Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gama tsaruwa ba ta nufi bedroom nata kai tsaye. Ita kuma Mameey'n tana fita zuciyan ta na raya mata kamar tabi Meesherh ɗin kawai ma ta shaƙeta harse ta mutu. Duguwan rigan jikinta kawai ta sutale tana faɗa cikin Lafiyayyan toilet nata da yake da girma sosai komai kuma a tsare, ƙamshi ne me sanyin daɗi da nutsuwa yake tashi a cikinsa. Ruwa masu ɗumi ta haɗawa kanta tana fara yin wankan a natse ƙamshin shower gel ɗinta me kyau da tsada yana sake tashi, haka harta gama wankan ta kashe shower ɗin tare da miƙa hannu ta janyo towel ta ɗauro a jikinta ta fito cikin Lafiyayyar bathtub ɗin ta nufi gaban mirror'n daya kusan cike rabin bangon toilet din ta tsaya cak ta zubawa kanta fararen idanuwanta da suka sanja sakamakon ruwan da suka shiga cikin su. Hannunta na dama ta sanya ahankali ta dora daidai setin Heart nata tana jin zuciyarta dake bugawa akan a hankali. lumshe fararen kyawawan idanuwanta tayi tana sauƙe numfashi ahankali me dumi. ɗaure da fari ƙal ɗin towel me ɗan girma a jikinta ta fito, Anutsen ta ta zauna kan stool na mirror, blow drying gashin kanta fara yi tana kama lallausan gashin kanta tayi parking nashi cikin woni mini riboms, wasu sprays masu tsada da ƙamshi ta ɗauka ta feffesa ma gashin, sannan cikin sanyin da jikinta yayi ta shafa lotion masu sanya laushi tayi. Ko inda parfumes suke bata kalla ba domin bata a mood me daɗin da zata iya tsayawa zaman sanya wan. Cikin clothes na kayanta ta shige wasu nude riga da wando dogwaye masu ɗan faɗi ta sanya. Wow ko Ni AMMEY LAYLERH saida nace ma sha ALLAH dan there’s no way idan ka kalleta baza kaso ɗauke Idonka akan ta ba, don wani kalam masifar ƙyau tayi cikin kayan tamkar wacce taje hutun honeymoon ta dawo dan yadda farar lafiyayyar fatar ta ke ƙyalli cikin kayan, tabbas Meesherh me ƙyau ce idan nace ƙyau ina nufin ƙarshe maƙura kenan. Kan lafiyayyan gadon ta kwanta tana Sake lafewa a cikin lallausan fari ƙal ɗin duvet cover ɗin ta. Wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauƙe loƙacin da taji abinda yay mata tsai a zuciya na komawa ya kwanta luff cikin tsaƙiyar Heart nata. Moh Ameern ne ya shigo har cikin bedroom ɗin kasancewan se yanzu ne shi yake dawowa daga wurin aiki. Zama yayi dap da ita sosai yana ƙoƙarin yaye duvet ɗin da take ciki. Saurin ƙanƙame duvet ɗin tayi se a yanzu nema take sanin da mutum ya shigo mata ɗakin. Cikin matuƙar ɓacin rai da gajiya da ire-iren abubuwan da Moh ɗin ke mata ta furta. "Shin babu zuciyane a ƙirjinka wai Moh Ameern? kokuwa dai kana tunani da zuciyar takane bada ƙwaƙwalwa ba?, Ji ina ƙarshen haɗuwana dakai last worning na ƙarshe dana maka akan kusanta kanka gareni ne! Na ce ma banaso banso bana so to ka ƙyaleni mana" Meesherh ta faɗi fuskanta ɗauke da mugun ɓacin rai. Kafe ta yay da idanunsa da suke kamanceceniya da nata kasancewar kusan duka family's din kwayar idonsu kala ɗaya ne fara ƙal seda na wani yafi na wani haske. Kallonta yake daga sama har ƙasa ta cikin shegen eye glasess ɗin da manne idonsa dashi, ba tare da yama nuna alamar ya fahimta yaren da take maganar da shiba ko nuna yama ji zafin maganar nata se ma furta. "Hope jikinki yayi sauƙi kenan tunda har kika sama bakin tsiya haka"Ya sake faɗa a hankali yana janye idanunsa akanta. Kin sake yanka shi tayi sai kawai ma woyanta data ɗauka tana manna Bluetooth a kunnenta ta doka ƙiran syster Ashley Agar da tayi babbar aminiyar