An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
DAN BAIWA
Yaro ne da bai fi shekara tara ba ya ratso ta tsakiyar
kasuwa a guje yana ihu yana waigen bayansa kai
da ganinsa kasan gudun ceton rai yake yi, amman
ko da mutane suka wanda yake biyo bayansa aka
rasa wanda zai ceceshi.
Wanda ya biyo yaron wani makeken qato ne mai qira
mutanen farko riqe da wata zabgegiyar takobi tsirara, babu komai a
jikin wannan qaton ila bujen wando gami da takalmin fata farxe a
qafarsa a kanshi kuma akwai qaramin zagayayyen rawani a goshinsa
kuma an masa bule da zabibi kana ganin wanan qaton kasan ba indiye
ne.
Badakaren na gidan sarki, haka ya riqa baje hajojin mutane
yana bangaje jama’a yana kuma tattake musu dukiya yana bi takansu
amma sabi sa tsoron masarauta da ake yi an rasa wanda zai yiwa qaton
magana. Haka suka ci gaba da zagaye kasuwa shi yaron yaqi kamuwa
haka kuma qaton bai daina binsa ba su kurxa nan su kurxa can su fita
su shiga wannan saqon haka sukaita yawo a cikin kasuwar suna yiwa
jama’a varna da dukiya da suka kasa.
Shi dai wannan yaron da wannan qaton yake bi ba wani abu
ya aikata ba face satar gurasa a gidan sarkin qasar ta Hindu saboda
yunwa da take damunsa bai samu abinda zai ci ba, yana cikin bara ne
yaga ana rabawa bayi gidan sarki gurasa a hannu su kuma sun kafa
wani dogon layi suna bi xaya bayan xaya ana basu.
Da wannan damar ya bi ya daki idanun masu rabawa ya
kuna kai cikin gidan ya faki idanun mai raba gurasar ya suri guda xaya,
ashe sarki yana zaune a gefe guda yana kallon shigarsa da lokacin daya
xauki gurasar da ake rabawa bayi kuma a qirge take ta bayi xari uku ce
daidai babu daxi babu qari kuma an kawo ne domin a ciyar da bayin da
suka yini suna aiki a gonar sarki.
Kuma an basu da zumar suna gama cin gurasar xai-xai da
aka basu a maida su gonar sarki su ci gaba da aiki, ai kuwa koda sarki
Mazwan yaga wannan yaron ya suri gurasa xaya ya zura da gudu zuwa
wajen gidan sarautar sai ya dakawa wannan qaton tsawo yace masa.
3
DAN BAIWA
“Maza ku bi wannan yaron ku saro min kansa kuma ku
daddatso sassan jikinsa a kawo min zan ciyar da kadojina” Kafin sarki
Mazwan ya gama rufe bakinsa tuni wannan qaton ya zare takobinsa
suka kasa tsere da wannan yaron.
Haka suka ci gaba da gudu yaron yana gudun ceton ransa a
cikin kasuwa da zarar ya tsagaita ya waigo sai yaga qaton ya kusa cin
masa sai ya kuma azama wajen gudu.
Baya iya ganin gabansa duk abinda yake gabansa fatali
yake yi da shi ya qara gaba ana cikin haka sai yaron ya yi tuntuve da
wani kututturen gunki ya faxi qasa kafin ya miqe tsaye ya ci gaba da
gudu tuni qaton ya cin masa ya zo ya kansa ya raba qafafunsa biyu.
Ya kalli yaron cikin tsantsar rashin imani ya tofa masa
yawu a fuska sannan ya xaga takobinsa sama zai datse masa kai
kwatsam babu zato babu tsamani sai narkeken qaton ya ji an daki
qirjinsa saboda qarfin dukan sai daya yi tsale sama ya faxo qasa akan
wata rumfar karat a cikin kasuwar.
Rumfar ta ruguje ya baje akanta a fusace narkeken qaton ya
miqe tsaye zumbur koda ya waiga don ganin wanda ya yi masa wannan
dukan sai mamaki ya turnuqeshi ya kuma sake fusata ainun.
