Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Haleemah wacce ta kasance kaka a gareshi ya fara cin karo. Gwaggo Haleemah yaya ce ga Ama kuma ita kaɗai take da ita ƴar uwa anan kusa idan ka cire dangin su dake saudia. "Aaaahhh lale marabu da babban angona, Juraij yau kuma kaine da kanka?, Kodai ɓatan hanya kayi Ni Ko nace banda wajen zaman masu ɓatan hanyar?" Tay maganar da murmushi kwance saman fuskarta. Zama yay daga saman 1str ɗin dake kusanta. Zamansa babu daɗewa kamar an cillota Samha ta shigo cikin parlour'n zaram tamkar ana tunkuɗota. Samha ƴa ce ga Surayya ƙanwa ga Annie kenan wacce kuma suke ƙoƙarin haɗa aurentane kuma da juraij ɗin, sedai sam yarinyan bata da kamun kai amma su basa ganin hakan babban burinsu kawai auren ya haɗu. Se data ta shigo kuma cikin mugun bariki da kisisina ta wani sinne kanta ƙasa tana furta. "Laaaah dama uncle kaine? To sannu da zuwa Bara a kawo maka juice" da hannu ya mata halaman bai buƙata. Dan faɗa fuska tayi tare da duban gwaggo Haleemah tana furta, "Gaskiya gwaggo ki ma Uncle juh magana! Shikenan yazo shi kullum ba zai ci abincin mu ba inda Ni ce na ce zan kawo mishi" Dan murmushi irin nasu na manya gwaggo Haleemah ta yi tana furta "Yo in banda abin kima Samha kwana nawa ya rage miki, ku ce kan kita masa girkin kalan wanda yake so, kuma dai kinsan juraij bai fiye son komai a sake ba, amma idan da gake se shi ne seki ta lallaɓa kayanki ko" ta ƙarishe maganan da Murmushin nan ɗauke saman fuskarta. Dariya ta saki tana rufe idonta wai ita ala nan dole an bata kunya.Daga haka ta shige dayan parlour'n dake kusa da wannan ɗin shi kuwa a natse yaja fruits ɗin dake gaban gwaggo'n apple ya ɗauka ya ɗan ci kaɗan. Bayan bata saƙon da yay ya miƙe da shirin tafiya. Suraj ne ya shigo parlour'n da yake shima jika ne ga gwaggo Haleemah'n. Gefensa ɗan wani matashin saurayi ne suna tafe gwanin birgewa. "Ahhhh yau wa nake gani kamar babban malami" ya fadi a washe hakwaronsa farare tasss waje, Bai bi ta kan iya shegen da suraj ɗin ya soma mashi ba yana bama matashin hannun suyi masabaha. Don ya san idan ya biye ma suraj ɗin babu ruwansa kunya ne kawai ze bashi. Ita kuwa gwaggo Haleemah bin bayan Samha tay, zama tay gefenta suka soma fira cikin dabara gwaggo take dan son lurar da Samha'n kan lamarin Sheikh juraij ɗin da ake shirin aura masa dap. Sedai maganan bawai tama ko fita bane iyaka yasu ya sune suke ƙusƙus dinsu tsakani. Sosai firan da gwaggo take mata akan juraij ɗin ke mata daɗi da sanyata nishaɗi ♡ Rasss gabanta ya mugun buga mata don ganin drector Muhsin Aliey Yahaya tsaye da wasu yara wanda kana kallon su kwanyarka zata Hasko maka cewan ƴan daba ne. Sedai shanye tsoron nata bayyanuwa tay tana karasa fitowa a motar nata kai tsaye ba tare data kalla inda yake ba ta shigewanta inda zasu gabatar da shooting film ɗin ta na. ★TAURARUWA♡ Film ne da take son yin cleaning up nashi Kan yadda waɗanda taurarinsa suke Haskawa a cikin duniyar suke wulaƙanta mabiya dama masoyansa. Tana shiga hall ɗin Hotels din da za'a gudanar da shot ɗin suka dauki sowa da ihun ƙiran sunanta. Kanta ta ɗauke daga kallon Moh Ameern Saif daya kafeta da ido. Nan aka soma gudanar da shirin cike da birgewa. Ba itane ta sama kanta ba se wajajen 5:40 pm. A matuƙar gajiye lilis ta fito daga cikin hall ɗin tana jin matuƙar haushin kanta na kin tahowa da ko gurds ɗaya da batay ba. Jingina da jikin Railer'n dake gaban hall ɗin tay idanunta