bashi da ikon busa mata rai ta
tashi tayi motsi, a zaman daya yi a gefen kushewarta matarsa,
yana cikin halwa ne na son gano yadda zai busawa wannan
sunduqin rai amman har shekara ukun bai gano ba.
Abinda ya gano a cikin halwarsa duk abinda yake so
ba zai samu ba, mafita xaya ce idan yana son ta motsa, sai dai
13
DAN BAIWA
ya samo wata budurwa macen aljanu ya sakata a cikin jikin
robar mai sifar matarsa sai ta riqa motsawa.
Wannan abin daya gani shi yasa ya zauna yin halwa
tsafi har sai daya nemo budurwa Aljana mafi kyawu a cikin
yankin aljanu ya kamota ya sata a cikin butar tsafi ya xauki
butar tsafin ya saka a jikin wannan gangar jikin roba. Da
wannan ya tashi gangar jikin ya zama tana iya motsi tana iya
tafiya tana iya magana.
Ganin wannan nasarar daya samu ya saka ya xauki
sirrin tsafi dubu xari tara ya saka a cikin jikinta, ya kuma saka
mata qarfin sadaukai dubu ya saka mata hikima da balaga ta
magana, wannan ita ce irinta ta farko da wani boka a duniya ya
qirqira kuma mafi hatsari a duniya.
Duk lokacin daya so ita kaxai yake turawa wani gari
taje ta yaqi duk girman daular daya ga dama, haka kuma idan
ta saka dakaru a gaba bata gajiya tana iya yin shekara guda
tana yaqi bata gajiya ba, tunda ita bata ci bata sha bata da wani
aiki sai yin biyayya ga boka, idan aka koma fanin tsafi idan
tana faxar kalaman tsafi sai ka yi tsamanin duk duniya babu
kamarta, hatta a wannan zamanin banda ni babu wanda ya kaita
sanin sirrin bokanci, wannan fafatawar da kuka yi don na
baiwa qasar nan kariya na tsafi shi yasa bata yaqe ku kuma tayi
galaba akan ku ba, amman ba don haka babu shakka da kaga
azaba irin wacce baka tava ganin irinta ba” Ya yi shiru yana
kallonsa.
Sarki mazwan ya yi shiru yana kallonsa Boka
marmasi ya saukar da ajiyar zuciya ya qara cewa da shi.
“Yanzu ya kake ganin za a yi yadda za mu qara
mallakar takobinmu data karva kuma ka sanar da ni cewar kar
na sake takai birnin Nur saboda sarki Lambo zai iya mallakar
14
DAN BAIWA
wannan takobin tawa” Boka marmasi ya bushe da wata dariya
sannan ya dafa kafaxar sarki mazwan yace masa.
“Naga hankalinka ya tashi ka kwantar da hankalinka
bisa wannan buqatar da ka zo min da ita, don haka zan aika
saqo gareta bisa tafarkin tsafi kuma zan dawo maka da takobin
taka domin na faranta maka rai” jin wannan kalamin ba
qaramin faranta ransa ya yi ban an take fuskarsa ta washe zuwa
ga murmushi.
Daga nan suka yi sallama Boka marmasi ya vace
daga cikin gidan sarautar.
**
Lokacin da su macen sirri suka nausa suka shiga
cikin daji tana kan ingaraman dokin data hau ganin tafiyar bata
yi musu sauri sai ta tsayar da dokin ta xauki sham ta sava akan
kafaxa ta ruga da gudu, kamar wacce take gudu akan iska kafin
wani lokaci ta yi nisa da birnin Hindu.
Wannan karon kana ganin fuskarta kasan ranta a
matuqar vace yake, saboda babu anuri ko farin ciki hakan ya
faru ne saboda ganin irin raunin da sarki mazwan ya yi wa
sham. Tasan sham sadauki ne wanda baya tsoro ko fargaba,
amman sarki mazwan ya shamace shi ya kafta masa sara
wanda tun sanda aka yi masa bai kuma motsawa ba.