Ba kowa ya gani ba face wata yarinya ‘yar qabilar indiyan
daji tana tsaye ta rataya kwari da bakanta a bayanta kuma ta dunqule
hannayenta alamar a shirye take ta fafata da qaton duk da cewar
shekarun yarinya basu haura takwas ba.gaba xaya mutanen da suke
cikin kasuwar sai wannan al’amarin ya xaure musu kai suka cika da
mamaki kuma suka taru waje xaya suna kallon ikon Allah.
Shi kuma narkeken qaton ya taso mata, da dukanin qarfinsa
ya kawo mata sara akan kafaxarta da zumar ya tsargata gida biyu amma
sai ta gocewa saran cikin baqin zafin nama takobin tasa ta sari iska.
Kafin ya kuma dawowa ya kawo mata wani saran tuni tayi
tsale sama ta dawo ta dake shi da gwiwar hannunta ta baya, take qashin
qafarsa ya karye ya kurma wani ihu ya durqushe a qasa, ai kuwa sai
gaba xaya jama’ar da suke wajen suka bushe da dariya.
Ko da wannan narkeken qaton yaga ana masa dariya kuma
gashi wannan qaramar yarinya ta karya shi sai ya yi wuf ya xauko wani
qaho daga cikin aljihun bujen wandonsa ya soma busawa da qarfi,
4
DAN BAIWA
faruwar hakan ke da wuya sai ga wasu dakaru kimanin irinsa su arba’in
sun shigo cikin kasuwar da gudu suna riqe da goruna da takuba a
hannunsu nan suka hau dukan jama’a suna tattake dukiyoyinsu.
Koda ganin haka sai wannan yarinyar indiyan daji tayi wuf
ta kama hannun wannan yaron varawon gurasa ta jashi da gudu suka
nausa zuwa cikin daji shi kuma yaci gaba da binta ba tare daya san inda
za su ba.
Haka suka ci gaba da gudu a cikin dokar daji yaron yabi ya
gaji kawai yana gudu baya sanin wajen da yake saka qafarsa, ita kuwa
yarinyar indiyan daji sai tsale-tsale take daga nan zuwa can kana gani
kasan tasan sirrin daji, haka ya haqura ya daure yaci gaba da binta duk
ya galabaita yasha wahala ya fiya hayaccinsa.
Shi dai wannan yaron varawon gurasa sunansa Salhim ya
kasance maraya tun yana jariri aka kashe iyayensa a wata rana da sarki
Mazwan ya turo dakaru karva haraji a hannunsu koda dakarun suka zo
suka iske iyayen salhim basu da kuxin da za su iya biyan haraji sai suka
rufe su da duka har da suka sumar da su.
A lokacin salhim yana ta tsala kuka irin na jarirai an ajiye
shi akan harawa doki amma saboda rashin imani na dakarun ko kallonsa
basu yi ba. Da haka ma sai ci gaba da dukan iyayen salhim suka yi suka
shiga cikin gidan suka kwashe duk abinda yake cikin gidan suka kuma
cinawa gidan wuta suka yi tafiyarsu.
Kafin iyayen salhim su farfaxo daga suman da suka yi tuni
wuta ta kama ko ina a cikin gidan babu ta wajen da za su iya bi su fita
har su tsira haka suka yi ta dawurwura a cikin wajen har hayaqin wutar
ya kuma bugar da su suka faxi a wajen wuta ta kama su suka babbake
suka cinye.
Shi kuma salhim wani ikon Allah da yake ciyawar xanya ce
kuma a jiqe take da ruwa sai taqi kamawa da wuta, bayan komai ya lafa
shima yaci gaba da tsala kuka abinsa.
A waje mutane sun taru jingim suna ji suna gani haka gidan
ya cinye qurmus ya zama toka amma ba a samu wanda yaje dan kai
musu xauki ba domin kowa yana gudun kar ya gogawa kansa kashin
kaji shima ya gamu da fushin sarki.
