An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
𝓉𝒽ℯ 𝒻𝒾𝓇ℯ & 𝒾𝒸ℯ.
༄ZUBAR HAWAYE༄
𝗔𝘀𝗵𝗮𝗻𝘁𝘆 𝗹𝗼𝘃𝗲.
official pilot.
VOL/ 1-5.
𝑨𝑫𝑨𝑴𝑨𝑾𝑨 𝑺𝑻𝑨𝑻𝑬.
MAIHA.
"Sanaah, Sanaah. Ki fito mana kinsan fa mun makara"
Kyakkyawar yarinya ce ke magana sanye da uniform na makaranta dogon hijabin dake jikin ta har k'asa yake ja hannun ta riƙe da niƙaf da jakar makaranta rataye b'arin hannunta na hagu. Kallo d'aya za kayi mata ka hango tsantsan kyau da Allah ya bata. Farace tas kamar ka latsa ta jini ya fito. Tana da tsayi ba can ba zamu kirata tsaka-tsaki. Wato ita ba doguwa ba ita ba gajere ba. Tana da round face dake ɗauke da d'an ƙaramin lips da dogon hanci da manyan idanu da kwayar take bak'a siɗik da ita ga eye lashes nata daya kara kwata idon nata zara- zara dasu. Girar ta bata da cika sosai amma bak'ak'irin take.
Masha Allah duk da cewa hijabine a jikinta bai hana kaga tudun ƙirjinta ba da suka taso sosai. Muryar babbar macece ta biyo bayan ta tana fitowa daga banɗaki rike da butu a hannun. Kallo d'aya za kayiwa matar kasan cewa ita ce mahaifiyar ta saboda tsananin kama da suke kaman an tsaga kara har hasken nasu iri ɗaya.
"Au Marwah wai bata fito ba har yanzu? Ke Sanaah wlh ki ka bari na shigo na same ki sai jikin ki ya gaya miki. Na rasa wace irin yarinya ce ke da Sam kin ƙi jinin makaranta musamman ta addini. Kullum sai anyi dake ki shirya ki tafi makaranta?kece babba amma kina cin ƙasa ƴar uwar ki ta fiki hankali. Zaki fito ko sai ranki ya ɓaci ?"
Da fad'a sosai take maganan tana ƙoƙarin nufar ƴar ƙofa dake daya daga cikin ɗakunan gidan mai ɗauke da d'an tsakar gida da ɗan kitchen sai banɗaki. Ƙaramin gida ne sosai na rufin asiri. Kafin ta k'arasa ɗakin ta ɗaga labule ta fito sanye da kayan makaranta kaman na Marwah sai dai nata hijabin bai kai ƙasa ba iya gwiwa ne sai dogon wando .Saboda ɗan kaurin hijabin ne ya hana aga yar vest ɗin dake jikinta.
Tsakanin ta da Marwah sam babu banbanci sai haske da Marwah zata nuna mata don ita fatar ta irin brown ɗin nan ce mai tsananin haske har wani maik'o fatar take. Tafi Marwah doguwar fuska da dogon hanci haka nata idon a lumshe suke kaman maijin barci .Abun mamakin ita nata kwayar idon brown ce sosai saɓanin Marwah da nata yake baƙi. Sannan girar ta tafi ta Marwah cika sosai. Masha Allah da alama za tafi Marwah tsayi dan
doguwa ce babu laifi. A kumbure ta fito kaman za tayi bindiga tana ƙoƙarin sa takarmi.
Tsaki mai ƙarfi Maman tasu taja tana kallon ta sai kumburi take kaman bomb dake jiran fashewa.
"Iskancin banza da wofi ke dai kullum sai anyi dake kan makaranta. Yarinya ce ke ƙarama da ki ke so sai na goya ki na kai ki? Na rasa wace irin yarinya ce ke? Haka ki ka ga Marwah nayi ? Ta fiki hankali wai ke da sunan babba da take bi"
Hawayen bak'in ciki suka cika min ido. Mai yasa a kullum sai an had'ani da ita.? Marwah kaza, Marwah kaza. Yanda Mamee ke wannan fad'an sai ayi tunanin wasu shekaru masu tsayi na bata bayan ko wata ban bata ba a takaice ma ko kwana ɗaya ban bata ba sa'a biyu ce kawai tsakanin mu. Yes we are twin's amma ita ce the perfect daughter. Like maganan kowa a koda yaushe
KI ZAMA KAMAN MARWAH.
