sarki ya ajiye wanna xin,
60
DAN BAIWA
idan har sarki ba xauko littafin ya yi ba ya buxe babu yadda za a yi ya
gane cewa an xauke na gaskiyar” Koda kuyangar ta zo nan a zancenta
sai sarkin yaqi Marhat ya yi doguwar ajiyar zuciya, sannan ya dubi
kuyangar cikin alamun tsananin damuwa yace.
“Yanzu saboda Gimbiya bata son rasa ni, shi ne tayi
gangancin xauko wannan littafin na sarki?” Kuyangar ta gyaxa kai tace.
“Qwarai kuwa kuma ina tabbatar maka da cewar idan har
Gimbiya bata mallake ka ba, duk wanda ya yi qoqarin mallakarta sai
dai ya sami gawarta, zan dawo nan da cikar kwana shida da tsakar dare
na karvi wannan littafin daga hannunka domin a mayar da shi inda yake,
kafin washe garin ranar da za ku cika sharuxan zama ‘yan uwan mu”
Koda gama faxin haka sai kuyangar ta yiwa sarkin yaqi marhat sallama
ta tafi.
Shi kuma sai ya miqe da hanzari ya je ya voye wannan
littafin a cikin jakarsa ya guzuri ya zauna yana tunani gami da nazarin
abubuwan da ke gabansa. A daidai wannan lokacin Dakarun nasa suka
sake dawowa suka zauna suna masu kewayeshi nan take babban cikin
nasu ya dubi Marhat ya ce.
“Ya shugabana waye ya aiko wannan kuyangar kuma wane
abu ta kawo maka a cikin mayafinta a qunshe?” Koda jin wannan
tambayar sai Marnat ya yi murtuke fuskarsa yace.
“Baya daga cikin halina na bayyana sirrin wani,shin baka ji
abinda kuyangar tace ba? Cewar ta zo ne da sirri a gareta” koda jin haka
sai kunya ta kama shugaban Dakarun ya sunkuyar da kansa qasa ya yi
shiru bai qara cewa uffanba.
Kamar yadda marhat ya tsara haka al’amarin ya kasance wato
dare na rabawa ya tashi gaba xayan Dakarun nasa suka tafi izuwa bayan
garin da suke, nan take Marhat ya fara basu horon yaqi na musamman
irin wanda sam basu tava gani ba a rayuwarsu mai tsananin wuyar
gaske.
Haka dai marhat ya yi ta basu wannan horon har izuwa gefen
alfijir saboda tsananin wahalar da suka sha a wannan horon yaqin said a
wasunsu suka rinqa zubar da qwallar wuya.
61
DAN BAIWA
Lokacin da aka shafe kwana uku ana wannan horon sai ya
zamana cewar kowa jikinsa ya saba suna iya jurewa koma a sannane
kowannensu ya sami gagarumin qarfi da jarumtaka ta musamman
wacce bai tava jin kamarta ba a cikin jikinsa.
A ranar dare na uku ne bayan sun tashi daga karvar horon sun
zauna suna hutawa sai shugaban Dakaru ya dubi sarkin yaqi marhat
yace.
“Ya shugabana wai shin me yasa ka zavi mu rinqa yin
wannan horon na yaqi a sirrance a cikin tsakiyar dare?” Koda jin
wannan tambayar sai sarkin yaqi marhat ya dubi badakaren yayi
murmushi yace.
“Abin da yasa nake baku wannan horon a tsakiyar dare shi ne
bana son Dakarun da zamu fafata dasu su san cewa muna yin wani
qoqari don tunkarar su, tunda sun san cewar sun fi mu qarfi da iya yaqi
ba za su yi tunanin suyi wani tanadi ba za su saki jikinsu saboda suna
ganin cewar farat xaya za su gama damu.
Ina mai tammabat muku da cewar yanzu da wannan horon
yaqin da muke dashi zamu iya samun nasara akan su ammafa zamu iya
shanwuyar gaske” Koda sarkin yaqi marhat ya zo nan a jawabinsa sai
murna ta kama gaba xayan Dakarun amma sai qaramin cikinsu mai
suna Lazyan ya dubi marhat yace.
