shi bata su yake ba abinda ya kawo shi kawai
yake yi.
Bayan ya gaji da nema har zuwa yamma rana ta tafi
faxuwa a lokacin ya gaji tiqis da nema ya fita da ran samun wannan
27
DAN BAIWA
baqar baiwa ya zo fita daga cikin kasuwar bayin ya ci karo da wani
ayari na fatake sun shigo cikin kasuwar ga alama zuwansu kenan a
cikin bayin daya gani suna cikin sarka hard a wata kyakkyawar
baqar fata baiwa tana cikin sarqa hannu da qafa kanzu ya zuba mata
idanu yana kallonta babu shakka ita ya zo nema.
Cikin sauri ya sha gaban shugaban ayarin shugaban su
yana ganinsa ya yi sauri zubewa a gabansa yana gaisuwa yace masa
cikin nutsuwa “Ya shugabana me kake nema a wajena?” Kanzu yace
mata.
“Wacan baqar baiwa na gani nake so a wajenka zan
saya” Cikin sauri ya juya yana kallon baqar baiwar da kuma firgici
yace masa.
“Ka yi min rai ya shugabana wanan baiwar da kake
ganinta takanas na sayota saboda Jamru, shi ya bani umarnin siyo
masa baqar baiwa akan dinare dubu, ban samo wannan baqar baiwar
ba sai dana dangana zuwa ga qasar Habasha” Jin an ambaci Habasha
ya saka ya samu yaqinin lallai ita ce ake magana akanta. Amman jin
an ambaci Jamru shi ya bada saqon a siyo masa ita sai hankalinsa ya
tashi ya yi imani wani sihiri zai aikata da wannan baqar baiwa don
haka ba zai yi sake wajen mallakarta ba koda kuwa hakan yana nuni
cewar sai ya nuna izza ta mulki da isa wannan dalilin yasa ya kalli
shugaban fataken cikin izza yace masa.
“To ni kuma ita na gani ina son siye kuma ko kana so ko
baka so sai ka siyar min da ita, idan kuma ba haka ba lallai zan
amshe ta da qarfin tsiya” Ya saurara yana duban shugaban fataken.
“Ka yi min rai ya shugabana idan na je babu wannan
macen jamru zai kashe ni’ Ya yi murmushin qarfin hali. “Nima idan
baka ba ni ita ba kashe ka zan yi” Jin haka take ya soma karkarwa.
‘Ka zavi xaya da wanda zai kasheka anjima wanda kafin lokacin ka
yi tunanin mafita da wanda zai kashe ka yanzu take” Nan take ya
faxi gaban kanzu yana neman yafiya ya kuma bada umarnin a
kwance macen a ba shi.
Ya qare mata kallo mace mai kyawu cikar zati da anuri
yana fita daga cikin fuskarta, wannan macen tasha bamban da duk
28
DAN BAIWA
matan da ake kawo su a matsayin bayi. Nan take ya xauko darhami
mai yawa ya bashi, ganin yawan su sai daya saka shi susucewa nan
take ya zube yana godiya shi kuma bai bi ta kanshi ba ya yi gaba
abinsa suka nufi gidan sarauta. Koda suka soma tafiya sai shugaban
fataken ya yi murmushi ya soma tunanin qarya da zai yiwa jamru.
Lokacin da kanzu suka qarasa gida sai ya shiga da
wannan baqar baiwa ta varauniyar hanya babu wanda ya gansu har
suka qarasa varinsa, wani qaton gida ne wanda aka qawata shi da
kayan na’ikan kayan alatu ya kwance mta sarqa da take wuyanta.
“Ga wani xa ki can acan za ki zauna, za ki samu duk
abinda kike da buqata na rayuwa”.
“Me yasa ka siyo ni ka kawo ni nan?” Bai faxa mata
komai ba ya juya ya fita abinsa yana mai faxin “Yawan tambaya ba
na ki bane, sanu a hankali za ki fahimci komai”.
Al’amarin shugaban fatake kuma yan zuwa wajen jamru
ya zube a gabansa yana rawar jiki da fargaba cikin fushi jamru ya
daka masa tsawa “Ina baqar fatar dana baka umarnin ka siyo min?”
Cikin rawar jiki yace masa.