5
DAN BAIWA
Shi kuma jariri salhim tun yana kuka da qarfi murya har
murya shi ta soma dashewa amma an rasa wani mai tausayin da zai
shiga cikin qonanen gidan ya xauko shi har sai da dare ya soma kowa
ya watse sannan wata tsohuwar almajira ta yi ta maza ta faxa cikin
gidan ta xauko jaririn salhim tabi duhun dare ta gudu da shi.
Daga wannan rana almajirar taci gaba da rainonsa tana
bashi madara shanu tunda ita ta tsufa ba zata iya shayar da shi ba, wata
rana haka zata yini tana bara kafin ta samu xan abinda zata sayawa
jariri salhim madarar shanu da zata bashi.
Don haka yasha yini da yinwa tun yana jariri haka zai ta
tsotsar hannu idan yana jin yunwa yana jikinta suna zagaya kasuwa
suna yin bara, wani wajen a basu haquri wani wajen kuma zagi da
baqar magana saboda yanda suma jama’ar Hindu talauci ya yi musu
katutu, ya saba yini da yinwa amma bai tava galabaita ba.
Rayuwar wannan yaron tana baiwa wannan tsohuwar
almajirar mamaki yanda yaron yake da juriya da jarumtaka tun yana
qaramin yaro, hakan yasa take iyakacin qoqarinta don ganin ta samu
abinda zata ciyar da shi.
Wannan mulkin zallunci da tauye haqqi da ake yi a qasar
Hindu yana damun kowa idan ka yi magana kuma a saka dakaru su yi
maka qawanya har sai sun kawo qarshen rayuwarka, don haka jama’a
suna cikin baqin talauci da rashin tabbas na rayuwa.
Wannan dalilin yasa koda ta sha wahala wajen yin bara
bata samu ba bata damuwa saboda tasan halin da jama’a suke ciki suma
suna cikin halin fatara da talauci a qasar.
Haka dai almajira Harsum taci gaba da renon salhim har ya
tasa ya zama xan shekara huxu. Ta shaqu sosai das hi tana masifar son
shi a iya zaman su bai tava kawowa ba ita ce ta haife shi ba. A yanzu ko
bara zata fita tare da salhim suke fita, tun yana qarami ya iya bara kuma
yasan cewa uwarsa bata da wata sana’a data wuce bara amman wajen
da matsala take mutanen qasar Hindu suna fama da tsananin talauci na
mulkin azzalumin sarki Mazwan.
Duk abinci gona da mutum ya noma a qasar to kaso biyu
cikin uku na sarki ne kuma duk da haka ma sai ka biya haraji mai tsoka
duk qarshen wata guda. Kai bama xan gari ba hatta baqo idan hanya ta
6
DAN BAIWA
biyo da shi ya zo giftawa ta kusa da birnin Hindu sai an tsare shi ya
biya harajin sarki idan kuma yaqi biya sai a kama shi da qarfin tsiya a
maida shi bawan sarki kuma idan yana da mace da sauran dukiya duk
sun zama na sarki Mazwan.
Idan kuma ya yi wa sarki wata baqar magana take za a
yanke masa hukunci kisa za a buga hatimi a kashe shi, idan an yi masa
da sauqi shi ne za a yanke masa hukunci xaurin rai da rai a gidan maza.
Don haka a tarihin masarautar Hindu tun da aka kafata, ake
yin sarakuna tsawon dubunan shekaru ba a tava yin azzalumin sarki
kamar mazwan ba.
**
A shekarun baya da suka gaba akwai ranar da sarki
mazwan ya tava fita ran gadi da kansa ya saka aka saka masa hemomi a
bayan gari ya zauna yana shan iska fadawa suna fadanci.
Suna zaune sai ga wani matafiyi da matarsa suna tafiya
cikin nutsuwa da kamala tana haye akan raqumi shi kuma yana qasa
yana janye da ita.
Koda sarki mazwan ya gansu sai ya yi duba zuwa ga
dakarunsa ya basu izinin maza su gabato masa da wannan matafiyin ai
kuwa kafin ya kammala rufe bakinsa harma sun cika aikinsu sun qarasa
gaban matafiyin suka dakatar da shi.