Hakan yana nuni cewar akwai sirrin tsafi a tattare da
takobin, don haka ta qara azama ta shiga cikin dajin a lokacin
ta qarasa wani waje mai yawan rairayi da kuma ruwa mai kyau
yana gudana a wata qorama gefe guda kuma ga wasu ‘ya ‘yan
itatuwa jere reres gwanin ban sha’awa.
Tana qarasawa ta samu waje ta ajiye shi akan rairayi
mai sanyi ta zauna tana kallonsa, har zuwa lokacin banda idanu
babu abinda yake juyawa nan take tausayinsa ya kamata ta
15
DAN BAIWA
miqe ta komo kansa ta tsaya tana kallonsa da idanunta masu
haske fari qal.
Zuwa wani lokaci ta soma karanto wasu xalasimai
na tsafi kala-kala take abubuwa suka bayyana garai-garai
gareta cikin gaggawa ta buxe idanunta daga rufewar data yi
takai dubanta zuwa ga wajen da yake ga mamakinta babu shi
sama ko qasa.
Ta juya ya kuma juyawa ya duba ko zata ga wata
alama da zata nuna mata sawun wani abu amma sam babu
wata alama, wane wannan ya aikata wannan zunibin gareta?
Tabbas ko wane sai ta azabtar da shi da irin azaba irin ta yaqi,
nan take ta taqarqare ta kumarma ihu wanda sai daya saka
duwatsun da suke cikin dajin amsawa. Tsuntsaye da suke bakin
ruwan suka bazama suka tashi sama, igiyar ruwa ta soma
ambaliya kafin kace kwabo tuni launin wajen ya sauya saboda
wannan ihun da macen sirri ta kurma.
Idanunta suka kaxa suka yi ja, saboda tsananin
fusata da tayi kamanita suka sauya daga kyakkyawar mace
zuwa wata kalar ta daban. Lokaci guda ta soma nazari akan
abinda ya shafi babi na tsafinta kafin wani lokaci duk wani abu
daya faru ya bayana a gareta. A gaba da wajen da yake nesa
kaxan akwai wasu arnan daji da suka kasance suna bauta ga
wani dodon gunki da suka sassaqa shi daga itace. Wannan abin
bautar na su ya kasance suna yi masa hadaya duk qarshen wata
da jinin baqon matafiyi wanda hanya ta biyo das hi, hakan ya
saka suka kafa wajen wannan qorama a matsayin tarko da suke
kama baqi.
Hakan ya saka suka sace sham suka nufi birin nasu
na arnan daji domin yau kwana uku kenan ba su samu wanda
za su yi hadaya da shi ba, wannan birnin ya kasance shi ne
kusa da birnin Hindu kuma shekara da shekaru babu basa ga
16
DAN BAIWA
maciji da masarautar birnin Hindu, wannan gabar ya saka
jama’ar birnin Hindu basa iya shiga cikin dajin yin farauta ko
kuma yin itace domin gudun gamuwa da tarkon arnan daji.
Sarki mazwan yana sha’awar fita farauta amman
saboda baqar gabar dake tsakaninsu hakan ya saka ya haqura,
ya aika qashen da suke kusa da su aka sayo masa duk wani
na’ika na dabobin daji ya zuba a cikin wani faffaxan waje daya
kilace ya kuma qaramin kogi a gidansa yana kiwon kadoji.
Wannan birnin na arnan daji ya kasance yana da
kyau da kuma tsari anyi gidajen daga duwatsu suna mulki a
qarqashin sarkin su Jamhas wanda ya kasance gawurtacen
jarumi mai juriya da kuma bajinta a fagen fama.
Matsala xaya take damun sarki jamhas shi ne rashin
samun haihuwa, ya yi maganin ya kuma bi bokaye da ‘yan
tsubu ya yi tsatsuba amman haihuwar bata samu ba hakan ya
saka ya haqura ya saka sha’anin sarautarsa a gaba.
