kansa kuma suka daddatsa sassan
38
DAN BAIWA
jikinsa suka kaiwa sarki muzwan ya saka aka watsawa kadojinsa sassan
jikin wannn yaron suka kama ci har suna faxa a junansu.
Kadojin da sarki mazwan yake kiwatawa sun kai guda arba’in da uku
kuma ko wacce a cikinsu takai girman bil’adama saboda zallunci sarki
muzwan ko wani qaramin laifi mutum ya aikata sai ya saka a kawo shi
da ransa ya saka a cila shi cikin kadojin su kuma su hau watanda da
sassan jikinsa.
Baya kadojin sun gama cinye sassan jikin wannan yaron xan
mahaukaciya sai sarki mazwan ya salami waxannan dakarun da suka yi
aikin, tafiyarsu ke da wuya sai boka marmarsi ya bayyana tsulum a
gabansa ya kalleshi fuskarshi a murtuke yace masa.
“Babu shakka ya kai wannan babban sarki ka yi sani cewar ka tafka
babban kuskure sama da irin wand aka aikata akan macen sirri ka yi
sani cewar waxannan dakarun naka daka aika akan su kawo maka
sassan jikin yaron ha’intarka suka yi don yaron daka ce su kasha ba shi
suka kashe ba tuni wannan yaron ya gudu bisa xauki na ‘yar arna daji.
Kuma idan baka tura an nemo maka shi ba duk inda yake ba to ina mai
tabbatar maka wannan karon wannan yaron shi zai kawo qarshen
mulkinka ya kuma kawo qarshen rayuwarka kamar yadda macen sirri ta
faxa maka.
Kuma babu shakka bayan ya kashe ka zai hau kan karagar mulkinka zai
sauya rayuwar mutanen birnin hindu ya kawar da tsoro a zukatan duk
mutanen da suke rayuwa a cikin birnin. Kuma zai kawo qarshen fatara
da talauci daya adabi jama’a duk tsoro da talaka suke masa zai fifitasu
akan sarakai da attajirai da bokaye lallai wannan yaron zai zama
gawurtaccen jarumi kuma xan baiwa da zai gagari kowa zai zama
alaqaqai a nahiyar nan gaba xaya a rasa wanda zai iya cin nasara da
qarfin damtse ko na sihiri akansa” Lokacin daya zo nan wajen sai sarki
mazwan ya taqarqare ya qwala ihu cikin tsananin takaici da baqin ciki
gami da dugunzumar hankali nan take ya tura aka kirawo masa sarkin
yaqinsa sadauki marhat ya bashi umarni akan aje a kamo dakarun da
suka kawo sassan jikin xan mahaukaciya. Kafin ya gama Magana tuni
an gabato da su gaba xayansu su arba’in nan aka yi musu kisan gilla
nan take. Bayan nan sai sarki muzwan ya yi wa sadauki marhat bayanin
yaro salhim da bayanin cewar ‘yar sarki arnan daji ta xauke shi don
39
DAN BAIWA
haka ya xauki dakaru dubu xari biyar ya tafi da su birnin arnan daji ya
buqaci su bashi wannan yaron salhim.
Idan suka qi ba shi ya kashe kowa kuma ya zo da kan yaron salhim ta
ko wanne hali, nan take sadauki marhat ya risina ga sarki muzwan yace
masa.
“An gama ya shugabana” Kawai sai ya juya ya fice daga cikin gidan
sarauta da zumar yaje y haxo wannan runduna da aka ba shi umarnin
haxawa kuma ya yi shirin tafiya.