Ya xaga kai yana kallonsu xaya bayan xaya kamar ba zai yi
musu magana ba zuwa can yace musu “Mene ina kan hanyata ta tafiya
za ku dakatar da ni” Dakaru suka kalli juna suka bushe da dariya.
“Mu ‘yan aike ne daga sarki mun zo amsar harajin hanya”
mutumin mai suna sham ya kalli dakarun su duka cikin alamun
jarumtaka yace musu.
“Ku koma ku faxawa sarki mazwan cewar ni sham ba zan
biya haraji ba sai dai ya yi amfani da qarfin dakarunsa ya amsa” Jin
wannan kalamin ya saka dakarun suka zare makamansu suka saka shi a
tsakiya suna kewa ya shi.
“Ahir xinka xan saurayi giggiwa ba taka bace ba a faxar
gaka a gaban mashahurin sarki daka biya haraji ka wuce daya fi maka
tsayawa yin taurin kai” Wani qato yace masa lokacin guda yana
tunkarar shi cikin alamun fushi na zuciya yana qarasawa ya kai masa
7
DAN BAIWA
sara da zumar raba kansa da jikinsa amma ga mamakinsa sai yaga ya yi
zamiya cikin sauri yabar wajen saran ya wuce.
Ya zare takobinsa shima take ya yi wa wannan qaton
tsargen kaxanya ya rabashi biyu ko wane sashe ya faxi qasa jini ya
soma kwaranya qasa. Ganin irin wannan mummunan kisan daya yiwa
wannan qaton sai ya fusata sauran dakarun suka yo xauki kansa su duka
nan fa kasuwar yaqi ta soma ci cinikin rayuka ta soma wanzuwa.
Duk wajen da sham ya saka kai sai dai kaga kawuna suna
tashi sama kamar tsintsaye jini yana famtsama a wajen kafin wani taqin
lokaci ya yi wa dakarun sarki mazwan kaca-kaca, amman hakan bai
tsorata su ba yana kashe su suna qara danowa haka ya riqa xauki babu
daxi da su shi kuma sarki mazwan yana zaune a cikin hemomin da aka
saka mishi yana kallon wannan jarumtaka da wannan sadaukin yake yi.
Ganin yanda yake masa varna jama’a kuma yasan idan ya
barshi zuwa wasu daqiqai babu shakka zai masa varna dakaru hakan
yasa ya juya ya kalli dakaren dake kusa da shi ya miqa masa hannu
alamar ya bashi takobinsa cikin gagawa ya zare takobin ya miqa masa.
Ya tashi tsaye yana juyata a hankali a hannunsa lokaci guda
kuma ya yi wata fitar burtu a guje ya yi xauki akan sadauki sham yana
zuwa ya kai masa sara akaikaice sham baiga zuwan shi ba hakan ya
saka kafin ya Ankara sarki mazwan ya yi masa wani wawan sara a
hannu take wajen ya buxe jini ya soma gudana.
Saran sai daya saka sham ya yi baya can ya faxi qasa sarki
mazwan ya dube shi cikin qasqanci yana ci gaba da juya wuqar da take
hannunsa.
“Bana son xaukar makami a fagen fama don haka yana
nufin rayuka da dama za su salwanta idan na fito da makamina” Sarki
Mazwan ya qarasa magana, da qyar sham ya dafa ya tashi saboda saran
ya galabaita shi.
“Ai tsoro shi yake sawa ‘yan maza suna bin cikin duhu,
daka san kai jarumi ne sai ka bari muyi gaba da gaba da kai” Sarki
mazwan ya shafa goshinsa.
“Kai yaro ne ai kuwa babu shakka yaro bai san wuta ba sai
ya takata don haka kai yanzu ka zama ribatace sai wani ba kai ba” Ya yi
nuni ga dakarunsa.
8
DAN BAIWA
“Maza ku kamo shi cikin sarqa” Sham yanzu bashi da wani
kuzari saboda saran da sarki mazwan ya yi masa irin saran da babu shiri
ya so tirjewa amman bai samu ikon yin haka ba a haka dakarun qasar
Hindu suka kama shi suka saka shi cikin sarqa.
