afka cikin qaunarka, ba zan iya rayuwa ba idan na
rasaka” Tana faxar maganganun tana zubar da hawaye na takaici da
tsananin baqin ciki.
Jin wannan kalaman nata su ne suka saka zaiyan ya nufi
wajen cikin gaggawa yana zuwa ya miqa hannu ya kamo hannun salhim
ya riqe wata jijiyar hannunsa, zuwa wani xan lokaci ya sauke ajiyar
zuciya ganin haka sai Gimbiya Zasmin tace masa.
“Kai taimake ni zaiyan kar salhim ya halaka, ka ceci rayuwar
mutum biyu domin tabbas idan ya halaka ni ma sai na halaka” Zasmin
ya buxe wata ‘yar qaramar jaka dake gefen damtsensa ya xauko wani
xan guntun garin magani, ya xebo shi ya na mai amnaton sunan Allah
sannan ya zuba a wajen da macijiyar ta yiwa salhim rauni.
Bai daxe da zubawa ba sai salhim ya soma motsawa, bayan
kamar wasu ‘yan mintina kuma sai ya miqe yana mai kwarara wani
baqin amai, duk sai daya amayar da dafin macijiyar sannan ya xago kai
yana duban Gimbiya Zasmin da Zaiyan.
“Ku bani ruwa na sha” Ya faxa cikin galabaita, zaiyan ya
xauko wani jalo na shi dake cike da ruwa ya bashi yasha, ya dube shi
yace masa.
73
DAN BAIWA
“Na gode da taimakona da ka yi wajen ceton rayuwat” Zaiyan
ya yi murmushi.
“Ba ni za ka yiwa godiya ba, Gimbiya Zasmin za ka yiwa
domin daga ni har kai ita ta ceci rayuwar mu” Salhim ya juya yana
kallonta ga mamakinsa sai yaga ta sunkuyar da kanta cike da jin kunya,
sannan lokaci xaya kuma hawayen farin ciki suna fita daga cikin
idanunta.
“Mene ne ya saka ki zubar hawaye? Ai gani ban halaka ba”
Gimbiya Zasmin ta xan xago idanu ta kalle shi sannan tace masa.
“Na godewa abin bautar zaiyan daya kuvutar min da kai”
Koda jin haka sai zaiyan ya dubeta cike da mamaki.
‘Me yasa kika yi godiya da abin bautata alhalin baku yi imani
da shi ba” Gimbiya Zasmin tayi murmushi.
“Ai kuwa yanzu ne na samu yaqini akansa, domin a lokacin
da naga wannan macijiyar ta kama salhim tana shirin halaka sai na ji ina
mai neman taimakon abin bautarka, kuma lokacin dana xaga takobi zan
sari macijiyar taimakon abin bautarka na nema don haka ka yi sani ni
kam na yi imani da shi, na kuma aminta lallai shi ne abin bauta na
gaskiya” Su duka suka yi shiru suna kallon Zaiyan can salhim shima ya
ce.
“Nima yanzu na yi yaqini da abinda Gimbiya Zasmin ta faxa,
kuma na bada gaskiya da abin bautarka ka faxa mana yadda za mu
shiga cikin wannan addinin naka” Koda zaiyan ya ji haka sai farin ciki
ya lulluve shi, nan take ya faxa musu yadda za su zama musulmai suka
nanata suka zama ma’abota bin addinin musulunci.
Nan take zaiyan ya rungume salhim cikin tsananin farin ciki
yana faxin.
“Daga yanzu kun zama ‘yan uwana na musulunci...” bai
qarasa magana ba sakamakon wata iska da suka ji tana busawa, bayan
wani xan lokaci sai suka ga wani jibgegen aljani ya sauka a gabansu
yana sauka sai Gimbiya Lazma ta bayyana cikin shiga ta bokanci, tana
sauka sai ta yi nuni gasu zaiyan da salhim da Gimbiya zasmin tana
ambaton wasu kalamai na sihiri nan take suka ji kamar an saka sarqa an
xaxxaure su duk kuzarin jikinsu ya qare, suka yanke jiki suka faxi.
74
DAN BAIWA
Gimbiya Lazma ta yi murmushi a hankali cikin taqama ta
qarasa wajen da su zaiyan suke kwance ta sunkuya a gabansu tace musu.
“Ai baku isa ku tserewa mahaifina boka marmasi ba, lallai
yanzu nan zan miqa ku hannun sarki mazwan ya cika qudurinsa akan
ku”.