“Ka yi min rai ya shugabana na siyo wannan macen
amman a hanya abokin gabarka kanzu ya tare mu ya amshe ta…” Ai
baima bari ya qarasa magana ba ya yi saurin surar maqoshinsa ya
cira shi sama nan take ya soma wutsil-wutsil a sama kamar an xaga
xan tsako nan take idanunsa suka zazzaro.
“Qarya shi tasha qarya”.
“Ka yi min rai ya shugabana ba ni da ikon hana shi” Nan
take ya sake shi tim! Ya faxo qasa.
“Lallai kanzu ya xauko rikicin da duk duniya babu
wanda ya isa kawo qarshensa” koda shugaban fataken ya samu da
qyar ya tsira sai ya koma bayan Katanga ya rakave.
Da tsakar dare jamru ya miqe ya haxa duk kayan
tsatsubarsa ya yi wani sihiri take duk wasu jama’ar gidan sarauta
suka shiga barci. Wannan barcin daya saka su ya yanke burin yau zai
29
DAN BAIWA
yanko kan sarki laqamu kafin ya koma kan xansa ya karve wannan
baqar fatar.
Zai kuma kashe shi a bainar jama’a, bayan ya kammala
duk abinda ya kamata ya nufi gidan sarauta cikin taqama kai tsaye
ya shiga cikin turakar sarki laqama ya same shi yana barci bisa
tafarkin sihirin daya saka shi, ya saka takobi ya yanke masa kai nan
take jini ya soma gudana a qasa yana kwaranya.
Ya xauko kan sarki laqamu ya xaga sama yana
murmushin mugunta kafin ya juya cikin sauri ya nufi sashen gidan
kanzu. A lokacin da jamru ya shiga sashen kanzu babu motsin komai
yana tafiya takobinsa tana xigar jini, ya qarasa xakin kamzu ya same
shi shima yana barcin sihirin yace masa.
“Idan na so halakar da kai da yanzu na yanke kanka
kamar yanda na yanke na mahaifinka,amman sai na tara jama’a na
maka bayanin yadda na kashe mahaifinka sannan na kashe ka” Nan
take ya xauko wani ruwa a cikin gora ya zuba masa nan take ya
farka suka yi kallon-kallo shi da jamru sannan ya mayar da kallonsa
zuwa ga hannunsa dake xauke da kan mahaifinsa.
Ku min afuwa mu gamu a littafi na 2 domin jin ci gaban
labarin.
JARUMI XAN BAIWA 2
Idanun kanzu suka rufe ya rasa me yake masa daxi a duniya ya ji duk
wani tsoro da fargaba ya fita daga cikin ransa, cikin qarfin zuciya ya
taso a fusace da zumar surar Jamru su soma fafatawa amma ya makara
saboda jamru ya gano manufarsa. Kafin ya qasara gareshi tuni ya yi
zamiya kai tsaye Kanzu ya wuce ya gwaru da ganuwar ginin xakin ya
yi wata faxuwa ya dawo daya ya yi zaman ‘yan bori.
Jamru ya saka qafa ya daki gefen fuskarsa da takalmin da ke qafarsa
take bakinsa ya fashe jinni ya soma kwaranya qarfin duka da ya yi masa
sai daya sa ya yi tsalle gefe guda kamar an xauki karmamin itace an yi
jifa da shi ya tafi can gefe guda ya faxi qasa. A hankali jamru ya taka
30
DAN BAIWA
ya qarasa zuwa gareshi ya tsaya akansa yana kallonsa yana yi masa
dariyar mugunta ya dube shi da duban wulaqanci yace masa.
“Ka xauka cewar zan manta bashing aba da kuka ci nawa? Don haka
kayi sani cewar wannan kan da kake gani a hannuna na mahaifinka ne
sarki laqamu wanda mutuwa ta xauke shi kuma ni xinnan da kake gani
da hannuna na yanka shi na kawo maka kan saboda ya zama abokin
mutuwarka kafin zuwa washe gari” Ya bushe da dariya yana kallonsa
ya ci gaba da Magana.