“Ya shugabana yaya batun ka na koyon yaren mutanan
garinnan da akace kayi? Har yanzu banga kana yin wani yunquri akan
hakan ba” Koda jin wannan batun sai marhat ya yi murmushi yace.
‘Kabar wannan batun kawai” Koda gama faxin haka sai
marhat ya miqe tsaye ya shige izuwa cikin qurya turakarsa ya kwanta
ya kama barci.
Da dare sarkin yaqi marhat yana zaune ya yi shiru yana
tunani abinda zai iya faruwa washe gari a fada sai sarkin Dakaru ya
shigo yace masa.
“Ka yi baquwa wannan kuyangar nan ce data zo kwanaki” Ya
xan yi jim kamar bai ji abinda yace ba, har zuwa wa su ‘yan daqiqai
sannan yace masa.
62
DAN BAIWA
“Kace mata ta shigo” Ya juya ya koma wajenta ba a fi
mintina ba sai gata ta shigo ta faxi gabansa ta yi gaisuwa.
“Shugabata tace na gaishe ka”.
“Ina amsa wa” Ya faxa a taqaice sannan ya miqe zuwa wajen
daya adana littafin data kawo masa ya xauko ya bata.
“Bansa irin godiyar da zan yi ba, domin wannan littafin ba
qaramin taimaka min ya yi ba yanzu ka mina da qarfin gwiwa xari bisa
xari akan lallai zan samu nasara akan wannan lamarin”.
Kuyangar ta xago da kai a hankali ta dube shi sannan cikin
qwarin gwiwa itama tace masa.
“Ina godiya ga abin bauta da yake shirin cikawa Gimbiya
burinta na son mallakar abinda take so”. Ya dubeta.
“Kina da tabbaci akan abinda kika faxa?” Ta gyara zama.
“Kamar yadda kwanaki na faxa maka cewar duk wanda ya
auri Gimbiya bayan kai to sai dai ya auri gawarta amman ba ita ba,
domin ina da yaqini xari bisa xari akan irin qaunar da take yi maka”.
Sarkin yaqi marhat ya yi murmushi cike da jin daxi.
“Wannan kalaman naki suna qara bani qarfin gwiwa sosai
game da samun nasarata” Ya xan xaga kai sama yana duban saman
xakin sannan ya ci gaba da magana.
“Yanzu a wane yanayi Gimbiya take?” Kuyangar ta kuma
sunkuyawa a gabansa.
“Tana cikin halin begenka, na barota cikin fargaba da tsoron
shin bayan ka karance littafin ka iya yaren namu, na kuma ga alamar
tsoro a tattare da ita don bata son rasa ka” Koda jin haka sai sarkin
yaaqi marhat ya yi murmushi yace mata.
“Ina son ki baiwa Gimbiya tabbacin lallai ni ne mai nasara a
wannan lamarin, kuma babu wani wanda zai zama mijinta face ni, don
haka idan kin damqa mata wannan littafin ki faxa mata cewar ina bata
tabbacin nan da wasu ‘yan kwanaki muna tare da ita a matsayinta na
mata a gare ni” Koda jin haka sai kuyangar tayi murmushi sannan a
hankali ta miqe tare da kuma yi masa fatan samun nasara.
Bayan fitarta sarkin yaqi Marhat ya yi shiru sai tunanin
matarsa da kuma xansa suka kuma dawo masa a cikin zuciyarsa, ya
63
DAN BAIWA
sunkuyar da kansa qasa kawai ga mamakinsa sai ya ji hawaye yana fita
daga cikin idanunsa.
**
Kwana bakwai na cika tun da sassafe fadar sarki jamhas ta
cika ta batse da al’umma domin a ga yadda za a qure su sarkin yaqi
marhat saboda kowa gani yake cewa basu isa su tsallake wannan
sharaxin da aka gindaya musu ba.