Sarkin yaqi marhat ya kasance gwarzon mayaqi mai tarwatsa maza
wanda kowa yake shakunsa a gaba xaya mayaqan da suke nahiyar
saboda tsananin qarfin damtsensa da iya yaqinsa da kuma qarfin
sihirinsa na tsafi. Sadauki marhat yana da xa guda xaya a duniya mai
suna shamzan tare da matarsa itama guda xaya tak wato mahaifiyar
shamzan ana kiranta da suna larufa a duniya babu abinda sadauki
marhat yake so sama da wannan xan nasa wanda sun shaqu ainun da
shi ko kaxan baya son ganin abinda zai rabasu dai-dai da rana xaya.
Lokacin daya shiga gidansa cikin sauri ya soma haxa kayan yaqi ganin
haka sai hankalin xansa dana matarsa ya dugunzuma cikin alamun
firgici xansa shamzan ya ruga da gudu izuwa jikinsa ya qanqame
hannayen shi guda biyu ya fashe da kuka. Ko da ganin haka shima sai
hankalinsa ya tashi ya shiga lallashin shmzan yana mai tambayarsa.
“Ya kai xana meye ya vata maka rai haka?” Shima ya dubi mahaifinsa
yace masa.
“Abba ina amfanin wannan shirin na gaggawa haka, shin yaqi zaka fita
ko kuma wani abune ya faru mara daxi?” Koda jin wannan tambayar sai
jikin sarkin yaqi marhat ya yi sanyi ya tsuguna a gaban shamzan ya riqe
kafaxunsa da hannunsa guda biyu ya kalle shi cikin nutsuwa yace masa.
“Ya kai xana kayi sani cewar sarki ne ya bani umarni akan na tafi can
birni arna indiyawan daji na xauko wani yaro wanda idan ba akawo shi
an kashe shi ba to nan gaba zai rushe mulkin sarki ya kuma halakashi
sannan ya haye kan karagar sa kuma ya kawo sauyi a cikin qasar” Sa’ar
da marhat ya zo nan a maganarsa sai zuciyar shamzan ta buga da qarfi
ya kalli mahaifinsa yace masa.
“Wanne yaro ne haka har zai firgita sarki ya xaga masa hankali kamar
haka?” Ya kalli xansa yace masa.
40
DAN BAIWA
“Sunan shi salhim kuma ya kansace xan wata almajira marigayya da ta
rasu” Koda jin wannan maganar sai shamzan ya yanke jiki ya daxi qasa
sumamme cikin ximuwa da gigita mahaifinsa ya ruga da gudu ya samo
ruwa ya yayyafa masa ya farfaxo da qyar. Koda ya buxe idonansa ya
kalli mahaifinsa nan take sai qwalla ta cika masa idanu ya soma
Magana cikin murya kuka.
“Ya kai Abbana kayi sani cewar wannan yaron da kake shirin zuwa ka
kamo shi ka saka akashe shi abokina ne kuma aminina saboda akwai
ranar daya ceci rayuwata daga faxawa rijiyar nan ta bayan kasuwa
muna cikin wasa, muna cikin wasa sai kwatsam mukaga wannan
macijiyar ta cikin rijiya ta fasa kai a daidai wajen da nake zaune ta yo
kaina tana shirin sarana ko da ganin haka sai salhim ya dako tsale daga
wajen da yake ya rungumi macijiyar.
Ai kuwa sai ta kananaxeshi da nufin ta karya sassan jikinsa amma sai
naga ya zaro wani xan siririn itace daga jikinsa ya cakawa macijiyar a
cikin idonta guda xaya take idon ya tsiyaye ta saki salhim ta faxi qasa
tana birgima anan take ta mutu tun daga wannan rana muka zama
abokai ni da shi. Don haka yanzu wanda ya ceci rayuwata shi zaka
kashe?” Koda jin wannan tambayar sai jikin mahaifinsa ya yi sanyi
kuma hankalinsa ya dugunzuma ainun ya sake duban shamzan cikin
alamun tsananin damuwa yace.