“Kayi sani cewar babu gudu babu ja da baya tabbas washe gari zan
kasha ka da mutuwa mafi muni da wani xan adam bai tava irinta ba a
cikin qasarnan” Yana kammala faxar haka ya juya cikin isa da taqama
ya xauko wani qaramin qaho daga cikin qugunsa ya soma busawa a
hankali. Ai kuwa faruwar hakan ke da wuya sai gashi jama’ar qasar da
suka shiga wannan bacci na sihiri suna farkawa xaya bayan xaya. Kowa
ya farka sai ya cika da mamakin dalilin daya sashi yin bacci a lokacin
da bai shirya ba. Jamru yana gama busa qahon sai ya yi wajen gidan
kan sarki laqamu a hannunsa ai kuwa duk bafaden daya ci karo da shi
yana ganin kan sarki laqamu a hannun jamru sai ya zube qasa yana
mubaya’a ga jamru.
Kai tsaye fada ya wuce yana zuwa ya samu waje akan kujera sarki
laqamu ya zauna kafin wani lokaci fada ta cika maqil da jama’a ko
wanne ya yi shiru yana jiran yaji abinda jamru zaice.
Bayan ya qare musu kallo na tsawon wani lokaci sannan ya saukar da
ajiyar zuciya cikin izza ta mulki ya soma Magana. “Yauce rana ta farko
da burina ya cika na zama sarkin qasar shamara bayan na halaka da
ruhin tsohon sarki laqamu kuma kuyi sani cewar washe gari babu
shakka zan yiwa babban abokin gabata kanzu kisan gilla” Ya dubi
jama’ar qasar gabaki xaya.
“Da wannan kalamin nawa nake cewa daku kowa ya halarci bakin fada
gobe da safe don ganin kisan da zan yiwa kanzu” Yana kammala faxar
haka ya miqe kai tsaye ya nufi hanyar shiga cikin gidan saeki laqamu
vangaren da matan sarki suke da bayani da kuyangi. Yana qarasawa ya
saka sarkin gida ya fito masa da su dukansu suka tsaya carko-carko ya
soma bi yana kallonsu xaya bayan xaya yana neman baqar kuyanga da
kanzu ya amsa.
31
DAN BAIWA
Har ya kammala dubansa bai ga mai kama da it aba yaja tsaki cikin
fushi ya xauko madubin tsafi ya soma dubawa yaga ai tana vangaren
kanzu daya baro. Ya yi murmushi ya kalli kuyangi da matan sarki
laqamu yace musu.
“Ku daga yau na maisheku matana kamar yadda tsohon sarki ya zauna
daku a matsayin mata haka kuma kuyangi” Ya yi shiru yana kallonsu ya
xan soma takawa a hankali har zuwa wajen jakadiya ya tsaya a wajen
yana kallonta sai ya saka hannu ya fizgota kusa da shi yace mata.
“Ke munafukace kece jakadiyar kakana don haka babu shakka kin tsufa
da yawa mutuwa ce ta kamata da shekarunki” Ta zube gabanshi ta soma
neman tuba amma ina ta makara don kafin ta kuma yin Magana ya saka
kaifin takobi ya sare mata kai kan ya faxi qasa yana cizon rairayi.
“Wannann izina gare ku sauran matan gidan sai kuma naga wacce zata
kuma kawo min cikas akan abinda ya shafi sha’anin mulkina duk wacce
tayi gardama hakace zata kasance da ita” Nan take jikinsu yayi sanyi
jikinsu ya soma karkarwa don ganin baqin zallunci daya taya same su.
Ya kaxa kai ya juya wannan karon cikin sauri da zafin nama da zumar
isa vangaren kanzu daya baro yasan wannan dukan dayayi wa kanzu na
jarumtaka babu abinda zai sashi moruwa daga yanzu har zuwa washe
gari. Yana qarasawa ya samu kanzu yana kwance shame-shame kamar
yadda ya fita ya barshi a wajen ya sunkuya ya cakumo shi ya soma
jijjiga shi a hankali ya buxe ido da qyar yana kallonshi.
“Ina baqar baiwar nan daka amsa a hannun shugaban fatake?” Kanzu
yayi murmushi a hankali yace masa “Ai ko kasheni zaka yi sai dai ka
kashe ni amma ba zaka tava sanin wajen da take ba” Jamru ya yi
murmushin mugunta.
“Kamar wani jarumin kirki har kake dagewa cewar ba zaka faxi wajen
da take ba, ai ragwaye masu zuciyar mata basu da wani tasiri a rayuwa
haka kuma babu abinda za su iya da hakan yafi maka kwanciyar hankali
ka faxan wajen da take kafin mutuwa ta riskeka” Kanzu ya yi murmushi.