lumshe. Ko dinner gaza yi tayi haka har wata actress me suna Khadija Yobe ta fito itama ta sameta. "Meesherh lafiyan ki kuwa?" "Hummm kedai Khadijah kyaleni wllh duk a gajiye nake jima nake kamar bazan iya driving ɗin nan bane ma wllh" "Me zai hana idan har babu damuwa na miƙaƙi gidan" ɗan numfashi ta fesar tana furta "No ba ma se kin hawal da kanki ba na kira ayrah amoh nace ta biyo ta nan ta tafi dani" "Kuma kina ganin har loƙaci bazai ƙure miki ba kanta ƙara so?" Khadijah yoben ta tambaye ta ko kafin ma ta bata amsar sega wata arniyar farar Roy *R* Rayce nan na danno Kanta cikin Hotels ɗin. Har gab dasu motar ta ƙaraso kafin a natse aka soma yin kasa da glass na motar, wani kalan zaro fararen idanuwanta woje tay don ganin.............. To ai Shikenan muma semu gimtse 👌 *BY AMMEY LAYLERH* Chat mee view My phone 07085041758 Or 08104493215 Don son magana dani AMMEY LAYLERH chart Mee or call a wannan No ɗin 08104493215 Masu neman *MIKIYA* ma har yanzun ƙofarku a buɗe take har yanzu yana nan akan farashin sa na ₦ 500 ban ƙara ba kamar yacce na ce a baya. https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D ༺༻ *༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻* _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _ ♡ 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ 𝙋a𝙜𝙚 9&10 ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* *𝙄 𝘿𝙀𝘿𝙄𝘾𝘼𝙏𝙀𝘿 𝙏𝙊 𝙂𝙊𝙑𝙀𝙍𝙉𝙈𝙀𝙉𝙏 𝙂𝙄𝙍𝙇 𝙐𝙉𝙄𝙏𝙔 𝙎𝙀𝘾𝙊𝙉𝘿𝘼𝙍𝙔 𝙎𝘾𝙃𝙊𝙊𝙇 𝙈𝘼𝙇𝘼𝙈 𝙈𝘼𝘿𝙊𝙍𝙄 𝙋𝙈𝘽 001* ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Don ganin Papiey'nta da tai zaune cikin car ɗin, duk da cewan ba abin mamaki bane a wurinta amma na yau ɗin se ya fi koda yaushe bata mamaki. Wata kyakykyawar ajiyar zuciya ta sauƙe me ɗan ƙarfi tare da nufo car ɗin ita da jaruma Khadijah yobe. Itane ta buɗe mata gaban motar kusa da Papiey'nta ta, car key nata ta miƙa mata bayan ta gaida Papiey'n tare da cewa tayo dropping car ɗin zuwa gidan su tun da dama ba sa da woni tazara sosai. Itama Khadijah yobe ƴar masu hannu da maiƙo ce sedai idan dasu Meesherh Jedaans a wuri babu Powerful ɗin kowa da ke aiki a kafff ma faɗin garin Kd da zagayenta. "Papiey yau ka tuna dani kenan?" Shi ne tambayar data fara jefa ma mahaifin nata Duk da tasan cewan tasan kwanan zancen ba zai wuce sake kwantar mata da zuciya da zai yi ba. Left hand nashi da baya driving dashi ya sanya yana kama nata tafin tare da jimƙewa a cikin nashi, cikin tsananin jarumta da ƙarfin hali da kuma son kwantar mata da hankali ya furta. "Baby ita Rayuwa da kike kallo komai yana zuwarma bawa ne ga bisa umarnin abinda ya tsara a cikin tarin Rayuwarka! Ina son kici gaba da shanye komai da zakici gaba da fuskanta daga can gida, amma ba ta yadda komai ɗin ze zama illa wa taki Rayuwar ba. Insha Allah wannan karan komai ya kusa daidaita da yardan me du ka wato Ilahu Sarki ALLAH, Sarkin da babu kamarsa buwayi gagara misali ina..jin... Ina...jin...ina.........jin matuƙar ciwo sosai da ɗaci kan aibantamin MY BABY'n Papiey da ake... Muryan shi ce ta soma rawa da ƙoƙarin karyewa dan haka yay shiru yana sake damqe hannuwan Meesherh ɗin da ɗan ƙarfi yana qasa da idanuwansa da suke neman cikowa da hawaye. Don sosai Maganan Anniey ya buge shi se dai samm baya taɓa damuwan komi akan face nashi kan duk wani mahluki dake cikin estate ɗin nasu koma na ce family. Jin rauni ya wanzu a cikin muryan papiey ne ya sanya ta itama ɗin sake kame hannuwansa cikin nata ta na kasa cewa komai