Sarki mazwan ya koma cikin himarshi ya zauna yana kallon
sham da aka kama, wasu suka kama raqumin aka kwantar da shi aka
kamo macen dake kai aka gabatar da ita gaban sarki mazwan ya yi duba
ga fuskarta ya ganta kyakkyawar mace ta gaban kwatance tunda yake
bai tava ganin kyakkyawa kamarta ba.
“Ya sunanki?” Ya tambayeta.
Ta xaga kai cikin nuna tsana da qyamarsa tace “Mene
amfanin sanin sunana bayan babu amfanin da zai yi maka” Sarki
mazwan ya bushe da dariya ya ci gaba da kallonta can ya tashi daga kan
karagarsa ya qarasa har zuwa wajen da take ya dubeta karo na biyu.
“Ya sunanki?” Ya qara tambayarta.
“Wahala da uquba ba zai saka ka ji sunan dab a zai maka
wani amfani ba” Ya dubeta wannan karon babu fara’a akan fuskarsa.
“Idan kin qi faxa min ni sai na baki suna, daga yau sunan ki
Hasma kuma na maida ke saxakata, shi kuma mijinki zan saka a xaure
shi a gidan yari xaurin rai da rai kuma kullum sai an gana masa azaba”
Sham ya xago kai cikin sauri jin abinda sarki mazwan ya faxa take
idanunsa suka kaxa ya dubi matarsa yace mata.
“Kinga yanda Allah ya maida mu ki zama mai tawakali
akan wannan qaddara da Allah ya jarrabemu da ita da ikon Allah waxan
nan ba za su samu nasara akan mu ba” Itama hawaye ya soma
gangarowa daga cikin idanunta tana kallon mijinta sham tace masa.
“Ai na yarda da ikon ubangiji musulunci kuma ina da
yaqinin ba zai bari wannan Azzalumin ya samu nasara akan mu, kai ka
san cewa sun kashe maciji ne basu sare kan ba” Sarki Mazwan ya bushe
da dariya jin abinda ta faxa.
“Kina da matakin da za ki xauka kenan akan wannan abun
dana yanke akan ku?” Ya qarasa magana yana mai xora hannunsa xaya
akan xaya.
“Na yi imani da abin bautar mu, na kuma yi imani yanzu da
za ku zagaye wannan duniyar zan biku har sai na kamo ku sannan zan
9
DAN BAIWA
daina farautar ku” Tayi murmushi tana kallonsa wannan karon cikin
jarumta tayi magana.
“Ka yi sani babu makawa sai na kuvuta daga hannunka, ba
zan dauwama a qarqashin maqasqanci kamar ka ba, koman daren
daxewa sai na dawo”. Sarki mazwan ya bushe da dariya ya dubi
dakarunsa yace.
“Kunji fa wai zata kuvuta daga hannuna, sai na ji maganar
kamar tatsuniya” Dakarun suka bushe da dariya.
“Shi lokaci baya qarya, su kuma mashahuran jarumai ba a
tava kama su a hannu su dauwama, don haka duk daren daxewa sai
mun kawo qarshen zalluncinka” Sarki Mazwan ya dubeta da qananun
idanunsa ya taka a hankali ya matsa zuwa wajen da take ya tsuguna ya
kamo gashin kanta ya cizge sumarta yace mata.
“Ba irin mu ake yiwa barazana ba duk duniya babu daula
mai girma da xaukaka kamar tawa, babu wani sarki daya kai ni qarfin
iko da isa da kuma faxin qasa” Ya saukar da ajiyar zuciya yana kallon
Dakaru.
Kafin ya gama kallon su Hasma tayi wuf ta zare takobin da
take jikin kuben ta a jikin damtsen sarki mazwan ta yi wani ihu na nuna
tsantsar jarumta ta ture shi ya faxi can gefe guda ta kai masa wani sara
cikin gwaninta da zumar tsarge shi gida biyu amma cikin tsananin zafin
nama ua janye jikinsa duk da haka sai sai data yanke masa rabin kunne
jini ya zuba qasa.