Sai da kowa ya hallara a fadar amma sarki bai zo ba har
izuwa tsawon ‘yan sa’o’i al’amarin daya dugunzuma hankalin ‘yan
majalisa kenan da sauran mutanen gari,bisa wannan dalilin fadawa suka
tashi manzo ya tashi ya shiga cikin gidan sarautar domin gano ko lafiya.
A
jarumi Dan Baiwa 5
she acan gidan sarautar hankalin sarki jamhas ne
ya dugunzuma ainun sakamakon wani mafarki da
ya yi. A cikin mafarkin an nuna masa cewar sarkin
yaqi Marhat sun tsallake dukkan sharuxxan da aka
gindaya musu amma sun yi amfani da najikinsa
wajen samun nasara.
Nan take sarki ya xauko madubin tsafinsa ya shiga bincike
domin ya gano ta hanyar da su marhat za su sami wannan nasarar amma
sai abu ya gagara. Koda ganin haka sai sarki jamhas ya zauna ya rinqa
tunani har izuwa lokaci mai tsawo.
Yana cikin wannan tunanin ya tuno da wannan littafin mai
fassarar yaren qabilarsu cikin hazari sarki jamhas ya miqe tsaye ya tafi
izuwa xkin da yake adana kayan tarihin qasar, da shigarsa sai ya durfafi
inda wata farar akwatin zinare take cikin hanzari sarki ya buxe akwatin
ya yi arba da littafin yananan kamar yadda ya ajiyeshi ko qurar jiki ba a
goge ba.
Kai hatta yana dake cikin akwatin tananan alamar cewa an
daxe ba a buxe ba. Duk da haka sai sarki jamhas ya kai hannu da nufin
ya xauko littafin ya buxe sai kawai ya ji an kirawo sunansa cikin fushi
sarki jamhas ya waigo ya dubi mai kiran sunansa.
64
DAN BAIWA
Ba wata bace face mahaifiyar Gimbiya Hamrita cikin sairi ta
qaraso gareshi tace.
“Haba ya kai mijina kayi sani cewa fiye da sa’a uku fada ta
cika ta batse,kai kaxai ake jira har fadawanka sun qosa sun aiko
manzo” Koda jin haka sai sarki jamgas ya yi tsaki ya mayar da murfin
akwatin ya kulle ya datse da kwaxo ya sanya makulin a jikin mazugin
wandonsa ya zuge sannan ya fice daga cikin turakarsa ya nufi fada kai
tsaye.
Koda ganin haka sai mahaifiyar Hamrita tayi doguwar ajiyar
zuciya tana mai dafe qirjinta a lokacin ne Gimbiya Hamrita ta fito daga
bayan wata qofa data lave suka dubi junansu suka yi murmushin farin
ciki bisa ganin cewa asirinsu bai tonuba.
Lokacin da sarki jamhas ya iso filin fada sai mutane suka
ruxe da shewa aka kama yi masa jinjina makaxa da mawaqa suka shiga
yi masa kirari nan danan Dakaru suka buxe masa hanya ya isa har inda
karagar mulkinsa take ya zauna.
A wannan lokacin su sarkin yaqi na tsaye a tsakiyar filin
fadar a gefe xaya su goma. A wani gefan guda kuma manyan
zakwaquran mayaqan qasarne a tsaye cikin gagarumin shigar yaqi,
sarkin yaqin birnin ne shugabansu, suma xin su goma ne kuma
kowanne daga cikinsu girman surar jikinsa ta sadaukai da tsawonsa ta
ninka tasu Marhat sau biyu.
Ba tare da vata wani lokaci ba sarki jamhas ya miqe tsaye
daga kan karagarsa ta mulki ya fuskanci jama’a ya farad a gaishesu
gami da neman afuwa bisa rashin fitowarsa da wuri bisa wata larura.
Bayannan sai yace “Yak u jama’ar wannan birnin namu mai
albarka kuyi sani cewa rana bata qarya sai dai uwar xiya ta ji kunya,
yau ce ranar da su sarkin yaqi marhat za su cika sharuxxan da muka
gindaya musu domin mu karvesu a matsayin ‘yan uwanmu kuma na
baiwa sarkin yaqi marhat auren ‘yarta Gimbiya Hamrita” A daidai
wannan lokaci ne aka ji an buga tambura kuma an busa algaita sai ga
Gimbiya Hamrita ta fito daga cikin gidan sarautar kuyangi kimanin
guda xari na take mata baya.
65
DAN BAIWA
A wannan lokacin Gimbiya Hamrita ta cava ado na gaban
kwatance wato na qure adaka kuma fuskarta cike take da murmushi
gami da annuri tamkar wacce aka biya mata dukkan buqatunta na
duniya.
Kai tsaye Gimbiya Hamrita ta nufi inda sarkin yake tsaye ta
rungumeshi sannan ta sumbaci goshinsa, shima sai ya kama hannayenta
ya sumbata sannan ya zaunar da ita bisa kujerar dake daf da karagarsa
ta mulki sannan ya juyo ya sake fuskantar jama’ar sa ya ce.
“Yanzu za mu fara ne da sauyawa baqin mu addininsu da
al’adarsu” koda gama faxin hakan sai sarki jamhas ya tafa hannayensa
sau biyu.
Nan take waxansu hadimai goma suka shigo cikin filin fadar
xauke da tufafi akan farantai goma. A gaban bainar taron suka kwave
tufafin dake jikin su, sarkin yaqi marhat suka sanya musu irin nasu,
sannan hadiman suka fice.
Fitarsu ke da wuya sai sarki jamhas ya sake tafa hannayensa
sau uku, nan take malaman addinin qasar su goma suka shigo cikin filin
ruqe da farantai.
Kowane faranti akansa akwai ruwan jini a cikin kuttu da
kuma silin gashin tsuntsun alhuda-huda. Nan take aka shafawa su sarkin
yaqi marhat zanen kibiya akan kumatunsu da wannan ruwan jinin kuma
aka soka gashin alhuda-huda a cikin gashin kansu guda daidai.
Koda aka gama yi musu wannan adon sai suka ga ashe irin
shigar dakarun qasar aka yi musu,bambancinsu dasu kawai shi ne su
Dakarun birnin na arnan daji kalar tufafin jikinsu ruwan xorawa ne su
kuma su marhat nasu tufafin shuxine nan take aka biyawa su marhat
sunan gunki da ake bautawa a garin har sau uku suna maimaitawa.
Faruwar hakan ke da wuya sai filin ya ruxe da sowa gami da
tafi saboda ganin cewa malaman addinin suka fice daga cikin fiin
sannan sarki jamhas yace.
“Yanzu baqin mu sun cika sharuxa na farko daga cikin
sharuxan da muka gindaya musu don haka za mu tafi izuwa kan sharaxi
na biyu wanda shi ne muna son a yi hira da sarkin yaqi Marhat da
yarenmu izuwa tsawon sa’a xaya ba tare da yayi kuskure ko tuntuven
harshe ba a cikin ambaton kalmomi” Koda jin wannan batu sai hankalin
66
DAN BAIWA
kowa ya dugunzuma domin ba a ga ta yadda marhat zai iya tsallake
wannan matakin ba.
Nan take wani dattijon mutum masanin yarensu sosai wanda
yafi shekara xari a duniya ya shigo cikin filin fadar ya iso har gaban
sarkin yaqi marhat ya tsaya suka qurawa juna idanu. Nan take fadar tayi
tsit! Tamkar mutuwa ta gifta,kowa ya kasa kunnuwansu domin ya ji
yadda sarkin yaqi marhat zai yi magana sosai a cikin yaren arnan dajin.
Da yawa daga cikin jama’ar dake fadar sun san cewa ko
sarkin yaqi marhat aljanine bai isa ya iya wannan yaren a cikin sati
xaya jal ba kuma dolene wannan dattijon ya qureshi saboda shi ne
mutumin dayafi kowa iya yaren a birnin.
Ba tare da vata wani lokaci ba kuma sai dattijon ya buxe bai
ya fara yiwa marhat tambayoyi akan waxansu al’adu na qasar da yadda
ake gabatar dasu.
Wohoho! Abin mamaki baya qarewa akan doron qasa. Nan
take jama’a suka ji marhat yana bayar da amsoshin dukkanin
tambayoyin da ake yi masa harma yana qarin bayani fiye da wanda
masana yaren da al’adar za su yi.
Bawai jama’ar garinba hatta sarki jamhas da matarsa da kuma
‘yarsa Gimbiya Hamrita said a suka kamu da tsananin mamaki.
Musamman Hamrita da mahaifiyarta sunfi kowa mamaki saboda Karin
bayanin da marhat ke yi babu shi a rubuce a cikin wannan littafin da
suka bashi.
Shi kansa Dattijon da yake yiwa marhat waxannan
tambayoyin said a ya jinjina masa kuma ya sallamasa yace.
“A yaun jaji kalmomin da ni kaina na manta dasu a cikin
yarenmu daga bakinka saboda haka ina neman alfarmar na zo gareka na
xauki karatu”.
Koda jin haka sai fadar ta ruxe da shewa mutane suka rinqa
yiwa sarkin yqi marhat jinjina da tafi.
Bayan su marhat su gama haye duk kan matakan ya zamana
cewa sauran matakin gumurzu tsakaninsu da manyan mayaqan qasar
sai fadar ta sake yin tsit fiye da karo na farko. Inda ace tsinke zai faxo
qasa daga sama sai anji qarar dirarsa akan tsakiyar filin da su marhat ke
tsaye saboda tsananin shirun da aka yi.
67
DAN BAIWA
Nan take sarkin jamhas ya dubi jaruman qasarsa gami da su
sarki marhat yace.
“Yanzu na za ku fafata muga iyakar qoqarin bakinmu, ku
sani cewa babu sani ko sabo a cikin wannan faxan,kowa zai iya rasa
rayuwarsa a wannan gumurzun amma duk wanda ya ji tsoro ya faxi
qasa za a qyaleshi ammafa ya faxi gasar” Koda gama faxin hakan sai
sarki jamhas ya xaga hannunsa guda sama, yana ajiye hannunsa sa qas
sai aka buga gangar fara gumurzu ai kuwa sai zaqwaquran Dakarun
birnin arnan dajin suka zare takubbansu suka rugo da gudu izuwa kan
su sarkin yaqi marhat suna kururuwa mai ban tsoro.
Qarfin gudun sawayensu ya haddasa tashin qura a filin, koda
su sarkin yaqi marhat suka ga waxannan dakarun sun taso musu sai
suma suka zare nasu takubban suka ruga suka taresu aka ruguntsume da
masifaffan yaqi.
Wahoho!, tabbas tashin hankali bashi da daxi kuma ita masifa
ba a sa mata rana. Lokacin da aka runguntsume da masifaffan yaqi
tsakanin rundunar biyu sai hankalin kowa ya dugunzuma a filin fadar
saboda tsananin qarar haxuwar takubba gami da ihun mazaje da kuma
qarar dudufniyarsu akan qasa.
Ganin yadda rundunar biyu ke kaiwa junansu sara da suka
cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta ne yasa kowa ya ximauce
domin ba a tava ganin gumurzu irinsaba saboda karamin alhakin ya
zama abin tsoro.
Duk irin qarfin saran dakarun birnin ainan sai gashi su marhat
na iya karewa gami da maida martani,kowa sai daya cika da xumbin
al’ajabi saboda an zata cewa farat xaya za a gama dasu marhat.
Abu dai kamar wasa said a aka shafe kusan rabin sa’a ana yin
mugun artabu ba tare da an lakaci jikin koda mutum xayaba daga cikin
rundunar biyu, kamar haxin baki sai rundunonin biyu suka ja da baya a
tare lokaci guda suka yi carko-carko suna haki da kallon-kallo na juna
kamar zakaru. Kai da gani kasan cewa kowane vangare na tunanin
hanyar da zai bi ya sami nasara.
A lokacinne sarki yaqin arnan dajin ya yiwa sauran ‘yan
uwansa Dakarun raxa a kunne,kawai sai gani aka yi sun yunqura cikin
zafin nama sun sake afkawa su sarkin yaqi marhat kuma wannan karon
68
DAN BAIWA
sun sauya salon yaqin domin kowannensu ya zavi abokin gwafzawarsa
ya afka masa da dukkan qarfinsa kuma ya haxa da kai masa sara da
suka cikin tsananin zafin nama da mugun nufi.
Ai kuwa nan take labari yasha bamban domin a cikin daqiqu
basu fi arba’in bay a zamana cewa gaba xaya Dakarun sarkin yaqi
Marhat an yi musu rauni babu wanda ba a sare shi ba ko yankarsa
kamar sau uku ba.
Sai gashi jini na zuba a jikinsu amma saboda baqin naci da
tsananin juriya sun qi yarda su faxi qasa. Koda sarkin yaqi marhat yaga
yadda aka yiwa yaransa wannan mummunar varna sai ransa ya vaci
kuma zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata qone.
Cikin tsananin fushi ya shammaci sarkin yaqin arnan daji ya
daka tsalle sama ya doki qirjinsa da qafarsa guda, saboda qarfin dukan
sai da sarkin yaqin ya yi taga-taga da baya yana neman faxuwa qasa.
Ba zato ba tsammani sai aka gay a xago sama ya yi wuf cikin
baqin zafin nama ya damqi maqoshin marhat kawai sai ganin marhat
aka yi yana wutsil-wutsil qafafunsa yana qoqarin cire hannun sarkin
yaqin arnan daga kan wuyansa a lokacin da idanunsa suka kaxa suka yi
jawur yana qoqari har sarkin yaqin arnan daji ya yunqura zai maka
marhat a qasa sai kawai ya kasa.
Ba komai ne ya janyo haka ba face jin sukuwar dubunnan
dawakai sun durfafo fadar cikin ximauta mutane suka waiga sai akaga
ashe Dakarun yaqin birnin Hindune wanda yawan adadinsu ya kai
mutum dubu suka kawo harin bazato.
Sarki mazwan ne da kansa ke jagorantar wannan rundunar ya
xaga takobinsa sama yana ruri da kururuwa.
***
Su jarumi xan baiwa suka ci gaba da tafiya a cikin qungurmin
daji duk a cikin niyarsu ta son qarasawa zuwa birnin sin bayan sun yi
doguwar tafiya kamar yadda suka saba suka qaraso wajen wata qorama
mai xauke da ‘ya ‘yan itatuwa da kuma sanyi yana tashi a wajen, suna
zuwa wajen cikin azama da salhim ya soma cire ‘ya ‘yan itatuwa yana
Tarawa ita kuma Gimbiya zasmin da azama ta saki dokinta ta nufi
wajen da ruwan qoramar nan yake gudana.
69
DAN BAIWA
Tana zuwa ta tsuguna ta kai hannunta ta xebo ruwan ta kai
bakinta zata sha sai ta ji an yi mata magana cikin xaga murya, ta xago a
hankali suka xaha idanu da Raiyan yana tsaye daga can gefe guda.
“Kar ki sake ki sha ruwan nan” Ya nufo wajen da take a
lokacin salhim shima ya qaraso wajen cike da gajiya ga kuma tsananin
qishir ruwa daya kama shi.
“Saboda me, ina ganin ruwa gwanin kyau za ka hanani sha?”
Raiyan ya qarasa wajen yana xan yin murmushi.
“Wannan ruwan da kike ganinsa tarko ne na wata shu’umar
bokanya da take xanawa domin fatake masu tafiya, tana amfani da shi
ne kuma domin kama duk wani wanda ya shiga hannunta sai ta mayar
da su bayi tana bautar da su, duk wanda yasa wannan ruwan bashi da
ikon savawa umarninta” Salhim da Gimbiya Zasmin suka saki baki
kawai suna kallonsa cike da mamaki.
“Amman gaskiya ba mu ga wata alama da zata nuna mana
haka ba, don haka ni dai yadda nake jin qishin ruwa kuma ga ruwan ina
gani babu abinda zai hanani sha” Salhim ya faxa yana mai sunkuyawa
ya xebo ruwan.
Kafin Zaiyan ya yi wani yunquri tuni har salhim ya soma
shan wannan ruwan, bayan ya sha ya qoshi sai ya koma gefe guda ya
zauna ya xauko ‘ya ‘yan itatuwan daya tsinko ya soma ci.
Zaiyan ya yi shiru kawai yana kallonsa, ganin haka sai
Gimbiya Zasmin ta kalli Salhim na wani xan lokaci sannan ta dubi
Zaiyan.
“Kace idan muka sha wani abu zai faru amman kuma ga
salhim yasha babu abinda ya same shi” Zaiyan ya yi murmushi kawai.
Koda ganin haka sai itama Gimbiya Zasmin ta sunkuya ta
xebi ruwan ta sha, ta koma can kusa da salhim suka zauna suna cin ‘ya
‘yan itatuwan abin su.
Ai kuwa Gimbiya Zasmin bata jima da zama ba sai suka ji
wata qara mai tsananin firgitarwa ta karaxe wajen, bayan wani xan
taqin lokaci sai wata baqar guguwa ta turniqe ilahirin wajen, nan fa su
Gimbiya Zasmin da Salhim suka miqe cike da tsananin tsoro suna
kallon wannan baqar guguwar da ta turnuqe tana toroqo sama.
70
DAN BAIWA
Can bayan wani lokaci sai ta soma lafawa a hankali a hankali
har zuwa wani xan taqin lokaci kafin daga bisani ta sarara a lokacin
kuma suka ga wata sharveviyar macijiya ta bayyana ta tunkaro wajen
da suke, lokaci guda ta buxe wangamemen bakinta tana haxiye duk
abinda tayi karo da shi.
Koda ganin haka sai su salhim suka ruga da gudu domin tsirar
da ransu daga hakala. Duk gudun da suke yi da zarar sun juya domin
ganin ko sun yiwa wannan macijiyar nisa sai suka tana qara kusanto su.
Hakan ne ya qara xaga musu hankali sosai domin ganin lallai
halaka tana qara kusanto su, a haka sai daya zama bai fi taku xaya
wannan shu’umar macijiyar ta qaraso wajen su Gimbiya Zasmin sai
suka yanke jiki suka faxi, ganin haka ya saka macijiyar ta tsaya da
binsu suka tsaya suna kallon-kallo tsakaninta da su Salhim.
Nan fa ido ya raina fata, ya juya yana kallon Gimbiya Zasmin
a hankali yace mata.
“Kinga abinda kika jawo mana” Ta buga masa harara.
“Ni na jawo mana? Ka dai jawo mana ai daman sai da Zaiyan
ya hana ka amman ka yi taurin kai yanzu gashi babu makawa halaka za
mu yi” Salhim ya sunkuyar da kai cike da takaici yace mata.
“Ni fa bana son mutuwa yanzu, domin kinga ban samu na
cika burina ba na xaukar fansa akan sarki Mazwan” Gimbiya Zasmin ta
dube shi cikin tsananin damuwa.
“Yanzu dai bamu ga tsuntsu bamu ga tarko, yanzu dai ka
gwada baiwar ka kamar yadda ka saba kuvutar da mu a baya” Ya buga
mata harara.
“Da hakan zata yiwu ai bama zan bari mu sha wannan
wahalar da muka sha ba” Yana rufe bakinsa sai suka ga wannan
macijiyar tayo kansu gadan-gadan bakinta a buxe da zumar cinye su,
amman kafin ta qaraso zuwa wajensu sai suka ga taja ta tsaya, cikin
tsananin mamaki suka juya bayansu domin ganin abinda yake tsaye a
bayansu.
Nan suka yi arba da Zaiyan a tsaye cikin shiri na yaqi, a
hannunsa riqe da wata sharveviyar takobi, nan fa wannan macijiyar ta
doko tsalle ta nufi Zaiyan da nufin haxiye shi, shima nan ya doka wani
tsalle sama ya tunkareta.