“Ai wanda mutuwa take gaf da shi babu tsoron da zata ba shi amma
kuma ko banza nasan cewar idan ka kasheni zaka riqa tunawa da ni a
matsayin abokin gabarka kuma haka zaka riqa tunawa da ni a duk
lokacin daka tuna har bayan mutuwata baka samu damar mallakar baqar
baiwa ba” Maganar da Kanzu ya faxa mas aba qaramin ci masa rai ta yi
32
DAN BAIWA
ba hakan yasa cikin fushi ya zare takobi da zumar sare maswa kai ayita
ta qare. Amma abin mamaki koda ya kai sara da zumar sare masa kai
sai yaji an tare saran daya kai masa jamru ya juya cikin fushi don ganin
wanne ya masa wannan aika-aikan ai kuwa sai suka haxa idonu da
baqar baiwar nan da yake nema.
“Ai koda ka tsawaita bincike baka isa ka gano inda nake ba, ubangijin
musulunci ya bani kariya ya tsareni daga duk wani tsafi naka kuma ka
yi sani cewar tunda ka zama azzalumi babu shakka ba z aka yi tasiri
wajen aiwatar da zallunci ba yanzu nan kaima zan kawo qarshen
burinka na son zama sarki” Cikin tsananin vacin rai yace mata.
“Ke shashashar banza kada ki xauka kowa soko ne kamarki ki kalli
jarumi kamata kuma sarki mai girman daraja kina jin za ki iya xaukar
wani mataki akaina to ki sani ‘yan maza ma sunyi sun kasa bare ke”
Baqar baiwa ta gyara riqon takobinta tace masa.
“Ai kaine ragon maza da ka maida zallunci ado tabbas yanzu za ka yi
dana sanin yin haka” Ai kuwa sai takaiwa jamru sara da takobin dake
hannunta ya yi saurin karewa amma duk da haka sai data yi nasa yi
masa bile a fuska.
Wannan abun data yi masa shi ya kuma harzuqa shi ya qona masa rai
cikin tsananin fushi ya mayar mata da martanin sara data kawo masa,
itama ta kare suka soma musayar kai sara da suka kafin wani lokaci duk
wani abu da yake cikin xakin sun tarwatsa shi.
Saboda duk wajen da suka kai sara basu samu juna ba sai dai kaga sun
tashi wani abu sama nan danan suka hargitsa komai suka fito wajen
gidan suna musayar sara da suka cikin gwaninta da nuna jariya ta yaqi.
Kana ganin yadda wannan baqar baiwa take kare saran da jamru yake
kawo mata kasan cewar ta gwanance wajen iya yaqi kuma jarumace ta
gaske.
Furuwar haka ya baiwa jamru mamaki kuma ya samu tabbacin idan bai
zage damtse ba babu shakka wankin hula zai kaisa dare, don haka ya
soma sauya salo-salo na yaqi da zumar samun nasara akanta amma duk
salon daya sauya si ya samu tasanshi.
Nan fa suka ci gaba da farauta ran junansu a haka gari ya waye jama’a
suka taru suna kallon wannan fafatawar da suke yi kowa yana faxin
33
DAN BAIWA
albarkacin bakinsa akan wannan faxan da ake yi wanda aka rasa wanda
zai raba shi hakan nan kuma an rasa wanda zai samu nasara a cikinsu.
Zuwa takewar rana sai jamru ya soma gajiya kuma duk wani salo na
faxansa ya qare sai maimaici yake na wanda yayi na farko amma ita
kuma kamar yanzu take kuma samun qwarin gwiwa da kuma wata
hazaqa ta na shiga jikinta. Ai kuwa nan da nan jamru ya soma sarewa
qarfinsa ya qare ya zama baya iya kai sara sai dai karewa ai kuwa yana
ganin haka sai ya yarda takobin hannunsa suka tsaya carko-carko kamar
zakaru yana kallon baqar baiwa cikin maida numfashi yace mata.
“Babu shakka kin samu nasara wannan karon akaina wanda a tarihin
babu wani jarumi daya tava tsayawa a gabana yayi tsawon sa’a guda ba
tare dana halakar da shi ba amma ke gashi mun xauki tsawon sa’o’i
kusan goma muna fafatawa amma babu wanda ya yi nasara saboda haka
kiyi sani cewar idan hagu ta qiya sai a koma dama yanzu zan halakar
dake ta hanyar tsafi” Ai kuwa yana faxar haka sai baqar baiwa ta yi
murmushi sannan itama tace masa.
