Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gaba ɗaya kuncewa yaji yana naiman hakan ya sanya shi ja baya yana raɓata a hankali da nutsuwansa yana barin wurin. Kafe bayansa da idonta da suka kusan tara ruwan hawaye tayi tana kallonsa a hankali cikin yanayin daya sanya numfashinta neman yankewa Amma tana danne hakan a natsen ta kuma ta janye. Tuni Samha kuwa cikin wani irin uban tashin hankalin abinda ya faru da maganar da Sheikh juraij ɗin ya yanka mata akan taɓa koda da farcen karen gidan daya kasance ahalinsa ne ta sake yin ƙurinyi to kuwa tabbas anan ne kaɗai zata gane cewan me aka nufi da hasalin ƙure haƙurin me haƙuri da kaishi bango. Ta bangaren Meesherh kuwa kota kan banzar bata sake biba sema su Aysha da tama magana tare da basu wata farar envelope tace su hau machine. Tunda suka ɗauki hanya suke maida zancen yadda abin ya faru. "Wai kinsan wllh a loƙacin nan har wani zazzaɓi naji na neman rufeni kuwa take?" Caraf Rumaisa ta amshe da cewa "ayke zazzaɓi ma kikace da sauƙi Aysha ni wllh Jima nayi kamar nayi fitsari a wurin ashe haka ta iya wanza almasifatu itama. kai jama'a yaseen ALLAH ka rabamu dayin amai mu lashe abinmu jiday woni faɗan rashin gaskiya a wurin matar cen fa" Rumaisan ta karasa da alamun mamaki tattare da ita. "Wai kam nace ni baki lura da kamar cewa ita ɗayar tamkar tana kishi ne da Aunty Meesherh'n bane? Cewar aysha'n. "Nifa tsaya kiji ma A'isha wllh se da nai tantamar wai wannan itace matar da ze Aura, ke kina ganin ta wllh kinga wankakkiyar ƴar duniya wllh samm basu ma dace ba dan se sukafi ma dacewa da Aunty Meesherh'n" hmmmmm A'isha'n ta kawo ijiyar zuciya tare da furta "Kinga forko dai shi mutum ne wanda ubangijin yayi mishi baiwar ilimin addini dana zamani.kana yana ɗaya daga cikin manyan malam da Afirka kai dama duniyar baki ɗaya ke ji dashi. Sabida a duk ƙiyasin malamai babu yaro matashi mai jini a jika da tarin ilimin addini kamarshi suka gama ratsashi wanda akace tun yana da ƙananun shekaru ya gama haddace al'ƙur'ani mai girma a kansa.kana ga jibgin littatufan dake kansa suma da yake da haddarsu suma a kanshi fiye da zaton me tunani.ga tarin baiwa daraja ɗaukaka amma kuma a ce ya ƙare a wannan abar!?, Ni wllh sammm banma ji ta ko kwanta min a raina ba. Kifa duba kaff girman Kaduna babu malami babba kamarsa daga nan har Lagos kai harda ma sauran garuruwa Kinga nasaba kan nasaba kenan. In kyau ne kuwa na halitta babu ta inda ta isa ta ko kamo tafin ƙafar sane, In kuwa kuɗine ai base an baki labarin ko su waye JEDAANS ba, Shi mutun ne wanda ya gama samun kekykyawan zato a wurin mutanen duniya baki ɗaya, to kuwa kinga tako ta ina ya tserema tsararta kuma bazance wannan aikin asiri bane don wllh ko kaffara bazan yiba duk da ance asiri gaskiyar me shi wanda ko Annabin ALLAH be kauce masa ba amma kuma IN SHA ALLAH wannan asiri bazai taɓa kama shi ba don shi ɗin. SPECIAL ne" Duka a tare suka sauke ajiyan zuciya suna yin shiru kuma suna rasa abin faɗa ma baki ɗaya. ꨄ Sosai aka shiga shirye shiryen yadda ɗaurin Auren Sheykh da Samha zai kasance a duka family biyun,Inda amarya Samha se wani jiji da akai ake za'a auri babban mutum kamar Sheikh juraij Jedaans uwa uba kuma tarin dukiyan dashi kansa bema San adadin tashi ba bare aje kan ta ahalin kuma. Sosai shirye shiryen komai ya gama kankama cikin ƙanƙanin lokacin daya musu saura, iyayen Samha kuwa se aikin banka mata magungunan mata suke. Banda wanda ita kanta