sannan ta juyo sosai tana murmushi tace
"Wai Zubair ya fasa auren Khadija. Tun shekaran jiya yake ta sintiri a gidanmu yana neman yafiya ta "
Ido na zaro " haba ya aka yi garin ya?"
Kallona tayi cike da mamaki tace "wai kina nufin ba aikin ki bane wannan?"
Kaina girgiza ni ina ma na samu lokaci nida nake kwance bani da lfy.
"Ikon Allah to lallai babu abun yabo da bauta sai Allah. Wlh ya dawo duk ya rikice ga uban waya da yake damuna dashi nayi blocking number tashi. Shine yake ta sintiri a gida wai shi wlh baisan yarda aka yi har maganan shi da Khadija takai haka ba. Naga amfanin Addu'a saboda ita kaɗai ce makarin Mumini "
Murmushi Marwah tayi ta karb'e zancen da cewa "Tabbas kuwa Babu wani abu da yafi k'arfi Addu'a. Dama Allah yace ku rokeni na amsa muku. Kinga gashi kinga ribar hak'uri da kuma Addu'a tun ba'a je ko ina ba"
Tabbas kuwa a tare muka sauke ajiyar zuciya. Wato idan na fuskanta akwai abunda Khadija tayi ta kawar da hankalin Zubair daga kan Harira. Lallai kuwa idan haka ne mak'iyin ka na tare da kai baka sani ba. Ashe simimi kasauce mai fuska biyu. Duk cikin mu tafi mu sanyi da hak'uri ashe munafukace. Gashi Allah ya nuna mata illar butulci tunma ba'aje ko ina ba.
K'arar wayata ya katsemin tunanin da nake na miƙa hannu a hankali na d'auko ina duba bak'uwar number dake kira. Kaman karna d'aga na dai d'aga
"Hello?"
"Hi, Sanaah ,Beelah ce"
"Ohh"
Nace ina kallon Marwah dake kallona
"Dama Zabina ta bani number naki tace na kira ki na tuna miki gobe ne Birthday d'in da misalin k'arfe hud'u"
A hankali nace "OK" Ban k'ara cewa komai ba na kashe wayar da sauri.
"Waye?"
"K'awata ce"
Kallon tuhuma ta kara jefamin
"Wacece k'awar taki da ban san taba?"
A harzuk'e nace "ina ruwan ki ne wai? Dole ne sai kinsan duka kewaye na"
Bata ce komai ba ta girgiza kai ta miƙe ta fice na bita da Harara. Kai Harira ta girgiza a sanyaye tace
"Wlh Sanaah banajin dad'in abunda ki ke wa Marwah. Tana kulawa ne dake fa matsayin ta na y'ar uwar ki"
"To sai me? Nida ita waye babba bana son sa ido kaman wata uwata"
Miƙewa tayi tana cewa "To ai shikenan bari na wuce dama nace bari nazo na duba jikin ki "
Da sauri na riƙe ta "Yauwa tunda kinzo fad'uwa tayi daidai da zama muje gurin Mamee kice mata gobe zan raka ki unguwa pls"
Ido ta zaro dafe da k'irjin. "A'a rufamin asiri taje ta b'aci ki shafamin kashin kaji bada ni ba babu ruwana"
Fuska na had'e "idan baza kiyimin ba shikenan ki rubuta daga yau mun daina k'awa.."
Ban k'arasa ba ta tari numfashi na "Shikenan muje amma idan ta b'aci wlh zan fad'a musu gaskiya baza kisa Mamee tayi fushi da ni ba"
"Naji muje"
Kaman yanda nayi zato kuwa Mamee bata musa ba ta amince amma tace karna zauna. Haka muka fito raina fes Marwah dake zaune tsakar gida kare da waya a kunne ta bimu da kallo har muka yi waje. Tunda na fuskanci tana waya naji jikina gaba d'aya ya yi sanyi har Harira ta fuskanta saida muka fito k'ofar gida ta juyu tana kallona
"Wai meya same ki ne yanzu-yanzu naga duk kin chanza?"