dan tasan kuma ba zai iya ci gaba da maganan ba kenan. Ɗan lumshe fararen idanuwanta tayi A bayyane kuma ta shiga furta adda'ar "Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir³ Ra rabbi inni magalubun fantasir³ la haula wala quwwati illa billahil aliyal azeem³, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ³" haka ta shiga ambata tare da sauran adda'o'in da duk suka zo cikin bakinta. Ajiyar zuciya me sanyi papiey ɗin ya sauƙe a natse yanajin hankalinsa na dawowa jikinsa take yaji dacin zuciyarsa ya ragu sbd yadda adda'o'in data karanto ɗin suka ratsa shi sosai tare da zuciyarsa. slowly kuma ta shiga ware idanunta tare da sake sanya hannunta tana jinginar da kanta jikin papiey ɗin nata, daga haka tafiyan nasu ya koma na kurame har suka ƙara so mahaukacin estate ɗin su, Shi ya fara fita jikinsa duk a wani kalan amma yadda yake tafiyan cikin nutsuwa kai kace babu abinda ke damun Rayuwar sa nan. Lugagge bag na papiey kawai ta dauke se handbag nata tana bin bayan mahaifin nata. tana tafiyar ne kuma tana ɗan shedding tears nata zuciyan ta na ƙara yin nauyin abubuwa da yawa da suka kanainaye cikin rayuwarta. A bakin entry na babban parlour'n gidan sukayi kiciɓus da Moh Ameern Saif inda ita ta tura shi kuma ya turo. Kin sakin ƙofan tayi tana kuma ƙin kallonsa, sake murɗa handle door ɗin yay yana jan ƙofar baya ya kuma ja ya tsaye yana ƙare mata kallo tun daga samanta zuwa ƙasa. A ɗan kausashe ta furta "Moh Bani hanya" Ɗan girgiza kai yayi kawai tare da ɗan taunar lisp nashi, Wani shegen killer smile yayi tare da ɗan shafar gashin ƙeyarsa yana me furta "Ohh Ohhh beb wai cikin sauƙi haka?" Yay tambayan cikin ɗan iskan salon jan hankali da kuma rashin mutumci. Chakkk ta tsaya daga ƙoƙarin raɓa gefen Moh Ameern ɗin da take niyar yi. Sakamakon tausasan hannuwan da taji ya raba tsakanin su ta hanyar janye ta daga niyar shigan, ko bata juyo ba ZUCIYAR TA ta riga da ta gama sanar mata ko wa ne ne. Hakan yasa ta jan idanunta ta lumshe su gaba ɗaya. Moh Ameern daya ƙame cike da tsoro da kuma kafe Sheikh juraij ɗin da ido yake kallonsa, Shima idanuwansa da suke a rufen ya buɗe tarrr akan Moh Ameern. Kafin ya saki wani murmushin rainin wayo tare da zamar da ƙasan lips nashi ya furta. "Shi kuma wannan ko a cikin wanne hadisin ne ko sura ohooooo, amma ko ba komi abin ya bada gitta da ƙyau Sheikh babban salo!!!" Haka muryan juraij ɗin ya dake shi Sheikh juraij ɗin. A natse ba tare da garajen komi ba ya rabata da jikinsa yana jefawa Moh Ameern ɗin wani kalan mugun kallo me tattare da cikakken gargaɗi. Ita ne ta fara barin wurin tana jin yadda ƙirjinta ya ɗan ƙare mata tare da mata wani kalan nauyi wanda dama har yanzun bawai ta gama warkewa bane rass. ★A ƙaton parlour'n su wanda yake ɗauke da duk wani nau'in jin daɗin rayuwa ta tarar da duka su Maamah har dama ƙarin babbar yayarsu ummeterh. Da sauri ummeterh ta nufo ta tare da riƙe hannunta fuskanta ɗauke da kyakykyawan Murmushin da ya sake fidda tsananin kamanninsu kasancewar su duka Ukun kamanninsu ɗaya. "Ma sha ALLAH Dear lallai jiki yayi sauƙi tunda har aka iya fita shooting yau" ɗan murmushin yaƙe tayi tana shafa kan baby'n nuwaira da ita ma ta nufo su fuskanta cike da farin cikin ganin Aunty Meesherh ɗin. "Dama ay duk laifin Maamah ne banda haka ai naji sauƙin sosai!" Maama'n da itama ta taso daga idda take zaune ne ta dawo ɗayan gefen Meesherh'n ta zauna ahankali tare da dafata fuskan ta