Tana gama faxin haka ta miqe nan take zaiyan ya yunqura ya
miqe,yana kallonta sannan cikin qwarin gwiwa yace mata “Haba
kyakkyawa me ya ribaci zuciyarki kika bi ra’ayin mahaifinki kika zama
bokanya tun da quruciyarki?” Koda jin sautin murya zaiyan sai
Gimbiya Lazma ta qura masa ido tana kallonsa nan take gabanta ya
yanke ya faxi.
“Zaiyan?” Ta faxa cike da mamaki, shima ya qura mata idanu
suna kallon-kallo nan take ya tuno wajen daya tava ganin Gimbiya
Lazma, sun tava haxuwa a kasuwar bayi ta qasar sham ta shiga tare da
kuyanginta suna sayen bayi sai kawai wani zaki da sarki yake kiwo ya
kwace daga kejinsa ya shigo kasuwa yana banke mutane yana kashewa,
nan fa aka shiga guje-guje nan take kuyangin Gimbiya Lazma suka
tsere suka barta a lokacin wannan zakin ya ritsarta ita kuma saboda
tsananin firgita ta kasa aiwatar da komai.
Lokacin daya yo kanta da zumar halakata sai zaiyan ya dako
tsalle ya rungumi wannan zakin suka soma kokawa, sun jima suna
fafatawa kafin ya samu ya halaka shi, tun daga wannan lokacin
Gimbiya Lazma ta faxa cikin tafkin qaunar zaiyan amman abinda ya yi
mata shamaki da shi data gano shi ma’abocin addinin musulunci ne.
Ta xauka gano hakan zai cire mata qaunarsa, domin duk
duniya babu wanda taqi ji sama da ma’aboncin musulunci amma kuma
sai ya zamana kullum zaiyan yana cikin zuciyarta, ta kasa samun ikon
cire son shi daga cikin zuciyarta. Tun daga lokacin take nemansa
amman ta kasa samun sa domin iya bincikenta na tsafi ya qi nuna mata
wajen da yake.
Sai yanzu data gano su jarumi xan baiwa, shima bata gano shi
ba, kawai taga wani ma’abocin musulunci yana taimaka musu shi yasa
tsawon lokaci ita da babanta suka kasa gano su.
”Gimbiya Lazmin?” Shima ya faxa cikin tsananin mamaki.
75
DAN BAIWA
“Daman kunsa juna?” Salhim da Gimbiya Zasmin suka haxa
baki wajen tambayar su.
Nan take cikin sanyin jiki ta yi nuni garesu nan take suka ji
wannan xaurin da aka yiwa jijiyoyin jikinsu ya yayye, suka zubawa
juna idanu suna kallon-kallon ‘Daman kai ne kake taimakon su
Salhim?” Ya gyaxa kai.
“Kwarai ma kuwa, na kuma san mahaifinki Boka Marmasi da
sarki mazwan suna qoqarin ganin an kamo salhim da Gimbiya zasmin
an kai masa domin ya halaka su” Ta dube shi cikin tsananin mamaki
tace masa.
“Ya aka yi kasan haka?” Ya yi murmushi.
“Wanda sarki jamhas ya aika su salhim da Gimbiya zasmin
wajensu a qasar sin ki sani ba kowa bane face mahaifina, kamar yadda
kema mahaifinki ya kasance boka haka nima mahaifina ya kasance
mashahurin boka amman da shiriya ta zo masa sai ya amshi addinin
musulunci ya kuma daina yin sha’anin bokanci, a lokacin da aka aiko su
salhim shi ne ya kirawo ni ya bani umarnin na kawo musu xauki domin
mahaifinki da sarki mazwan suna qoqarin halaka su, wannan dalilin ne
yasa na zo nake taimakon su”. Cike da mamaki Gimbiya Lazmin ta
dube su, har ta buxa baki zata kuma yin wata maganar sai suka ji wata
qara haxi da rugugin aradu, nan take kuma wata walqiya ta bayyana
kafin su zaiyan su yi wani yinquri sai suka ji an suresu anyi sama dasu.
Nan take suka vace vat daga wajen.
**
Sarki mazwan ya qarasa shiga har cikin tsakiyar fadar
takobinsa a sama suka yi kallon-kallon tsakaninsa da sarki jamhas cikin
tsananin fushi ya miqe daga kan karagarsa.
