aiki yana fita dasu. Tun a take yay ordering daga ɗayan company'n suka zo suka sake docoret na office ɗin. Zaman meeting ɗin da ba'ai ba kenan a ranar Iklimar ce ma ta taimaka mata wajen dawo da ita gida.
Kasancewar da night bayan sun dawo a sallah al'adanshi ne se yaje yayo sabon wanka ne yake sanya shi zuwa dining room din a ƙurarren loƙaci kullum.Fararen riga da wando na fendi masu azabar laushii da kwanciya a jikin mutum ne a jikinsa. Fararen sawayensa kuma suna sanye cikin Blue Lorenzo's slippers masu taushi, ga wannan mayen ƙamshinsa dake rige rigen kaima hancinansu ziyara tun kafin isowansa parlour'n.
Wani irin tsalle taji zuciyarta yayi a karo na biyu,iyaka ƙamshinsa kaɗai karyar mata da zuciya yake, se dai kwarai da gaske tana ƙoƙari wajen shanye hakan,Cikin irin jarumtar da take da ne ya sanya kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kanta tana ci gaba da sipping coffee creamer ɗin ta. A cikin zuciyarta ayyanawa take ehhhhhh lallai Pa'apanta na daban ne kuma me kyau ne da kuma tsafta. Wanda indai magana ake ta wanka yabi jiki to kuwa ba tantama tasan pa'apanta ƙarshe ne. Sam babu ko ɗigon annuri a kyakykyawan farar fuskan shi haka babu wasa ko alamarsa a saman fuskarsa nashi da tai wani kalan fayau, wanda kai tsaye ita tasan dalilin daya haddasa may hakan.
Don kamar yadda yasan duka halayensa haka itama ta san duka halayensa da kuma kalan damuwan da yake shiga ko akasin hakan. Kowa dake parlour'n wani kalan shiru yay har ya gama saƙƙowa,kallon kowa baiyi a cikin parlour'n ba saima ta bayan parlour'n daya zaga yana shigewa cikin balcony in da kai tsaye nan ake jera may abu mara nauyi duk daren duniya ba tare da su yake yin lonch ba. Wayane maƙale a kunnensa wanda da dukkan alamu wata wayace yake yi muhimmanci.
yana yin wayar ne kuma hannunsa na ɗauke da wani haɗaɗɗen glass cup mai ɗauke da Whipped cream a ciki yana sha. Gefensa kuma Mohan ne da bay jima da biyo bayansa ba shima zaune saman sofa se woyansa da yake aikin dannawa wanda alamu suka nuna kai tsaye chatting ne yake yi. Shima nashi hannun ɗauke da Extreme milk shakes ɗin dake a saman ɗan table ɗin dake gaban Sheikh juraij ɗin.
★ Bayan ya kammala woyan kai tsaye ya maida kallonsa ga Mohan ɗin. "Yaya abubuwa sosae suke yin kyau game da binciken sirrin da muke yi kamar yadda ka buƙatan ama. To Alhamdulillh se dai mu ce Masha Allah" Gefin lips nashi ya ɗan ciza kaɗan se kuma ya furta "don't worry zamu magana daga baya ina buƙatan hutawa yanzu" kansa ya gyaɗa may yana miƙewa harya fara tafiya kuma ya tsinkayi muryan babban yayan nasu yana ambatar sunan shi kai tsaye da *Mohan Sameer* chakk ya tsaye tare da waigowa alamar gaskata in ƙiran ne ya koma. nodding Kansa yay alaman ehhhhhh ƙiran yay, baya ya dawo yana zama inda ya tashi. Magana yake son may game da Meesherh amma bakinsa ya masa nauyi se kawai ya fiddo da wani kyakkyawan ƙaramin kwali me kyau da ɗaukan hankali "Na lil juraij Mohan ne" amsa yay fuskansa ƙawace da murmushin jin daɗin kulawan da Sheikh ɗin kema yaron san, duk da yasan kome yake da buƙata shima a cikin duniyar yakan iya narka kuɗaɗen sa wajen siyan ko miye se dai ita kyauta ɗaya ce kuma daban take. Duk yawan tarin dukiyar da kake da to fa idan wani ze ciri wani abu ya baka as matsayin kyautatawa wani kalan jin daɗi kake. Kwarai kyauta Rahma ce kuma takan sanya mutum yaji daɗi da shauƙin kyautan da aka masa. Godiya ya may cike da fara'a yana barin wurin gaba ɗaya don bashi space ɗin kamar yadda ya buƙata.
A ƙalla seda ya debi wasu ƴan lukuta masu tsayi kana ya miƙe yana bin ƙofan fita wajen parlour'n ta baya.
Ji yay a jikinsa tamkar ana kallonsa loƙacin da yake tafiya domin nufar ɓangaren sa, tana tsaye cikin kayan shan iska amma ba masu nuna tsiracin mutum ba kanta babu cap hannunta riƙe da woya tana daddannawa. Ido biyu sukai tay saurin janye nata tamkar dama can ba shi take kallo. Se hakan ya Hasko wani abu daga cikin memory'n baya cann. Ko me ya tuno kuma oho amma kome ya tuni me girma ne dan wani kalan tattausan Murmushin gefin baki ya saki yana wucewar sa kai tsaye. Wani kalan luuuuuuu da nata idanun itama tayy tana yin bayaaaaaa......
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
More Information
08104493215
https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D
༺༻
*♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆*
༺༻
_𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ_
𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 Naseer ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ
_AMMEY LAYLERH_
Page
7&8
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Ƙafar benen tay hanzarin kamawa tana sakin wata munafukar ɓoyayyar ijiyar zuciya ta saki acan ƙasan ranta. Juyowar da zatai tay ido biyu da Mammanta wacce ta tsarera da ido, Ɗan faɗuwa taji gabanta yayi ganin yadda Mah ɗin ta wani kalan tsareta da idanunta."Me ki ke yi anan?" kai tsaye Mah ta cilla mata tambayar fuskanta babu alamun wasa don ita mace ce bame son ɗaukan wargi ba ko daga yaran natane kuwa. "Ina shan iska ne maah" Rolex watch ɗin dake daure a tsintsiyar hannun ta Mah ɗin ta kalla tana furta. "Kalla ki gani ƙarfe nawa yanzun da kike nan tsaye har yanzun baki kwanta ba?" Kanta ta ɗan rausayar gefe ba tare data ko sake furta wata magana ba Mah ta kama hannunta tana kaita har bakin ƙofar parlour'n ta.
Ita kuwa Meesherh Koda ta shige room ɗin nata ma bata shige bedroom nata ba kwance kawai tay anan bisa 3 str daga ita sai wata yellow ɗin doguwar rigar baccin dake jikinta irin me santsin nan me kuma bin jikin mutum.Sai wata tattausar hular sanyin dake kanta yellow, yayinda himilin gashinta yayi luf luf yana kwanciya har gadon bayanta se dai ba can ba, don da kaɗan ya zarce kafaɗunta. Sosai tay wani kalan masifar kyau duk da kasancewar kayan bacci ne a jikinta,kasancewar ita ɗin me kyau ce wanda shi wannan kyaun ya haɗu da aji da kuma tsantsar hutu da jin daɗin Rayuwa. Har ta kama doorhandle na ƙofar parlour'n ta seta juyo da baya tana jin kamar ba daidai ba, kodan kasancewar ta auta ne ya sanya duk daren duniya bata taɓa iya bacci ba tare da ita taga baccin babyn nata ba. Kamar yadda take a kwance a parlour'n haka Mah ta tarar da ita kwance hankalin kwance kuma take baccin abinta.Gashin kanta dake ɗaure cikin jan riboms ƙwara ɗaya ya zame yayi nashi wuri, se hakan ya bama gashin damar bajewa akan 3 str ɗin da take kwance akai.Se sheƙi da walainiyar kyau yake gwanin birgewa. Zama tay gefenta farar fuskanta irin ta Mahaifinta Sameer Jedaans sak ta ɗan shafa,sauƙe ajiyar zuciya tay tana zuba mata idanu sosai, A natse kuma ta shiga tashinta ba yadda zata firgita kota tsorata ba. Idanunta ta baccin sosai ya fara cin ƙarfin su ta ware akan mahaifiyar nata. Ɗan Murmushi me laushi ta sakar mata tana kamata ta mikar da ita tsaye.
Kasancewar ta bame nauyin bacci sosai bace ya sanyata miƙewa Mah na taimaka mata wajen soma tafiya da ita. Akan lallausan gadonta ta kwantar da ita haɗi da tattare mata gashin tan wuri guda tana sake ɗaure mata shi da ribboms ɗin cen ƙasan ƙeyarta don karya dameta wajen baccin. Adda'an barci ta mata haɗi da neman tsari kafin ta tsareta da ido a cikin ranta kuwa faɗi take {ya Allah ga baiwar ka nan Meesherh ka kula min da ita cikin amincinka da buwayarka, kaci gaba da tseratar min da ita daga duk wasu masu nufarta da mugun nufi. Na bayyane da na ɓoye, ya Ilahi ya mujibud da'awati karkaci gaba dabe kowa damar sake cutatarmaka da wannan bewar take me raunin zuciya!!! Ya Allah} Se kuma A hankali ta ja abin rufa ta rufe mata daidai saman ƙirjinta haɗi da ɗan ɗukawa tana manna mata kiss a goshinta.
"Ya Allah kamar yadda ka raba tsakani idan har babu Alkhairi karka kuma jarabtar wannan baiwa taka da wani abu na daban" wannan karon kam a bayyane tay maganar Jiki sanyaye ta juya tana barin bedroom ɗin. Itama jikinta sanye da kayan bacin dogon wando da riga sakake sosai da riga buɗaɗɗiya sosai irin fararen nan masu faɗi dai haka sosai. Kamar yadda ta fita haka ta dawo ta tarar da prof Sameer Jedaans yana nan zaune gaban System nashi sai faman aikin sarrafata yake idanunsa sanye da farin gilashi, bare daya ɗago ba ya furta "Se yanzun kike dawowa? Kin gama lallaɓa Babyn taki kenan har tayi baccin!" Murmushi kawai ta yi ba tare da tace komai ba ta wuce Bathroom don haɗa masa ruwan wanka me ɗumi da ƙamshi. Don al'adansane baya taɓa kwanciya har se yayi wanka. Zama tay kusa dashi tare da ɗan Murmushi ɗauke saman fuskarta. Kanta ta kwantar da kanta saman shoulder nashi, "Papiey'n Meeshel ruwan wankanka is ready"
Kansa kawai Papiey'n ya ɗan girgiza yana lumshe idannuwansa ƙaunar matarshin abin sonshi na sake ratsa shi. Kayan jikinsa ya rage yana faɗawa bayin.
Bayan ya fito ɗaure da alwulan da al'adan gidan ne ba'a kwanciya ba tare da alwulan ba, sedai wasu sukan yi wasu kuma basu yi haka nan tsarin yake. Ko kafin ya fito tuni Mah ta sake gyare bed ɗin daga nan suka kwanta abinsu se bacci.
☆☆☆☆
Ance wai dare mahutar bawa, kamar ko wanne rai me numfashi ke kwance domin samun hutu ga rayuwarsa cikin kwanciyar hankali yana barcinsa, Se dai a dai-dai wannan loƙacin Sheikh juraij thabit ke zaune saman darduma yana rera karatun Al- Qur'ani mai girma,Cikin wani irin amo madaidaiciyar muryarsa mai daɗin sauraro da sanya ma zuciyoyi nutsuwa yake raira karatun. Idanunsa lumshe suke daga can cikin ƙasan ƙasan zuciyarsa karatun ke fitowa.
Wani kalan Nunfashi mai nauyi Abba dake tsaye tun da jimawa a ƙofar shigowa parlour'n yaron nasa yaja. kana ya fesar tare da cike da sanyin jiki ya turo ƙofar ya shigo a natse. Jin motsin ne ya sanya Sheikh juraij buɗe idanunsa da suke a lumshe har zuwa loƙacin. Akan Abbansa ya sauƙe ganinsa kai tsaye, saurin tashi tsaye yay yana me nufo abban.
Sanya hannun sa masu taushi yay yana kama na sheik ɗin cikin nashi, bakin bed ɗin Sheikh ɗin Abba ya zaunar dashi shima yana zama kusa dashi. Se daya ɗan ja wasu second haka kafin cike da tsananin tausayin yaron nashi ya furta.
"JURAIJ akwai wata alfarma da nake nema awajenka!" Cike da wani Irin baƙon yanayin da zuciya ke ɗauka a bazata ya ɗago kansa yana kallon Abban cike da girmamawa ya furta.
"Abba kawai kace wani Umarni zaka bani amma ba alfarma zaka nema daga gareni ba. Saboda kafi ƙarfin neman alfarma awajena sai dai ka bani Umarninka kawai, Ni kuma a koda yaushe me biyayya ne ga dukkanin umarninka"
Zama da kyau Abba ya gyara kana ya fuskancesa da kyau cikin raunin zuciya da amincin da yakeji akan Sheikh juraij ɗin yace.
"Um-um Juraij alfarmar dai kam nake nema" Cikin jin nauyin mahaifin nashi da ganin kimansa ya sake risinar da kansa ƙasa, muryan sa har na shirin karyewan raunin da tay ya furta. "Idan har Abbana ya zaman yana nema alfarma daga gareni to ni a gun waye zan nemi ta wa alfarmar, idan kana faɗin hakan Abba kunya nake ji duk loƙacin da naji kana furta kalmar neman alfarma daga gareni Abbana"
Kai Abban ya ɗan girgiza cikin sauƙe wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya furta. "Sai alfarmar da zan nema daga wurinka inason ya kasance iyaka ni da kaine, a iyaka mu nake son maganar ya tsaya" kansa yake geɗawa Abban tamkar irin wanda bay maganan nan. Kafin cikin wani irin yanayi mai gauraye da damuwa da rauni ya furta. "Insha Allah Abba a koda yaushe ni me bin umarnin kane kamar yadda ni me riƙe maka sirrinka ne"
"Meesherh!!!, Meesherh itane damuwar juraij tare da Mahaifiyar ka na rasa ta yadda zan fuskanci wannan al'amari Juraij....." Daga nan suka juye baki zuwa wani yare na daban wanda Ni AMMEY LAYLERH'NKU banjin duk abinda suke faɗi ɗin kuwa. Sun ɗauki a ƙalla sama da 40 minutes suna magana kuma cikin wannan juyayyen harshen da suka juyemin. Kafin daga bisani Abban ya miƙe cikin yanayi na ƴar damuwa Sheikh ɗin na biye a bayansa. Da sauri Inuwar da tun farkon fara zancen nasu take tsaye ta gilma alamar ta kauce. Kafe wurin da ido Sheikh juraij yay zuciyan sa na beating na ɓacin ran hakan da aka jima ana mai wato laɓe....
*Around 4:20 Am*
Ƙarar Alarm ɗin data sets duk asubahin duniya shi ne ya farkar da ita. A hankali ta shiga ware lumsassun idanunta da suke cike da barci har yanzun kana suka mata nauyi.da adda'an tashi a bacci ta tashi a bakinta.
A natse ta ziro fararen santala santalan sawayenta kan tattausan canies carpet ɗin dake gaban gadon, ɗan miƙa tayi haɗi da shigewa cikin bathroom. Alwula ta ɗauro tazo ta fara gabatar da raka'atanil fijr,tana nan zaune da Rabbana Arba'in riƙe a hannun ta na Adda'o'i taji wannan amintaccen sautin nashi na ratsa duka cikin jikinta. Cike da tarin nutsuwa take binsu sallar subhi ɗin.
Bayan an idar komawarta kwance tay tana sake shigewa cikin lallausan duvet ɗin ta. Ba itane ta farka se wajajen 11:40 kasancewar weekend ce, Kai tsaye bathroom ta shige tana sakar ma kanta shower. Se da ta ɗauki sama da 40mins a cikin bayin kana ta fito jikinta sanye da peach cobbler bathrobe a jikinta, Kanta kuma na cikin fari tass ɗin towel mini.
A kan stool in dake gaban 1 mirro'rnta ta zaune kanta ta fara busarwa, kana ta shiga tsane ruwan jikinta. very expensive lotions ɗinta ta ɗauka take levelling lower skin ɗin nan nata me kala dana new born baby Wanda hasalin Luxury da Luxury ya gaka ratsawa. Farar powder me hasalin maiƙo ta shafa a face nata daga haka kuma ta shige cikin closet nata don shiryawa.
Sanye ta fito cikin wani mahaukacin milk and coffee colours One Millions all stones yaɗi halp bubu, Yaɗine me shegen kyau da kuma tsada na manyan yaran ƴaƴan gata. Siririn mayanin yadin ta ɗora iyaka gefen shoulder nata na dama.Kai tsaye Phone nata dake jikin Rinlight already ta nufa. Seta cameras na woyan tay ta cikin tiktok nata. Wannan fitacciyar wakar da tay trend a media ta saki ta Ƴar Arewa. Wacce jarumi Sadeeq sale ya saki, har wani ɗan lullumshewa idanunta keyi. Tana gama yin Vedio'n tayi posting nata a duka pages nata na media, take mutane suka ringa likes kan videos ɗin nata kamar kullum.
Daga haka ta nufo ƙasa ta sauƙo kamar yadda ta zata duk iyayentan suna babban parlour'n gidan ne. Tun kamin ta iso wannan shegen ƙamshin tan nan ya gama sanar musu cewar me zuciyar j̶e̶d̶a̶a̶n̶s̶ ce gaba ɗaya ke tafe wato 𝘿𝙄𝘼𝙈𝙊𝙉 Ꮇ𝞔𝞔𝘚Η𝞔Ʀ 𝙎𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 𝕁𝔼ᴰᴬᴬᴺˢ. Daga gefen Mah ta zauna bayan ta gaida kowa dake dining room ɗin. plate ɗin dake ɗauke da donut, pizza se picanto taja gabanta tare da ɗauka tana ɗora shi kan cinyarta tare. Metres sarvice ɗin dake aikin shirya kitchen Meesherh ta kwalama ƙira tana bata umarnin kawo mata fruits. Babu jimawa kuwa se gata hannunta riƙe da plate da yankakkun fruits ɗin a ciki masu sanyi, da akama yanka ƙananu².
Nanameerah ce ta ɗan kalla inda Meesherh ke zaune ƙanwa Moh Ameern Saif ta furta wallh Aunty Meesherh kalan yadda kike gudanar da acting naki wurin aikin ku na burgeni wllh" Ɗan murmushi me faɗi tay tana kallon Nanameerah'n itama tare da furta. "Sosai mutane ke faɗin wllh aikin mu film na burgesu sosaifa Nanameerah" a tare kuma suka saki murmushi wa junan su cike da shaƙuwa. Annie ce ta kalla sashin da Meesherh ɗin take tare da furta. "Aikin me? Ke yanzu har wani abun kirki da alfahari kika ɗauki sana'ar taki, Ko da yake aifa aikin tallata jiki a yanzun kam shine babbar sana'a a Nigeria"
A rene cikin wani ɗan iskan renin wayo da rainin hankali ba tare data ko kalla inda Annien take ba ta furta "Nagode!"
Tsaye ta miƙe da niyar barin dining room ɗin. Abba ne ya kalleta da alamun damuwa a ranshi ya furta.
"Mamana ina kuma zaki bayan baki ko kammala yin dinner naki ba?"
Shafafen cikinta da ba kamar yanzu ta gama cin donut da pizza haɗi da picanto ba sam kai ba kace ma kwai ƴaƴan hanji a cikin cikin nata ba. Ɗan shafa cikin nata tay tare da furta.
"Alhamdulilah na ƙoshi ne Abba"
"Ok shikenan Mamana Ubangiji yay Miki Albarka, da ameen ta amsa bayan ta sake musu sallama don yau tana da wani shooting film da za'a ɗauka wanda Film ɗin tane itane da kanta ta tsara abinta.Har taje bakin ƙofar parlour'n kamar daga sama ta tsinkayi muryawan Ama tana me furta. "Takwarata taimaka ki sauƙe min yayanku a gidan gwaggo Haleemah"
Cike da ɓacin Ran daya kasa dannuwa Annie ke kallon Ama data kasance surukuwa a gare su kafin cikin hucin ɓacin rai ta furta
"Haba ama bayan batama zuri'armu suna da tay, duk hakan be isheku ba sema ƙoƙarin dan gan tata da Mutum tsarkakakke kamar juraij da kuke! Don me ake min haka ne eye? Kodan kawai kina matsayin Yaya ga Mahaifiyata? To ni wllh na gaji nima kawai daga yau ki dawo yimin kallon surukuwarki ba ƴar ki b......
"Zeynab!!!"
Abba ya wani irin ƙira sunanta a mugun tsawacen da ya sanya kowa rawan jiki a wurin. Don ba abu bane daya taɓa faruwa a zahirance duk kuwa irin tijara da jalalar da Annie'n keyi akan duk wani abu daya danganci Meesherh ɗin. I'm sorry Abban jur..."
Ta furta muryan ta na rawa.
"I said get out my friend!"
ya sake buga mata wata uwar tsawar da tafi ta farko ba shiri ta haɗiye maganar da bata ƙarasa taba tana barin wurin don A yadda ta ji muryarsa a kausashe kam ta tabbata babu wasa a cikinta.
Jiki a sanyaye kowa ya shiga darewa banda Mah da jikinta har wani jijjiga jijjigan ɓacin rai da baƙin cike take yi, Sa'ar ta ɗaya sunan ALLAH ne ya fara zuwa bakinta kafin komi shi yasa ta dinga nanata sunayen ALLAH'n a bakinta.
Meesherh kuwa tana fitowa compound na gidan ta tsaya tare da ɗan sa hannunta na dama tana riƙe ƙugunta. Nainarh ce tsaye ƙaramar autarsu Sheikh juraij jingine da jikin motar ta. Wani irin kallo Nainerh take watsama Meesher'n tare da furta. "Har ke wa ce ce a cikin gidan nan da har zaki ringa mahaifana meda yawu akan ki gaban mutane?"
Wani kalan sheƙeƙe Meesherh ta mata "Kin ga kenan ke da kanki kin ba kanki cikakkiyar amsarn cewa Ni ɗin wata aba ce me girma a cikin gidan nan, Idan kin gama bani hanya ta zan wuce"
Tay maganar tana kama murfin car nata tana ɗora haɓarta akai, ta buɗe baki kenan da nufin sake watsoma Meesherh ɗin wata rashin kunyar idanunta ya sauƙa akan babban yaya wato Sheikh juraij thabit Jedaans. Babu shiri ta gimtse bakinta tana haɗiye sauran maganar data saura a cikin bakinta. Tamkar kiftar ido haka Nainerh ta ɓace a wurin. Zuciyanta a cunkushe ta shige Motan tana zama mazaunin Driver yayin da ya zauna gefen mai zaman banza. A natse tasa hannunta farare ta kunna motar cikin yanayin nutsuwa take driving nata, Yayin da shi kuma yake gefenta zaune. Ahankali yake ƙarema zara-zaran yatsun hannunta dake kan stearing tana juyawa kallo,me kama da kalan nashi don sosai abubuwan su suke ɗibar kamanni harta da sawayenta kalan nashi ne futiƙ,wani ɗan numfashi ya fesar tare da furta.
"Bani motar nan b.... Ji yay ya tsinta kansa da kasa ƙarasa sunan Babyn da yay niyar faɗi.Se ma lumshe idanunsa dayay tare da shaƙan ƙamshin humranta daya cika motar. Ita kuwa bata kawo komi a ranta ba sema kallon yanda ya lumshe idanunsa tay se taga ba ƙaramin kyau ya mata ba. A jikinsa yaji kallonsa take se kawai ya gyara fuskan da kyau yana jingina kansa da jikin motar, Kamar kuma ba zai yi magana ba buɗe lips inshi a hankali yay tare da furta. "Kallon fa?"
Kanta ta ɗauke wani munafikin murmushi ɗauke saman fuskanta. "Pa'apahh!!!" Ta ƙira hasalin ainihin cikakken sunan shi gareta tun yarinta.Hakan ne ya sanya Idanunsa dake lumshe ya shiga motsasu ahankali yana son buɗe su tare da faɗin. "Buddies kiyi abinda ke gabanki, ko kiban motan!"
Buɗe idon ta da yanzu ne ta lumshe su dama tare da juyowa ta kalli inda yake zaune, iyaka muryansa kaɗai da taji ya sauƙar mata da samun nutsuwa. "Pa'apahh to kace ka yafe min pls" tay maganan da alamun rauni sosai tattare da ita. "Da ki kamin me kenan fa?" Yay maganan cikin ko in kula. "Everything forget itt" Kansa ya dauke a kallonta yana maida shi can kusa da closed windown motar, Itama se bata sake furta komai ba don tasan bayi son maganar kenan.Nuvel script ɗin ta dake gefe ta ciro me ɗauke da photon'nta tana budewa ta ɗaura shi saman gaban motar. A duka sassan jikinsa ya soma jin banbancin yanayi.
Sake buɗe idanunsa calmly akanta yay, wacce ta nutsu wurin driving nata a kuma daidai loƙacin suka kawo ƙofar get na wani makeken ƙaton get. nitsatsassun fararen idanuwan ta da suke nan sakk nashi kawai ta zuba akansa. tamkar wacce bata da wata matsala a rayuwarta tamkar babu abinda ke damun zuciyarta ta furta. "Pa'ap.... Bai bata wani dama na ƙara sa ambatar sunan shi da tay shirin yiba ya fi ce a motar. Wani irin shiru tay tana me binsa da kallo da raunatattun idanunta. dan Shiru tayi na wani loƙaci kana taja kan motar ta tay reverse tana shan kwanar da zata bi. Cikin son shanye komi cike da nitsuwa take ci gaba da tafiyanta kamar daga sama taga wata babbar mota tayo kanta. Tamkar wacce aka bugama guduma haka taji amon muryansa cikin wani shuɗaɗɗen lamari yana furta "Babyyyyyy.....
A wani irin tsiyace ta taka wani mahaukacin birki tare da juya kan motar ta zuwa ɓangaren gabas, wannan babbar motar da tayo kanta na bugar wata motar daban ba ita ba.
★★
Slowly ta shiga buɗe idanunta da taji sun mata nauyi loƙaci guda, ɗan lumshesu ta sake yi tana ƙoƙarin saita kanta dan koda wasa batai tunanin zerewa motar ba. Wata ƙatuwar Ajiyar zuciya ta sauƙe me nauyi. Tana ambatar sunan ALLAH cikin rai da ruhinta. ★ Ɓangaren Sheikh juraij kuwa a natse ya sanya kansa cikin ƙaton parlour'n gidan, da gwaggo
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 14