“Kayi sani idan banje na kamo salhim na kawo shi gaban sarki ba to
babu shakka rayuwarka data mahaifiyarka tana cikin hatsari a hannun
sarki kuma kafi kowa sanin baqin halinsa don haka sai ka zava da
rayuwarka data salhim wacce kafi qauna?” Hawaye ya soma zuba
shar…shar daga cikin idanunsa yacewa mahaifinsa.
“Idan har rayuwata zata fanshi tasa to na sadaukar da rayuwata akan ta
shi” Kafin shamzan ya gama rufe bakinsa tuni mahaifinsa ya daka masa
tsawa cikin vacin rai yace da shi.
“Baka da hankali ne? wane hali kake tunanin zamu shiga ni da
mahaifiyarka idan muka rasaka bayan mun fitar da ran samunka sannan
muka samu haihuwa. Shekara goma muna son haihuwa bamu samu ba
sai akan ka” Koda jin wannan maganar sai shamzan ya yi wuf zai ruga
da gudu zuwa waje amma sai mahaifinsa ya yi zafin nama ya kama shi
ya soma jansa da qarfin tsiya yana ta faman daddagewa. Tare da kukan
41
DAN BAIWA
baqin ciki a haka ya jefa shi cikin xakinsa ya janyo xakin ya dates da
makuli daga waje, cikin hanzari ya juya ya ci gaba da yin shirinsa ya
xauki takobinsa da garkuwa ya nufi qofar fita daga cikin gidan amma
sai matarshi Larufa tasha gabansa a lokacin da hawaye suke suvucewa
daga cikin idanunta sannan tace masa.
“Ni alfarma guda xaya nake nema a wajenka idan har kayi nasara kama
yaro salhim kada ka bari ai masa kisan gilla lallai ai masa kisa na farat
xaya wanda ba zai sha azaba ba” Ya kalleta ba tare daya bari sun haxa
idanu da ita ba yace mata.
“Ba komai lallai zan yi iyakacin qoqarina naga hakan bai faru ba” Ya
miqa hannu ya dafa kafaxarta yayi gaba abinsa kafin ya fita tace masa.
“Babu matsala” Ya qarasa fita daga cikin gidan ya nufi wajen da barga
dawakansa take bawan da yake kula da barga yayi saurin jawo masa
dokinsa wanda dama tuni ya kammala xaura masa sirdi take sadauki
marhat ya kama dokinsa ya haye sannan ya zabureshi da gudu ya fice
daga cikin gidan.
Marhat yana zuwa qofar fada ya iske dakarun da za su yi masa rakiya
izuwa birnin arnan daji suna bisa dawakai xauke da muggan makamai
sarki muzwan na tsaye a gefe guda ya fuskance su fuskarshi a murtuke
babu sassauci koda sarkin yaqi marhat ya qaraso sai sarki ya kalle shi
yace masa.
“Kayi sani kai da wannan dakarun ba za ku iya yaqar mutanen birnin
arnan daji ba, amma ina son ka isar da saqona ga sarkin su cewar idan
har wannan yaro yana hannunsa to ya bani shi cikin ruwan sanyi idan
kuma ba haka ba zaman lafiyar da yake a tsakanin mu ka isar masa da
wannan saqon a matsayin saqon dana baku kwa iya tafiya na sallame
ku” Koda sarki muzwan ya zo nan a zancensa sai sarkin yaqi marhat ya
nisa bisa girmamawa yace.
“Za muyi komai kamar yadda ka umarta” Nan take sarkin yaqi ya kaxa
linzamin dokinsa ya nufi hanyar fita daga cikin gidan sarauta da gudu
cikin hanzari ragowar dakarun suka rufa masa baya. Shi kuma sarki
muzwan ya bisu da kallo yana yin wani guntun murmushi mugunta. A
daidai lokacin wani hadiminsa mai kula da komai nasa mai qaton ciki
42
DAN BAIWA
kamar an kifa masa qwarya da wani murtukeken gashin bakinsa ya ruga
da gudu zuwa wajen sarki muzwan yana qyalqyala dariya yace masa.
“Ya shugabana ka tura musu dodon maza kuma sa gudu maganin qi
gudu, ina mai tabbatar maka marhat sai ya zo maka da wannan yaron
salhim ko a mace ko a raye saboda baka tava tura shi aikin daya
gagareshi ba” Koda jin haka sai sarki muzwaan ya kwaxawa shambur
mari kuma ya qyalqyale da dariya shima shambur sai shima ya
qyalqyale da dariya yana sosa kuncinsa.
A kullum ta Allah sarki muzwan yakan mari shambur sau ashirin ko sau
goma sha a duk lokaci da ya yi abinda ya bashi dariya ko kuma ya bashi
haushi ko kuma ya burgeshi. Duk da cewar shambur yana shan wannan
marin amma ya nacewa sarki muzwan ko yaushe suna tare saboda kaf
qasar Hindu babu wani mutum da yake samun kuxi a jikin sarki sai
shambur saboda duk mari xaya a matsayin dinare dubu yake.
Shambur ya tara dukiya mai yawa a jikin sarki muzwan har takai kaf
birnin Hindu babu gidan manomi kamarsa amma kasancewar shi da
sarki hakan baya hana shi biyan haraji da kuma raba noman shi ya
baiwa sarki kaso biyu a cikin uku na duk abinda ya noma.
Koda sarki yaga shambur ya soma sosa kuncinsa daga marin daya yi
masa na farko a ranar sai ya qara qyalqyalewa da dariya yace masa.
“Idan ka yi wasa yau ba zaka samu kuxi ma su yawa ba, saboda bana
son kowa ya zo wajena har sai sarkin yaqi ya dawo gareni da
kyakkyawan labari” Koda gama faxin haka sai sarki muzwan ya juya ya
kama hanyar da zata kais a cikin turakarsa. A ko wanne lokaci idan ya
shiga cikin turakar tashi akwai kuyangi da suke binsa suna masa fifita
suna kuma yi masa tausa har sai ya yi bacci amma yau sai ya koresu ya
kuma hana kowa zuwa gareshi kai tsaye ya shiga cikin turakarsa.
Shi kuma shambur ya bi sarki da kallo cikin tsananin takaici bai san
lokacin da zancen shi ya fito fili ba yace.
“Haqqiqa wannan sarki ka cika azzalumi idan banda zallunci ka
gawurta amma qananan yaran ma baka qyale ba” Koda shambur ya
fahimta a waje ya yi Magana sai ya yi saurin marin bakinsa. “Kai xan
banza kar ka jawo mun hukunci kisa a banza” Yana gama faxin haka
sai ya juya da gudu ya nufi varin da gidansa yake a cikin masarautar.
*
43
DAN BAIWA
Al’amarin su yaro salhim kuwa tun daga lokacin da wannan yarinya
‘yar qabilar arna daji ta jashi da gudu sai su ka yi ta gudu babu
sassautawa abinda ya xaurewa salhim kai wani irin gudu suke na ban
al’ajabi. Harma qafaffunsa suna rabuwa da qasa tamkar za su tashi
sama kuma gudun da suke yi abin ya wuce qima saboda suna wuce
komai na dajin kamar wucewar tauraruwa mai wutsiya.
Nan take salhim ya fahimci wannan yarinya tana da qarfin sihiri na tsafi
saboda tun lokacin data kama hannunsa suna wannan gudu ko kaxan
bai ji wata gajiya ba kuma gashi har kusan sa’a biyu suna wannan
gudun. Abu guda ne yake kai kawo a cikin zuciyarsa me yasa wannan
yarinya ta ceci rayuwarsa? Kuma yanzu ina zata kai shi? Amsar da
salhim ya kasa baiwa kanshi kenan.
Sai da suka kuma shafe rabin sa’a suna wannan azababen gudun sannan
suka iso birnin arna daji. Tun daga nesa mamaki ya cika salhim don
ganin gidajen arna daji birjik a wajen wanda aka yisu da baqin dutse na
wuta. Girman wannan gari ya ninka cikin ainahin birnin hindu da kuma
faxi sau goma. Kuma a tsakiyar birnin aka gina fadar sarkinsu da
isowar su qofar shiga birni tare da wannan yarinya sai dakarun da suke
tsare qofar wasu qarfi majiya qarfi kimanin su xari uku suka soma
risinawa suna gaida yarinya.
Su dai waxannan dakarun sun kasance babu komai a jikinsu sai wani
warki kuma sun kasance ma su tarin qwanji da murxewa jiki kuma sun
kasance ko wanne su yana rataye da takobi, kwari da baka da kuma
wuqaqe masu yawa a jikinsu. Koda salhim yaga waxannan masu gadin
sun rusuna suna gaishe da wannan yarinya sai jikinsa ya bashi cewar ta
kasance ‘yar wani babban mutum xaya daga cikin jama’ar birnin.
Babban abinda yake damun salhim babu damar ya yi hira da wannan
yarinya ko kuma ya ji daga gareta amma banda haka yana da tambayoyi
masu yawa da yake da buqatar yi mata amma kuma bai iya yarensu ba
haka itama bata iya nasa ba.
Hakan yasa tun da suka baro birnin Hindu babu wanda yace da xan
uwansa qala sai dai duk lokacin da suka haxa idanu sai dai kawai yaga
ta yi masa murmushi. Da shigar su salhim cikin wannan birnin arna daji
sai ya zama wani xan qauye ya soma kalle-kalle yanda yanayin
rayuwarsu ya burgeshi matuqa, suma matan garin babu wata sutura ta
44
DAN BAIWA
kirki a jikinsu domin qirjinsu da qasansu ne kawai a kare da wani yadi
mai kauri wanda sune suka saqa shi da tasu hikimar ta sarafa auduga.
Su kuma maza da qananun yaran qasansu kawai suke suturcewa da
wani qaramin zani iya cinya babu abinda ya kuma qara burge shi sai
yanda mata su ka yi ado da sarqoqi a wuyansu da kuma qafafunsu
wanda aka yi su da ‘ya ‘yan wuri.
Babban mutum a cikinsu wanda ya zama basarake ko kuma attajiri shi
ne yake yafe da mayafi bayan haka kuma matan cikinsu masu daraja
suna yin ado da sarqa lu’u lu’u ko zinare gaba xaya jama’ar birnin suna
gabatar da sabgoginsu kuma ga kasuwa tana ci ana ta cinikayar
kayayyaki iri-iri na amfanin yau da kullum kayan abinci kala-kala da
kuma kayan ado iri-iri.
Koda shigar su salhim cikin garin tare da wannan yarinya sai kallo ya
koma kansu kowa ya zuba musu idanu aka tsaya cak da gabatar da
komai amma kuma duk wajen da suka ratsa sai salhim yaga ana gaida
wannan yarinya cikin biyayya da girmama kuma sai jama’a suka riqa
binsu a baya xu tamkar jama’ar gari ba su tava ganin mutum mai sutura
irin na salhim ba har zuwa wannan lokacin wannan yarinya tana riqe da
hannun salhim bata sake shi ba. Nan suka durfafi wajen da fadar sarki
take kai tsaye ba tare da shayin komai ba kafin su isa qofar fadar tuni
labari ya riski sarki jamhas cewar Gimbiya zasmin ta shigo gari da wani
irin mutanen hindu. Koda jin haka sai hankalin sarki jamhas ya tashi
ainun ya tashi tsaye cikin sauri ya hau kan wani gini mai tudu inda aka
girke wani tebur xauke da tarkacen kayan tsafi da sihiri na tsubacetsubace cikin sauri ya xauki madubin tsafinsa ya shafe shi. Nan take
yaga hoton komai daya faru a birnin hindu daga lokacin da salhim ya yi
yana yawo yana bara bai samu abinci ba zuwa lokaci daya shiga gidan
sarki muzwan ya saci gurasa guda xaya da kuma umarnin da sarki ya
bayar akan cewar a bishi a saro kanshi amma kuma sai gimbiya zasmin
ta ceci rayuwarsa ta gudo da shi zuwa wannan birnin na su.
Bayan da sarki jamhas ya gama ganin wannan abinda ya faru nan take
ya ji ya kamu da tsananin tausayin yaro salhim abinda ya saka kenan ya
kuma bincike akan yaron salhim yaga irin zallunci da sarki muzwan ya
yi wa iyayensa bayan an kwashe dukiyar su kuma aka qona iyayen
45
DAN BAIWA
nashi a cikin gidansu bisa sa’a da kuma nisan kwana yaro salhim ya
tsira da rayuwarsa.
Koda sarki jamhas yaga wannan abubuwan sai ya ji ya kamu da
tsananin son shi gami da tausayinsa har sai da qwala ta zubo masa ya ci
gaba da bincike a cikin bincikensa nasa gano lallai wannan yaron xan
baiwa ne nan gaba sai ya gawurta ya shafe duk wani tarihi da wani
jarumi ya kafa a yanki kuma zai kafa tarihin da wani bai tava kafawa ba
a duniyar ba. Koda ganin wannan lamari sai hankalin sarki jamhas ya
kuma dugunzuma ya miqe zumbur daga kan turakar shi ya nufi can
wajen da babbar fada take yana isa ya iske fadar ta cika maqil da kusa
gaba xaya jama’ar da suke qasar wanda suna tsaye suna jiran bayani
daga bakinsa. Su kuma salhim da Gimbiya Zasmin suna tsaye a tsakiyar
fadar suna fuskantar wajen da sarki jamhas zai fito zuwa wani lokaci sai
taga ya fito fuskarsa a murtuke ganin haka ya saka zuciyarta bugawa da
qarfi kuma tsoro ya kamata lokaci guda fadar ta yi tsit.
Kwatsam babu zato babu tsamani sai salhim yaga sarki ya kalle shi
cikin murmushi da yaren mutanen Himdu yace masa ‘Marhaba da
salhim xan baiwa ni ne sarki jamhas mahaifin Gimbiya Zasmin yarinya
dake riqe da hannunka” Koda ya zo nan a maganarsa sai ya juya ya
kalli Gimbiya Zasmin cikin mamaki sannan cikin sauri ya cire hannunsa
daga nata ya duqar da kansa qasa gareta cikin alamun girmawa don
yasan a matsayinsa na talaka bai kamata ya haxa hannu da ‘yar sarki ba
bare har hannunsa ya tava nata.
A daidai wannan lokacin ne kuma sarki jamhas ya kalli Gimbiya
zasmin wannan karon fuskarshi ta sauya zuwa vacin rai kamar ba shi
bane ya yi murmushi ba yanzu yace mata.
‘Me yasa kika ceci rayuwar wannan yaron shin kinsa irin bala’in da za
mu shiga a dalilin wannan laifin da kika aikata?” Koda jin wannan
tambayar sai jikin Gimbiya Zasmin ya kuma yin sanyi ta sunkuyar da
kanta qasa ta buxe baki cikin murya mai xauke da sautin tsoro tace.
“Ka gafarce ni ya Abbana ka sani ba komai ne yasa na ceci rayuwarsa
ba face yau kimanin sati biyu kenan ina bincike akan madubin tsafina
naga komai akan tarihinsa kuma taurarin sa’a da xaukaka suna kan
rayuwarsa anan take tausayinsa ya kamani kuma na Aiyana hakan
cewar sai na taimaka masa a rayuwata na ceci rayuwarsa. Sanin kanka
46
DAN BAIWA
ne idan ban ceci rayuwarsa ba to babu shakka macen sirri za ta zo ta
kuvutar da shi wane irin hukunci kake ganin cewar za ta yi mana idan
ya zama ita ta aikata hakan? Kafi kowa sanin ta dalilinta muka samu
‘yanci muka samu xaukaka qasar wajen mu take noma har muka samu
damar da mazajenmu sue iya tsayawa a fagen fama su yi yaqi da
dakarun qasar Himdu wanda a baya basa iya yin haka.
Akan wannan dalilin yasa na shiga cikin birninsu a yau saboda tuni
naga abinda zai faru da shi a bisa satar gurasa don haka ina mai roqonka
alfarma daka tsare rayuwar salhim ta ko wacce hanya saboda nasan
zaka iya yin haka” Sa’ar da Gimbiya Zasmin ta zo nan a maganarta sai
sarki jamhas yaja dogon numfashi gami da ajiyar zuciya yace.
“Yake ‘ya ta haqiqa kin tsokano tsuliyar dodo domin karo da sarki
mazwan haqiqa ba qaramin bala’i bane banda ni da shi xin kar tasa kar
da abinda yanzu kika aikata zai iya zama sanadin rushewar birnin mu da
kuma asara rayukan jama’armu. Fiye da shekara arba’in bay muna
zaman lafiya da juna bamu da wata matsala da masarauta qasar Hindu
bisa waxansu qa’idoji da aka yi su a rubuce daga lokacin yaqi bai kuma
varkewa a tsakaninmu ba amma sai gashi yanzu kike neman kawo
qarshen wannan alaqar daga tsakanin mu ki kawo qarshen kwanciyar
hankali a garemu.
Yanzu dai hanya xaya zanbi na tserar da rayuwar wannan yaron kema
kuma na tsera dake daga shiga halaka bisa wannan laifin da kika aikata
yanzu mafiya guda xaya ce ya zama dole dake da shi ku bar wannan
nahiyar gaba xaya ku koma can birnin sin wajen aminina Boka sambul
inda za ku ci gaba da rayuwa har zuwa matakin matasa inda anan za ku
ci gaba da karva horo na yaqi kuma a tsumaku a cikin kwatarniyar tsafi
idan har baku nesanta daga wannan nahiyar ba babu yanda za a yi na
iya kareku daga farmakin sarki muzwan.
Amma idan kuka yi nisa da wannan nahiyar har zuwa lokacin da sarki
muzwan zai daina farautar ku. Kuma nasan ma zai wahala ya daina
farauta ku tunda Boka marmasi ya yi masa bayani akan shi saboda haka
har abada hankalin sarki muzwan ba zai tava kwanciya ba don haka
dole ne kuyi yanda za ku iya kare kanku a can birnin sin kafin sarki
muzwan ya gano cewar kuma can ya aika da dakaru da za su yi farautar
ku.
47
DAN BAIWA
Kuma yanzu haka baifi sa’a uku ba sarki mazwan ya aiko sarkin
yaqinsa marhat akan umarnin ya zo nan garin da zaqaquran sadaukai
majiya qarfi akan ya zo ya farauce ku saboda haka ku zo yanzu mu je
na shirya ku cikin sauri kubar wannan nahiyar tamu” Ko da kammala
faxar wannan Magana sai sarki jamhas ya nufi wata qofa ta daban cikin
sauri su salhim da gimbiya zasmin suka bishi a baya kai tsaye barga
dawakai ya shiga ya zavo wasu qosasun dawakai guda biyu fari da baqi
ya miqa musu yace musu.
“Maza ku hau waxannan dawakai kubi wannan hanyar kuyi maza ku
fita daga cikin wannan qasar kuma kuyi sani cewar waxannan dawakai
sune za su yi musu jagora har zuwa gidan aminina boka sabir na birnin
sin kuma tafiya ce ta kwanaki xari da sitin amma dawakan na ku za su
gajarceta su yi muku ita a kwanaki arba’in da xaya. Duk wani guzuri da
kuke buqata ko abinci ku samarwa kanku a cikin daji ko kuma duk
garin da kuka ratsa akan hanyarku ta tafiya kuma duk wani mutum daya
kawo muku hari walau mutum ko aljan ko wata muguwar da bar ku
kare kanku” Koda sarki jamhas ya zo nan a maganarsa sai salhim ya
kalleshi cikin alamun tsananin tsoro da fargaba yace masa.
“Ya shugabana nifa ban tava hawa doki ba bare na sarafa shi sannan
kuma ban iya riqe koda takobi ba bare na iya kare kaina daga harin
wani mugun abu, kuma ya yaya zan iya rayuwa a cikin daji har tsawon
kwana arba’in alhalin yauce rana farko dana soma shiga cikin daji a
rayuwata. Nifa babu abinda na iya face bara a cikin kasuwar garinmu
ina neman abinci da zan saka a cikin bakina” Koda salhim ya zo nan a
maganarsa sai sarki jamhas ya dube shi yaxan yi murmushi ya dafa
kafaxarsa yace masa.
“Kada ka damu ya kai jarumin gobe ka yi sani cewar babu wani bala’i
da z aka shiga ba tare da ka kuvuta ba saboda kai xan baiwa ne haka
qaddaraka take” Ko da sarki jamhas y agama Magana sai ya xaga
salhim sannan ya xora shi akan farin doki ya sashi ya riqe linzamin
dokin ko da ganin haka sai gimbiya zasmin ta daka tsale sama ta haye
kan baqin dokin sannan ta yiwa sarki jamhas kallon bankwana a lokacin
da idanunta suka ciko da kwalla tace masa.
“Ya kai abbana nasan cewar zamu xauki lokaci mai tsawo bamu haxu
ba kai ba amma ina roqon a duk lokacin daka samu damar kai mana
48
DAN BAIWA
ziyara ka kawo mana a birnin sin” Tana gama Magana sai ta juya ta
zaburi dokinta da gudu ta nufi hanyar sa sarki jamhas yace su bi ai
kuwa dokin nata yana motsawa sai na salhim ya bishi a baya. Salhim ya
ji kamar zai faxo a lokacin da kuma xan jiri ya xauke shi sakamakon
rashin sabo da hawa dokin amma sai ya qanqame jikinsa da qafafunsa a
jikin dokin zuciyar shi tana bugawa da qarfi sakamakon tsoro daya
kama shi.
Koda gimbiya zasmin ta waigo taga halin da salhim yake ciki sai ta
bushe da dariya tana dariya tace masa “Kada ka damu jarumin gobe da
sannu zaka zama gwanin iya doki wanda zai zama gwarzo mai lashe
gasar sukuwa da doki” Koda jin wannan sai mamaki ya cika zuciyar
salhim yace ta yay azan zama gwarzon da zan lashe sukuwa alhalin
tsoro garen kamar farar kura.
Lokacin da gimbiya zasmin tabi hanyar da sarki jamhas ya nuna musu
su bi suna binta sai suka cika da tsananin mamaki kawai tsintar kansu
su ka yi a cikin wani qungurmin daji wanda basu tava ganin kamarsa ba
wannan dajin ya fita daban da irin yanayi da dukan dazukan dake can
nahiyarsu. Hakan ya nuna mata ta fahimci lallai tsafi gaskiyar mai shi
tafiyar lokaci mai tsawo suka gajarce tafiyar haka dai gimbiya zasmin
da salhim su ka ci gaba da tafiya a cikin dokar daji ba tare da sanin inda
suka nufa ba. Dawakan na su ne suke tafiya akan hanyar ba tare da sun
sani ba.
Sai da suka yini suna tafiya