Har ya buxe baki zai yi magana sai suka ji wata qara gami da
walqiya da rugugi bayan wucewar wasu ‘yan sakani sai boka marmasi
ya bayyana, ya watso da su salhim da Gimbiya zasmin da zaiyan da
Gimbiya Lazma a gaban sarki jamhas ya bushe da dariya.
“Ai basu isa su gujewa halakar sarki mazwan ba, na kawo su
ne domin sarki mazwan ya halaka su akan idonka kafin kaima ya sare
kan ka” Yana gama faxin haka sai ya juya gaban sarki mazwan dake
tsaye takobi zare a hannunsa ya ce masa.
76
DAN BAIWA
“Ya shugabana ga abokan gabarka daka daxe kana neman su,
na kawo maka su ka yi duk yadda ka yi niya da su” Koda ganin su
salhim da Gimbiya Zasmin sai daxi ya cikawa sarki mazwan rai amman
ganin ‘yar boka marmasi sai ya xaure masa kai yace masa.
“Ya naga Gimbiya Lazma?” Boka marmasi ya sunkuya yace
masa.
“Cin amana ta tayi, na gargaxeta akan afkawa cikin soyayyar
ma’abota musulunci amman taqi don haka gwara itama ta halaka” Koda
jin haka sai sarki mazwan ya jinjina wa boka marmasi nan take kuma ya
baiwa dakarunsa damar su afkawa abokan gabarsa.
Nan fa suma sauran tsirarun dakarun arnan daji da su sarkin
yaqi marhat suka yo xauki akan dakarun qasar Hindu nan fa aka yi
wata qazamar haxuwa aka soma fafatawa, nan take kasuwar yaqi ta
soma ci, shima sarki mazwan ya zaburo kan su salhim da Gimbiya
zasmin da zumar sare kawunansu.
Yana qarasawa ya kai musu wani wawan sara, amman kafin
ya qarasa sai zaiyan ya saka takobinsa ya kare saran, nan take ya juyo
kan zaiyan da nufin kawo qarshen numfashinsa, nan fa kallo ya koma
sama, suka soma wani baqin gumurzu banda qarar takubansu babu
abinda kake ji.
Haka suma sarkin yaqi marhat da sarkin yaqin qasar arnan
daji suka kasance, duk wajen da suka tunkara sai dai kaga kawuna suna
tashi sama,nan fa jini ya riqa gudana a qasan fadar.
Faxa ya rincave babu abinda kake ji sai qarar haxuwar takuba,
nan fa aka riqa wannan baqin gumurzun, yadda sarki marwan ya yi
tsamani sai yaga wanki hula yana neman kai shi dare domin dakarun
arnan daji sun tirje sun kuma jajirce.
Haka shima da suka ci gaba da fafatawa da zaiyan ya xauka
cewar zai samu nasara akan shi cikin ‘yan lokuta amman sai haqarshi
taqi cima ruwa domin kuwa ya same shi ne sadauki ne shima mai
tsananin jarumtaka.
Koda ganin yadda waje ya rincave da yaqi sai boka marmasi
ya yi gaggawar matsawa wajen da ‘yarsa take ya kamo hannunta cikin
tsananin fushi yace mata.
77
DAN BAIWA
“Maza ki nemi hanyar guduwa tun kafin sarki mazwan ya
kashe saurayin naki ya dawo kanki” Ta bugawa mahaifinta harara tace
masa.
“Har kana tunanin wannan tsohon azzalumin zai samu nasara
akan zaiyan, to idan baka san wane zaiyan ba ka tashi daga magagin
baccin daka ke yi domin kuwa shi xan boka sambul ne mashahurin
bokan nan na birnin sin wanda ya tumbatsa a duniyar bokaye” Ai kuwa
boka marmasi yana jin haka sai ya taqarqare ya qwala wata qara domin
kuma tun tsawon zamani abinda tsafinsa yake nuna masa kenan cewar
ba ma’abota musulunci ne za su samu nasara akan sarki mazwan ba,
wanda zai samu nasara akan shi yaro ne kuma da tsafi zai kashe sarki
mazwan, amman yanzu daya ji zaiyan xan boka sambul ne sai ya samu
yaqinin lallai shi ne wanda zai samu nasara akan sarki mazwan kuma ya
mulki qasar Hindu.
Ai kuwa kafin boka marmasi ya gama rufe bakinsa sai ya
hangi hannun sarki mazwan dake riqe da takobi an yanke shi ya yi sama,
shi kuma sarki mazwan ya qwala wata qara cikin razana, yana riqe da
gundulmin hannun da zaiyan ya yanke yana faman tsartuwar jini.
