Dr ba buƙatan wannan Injection ɗin! *Keep him under anesthesia"* wani kalan waro idanunsa waje Dr John Amaan yayi cikin kamilallen English ɗin daya gama riƙa a bakinsa ya furta.
"Amma His life'd be in danger if we give him an overdose I can'ttake that risk, don haka ba zanyi mata wannan allurarn ba" Wani shegen murmurshi Dr Masheer yayi saying tare da furta "Do as I say?" Kallonsa da jajayen idonsa da suka surku da ɓacin rai Dr John Amaan yayi tare da furta. "Watch and See, it will be really fun and hilarious, Maheer reshe ne zai juye da mujiya kikayi kuma ya koma kan masheƙi,don baka san match ɗin da kake shirin taroma kanka bane. Kasan kuwa ita ɗin wacece? Kasan kuwa ko su waye Asalin JEDAANS!!!?"
Tsaye Maheer ya miƙe tareda murtuke fuska ya furta "Enough... Enough is enough! Enough of it Mana kada fa ka nemi raina min wayo anan john kaine ma wato zaka faɗa min ko su waye JEDAANS ɗin?, To ƙarewanta daga tacan familyn JEDAANS ɗin ne aka bani maƙudan kuɗaɗe dan kawai na kawar da rayuwar yarinyar"
"Uhmmm kaifa Maheer na gama lura baki ɗaya baka san zuru ba"
Ɗan ware idonsa Maheer yayi tare da furta "Lallai ba shakka kuwa da dukkan alamu kaima wani daga cikin su ya maka tayin babban kamu ne duk yacce akai" Shima cikin ɓacin rai da ɗaga murya cike da ihu yace.
"But you are the causer Maheer bcoz at ever never naci amanan wani Kona ha'ince woni"
Da sauri Maheer ya ɗan girgiza kai tare da kwantar da murya yana furta
"Cool down John please ni nasan hanyar da zamu bi muyi handling ɗin yarinyan ba tare da barin wata ƙofar da za'a iya zargan woni abu ba kawai mu fara aikin"
"Maheer zaka fara ko? Okay then mu buga wasan aka wanda zai cin ye" ♡ A can masauƙin su Prof Sameer kuwa suna isa aka shige dasu wani lafiyayyan parlour'n jira ko wannensu zama yayi cikin yanayi mara daɗi da yanayi na cunkushewar zuciya. Prof ne ya fara miƙewa tare da dauro alwula ya fara kai kukansa ga mahaliccin sa akan neman sassauci daga garesa, ganin hakan ya sanya ita ma Maah tashi ta fara gabatar da nata duk da bata a mood me daɗi, ko wannensu da abinda zuciyarsa ke saƙa masa.
♡
Around 5:15
Bayan kusan kwanan tsayen da sukai akan Meesherh suka samu numfashin ta ya yakawo sau ɗaya. fitan su da kamar 15 minute wata muguwar ƙara ta karaɗe iyaka room ɗin da Meesherh take. Hakan ya sanya a guje duk wasu manyan dactor's sukai room ɗin a guje. Turus John Amaan ya tsaya yana kallon Maheer dake tsaye kan Meesherh wacce kallo ɗaya zaka mata indai kai cikakken dactor ne kasan cewan tabbas babu numfashi tare da ita.
♡
Kallon me kake nufi John yake ma Maheer Scowl ɗin dake fuskarshi yana ƙara zurfafa, da kuma fuskan mamaki John ɗin ya ɗora da faɗin. "Maheer me ne kai ma patient ɗina?"
