafin yace "She still breathing. Amma faintly zuciyar ta ke bugawa tana buƙatar a kaita asibiti cikin gaggawa " Wani irin hamdala da kabbara wajen ya d'auke sai a lokacin wani irin relief ya kamani na tafi luu na zube jikinsa. Daga nan ne bansa yanda aka yi ba sai bayan na farka ne nake jin Deen shiya bada jinin sa aka sa miki saboda shine wanda jinin ku yazo d'aya dashi. Kuma saboda yanayin tashin hankali da yaga muna ciki ana tambaya kafin ma wani yace wani abu yace a debi nashi a gwada." Hannuwa ta riƙe tana kallon cikin idona da jajayen idonta. "Ki gayamin Sanaah. Menene yake damunki hka da har zuciyar ki ta daina aiki na wasu lokoto?, mene ya yi zafi haka da har ki ka kamu da ciwon zuciya haka?. Ki gayamin don Allah ki gayamin meke damun ki" Ido kawai na zuba mata hawaye na gudu kan fuskata kafin nayi murmushi mai ciwo ina girgiza kai alamun babu komai. Numfashi kawai taja ta miƙe ta fice daga dakin na bita da kallo ina tunanin me yasa Deen ya bani jinin sa?. Yanzu ina yake? Alhamdulillahi kodan saboda a karfafa musu gwiwa nayi k'ok'ari wajen ganin na samu lfy duk da ita lfy Allah ke bayarwa. Ina gudun tambaya su shi yasa nasawa kaina k'arfin hali sosai kuma ina samun progress sosai. Sati na d'aya asibiti ina takawa da kaina na shiga banɗaki, har Sallah ina yi da kaina. Nayi wanka na shirya, naci abincin. Naga kauna ta ko ina Baffa da Mamee ba'a cewa komai bare Ya Khamis da Ya Aliyu. Abokan Arziƙi da dangi duk sunzo Harira har kwana tayi wajena duk da ita dama kullum tana hanya. Sati d'aya da y'an kwanaki aka sallame ni daga asibiti. Kai tsaye gida mukayi washegari saiga mahaifin Deen da wasu daga cikin dangin su sunzo tafiya da Marwah. Nayi iya duk k'ok'arina wajen nuna farin cikina . A daren mukayi Sallama washegari asubar fari muka raka su Airport duka gidan banda Mamee. Bamu dade ba jirgin su ya tashi bayan y'an koke-koke. Ido na zubawa jirgin su Marwah dake tashi sama da murmushi mai ciwo kan fuskata hawaye na biyu kuncina. InshaAllahu zanyi k'ok'ari naga na cire son Deen cikin raina. Marwah ita tafini cancanta da samun shi matsayin miji. Taimakona da ya yimin zan cigaba da gode masa har k'arshen rayuwa ta, but for now zan sashi chan k'asan zuciyata na rufe. He will for ever be my first love and my hidden secret. Da wannan tunanin muka koma gida na kudurtawa kaina zan buɗe new chapter na rayuwa. Zanyi living dreams d'ina, zanyi living life d'ina to the fullest har k'arshen rayuwata. We leave once ,life is to short so leave as long as your still breathing. Zan maida hankali nayi karatu don nayi achieved na dreams d'ina nida Marwah. Dreams nasu na zama manyan fashion designers da duniya zatayi alfahari dasu. I will fulfil our dreams InshaAllahu. SOME YEARS LATER.... 𝓉𝒽ℯ 𝒻𝒾𝓇𝓇ℯ & 𝒾𝒸ℯ. ༄ZUBAR HAWAYE༄ 𝗔𝘀𝗵𝗮𝗻𝘁𝘆 𝗹𝗼𝘃𝗲. Vol/56-60. Murmushi ne kwance kan fuskata ina kallon Baby Tina dake zumburamin baki da fuskarta ta fito rad'am jikin laptop d'ina. Farin glass din dake kwance kan fuskata na gyarawa zama kafin nace "ANGEL kiyi hak'uri mana haka a daina fushin da momy uhmm. Zanzo fa very soon" Baki ta k'ara zumburawa tana kauda kai gefe. Fuska na kwabe a d'an shagwaɓe nace "I'm sorry Baby na. Please forgive me. Mummy will come very soon " Hard'e y'an hannunwan ta tayi a k'irji tana cewa cikin tsantsan American English. "No. You said that all the time. I did not believe you" Muryar Marwah naji daga gefen ta tana cewa "Yes .kice baza ki k'ara kiran ta a waya ba tunda taki zuwa inda ki ke" Ajiyar zuciya na sauke ina kama goshina saboda wani ciwon kai da nake sakamakon kwana da nayi ina had'a wata gwon da ake buƙatar ta cikin gaggawa. I know nasan kuna da tambayoyi da dama. The thing is. Life namu ya chanza gaba d'aya. Kaman yanda na d'aukan wa kaina alkawari. Nayi karatu na both na addini dana boko. Sauka ta biyu a islamiya biye da hadda. Haka na kammala karatuna na boko nayi degrees da Masters d'ina cikin d'an k'ank'anin lokaci. Shekaran Marwah biyu a LONDON ta haifo mana Angel d'in mu. Wato Baby Aysha dataci sunan Mamee. Muna ce mata Tina. Although duk cikin wannan lokacin Deen na nan k'asan zuciyata. Duk wani sakan ko sa'a d'aya sai zuciya ta ta shedamin cewa the man am inlove with yana tare da twin sister d'ina. Showering her with love. Kisses, love making ,everything a girl wishes for from the love of her life. Babu ta inda ya ragi Marwah. Duniya ta sheda matsanancin son da kulawa da yakewa Marwah .bayan haka ta haifo masa kyakkyawar yarinya dake matuƙar kama dashi komai nasu iri daya har dimples nashi. All this time i was depressed and heartbroken knowing bazan taba samu irin wannan soyayyar ba. Bawai bani da masoya bane . No, but babu wani namiji daya maye gurbin Deen ciki zuciyata. And I'm trying so hard naga na bawa wani chance cikin mane mana. Duk wannan k'ok'arin da nake na kasa. But hakan bai hanani basu dama ba wajen winning heart d'ina. Depression da heartbreak da nake ciki bai hanani dagewa wajen maida hankali nayi karatu ba har na kai matsayin da nake yanzu na AMBASSADOR a company na LOUIS VUITTON dake UK. Tunda nayi wata design na wata gown na d'ura a IG d'ina ta zama viral ana ta kira na k'asa-k'asa idan ta siyar wace. A take sukayi contact d'ina suka yi hiring d'ina matsayin ambassador. Idan suna buƙatar design zan tura musu su kuma su d'inka ta. Cikin ikon Allah duk abunda na tura sai ya zama hit . A take zaiyi sold out. Sunsha turomin kati na gayyata UK don zuwa halaltar taro na samun nasara da kuma cigaba da company nasu ke samu amma ina turning d'in su down. Bawai kuma babu yanda zanyi bane A'a. Bayan auren Marwah abubuwa suka chanza mana samun ya Aliyu da ya Khamis ya k'ara habb'aka ga Marwah dake da company na motoci KIRAR KAI da Mahaifin Deen ya bata kyauta kacakom bayan haihuwar Tina saboda farin ciki. Babu abunda zamuce sai Alhamdulillahi. Don a yanzu haka mun dawo garin Abuja da zama nan unguwar Maitama. Katon Mansion muka samu dake da b'angarori uku. D'aya nida su Baffa da Mamee. D'aya na ya Khamis da Harira dake matar sa yanzu. Suprise, Suprise. Bayan auren Marwah soyayyar da suke b'oyewa ta fito sarari. Sanda ya fito da maganan neman auren ta shima ya Aliyu ya fito da zancen sa shida Janaah y'ar kanwar Mamee. Ashe tun zuwanta bikin Marwah suka kulle. Lokaci d'aya aka had'a bikin nasu shekara hud'u da suka wuce. Abun sai wanda ya gani nafi kowa farin cikin auren Harira da ya Khamis. Lokacin da Marwah tazo bikin da k'aton cikin ta .I was so hurt and heartbroken again. But despite that na bata kulawa saboda matsanancin soyayyar abunda ke cikinta daya shigeni tafar d'aya, ranan dana fara jin kick nashi. Bayan aurensu aka k'arawa ya Aliyu girma ya zama shike bin Deen yanzu saboda jarumtar shi wajen aikin sa. Saboda haka shima aka bashi sojoji dake kulawa dashi . A yanzu I'm proud nace ina da y'an uwa dake millionaires, sannan ni kaina duk wata LOUIS VUITTON Suna biyana dollar 1m. Baffa da Mamee sunfi kowa alfahari damu da abunda muka zama. Ya Khamis babba d'an kasuwa ne dake harkar gwala-gwagwalai. Harira shekarar ta d'aya da rabi ta haifi Bonboy Alee junior . Muna ce masa Bonboy. Yana da shekara d'aya ciff tayi bari . Wata d'aya da yin b'arin ta sake yin wani saboda haka tayi planning bayan family Dr namu ya bata shawara tayi. Janaah kusan tare suka haihu da Marwah. Ta haifi baby girl. NEELAM. sai yanzu da take da tsohon ciki. Numfashi na k'ara ja ina kallin Angel dake fushi har yanzu taki yimin magana. Why take fushi? See tunda Marwah tayi aure har yanzu da nake 23yrs old na kasa zuwa gidan ta. Kaf family namu ,su Hajja dasu Harira babu wanda baije yaga gidan taba dake UK. Kowa ya dawo da irin yabo da tsananin kauna da Deen ke nuna mata gaban kowa suke maidawa. Bazan iya zuwa naga kalan soyayyar da suke furtawa yake mata ba bare na iya jurewa. So anytime da aka shirya zuwa zan kawo excuse da dole sai dai su tafi babu ni. Tun Marwah tana min mita har tazo tana min kuka, daga baya ta hau fushi dani mai tsanani. Ko wayata ta daina d'agawa . Saidai naji tana waya da Mamee ko Baffa ,ko su ya Khamis dasu Harira . Yanzu fushin ba ita kaɗai

Chapter 6 of 9