71
DAN BAIWA
Wohoho! Nan fa kallo ya koma sama,wai shaho ya xauki
giwa domin wannan macijiyar tana kawowa zaiyan sara yana gocewa
shima yana kai mata sara da tashi takobin, amman sai yaga ta goce cikin
tsananin zafin nama, ta kawo masa duka da sharveviyar jelarta shima ya
goce cikin zafin nama.
Nan suka cure suna wannan gumurzun mai ban mamaki, sai
da suka shuxe sa’ani bakwai suna fafatawa ba tare da wani ya samu
nasara akan wani ba, ganin haka sai zaiyan ya qara azama da qarfin kai
saransa da zumar ganin ya halaka wannan macijiyar, yana cikin kai
mata sara sai ya yi tuntuve da wani dutse ya yanke jiki ya faxi qasa.
Koda macijiyar nan taga haka sai ta yo kansa gaba xaya baki
buxe da zumar haxiye shi, tana zubawa ta kawo masa cafka da baki
cikin wani tsananin zafin nama ya goce, amman bai qarasa barin wajen
ba ta saka jelarta ta mako shi kafin ya yi wani yinquri sai ta nannaxe shi
da jelarta.
Ta matse shi, zaiyan ya ji numfashinsa ya soma xaukewa
saboda tsananin matsar data yi masa. Koda ganin haka sai hankalin su
salhim da Gimbiya Zasmin ya yi tsananin tashi,domin suna da tabbacin
lallai wannan kananaxewar da wannan macijiyar tayi wa zasmin babu
makawa ya riga ya halaka.
“Ka yi wani abu mana salhim” Gimbiya Zasmin tace masa.
Shima ya dubeta a fusace “Da zan iya yin wani abu na faxa
miki da tuni na yi” Ta kamo hannunsa cikin sauri.
“Haba nawan kar ka bada ni mana, kaifa nawa ne nasan irin
baiwar da kake da ita” Wannan maganar da Gimbiya Zasmin ta faxa sai
salhim ya dubeta cike da mamaki suna haxa ido ta yi masa wani
ni’imtaccen murmushi.
Nan fa Salhim ya ji kamar alura ta yi masa, nan take ya zare
takobinsa ya tunkari wannan qatuwar macijiyar yana zuwa wajen da
take ya daka tsalle sama ya kai mata sara amman kafin saran yakai
jikinta sai ta waiwayo ta cafke shi da bakinta ta soma qoqarin haxiye
shi.
Haba wa Gimbiya Zasmin tana ganin haka sai ta miqe cikin
tsananin fusata ta rugo itama da gudu, hannunta zare da takobinta tana
zuwa ta soma saka kaifin takobinta ta sari jelar wannan qatuwar
72
DAN BAIWA
macijiyar nan take ta gutsire jelarta saboda qarfin saran data yi mata,
nan fa macijiyar ta saki salhim dake bakinta saboda tsananin jin zafin
wannan saran da Gimbiya Zasmin ta yi mata.
Ta juyo kan Gimbiya Zasmin a fusace da zumar halakata,
wannan karkatowar data yi kanta shi yasa zaiyan ya yunqura cikin sauri
shima ya xauki takobinsa ya doka tsalle sama ya saka kaifin takobinsa
ya sare kan macijiyar nan take kan ya faxo qasa, gangar jikinta ta faxi
can gefe guda jini yana malala.
Zaiyan ya sunkuya qasa yana sauke numfashin gajiya, ita
kuwa Gimbiya Zasmin ta tashi cikin sauri ta ruga da gudu ta nufi wajen
da Salhim yake kwance tana zuwa ta kamo kansa ta xora akan cinyarta
ta zuba masa ido tana kallonsa, sam baya cikin hayyacinsa domin
wannan macijiyar ta saka masa dafinta a cikin jikinsa.
Ganin haka sai Gimbiya Zasmin ta yi tsamanin ya halaka nan
take ta soma kuka tana faxin.
“Kar ka tafi ka barni ni kaxai, kasan tun lokacin da muka
haxu dakai na