Haka suka ci gaba bauta ga wannan gunki suna yi
masa hadaya da jinin duk wani baqo da suka kamo,kuma
hasalin yiwa gunki hadaya ya samo asali ne daga gaqar gabar
da suke yi da jama’ar Birnin Hindu wanda gunki ne yake basu
sa’a a duk lokacin da suka tashi yin artabu da dakarun birnin
Hindu.
Ana kawo sham gaban sarki jamhas ya tashi yana
dubansa cikin nutsuwa ya xaga kai yana kallon dakarunsa yace
musu.
‘Ya naganshi a cikin wannan halin na galabaita
kuma ga ciwo a jikinsa? Anya kuwa abin bautar mu zai amshi
wannan a matsayin hadayar da za mu yi masa?” Ya ci gaba da
kallon sham sannan ya tashi yana zagaya shi.
“Wane irin ciwo ne ya samu wannan har ya kasance
a kwance kamar matacce?” colom sauri ya shiga wani xakin da
17
DAN BAIWA
yake kusa da fadar wanda anan kayan tsatsubarsa yake. Ya
xauko madubin sihiri ya soma bincike akansa nan yaga artabun
da ya yi da jama’ar qasar Hindu da yanda suka shigo cikin
dajin tare da macen sirri. Amman abinda ya bashi mamaki ya
kuma xaure masa kai yadda madubinsa ya kasa nuna masa
macen sirrin.
Ya yi iya yinsa domin ganin ya samu bayani akan
macen sirri da kuma nemo daga wane jinsi ta fito ganin haka
ya saka hankalin sarki jamhas ya tashi, cikin zafin nama ya
ajiye madubin tsafin ya xauko kayan tsatsuba ya buxe
kwatarniyar tsafi ya baza wuri ya soma duba bisa tafarkin tsafi.
A lokacin da yake wannan binciken game da wacce
ce macen sirri ita kuma a lokacin ta shigo cikin birnin arnan
daji cikin fushi da fusatar zuciya.
Macen sirrin ta kai tsaye ta shiga cikin fada ai kuwa
dakarun fada suna ganinta suka yo kanta cikin halin fushi suna
daka mata tsawa.
“Ke yarinya wane ya baki izinin shigowa cikin garin
nan babu shakka halaka ce ta kawo ki” Macen sirri ta xaga kai
tana dubansa kafin tayi wani murmushi mai xauke da fushi
tana kallon yadda suke kusanto kawunan su zuwa ga halaka
tabbas yaro baisan wuta ba sai ya takata.
“Kana kallona kasan ban yi kama da yarinya ba,
domin yarinta tana bayan mahaifiyarta ahir! Xinka da kuma
gangancin kuma faxar wannan Kalmar, maza ku miqo min
abokin tafiyata cikin ruwan sanyi idan ba haka ba fushina ya
sauka akan ku” Nan wani ma gigiwa ya yo kanta cikin fusata
musamman domin ganin mace ce bata da wani jarumtaka.
Rashin sani yafi dare duhu. Yana zuwa kusa da ita
yakai hannu da zumar zungure mata hanci amman ga
18
DAN BAIWA
mamakinsa sai ya ji hannunsa ya soma laqwashewa yana
komawa zuwa cikin hancinsa, nan yaga lamarin bana wasa
bane, ya soma qoqarin hana faruwar hakan amman ya kasa
take ya soma kwaranya ihu take jini ya soma fita daga cikin
hancinsa ta sake ke shi ya faxi yana burgima a qasa.
Ganin wannan abin mamakin daya faru ya saka
sauran dakarun suka sha jinin jikinsu, tabbas wanan macen
tana taqama da sirrin tsafi idan kuma haka ne gidan shi ta zo,
haka ya saka suka ja da baya wasu dakaru da aka horesu da
tsafi suka dawo gaba nan suka soma tsatsuba sai kaga badakare
ya zama zaki yayo kanta da gudu, kafin ya qaraso wajenta sai
dai kaga ta kalle shi da ido sai kaga wata iska ta sure shi tayi
watsi da shi can gefe guda.
Sai kaga wasu a cikinsu sun zama wuta kafin su zo
wajen sai wani ruwa ya baiyana ya haxiye su. Ai ko da ganin
sirrinta yafi na su sai suka yi xauki kanta da takobi a zare,
masu kibiya suka soma yi mata ruwan kibiya amman abin
mamaki duk kibiyar data je jikinta sai kaga ta narke ta zama
ruwa ta zube a qasa.
Hakan bai hana su xauki kanta,ho abin kallo ya
samu nan suka gauraya ta zare takobin sarki samzan data amsa
nan fa kasuwar yaqi ta soma ci, mutuwa ta soma shawagi a
tsakaninsu kawunan sadaukai na birnin arnan daji ya soma
zuba a qasa kamar ana sassabe.
Babu abinda zaka gani sai gilmawar makamin
macen sirri yana ratsa tsakanin mazaje yana fasa qirjinsu
zuciya tana faxowa qasa jini yana zuba shaaa! Kamar gulbin
ruwa. Kalar jan jinin dakarun birnin Arnan daji su kansu suka
san cewar yau wata shaixaniya ta sauka a qasar su yau kam sun
tsokano tsuliyar dodo.
19
DAN BAIWA
Suna cikin wannan xauki ba daxi suka ji an
kwatsama musu wata tsawa cikin sauri suka ja da baya suka
tsaya carko-carko kamar zakaru suna kallon junansu a lokacin
sarki jamhas ya fito daga cikin xakin tsatsubar shi cikin fushi
ya dubi ginin fadar yaga yadda ya rine da jinin jama’arsa ya
dubi qasa yaga yanda kawuna suka wadata a zube babu jikuna
take ya tsorata da shu’umanci macen sirri babu shakka yanzu
ya gamsu ita ce.
Ya yi saurin dakawa jama’arsa tsawa da cewar.
‘Maza ku zubar da makamanku kuma ku zube gabanta domin
nemn afuwa akan zunubin da kuka aikata mata” Ai kuwa da jin
wannan kalaman na sarki sai mamaki ya kama su suka zube a
gaban macen sirri suna neman tuba.
Sarki jamhas ya qarasa gabanta ya kalleta cikin
girmamawa yace mata.
‘Muna neman afuwa bisa laifin da muka aikata cikin
rashin sani. Tun sanda naga abokin tafiyarki na shiga cikin
xakin bokancina domin gano wane shi, a bincikena ne komai
na ki ya bayyana a gare ni don haka muna neman afuwa a
gareki bisa wannan lamarin da muka aikata miki” Jin
kalaminsa ya saka macen sirri ta maida makaminta ba tare data
ce komai ba ta nufi wajen da sham yake tana zuwa ta sunkuya
ta xauke shi cak kamar ta xauki karmami ta nufi wajen da
karagar sarki jamhas take ta kwantar da shi ta tsaya tana
kallonsa har lokacin numfashinsa yana fita.
Sarki jamhas ya yo wajenta cikin sauri ya zo kanta
yana kallon sham zuwa wani lokaci ya nisa yace mata.
“Takobin sarki mazwan ce tana xauke da wani dafi,
kuma wannan dafin yana halaka mutum. Badon sham yana da
nisan kwana ba da tuni ya halaka. Don haka mu jama’ar daji za
mu karya wanna sirrin da yake jikin takobin” Take ya buxa
20
DAN BAIWA
gefen duga-diginsa ya xauko wata ‘yar buta ya xauko wani
guntun xan itace ya karyo shi ya saka a baki ya taunashi ya
soma marmasa masa a wajen daya ji ciwon.
Ai kuwa mintina goma da yin haka sai ciwon ya
soma wata irin kumfa wajen yana tafasa kamar an saka abu a
cikin wuta, kafin wani lokaci wajen ya gama zavalvala a
hankali ya soma kamewa yana komawa kamar babu abinda ya
faru a wajen a lokacin sham ya buxe idonsa suka haxa ido da
macen sirri suka yi murmushi.
Ya miqe yana duban jama’ar Arnan daji sannan ya
maida hankalinsa zuwa ga sarki jamhas. ‘Ina godiya bisa
kuvutar da ni da ka yi, kuma ina yi maka jajen rashin jama’ar
ka da ka yi wanda macen sirri ta yi maka, nasan idan za ku
shekara kuna fafatawa ba zata tava saduda ba. Ita da kuke
ganinta hata ni tsoron fushinta nake saboda bata san ayi haquri
ba. Kune alqarya da kuka vata mata rai bata qarar da ku ba”
Macen sirri ta yi murmushi jin abinda ya faxa ta dubi sarki
jamhas tace masa.
“Kar ka damu nima zan saka maka da alheri kamar
yadda ka taimake ni, zan baka maganin matsalarka ta rashin
samun haihuwa, matarka zata haifa maka ‘ya mace wacce zata
zama jaruma mai bajinta, kuma zan kawo wannan baqar gabar
da take tsakaninka da sarki mazwan wanda hakan zai bunqasa
tattalin arziqin ku” Tayi shiru tana duban cikin birnin arnan
daji ta kuma kallon sarki jamhas wannan karon babu walwala
akan fuskarta.
“Ina baqin cikin sanar da kai nan gaba za a haifi
wani yaro da zai kawo qarshen wanan zaman lafiyan da zan
samar a tsakaninka da sarki mazwan. Yaron zai zo birnin ku
yana neman taimakon ka, saboda sarki mazwan yana son
halaka yaron kai kuma ya zamar maka dole ka taimake shi ka
21
DAN BAIWA
kuvutar da shi, zan mallaka maka wasu dawakai guda biyu
baqi da fari kuma zan yi wata tsatsuba a bayan gidanka tanan
zaka fitar da yaron kuma dole ka haxasu da ‘yarka shi ka bashi
farin doki ita kuma ka bata baqi ka aika da su zuwa birnin sin
anan za a koya musu horo na yaqi” Ta xan saurara kaxan taci
gaba.
“Ka sani yakai jamhas duk wanda bai taimaki
wannan yaron ba babu shakka nan gaba zai kasance cikin
qasqanci saboda jarumi ne xan baiwa. Yana da abin al’ajabi
mai tarin yawa shi ne kuma zai kawo qarshen baqin zallunci
sarki mazwan zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali, ka
sani duk duniya babu wani wanda ya isa yin nasara akan sarki
mazwan face wannan yaron, tabbas ya bayyana gare ni sai ya
zo wannan birnin naku, kuma tsakanin kai da sarki qasar Nur
xaya daga cikinku wani zai mallaki takobin sarki mazwan
wacce ita ce sirrin mulkinsa.
Amman abinda sarki mazwan da bokansa basu sani
ba wannan takobin ba komai bace a tarihin mulkinsa, wannan
lamarin ya voyewa boka marmasi a cikin sha’anin bokancinsa
kuma ba zai tava gano hakan ba sai lokacin da yaro xan baiwa
ya bayyana, za su fahimci sun aikata kuskure wanda ba za su
tava gyara shi ba kasan shi zallunci baya tava xorewa”
Waxannan kalaman ba qaramin xaurewa sarki jamhas kai ya yi
ba.
‘Mene abin yi yanzu?”
“Ka taimaka masa ka tura shi zuwa birnin sin” Cikin
kaxu yace mata.
“Birnin sin fa kika ce birnin da zuwan sa yafi komai
tashin hankali da hatsari na tsafafiyar birinya da kuma
mashahuran ‘yan fashi ga bala’i kala-kala a hanyar zuwa qasar
ta sin, haka idan mutum ya isa birnin bai tsira ba saboda acan
22
DAN BAIWA
cibiyar mashahuran bokaye ta duniya take kuma a can ake saye
da sayarwa na tsafi akan hanya a ko ina zaka koyi sihiri na tsafi
acan idan baka zama matsafi ba tabbas ba zaka iya zaman
qasar ba” Jin wannan kalamin ya saka macen sirri ta yi
murmushi har sai da haqoranta suka bayyana.
‘Wannan duk abinda kake gani lamari ne na sihiri
domin a riqa wahalar da jama’a, wannan birinyar da take tsare
fatake tana kashe su wani boka ne ya samar da ita domin ta
adabi jama’ar da suke kai kawo a wannan dajin zuwa birnin sin.
Anyi haka ne domin hana jama’ar da suke tureniyar zuwa
birnin sin domin koyon tsatsuba da kuma kai bayi.
Nasan baka da sanin qasar shamawa ta kasance
babbar daula data shahara wajen sayen bayi da kuma sayar da
su zuwa ga manya dauloli wannan damar ya saka ta qula
yarjejeniya da qasashe masu yawa” Sarki jamhas ya yi shiru
yana kallon macen sirri a hankali yace mata.
‘Ina jinki kina bayani game da samuwar birinyar
tsafi wacce ta adabi aljanu da mutanen da suke ilahirin dajin”
Macen sirri tayi murmushi a hankali tace masa.
“Ku ‘yan adam kuna son jin labarai, bari ka ji
labarin na su a taqaice, duk dana san tarihin ba zai zame maka
mai amfani ba tunda nasan duk duniya babu mai halaka
tsafafiyar birinya sai jarumi xan baiwa” Ta saurara tana
kallonsa sannan ta ci gaba.
Bayan wani dogon zamani sarakuna sun gabata a
wani qarni aka yi babbar daula ta qasar sin, ita kuma qasar
shamara tana can gefe da qasar judan qaramar qasa ce da take
cikin tsuburi da sai ka ratsa kwazazzabai da dajujjuka sannan
zaka qarasa zuwa qasar sin.
23
DAN BAIWA
A wannan lokacin babu abinda yake ci sama da tsafi
duk wanda ya iya tsafi shi ne mai dukiya mai kuma iko da
kowa a garin. Wannan dalilin yasa jama’a da dama suka riqa
bazama cikin duniya domin koyo tsafi.
Qasar shamara suna bin tafarkin duk wanda yafi wani
qarfin tsafi shi ne zai zama sarkin daular wannan dalilin ya saka
sarakunan da suke qasar basa jimawa akan mulki, saboda duk
lokacin da wanda ya fi ka qarfi ya zo zai kashe ka ya haye kan
karagar.
Wannan tsarin da suke kai yana matuqar damun jama’ar
qasar da kuma wani shashashan xan sarki wanda duniya bata dame
shi ba, a iya tarihin qasar ba a tava yin sokon xan sarki kamarsa ba.
Mulkin babansa bai dame shi ba zaka same shi ko wane
lokaci a qarqashin bishiyar mangwaro yana xan kallo iskar dake
kaxa ruwan wani tabki da yake gaba kaxan da gidan sarki, wannan
xabi’ar tasa tana damun mahaifinsa ganin cewar tsufa ya kama shi
kuma gashi xansa ba zai gaje shi ba saboda bai san tsafi ba ko na
sisin kwabo.
Hakan ya saka ya kasance cikin fargaba da faxuwar gaba,
wannan dalilin ya saka sha’anin mulki ya soma tangarxa yana samun
koma baya. Saboda yasan tabbas idan ya faxi ya mutu abokin
gabanshi xan boka duqum ne zai gaji sarautar. Kuma yasan halin
jamru ba shi da tausayi bai qi idan aka zo fitar da gwani na magajin
sarauta ba ya kashe xansa kamzu, saboda yana buqatar xaukar fansar
abinda sarki ya yi wa kakansu ya amshe mulki a hannunsa.
Yasan babu makawa sai jamru ya yi amfani da tsatsub
kala-kala saboda ganin bayan kamzu, hakan yana nuna za a yi
haihuwar guzuma xa kwance uwa kwance zai zama mutuwarsa data
xansa taqin sa’a ne.
Tunda ana gudanar da gasar zama sabon sarki ne sa a
uku bayan mutuwar tsohon sarki duk mai sha’awar shiga zai zama
ya iya tsatsuba gwani kuma wajen iya bokanci.
24
DAN BAIWA
A safiyar yau ne sarki laqamu ya kirawo xansa cikin
turakarsa yana kishingixe suka zauna yana kallonsa cikin nutsuwa
fuskarsa sam babu walwala yace masa “Me ka tanada domin gadona
bayan mutuwata?” Ya xago yana dubansa.
“Ban tanadi komai ba, tunda kaga ni ba jarumi ne bane
kuma ban iya tsafi ba. Haka kuma ban maida hankali domin koyon
ko xaya ba” Jin wannan maganar ba qaramin qonawa sarki rai ta yi
ba.
“Kai tafi can soko sulutun banza gwara haihuwar mace
da kai… kana zaton akwai wanda zai gaji sarauta cikin sauqi, ya
zama dole ka tashi tsaye domin neman kariya idan bah aka ba tabbas
jamru ba zai sassauta maka ba. Ni kuma da kake gani kaga dai tsufa
ya riske ni babu wani taimako da zan iya baka sai dai wanda ba a
rasa ba, saboda duk wanda zan baka zuwa yanzu jamru yasan shi,
saboda ya zama gagarabadau a fagen sihirin tsafi” Waxannan
kalaman sun xagawa kanzu hankali, shi a ra’ayinsa sam babu
ruwansa da sarauta saboda baya fatan gadon mahaifinsa saboda
ganin yadda ake fama da tsatsuba da amfani da jinin mutane ana yin
bokanci.
Wannan abun yana damunsa yasan zallunci ne da kuma
neman duniya. Yana gani wani lokacin za a yanka jarirai a yi sihiri
das hi ko kuma a bine mutum da ranshi a qasa sai ya yi kwana goma
sanan a tono sassan jikinsa a yi sihiri da shi, ganin wannan zallunci
ne yana xaga masa hankali yasa baya qaunar mulkin na mahaifinsa.
Amman wannan kalamin na mahaifinsa sun tsuma masa
zuciya, ya soma tunanin kalamin da zai faxawa mahaifinsa domin
kwantar masa da hankali. “Kayi haquri ya mahaifina tabbas baya
tava yiyuwa barewa tayi gudu xanta ya yi rarafe, kai ka zama
maxaukaki shi yasa kowa yake tsoronka amma ni kuma ban xauki
ko xaya daga cikin halinka ba, amman tabas ba zan baka kunya ba
idan wannan ranar ta zo, zan so wannan ranar ta zo min a lokacin
kana numfashi tabbas da ka sai ka yi alfahari da ni domin zan zama
mashahuri, kuma zan kauda tsafi daga doron duniya domin ni sam
25
DAN BAIWA
ban bada imani da su ba” Wannan maganar ba qaramin xagawa
mahaifinsa hankali ta yi ba.
“Kar ka zo min da irin wannan salon na maganar bana
jin wanan maganar zata zama mai tasiri a gare ni, don haka na
umarce ka daka tashi tsaye domin neman tsatsuba da sirrin tsafi
domin kare kanka” Ya jinjina kai.
“Zan nemi mafita wacce zata kare ni” Yana gama faxin
haka ya tashi ya fita ya nufi can wajen daya saba zuwa yana zama,
shi kam yasan jarumtaka ba zata kai shi tudun muntsira ba domin
jamru ya kasance gawurtacen jarumi haka kuma mashahuri a fagen
tsafi idan haka ne ta yaya rago kamarsa zai samu nasara akansa har
ya xare kan karagar sarautar mahaifinsa? Sanin hakan ba mai
yiwuwa bane shi yasa ya cire ransa daga kan lamarin yasan kuma
duk lokacin da jamru ya zama sarkin qasar sai dai shi da iyayensa su
idan kuma ba haka ba sai ya kashe su ko kuma ya riqa gana musu
azaba har zuwa lokacin da za su halaka don haka ya zamar masa
dole ya nemo mafita.