Samha'n take banka da ƙawayenta suke kawo mata tsadaddu masu shegiyar tsada. Mayuka kamm na bleaching ai ba'a magana wai duk suma a cikin kaya na gyaran jiki suke. Wanda kuma Ayau ne gidansu su juraij suka kai kayan lefe gidansu Samha, Inda suka sami tarɓa ta girma da girmamawa. Inda babu kunya samha ta fito tare da tarin ƙawayenta da suka cika gidan kallon kaya tun a gaban su ƴan gidan. Yayinda su papiey ke can suna tattauna yadda ɗaurin auren ze kaya. Wanda cikin masu kai kayan harda Aunty Ummeterh Amma Maah bata je ba. Ita dai Aunty Ummeterh a ranta take ayyana lallai akwai gyara a lamarin wannan amarya, duk da kuwa kasancewar itama kamar ƴar gida ce dan sun santa sosai, don wllh ita har cikin ranta take jin tausayin Sheikh ɗin kasancewarsa bai wani cika zafi da yawan magana ba'a mafi yawan lokuta. Ita kuwa Samha se wani gani gani take ma Aunty Ummeterh ta dan itama tun kan haka take jin ta tsani duk wani wanda suka haɗa jini da Meesherh haka kawai. Wando da riga ne a jikinta ƙirar ƙasar kuwait inda farin nan ko nace jan nan har wani shuni shuni yake irin me ɗaukan idon nan . ꨄ Ata ɓangaren Meesherh kuwa gaba ɗaya tayi sanyi sosai da zancen Auren ganin dai tabbas gadan gadan kullum maganar da ranakun ƙara kusanto kansu suke se kawai ta ware kanta ta a komawa rayuwarta ita kaɗai babu ruwanta da kowa, sema harkan Film ɗin da take son ta saki a cikin satin da suke ciki shi ya sake dauke hankalinta daga bikin. *BY AMMEY LAYLERH ✍️* ꨄ *༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻* _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _ ♡ 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ 𝙋a𝙜𝙚 21&22 https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* Waɗanda suke buƙatar samun litattafan *AMEEY LAYLERH* za ku iya shiga shafin ta na Telegram don samun su kai tsaye daga wurin ta. Ga link nan ga masu buƙatar shiga 👉https://t.me/ammeylaylerh_novel ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Masu iya magana sukace wai Rana bata ƙarya, tabbas wannan karin magana haka take don kuwa a yau ne ranar asabar dubban jama'a suka shaida ɗaurin Sheikh juraij thabit Jedaans tare da amaryarsa Samha Abdulkareem Wada a babban masallacin dake nan cikin anguwarsu. Biki da bidi'a sosai dangin amarya suka shirya wanda suka san ko guguwar me Sheikh ya sha sun san bazai jeba. Haka suka inga gudanar da taron bikinsu Amarya Samha kuwa ba'a cewa komi. Don wani irin zumuɗi take yi na bikin. Wanda kuma a daren ranan ne aka dangan tata da gidan Sheikh ɗin, dake sun san tsarinsa babu bidi'a ko kaɗan ya sanya baffanta da kanta ya kai ta har ɗakin mijin nata. Sedai ya tarar da wasu dangin mahaifiyarta a gidan shidai seda ya tabbatar ya danganata da ɗakin mijinta kana ya mata yar nashiharsa kan tabi mijinta kar kuma ta ɗauka halin mahaifiyarta. Fitowarsa daga wanko kenan ta shigo kamar an jehota room ɗin. Kawai sai sauƙar hannuwanta yaji saman fresh naked skin ɗin sa, farko seda gabansa yaji ya may wani mummunan bugu amma yana jinta bai ko motsa bare  ta saka ran zai tanka ta, cik6 nutsensa ya zame hannuwanta data zagaye shi yana zaunar da ita gefe da bed ɗin. Kai tsaye kayansa na bacci farare ya kwasa yana komawa bethroom ɗin daya fito ya kimtso kansa cikin dogayen lallausan kayan baccinsa na long sleeve pyjamas, seda ya gabatar da nafilfili kana ya dawo kan gadon yana kwanciya don shi shafff ma ya manda da wata ana Samha zaune a dakin. Daga inda take zaune ta miƙa hannunta a bayansa kasancewar rufda ciki ya yi slowry ta fara shafa bayansa she's try to make him feel emotions for her, da wani irin tarin mamaki al'ajabi ya yayi saurin juyowa yana sauƙe kallonsa a kanta. "YA SHEIKH BACCI" ta furta cikin wata shegiyar murya wai irin zata rinjaye shi ɗin nan tare da sake ɗora hannunta a waist ɗinsa ta zagaye ƙugunsa da duka hannuwantan, duk abinda dake mishi yana jinta sai dai he's not interested bai da feelings ko guda a kanta bare ta yi tunanin zai ji wani abu dangane da abinda take masan, abinda kawai ya sani feelings nashi yana jin sane kawai akan mutum ɗaya wanda a farko ma shi yasa kota kota baida cikakken lafiyane irin na kowanne cikakken ɗa namiji. Se daga baya ya gane ba haka hasalin karatun yake ba shi wannan feelings ɗin akan tane kaɗai yake tasiri domin duk inda cikar mace takai mace to ko ɗan yatsar ƙafarsa bai harbawa bare har aje garin jin feelings a knata. shiru kawai yayi yana jinta yana son mata magana Amma kuma baison shiga haƙƙinta gudun kar ALLAH ya kamashi da laifin rashin kyautatawa a gareta tunda yanzu mallakinsa ce ta zama matarsa ta sunna. Daɗi da ƙari baison hayaniyar komi saboda yadda yaji gaba daya komi da komi na sire mishi kansa kuma kamar zai fashe ya tsage gida biyu,jin tana ƙoƙarin sanya hannunta cikin bxer ɗinsa ne ya sanya ya yi saurin haɗe ƙafafunsa tare da mirginawa ya ware fararen idanunsa a kanta, ita kuwa samha jin ya dakatar da itane ya sanya ta buɗe idanunta don ta riga da ta gama sakawa ranta cewan yau zata kwashi romonsa. Jikinsa har wata tsuma tsuma yake ya mike tsaye tare da mata nuni ta fita. Ƙi yawa tayi sema sake ƙoƙarin rarumarsa da take sake niyan yi hakan ya sanya shi miƙewa tsaye yana furta "pls Samh kije bana cikin ko wanne kalan mood moment ne" cikin wata maraitacciyar murya ta furta "Please jurh ka saurare ni wllh I love you to the rest of my life,kai kawai nake gani na ji farinciki,I want to stay with you forever! I want to stand by your side Ina sonka wllh na yarda zan kwana anan ba tare da munyi komi ba" Wani irin yunƙuri yaji zuciyansa ta masa wanda yake ƙoƙarin danne ɓacin ransa a kanta amma duk yacce yakai ga hakan hakan seda ya gagara hakan ya sanya shi nufar inda take cikin tafasar zuciya amma a normal nashi yake.haka ya ja hannunta kiiiiiiiiiiiy har nakin doorhandle na room ɗin ya a cillata woje tare da rufe ƙofar yana jingina da jikinta, yana jin tamkar ana gasa kanshi ne a cikin ovan, daga ta cen ƙasan zuciyarsa kuma yana jin tamkar hakan dayay ya saɓa wota lamba ce, yana jin tamkar ya aykata ma abu mafi soyuwa a cikin zuciyarsa wani abu ba daidai ba. Yana jin idan da ace itace yau a matsayin mallakinsa kuma halaliyara a yau zata kwana a gidansa matsayin matarsa to kuwa da babu abinda ze hana komai faruwa a wannan daren. Don yana mata wani irin Mahaukacin S0 ne wanda ko a baki aka tambayeshi wanne irin so yake mata bazai taɓa iya furta shi ba abinda kawai ya sani yasan He luv her more & more & more for ever never. Se dai kashhhh idan ya tuna a yanzu ko wacece ita wani irin zafine ke yankar zuciyarsa da ƙirjinsa na irin yacce take gudanar da rayuwarta yanda take so, Ya so ta taso killace a kamile cikin kamalar rayuwa bawai ta zamo me talla wa jikinta ga wasu mazajen duniya na amma wannan kalma ta ƙaddara ta riga fata, ta riga ta gama yima kanta gurbi daram a cikin babin ƙaddarorinsu da haka ALLAH ya rigada ya gama tsaro musu, wanda sau da dama idan ya tuna yacce take mu'amulantar jama'a yakanji ma kwata kwata tama gama sirewa a kansa, amma dake ance so jarabta ne so masifa ne duk yacce yakai ga munana ta a cikin zuciya dama kwayar idonsa da ruhinsa se abin yaƙi tasirantuwa a cikin brain nashi. Innalillahi ya shiga natata yana jin tamkar yana masa dakan ɗaka ne a cikin taaƙiyar ƙirjinsa. ✯ Washe garin ranar. Zaune take akan sofar dake parlon hannunta ɗauke da wayarta tana ƙoƙarin saka ƙiran mahaifiyarta kana ganin yanayinta kasan She is not felling Wall,Idonta ya kumbura sosai saboda kukan data kwana ta nayi a daren jiya lips nata har tashi yayi saboda tsaban kukan data kwana da kuma irin yadda mararta ta azabtar da ita. Shi kuma Sheikh ya rufe mata ƙofa tayi bugun duniyar yaƙi buɗe mata kofa tunda ya hankaɗota wojen nan.Jin kamar an zauna kusa da ita ne yasa ta ɗaga rinannu idanunta tare da sauƙewa akan Sheikh wanda ya zuba mata ido tare da furta. "Are you Okay?" Zuba masa idanun nata tayi jin har yana da bakin da zai iya tambayan abinda ke damunta se kawai ta fashe da kuka wanda ya sanya Sheikh Runtse fararen idanunsa domin ya tsani yaji ana kuka kusa dashi, kukan ma ace na mace, macen ba kuma wacce take matsayin mallakinsa. gyara zaman sa yayi har laps nasu na gogan juna wanda ita hakan ya sanya tsikan jikinta wani kalan zubawa, shi kuwa babu abinda yaji. Yana ƙoƙarin sake mata magana kawai ta faɗa jikinsa tare da ƙanƙameshi tana sake sakin woni kukan tare da cusa kanta cikin tsaƙiyar ƙirjinsa. Wani irin yankewa yaji gabansa yayi ya faɗi kansa na sarar masa loƙaci guda.ita kuwa Samha jinta cikin jikinsa ya sanya ta ƙara ƙanƙameshi tana jin kamar tayi may faɗe. Se kuma cikin muryan kuka ta furta"Kai ne! Ba kai bane jiya ka rufe ɗakin ka ba nayi ta bugu kaƙi ka buɗe min kuma" wani kalan dafe kansa yay domin shi sammm hakan ya ɗauka ba woni matsala bane. Ƙoƙarin janye ta a jikinsa yake tare da furta "OK shi ne kawai matsalan?" Kanta ta jinjina masa tana sake maƙaleshi. Sadda kansa ƙasa kawai yayi haɗe da lumshe fararen manyan Idonsa haɗi da ɗan taunar gefin lips nashi ba da yawa ba yana jan idanunsa ya lumshe saboda yadda yaji zuciyansa na bada bugu da ƙarfi har yana iya jin yanayin yadda gudun zuciyar san ke ƙaruwa. wani wahalallen numfashi yaja sleep'yn eyes nashi wanda suke koda yaushe lumshe na sake janyewa yana amsan yadda bugun zuciyarsa ke ƙara tsanananta. ♡ A mugun firgice ta farka daga ɗan baccin data samu ya ɗauketa bayan tayi sallarn subhi, wanda kwana tayi bata runtsa ba data rufe idanunta pisc na shi kawai ke mata gizo a tsakar kanta tare da wata macen rungume a jikinsa.wani kalan cukukkuye jikinta wuri guda tayi tare da sakin Shassheƙar kukan da bata san sadda ya zo mata ba har eyes ball ɗin ta na ƙanƙancewa jikinta kuma ya shiga rawa jijiyoyin ƙanta na tashi da ƙyar ta samu cikin wani tear out voice ɗinta dake creating ta furta "I don't love him anymore, My life is nothing for him, ba haka ya kamata kamin ba, ba yadda nai zata na samu ba WHO? why? Why pa'apahh da zaka ma zuciyana irin wannan mummunan horon da kai tsaye ze iya illatar da ita. Sake lafewa tay tana maƙale jikin fuskar gadon tare da rufe idanunta tana jin kamar shi ne ya shigo wai yazo ze rarrasheta. Hakan ya sa cikin cira sauti ta furta "Ahhhhhhhh A ahhhh don't touch me! Don't touch me pls paah ka fita a rayuwana kamar baya bana so bana son duk hakan in ba haka ba wllh zan haukace kowa ma ya huta I hate all off you about....... Sosai zucyarta ke beating very fass,gefe guda kuma ji take kamar ana buga mata wani abu a tsakiyar kanta,dalilin hakan yasa jijiyoyin kanta sukai raɗa² yayinda jikinta ya shiga rawa take ta fara wata irin jijjaga ta fitar hankali. Shi kuwa can ɓangaren Sheikh juraij duk abinda Samha take masa kawai ƙyaleta yayi tunda kamar yaga hakan take buƙata bawai dan yana jin komai dangane da hakan bane, amma fa duk sadda hannunta ze sauƙa a wani sashi na jikinsa ji yake tamkar narkakken dalma take ɗiga masa a wurin. wani kalan jakin numfashi ne so sarƙe shi zuciyarsa na kamar zata faso ƙirjinsa ta fito da gudun bala'i, ga wani mugun kalan zafin dake daɗa mamaye tsakiyar ƙirjinsa, tamkar wacce aka zabureshi haka ya wani kalan janyeta da ƙarfin bala'i daga jikinsa yana miƙewa tsaye tare da fara ja da baya baya yana ficewa a parlour'n kai tsaye ya nufa inda indara Land cruiser car nashi take. Wani irin gudu na ceton numfashi ya shiga gudu na tashin hankali. ALLAH ne kaɗai ya kawo shi gidansu lafiya dan wani irin gudun tashin duniya yayi wanda tunda yake a rayuwarsa ba zai iya r̃iƙe rana me kamar haka dayay kalan wannan gudun ba. Loƙacin daya shiga gidan daidai da sanda Meesherh ke duƙe gaban Railer'n parlour'n ta. "Baby!!!" Sheikh ya ƙi rayi sunan da kaf duniya shi kaɗai ne me ƙiranta da wannan sunan idanunsa zube a kanta, ganin yacce take a duƙe a wurin hakan ya sanya shi nufota. Cike da wani kalan kwarin gwiwan da ita kanta bata san tana dashi bane ya sanya ta miƙewa a mugun hargitse tamkar wanda tayi tozali da dodo, tunkararta yake tana dada ja baya tana ƙokarin ganin ta miƙe ta gudu domin iyaka ganinshi wani shegen zafin zuciya yake haifar mata. Taku ɗaya ana biyu ya sanya hannunsa yana jawota yana tsaidata kan ƙafafunta, Innalillahi! Ya amtabata a cikin zuciyarsa don ganin yacce idanunta suka yi wani kalan ja da kuma tashin da sukai alamun taci kuka sosai harta gode ALLAH. Zuciyar sa ce yaji ta fara rawa tana wani irin yunƙuro masa domin har maƙoshinsa yake jin numfashinsa na kawowa, sake ware idanunsa akanta sosai yayi don yanajin yadda ƙafafunsa ke gaza ɗaukar gangar jikinsa. "What brought you here Baby?" Ƙara ja baya tayi tana matsawa can nesa dashi da hannu take masa alamun ya dakata kada ya motsa inda take tana yi tana girgiza masa kai irin ya dakata ɗin nan, he just trying to get more close to her. a gigice kuma ta furta "Stop Stop Stop it pa'apahh, Don't touch meeee!!!" jikinta duka rawa yake domin tamkar gani take shikenan pa'apahh'n nata ya rigada ya gama cin amanar tane. Ita kanta bata san sanda wasu wahalallun hawaye suka shiga zuba mata ba daga cikin idanunta sai da ta ji sauƙan lallausan tafin hannunsa kan fuskanta yana share mata hawayen dake zubo mata. Kanta ta ɗago a raunace tana kallonsa amma ga mamakinta se taga ya sakar mata woni kyakykyawan murmushin da zata iya rantsewa rabonta dashi tun tana ƴar yarinyantan. Tamkar wota baby'n kuwa haka ya ɗauke ta cilak yana nufar bedroom nata. Kai tsaye a katafaren gadonta ya kwantar da ita komai bai ce mata ba ya juya yana barin bedroom ɗin. Zaune take tsakiyar royal bed nata tun fitar shi ta gaza taɓuka komi sema curewa waje guda da tay banda sauƙe numfashi babu abinda take,sai yalwataccen gashinta wanda ya rufe duka fuskanta. A hankali ta ɗago lulu eyes ɗinta wanda suke always sleepyn ta zubasu kan oval face ɗinsa mai matuƙar kyau da kuma tsari Allah yay masa baiwar kyau da kuma kwarjinin da ba zaka taɓa iya yin 4eyes dashi ba, a pisc ne amma se take kallan tamkar yana a gaban tane dubanta takai kan faffaɗan ƙirjinsa wanda yake yalwace da kwantaccen baƙi siɗik ɗin gashi mai sheƙi,Wasu siraran hawaye ne suka shiga zubo mata tuno da cewan wata ta rigada ta mata shamaki da abinda kaff duniyar tafi ƙauna fiye da komai dake cikin ta idan aka ɗauke iyayenta. Jinta take tamkar wata zautacciya irin wacce take daf da kamuwa da ciwon haukar nan. A matuƙar galaɓaice ta mike tsaye ta shiga cilli da duk wani abu data ci karo da shi, kafin takai zaune yaraf kan tsakiyar gadon ta dafe saitin Heart nata ta shiga furta. _Na yarda da shiiiii! sabo dani dashiiii,kaga ni dakai ɗaya na dogara ba rabuwa da kai.... _ Ta faɗi wasu hawaye masu zafin azaba na zubo mata, sake matse jikinta wuri guda tayi tare ware hannuwanta tana buɗe idanunta gaba ɗaya da dira gwiwowinta kan tsakiyar bed ɗin taci gaba da furta _Ni ba haka ya kamata kai min baaa, ba yanda nai zato na samu ba fiye da haka ɗan uwanaaaa fiye da haka pa'apahh Naaaaa..._ Taunar gefin lips nata tayi da ƙarfin daya sets taji a jikinta amma kuma bata damu ba taci da rera waƙar ta. _Ashe sabo shi haka yake, yasa zuciyata ta tsiƙe gaɓoɓin jikina su sake,silar kaneeee silar kaneeee, kullum da s0n ka zuciyata ta kwana kai kai kaɗai nake ba loƙacina tunaninka ne kawai a gabana. Dan deda s0 a ɗau kiyayya da zafi....._ _fiye da hakaaaaa.kada kai hakaaaa kada kai haka._ Ta furta tane riƙe kanta da take jin kamar ze tarwaste gida biyu. _Duka kakkausan lafuzanka zanji taushinsu, na baka kaina kaima kamin biyan bashi!, kome kake S0 ♥️ ka ambaceshi zan yishi, da haka na fige fiffiken s0nka ba batun tashi_ ta faɗi kamar zata zata tashin sedai tana kasawa hakan tamkar yana a gabanta ta nuna pisc nashi dake gabanta ta furta. _Na baka yardaaaa, na baka yarda na duka_ Tana jin yadda zuciyan ta ke barazana wa rayuwanta ta furta. _Niii! baka haka ya kamata kai min baaaa!, duk da hakan ma ban raina ba ka wuce hakaaaa ɗan uwana Naaaaaa fiye da haka jinin jiki Naaaaa_ se kuma tunani shi tana me ambatar. _Komai na faɗa kana jinaaa! na gane kana fahimtana, kaban madaraaaa kanan madara na ɗan ƙurfa ka bani cikon muradinaaaa....._ Ta furta hakan numfashin ta na tsayawa da aikinsa cakkkk. Tun misalin ƙarfe 4:55 ta gama shiryawa cikin shigarta ta alfmar inda tayi wani irin sahihin yau na gaske gashinta ya sauƙa har gadon bayanta kasancewar vail ɗin da tay Rolling dashi ƙaramine, se hand bag nata dake gefenta. Ɗan sake duban wrist watch ɗin dake hannunta tayi a karo na biyu, Fitowan Maah da kuma papiey'nta ne ya saka ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya, domin ALLAH ² take tayi tabar gidan ma baki ɗaya kai harda garin ma tun da yau ne zataje Lagos inda wasu manyan jarumai da kuma wasu ƙushoshin kasar suka roƙi da taje a fara haska wannan zazzafan Film ɗin nata na TAURARUWA a gidan Cineme mar dake Lagos ɗin, inda da taƙi yarda da tsarin nasu se kuma wannan abin na daren jiya ya sanya ta amincewa ko nauyin dake danƙare a cikin zuciyarta ze ragu. Maah ce ta fara kaiwa zaune saman sofar parlour'n kafin papiey shima, ɗan murmushi tayi cikin tsananin ƙaunar Meesherh ɗin tare da furta "inyeeeeeee ƴen Matan ma'ama ɗin ta har an gama shiryawa kenan? Wato irin an matsu abar nan ko?" Ɗan murmushi itama tayi tare ɗan jingina kanta a jikin Maah ɗin tana furta.

Chapter 12 of 14