Zaiyan ya xaga takobinsa zai sare masa kai nan fa ya zube
akan gwiyoyinsa yana neman afuwar zaiyan akan ya yi masa rai, zai ba
shi duk abinda yake buqata, ganin haka yasa duk Dakarun qasar Hindu
suka zubar da makamansu ganin sarki mazwan a cikin halin qasqanci.
Zaiyan ya juya ya dubi salhim da Gimbiya Zasmin a hankali
yace masa.
“Ya kai yaro xan baiwa salhim ka yi sani cewar yau ga ranar
daka daxe kana jira don haka sai ka zo ka cika burinka” Ai koda xan
baiwa ya ji haka sai ya zaburo cikin gaggawa takobi riqe a hannunsa ya
qaraso har gaban sarki mazwan.
“Kar ka kashe ni” Salhim ya girgiza kai.
“Ashe akwai ranar da zaka ji tsoron mutuwa? Har ka manta
kisan da ka yiwa mahaifiyata ka manta yaron daka kashe ka baiwa
kadojinka namansa? Ai ba a san gwarzon namiji da kururuwa ba idan
mutuwa ta zo masa” Yana gama rufe bakinsa ya kafta masa sara a dokin
wuya take kan shi ya tashi sama gangar jikin ta faxi qasa a gefe.
78
DAN BAIWA
Koda boka marmasi yaga haka sai ya zube gaban zaiyan yana
tuba, yana faxin.
“Ka yi min rai, na aminta zan bar bokanci na komo addininka
na musulunci” Koda jin haka sai ya xago idanunsa ya kalli Gimbiya
Lazma koda suka haxa ido da ita sai yaga ta sunkuyar da kanta qasa,
hakan ne yasa ya taka a hankali ya matsa zuwa wajen da take a cikin
kwantar da murya yace mata.
“Ba zan zarta da hukunci komai akan mahaifinki ba, amman
ke kina da ikon yin duk abinda kika ga ya dace akansa” Yana gama
faxin haka sai ya nufi wajen da karagar sarki jamhas take yana zuwa
suna haxa ido sai aka ga sarki jamhas ya sauka daga kan karagarsa ya
kamo hannun zaiyan ya xora shi akan karagar mulkin hakan shi ya
baiwa kowa mamaki.
Bayan zaiyan ya zauna akan karaga sannan ya soma magana
cikin xaga sauti.
“Ya ku jama’ar qasar Hindu da qasar arnan daji ku yi sani
cewar ni ne Yarima zaiyan xan sarkin qasar sin, kuma xa ga
mashahurin boka sambul don haka kamar yadda labari ya riski sarkin
ku mahaifina ya zama ma’aboncin addinin musulunci, to ya aiko ni
domin na zo wajen amininsa sarki jamhas na yi kira gare shi zuwa ga
addinin gaskiya wato addinin musulunci, don haka ina kira gare ku
domin shiga cikin wannan addinin na tsira” Bayan ya kammala
maganar sai aka ga sarki jamhas ya miqe yaje gabansa ya tsuguna
sannan ya ce masa.
“Tabbas tunda aminina yabar addinin gargajiya ya shiga
wannan addinin to wannan hanyace mai kai mu tudun mun tsira don
haka maza ka faxa min yadda zan kasance daga cikin wannan addinin”
Nan take zaiyan ya faxa musa.
Nan take jama’ar qasar dana qasar Hindu suka amshi Kalmar
shahada suka zama ma’abota musulunci.
Daga nan aka shiga sha’anin rayuwa cikin kwanciyar hankali,
jama’ar qasar Hindu dana qasar arnar daji suka zama kamar ‘yan uwan
juna. Bayan komai ya nutsa aka xunguma aka koma can qasar Hindu
inda za a sha shagalin bikin zaiyan da Gimbiya lazma da kuma sarkin
yaqi marhat da Gimbiya Hamrita.
79
DAN BAIWA
Yanzu kam sarki yaqi marhat ya daina fargaba domin yana da
yaqinin addinin musulunci ya bashi ‘yanci auren mata huxu bama biyu
ba.
Haka rayuwa ta ci gaba da gudana cikin ‘yanci da haxa zuri’a
tsakanin qasahen biyu.
MASHA ALLAHU
QARSHE
80
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels