Daga ta can ɓangaren me ƙiran kuwa ɗan lumshe ido Moh yayi duk jikinsa sanyaye babu daɗi ya furta. "Wllh Meesherh tana cikin wani yanayi sosai director muhsin se dai a taya mu da adda'a" yana katse ƙiran ya fesar da wani zazzafan numfashin da ya sanya Mohan Sameer Jedaans dubansa yana tambayar ko lafiya? Amsa ya bashi kan abinda Muhsin ɗin ya tambaye shi. Chakkk Sheikh juraij thabit dake woya ya tsaya chakkk na wosu mintinan, kafin yay saurin ɗauke kansa daga garesu jin tambayar da Mohan Sameer ya cillama Moh Ameern ɗin. "Amma daamaki taya maganar da bata fita ba har shi yasan abinda ke faruwa da Meesherh ɗin?" Panping hand nashi yay irin oho ɗin nan.☆
☆Umarnin kowa ya tafi haka nan Sheikh juraij ya bayar ganin har zuwa loƙacin bata farfaɗo ba wanda kuma dama can basu sanya Rai da hakan ba kodan a yanayin da take a ciki, Domin maƙil suka cika Hospital ɗin da duka ajalinsa babu wanda be zoba har na nesa kuwa masu aure a garuruwa daban daban amma banda Anniey. Bisa dole don sun nan ba'a wasa da umarnin Sheikh ɗin ya sanya wasu tafiya wasu kuwa sunja sun kafe kan dole suna nan kodan shige da ficen su Maah ɗin. Haka aka ɗin ga ɗibansu a lafiyayyun manyan motoci ana tafiya dasu can Jedaans Mention ɗin.
A fusace thabit Jedaans daddy'n juraij ya shigo gidan zaune ya tarar da Madam anniey da kayan maƙulashe gabanta cikin shiga ta alfarma. "Yanzu ke A'isha abinda kike aikatawa kina kallon ya kamata kenan? Ke kuwa me wannan yarinya da uwarta suka aikata miki da zafi har haka? Koma dai miye jinya ta kori komi da kike ji da gani Wllh. Domin ita gata can bamuma tunanin zata rayu amma ki kasa sanya ƙafarki asibitin wllh rashin imanin ki kullum sake gaba gaba yake A'isha na rasa wacce kalan zuciya garek. ki sani Allah (S.W.T) da kansa yace karmu tsani kowa a Rayuwa" Zamanta ta gyara sosai tare da fuskantar mijin nata kana ta furta " Amma ai yace mu naisanta kammu ga waɗan da zasuci zarafinmu ko mutuncinmu, kaga kenan bana da laifi akan hakan ko?kuma shi da kansa yace kada ka damu da wanda bai damu dakai ba,kana yace kada ka matsanta son wanda baya sonka!! Shi kenan dan banje asibitin suba kenan nayi laifi? Sanin kanka ne ba ƙaunata Haleema takeyi dan me ni zan kaunaceta duniya ai cewa tai kaso duk wanda ya nuna maka ƙauna ka nesanci duk wanda baya ƙaunar ka amma ka kaucewa nuna wanda baya sonka ƙauna ta hanyar shishshigi dan banyi hakan ba shikenan nayi laifi" tana gama faɗin hakan tayi tafiyarta a wurin.