“Ai kuwa ka zo wajen da zan nuna maka cewar tsafi harka qarya ce da
kuma son zuciya da son vatar da jama’a babu shakka yau Addinin
gaskiya zai dane na qarya”. Jamru yana jin haka sai ya soma karanto
xalasiman tsafi ya yi nunu da baqar baiwa da zumar iska ta xauketa ta
karkaryata. Nan take wata baqar guguwa ta tashi me qarfi ta nufi wajen
baqar baiwa take duk abinda taci karo da shi kafin ta qarasa sai dai kaga
ta sureshi tayi sama da shi tana rugurguza shi, amma ita tana tsaye qam
bata motsa ko nan da can ba, a cikin zuciyarta ta soma neman taimakon
Ubangijin musulunci tana neman xauki gareshi.
Ai kuwa guguwar tana zuwa wajenta sai ta tsaya waje xaya tana juyi
zuwa wani lokaci kuma sai ta lafa ta koma kamar ba guguwa ba. Ganin
haka yasa yaa kuma wani sihirin ya aiko mata da wuta tana turuqo tana
cinye duk abinda taci karo shi ta tunkari baqar baiwa amma tana zuwa
kusa da ita sai ta zama hayaqi ta tashi sama.
“Ke da me kike taqama wane irin sihiri kike yi?” Ta yi murmushi.
“Ai bana yin tsafi kawai na dogara da izinin Allah, ubangijin musulunci
wanda ya aiko da manzon Allah da gaskiya kuma yake kira da izinin
Allah ga mutane da su zama suna bautawa Allah shi kaxai. A cikin
addinin aka sanar damu cewar tsafi shirka ne kuma duk wanda ya yi
34
DAN BAIWA
Imani da Allah to babu shakka Allah zai kare shi kamar yadda ka gani
da idonka yanzu ka aikata wannan sihirin bai yi tasiri akaina ba. Yanzu
ina kira gareka daka zama mai tsoron Allah ka yi Imani da shi ka sani
cewar wannan aikin da kake aikatawa zallunci ne da kuma shirka idan
hark a tuba ga Allah zai amshi tubanka” Jamru ya yi murmushi.
“Kina cikin ma’abota musulunci kema?” Ta gyaxa masa kai.
“Tabbas hake kuma ina kira gareka daka zama kaima ma’abocinsa” Ya
yi murmushi.
“Ai kuma an faxa mun duk ranar daa gamu da ma’abocin musulunci to
rana ita ce rana mutuwa ta babu shakka ko wane lokaci idan na duba
madubin tsafina sai naga namiji ne ya kashe ni amma kuma yanzu ya
zan ga savanin haka mace ce zata halakar da mashahurin jarumi kamata.
Bana jin zanyi wannan faxuwar baqar tasa tabbas ba zai tava faruwa ba,
har abada ba zan amshi amshi wannan Addinin da kike min tayinsa ba
kamar yadda na sani cewar ba zan samu nasara akan ki ba don haka zan
xauki matakin da boka zalzabu ya xauka a lokacin da ma’abota addinin
musulunci suka ci qasar shi da yaqi ya kasha kansa saboda baqin ciki
nima ki sani yanzu nan zan kashe kaina, amma ki sani cewar da zarar na
halaka kaina sirrin tsafina zai koma jikin wata birinya da nake kiwonta
a wannan biranya zata hana duk wani mai shirin zuwa qasar sin koyon
tsafi kuma zata adabi duk wasu fatake da aljanu da dabbobi da suka
wanzu suna rayuwa a waje ba zata halaka ba har tsawon zamani” Ai
kuwa koda gama wannan maganar sai ya suri wuqar dake qasa ya
sokata a qirjinsa take ya faxi qasa yana shure-shuren mutuwa.
Baqar baiwa ta qarasa kanshi ta tsaya tana kallonsa yanda yake fama da
magagin mutuwa ta yi murmushi tace masa.
“Maza sun faxi… amma ka yi sani cewar da izinin Allah yaro xan
baiwa shi ne zai halakar da ita” Ta juya zata soma tafiya a cikin
magagin mutuwa taji yace mata.
“Wane kuma yaro xan baiwa?” Ta juyo tana murmushi tace masa.
