take dani ba har Angel don ita take zugata nak'i zuwa na ganta. I just can't bring my heart naje gidan ta. In har na ganshi zuciyata zata karye. Yanzu da bana ganinsa nafi jindaɗin life d'ina.
Numfashi na k'ara ja da lallami na k'ara cewa
"Angel, please look at me. I'm sorry ."
Kafad'a ta mak'ale very cutely tace "No " sai kit ta kashe Zoom call d'in da muke. Numfashi na k'ara ja na cire glass dake ido ina murza su. Oho ni Sanaah. Marwah aiki kawai take son taja min. D'agowar da zanyi ido na ya Fad'a cikin na Ya Aliyu dake jingina jikin k'ofar d'akina ya harde k'afa hannun sa zube cikin aljihun wandon sa.
Ya Aliyu ya k'ara girma da kyau mata ta ko ina sai kawo musu hari suke. Amma yayyen nawa idan su nakan matan su ne kad'ai. K'arasa shigowa ya yi ya zauna gefen gadon yana kallona cike da tuhuma.
"Now kafin kice zaki b'oye min. Ki gayamin dalilin da yasa baki son zuwa UK wajen Marwah "
Da inda-inda nace "Allah kuwa ya Aliyu babu komai zuwan ne dai Allah baiyi ba yanzu, amma inshaAllahu zanje"
Ido ya zubamin na rashin yarda da magana har na tsawon mintuna. Duk nayi tsuru -tsuru dani na rashin gaskiya. Kai ya jinjina ya miƙe tsaye yana kallo na
"Ki dai yiwa kan ki adalci kije kiga Marwah. Kina tunanin idan kinyi aure kema zata zo gidan ki ?"
Shiru nayi bance komai ya girgiza kai. Matsowa ya yi ya sumbaci goshina kafin ya juya ya fice na bishi da kallo da tunani kala-kala cikin raina. Washegari na fito sanye cikin doguwar riga y'ar kanti mai tattara daga kugu zuwa kirji sai d'an siririn hannu kaman mad'aurai. Gashin kaina na tufke shi tsakiyar kai na saki jelar ta zubo har Mazaunai na. Flat takarmi ne a k'afata hannuna riƙe da waya ina kiran number Angel saboda da fushin ta na kwana a rai.
Ban sami layin nata ba na kira Marwah kuma taki d'auka. Main falo na iske Baffa dake karatun jarida Mamee na had'a masa coffee cikin kwalliyar ta. A shagwaɓe na zauna kusa da Baffa ina gaishe su . Ajiye jaridar ya yi ya amsa da murmushi kwance kan fuskar . Tashi nayi nayi kitchen don neman abinci. Soyayyar agada aka yi da kwai sai chips ga kuma gashin kaza. Saida na zuba yanda zaiyi min na dawo na zauna kusa da Baffa da a yanzu yake kallon labarai.
Ban dad'e da zama ba saiga su Bonboy da Neelam Harira da Janaah biye dasu . Basu jima da shigowa ba saiga su ya Khamis. Gaba d'aya muka had'u ana karyawa ana raha . Can labarai ya d'auke mana hankali saboda sunan Deen da ake ta kira. Gaba d'aya muka bada hankali muna sauran labaran da ake sanarwa. Deen ya yi nasarar kama wani shugaban yan Mafia dake COSTA RICA mai tsananin had'arin gaske amma Deen da yaran sa sun kamoshi cikin d'an k'ank'anin lokaci.
Wani irin murmushi ne ya kwacewa ya Aliyu na tsananin proud ya miƙe ya fice da sauri yana k'ok'arin kiran waya da nasan babu tantama shi zai kira. Tunda aka fara kiran sa na sadda kaina k'asa zuciyata na harbawa da gudu. Muryar Neelam naji gefena tana cewa
"Mummy Sanaah kin koshi ni na cinye?"
D'agowa nayi ina y'ar dariya kafin nace wani abu idona ya fad'a cikin na Harira dake kallona da wani irin expression kan fuskarta. Da sauri na kawar da kai na turawa Neelam abincin shima Bonboy ya tada rigima shima sai na k'ara masa.
To har wajen la'asar muna zaune nan falo ana hira ,jefi-jefi ina duba laptop d'ina ko za'a nemi wajen aiki gashi har zuwa lokacin wayar Angel a kashe. Wayata dake gefena ta hau k'ara. Kallon wayar nayi da sunan WIZAD ke yawo a kai. Numfashi naja mai k'arfi ina jan d'an k'aramin tsaki. Wizad d'an Sanet Alhaji Ishak ne dake nan garin Abuja. Tun wani had'uwa da mukayi a Saudiya munje umra ya dameni har na bashi number na.
Kar kuji mamaki ta ko wace siga ya had'u. Irin handsome black beauty d'in nan ne da hutu da jindaɗi yasa fatarsa ta zama kaman ta Black Americans. Yana da dogon hanci da manyan lumshashshun idanuwa. Dogo ne daidai misila ga body mafarkin ko wace yarinya. Ga kyau ga kuɗi. Nayi duk yanda zanyi na cusa shi cikin raina abun ya gagara. Despite irin matsanancin son da yake nunamin.
Har wayar ta tsinke ban d'auka ba wani kiran ya k'ara shigowa. Ban ankara ba Janaah ta matso da tulelen cikin ta ta warce ta da sauri. Did i mention ya zama d'an gida?. No?. Oops. Bashi da shamaki da gidanmu sam. Ko yaushe zuwa yake ya zama kaman d'an gida.
"Wizad barka da yamma"
"Bata kusa ne amma gata nan ta fito bari na bata ."
Mik'o min wayar tayi tana zabga min harara na k'arba ina cije bak'i saboda haushi na kara a kunne nace "Slma "
Ajiyar zuciya ya fara saukewa kafin yace
"My dear how are you ?"
Da kyar na iya cewa "lfy "ina kallon laptop d'ina da email ya shigo daga LOUIS VUITTON.
"My Dear yaushe zanzo na ganki please?. Ina son na kara ganin kyakkyawar fuskar ki"
D'an numfashi na furzar nace "Wizad jiya fa kazo da yamma"
"So,? Bazan tab'a iya gajiya da kallon kyakkyawar fuskar ki ba. Did you know how beautiful and gorgeous you are?. "
"Wai don Allah me yasa kin k'i ki bari na turo gidan ku?. Kinsan Baffa ya bani dama na tura ,but bana son abunda zai b'ata miki rai. Ina san approval naki .why ki ke reject d'ina? "
Ya k'arasa maganan da desperate tone. Shiru nayi jikina ya yi sanyi idona kan sakon dana gama karantawa. Numfashi na k'ara ja a hankali nace
"I'm sorry inshaAllahu idan na dawo zan baka chance ka aiko"
Wani ihu ya saki " Baby da gaske ki ke? ,but ina zaki?"
D'agowa nayi na kalli Mamee dake hira dasu Harira . This is my chance na farantawa Mamee da Baffa wajen fidda miji don burin su kenan suga nima ina d'akin mijina. Kuma chance d'inane da zan wanke kaina gurin Marwah. Nima ya kamata na samu happiness d'in nan da kowa ke samu tare da mijinsa. I need to get married ko dan na manta dashi gaba d'aya a rayuwata ta.
"UK. I'm going to UK tomorrow inshaAllahu "
Little did i know . Zuwana shi ne babban kuskure da zan tafka a rayuwata.
𝓉𝒽ℯ 𝒻𝒾𝓇𝓇ℯ & 𝒾𝒸ℯ.
༄ZUBAR HAWAYE༄
𝗔𝘀𝗵𝗮𝗻𝘁𝘆 𝗹𝗼𝘃𝗲.
Vol/61-65.
Bayan munyi sallama na ajiye wayar ina maida numfashi. Kallon su Mamee nayi nace
"Mamee gobe zanje UK. Yanzu sako ya shigomin suna buƙata ta. Wai coronation ne za'ayi na sarauniyar su to kuma su ta zaba suyi mata kayan da zata sa. Shine suka aiko min harda ticket na jirgi da komai don Allah naje nice best option nasu. "
Murmushi Mamee tayi cike da jindaɗi tace
"MashaAllah .Ubangiji ya k'ara d'auka ku duniya da lahira. Hakan yana da kyau kinga sai ki sauka gidan Marwah. "
Kai kawai na d'aga na miƙe ina cewa bari naje na fara had'a kayana. D'akina nayi kai tsaye ina shiga Harira ta biyo bayana. Ban kalleta ba na shiga walk in clothes d'ina na fito da akwatina mai kyau na Louis vuitton na dora kan gado. D'aya bayan d'aya nake d'auko kayana ina jera su while Harira na zaune tana bina da kallo.
Ina saka undes d'ina tace
"Mene ya chanza ra'ayin ki yanzu zakije Uk?"
Ban kalleta ba nace "amma kina ji nayiwa Mamee bayani ko?. What else da zai kaini bayan wannan ?"
"I don't know. Ai ba yau ne suka fara miki irin wannan tayin ba amma ki ke kin zuwa. Why know and why yasa bakya san zuwa?"
D'agowa nayi na kalleta na bata rai" wai interrogation d'in na mene? Kaman wacce tayi sata?, idan akwai abunda zaki fad'a ne kawai ki fad'a. Stop beating around the bushes "
Na cigaba da jera kayan raina a b'ace. Murmushi naji tayi kafin tace
"You know. All this time da zuciyata ke gayamin abunda naki yarda dashi yau na yarda da hakan."
Kallo na watsa mata bance komai ba ta cigaba da cewa
"I know your inlove with Deen"
Dum k'irjina ya buga na d'ago a razane ina kallon ta ido waje. Murmushi tayi ta miƙe tsaye tana kallo. How? How did she know?
"Lokacin da ki ka kwanta. I find it hard to believe saboda Auren Deen da Marwah yasa heart naki tsayawa. After making the piece together na gane dalilin da yasa bakya san zuwa gidan Marwah. Because of Deen the person your in love with right?"
Shar hawaye suka biyo kuncina. All this time da nake hidden wannan big secret nawa. She knows, tasan komai tayi choosing tayi ignore nashi. Matsowa tayi gabana hawaye sun cika idon ta.
"But Sanaah ina so ki sani Deen Marwah yake aure. He's a forbidden fruit a gare ki. His forbidden for you to be in love with. Ki cire shi a ranki haka. For how long zaki cigaba da suffering kan wanda baisan kina yi ba?"
Sosai na fashe da kuka ina dukan k'irjina da wani irin heartbreaking voice nace
"Did you think I'm proud of son shi da nake? .kinsan hau many hours, day and night nake gurfane gaban Allah ina mai kaskantar da kaina da rokon yaya yemin son shi a cikin zuciyata? How many times nake tsayawa gaban ka'aba ina zubda hawaye da rokon Allah ya musanyamin da mafi Alkhairin sa? Ko kin d'auka sintirin da nake Umrah ina zuwa ne saboda jindaɗi?. Everytime Maimakon sanshi ya ragu cikin raina sai nunkuwa da yake. I did everything and still doing don naga na cire shi cikin zuciyata, but no matter how much i try is pointless and it's kills me.
Na tsani kaina saboda son shi. Ina blaming kaina son mijin twin sister d'ina da har nake kishin ta. It's killing me every time..."
Full on crying nake ina dukan k'irjina da nake jinsa ya yi min nauyi. Da sauri ta rungume ni tana kuka itama sosai.
"Shh. Please it's OK. Kinsan baki da cikakkiyar lfy. Stop crying Please. Allah shiya fimu sanan ikon sa. InshaAllahu akwai alkhairi nan gaba. Jarabawa ce Allah ya d'ora miki .shi mumini dama kullum cikin Jarabawar ubangiji yake don k'ara kusanci dashi. Amma fa hakan na faruwa ga wanda ya yi hak'uri ne ya cinye ta. InshaAllahu zaki ga alkhairi. Allah zai musanya miki da wanda yafi shi. Stop crying Please "
Mun jima a haka kafin na janye ina goge fuskata nace.
"Don't worry. Kaman yanda na rufe shi can k'asan zuciyata matsayin hidden secret d'ina. He will for ever be, after all he doesn't want me. "
Numfashi taja jiki a matuƙar sanyaye ta taimaka min muka k'arasa shirya kayana kafin mu fito falo gaba d'aya. Mun iske Baffa da su ya Khamis da suka dawo daga masallaci na gaya musu tafiyar da zanyi gobe. Ya Khamis yace zai kaini Airport. Da Mamee tace zata kira Marwah ta gaya mata nace su barta ina so nayi suprise nasu ne.
Washegari k'arfe bakwai na fito janye da trolley d'ina. Sanye nake da maroon suit ta mata mai wando kaman buje. Sai farar singlet dana saka a ciki nayi tuck d'inta jikin wandon saman ta na dora coat ta wando data kai har gwiwa ta. Kaina kuwa na rolling nashi da d'an k'aramin maroon mayafi bayan na tufke gashina kaman gammo. Takarmi ne mai d'an tudu a k'afa sai jakata dana rataya dake d'auke da wayata da laptop's dina.
Ni kaina nasan nayu kyau na fito ina duba agogon dake d'aure a hannuna. Karfe takwas daidai jirgina zai tashi ya kamata na hanzarta zuwa before 8. Ina fitowa naci karo dasu Harira gaba d'ayan su a shirye alamun ni suke jira. Y'ar dariya nayi ta jindaɗi. Ko basu fad'a ba nasan rakiya za suyi min. Gurin su Mamee na k'arasa na rungume kafin muyi sallama duk muka fito gaba d'aya dasu ya Aliyu.
Takwas daidai muka isa Nnamdi Azikiwe International Airport. Muna zuwa ana kiran Board namu dan haka ban b'ata lokaci ba mukayi sallama na bisu d'aya bayan d'aya na rungume kafin naja trolley d'ina na wuce ina d'aga musu hannu suma suna d'ago min.
First class ne seat d'ina. Mu uku ne kacal a first class. Tunda na shiga na zauna nayi zurfi cikin tunanin abunda zai faru kuma idan na isa UK. Ina fata naje lfy n dawo lfy. Rass gabana ya yanke ya fad'i bayan na gama wannan Addu'ar. Wani irin unsettling feeling ya ziyarce ni sai nake ji kaman zuwan nawa kuskure ne mai girma.
Dafe k'irjina nayi ina yin duk Addu'ar data zo bakina har jirgin mu ya d'aga sararin samaniya.
♡︎♡︎♡︎
UK. UNITED KINGDOM
lokacin da jirgin mu ya sauka safiya ce a UK. Sanda na taso daga can Nigeria su gurin su dare ne. Lokacin dana sauka safiya ce 9pm.
Fitowa nayi ina jan trolley d'ina riƙe da wayata ina duba mutane dake tsaye da banner dake d'auke da sunan wanda suka zo d'auka. D'aya bayan d'aya na bisu da kallo ina tunanin abunyi. Ban kira company na LOUIS VUITTON ba saboda suma ina so nayi musu suprise ne. Nasan da ace na gaya musu nayi approve na zuwan zasu aiko da wanda zai d'auke ni.
Numfashi na fesar mai zafi na samu guri na zaune harabar Airport d'in ina tunanin abunda zanyi tunda bansan wani Street Marwah take ba cikin wannan katon garin. Number d'in da nake tunanin har na mutu bazan k'ara kallo ba na lalubo k'irjina na harbawa. Ido kawai na zubawa number na kasa kira har tsawon minti biyar.
Da kyar na aro jarumta na danna mata kira. Hannu dafe da k'irjina da nake jin kaman zai tarwatse na k'ara wayar a kunne ina jin tana ringing. Har na fidda rai bazai d'auka ba jiki a matuƙar sanyaye na fara k'ok'arin cire ta a kunne wannan muryar tashi da take so deep. If not possible ta k'ara zama wani irin deep yace
"Hello"
Kar kuso kuga bugun da k'irjina ya yi jikina ya fara rawa na kasa cewa komai sai rawa da bakina yake. Shima bai k'ara cewa komai ba har tsawon sakon biyu kafin naji yace
"Sanaah"
Tsananin shock yasa na hangame baki totally speechless. Dama yasan number na?. How?. Zuciyata tace you have to be brave Sanaah. Show him your over him. Wani irin courage ya zomin na gyara murya ta dake rawa
"Uhmm. Hi ,DEEN"
"Dama am in UK ne yanzu ina Airport. Bansan inda ku ke ba ko zaka bani address na samu cab.. please "
Na k'arasa please d'in da y'ar siririyar murya kaman mai rad'a. Shiru ne ya ratsa wayar na tsawon minti d'aya kafin yace da wata irin calm deep voice.
"I will come get you"
Kit ya kashe wayar ya barni da ita a kunne jikina na shaking .what will i do? His coming to get me. The one and mighty General DEEN. Ya rabbi.
♡︎♡︎♡︎
ASTRAZENECA COMPANY
The biggest company da ya yi worth na dallar E191.9 billion dollars. And it's belongs to the one and only GENERAL.
Miƙewa ya yi daga kan kujerar da yake zaune bayan ya ajiye wayar. Numfashi yaja mai k'arfi ya kai hannu ya tura cikin coily long hair nashi yana ya mutsawa kaman yanda ya saba. Sanye yake da wata arniyar black three pieces suit data bala'in kama faffaɗan kirjinsa kaman ya rabe biyu.