Wata ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauƙe shima yana nufar bangarensa yana jin sammm babu daɗi hakan har can kasan zuciyarsa. Daga haka kowa ya kwanta wasu zuciyoyin duk babu daɗi da masu akasin hakan. Tun kan 10 na safe ya cika wasu suka soma tafiya Hospital ɗin. Sheikh juraij kamm seda ya tabbatar da cewan kowa na gidan ya fita kana ya nufi ɓangaren mahaifiyarsa don jiya da dare daddy'n sa ya ƙira shi kan dan ALLAH ya gwada sa'ar sa ko ALLAH zai sa a dace ya lallashi Anniey'nsa ko za'a dace ta yarda yau taje asibitin. Tana zaune cikin ado tamkar jiyan se baza ƙamshi take kai ba kace itane ta haifa bazaraten saurayi kamar Sheikh juraij ɗin ba. Zaman shima yay a gabanta tare da tonƙoshe ƙafafu yana jan ƙafarta tare da fara matsa mata su. Gaisheta yay Cike da kulawa kalan na kowacce uwa da ɗan ta. Bayan ta amsa shi fuskanta babu walwala sosai. Seda yaja numfashi kana ya fuskanceta cikin wannan nutsuwarsan da Ubangiji ya masa ya shiga furta.
☆
"_Duk yadda ka kai da kyautatama mutane ba kowa ne zai soka ba.kamar duk yacce kakai da nuna ƙi wa mutum ba. Domin da abinda wani ya soka shi ne dalilin da wani zai ƙi ka, abu mai muhimmanci a nan shi ne ka kyautata niyar ka akan komai, domin gobe bata da tabbas, sai iya ka abinda ka gani kawai. Don haka ake son ka koyi yin tsari a rayuwar ka da samawa kanka mafita me kyau, sune zasu taimaka wajen samun alkiblarka domin sanin abinda ya kamata kayi a duk minti guda na kwanan duniya.
Anniey bawai ina faɗin hakan bane wai don son raina sedan faɗin Annabin ALLAH ne.Nauyi na kara hawa kan ko wanne bawa ne a duk loƙacin da yake ƙara shekaru. Wato babu ranar da za a wayi gari face nauyin da ka sauƙe jiya yafi sauki akan wanda ke tafe a gobe'nka. Wannan nauyin ko ya haɗa da nauyin da ya zamar maka wajibi da na wanda ba dole ba. Kamar na iyaye, ƴan uwa, makwafta, abokai har dama wanda baka sani ba. To amma ana son a kullum mutum ya zamo me yawan sassauci'n zuciya to da yiwuwar ka dinga jin abinda kakeji akan waninka yazo maka da sauki. Don shi Loƙaci baya taɓa jira sedai a jira shi ma'ana duk minti guda na rayuwarka da baka amfane shi ba, to kayi asarar shi kenan har gaban abada. Don haka zaman kullatar wani a cikin zuciyarka ba komi zai haifar maka ba fa ce ɓata shi wannan loƙacin da baya jira!!!. Mafi mahimmancin shi wannan loƙacin da zaka mora to fa shi ne kake ka faɗa wajen riƙon wani. Anniey komai na duniya da kike gani ba mai ɗorewa bane farin ciki ko akasinsa. To mafita anan shi ne ka yadda da ƙaddara ka kuma ringa karɓar kuskuren ka a koda yaushe kuma ka ringa ƙarɓar sauyi ta yadda ko wani zamani zai tafi da kai. Kamar Kyautata alaƙar ka da kowa yana da matuƙar muhimmanci a wannan gaɓar, kuma duk hakan yana nuni ne akan haƙurin zama da mutane. Ka Kuma fahimci cewa ko wanne ɗan Adam zai iya maka rana_" ya ƙara sa maganan kansa a kasa shiru ne ya ratsa wurin na kamar minti biyar. Ijiyan zuciya ya sauƙe loƙacin da yaji Anniey ta zame ƙafafunta tana karkaɗe jikinta tamkar dai yacce tama daddy.
Idanunsa shima yaka ya lumshe jim kaɗan kuma ya ɗauki Littafin Ayoodah na tsofin labaran gaskiya dana zahiri dake hannunsa ya buɗe. Don yana san damuwar da yake a ciki yaɗan sassauta. Lumshe manyan fararen idanunsa yay kalmomin da yanzun nan ya karanta su na sake amsa kuwwa a tsakar kansa.
_Kamata yay ace dukkan wata alaƙa ta kasance kamar Hannaye da Idanu.
Idan hannaye su ka ji ciwo idanu su zub da hawaye idan kuma idanu suka zub da hawaye hannaye su share hawayen_ Abinda wannan kalma ke nufi se yake kallan tamkar akan kansa ne aka gina maganar da mahaifiyarsa, domin kuwa kalmar na nuni ne akan cewa a duk loƙacin da ɗa ya nema kaucewa daga tafarkin da ba na daidai ba uwa itace mutum ta farko daya kamata ta fara dawo da shi wannan dan nata zuwa kan hanyar daidai. Amma shi se gashi shi ne wanda a kullum yake ƙoƙarin ganin ya seto da Rayuwar tashi mahaifiyar kan hanyar dede bawai kuma dan bata da ilimi na addinin bane. Sedan hakan dole yana daga cikin jarrabobin rayuwarta da kuma son zuciya ta biye mata da tsananin rashin rabo. Tsamm ya mike jin zuciyan da yake son ya sama sallama ta na ƙoƙarin sake kumbura.
Kai tsaye ya fice a gidan ma baki ɗaya yana me nufar Hospital ɗin.
_To fa lallai wannan shi ne ana wata ga wata_
_lalai akwai ƙura kenan a cikin tafiyar wanda kawai da me tsananin Rabo ne Za ai tafiyar tamkar da littafin MIKIYA,don shima se masu rabo ne suka dinga samu_
_lallai aka ce idan da ranka kasha kallo kuma na zaune be ga zama inji masu azancin magana_
_to se ku buyo Ni AMMEY LAYLERH don jin yacce tafiyan zata kaya, kuma kada ku manta nace duk yacce kuka tunani to kuwa tabbas Ni AMMEY LAYLERH nace ba haka tafiyan yake ba🤗_
*BY AMMEY LAYLARH ✍️*
*༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻*
_𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _
♡
𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ
_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_
𝙋a𝙜𝙚
13&14
https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D
✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫*
(J.W.A)
♡
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
A Parking car na gidan ya haɗu da Nainerh tamkar yacce ya bata umarni tana tsaye hannunta riƙe da basket. Buɗe car ɗin yayi da kansa yana shigewa mazaunin driver ita ma buɗe motar tayi ta shige tana zama side da inda yake. Gaidashi tayi ya amsa har ya kunna car ɗin yayi yana ƙoƙarin yin reverse Anniey ta ƙara so wurin ba ta yi masa magana ba ta buɗe kujerar baya ta shige tana ɗauke kanta.Motar yaja da hanzari yana barin harabar gidan don yasan adda'ar sace ta karɓu tunda har Annie ta yarda zaraje Hospital ɗin. A hankali yake jan motar kasancewansa bame garaje a komin saba, Shiru motan ta ɗauka haka har suka isa Hospital ɗin loƙacin kuma wajen Sha ɗaya da wasu mintoci ake magana, Ita ce ta fara fita a motan Nainerh nabin bayan ta shi ne na ƙarshe kuma seya tsaya da wasu cikin dactor's ɗin donjin yadda suka kaya.Anan suke sanar dashi lallai da akwai gagarumar matsala don duk yacce suke tunanin abin to kuwa abin ya wuce saninsu. Har yanzu numfashin ta yana a mataki na 0-6 ne wanda kuma hakan shike tabbar musu da cewan lallai akwai matsala kenan. Kana a daren jiya kwana sukai basu bacci ba akan binciken kwallkwalwarta da suka kwana yi. Don haka dolen dole se an fita da ita woje don mata aiki. So d0n haka ma suka ƙira prof Sameer tun a daren jiyan suka sanar masa da komi yanzu haka ma ya shirya musu fita waje can ƙasar Spain daga can su wuce Madina. Kansa ya ɗago fararen idanuwansa da sukai nauyi kana suka ɗan sanja ya kalla likitan da kallo ɗaya ya ɗauke kansa daga kallonshi yana soma takawa ya zuwa ainihin cikin room ɗin da Meesherh take yana tafiya yana s nazarin maganar fitan dole wanda yake sake ƙoƙarin nazartan ma'anar fitan damuwa na sake wanzuwa akan fuskarshi'n. ba dan kai tsaye wani na iya karantarn yanayi na damuwar akan fuskarshi'n ba,Dan shi samm baya yadda da damuwa akan face nashi dan ba mutum bane me barin damuwan wani abu ya wanzu a face nashi ba.