“Wani yaro ne da za a haife shi kuma Allah zai tsare shi ya kuma ba shi
baiwa ta daban, duk tsafinka baka tava dubo wannan abun ba” Ta kaxa
kai tayi gaba nan jamru ya yi mushe a wajen ugulaye suka sauka akan
gawarsa suna tsatsagar namansa.
35
DAN BAIWA
Kanzu ya fito yana yiwa baqar baiwa jinjina akan wannan aikin da ta yi
kuma ya yi Imani da cewar duk wanda ya aikata alheri babu shakka zai
samu sakayya me kyau. Nan ya amshi addinin musulunci kuma ya bada
umarni ga jama’arsa da kowa ya amshi Addinin musulunci nan take
jama’a suka yi ta shiga Addinin gaskiya. Daga ranar qasar shamara ta
zama qasar da take zama cikin jin daxi da adalci da kwanciyar hankali
haka ya yi Imani da cewar adalci shi ne yake zaunar da qasa lafiya.
Ya dubeta cikin nutsuwa yace mata.
“Wannan labarin ya tavani sosai kuma ya haska mun gabana akan
cewar yiwa jama’ar qasa adalci shi ne yake sakawa sarki ya samu
xaukaka, amma kuma kina ganin maganar da baqar baiwa ta faxa na
cewar xan baiwa zai kashe birinya zai tabbata kuwa?” Macen sihiri ta yi
murmushi.
“Ai babu makawa shi kaxai zai iya halakar da ita zai kuma samu nasara
akan sauran abokan gabansa wannan yaron duk yadda kake tunaninsa
ya wuce nan kuma zaka sha mamaki lokacin da zai zo qasarka yana
neman taimakonka” Ta juya tana kallon sham.
“Nayi Imani da sham yana da iko daya taimaki wannan yaron sama da
yadda yake taimakona” Sham ya yi murmushi.
“Ai kuwa yanda kika bani labarinsa abin tausayi ne kuma abin a
taimaka masa a bashi qwarin gwiwa ya samu damar halaka azzalumin
sarki mazwan” Ta miqe tana qare musu kallo su duka sannan tace musu.
“Yanzu aiki xaya zan maka shi ne idan na samar da dawakai guda biyu
wanda yaro xan baiwa zai yi amfani da su wajen guduwa a lokacin da
sarki mazwan zai so halakar da shi to zan kuma naxe nisan tafiya ta
hanyar amfani da alqaluman sihiri wanda hakan zai bada gudumaewa
wajen su sawa su gujewa mayaqan sarki mazwan. Babu shakka wannan
zai taimaka masa matuqa wajen tsera da shi daga halaka amma idan bah
aka ba sai sun samu nasara akansa” Sarki hamhas ya saukar da
numfashi.
“Amma kuma ta yaya kike ganin za mu tserar daa shi bayan mun zama
bama ga maciji da sarki mazwa? Ta yi murmushi.
“Kada ka damu da wannan abun yanzu zan sana’anta sirrin tsafi na
aikawa da boka marmasi a cikin ilimin tsafi zai gane cewar ya zama
dole idan suna son samun xaukaka to sai sun qula sulhu da ku sun
36
DAN BAIWA
zauna lafiya da ku sun daina gaba da ku, ba zai tava ganin cewar sihirin
qarya bane don haka idan yaga haka zai samu sarki mazwan ya faxa
masa shi kuma yana bin duk maganar da boka marmasi ya je masa da
ita.
Idan haka ta kasance za su aiko da wasiqa neman sulhu ku kuma sai ku
amince da haka amma babu shakka wannan gabar zata dawo bayan
tsawon zamani yanda zai zama kun zama abokan gaba sama da yadda
kuka kasance a yanzu zaai zama kuna neman farauta rayukan juna sama
da wannan lokacin” Koda jin haka sai sarki jamhas ya yi murmushi.
“Ai kuwa idan haka ta kasance zanji daxi na kuma yi farin ciki sosai
saboda babu makawa nasan lokacin jama’ata sun samu ci gaba sama da
na yanzu haka kuma dakaruna sun qara yawa ga faxin qasa da zamu
qara haka kuma jama’a ta sun qaru idan hakae lokacin ba zamu yi
shakkar tunkara sarki mazwan ba” Macen sihiri ta koma ta zauna.