Da kalan kallon Mamaki da kuma rainin Hankali Maheer ke jifan John tare da kuma da furta "What is with the look? Kana mun kaman baka san da komi ba? Bayan kuma kaine kace mu buga wasan, toni yanzu ne nawan ya soma don haka in kana dawowa da wanda ya riga ya sheƙa numfashi seka dawo mata dashi ba iyaka allurar anesthesia na mata ba harda crecenial risk na mata" Girgiza ma Maheer kai John yake yana ja baya. A cikin zuciyar kuma yana tabbata lallai duk inda ƙarshen mara Imani yake to kuwa ga babansa don a yau ya sake tabbatarma da kansa cewan Maheer samm baya da zuciya a cikin ƙirjinsa, don ko shi da yake Christian wllh ba zai taɓa iyama ko dabba bane wannan allurar. Cikin wannan goggagan turancin irin wanda se a ƙasar turawa kawai zaka iya jinsa,Dr John Amaan ya juye baki da muryarsa mai tafiyar da yannayin halitar zafin sa kai tsaye irin na ƴaƴan arna ya shiga balbale Dr Maheer da ruwan masifa, domin dama Maheer ya daɗi yana musu irin wannan ɓarnar don kawai saboda wasu ƴan kuɗaɗe da yake amsa. Abu ɗaya ne kawai ya Dr John Amaan ke rufa masa asiri shi ne tsoratamar hukuncin ƙasar su da yake. Amma yanzu tunda shi bai san zuru INSHA ALLAH daga kan wannan patiend ɗin ba zai sake ƙoƙarin aikata woni kuskuren ba. Don haka ya bama Dr *Randeep Hooda* da *Dr Jackie Shroff* umarnin su kama Maheer ɗin. A natse cike da cikata aikin ogansu a fannin aiki suka sanya ƙiran Hukumar Asibitin suka zo suka tafi da Maheer ɗin. Amma dake ɗan bala'i ne memakon kaga ladamar hakan a ransa sema baki da ya taɓe tare da kallon Dr John ɗin yana furta masa zasu haɗe.
Kallonsa shima yayi tare da sauran ma'aikatansu da yannayi na Expression ɗin fuskarsa ya furta
"Ban sanya an kama ka don aikata S0n raina bane maheer, kawai dai na yi mamaki ne a matsayinsa na jinin Musulmai kuma a same ka da aikata babbar ɓarna irin haka wajen taɓarɓare addininku, da kuma rugujewar tarbiyar irin ta ƴayán Hausa. Musulunci'n da ya riga da ya gama gina tarbiyyar ƴaƴansa wanda har sauran wasu yaren ke sha'awan shiga cikin ku, saboda yadda tsarin addinin Musulincin ke burge su, to kuwa tabbas irinkune masu danne niyar masu son musulinta da masu muguwar zuciya irin taku"
Ya ajiye maganarsa hankali kwance yana ƙoƙarin ganin ya haɗa wata ruwan allurar da iyaka ita kaɗai idan kaji kuɗinta kan ruguza ƴaƴan hanjinka. Kana ya buɗe wata na'urar computer'n da suka gama rufewa a ɗazun. Kasancewarsa babban likitan da ko a sauran ƙasashe ji ake dashi ya fara sarrafa wasu abubuwa daga cikin ta. tsari irin na wanda ya gama laƙantar abin ya shiga sarrafa ta,seda ya ɗauka wasu lokuta masu ɗan nauyi kana ya rufe yana sharce zubar data gama jiƙa gaban goshinsa wata ƙatotuwar damuwa na rufe shi.
Kusan a tare Prof Sameer da kuma Maah suka miƙe tsaye ƙirjinsu na wani irin bugawa, jin wannan ƙarar data karaɗe ilahirin cikin Hospital ɗin.Allah sarki cike da raunin rai dana ruhi suka kalli juna sai dai duk cikin su babu wanda ya iya furta wani abu. Kai tsaye suka nufa room ɗin zuwansu daidai loƙacin da kunnuwan Maah da papiey suka jiyo masu wannan mummunan tashin hankalin. A take anan Maah ta zube sumammiya cikin sauri nurse's suka dauketa suna shiga wani room na daban da ita.
A hankali Maah shiga buɗe idanunta da take kallon komi dishi dishi.
Hannunta ɗaya ta ɗaga da ƙyar ta kamo na Prof Sameer wasu zafafan hawaye na silalo mata daga cikin idanunta. Cikin rawar murya ta shiga furta ,"Da gaske mun rasata ko? Da gaske mun rasa Meesherh ɗin mu ko" sai kuma ta taci gaba da hawaye tana ɗan jujjaya kanta.
Ƙasa papiey yay da kansa shima hawayen na ƙoƙarin ciko nasa idanunn. dan baya da tabbacin Meesherh ɗin tana a raye ne ko a mace,Cike da matsanancin tausayin kansu da kansu ya zame hannunsa daga cikin na Maah ɗin ya miƙe. Saurin riƙosa Maah tayi tana girgiza masa kai. "Please Prof ka faɗamin gaskiya wllh ba zan yi komai ba bazanyi kuka ba kaji na rantse ko? Wllh ka faɗa min gaskiya ba kuka zanyi ba"
Kai papiey ɗin ya shiga girgiza mata cike da damuwa ya shiga faɗin. "Basu ce mana komai ba har yanzun Mamamsu. Tun da aka kawo ki nan suka sake komawa ɗakin har yanzu basu fitoba kuma.... Tun kafin ya ida maganar Maah ta miƙe da sauri, Sai dai ta yi saurin komawa zaune tare da dafe kanta da hannuwanta saboda tsananin sara matan da yayi. Saurin riƙota papiey yayi yana me furta "Please cool down Maah"
Kanta ta ke jujjaya masa tamkar kuma wacce aka zaburo ta furta, "Bazan iya ba Papiey'n Meesherh inaso zanje na ganta ne a duk yanayin da take a ciki zan iya jurewa Meesherh ta kawai nake da buƙatar gani a halin yanzu!"
Duk yanda papiey yaso Maah ta haƙura taƙi ta saurarensa sam, dole ya taimaka mata suka fito a ɗakin da aka kwantar da ita tana dafe da kanta,Sai dai dole a ƙofar ɗakin aka tsayar dasu kasancewar doka ce babu me shiga se nan da farfaɗowan patient din. Wani ɗan abu dake a jikin Computer ɗin dake maƙale a bangon ɗakin ɗaya daga cikin dactor's ɗin dake zagaye da wurin ya danns, seda ƙofar ta ɗauka kamar mintuna uku zuwa huɗu haka kana ƙofar wata gilashi ta zuge. A kwance duk suka hangota harma tafi sanda suka kawo ta kyan gani sosai. Ai daga papiey har Maah babu me ƙarfin zuciyar da a cikin su ya iya tare hawaye da suka zuba musu.
Da ƙyar suka shiga ringa ja da baya ƙafarsu na musu nauyi tsoro da fargaban rasa Meesherh ɗin na sake riskarsu. A tare duk Doctors ɗin suka juyo suna kallonsu domin abin a tausamane. Don su gani suke sun ma gama yarda kawai sun ma rasata ne, Dan haka duka su biyun suke tafiya da baya da bayan hawaye naci gaba da gangaro musu a saman fuskokinsu. A hankali Dr John Amaan daya fito ya tsaya Cak da ga yunƙurin fitowa daga cikin room ɗin da yake, Sai kawai ya tsinta kansa da kasa juyowa ya haɗa ido dasu. da ƙyar ya iya ƙaƙaro murmushin yaƙe yana samun kwarin gwiwan nufosu murmushin ɗauke a saman fuskanshi. ✯
"Smiles pls INSHA ALLAH PATIEND namu a koda yaushe zata iya farkawa kuma cikin hankalinta ba tare da wota damuwa, kawai ku taya ta da adda'an ku" Yay maganar yana jin kwarin gwiwan yin hakan kodan ransu ya kwanta.
✯
"Amma John nake kallon kamar ka bar maganan Maheer haka nan" yay maganan Slowly yana duban John ɗin. Kasancewar sa shi mutun ne me tsananin riƙo da gaskiyar sa da kuma amana ya sanya sammm baison yaga woni na aikata ba daidai ba kuma ya iya kyalewa, Yabi Maheer da nasiha akan ya dena wancan banzan halin nashi amma ya ƙi denawa don haka yake jin a wannan karon dole a nunama kurciya baka ko ta shiga taitayinta. Hannunsa ya cira may tare da furta ✯ " Kaga raina a bace yake Randeep. Don't just don't wllh Raina bazaiyi sanyi ba Randeep har se na kalla an hukunta duk wasu masu hannu a cikin wannan case ɗin. Dr John ya faɗi yana jin ze iya Shari'a da kowa akan Ahalin JEDAANS.
Mayar da bakinshi yayi ya rufe yana bin John ɗin da kallo don yasan ko waye shi akan riƙo da ɗabi'unsa. Haka harya ɓace ma ganinsa sauƙe numfashi Dr Randeep yayi badon maganar daya faɗi ɗin ba har ransa ba shima.
Acan ɓangaren su Maah kuwa da kyar suka kai kansu room ɗin da suke cikin kwarin gwiwa da kuma ƙarfin zuciyan da Papiey'n yafi Maah ya dube ta tare da furta........
To ai shikenan semu bari mu haɗe a page na gaba, don wllh hannuna ya gama nuna da ɗan banzan ciwoooo.
*BY AMMEY LAYLARH ✍️*
*༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻*
_𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _
♡
𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ
_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_
𝙋a𝙜𝙚
15&16
https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D
✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫*
(J.W.A)
♡
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
Waɗanda suke buƙatar samun litattafan *AMEEY LAYLERH* za ku iya shiga shafin ta na Telegram don samun su kai tsaye daga wurin ta.
Ga link nan ga masu buƙatar shiga
👉https://t.me/ammeylaylerh_novel
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
"Ita Rayuwar duniya da kike kallo tana iya juyama ko wanne baya ajin da yake tamkar yacce Rayuwar mutane ita take iya sauyamana a duk lokacin datay niyar sanjawar, People change, things go wrong. Just remember life goes on Sauyi na rayuwa yakan zo loƙaci ɗaya ne. Wasu loƙuttan kuma sauyin kan zo ma na da yarin ƙalunale n rayuwa ne. No one is born with Positive Passion. This Power is ignited by Inspiration!Komai na da alaƙa da yanda tsarin ƙaddararmu take. Ko yatsun hannuwanmu idan kika duba suna da banbanci da junansu. Saboda me mu zamu tsaya ɓatama kanmu loƙaci wajen ja da kaddararmu data zamo iri ɗayace. Gode wa ALLAH ya kamata muyi yayin samu ko rashi. Don bamu isa ja da hukuncin Ubangiji ba, Amma idan mukai haƙuri Allah na tare damu a ko wanne yanayi adda'an mu SAMEESHERH take da buƙata bawai kuka ba!!. Silalewa a wurin Maah tayi hannuwanta da ƙafafunta na rawa ta zame ƙasa tana son tayi koda numfashi me ƙarfi ne amma ƙirjinta ya toshe ya tsaya mata cak wani abu me nauyin gaske na danne mata ƙirji zuwa maƙoshinta. Paah kuwa Idanuwansa ne suka wani irin ja yana kasa hana hawayen sa zuba sosai shima.A cikin su biyun duk aka rasa me rarrashin wani ko me be wani kwarin gwiwa a cikin su, domin kuka suke sosai suna haɗe kansu a wuri guda suna riskar kuka, cikin kukan Maah take furta "Meesherh dan ALLAH karki tafi ki barmu kece sanyin idaniyanmu ya Rabb ka kawo mana ɗauki Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ³" Jajur idanunsa suka se a yanzu ma yake tunowa da gida dan haka kai tsaye woyan sa ya ciro yana ƙiran babban yayansa thabit Jedaans.
Sanar musu yay halin da ake ciki suma se hankalinsu duk suma ɗin ya tashi don haka suna yanke woyar a washe garin ranar su daddy dama duka sauran families suka biyu Flight zuwa ƙasar SPAIN ɗin. Se ganinsu kawai su Prof ɗin sukai amma juraij be zo ba kasancewan ma ashe shi baya a ƙasar ne ma. A kuma washe garin ranar wanda yay daidai da kwanan Meesherh biyar kenan a kasar aka shiga da ita aikin daya gama kassara jikin kowa. A kuma daren ranan ne Sheikh juraij thabit Jedaans ya dira a ƙasar spain ɗin wanda babu wanda yayi tsammanin ganinsa. Domin kuwa can Ƙasar Sudan ya tafi, tun a daren aka fara mata aikin har zuwa ƙarfe 5:30 na asuba. Kum Alhamdulillh aiki yayi kyau sosai sai fatan farfaɗowanta lafiya da kuma adda'ar ta tashi lafiya ƙalau IN SHA ALLAH. Haka suka dinga fitowa fuskansu ɗauke da murmushin cimma nasara a aikin nasu.Suna fitowa baki ɗaya duka Family'n JEDAANS sune cike a compound na hospital ɗin tamkar wanda suke a Nigeria. Dr John Amaan ne cikin murmushin jin daɗi da kuma ƙaunar Ahalin JEDAANS ɗin ya miƙa ma Prof Sameer hannu yana furta. "Congratulations Sir anyi aiki cikin nasara da kuma dacewa IN SHA ALLAH zata farka cikin hayyaci da nutsiwanta, kana anyi mata gyaran karayan da tayi se nan da Awa shida zuwa bakwai za'a fiddota, daga nan se adda'an fatan farfaɗowarta gaba ɗaya kuma" hannun Dr John Amaan ɗin sosai papiey ya riƙe ya kasa saki yanaji tamkar Meesherh ɗin ce ma gabansa tsaye haka. Dr John na barin wurin su daddy suka ringa rungume ɗan uwan nasu suna taya kansu murna. Ganin irin farin cikin dake kwance tattare da fuskokin kowannensu ne ya sanya wasu hawaye wanko fuskan prof Sameer ɗin. Daddy ne ya ƙira gida Nigeria yana sanarma Ama da kuma JEDAANS TURAKI nasararn aikin da akay.♡
✯ Ranta a mugun ɓace bayan ta zagaya ta bayan asibitin ta ɗauki woyanta kai tsaye tana dokama Dr Maheer da yake can a tsare ƙira.Domin kuwa sunyi da shi lallai Meesherh bazata tashi ba se kuma gashi taga saɓanin hakan. dan sun gama yi dashi zaiyi duk abinda zaiyi ya kasheta tun a wajen aikin. Sai dai har wayar ta katse ba'a ɗauka ba. Maida akalar ƙiran kan wata nurse da zasu aikin tare tayi tana jin yadda zuciyar ta ke tafasa, Ba ƙaramin sake haukacewa Mameey tayi ba kuwa ganin itama ba amsa. Hakan ya sanya ta ringa zazzaga bala'i, Ita da tazo ganin yadda iyayen yarinya'n zasu zauce hankalindu ya tashi daga nan suma in yaso su haɗiyi zuciya su mutu, Domin ita macece data rayu da tsantsan kishin Maah da papiey, kasamcewarn sune gaba ɗaya ƙarfin tattalin JEDAANS ɗin. Kana sunfi kowa Power a cikin family dama sauran dangi duka. Wannan shi ne dalilin da ya sanya ta rayuwa da ƙiyayyar Maah da papiey, dama sauran yaran da suka haifa se kuma akalar tsanan nata ya koma kan Meesherh a loƙacin data gama fahimtar Meesherh ce ta kasance zuciyar kowa daga cikin Jedaans ɗin. Hakan ne ma ya sanya ta cusa babban ɗan ta Moh Ameern Saif shiga ƙarƙashin Meesherh ɗin shi kansa ba tare da yasan mi hakan ke nufi ba, domin Mameey irin makiran matan nanne masu shegen iya takunsu da taka tsantsan wajen iya tuggunsu. A zahiri ma idan kai rayuwa a JEDAANS kai tsaye itace mace ta farko da zaka fara sheda da cewar ita kaɗai ce mace ta kirki akan sauran matan. A loƙacin da ta buɗi ido kuwa taga kalan shaƙuwan dake tsakanin juraij da Meesherh zaucewane kawai batayi ba. Tun daga loƙacin ta shiga ta fita seda taga ta raba ƙarfin alaƙar dake tsakanin su kana hankalinta ya kwanta. Itace nan ta sanya a kan garar mata da Meesherh ɗin hakan be yiyuwa ba, shi ne ta sanya aka ɗora mata masifan don kiɗe kiɗe kuma bayan hakan bawai ta barta bane don so tayi ma ta zama tantiriyar karuwa lamba ɗaya,Sai dai kuma shi UBANGIJI alhakimu ne kuma ba azzalumin bawan sa bane, dan hakan data aikata sai hakan beyi tasiri akan Meesherh ɗin ba. Bata so hakan ba amma ya ta iya dole ta haƙura. Kuma itace take sake sanya muguwar tsana me ƙarfi tsakanin Maah da kuma anniey To yanzu kuwa inhar ba ganin gawar Meesherh tayi ba to kuwa lallai zuciyarta ba zata huta mata ba.
Tun Meesherh na yarinya Mameey ta gama ruguza rayuwarta wanda badan tsarewar Ubangiji ba da tuni wani zancen ake ba wannan ɗin ba. Don bayan a sanya mata jin tsanar juraij ɗin harda taurin kai na bugawa a jarida yadda zata gallabi kowa Mameey ta sanya a sakawa Meesherh ɗin duk ita kaɗai. Duk loƙacin da taga ƙarfin aikinta ya soma rawa zuwa take ta sanya a sake rura wutar tsanar dake tsakanin juraij da Meesherh, Anniey da Maah, sedai bokan nata sau tari yakan faɗa mata cewar destiny ɗin Meesherh da juraij a sarƙe suke kuma daɗi da ƙari shi duk wani aiki da za'a buga a kansa baya ko tunkarar inda yake balle har yay tasiri akansa, Sedai sunyi amfani da rashin jin maganar ta da kuma daɗe gangarar da Iran da suke shi ne salon aikin kawai dake tasiri a cikin aikin juraij ɗin yana sake jin Meesherh ɗin na ficewa a ransa gaba ɗaya. Da yadda itama baza'a bari ta so shi kamar dai baya koda kuwa na minti guda ne, Kai hatta mahaifinta mameey bata bari ba seda taso sanya mishi tsanar ƴarsa ta cikinsa wanda jinin dake gudana a nashi jinin shi ne ke gudana a cikin nata jinin jiki. Dan haka ƙarfin jinin dake yawo yana zagaya tsakanin su ya hana mata cimma burin ta, se gashi ma a maimakon kowa yaƙi Meesherh ɗin se ya kasance kowa tamkar an buɗe zuciyarsa ne an ɗiga masa mugun ƙaunar Meesherh ɗin ne, dan ta kasance ma tamkar itane zuciyar JEDAANS ɗin baki ɗaya. Sa'ar ta ɗaya shi ne kawai dama can akwai ƴar tsama tsakanin Maah da kuma anniey wanda kuma dama irin dan faccalanci ɗin nan ne haka, se tay amfani da wannan damar ta sake rura musu wutar tsanar junansu haka kawai, sedai aikin ma kusan zamu iya cewa iyaka akan Anniey'n ne ke tasiri kawai don ita Maah bawai tsanar Anniey'n take ji ba abinda kawai bata so shi ne a wulaƙanta ko yaranta. Wanda dama hakan kuma can ɗabi'ar Anniey'n ne kodan ita ta kasance jinin Ama ce oho wacce take ganin ai ita dasu daddy'n duk abu ɗaya ne,tunda mahaifiyarta ita ce ta kasan yaya ga Ama ɗin dan hatta Auren ta da Daddy Ama ɗin ce ta haɗa, kasancewarn daddy'n Juraij ba mutum bane shi me ƙin biyayya ga mahaifansa hakan ne ya sanya shi amsan Auren Anniey'n babu musu. Da shigowarta gidan ita kuma ganin ƴar uwace garesu ya sanya take son seta mulki sauran matan dake gidan tunda ita ɗin jinin suce.
Saurin dafe kanta haɗi da dawowa daga duniyar tunanin data yafi mameey'n tayi jin numfashinta na ƙoƙarin fara seizing. Tuno wasu abubuwan da suka riga suka shuɗe datay. Wanda kuma take jin har a yanzun bawai ta saduda bane se dan ma tanajin har a yanzun tana kan bakarta bawai ta gajiya bane. Cikin iya taku da kuma yaudarar data saba tamkar koda yaushe tana komawa cikin room ɗin.
{Anan ina son haska mana wata ƴar hanya ce ta cewar. Ba kowa bane ze nuna maka soyayya a fili kuma har a zuciyarsa ta kasance hakan ba, haka kuma ba kowa bane ze nuna tsanarka a fili ya kasance kuma har cikin zuciyarshi haka ɗin abun yake ba. Kuma karka yadda zuciyan ka haka kawai taka rudarka akan haka kawai kaji ka tsani wancan ko kaji seka mulki wannan haka nan. Don haka karka yadda ka taɓa judging mutum by cover ba tare da ka tsaya ka gama karantar ya yanayin sa yake ba. Kuma kun ga anan ALLAH nason nuna mana cewan Meesherh yarinya ce kafin Allah, ba don Allah na tare da ita ba da yanzu ba wannan zancen ake ba}
✯
Alhamdulillah yau kwanaki uku kenan ciff da yima Meesherh aiki. A kuma yau ɗin ne kowa ke sanya rai da farfaɗowanta, dan haka tun sha biyu na daren yau ɗin kowa da kowa zuciyarsa take a cikin zullimi da kuma fargaban abinda ka iya zuwa yaje. Ƙarfe shida na safiyar ranar dayay daidai da Ranar juma'a Meesherh ta farka, Gaba ɗaya dactor's ɗin da suka mata aikin ne zagaye da ita suna fatan ta farka a gaban su ba tare da wota matsala ko damuwa game da aikin nasu ba, Se kuwa paah da Maah da suke cikin room ɗin suma, domin suma suna son ganin farkawan Shalelen nasu akan idonsu. Shi kaɗai ne ya lura da ɗan motsawan da yatsarta ƙwara ɗaya yay.hakan ya sanya shi kafe yatsar cak da kyawawan idanunsa akan yatsun ƙafarta nata dake motsawa, haka har zuwa hannayenta biyu da suma ke motsin. A hankali kuma gashin idanunta suma ke motsawarn kafin a hankali numfashin ta ke sauya salon fita daga na duniyar sumewa zuwa na wadda take a cikin duniyar rayayyu.
Da farko bata iya ganin komai ba se taci gaba da motsa idanun sannu a hankali har ta fara ganin jama'ar dake kewaye da dakin dishi dishi. Idanun ta maida ta rufe tana ɗan matse fuska tare da daƙuneta, jin yadda Gefen ciki da kuma kanta suka mata wani kalan kummmmm,
Ahankali ta shiga ƙoƙarin ɗaga hannunta dake ɗaure da canular tana son dafe kai da kuma cikin nata. Se a sannan kowa dake
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 14