★
Wannan maganar fitan da yaje kunnan Maah itace ta sake saka zuciyarta damuwa da ɗaukan wani irin nauyi tamkar wata zararra haka take jin kanta gani take yi tamkar komi ba a zahiri yake ba, gani take data rufe ido ta buɗe komi ze dawo mata Normal Kamar ba'ataɓa yinsa ba.a take takejin komi na shirin kwace mata kanta kuma na mata wani irin bala'in sara mata, ita kanta bata san sanda ta fasa kukan da babu mai jinsa ba bayan Allah da take fatan ya sassauta ma Rayuwar Meesherh. Don haka dole take son ƙarfafa jikinta kodan ai tafiyarn da ita don tasan halin Sameer akan taurin rai tsaf zaice bazata jeva, ita kuwa a wannan halin da Meesherh'n take ciki bata ga uban da isa hana mata binsu zuwa ko wacce ƙasa bace.
Dake dama already an riga an shirya fitan tun a daren jiya ya sanya
babu ɓata loƙacin komi aka fara shirye shiyen tafiyan.
Daidai da shigan sa cikin room ɗin daidai ake gangaro gadon da take kwance sanɓal ana tura ta dashi, komai nata a rufe ko fuskanta ba'a iya gani saboda kwata kwata tun jiyan ko motsi babu inda yayi a jikinta.yadda jikinta kuwa ya koma iyaka na jikinta kaɗai sune suke iya gane ta, domin kuwa duk kamanninta sun ɓace ɓat.Wani kalan rumtse idanuwansa yayi da suke sake sauyawa ƙirjinsa na wani irin bugu gaske ganin yau wacce yake ma kallon tamkar duniyarsa ce kwance a hali na mutuwa irin wannan, wanda idan aka ɗauke mahaifiya mahaifi a gareshi to kuwa Meesherh itace abu na farko da yake so fiyeda komai a rayuwarsa da komai daya mallaka, duk kuwa da cewan a yanzun duk babu wannan amma yana da tabbacin har yanzu zuciyarsu da ruhiznsu a tare suke rayuwa.
Jin yayi zuciyarsa na neman bugawa dan haka ya sauƙe wani irin numfashi me zafin gaske ya ɗago ahankali ya zubama Gadon da yay masa nisa idanuwansa sai yaji zuciyarsa na sake ƙoƙarin bajewa a wurin.Da hannu yama masu tura gadon alamun su dakata, a gabanta ya tsaya su kuma yana basu umarnin tafiya. zubawa fuskanta da yanzun ya ɗan zama ido yayi yana mata wani irin kallo me cike da tsantsan tausayawa,ƙauna, soyayyar da yake tunanin ta jima da mutuwa babu ita. Tin daga fuskanta yake kallon har zuwa iyaka shahsin daya buɗe ji yayi zuciyarsa na nauyi da kallonta a hakan, ashe dama bugun zuciyar daya taji akan tane kenan? Ashe wannan mummunan ƙaddarrar ce zata faru da ita shi yasa ya gaza runtsawa a daren wancan ranan? Ashe dama ashe dama ashe dama abubuwan da yawa har haka? Ashe ƙaddarorin masu girma ne har haka. Ta ita ya fara tafiya yana gungura gadon yana wuce sauran family's nasu. Duk suka rufa mashi baya suna jin tamkar abu mafi muhimmanci na shirin rabuwa dasu ne na har abada.
acikin series car aka jagoranci tafiyan nasu su uku kawai, Shi kansa uban gayyar se kuma Maah data dage dole itama se taje. Thabit Jedaans ne yace ma Sameer Jedaans ɗin kawai a tafi da ita daga nan se itama a duba ta tunda jikin nata babu daɗi itama. Hakan kuwa akai kai tsaye ta Lagos jirgin nasu ze tashi tacan jirginsu ze lula zuwa ƙasar Spain ɗin. Seda gaba ɗaya katafanin ahalinn Jedaans suka ma su Prof Sameer Jedaans rakiya har Lagos. Buɗe idanuwansa yayi ahankali tareda zubawa jirgin su daya fara landing na tashi yana kasa tantance a wanne mataki ya kamaci ace ya dauki hakan. Zurfafawan da dole dole yake son zurfafa Kansa ne ya sanya Wani irin ciwon kai dirar masa irin na loƙaci gudan nan. lumshe idanuwansa da suke masa zafi yay Mohan Sameer ne ya taimaka mashi wurin kaisa cikin car ɗin
♡
Tunda suka baro cikin airport ɗin ya kwantar da kansa jikin kujera yay shiru idanunsa dake da cikar baƙin gashi da gira a sama suna a lumshe suma. Bakinsa ne kawai ke motsawa alamun tasbihi yake a cikin zuciyarsa.
Duk yanayin da yake a ciki Mohan na kula ta cikin mirror'n hakanne ya sake sanyaya zuciyarsa akan du abubuwan da suka ringa faruwa. Haka dai sukaci gaba da tafiya kowa da abinda yake saƙawa a cikin rai da ruhinsa.Hakan ne ya sanya Mohan sake gudun motarsu sosai kai kace Jigawa suka nufa ba Kaduna ba. Tun kan 4pm tayi suka isa gida kai tsaye seda ya fara biyawa ɓangaren anniey kai tsaye loƙacin tana sama wurin Daddy, se kawai yay kwanciyar sa kan lallausar doguwar kujerar parlour'n ya fidda woyarsa yana saka ƙiran Hafeez Al'ameen a woyan. Babu jimawa kuma sega Anniey'n ta fito daga saman sanye cikin shiga ta alfarma kamar koda yaushe. Zaune ya tashi daga kwancen da yake gaidata yay ta amsa shi sama sama, daga haka taja bakinta tayi shiru se can kuma tamkar wacce aka tsikara ta ɗan dubeshi tare da sake tamke fuskanta me kyau sakk kalan tashi ta furta. "A ina maganar mu ta kwana" wani irin janye idanunsa daga kanta yayi yana jin yadda tambayar Anniey'n ta taɓa har cikin tsaƙiyar ƙirjinsa, uwa uba ga ciwon da kansa ke mai. "Anniey pls mubar wancan maganan don ALLAH!!!" Ya kai ƙarshen maganan cikin raunin murya sosai. "Auren Ƴar ƙanwar tawa kake cewa na ƙyale juraij, to wllh³ bara kaji na rantse sau uku to wllh seka auri Samha kuma nan da kwana kusa" fuuuuuu tabar wurin don sosai kanwar nata keta faman mata naci akan batun tare da sake hurata da rura mata wutar tsanar Meesherh da uwarta a cikin zuriyar ta. Sheikh kan tun da ya fita a gidan be sake dawowa ba se araoun 10pm wanka ko zaman dinner yau be yi ba tunda be shigo gidan bama. Ransa a jagule haka ya shigo gidan ko inda sassan mahaifansa suke bai nufa ba yay wucewansa nashi ɓangaren.
Tura ƙofar bedroom nashi yayi ahankali sanyin a/cn da kuma ƙamshin turarensa da baya taɓa ɓacewa na sake gauraye room ɗin baki ɗaya, kai tsaye bathroom ya wuce ya shower ya sakarma kansa ya fito jikinsa sanye da bathrobe. Fararen riga da wando na bacci dogaye ya sanya kai tsaye kan lafiyayyan gadonsa ya yay kwanciyansa yana dunƙulewa cikin fari ƙal ɗin duvet cover.