“Haka maganarka take ni yanzu zan zauna anan qasar taku zuwa wasu
‘yan kwanaki har sai sham ya warke sannan mu ci gaba da tafiya zuwa
wajen da muka nufa” Ta tashi ta koma kusa da sham ta zauna.
Sarki jamhas shi kuma ya tashi ya fita daga fada. Duk wannan abun ya
faru ne kafin a haifi Yaro xan baiwa.
**
Lokacin da yaro salhim ya cika shekara shida a lokacin tsufa ya rake
almajira harsu ya zamana cewar ko fita bata iya yi don haka dole tasa ta
koma zama da kuma kwana a cikin wata tsohuwar buka dake gefen
kasuwa wanda sau tari idan ruwan sama ya zo sharkaf suke jiqewa
saboda rufin bukar duk ya lalace kuma basu da kuxin da za su iya biya
a gyara musu. A kullum sai salhim ya je ya yi bara sannan yake samo
abinda za su sayo abinci da za su ci su kuma sha shi da ‘yar tsohuwa.
Ana cikin haka ciwon ajali ya kama ‘yar tsohuwa Harsum shekara tana
cika tace ga garin ku a wannan ranar salhim ya yi matsanancin kuka da
bai tava irinsa ba. A kuma bisa al’adar idan mamaci bashi da ‘yan uwa
ko kuma wasu da za su masa gata to baza’a yi bikin qona shi ba sai dai
kawai a xauki gawarsa akaita teku a jefar.
Itama gawar sai anga zata yi wari, ta damu mutane da suke wajen bisa
wannan dalilin yasa lokacin da tsohuwa ta mutu aka rasa waxanda za su
37
DAN BAIWA
kaita har sia datai yi kwanan keso, kafin safiya ta soma kumbura tana
wari nan fa salhim ya fashe da kuka ya dunga bin mutanen kasuwa yana
roqonsu akan su taimaka masa akai gawar.
A qarshe dai a wulaqance aka xaurawa gawar igiya aka jata a qasa har
zuwa bakin teku aka jefata cikin ruwa, tun daga wannan lokacin baqin
cikin abinda ya faru yasa Salhim ya xaukar wa kansa alqawarin idan ya
yi tsawon rai sai ya kawar da zallunci gami da jahilci da mutanen birnin
Hindu suke cikinsa.
Haka ya taso a cikin rayuwarsa cikin qunci da takura na rashin gata da
samun kulawa a cikin rayuwa a haka ya kai shekara goma. Rana ya yini
yana bara bai samu komai ba kuma yana jin yunwa ta isheshi kamar zai
mutu adaidai wannan lokacin ya zo giftawa ta qofar gidan sarki
muzwan yaga ana rabawa bayi gurasa don haka ya kutsa kai ya saci
xaya domin ya samu ya ceci rayuwarsa.
Wannan shi ne asalin dalilin daya saka wanan badakaren ya biyoshi da
gudu har suka shiga cikin kasuwa domin samun damar halaka shi bisa
umarnin sarki.
Lokacin da yarinya ‘yar indiyan daji ta kama hannun salhim suka ruga
da gudu daga cikin kasuwa har zuwa cikin dajin dakarun sarki mazwan
suna biye da su a guje amma sun kasa cin masu a haka suka vace musu
da gani. Nan fa hankalin dakaru ya tashi ainun, don sun san halin sarki
muzwan idan har basu kai masa sassan jikin wannan yaron ya ciyar da
kadojinsa ba to akansu zai huce fushinsa.
Nan fa suka rarrabu a cikin dajin kuma kuma suka rarrabu sashe-sashe
da zumar su samu damar kama yaron salhim amma ko xoriyarsa basu
jib a al’amarin daya kuma dugunzuma musu hankali suka tsaya suna
shawarwarin abinda ya kamata su yi wanda za su ceci kansu daga
hannun sarki mazwan.
Nan kuwa wata dabara ta faxo musu suka dawo cikin kasuwa wajen da
wata mahaukaciya take kwana tare da ‘ya ‘yanta guda uku suna zuwa
suka tarar da ‘ya ‘yanta suna kwance a cikin rufar kasuwa suna ta sharar
baccinsu kawai sai suka lallava suka sace babba wanda girmansa zai yi
daidai da salhim suka toshe masa baki yana wutsi-wutsin da qafaffunsa
suka kai shi can bayan gari suka sare