Coat d'in sa daya cire ya ajiye jikin kujera ya d'auka ya kwashi wayoyin sa a kan tankamememen glass tebir dake gabansa ya fara k'ok'arin fitowa. K'ofar katon office d'in nasa da ya yi entire flour biyu aka buga Adam ya shigo da nervousness kwance kan fuskar. Manya silver eyes nashi ya watsawa Adam alamun tambaya.
Da d'an inda-inda Adam yace
"Sir, you have a visitor"
"Who?"
D'an tari Adam ya yi yana sadda kai katsa
"It's MISS GEORGIA VALANTINO"
Wani irin d'aure fuskar ya yi yana kallonan Adam expressionless. The thing he despise yanzu haka shi ne drama. And Georgia all she wants was drama. Tsk sound ne ya fito bakinsa ya wuce Adam yana ce masa
"Tell her I'm busy "
Kafin Adam ya yi yunƙurin cewa wani abu har ya fice. Yana fita idan sa ya fad'a cikin na matar da yake kira Uwa. As always dressing elegantly kaman mai zuwa gasa ta kyau. Komai na jikin ta kukan kuɗi yake. Yanda yaga assistant nashi da masu tsaron sa sun yi tsantsan kaman masu tsoro yasa ya saki numfashi yana kallon yanda take kurban tea da aka kawo mata sai yatsuna take kaman tana cin kashi.
Kai ya girgiza kawai ya fara takowa don shiga lifter. A hanzarce Georgia ta miƙe ta tasha gaban sa da wani fake smile kwance kan fuskar ta ta ware hannuwa a tunanin ta gurin ta zaizo.
Kallon daya watsa mata saida taji kaman ta zura a guje. Duk wanda ke gurin saida ya sharce gumi saboda tension dake tsakanin uwa da d'an ta. Da wani irin disdain yace
"What did you want?"
D'an fake gasp tayi tana d'an zare ido
"Is this how you talk to your own mother?"
Harshe ya taune yana breathing don hana kanshi fad'an maganan dake k'ok'arin fitowa. Kai kawai ya jinjina ya rab'a gefen ta ya wuce .murya ta d'aga da sauri ganin zai tafi ya barta cikin embarrassments.
"MIGUEL we need to talk"
Miguel shine sunan da take kiransa dashi sunan su na LATINO. dan Latin ce Georgia. Tace baza ta kirashi da Deen ba saboda a duniya taki jin wannan addini na mahaifin sa.
Bai juyo ba saida ya shiga lifter ya watsa mata blood shot eyes nashi kafin yace da wani irin sinister look kan fuskarsa.
"It's Deen. Dear mother "
A guje Adam da suaran musu tsaron suka fad'a kafin lifter d'in ta rufe. Matsanancin kunya yasa Georgia ta zuya a zafafe cike da burin kuya na kunya tata da Deen ya yi gaban yaransa ta jiga wata lifter d'in ta fice daga company d'in gaba d'aya da zummar zata dawo.
Har suka shiga dankareriyar LIMO nashi ranshi a matsifar bace yake. Tada can b'angaren mazaunin direba Adam ya kira
"Sir, ina muka nufa?"
Lumshe manyan idon sa ya yi ya kwanta bayan kujera a kasalance yace
"To the airport. We have an important guest"
Daga can tsallake wata black SUV ce da kaman jira take. Motar Deen na tashi itama ta rufa mata baya. Adam ya k'ara kira ta landline d'in motar
"Sir, they are following us"
Buɗe manyan silver eyes nashi ya yi wani irin sinister look da deadly voice yace
"Let them."
To fa. Wasan yanzu ya fara. Gashi Sanaah ta shigo in the middle of something sinister.
𝓉𝒽ℯ 𝒻𝒾𝓇𝓇ℯ & 𝒾𝒸ℯ.
༄ZUBAR HAWAYE༄
𝗔𝘀𝗵𝗮𝗻𝘁𝘆 𝗹𝗼𝘃𝗲.
Not edited.
VOL/66-70.
Tunda yace gashi nan zuwa k'irjina da dukkanin wani sassa na jikina rawa yake. Sai had'a zufa nake kaman wacce take tsoron kar a hukunta saboda tayi mugun laifi. Tsawon minti ashirin ina nan zaune na kasa samun nutsuwa kaman ance na d'ago idona ya sarke cikin deep silver eyes nashi yana takowa majestically da wannan tafiyar tashi ta izza. Chak numfashi na ya d'auke na wara manyan idona cikin nasa dake nufoni security's nashi biye dashi.
Ya Hayyu ya Kayyumu. Fad'an irin kyau da girma daya k'ara abun bazai misaltuba. Yanda idonsa ke cikin nawa haka na kasa d'auke nawa idon daga kansa har saida suka kusa matsowa inda nake zaune. 'Kar ki manta matsayin sa a gurin ki, Sanaah' wani b'angare na zuciyata ya tunatar dani. Jiki a sanyaye na sauke nawa idon k'asa ina jan wani irin shaking numfashi.
Da jarumta na miƙe tsaye riƙe da trolley d'ina daidai suka k'araso inda nake. Komai na cikin Airport d'in tsayawa ya yi chak ,babu wani mutum dake motsi. Hankalin mutane gaba d'aya ya yi kan Deen dake cikin dakarun sa. Duk inda ka juya waya ce ke aikin. Masu yi masa hoto nayi, masu yi masa videos nayi. Matan nan duk sun rikice manya da yara .
Sai naji kaman irin a romance novel d'in nan muke. But sadly it's the opposite.
"Sanaah "
Ya kirani da muryar nashi dake sawa kayi wet na pant naka immediately. Da azama naje
"Hi. I'm sorry na taso ka unexpected "
Kai kawai ya d'aga fuskarsa babu wani expression ya juya ya kalli d'aya daga cikin yaransa. Wani ya matso da sauri ya karb'i jakata.
"Let's go"
Daga haka bai k'ara cewa komai ba ya juya abunsa nayi saurin binsa yaran sa suka rufa min baya. Har muka shiga limo nashi bai k'ara kallon inda nake ba. Nima kuma nayi k'ok'arin wajen ganin na maida hankali jikin window ina kallon THE GLAMOROUS UNITED KINGDOM.
Abunda bata sani ba. Even though tana tunanin baya kallon ta his looking at her beneath his eyes.
Tafiyar muka yi kaman ta minti goma sha biyar sai gamu bakin wani katon Gate da ta wajen sa kana hango bishiyu na furanni .gate d'in na buɗe muka hau katuwar kwallta mai tsananin kyau da aka kawata da fitilo da bishiyu. Saida mukayi y'ar tafiya wajen minti biyar sannan na fara hango tankamememen Mansion gari guda da saida na ware ido na saka fuskata jikin glass baki hangame ina kallon wannan Aljannar duniya.
Nan ne gidan da Marwah ke zaune? Wow. Gaskiya tana cikin Aljannar duniya. Motar na tsayawa aka buɗe min na fito da sauri don na kagu naga Angel. Wuce ni ya yi zuwa ciki nayi saurin binsa had'addiyar glass door daya tsaya yana saka passkey nashi. Tana buɗewa na saki baki hanci da ido ina kallo. Gaba d'aya na zama y'ar kauye . Gashi dai nima gidanmu gida ne na gani na fad'a amma ba irin wannan ba.
Ihu danaji yasa na d'aga kaina da sauri inda naji ihun. Marwah ke saukowa a guje Angel biye da ita daga kan had'adden glass stairs nasu dake tsakiya katon falon. Nima a guje na nufe su mukayi clash tsakiyar benen da wani irin gudu Marwah ta d'ane ni taba ihu har saida muka kusa gangarowa daga kan benen. Mutum kawai naji a bayana ban juya ba saboda hankalina ya yi kan Marwah da Angel dake k'ank'ame dani kaman zasu koma cikina.
Dariya nake yi mai had'e da kuka. Na janye Marwah dake kuka a jikina ina dariya.
"Wai da gaske ke ce ko mafarkin da na saba ne?"
Y'ar dariya nayi na suru Angel dake ta tsalle ta rasa inda zata sa kanta. Sumbatar yarinyar nayi a kunci ina jin wani irin sonta kaman ni na haife ta. Mun jima a haka kafin naji alamun an matsa daga bayana ya matso ya sumbaci Marwah dake goge hawaye mak'ale a k'afata . Saman ya haura ya barmu nan falo. Kai d'an uwa rabin jiki. Wuni mukayi muna hira kaman zan gudu. Ko banɗaki zanje to suna biye dani ita da Angel.
Nayi mamakin katon d'akin da suka bani wai nawa . Kuma dan ni kad'ai aka yi d'akin babu wanda ke shiga dan zuwa nane ma ta buɗe shi da mukulli. Y'ar dariya kawai shi yasa take fushi dani har d'aki na aka ajiye duk sanda nazo. Tunda muka kulle d'akin kuwa sallah ce kawai ke tada. Abunci duk bayan awa biyu za'a kawo shi