MARWAH TA FIKI HANKALI.
MARWAH TA FIKI KYAU.
MARWAH BATA DA FAD'A.
MARWAH TA FIKI HAK'URI.
Marwah, Marwah. Shikenan dai maganan a koda yaushe. Like very time da take ƙara proving maganganuna ta fara magana cikin wannan muryar ta ta mai tsananin sanyi dana tsana a koda yaushe.
"Kiyi haƙuri Mamee, inshaAllahu zamu gyara"
See, kunga abunda nake faɗa she's always trying to show she's the best a kan komai. Muguwar harara na watsa mata na wuce a zuciye na fice daga gidan zuciya ta na zafi. Na tsani idan ana haɗani da ita she's my twin amma muna da different personality . Like babu ta yanda za'a haɗa FIRE AND ICE guri ɗaya ba tare da an samu winner ba.
Yanda na fito a zafafe bana ganin gabana banyi aune ba sai ji nayi naci karo da mutum da sauri naja baya ina ƙoƙarin ɗaga kai naji an zubamin uban rankwashi da saida na kusa sakin fitsari a wando. Hannu na kai da sauri na dafe inda rankwashin ya sauka shar hawayen da nake riƙewa suka biyo kuncina. Ido na zubawa ya Ƙhamis dake tsaye gabana fuskarnan a turɓune. A kausasashe yace
"Matsa ki bani guri shashasha."
Wai me yasa ne kowa ya tsaneni a gidan nan? Mena tare musu? Muryar Marwah naji cikin sanyi tana cewa
"Sannu da zuwa ya Ƙhamis ina wuni?"
Murmushi naji ya yi mata mai sauti kafin ya bata amsa
"Lafiya lau Marwah. Kinga ita data fiki hankali tasan abunda ya kamata"
Ya ƙarasa maganan yana jifana da kallo mai kaman harara. Wucewa nayi ina sharar hawayen baƙin ciki. Ina jin sawun tafiyar Marwah bayana tana son ta cimma saurin da nake naƙi bata damar hakan. Magana tayi sai zuba haki take
"Sanaah ki tsaya mana don Allah mu tafi tare kinsan ban iya sauri ba"
Yanda kasan na juya na ɗauke ta da mari haka naji . Ƙwafa nayi na ƙarawa tafiya ta sauri kaman zan kifa. Ina karya kwana layin makaranta na hango ƴan makara da Mal Sule ya jera sai jibga yake kaman ya samu ƙarfe. Jibgegiyar dorinar dake hannun sa na kalla yanda yake ɗaga ta da iya ƙarfin sa yana zubawa daliɓai. Babu shiri naci burki ina tunanin ƙaryar da yau zanyi na tsira. Duk wacce tazo kaina sai naga bata gamshe ni ba. Marwah ce ta ƙaraso tana haki nayi saurin kallonta ina tunanin abin yi. Kai ta girgiza alamun ta gane munufata taja numfashi mai ƙarfi ta fesar.
Saurin janta nayi muka faɗa ɗan wani soro dake kusa damu na tsayar da kwayar idona cikin nata fuskata a tamke. Wani Numfashin ta ƙara ja ta fesar tana cewa
" Shikenan zanyi yanda ki ke so amma ki sani ba kullum ne irin wannan shirin naki zai tafi daidai ba"
Baki na taɓe nace " idan baza kiyi bane kice baza kiyi ba ,dama ai ba tun yau nasan son da ki ke min na ƙarya bane"
Wani irin dafe ƙirji tayi tana kallona idon ta rau-rau kaman zatayi kuka. Kauda kai nayi ina taɓe baki a zuciyata nace munafuka. Cire niƙaf ɗin tayi ta miƙo min na karɓa da sauri na cire hijabin dake jikana na bata ,na karɓi nata nasa na ciro nawa niƙaf ɗin daga jaka na bata ta sanya. Nasan za kuce mene hakan kuma? Wannan kaman charm work ɗina ned uk lokacin da nake son kuɓuta daga dukan Malam Sale ,Marwah taje a madadina. Zakuyi mamaki idan nace Sam baya ganewa tsabar toshewar basira irin tasa. Yoo in banda haka kowa yasan na fita tsayi amma ba chan ba.
Abunda yasa nake hakan saboda kowa yasan Marwah bata da wasa kan makaranta. Zancen da nake ma headgirl ce shugaban daliɓai. Ita ke kula da shige da ficen daliɓai da tsaftar su. Shi yasa kafin kowa yazo makaranta ita ke fara hallara ita ce kullum first ɗin zuwa. Hakan kuwa yasa nake cin karane babu babbaka sai naga dama nake zuwa makarantar . Sai na fito gida da zummar na tafi islamiya na wuce yawo abuna. Abun ya kai saida aka je gida tambayar abunda ke hanani zuwa makaranta Ya Ƙhamis ranan ba ƙaramin duka ya yimin ba shi yasa Sam bama shiri dashi ɗan abu kaɗan zai buge ka. muguntar sa tayi yawa.
Tun daga ranan ne Baffa yasa muke tafiya tare da Marwah amma wannan matsolamin Malamin saboda rashin imani irin nasa gashi dai tare muka zo sai dai ya dakeni ni kaɗai yace wai nina ke makarar da ita tunda kowa ya yi shedar bata makara saida aka ce mu dinga zuwa tare. Tunda naga haka wani lokacin nake sata karɓan dukan a madadina ai bani na sa ta jirani ba.
"Sanaah ina rigar makarantar na ganki da shimi?"
Maganan ta ya katse mun tunanin da nake nayi saurin kallon jikina na ɗago a yatsine ina kallon ta nace
"Banga damar sawa ba"
Ido ta zubamin tana jan numfashi daya zame mata kaman gado ta fesar(sighing). Kai kawai ta girgiza bata ce komai ta saka niƙaf ɗin ta fice na bita da harara haɗe da tsaki kafin na saka niƙaf ɗin na fice nima da sauri na cimmata. Muna ƙasarawa kuwa Mal Sale ya tare ta yana kollana yace
"Hala yauma saida aka yi da ita tukunna ta shirya ku ka tawo?"
Muryata na gyara sosai yanda za tayi kama da ta ta nace
"Eh Malam "
"Ai na sani. Wato ke baza ki fasa halin ki ba ko? To ni daidai nake dake in dai a kan rashin son makaranta ne zan dinga sawa har gida ana ɗauko ki. Wuce ki shiga Aji Marwah"
Bance komai ba na wuce zuciya ta fes ina kallon yanda ya daga bulalan ya zuba mata ajiki guda uku kwarara kafin yace ta wuce. Da sauri nayi hanyar banɗaki kaman yanda muka saba ina shiga itama ta shigo. Kallon ta na tsaya yi yanda take yin komai a sanyaye ga idonta cike da kwalla ta hanasu zubowa. Sai naji tausayin ta ya ɗan kamani amma ban bari ya nuna kan fuskata ba na cire hijabin ta da niƙaf nata na bata ,ita ma ta cire nawa ta miƙo min nasa na fice na bartanan tana ɗaura niƙaf sai wasi-wasi nake cikin raina .
Haƙurin Marwah ya yi yawa. Yawa irin wanda ake cewa cuta ne.
𝓉𝒽ℯ 𝒻𝒾𝓇𝓇ℯ & 𝒾𝒸ℯ.
༄ZUBAR HAWAYE༄
𝒜ɱαȥιɳɠ ★'★ ɯɾιƚҽɾʂ ϝσɾυɱ
( 𝒜, ★ ʂƚαɾ'ʂ ,ɯ ★ ϝ)
𝗔𝘀𝗵𝗮𝗻𝘁𝘆 𝗹𝗼𝘃𝗲.
"--𝑌𝑜𝑢 𝑑𝑒𝑠𝑒𝑟𝑣𝑒 𝑎 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑡ℎ𝑎𝑡 𝑤𝑜𝑛'𝑡 𝑘𝑒𝑒𝑝 𝑦𝑜𝑢 𝑢𝑝 𝑤𝑜𝑟𝑟𝑦𝑖𝑛𝑔.
-- 𝐴 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑡ℎ𝑎𝑡 𝑓𝑒𝑒𝑙𝑠 𝑙𝑖𝑘𝑒 ℎ𝑜𝑚𝑒.
-- 𝐴 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑡ℎ𝑎𝑡 𝑖𝑠 𝑐𝑒𝑟𝑡𝑎𝑖𝑛.
--𝐴 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑡ℎ𝑎𝑡 𝑚𝑎𝑘𝑒 𝑠𝑒𝑛𝑠𝑒. "
Vol/6-10
Kai tsaye gurin zamana na nufa na zauna kusa da babbar aminiyata Harira. Karatu suke mura'ija amma shigowa ta kowa ya yi shiru har Malamar mu Zainab duk suka zubamin ido har na zauna.
"Wato ke dai Sanaah baza kiji magana kan makara da fashi ba ko? Me ki ke so nayi miki ne da zai sa ki shiga hankalin ki dan naga duka yanzu ba komi bane a wajen ki"
Kallon Malama Zainab nayi ,nayi far da ido cikin rashin damuwa da maganan ta nace
"Ki yi haƙuri Malama ba laifina bane"
"Au to laifina ne kenan ko?"
Shiru nayi ban bata amsa ba ina cije lebe dan hana maganan dake kan harshena fita, in har ta fito fili to tabbas sai rai ya ɓaci. Ƙwafa taja ta gyara zama tana kallon ƴan aji da bada umarni a cigaba da karatu. Qur'anina na ɗauko nima na buɗe ina kallon inda suke yi don ba iyawa nayi ba tunda ban maida hankali ba sanda ake yi. Saida aka yi wajen shafi huɗu kafin a dakata saboda Lokacin sallan la'asar daya gabato.
Muna fitowa Sallah Harira ta iske ni wajen alwala.
"Wai yauma Marwah ki ka sa ta karɓi dukan makara?"
Kallon ta nayi bance komai ba saida na idar da alwala na miƙe ina cewa
"Me ki ka gani? Ita ta gaya miki?"
Girgiza kai tayi tace "Na ganta ne tana alwala a keɓan ce data cire hijabin naga kaman jini a rigar ta nasan kuma duka ne yasa"
Har cikin raina naji wani iri nayi jimm ina tunani. Ganin hakan yasa Harira ta girgiza kai ta karɓi butar dake hannuna
"Ya kamata ki daina sata tanayi miki komai Sanaah duk ranan da aka gane hakan kinsan akwai matsala. Malam Sale bazai kyale ki ba bare Ya Khamis da Ya Aliyu."
Haushi ya kamani a zafafe nace
"Idan kin fara goyon bayan ta ne kawai ki faɗa min ba sai kin tsaya kina kunbiya -kunbiya ba"
Murmushi tayi mai cike da damuwa ta girgiza kai ta wuce tana taran ruwa. Ido na zuba mata ina karantar ta. Duk da ƙoƙarin ɓoyemin da take na karanci damuwa sosai tattare da ita.
"Meke damun ki ne duk na gan ki wata iri?
Kallona tayi sai shar ga hawaye sun biyu kuncinta. Riƙo hannun ta nayi nace
"Menene? Meya faru?"
Kuka ta fashe dashi sosai tana sheshsheƙa tace
"Wai Zubair ne zaiyi aure kuma wai Khadija zai aura"
Ido na zaro ina ƙara maimaita sunan Khadija.
"Khadija , Khadija dai dana sani? Khadija fa ƙawar mu?"
Kai ta ɗaga tana kuka sosai. Abunda na tsana a rayuwata shine cin amana. Cin amanan ma ta rashin mutunci ka yarda da mutum ya daɓa maka wuƙa ta baya. Khadija kawar muce ƙud da ƙud. Mu ukun nan tamkar ƴan uku haka muke har kiran mu ake da ƴan uku don duk inda kaga ɗaya to za kaga ɗaya. Zubair saurayin Harira ne da dukkanin mu babu wanda bai sani ba har gidan su yaje kuma an bashi izini da tuni ma ya tura magabata to kuma sai aka samu jinkiri saboda yanayin aikin sa na ɗan kasuwa yau yana can gobe yana can aka ɗan jinkirta sai ya dawo. Ƴar iskar yarinya nan ashe ta zagaya bamu sani ba? .
Ni dama tunda Harira take cemin wannan dawowar tasa gaba ɗaya ya chanza mata bai cika kiranta a waya ba kaman yanda ya saba ko yazo zance gurin ta sai ta kirashi ya yi bata uzuri. Tun daga lokacin na fara tsarguwa da lamuran sa. Har ita Khadija muke zama muyita bata shawara ashe ta maida mu yan iska. Akwai bala'i kuwa don ta tabo Wuta wlh sai inda ƙarfina ya ƙare. Nifa shiya na tsani soyayya kai su kansu mazan na tsane su don gaba ɗaya kallon mugaye, azzalumai nake musu saboda ya Ƙhamis da ya Aliyu.
Nayi zargin ko wata ya hango can inda yaje yake neman yakice Harira wlh ban taɓa tunanin butulcin nashi ya kai nan ba daga shi har ita Khadijan. Ai kuwa sun taro March.
"Yaushe ne bikin nasu?"
Na jefa mata tambaya . Majina ta face ido jajur tace
"Nan da sati huɗu wai"
Wato shi yasa ta ƙaurace mana kwana biyu ko gidan su muka je bata nan tana can wai gidan kakannin ta Gombe. Kai na girgiza na fito da ƴar ƙaramar torch wayata nace ta bani number sa. Bata musa ba ta bani na kwafe ina ƙwafa.
To koda aka tashi banbi ta kan Marwah ba nayi gida abuna da tunanin shirin da zanyi na wargaza auren Khadija sai tayi nadamar butulci da tayi. Ƙofar gida na hango Baffa zaune kan tabarma kaman yanda ya saba da yamma yana bin littattafansa na addini. Gabana ne ya yanke ya faɗi hango ya Aliyu da nayi zaune kusa dashi cikin kakin sa na sojoji. Ya duru ƙasar kenan? Innalilllahi. See duk irin muguntar ya Khamis ya Aliyu ya kereshi ya shanye shi babu wasa ne cikin lamarin sa kullum fuskarnan a turɓune take babu annuri.
Tafiya ta na ragewa sauri ina tararradin ƙarasawa gurin su. Kaman ance ya ɗago kuwa idon sa ya faɗa cikin nawa. A take ya ƙara haɗe fuska yanda kasan gobara. Duk iskancina ina shakkar sa saboda shi na tsani dukkanin wani soja da irin labarai da nake jin wajen rashin imanin su. Dan ya Aliyu ƙarshe ne wajen mugunta.
Jiki babu kuzari na ƙarasa ban yarda mun ƙara haɗa ido ba. Durkusawa nayi kusa da Baffa kaman mutuniyar Arziƙi ina Gaida shi. Littafin dake hannunsa na kawa'idi ya rufe ya ɗago yana kallona sosai fuskarsa ɗauke da murmushi daya ƙara bayyana kyawun sa.
"Lfy lau HASSANA, kin taso? ,ina ƴar uwar taki?"
Kafin na bashi amsa na hango Marwah ta karyo kwana cikin tafiyar nan ta2 ta sanyi na sauke ƴar ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. Ta gefen ido na kalli Ya Aliyu da nake jin idonsa kaina kaman yana ganin ruhuni. A hankali nace
"Ina wuni ya Aliyu an sauka lafiya?"
Bai bani amsa har Marwah ta ƙaraso itama ta durkusa kaman yanda nayi tana gaida Baffa kafin ta juya kan ya Aliyu. Da dakakkiyar murya yace
"Lfy"
Daga haka bai ƙara cewa komai ba, haushi ya kamani nayi saurin miƙewa zan shige gida a fakaice na watsa masa harara ,cikin rashin sa'a kuwa ya gani da gudu na ƙarasa shigewa gida na tarar Mamee na tanƙaɗen garin masara. Kallona tayi fuska babu walwala tace
"Sarkin ƴan hankali kin shigo min gida ƙerere babu sallama kinja kin tsayamin a ka"
Da sauri nace "sannu da Gida Mamee"
Bata amsa ba sai kai data girgiza ta cigaba da tankaɗen ta. Marwah ta shigo bakin ta ɗauke da siririyar sallama ta ƙarasa gurin Mamee da sauri tana cewa
"Sannu da gida Mamee kawo na taya ki"
Mugun kallo Mamee ta watso min kafin ta juya kan Marwah tace
"Barshi Marwah jeki hutu na kusa gamawa ai"
Badan taso ba ta miƙe ta shige ɗaki nima nayi saurin binta saboda harara da Mamee ke zubamin. A kullum sai ta janyo abunda za'ace ta fini hankali da sanin abunda ya kamata. Kunga ashe idan ina jin haushin ta banyi laifi ba.