da ɗan murmushi ta furta "Ko yanzu nasan babay'n papah ba ta da cikakken lafiya kawai dai kina danne hakan ne na sani" "To banda abinki Mamman'su Karfa ki manta Meesherh fa ita ma ce ce wata rana haihuwa zatay, tun daga yanxun idan bata koyi ƙarfin hali ba se yaushe kike son ta koya?" Papah ya bata amsa da hakan yana hayewansa sama. Mohan Sameer da shigowansa kenan parlour'n shima yama kansa mazauni akan ɗaya daga cikin expensive chairs da suka ma parlour'n ƙawanya. Yana ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana fuskantansu su duka cike da farin cikin ganinsu su dukansu. Aunty Ummeterh ya fara gaisarwa kana ya sake gaida Maamah duk da kuwa cewan babu jimawa suka Hausa ɗin. Lil juraij dake riƙe da hannun Mohan ɗin ne ya zame cikin wayonsu irin na yara kai tsaye ya nufi inda Meesherh take, duk kuwa da yadda take ƙoƙarin ɗauke fuska daga yaron,cikin muryan gyaranci ba sosai ba ya ce "Otty kin ga ni paap ne ya bani kuma yace karna fatawa kowa ma" yay maganan cikin gwaranci ba sosai yana mata nuna da wani Rolex watch na diamond gold me kyau kalan na yaran nan me shegen tsada da kyau. Ɗan taɓe baki Maamah tayi tana juyar da kanta daga kallon yaron tana maidawa kansu Ummeterh da Mohan da suke wata maganar daban. Miƙewa tayi da niyar tafiya amma lil juraij ya maƙale mata duk yacce ta so data yagar dashi kuwa. Gashi zuwa loƙacin kanta sosai taji yana juya mata gashi wasu masallatan harsun fara ƙiran sallah, dole dashi ta tafi sama yana maƙale da ita. Duk da ido suka bita kafin Mohan ya kalla Maamah tare da furta "Maamah don ALLAH Meesherh ta dakata da aikin nata don yanzu kamata yay ace tana gidan aurenta, Ki duba fa tana age na 24 year's ba ai yaci ace ma tana da nata babay'n itama" tunda ya soma maganar Maamah ta kafe shi da ido ko ƙiftawa batayi seda ta tabbar da ya gama ta furta. "To sannu ubana da wannan ai kamata kawai yay ka bani umarni, ka ga Mohan ka fita ido na In rufe idan har kaima ba zaka iya bin Meesherh da fatan Alkhairi ba to kamata yayi kaima ka janye idanuwanka daga gare ta" ta ƙarasa maganan a fusace tana miƙewa tare da barin parlour'n baki ɗaya, don Maamah irin iyayen nan ne masu shegen S0n ƴaƴansu wanda basu ganin laifinsu ko kaɗan, se dai sammm bata barin ko waye daga cikin yaran nata ya aikata ba daidai ba kuma ita mutum ce da bata iya ƙunbiya ƙunbiya da abu ba ita ɗin karan tsaye ce ƴar kai tsaye me gaɓa². Ko waye ya taka ta to kuwa lallai itama zata taka shi don bata ɗaukar raini kamar yacce itama bata raina kowa se har in mutum shi ne ya fara shiga hurumin ta da wata sigar ta daban, to kuwa lallai anan ne zaka gane ko kai ɗin wane ne. Ajiyar zuciya me tattare da damuwa Ummeterh da Mohan Sameer suka sauƙe kusan loƙaci guda kan kalaman mahaifiyar nasu, duk kuwa da cewan ba yau bane suka saba fuskantar hakan daga gareta. kawai abinda suka sani suke kuma so shi ne suga sun inganta rayuwar Autar nasu, sun gaji da ce ce kucen da ake akan Meesherh ɗin daga media harma da nan cikin gidan nasu kuwa. Tabbas hakan na masu ciwo da kuma matuƙar ƙona musu zuciya. † *Sheikh juraij* Tunda yabar wurin kai tsaye cikin garden yay shigewansa, sanyi da kuma iskan dake kaɗawa a wurin na ratsashi wanda har yake jin kamar fatar jikinsa ce ta bude kai tsaye sanyin yake ratsa masa ko wanne sassa na jikinshi yana daskarar da duk wata magudanar jini ta jikinsa, kamar kullum yana sanye cikin shigar farin yadi me azabar laushi da