datai acan ƙasar SPAIN. Woyarta ta shiga yi da Syster Ashley Agar tana ma mantawa da woni halitta kusa da ita. Shigowan Maah ɗauke da plate na farfesun tsokar Mana datai ne ya sanya Moh Ameern tafiya.itama ta sanja kayanta daga wanda tazo dashi zuwa plat riga da zani na less mara nauyi ko kaɗan.zama tayi kusanta tana ɗan rungumo Meesherh ɗin zuwa jikinta, woyar ta nuna mata alamar woya take. Sunan kuma Ashley datay ne ya sanya murmushin Maah sake faɗaɗa domin Ashley da families nata ba mutane bane da zasu iya mancewa dasu cikin sauki don sune suka maye musu gurbin Family'n JEDAANS tattare dasu. Amsan woyan Maah tay tana furta. "Ashley doter se kika fara ƙiran bestie Mee taki kenan kafin Maah ɗin ko?" Har yanzu fuskanta ɗauke da murmushin. "Wllh Maah ba haka bane Besty Mee ita ne ta ƙirani Maah tambayar ta kiji ma" dariya kaɗan Maah ɗin tayi nan dai suka ɗan tattauna dangane da yanayin jikin Meesherh din. Daga nan suka yanke woyan ita da kanta Maah ta tayar da Meesherh ɗin zaune toilet ta kaita ta sake ɗaurayo mata bakinta ta sake dawo da ita tana bata naman a baki. A haka papiey ya shigo ya tarar dasu tare da tsokanar Meesherh ɗin da Shalelen kowa. Murmushi kawai tayi ƙaunar mahaifin nata da duka Family'n tan ma na sake zagayeta da jin alfahari dasu a ko ina take kuwa. ♡ Se bayan sallar Isha'i kowa da kowa ya sake fitowa zuwa babban parlour'n gidan. Ƙamshinta kawai da take fitarwa me yawa ne ya janyo hankalin duk wani dake zaune a parlour'n, ciki kuwa harda juraij sedai shi be juya ba tamkar yadda sauran su suka juya. Zama tay cike da gadara dajin kan daya kasance a cikin jinin jikinta yake, wanda ba koda yaushe ƴan jiji dakan ke tashi ba se ko in woni ya taɓo ta koya ɓata mata rai. To kuwa duk yanayin da take a ciki bata jumrewa se asalin jiji da kan na da gadarar sun motsa tabbas. ƙafarta ta ɗauka ta ɗora ɗaya kan daya tana jan idanunta ta lumshe su luff tana jiran taji me mata magana daga cikin tsageru da marasa haƙurin gidan tsaff ta tsefe su don daidai take jin kanta dasu. Wani shegen murmushin Mugunta anniey a zuciyarta ta saki a cikin ranta tana furta.(shegiya dan ubanki yanzu kuwa zanyi maganin ki, dama wannan ranar nake ta dokon jira). Kallon inda juraij ɗin yake zaune tayi cikin son ta ɓakanta ran Meesherh da uwarta ta furta. "JURAIJ amma yau ya kamata ka leƙa gidansu Matarka *SAMHA* ko?" Ta ƙare da alamar tambaya. Duk parlour'n babu wanda be ɗago ya kalleta ba idan ka ɗauke Maah dama ita kanta Meesherh'n, bawai don maganar bata shige ta ba a ahhh wani irin mugun bala'in bugun zuciya hakan ya haifar mata wanda har kusan sarƙewa numfashinta yayi amma ta yi saurin daidai ta kanta, Shi kuwa juraij yi yay tamkar bema jita ba hakan kuma dayay seyama daddy daɗi, don ba ƙaramin kunya Anniey'n ta bashi ba gaban Prof ɗin duk da kasancewan ƙani yake gare shi amma ai ba daɗi hakan. Duba da cewan a yau ne ƴarsa ta dawo daga zaman jinya har wata ƙasa, dan dama already kowa da kowa dake gidan ya rigada ya san da zancen Auren juraij ɗin, wanda uwarsa ce ta jajirjice har seda maganan tayi ƙarfi. Idan ka ɗauke Meesherh da uwar dan hatta Mohan Sameer yasan da maganar auren Sheikh din. Kuma wani tsantsan rashin kunyan ma ga anniey a loƙacin data tunkari mijinta da maganar ya mummunan ɓata mata rai akan kada ta yarda ta sake tararsa da zance me colour da wannan yayi, seta koma gun papiey'n Meesherh.wanda shi ne ya shige gaba akan komai har aka tsaida maganar watanni biyar masu zuwa gashi yau har anci kusan 3 Months kenan, wanda a lissafi bikin befi saura nan da 2 Months ba inma ze zarta to da ƴan sati kai ne. A natse ya miƙe daga zaman cikin tafiyarsan a natse ta zallar nutsuwar da ALLAH (S .W. T) yamar ya fice daga parlour'n baki ɗaya. Wanda har Annie ta so yimay magana amma wani kallo da Daddy ya mata ya sanya ta gimtse bakinta ba shiri. Don ba haka taso wasan ya tsaya haka nan ba. ~012 Alongside films shot~ *G 9 building* 4:22pm ✯ Yau kwanaki biyu 2 Kenan da haskaka wannan zazzafan film ɗin na *LOƘACI RIGA* wanda sammm jama'ar da suka kalla be woni karɓu sosai a wurinsu ba, domin sammm acress ɗin da aka bama role ma Bata ɗau ko hanyar iyawa ba. a kuma daren jiya ne suka saka Film ɗin wa duniya baki ɗaya wanda jaruman ciki suka kasance Khadijah yobe ce tare muhsin Aliey Yahya se kuma wani jarumi London boy tare da Naveen Wanda duniya ta san shi da can baya, se kuma gashi kwasam a daren jiyan sun sake ganinshi a cikin shirin *LOƘACI RIGA* wanda dama can baya da woni farin jini. Wanda tun a daren jiyan suke amsan ƙorafe ƙorafe daga jama'a da dama kan yadda film ɗin be fita ba kana kwata kwata be kuma fidda wota ma'anar komi ba. Wanda dama tun daga tallan Film ɗin wasu suka fara ƙorafin a sanya musu cikakkiyar jarumarsu wato 𝘿𝙄𝘼𝙈𝙊𝙉 Ꮇ𝞔𝞔𝘚Η𝞔Ʀh 𝕁𝔼ᴰᴬᴬᴺˢ, wanda ata sanadiyyar hakan ne komi daya faru da ita ya farun. Don su masana'antar ana su tunanin suna son dena aiki da Meesherh ɗin ne kawai wacce basu san cewan itace haske a cikin masana'antar tasu ba. Kacaniyace me ƙarfin gaske ta sake ɓallewa wanda ya sanya har wasu daga cikin tsirarin mutanen kewaye Industry ɗin. Dalili hakan ya sake jefa zuciyar muhsin Aliey cikin kunci da kuma hasalashi. Har yaji yana son sake kallar film ɗin tare da bi ɗaya bayan ɗaya yana karanta ƙorafi akan hakan. Zaman meeting na gaggawa Abdulazeez Dakata ya haɗa a take a wurin tare da direktocin da suka tace Film ɗin dama screen pleyar's da suka tace labarin. Wani gauran numfashi Abdulazeez Dakata ya sauƙe yana jingina kansa da jikin doguwar kujerar da yake kai yana duban duka kowa da kowa dake wurin tare da furta. "Ni kaina nayi mamaki da ganin hakan domin shi ne shirin Film na farko da aka taɓa aiwatar da irin wannan cakwakiya, Amma kuma idan mutum ya zauna ya nutsu ya kalla da kyau tabbas Film ɗin ya fidda ma'ana me kyau,amma kuma kafin nan ina son ganin marubucin labarin?" Ya faɗi kansa na sake juyewa da labarin sosai. Tsaye muhsin ya miƙe se wani kunbura dacin magani yake ya furta. "Idan na haɗu dashi ba" Hakan ya sanya kowa juyowa yana kallonsa da alamar tambayar suma. Kansa ya jijjaga alamar hakan se kuma ya furta. "Ni babu wani Writer daya min rubuta nida director Kamaal Jigawa muka rubuta muka kuma tsara labarin mu" se kuma kowa ya shiga sakin ijiyar zuciyan jin abinda muhsin ɗin ya faɗi. Daga nan suka sake tattauna wa akan wasu muhimman abubuwan da suka shafa Film ɗin. Amma duk da haka hazon be dena tashi a sama ta sake zama spreading tamkar gobara a bushashshen ciyayi. Wannan al'amari shi ne dalilin daya sanya har Meesherh da har yanzu take killace cikin gida ta magantu. Wani shahararren matashin tictoker Abis fulani shi ne ya fara ganin new video na Diamond Meesherh Jadeens. Ba tare da ko ya buɗe video'n ba kai tsaye yay Repost na video'n da Rubutu kamar haka..... *TURN ON THE LIGHT* Kan kace meee sega View's na mutane fiye da 1.5m sun kalla. Cikin