Muna shiga ta hau cire kayan makaranta dake jikinta na samu damar ganin ciwon da Harira ke faɗa .Ido kwai na zubawa bayan nata tana nannaɗe dogon gashinta tsakiyar kanta kaman donut. Kauda tunanin abunda ke raina nayi ,nayi saurin wucewa na cire nawa kayan na chanza zuwa riga da wando. Yar ƙaramar shirt data kamani da dogon wando jeans da shima ya kamani sosai ko numfashi bana iyayi mai kyau. A rayuwata ina san ƙananan kaya duk kayana kaɗan za kaga riga da sket. Suma sai na tabbatar wanjen ɗinkasu anyimin su tsam jikina sawa da kyar cirewa da kyar.
Ban saka hula ko ɗankwali ba na fito bayan na tufke gashin na na saki jelar ta sakko har Mazaunai na. Kallo ɗaya Mamee tayi min ta girgiza kai alamun gajiya da yimin magana .Tabarma na ɗauko na shimfiɗa mana nan tsakar gida kaman yanda muka saba na zauna ina latsa wayata. Fitowa Marwah tayi sanye da doguwar riga mai fadi baƙa da mayafin ta data ɗaura a kai. Kusa dani ta samu guri ta zauna tana jan Mamee da hira. Kaman saukar aradu naji Muryar Ya Aliyu cikin tsawa
"Ke"
Daga ni har Marwah muka ɗago da sauri muna kallonsa cikin kowa ya ɗuri ruwa. Idon sa kyam a kaina cikin fushi yace
"Zaki tashi kije ki canza wannan kayan ko sai nazo na baɓɓalla ki a nan?"
Jiki na rawa na tashi da sauri na shige ɗaki ina ƙunƙuni. Shikenan fa yanzu tunda yazo mutum bashi da sakewa. Kayana na cire na ɗauko wasu riga da sket da suma suka kamani sosai na ɗora ƙaramin gyale na fito ina raɓe-raɓe . Wani irin kallo ya watsomin shida ya Ƙhamis da naji shigowar sa bayan na shiga d'aki.
"Ka gani ko ya Aliyu, ai bata jin magana duk kayan ta haka suke. In anyi dukan anyi faɗan kaman ma kara tunzura ta ake"
Wani irin vein ne naga ya fito saman goshin sa da duk lokacin da yake cikin matsanancin ɓacin rai zaka ganshi. Cikina ya ƙara ɗurar ruwa na tawo a ɗaɗare na zauna kusa da Marwah . Daga Mamee har Marwah babu wanda yace komai bare suyi yunƙurin kare ni. Wata gigitacciyar tsawa ya ƙara dakamin na ƙara razana idona suka cika tab da hawaye.
"Don ubanki ba magana nake miki ba? , kar ki kuskura ki bari na tashi da ganan ki wuce ki ƙara chanza wasu"
Muryata na rawa kaman zanyi kuka nace
" wlh yaya haka kayan nawa suke"
"Haka kayan ki suke? Mamee kina kallo ki ka barta ake mata wad'annan shegun kayan"
Ya juya kan Mamee data ja ajiyar zuciya
"To ya zanyi da ita Aliyu? Kunnen ƙashi ne da ita nayi dukan, nayi faɗan taki ji. Bansan me take son nayi mata ba don haka nasa mata ido kawai ,saboda ita kaɗai bazan sawa kaina ciwon zuciya ba"
Wani irin tasowa ya Aliyu ya yi kaina na fashe da kuka ina neman hanyar tsira.
"Ash,Ash Aliyu mazan