Kanzu ya ji duk abin duniya ya yi masa yawa ya rasa ina
zai saka kansa, yana zaune a wajen da yake har zuwa gefen faxuwar
rana sai ya ji wani sanyi yana sirarowa sanyi da sai daya saka jikin
kanzu ya soma karkarwa yana makyarkyatar sanyi. Zuwa wani
lokaci sai iskar ta tsaya wata mace doguwa mai kyawun diri ta
bayyana tunda yake bai tava ganin kamarta bay a ga kai tsaye ta
nufo wajen da yake cikin tsananin tsoro ya miqe da zumar zurawa da
gudu amman sai ya ji qafafunsa sun saki sun koma kamar jiqaqen
lagwani yana wajen har farar macen ta qaraso wajensa zuwa wani
xan taqin lokaci tace masa.
“Ko kasan ni wacce?” Ya gyaxa kai.
“A’a amman alamu sun suna ke sarauniyar aljanu ce”
Tayi murmushi.
“Ka saki jikinka ka daina jin tsorona domin da ina da
nufin cutar da kai a duk lokacin daka zo bakin kogin nan ka zauna.
Ka sa ni na kasance sarauniyar aljanun cikin ruwa kuma bani da
wajen zama face wannan kogin na kasance ina bin addinin
26
DAN BAIWA
musulunci, babu cutarwa a cikinsa yana kuma hani da aikata zallunci
da mugunta da hani da aiwatar da kafirci” Ta saurara tana kallonsa
sannan ta ci gaba da magana.
“Ka yi sani cewar na zo ne domin na taimake ka, saboda
xa zu ina jin yadda kuka yi da mahaifinka kuma gaskiya ya faxa
maka saboda idan jamru ya zama sarki za ku kasance cikin qasqanci,
haka kuma jama’ar qasar za su kasance cikin qasqanci da tagayara
wanda babu ranar fita daga ciki. A wannan zamanin babu jarumi
kamar Jamru haka kuma a fanin tsafi, don haka ina kiranka daka
zamo ma’abocin musulunci addinin da bai aminta da tsafi ba” Ai
koda ya ji wannan maganar cikin sauri ya saukar da numfashi yace
mata.
“Ni kamar mahaukaci ne da yake jin yunwa komai na
samu ci zanyi haka kuma kamar wanda ruwa ne ya ci yo shi, don
haka zan amshi wanna addinin da kika zo min da shi idan har zan
tsira daga sharin jamru” Jin haka ya saka sarauniyar aljanun cikin
aljanu tayi murmushi.
“Babu shakka zaka kuvuta daga sharinsa yanzu abinda
nake so dakai shi ne ka shiga cikin kasuwar bayi zaka samu an kawo
wata baqar baiwa ka siyeta tana bin addinin musulunci, sai ka bata
aminci da salama ka kuma nemi ta sanar da kai komai daya shafi
addinin tsira hakan zai kuvutar dakai daga duk wani sharrin jamru”
Tana kawo wanan sai ya ji iskar da take kaxawa ta xauke ta koma
daidai kamar bata tava faruwa ba.
Ganin haka yasa ya sauke ajiyar zuciya ya tashi cikin
sauri da azama ya nufi cikin kasuwar bayi da zumar ya sayi wannan
baqar baiwar yana shiga cikin kasuwar ya soma dube-dube yana
waige-waige ko zai ga baqar baiwa amma ko kaxan bai samu damar
hakan ba. Haka ya yi ta yawo duk wajen daya gifta sai jama’a su
zube suna yin gaisuwa a gare shi wasu suna cewa gaisuwa ga sarki
mai jiran gado, amman