tsada ɗinkin jumper cables irin na zamanin nan amma kuma ba masu sherp da yawa ba irin na matasan yanzu. Sumar nan tasha gyara na musamman se fidda daɗdan ƙamshin take yi gami da daukar ido. Sajen nan yay luf luf abunsa har wani kalan shine blue yake bayarwa daga nesa. Sanyi haɗi da daɗin iskar ne ya sanya shi kasa zama wuri guda don haka ya shiga zagaye cikin garden ɗin,Hannuwansa goye a bayansa daga can ƙasan zuciyarsa kuwa yake furta. _Subhanallah,wal hamdu lillah, wala'ila ha ilallahu wallahu akhbar³_ Da dai duk sauran adda'o'in da duk suka zo bakinsa, kai tsaye ba zaka taɓa fuskantan tasbihi yake ba sedai ka kalla fatar lips nashi kaɗan tana motsawa. Sammm yama rigada ya manta da abinda ya farun yanzu ko na ce dazu. Ganin loƙacin ƙiran sallah yayi ne ya sanya shi fita, se da ya fara shiga bedroom nashi kana ya fito kai tsaye yana shigewa cikin babban masallacin dake cikin anguwarsu. Shi ne ya ƙira sallar ya kuma ja jami'i cikin wannan daddaɗan sautin nashi da sauraran yanda yake fidda tajweed nashi yake sanya mutane cika masallacin duk kuwa kalan girman da yake da. Dama shi ka'idan sane baya shigowa se bayan sallar Isha'i sosai shi yasa kowa na gidan ke riga shi kammaluwa a dining room ɗin,duk da kasancewar tonight baya zaman dining room ɗin amma kuma hakan jiran shigowarn nashi ya zama kamar al'adan kowa. Iyayensu mata kawai ya gaida kasancewar sun gaisa da iyayensu maza tun a can cikin masjid ɗin.Nan ƙannashi maza da matan suka gaida shi shima,A natsensa ya amsa su yana kallar bakin Meesherh da kuma Moh Ameern Saif da babu su a cikin jadawalin gaisuwar. Directly balcony ɗin da ya saba zama kai tsaye wuce maids ɗin dake aikin shirya dinner ɗin na binsa da tea plask ɗin dake ɗauke da zazzafan tea wanda duk daren duniya shi ne kawai yake sha. Jere mishi tay daga inda yake idanunsa lumshe yana ambatar sunan ALLAH acan ƙasan ranshi. Se da ya tabbatar ta bar wurin kana ya buɗe idon yana jan tea plask gabansa. A natse yake sipping tea ɗin abinsa daga gefe dashi kuma System nashi ce yake aikin sarrafa ta. Yau be daɗe a wurin ba kamar kullum ya tashi ya tafi don yana da abinda zeyi a daren. Ga yawan bugun da zuciyarsa ke mai akai akai yana jin tamkar wani abu mara daɗi na dab da faruwa dashi, Amma sosai yay ƙoƙarin danne hakan se adda'o'in sa da yaci gaba dayi yana adda'an koma miye zai faru dashi to Ubangiji ya kawo shi cikin sauki ya kuma takai ta ma masa ɗin, da haka yanar wurin yana daura alwula tare da fara jero nafil fili wa mahalicci'nsa... ☆ Meesherh kuwa koda ta koma bedroom nata wanka tayo ta shirya kanta cikin singlet ta mata da wando. Army green da farar singlet inda tayi stocking singlet ɗin cikin wandon ta ɗaure da beld. Sai light green ɗin top wadda ta ɓalle duka maɓallanta ta barta a buɗe, Iskar da ake kaɗawa a gurin na diban rigar nata tana kamar zata cire,gaba ɗaya rigar tabar jikinta sai singlet ɗin kawai, tsaye take daga jikin window na bedroom ɗin ta tayi crossing ƙafafunta suna a harɗe. Sosae iskar dake shigowa ta cikin window'n ɗakin ke mata daɗin shaƙa tare da ƙamshin flowering dake ata bayan window nan suke sake bata nishaɗi da jin cikakkiyar nutsuwa, saima taji ta nema ciwon kan data shigo dashi ta ne meshi ta rasa.♡ Shi yasa most especially Idan tana cikin yanayi mara daɗi idan bata son fita balcony takan tsaya a wurin ne ta yaye duka labulayen wurin nan take samun cikakken nishaɗi sosai. ☆ Lumshe fararen idanuwanta tayi tare da faɗawa wata duniyar ta daban, tunani take akan baya idan tace baya tana tunanin Baya cann da dadewa kafin rugujewar komi. A cikin idanunta dake lumshe komai daya faru yake dawo mata daki daki tamkar komai daya faru ne a waɗan can loƙutan haka komai ya Shiga zeroying mind nata. Saurin dawowa hayyacinta tayi sakamon zuciyan ta da taji tana son maido mata da hannun agogo baya, Bayan nan da har gaban abada bata fata da burin dawowarta cikin rayuwarta koda a matsayin mahaifin ne a gareta. Domin mahaifiyarsa ta rigada ta gama ɓata komi tun a wancen loƙacin. A yadda ta tashi ta tashi ne ta buɗe Ido da shi, Shi ne mutum na farko data fara ƙira da pa'apahh........... Akan shi ta fara koyan magana tana yima kowa ƙyuwwa amma banda shi ciki kuwa har da Maamah'nta. Domin matukar Meesherh tana wurin juraij bata yarda da kowa bata kuma zuwa wurin kowa se pa'apahh'nta juraij. Ta kai ta kawo ko bacci zatay se da shi a gefenta, shi ke maga wanka ya wanke mata fufu idan tayi, ya goye ta a gadon bayansa da zani irin yanda uwa kewa ɗan ta, a loƙacin shi yana da shekaru sha bakwai a duniya ita kuma tana da 1 year's a cikin duniyar, Shi ne ya Renata yaci kashinta yaci fitsarinta har zuwa sanda ta shekara biyar a duniya, A kuma daidai loƙacinne abubuwa suka soma Sanja kansu, suka kuma soma samun saɓani wanda shi ne farkon jinin tubalin da har ya kai su ga irin wannan matakin da suke kai a yanzu. ♡ Duk wasu ɗabi'iu kalan nashi take yi masu kyau a da can baya kai takai ta kawo ko cima bata cin abinda baya ci, iyaka abinda pa'apahh'nta yake ci itama shi take ci. Saɓanin farko da suka fara samu a cikin rayuwarsu shi ne tun da ta ɗan ƙara wasu shekaru a cikin shida zuwa tara/goma ya fuskanta ita ɗin mayyar jin kiɗe-kiɗe da waƙe waƙe ce, ga shegen son kallon tsiya a wurin ta kamar me, duk yacce zeyi don ganin ya cire mata hakan abin yaci tu ra. Har yakai ga ya dena shiga lamuranta na wasu ƴan loƙuta haka zata zo ta shige jikinsa tayi ta masa koke koken banza har se ya dawo ya kula ta, Amma hakan bazai hana gobe ta sake kunna casunta ba, haka zata sa ata sawo mata irin kayan indiyawa sune kayan sawanta. Ya tattare ya ƙone amma haka Maama zata sake sawo mata wasu. Kai har takai ta kawo Meesherh ta dena shiga cikin duk wasu lamura na Juraij ta dena tsoronsa ta dena ƙiransa da sunan data bashi na pa'apahh wanda a da yayyenta shi kuma ƙannensa koda mutum ne yay kuskuren ƙiran sunan shi da sunan da ita kaɗai take son take ƙiransa da abinda to kuwa ranan wunin rigima zata wuni tana yi. Amma se gashi sannu a hankali komi nasu na sake samun saɓanin ra'ayi. Se kuma a karo na biyu loƙacin da ya fahimta Film ta karanta, wannan shi ne tushen komi... Shi ne tubalin dayay sanadiyyar rugujewa da watsewar komi don a nan ne Mahaifansu suka samu babban saɓani na farko kowa ya nuna nashi na shi ne. Daga nan komi ya tsaya musu cakkkk kowa ya fita a rayuwar kowa fita wacce suke jin fita ce ta har gaban abada abadan. ☆ ★Wani gauron numfashi ta kawo me kyau lokacin data tuno kaɗan daga cikin wani sashi na rayuwar da suka shuɗe na baya. Tsaye ta miƙa daga zaunen data kai gefen bed nata zuciyarta na wani kalan bugu very slowly ta miƙe. Waƙar (pareshanura ) ta cikin film ɗin Dhruva na jarumi _Ram Charan_ Wacce sukai da _Rakul preet_ ta kunna tana ƙure volume ɗin. Waƙar na sata shiga wani yanayi mai wuyar fassara tare da ɗebe wan can tunanin nata tana ta rawa

Chapter 5 of 14