Kafin kuma Ahankali ya sanya hannunsa ɗaya ya janyo ɗayan pilonsa ba tareda ya buɗe idanunsa ba ya toshe kunnuwansa dashi saboda yadda kawai yanayin jikinta ke sake damun zuciyarsa, wajen karfe biyu da rabi na dare ake magana amma ya gaza yin bacci don haka ɗaura alwula ya dinga jera nafilfili tare da jera mata adda'o'in samun sassauci wa rayuwarta, ƙarfin ciwon da kansa ke masa na sake hauhawa.
~012 Alongside films shot~
*G 9 building* 4:22pm
✯
Zaune duka manyan director's dama ƙananun producer's suke cikin keɓan taccen wurin da suke gudanar da wasu manyan meeting nasu iyaka su yasu na. To yauma kamar kullum zaunen suke suna tattaunawa akan lamarin daya faru da ɗaya daga cikin manyan jarumansu wato *DIAMOND MEESHERH SAMEER JEDAANS* Se anan ne ma wasu ke jin abinda ya farun da itan. Tattaunawa sosai sukai director Abdulazeez Dakata daya kasance shi ne shugaban duka masana'antar shirya fina finan Hausa ne ya fara miƙewa daga nan se Muhsin Aliey Yahya shida Moh Ameern Saif. Mohan dake gabana ya juyo Yana kallon inda muhsin ke tsaye daga bayansa, hannuwansa cikin aljihun bakaken coat ɗin dake jikinsa. Iska se baza gashin kansa take har yana rufe may fuska. "Aikin ka na kyau babban abokin harƙalla" Moh Ameern Saif Jedaans ya faɗi da irin jinjinawar nan.
Dan gyara tsaiwarsa muhsin yay tare da fuskantar Moh Ameern ɗin se kuma ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya yana furta, "Ai tun ta gama nuna mana ita ɗin ƴar zafin kaice dole mu sauƙe mata shi right?" Shima dariyar Moh ameen saif ya fashe da ita tare da furta. "Mutumina baka da kyau fa ko kayi wanka!!!" Moh Ameern ya faɗi yana sake kashewa da wata mahaukaciyar dariyan."Jirgi ɗaya ne ya kwaso mu nida kai, kaidai kawai ALLAH yakai damo ga harbawa ko be ciba zeyi birgima" chakk kuma Moh ɗin ya tsaye da dariyan da yake tare da furta,"Se dai ban fahimci wannan hausan ba muhsin?" Don yasan halin Muhsin ɗin tsafff na cin amanar ko waye a masana'antar.(Idan na gama da ita banzar zan dake kanka nake nufi) ya furta a cikin ransa a baɗini kuma yana kama kafadar Moh ɗin suka ci gaba da tafiya, "Daɗi na da Moh tsoro tamkar ba namiji ba, ace kana gafjejen namiji kamar haka 👌 baka san wannan karin maganar ta ALLAH yakai damo ga harbawa ko be ciba zeyi birgima ba na jinjina maka" shima ya faɗi yana zaro wayarsa ƙirar apple tare da faɗin "Inji alert" ɗan hararan keyansa Moh Ameern yay a ransa yana ayyana kaima ka kusa barin duniyar ai.transper ya masa na 1:ml. A take yay hanzarin duba alert na kuɗin da suka shigo masa.
_Debit: 320XXXX397 Amt: NGN1000,000 Date: 03-MAR-2025 19:28:33 Desc: QS894:DT/101300014444937337/234703638033. Bal: NGN5,5000000 Dial *894*11# to get loan_ wani ɗan banzan kallo ya cillama Moh Ameern ɗin yana me furta. "Kasan kuwa abinda ka tura min Moh? One million kawai fa ka tura wanda iyaka kafin alƙalami ma ni tashin farko 2 billion na bama yaran da suka mana wannan aikin, amma kai da ka tashi seka tura min One kawai"
Wani ɗan zame jajayen laɓɓansa Moh yayi tare da furta. "Iyaka haka naga dama kuma iyaka hakan zan bada, ba kuma wai don bana shi ba A ahhh sai don kawai hakan na ga damar baka domin kai kanka kansa koda harafin Bb ba zaka taɓa samu a cikin zuriyar mu har ƙarshen rayuwarmu kuwa" "to kuwa wllh zan tone gaskiyan abinda muka bisne Ashe Moh"
"Idan ka fasa ba ɗan halak uwa da ubanka suka haifa ba, wa ya faɗa na ana wa ire irenmu barazana? Stop your dirty mouth all over again" daga haka ya tafiyarsan yana barin Muhsin da saƙar jaki. Khadijah yobe ce ta ƙara so wurin bayan data gama tabbatar da barin Moh daga masana'antar baki ɗaya. Ta na sanye ne cikin Wando palazzo pink colour da Shirt Navy blue , ta yi Rolling wani veil navy blue a kan ta shi ma, se ƴar karamar bag black Itama dake rataye a kafadarta, hannun kuma ɗauke da wayarta. Skin nata ba Farar nan ce kal ba dark skin gareta kalan Wanda ake yayi ɗin nan. Kana tana da manyan idanu ma su ɗaukar hankali wanda cikinsu yake farare ƙal ba laifi. Ta na da shape irin me ƙirar coca cola ɗin nan wato hips da breast din ta cike su ke bamm.
Ta ɗan ɗauka loƙaci tana nazartan yanayinsa kafin ta saki ƴar siriryar dariya tana dawowa ta gabansa tare da furta. "Da dukkan alamu wannan Moh Ameern ɗin na son kawo ma aikin mu wargi" Fesar da wata zazzafar iska ta bakinsa yayi yana naɗe hannuwansa saman shoulder nashi tare da furta. "Yobe pls I hate this.. a yanzun kawai hutu nake da buƙata ba ƙarin wata damuwar ba" yana faɗin hakan yau tafiyansa yana barin ta wurin tsaye, Miƙewa itama tayi tana rufa masa baya tana me furta "Muhsin can pls I promise me you'll wllh nayi alƙawarin tayaka kawo karshen waɗan can wawayen JEDAANS ɗin can Moh Ameern da kuma Meesherh cikin sauƙi" tayi maganan tanason cimmasa don ganin kamar ba zai tsaya ɗin ba, baki ta buɗe da nufin yin wota maganar ya riga ta ta hanyar furta. "Kin tabbata?"
"Yes I promise I will" ta amsa daidai loƙacin da take cimmasan.
"Thank you Yobe Naaaaa'' ya faɗi tare da kyakykyawan murmushi saman fuskansa. Wata Ajiyar zuciya tasaki loƙacin da yake mata magana kan ta shiga cikin car nashi. Cigarettes ya zaro a cikin gidanta seda ya kunna ta da lighter kana ya tada kan motar yana yin reverse tare da ficewa a wurin baki ɗaya.
*SPAIN*
Flight ɗinsu yana landing motor Ambulance ta Hospital ɗin tazo ta ɗaukesu.
*Welcome to Spain and Portugal Specialist hospital analyzing*
Dake magana ake ta kuɗi da kuɗi kai tsaye tun a daren ranan aka wuce da ita special screening room da ita. Dr John Amaan shi ne kan gaba wajen fara aikin. Dr Maheer Osman da ya kasance bahaushen ƙasar Nigeria ne tare suka ringa duk wani shirye-shiryen fara ma Meesherh aiki. Farin glass ɗin dake sanye a idanunsa Dr Masheer Osman ya gyara tare da kallar inda Dr John Amaan yake tsaye yana ƙoƙarin haɗa wata ruwan Injection."No
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 14