ƙanƙanin loƙaci gaba ɗaya media ta sake hargitsewa da kwarabniyar dawowan Meesherh. Inda video'n nata kai tsaye befi na wasu ƴan minutes ba. Ga abinda video'n ya ɗauka. Tana tsaye jingine da jikin Railer na upstairs nata, kayan dake sanye a jikinta kuwa ba wasu masu hayaniya bane riga da wando ne kawai marasa nauyi se covering face nata da tay da marsk. _Ɗaukakar jaruma ko sunan datay ba shi ne kaɗai abinda masu kallo ya kamata su fara fahimta tattare da ita jarumar ba_ Gyara tsaiwarnta tayi tare da crossing ƙafafunta kana taci gaba da furta. _Abinda masu kallo ya kamata su fara lura tattare da jarumarsu shi ne yaya Qualities nata yake? Amma kafin nan ma d0n ALLAH ina da wata tambaya?_ Ta sake fatar maganar tana ɗauke mask ɗin dake saman kyakykyawar beautiful Innocent face nata tare da harɗe hannuwanta a ƙirji kana tana me ci gaba da fadin. _Wai don ALLAH maimaita jaruma guda ɗaya a kowanne Film baya gundurar masu kallo ne?_ Se kuma ta sauƙe ijiyan zuciya tare da matso da face nata wurin video'n sosai ta furta. _Na faɗi hakan ne bawai don son ɓatama mabiyana rai ba A ahhhhhh se dan magana ake ta gaskiya da gaskiya, wanda kuma wannan gaskiya take fitowa tun daga ƙarƙashin ƙasan zuciyata. Kamata yay ace sunan jaruma ko kuma ɗaukakarta ba sune abubuwan da ya kamata kuna crossing failure na wasu jaruman ba, shi kansa yawan maimaita Film da jaruman da kuka fiye yawan gani koda yaushe a kowanne Film kan sanya masu kallo suji sun fara gmgundira dashi. Anan abinda nake son faɗi shi ne a duk loƙacin dakika taka wata *NASARA TA RAYUWA* To ƴan bayanki ya kamata jarumar ta fara waige, dalili na anan shi ne se ta ɗan bama sabbin fuskoki ƙofa suma su sanu sosai kafin kuma loƙaci ɗaya tay dirar MIKIYA ta dawo_ _Tamkar dai yadda cikakkun jaruman India keyi irin su PRABHAS sharukhan Rama Charan like haka, idan suka tashi dawowa kuma_ Se kuma ta ɗan buga ƙafa tare da furta _"WOhoho!!!, To anan ne ita kanta wannan jarumar zata gane me ake nufi da hasalin soyayyar Fan's, duk ma mu bar wannan maganar kai tsaye mu tafi kan maganar mu, Ni kaina na kalla Film na *LOƘACI RIGA* kuma tabbas Film ɗin ya fita sedai abu ɗaya ne kawai mutane ke da buƙata shi ne DIAMOND MEESHERH SAMEER JEDAANS. POWER Kenan to IN SHA ALLAH Meesherh Jedaans tayi alƙawarin sake wanko muku Film na LOƘACI RIGA duk da cewan ata sanadiyyar Film ɗin komai daya faru ya riga da ya faru kuma akwai abubbuwan ban mamakin da zato bai zace su ba Nagode ƙwarai. don haka akwai 🔥 Fire🔥🔥🔥🔥🔥🔥 a gaba amma a cikin Film nawa me suna *_☆TAURARUWAꨄ_* _Don haka Aaaaaaahhh gimtse👌😜_ Ta ƙara sa faɗin hakan da kashe Ido ɗaya daga nan kuma vedio'n ya ƙare. Wai WOhoho zokaga yadda ake hasalin tada hazo a yanar gizo gizo, daganan aka saki komai waɗan nan kalamai na Meesherh shi ne ya gigita Media ɗin ma baki ɗaya ba Tiktok kawai ba. Kai har matan aure a gidajensu zancen kawai suke wasu na faɗin abinda jarumar tayi daidai ne wasu na faɗin tsabar iyayi ne kawai don tasan ta gama daukaka ne. Kuma dama kunsan dole a sama hakan tsakanin mutane. Don duk inda mutane ya kai ga iya taku da taka tsantsan ɗin sa be isa yace ze haskaka duniya shi kadai ba, abinda kai wasu sukani sonka to kuwa wasu wannan abinda dakay wasun suka soka su kuma a shi ne zasu ƙiƙa haka taken wannan maganar yake. Don haka wata se mutane suka fara Repost na wasu paya payan video nata na baya masu shige da kalan waɗan nan kalaman. Kamar irin su inda take furta. _Kada ka yarda da kowa ka yarda da kanka kai kaɗai ɗin ka inda ka yarda da kanka to koma waye kada ka yarda dashi illah ka zama naka kai kaɗai.Yare ɗaya ne a duniyar nan wanda kowa yafi fahimtarsa, shi ne kada ka yarda da kowa wannan shi ne_ To fa kunsan dama haka media take da zarar an ɗan samu wani sabon update se a saki wanda ake kanyi a kama sabo, haka dai aka ci gaba da kaftawa wasu na goyan bayan maganganun Meesherh wasu kuma na kushewa. A loƙacin da wasu daga cikin jaruman fina finan suka kalla wasu da yawa ta birgesu tamkar yadda wasu da yawa bata birgesu ba ,don su gani kawai suke danta fito daga babban gida ne kuma dama duk wata fira da za'a i da ita idan aka tambaye ta menene dalilin daya sanya ta shigo kannywood amsar ɗaya ce shine *RA'AYI* Bawai don ta ɗauka hakan a matsayin sana'ar ta bane kawai Ra'ayin da ta ce to kuwa ra'ayin ne, don sun san in suna take nema to kuwa iyaka ƙarfin dukiyarsu ya gama zage ko ina bare kuma JEDAANS FAMILY. Wanda kowa babban fata da kuma burin sa shi ne JEDAANS FAMILY. *BY AMMEY LAYLARH ✍️* *༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻* _𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _ ♡ 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ 𝙋a𝙜𝙚 19&20 https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* Waɗanda suke buƙatar samun litattafan *AMEEY LAYLERH* za ku iya shiga shafin ta na Telegram don samun su kai tsaye daga wurin ta. Ga link nan ga masu buƙatar shiga 👉https://t.me/ammeylaylerh_novel ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ ꨄ_The third season of *Winter Wonderland # JEDAANS FAMILY* has kicked off, offering a unique winter experience that combines entertainment and fun activities for the entire family_ ꨄ Gaba ɗaya ɗakin tsit yake daga sautin karatun Sheikh juraij thabit ɗin daya sanya bakajin komai a room ɗin sai na sanyin AC kawai kakeji. Sai wani irin ƙamshin Air freshsheners da turarukaan wuta masu daɗi, Ɗakine me girman gaske dake ɗauke da setin royel furnitures masu tsananin kyawun gaske White colour sai ɗan adon milk da aka musu. Daga ta nan bakin bed ɗin wani haɗaɗɗen Islamabab carpet ne me tsananin laushi da aka shimfiɗa wanda yakai har tsaƙiyar room ɗin, daga gefen window's kuma wata keɓantacciyar Luxury sofa ce Ajiye da ƙaramin fridge. daga ta gefen mirror kuma wani babban table ne da aka jera littattafan Addini shimili guda gasunan, daga ta gefen gabas akayi wani zagayyen wuri na musamman wanda ke shimefiɗe da wata kalan lallausan praymed me taushin tsiya, sai wasu zagayayyun EGYPTANI'AN decoration's irin masu haskaka room ɗin na, sammm ɗakin baya da woni tarkace haka yake simple gwanin birgewa wanda mutum zaiyi normal real life nashi cike da bada cikakkar nutsuwa. Agogon ɗakin ne ya buga ƙarfe 10:31 daidai da Mirza handle na ƙofar bathroom ɗin da Sheikh juraij thabit Jedaans da yayi, Anutse ya fara ɗora santaleliyar ƙafarsa me cike da gargasan gashi baƙi siɗik akan ƙaramin carpet ɗin dake shimfiɗe bakin ƙofar bathroom ɗin. kafin ya Ida fitowa gaba ɗayansa a nutse ya fara taka sawayensa cike da nutsuwa take ɗakin ya gauraye da ƙamshin shower jurl ɗin da yayi wanka dashi. Ahankali ya nufi gaban dressing mirror yana sanye da rigan wanka navy blue wanda ya tsaya iyaka singallinsa sai wani milk saman wuyansa yana goge ruwan jikinsa dake yarara saman fatarsa da kai tsaye yake nuna cewa shi ɗin tsayayyen namiji ne me jini a jika sai faman walainiya fatar nan take tamkar woni beby sabuwan haihuwa. Wannan fuskar da cikar kamala mai nuna barazana wa maƙiyinsa a tinƙe ɗifff tun a daren jiya wanda dole ne ma mutum ya yarda yaci wannan suna na jarumi kuma ingarman namiji me ji dantashen samartaka wanda hasalin jin daɗin rayuwa ya gama ginashi, .wanda kai tsaye a cikin bathrobe ɗin se ya ɓoye asalin n manyantan da ya fara yi kaɗan. wanda kuma na tabbatar da zallar hutu da kuma jin daɗine suke sake ɓoye manyan tan nashi. Cikin wani irin tafiyan ɗaukan hankali ya fara tafiya da zaratan sawayensa, Komai yake yi cikin tacin zuciya yake tsafff ya gama shirya kansa cikin wasu sky blue cashmere se hular daya mirza saman kanshi inda ta haska farar lafayayyar cutie face nashi ta ƙara fidda ainihin taswirar kyawu da kuma zatinsa. A natse ya isa gaban Iphone nashi inda sautin karatun ke fita take karatun kuma ya tsaya sakamakon shigowan ƙira ɗan lumshe Ido yayi ya kuma sake buɗewa ya kalli agogon dake manne jikin bango, red lips nashi na motsawa kadan alaman tasbihi yake yana ɗaukan phone in dama yasan ƙiran bazai wuce Anniey'n shi bace, ba tare daya ɗauka wayan ba ya nufi hanyan fita, kamar yadda yana yinsa na rashin fara'a yake haka yafito daga cikin ɗakin hannunsa riƙe da key nashi na car. A nutsensa ciki wannan yanayin na kamewa da yan muskilanci da ya motsa yau yake saƙƙowa daga saman stairs ɗin,Directly Sassanta ya fara nufa tamkar yacce yayi zata kuwa tana zaune akan wata royal sofa ruwan zuma, tayi crossing ƙafafunta tana watching wani series film. Zana yayi a kusanta yanayin fuskan shi na sake sanjawa da ganin abinda take kallan. "Kafito kenan?" ta faɗi tana kallonsa itama tata fuskar a gimtse. Gaida ya fara yi kafin nan ya bata amsa da cewan wurin aiki ya nufa. Kai tsaye umarnin zuwa wurin Samha ta bashi tare da tura may wata leda kan ya bama Samha ɗin da hannuwansa. Seda ya ɗan dafe kansa zuciyan sa na kin amsan abinda woni sashe na daga cikin ta keson bijiro mishi dashi wato jin ba daɗi abinda Anniey'n kemai. Saurin istgfar ya fara a ranshi. Ba tare daya tsaya zaman diner tamkar yacce take may tayin ba yay fitansa. Inda kai tsaye mahaukacin street house parking loot na adana motocin gidan ya nufa Mai karatu idan nace zan tsaya zayyano muku adadin kuɗi masu tarin yawan da kawai aka narka wajen zuba ado a departmen house kawai na adana motocin ma wani sabon ɓatama kai loƙacinne sabo ma kuwa. Get uku ne a gidan kuma kowanne get akwai wuraren Parking car's, sedai gaba ɗaya wannan shi ne ƙarshe a komai wajen haɗuwa. Daga nan ya fice a gidan yana ɗaukan hanyan gidan gwaggo Haleemah don cika umarnin anniey. _ꨄ *Meesherh* Zaune take kan wata arniyar farar cough ta a sanye da top irin wannan wanda daga ƙasansu ake ɗinkewa sai crazy 3½, se kanta da yasha gyara sosai na musamman inda ke tubke cikin wata trap band. iPhone nata ne a hannunta tana duba irin yadda mutane keta sake kallar video'nta, da kuma irin ƙalubalantan ta da mutane ke sake yi. Ƙara lafewa cikin cough ɗin tay tare da ɗora wani ɗan ƙaramin rubutu kamar haka. 0o 0o 0o 0o 0o ꨄ _ꨄThank you for sharing your Videos with the world and enriching our lives with your beautiful FAN'S💃💐. May this special day bring you as much happiness as you bring to others. Wishing you endless love, success and fulfillment in all that you do. ❤️ All my love 😍_ tana ɗora rubutun tun kamin ta fita ta fara ganin kalan yacce mutane suka fara

Chapter 10 of 14