A sanyaye nace "babu komai". Ido ta zuban kaman maison karantar wani abu tana k'ok'arin k'ara magana sai ga Ya Khamis da Ya Aliyu. A take naga duk ta daburce kuncinta duk ya yi jaa tana Blushing. Blinking nayi don tabbatar da abunda nake gani tayi saurin sunkuyawa tana gaidasu. kaman yanda ya Aliyu ya saba a dake ya amsa ya shige gida ya Khamis ne ya tsaya yana amsa mata da wani abu kan fuskarsa dana kasa gane ko mene. Muna had'a ido dashi ya basar ya wuce ciki da sauri na bishi da kallo baki a sake kafin na juyo da kallona kan Harira dake ta zuba murmushi.
Lura da tayi kaman ina neman fuskantar wani abu ta juya da sauri tana cewa
"Sai anjima"
Bata jira nace komai ba ta wuce na bita da kallo cike da mamakin abunda na gani. Meke shirin faruwa ne tsakanin su? Kafad'a na d'aga Idan tayi tsami zamu ji. Juyawa nayi nima na shigs gida can falo naji muryar su nayi d'aki banyi zaton Marwah na ciki ba na same ta zaune kan gado shiga ta ya yi daidai da wani irin murmushi data saki na jindaɗi koma menene yake ce mata.
Kaman wadda aka d'auko dutse aka d'orawa a k'irji haka na k'arasa jiki babu laka na haye gadon na kwanta ina kallon bayan ta tana waya a hankali duk yanda na kasa kunne naji abunda take cewa ya faskara. Wani irin suya da d'aci zuciya ta take dani kaina na rasa dalilin hakan. Ya Aliyu ne ya kwala mata kira ta miƙe da sauri ta ajiye wayar ta fice. Ido na zubawa wayar jikina na rawa . Kaman bauraniya na d'auko wayar ta ta na zubawa number data ke kai ido zuciyata na ingizani nayi na d'auke number.
Number na d'auka cikin wayata ina kallon k'ofar karta shigo na ajiye wayar kaman yanda tayi ,nayi saurin komawa na kwanta k'ank'ame da wayar a k'irji ina sauke ajiyar zuciya. Wai meke damuna ne? Me yasa na kasa samun sukuni tunda naji sunan wannan mutumin?. Number na kira saboda azalzalata da zuciyata ke yi nason jin muryar sa. Har ta fara ringing nayi saurin katsewa na dafe k'irjina dake bugawa da k'arfi
'Idan ya d'aga kice masa me?'
Abunda zuciyata ta tambayeni kenan na katse wayar da saurin ina maida numfashi . Ban gama daidaita nutsuwa ta ba wayar tawa ta fara ringing har na firgita. Jiki na rawa nake kallon number dake rawa kan screen d'in ta.
'Ki d'aga '
'A'a kar ki d'aga in ki ka yi haka baki yiwa Marwah adalci ba. Kar ki zama Khadija '
Wasi-wasin da zuciyata keyi kenan . Maganan karshe ta tab'ani Jikina ya yi sanyi kalau. Na katse kiran cikin sauri na saka number d'in a blacklist. Wani irin nauyi kirjina ya yi da nake ji kaman wani b'angare na zuciyata na rufe. Wai me yasa na damu da mutumin da ban tab'a gani ba? me yasa zuciya ta ta kasa samun sukuni tunda naji muryar sa?.
𝓉𝒽ℯ 𝒻𝒾𝓇𝓇ℯ & 𝒾𝒸ℯ.
༄ZUBAR HAWAYE༄
𝒜ɱαȥιɳɠ ★'★ ɯɾιƚҽɾʂ ϝσɾυɱ
( 𝒜, ★ ʂƚαɾ'ʂ ,ɯ ★ ϝ)
𝗔𝘀𝗵𝗮𝗻𝘁𝘆 𝗹𝗼𝘃𝗲.
"--𝐼 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑦𝑜𝑢 𝑤𝑖𝑡ℎ𝑜𝑢𝑡 𝑘𝑛𝑜𝑤𝑖𝑛𝑔 ℎ𝑜𝑤, 𝑜𝑟 𝑤ℎ𝑒𝑛, 𝑜𝑟 𝑓𝑟𝑜𝑚 𝑤ℎ𝑒𝑟𝑒. 𝐼 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑦𝑜𝑢 𝑠𝑡𝑟𝑎𝑖𝑔ℎ𝑡 𝑓𝑜𝑟𝑤𝑎𝑟𝑑𝑙𝑦, 𝑤𝑖𝑡ℎ𝑜𝑢𝑡 𝑐𝑜𝑚𝑝𝑙𝑒𝑥𝑖𝑡𝑖𝑒𝑠 𝑜𝑟 𝑝𝑟𝑖𝑑𝑒.
-- 𝑆𝑜 𝑖 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑦𝑜𝑢 𝑏𝑒𝑐𝑎𝑢𝑠𝑒 𝑖 𝑘𝑛𝑜𝑤 𝑛𝑜 𝑜𝑡ℎ𝑒𝑟 𝑤𝑎𝑦."
VOL/31-35
LAGOS.
The George Hotel.
Duk irin girma da kyau na wannan Hotel dake garin LAGOS wanda duniya tasan cewa is the most expensive hotel a LAGOS. Za kuyi mamaki cewa mutum d'aya ne ya yi booking gaba d'ayan sa daga shi sai masu tsaron sa da kuma ma'aikatan hotel dake ta kai kawo wajen bawa Babban VIP guest nasu kulawa yanda ya kamata ,dan ko shugaban k'asa Albarka.
Bakon kuwa da suke ta kai kawo a kansa da masu tsaran sa tunda ya shigo ko takarmin sa basu k'ara gani ba. Mata da maza duk sun rikice duk inda ka wuce za kaga sun had'a grp ana maida zancen sa da zuzuta masifaffan kyau da bakun nasu keda shi. Har chanza room service suke ko Allah zai bawa wani cikin su sa'a ya shiga d'akin sa dake can koluwar sama wato PENTHOUSE na hotel din su ganshi ,amma da zarar sun k'arasa wasu jibga-jibgan sojoji ne cikin bak'aken kaya da makamai fuska sanye da mask da hula suke tare su a gurin zasu bar kayan su shiga dashi.
Daga cikin d'akunan PENTHOUSE d'in yake zaune cikin guda da yafi sauran d'akunan girma. Don wannan shi ake kira da master bedroom yana dauke da katon office da kitchen ,kai harma da swimming full a corridor d'in sa dake d'auke da wasu cushions masu kyau .
Sanye yake da singlet irin mai yankakken hammata da dogon wando baki. Yana zaune kan wata kujera mai tsananin laushi kaman gado. Laptop ce kan cinyarsa yana dannawa .Yanda ya maida hankali kanta zai tabbatar maka da aikine yake mai matuƙar muhimmanci. Gefen sa wani k'aramin glass tebir ne an d'ora masa coffee cikin mug mai kyau sai zuba uban tururi yake ga wasu dankara-dankara wayoyi guda uku. Biyu k'irar Galaxy Fold d'aya kuma lastest IPhone ce. Gaban sa kuma wani k'aramin kushin ne mai tsananin laushi kaman gashin mage ya d'ora kafafuwan sa gaba d'aya a kai.
Hannu ya kai ya tura cikin coily hair nashi daya zubo gaban goshin sa duk ya yamutse kaman wanda ya tashi daga barci saboda yawan kai hannu da yake cikin gashin nasa yana ya mutsawa. Kafin ya sauke hannun ya kai kan farin glass dake kan fuskarsa daya zauna rad'am kan dogon hancinsa kaman bero ya tura shi saman manyan silver eyes nashi dake tattare da gajiya alamun rashin barci tattare dasu.
K'ofar d'akin aka kwankwasa yaja ajiyar zuciya a hankali ya d'ago yana kallon Adam daya sawo kai cikin d'akin riƙe da wata envelop. A hanzarce Adam ya k'araso ya yi saurin sarawa ya kame kam, yanda suke wajen bawa shugaban nasu girma kafin ya fara magana yana k'ok'arin miƙa masa envelop d'in dake hannun sa.
"Sir, kaman yanda kace munyi bincike kuma mun samu arrest warrant na shiga gidan wanda muke zargi, muyi bincike kan miyagun kwayoyin da yake safara dasu ,da kuma saka hannun sa wajen Human trafficking na ya'ya mata ana a kai su kassashen wajen don yin karuwan ci"
Shiru Adam ya yi yana jiran shugaban nashi ya bashi umarni ya cigaba. Laptop d'in dake kan cinyarsa ya ajiye kan kujera ya yunƙura ya miƙe fuskarsa dake d'auke da gajiya ta riƙede lokaci d'aya zuwa wani irin deadly expression da saida Adam ya had'iye wani yawu kutt yana kallon ogan nasa daya d'auki mug nashi ya d'an kurba ya yi wajen glass din corridor hannun sa d'aya cikin aljihun wandon sa.
Saida ya kusa shanye coffee d'in sannan yace da wata irin deadly authorative calm voice
"And?"
Cikin azama Adam ya cigaba da cewa
"Kaman yanda kace mu zuba idanuwa don sanin shige da ficen sa. Munyi nasarar samo shi a waje yana cinikin wasu miyagun kwayoyi da RUSSO shugaban MAFIA na k'asar MEXICO.don shigowa dasu Nigeria. Haka kuma mun samu inda suke b'oye yaran da suke trafficking suna fita dasu so b'oye can UGANDA kafin a kai su kassashen da suke a kai su. Umarnin ka kawai muke jira Sir"
"Good, set the plane we are leaving at midnight to ambush his house "
Sarawa Adam ya yi da k'arfi yace
"Sir, yes Sir"
Ya juya da sauri ya barshi nan da coffee a hannu fuskarsa d'auke da wani irin sinister look. K'aran da d'aya daga cikin wayoyin sa ya fara ne yasa ya juyo kaman slow motion ya zuba mata ido kafin ya taka da wata irin tafiyar Izza ya d'auki wayar dake ta ruru sunan POPS na rawa kan screen. Murmushi ya yi da yasa one sided Dimple nashi lotsawa ya d'aga wayan a kasalance ya kara a kunne yana kiran
"Pop" a hankali kaman mai rad'a. Wanda aka kira da hakan ya amsa daga d'aya b'arin
"My kitten how are you?"
Ya yi maganan cike da zolaya. A take ya wani kwab'e fuska kaman wani d'an k'aramin yaro sai kayi mamaki idan aka ce maka shine d'azu da wannan sinister look ya riƙid'e cikin k'ank'anin lokaci haka.
"Dad, stop calling me that? Am not a kid"
Ya k'arasa maganan yana pouting(zunbura baki). Y'ar dariya ce ta fito ta cikin wayar ya juya harshe zuwa hausa.
"To yi hak'uri Sojo na mazajen fama. Kaci abinci?"
A d'an shagwaɓe yace "No" Nan da nan ya rikice cike da damuwa yace "why? Me yasa har yanzu baka ci abinci ba? A lissafe kuma yanzu a Nigeria almost 10 na dare kenan"
Murmushi ya yi jin yanda duk ya rikice "Relax Dad, nasha Coffee kasan i don't like eating heavy food before bed,I'm fine don't worry please "
Ajiyar zuciya ya sauke "OK. Naji dad'i dai finally burina ya kusa cika. Kaje yanzu ka kwanta ka hutu dan nasan ka sam baka san hutu, I will call you tomorrow Alright?, I love you "
Kai ya d'aga kaman yana kallon sa" OK Dad ,I love you more "
Ido ya zubawa wayar bayan sun katse kiran murmushi d'auke kan fuskarsa soyayyar mahaifin sa yana jinta jini da tsoka. Banɗaki ya wuce kai tsaye don watsa ruwa..
♡︎♡︎♡︎
Yau tunda na tashi nake jin fad'uwar gaba kaman wani abu gagarumi na shirin faruwa dani amma saboda sawa raina da nayi zuwa wajen party d'in ban bari hakan ya dameni ba don naci burin zuwa. Wajejen azahar na fara shiri tunda Mamee ta amince naje. Kaya na cire na d'aura zani na fice don na shiga wanka na bar Marwah a daki tana ta zane cikin paper. Bandade ba na fito ina k'ok'arin shiga d'aki ya Aliyu ya shigo sanye da kakin sa na sojoji da sukayi nasa masifar kyau. Tsayawa nayi ina kare masa kallo tunda na taso ban taɓa yatsawa na k'arewa yan gidanmu kallo haka ba duk da irin zuzuta kyawun mu da mutanen unguwa suke.
Don har suna aka samana idan za'ayi kwatance da gidanmu, da Sadaka Yalla ake kwatance. Yaune naga tsantsan kyau da Ya Aliyu ke dashi da mata duk suke rububi a kansa. Fuskar ya had'e da dakakkiyar murya yace
"Kina da hankali kin fito daga wanka kin tsaya kin kallona?"
Baki na tab'e ai kaji wannan bak'in halin nasa shi yasa bana ganin kyan nasa.
"Ni ki ke tab'ewa baki?
Da sauri na wuce ciki ina k'unk'uni naji ya yi kwafa yana cewa "Allah ya nunamin ranan da zan kakkarya ki a gidan nan"
A zuciyata nace ba Amin ba. Ina shiga na tsaya turus ganin Marwah riƙe da jakata ga kuɗin nan a hannun ta . Sosai gabana ya buga amma na had'e rai na tawo da sauri na warce kuɗin da jakata Allah yasa bata ga hutunan dana sa aka yi ba.
"Kuɗin mene wannan?"
"Ina ruwan ki?, me yasa ne kina son shiga sharo babu shuni?, babu abunda ya shafe ki da kuɗi na bana san munfurci"
Banji tasowar taba sai kafad'ata da naji ta kama ta juyo dani ina fuskantar ta. Yau karo na farko naga b'acin rai kwance kan fuskar ta.
"Wlh idan baki gayamin kuɗin mene ba zanje na gayawa Mamee. Kuɗin menene wannan Sanaah waye ya baki?"
A zafafe nace "bazan fad'a ba ina ruwanki ?"
Ido ta zubamin sai kuma ta juya zata fice nayi saurin riƙe ta ina cije lebe ji nake kaman na rufeta da duka. Ajiyar zuciya naja nace
"Ranan dana dawo daga makaranta da kayana a b'ace ne....."
Na kwashe komai na gaya mata. Numfashi naga taja na relief ta sauke.
"To me yasa baki gayawa Mamee ba tuntuni?"
"Taya ki ke tunanin zan gaya mata ta yarda?, ni na ajiye sune dama duk ranan da Allah ya k'ara had'ani dashi na bashi kayan sa."
Kai kawai ta jinjina batace komai ta fice daga d'akin na sauke ajiyar zuciya ina godewa Allah daya sa bata ga hutunan ba. Shiryawa nayi cikin matsattsen wando da y'ar riga da rayi masifar kamani da kyar ta haura cibina na tufke gashin kaina na nad'e shi kaman ganmo na d'aura mayafin da zanza idan naje a kaina. Tsayawa nayi ina kallon jikina da irin kira da Allah ya bani da ko y'an uwana mata sai sun juyo sun k'ara juyowa bare maza. Ina da cikakken kirji da suke a tsaye cir kaman balloons. Cikina kuwa a mugun shafe yake kaman baya daukan abinci ya yinda kuguna yake a masifar buɗe hips dina gasunan tabarakalla abun ba'a cewa komai.
Cikin kwabar Marwah na d'auko dogon hijabi na d'ora da y'ar jaka ta ratayawa sai flat shoe mai yatsa daya shiga da kayan na fito nayi falo dan yiwa Mamee sallama. Samu nayi Marwa nayi mata kalba kan dogon gashinta dake nan har kugu. Duk da girma ya kama baisa gashin ya zube ba yana nan bak'i sid'ik dashi. Ina shiga Ya Aliyu na ìbnuuiu8kbjfrlw8'ok'arin fitwo nayi saurin kaucewa na bashi hanya saboda mugun kallo daya jefeni dashi. Kusa da Mamee na zauna ina cewa
"Mamee bari naje sai na dawo"
"Tun yanzu Sanaah ?. Allah ya kiyaye . Don Allah a kula sai kin dawo"
Da farin ciki na amsa da Amin na fito . Tunda na fito bugun k'irjina ya tsanan ta ban fasa tafiyar ba har na k'asara gidan su Zabina. Layin nasu kuwa ya cika da motoci na zamani tun daga farkon layin kake jin k'aran dj na tashi murmushi nayi na kutsa kai ciki harabar gidan ta cika da y'an mata da samari y'an duniya ana ta cashewa yawancin su riƙe suke da cup na glass wasu kuma suna can gefe suna zukar wani abu cikin wani dogo abu .
Gaba d'aya ido ya yi kaina duk sai naji na tsargu wani b'angare na zuciyata yana cemin na juya kawai na koma gida. Shawarar zuciyan nawa na d'auka na juya zan fice murya Zabina ta katseni .
"Sanaah "
A hankali na juyo ina kallon ta ta nufo inda nake sanye da wani gown iya cinya data matse ta mutuka mara hannu taci wani uban gashin doki ga takarmi mai shegen tsini a k'afarta. A guje ta k'araso ta rungume ni Blessing da Beelah biye da ita suma sunci kanan kaya dasu da babu duk d'aya.
"Kai amma naji dad'i da ki ka zo ina ta wasi-wasi wlh. Muje ciki kisha drink"
Jana suka yi muka shiga falon gidan ta zaunar dani kan kujera Beela ta kawo min lemo . Kad'an nasha na ajiye don sai nake ji kaman nayi kuskuren zuwa gida kawai nake son komawa. Haka na zauna na kasa sakewa d'aya bayan d'aya mutumen suka fara shigowa sai kuma fatin ya dawo cikin daki suna ta tirkar rawa ta rashin mutunci irin ta y'an iska .hankalina ya tashi don abune da ban tab'a gani ba yanda maza ke gugan mata sun saka su tsakiyar suna murgude-murguden duwawu.
Kasa jurewa nayi na yunƙura na miƙe Zabina tayi saurin rike ni.
"Ina zaki kuma ba'a gama party din ba ko cake ban yanka ba"
Kaina ta Sara saboda hayak'i da Blessing ta hura wajen fuskata nayi saurin toshe hanci ina cewa
"Na gaji ne gida zan koma"
"Haba kar ki bada ni mana. Kece fa kawata ta musamman da nake bawa kowa labari kuma daga zuwan ki sai kice zaki tafi ko cake ban yanka ba?. Cire wannan hijabin kisha iska"
Kafin nayi wani yunƙuri ta kama hijabina ita da Beelah suka fisge shi da k'arfi na juyo a fusace zan d'auke ta da mari aka bugo k'ofar falon da wani irin k'arfi sai gata warwas a kasa. D'akin ya rikice da ihu sakamakon wasu jibga-jibgan sojoji da suka sawo kai cikin kayan su na soja irin na turawa gaba da bayan su shak'e da makamai.
Wani irin bugawa k'irjina ya yi nayi saurin kai hannuna dafe ina furta' Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un' a fili cikin matsanancin tashin hankali. Hijabina nabi zan d'auko banyi zato ba naji an fisgo ni da mugun k'arfi na dawo baya kaman zan fad'i juyowar da zanyi ido na ya Fad'a cikin na Ya Aliyu.
Nashiga uku ni Sanaah. Matsanancin b'acin rai dake tattare dashi abun ba'a cewa komai. Mahaukacin b'arin makauniya ya d'auke ni dashi saida na wuntsula gaba d'aya na tafi kum na bige da bango. Ya k'ara fisgo gashin kaina da k'araji d'akin kowa ya shiga taitayinsa duk sun tsure mazan su da matan yace
"Uban me ki ke yi a nan?"
Ban iya cewa komai ba sai kuka da nake mai gunji kaina ya d'auki matsanancin ciwo. K'ara fisgata ya yi na tawo da baya ina ihu hannuna kan nashi daya riƙe gashina dashi kaman zai ciremin kai. Wani irin harbawa zuciya ta tayi lokacin da idona ya sarke da wannan piercing Silver eyes d'in masu matuƙar shek'i. Gaba d'aya fuskarsa rufe take da mask sai idon kawai ka ke gani da gashin sa ya kusan rufe su. Sanye yake da bak'ar riga data kama shi tsam kaman kirjin zai tsaga da bakin wando. Komai nawa ya tsaya cak na daina ji na daina gani bana ganin komai sai shi. Kallon da yake min ya yi shattering heart d'ina into million pieces.
Mamaki ne kwamce kan fuskarsa da kwayar idon sa ta nuna yana kallona kafin realisation ya yi down kan fuskarsa. Da alama sai yanzu ya gane kaman da muke da Marwah nan da nan wani irin kallon disgust da hate ya yi flashing kwayar idon sa da yasa naji kaman an sokamin mashi kahon zuciya daya tarwatsa ta. Tunda na ganshi tare da ya Aliyu hakan na nufin shine DEEN?. shine mutanin dana fara gani ya hanani sukuni. Shine yake neman auren Marwah bayan nice na fara son sa?. Me yasa fate yake barazana da rayuwata?. Is not fair..
Shar hawaye suka wankemim fuska duk dukan da ya Aliyu yakemin bana jinsa. Ciwon da zuciyata take yafi dukan da yake min wanda a yanzu Belt nashi ya cire ya rufeni da matsanancin duka kaman babu gobe bani kad'ai ba harsu Zabina da sauran mutanen dake k'ok'arin tserewa. Saida suka yi mana lis ko yatsa bana iya d'agawa haka ido na bai bar kan Deen dake tsaye ba kaman hoto fuskarsa a mugun turb'une baya ko motsi sai su ya Aliyu dake jibgar mu.
Babu abunda zuciyata ta furta min illar
" A karo na biyu mun k'ara had'uwa cikin yanayi na rashin sa'a. A karo na biyu na k'ara ganin tsanata k'arara kwance kan fuskarsa. Tsana da kuma kyama. Zuciyata batayi min adalci ba don yau na k'ara tabbatar wa da kaina na fara san sa ba tare dani kaina na sani ba . kiyayya da nake gani tattare dashi banji komai ba sai ma keyasta kyawunsa da zuciyata take. It's not fair... why me?"
Tsabar yanda hawaye ke gudu kan fuskata na fara ganin sa Dishi-dishi. D'ago kaina ya Aliyu ya yi na kalleshi sai lokacin naga wasu hawaye kwance kwayar idonsa na k'ara rushewa da matsanancin kuka yana kallona cikin kunci da disappointed look. Duk yanda nake son furta cewa abunda yake zargi ba haka bane na k'asa furtawa saboda ciwo da nake ji kasan zuciyata idan na tuna DEEN, MARWAH CE yake so da aure.
Kee ya Aliyu ya jani ya yi waje dani na kasa motsi jikina babu inda baya ciwo ga wani irin rad'ad'i da gadon bayana yake wanda nasan babu tantama ya fashe. Cikin mota ya wurgani na buge da murfinta bai duba ba ya shigo motar a zuciye ya tayar bai tsaya jiran Deen ba dana hango yana fitowa cikin wata izza hannuwan sa zube cikin aljihun wandon sa. Duk taku d'aya idan ya yi bugun k'irjina na karuwa.
sojojin sa suna biye dashi dasu Zabina dake a masifar tsororace. Kallon sa nake ina hoping ko sau d'aya ne ya kalleni amma har ya Aliyu ya fisgi motar a guje ya fice bai ko waiwayi motar ba na runtse ido