Dakarun da suke wajen suka zare makamansu aka tsaya
carko-carko ana kallon juna da su.
Sarki mazwan ya shafi wajen data sare shi ya ji rabin
kunnensa ya fita, nan take ya saki wata qara ta fusatar rai da qunar
zuciya ya dubi dakarunsa ya daka musu tsawa.
Kafin kace wani abu tuni sun yi xauki kanta tayi xauki
itama kansu kaifin takobinta ya haxu da su walqiya da qara mai tsanani
suka cika wajen, kasuwar yaqi ta dawo sabuwa.
Kafin kace wani abu tuni har ta qarar da dakarun da
suke gabanta tayi wuf ta kaiwa sham xauki tana zuwa ta sare
sarqoqin da suke jikinsa ta xora shi akan wani ingaraman doki
10
DAN BAIWA
lokaci guda tayi masa qaimi suka nausa cikin daji a guje kamar
fitar kibiya daga kwari.
Ganin haka ya sa sarki mazwan ya dakawa
dakarunsa tsawa da zumar su bi bayansu su kamo su, nan
mahaya doki suka hau suka rufa musu baya amman sun makara
domin tuni Hasma tayi nisa a cikin daji.
Haka suka yi ta yawon nemanta, amma basu samu
ikon ganinta ba, suka koma cikin tsananin fargaba na tunanin
abinda za su faxawa sarki mazwan saboda sun san halinsa na
baqin zallunci.
A haka suka koma suka same shi yana tsaye a qofar
shiga birnin Hindu fuskarsa tayi baqi kamar an sassaqo daga
itace ransa ya yi matuqar vaci, tunda suke basu tava ganin
fushi irin na yau a fuskar sarki mazwan ba. Hakan ya saka tun
daga nan suka soma fargabar abinda zai faru.
‘Ina fatan kun saro min kawunansu sannan kuka
dawo?” Suka yi shiru suna kallon juna ganin haka yasa ya zare
takobi cikin fushi ya yi kansu da sara da suka sai daya ga babu
ko guda xaya da yake numfashi a cikinsu sannan ya kwarara
wani uban ihu da ilahirin birnin Hindu sai daya amsa.
Ya yi saurin komawa cikin birnin ransa a matuqar
vace, yana shiga cikin gidan sarauta a lokacin Bokan shi ya
bayyana a gare shi sarki mazwan ya tsaya yana kallonsa cikin
tsananin vacin rai.
“Da wane bayani ka zo min?” Bokan ya dubeshi ya
yi shiru yana nazarin fuskar sarki mazwan sannan yace masa.
“Babu dama na gyara maka wannan yankaken
kunnen da aka yanke tunda saran da tsafaffiyar takobinka aka
yi maka, ka kuma san duk abinda aka sara da ita yake
kasancewa” Ya yi shiru yana nazarin fuskar sa sannan ya ci
gaba da magana.
11
DAN BAIWA
“Babu shakka ya zama dole ka saka sarkin yaqi da
mayaqa su bi su a baya zuwa birnin nur yanzu suna daf da
shiga cikin wani qauye da ake kira da Yaxama shi wannan
qauyen yana qarqashin ikon sarki Nur kuma babu shakka idan
suka qarasa birnin nur to sarki lambu na qasar nur zai mallaki
tsafafiyar takobinka idan kuma ya mallaka zai iya cinka da
yaqi ya rusa birnin nan.
Sanin kanka ne tun tsawon zamani akwai gagarumar
gaba a tsakaninku da sarki lambu kuma babu abinda yake
fargaba a game da kai sai wannan tsafafiyar takobin, idan har
ya mallaketa to qasar Hindu tana cikin wani hali na qunci da
tashin hankali kuma mulkinka yana gaf da zuwa qarshe”
Wannan maganar da Boka ya faxa masa ba qaramin xaga masa
hankali ta yi ba.
“Mene mafita?” Boka ya kalli yankaken kunnen
sarki mazwan ya yi murmushi sannan yace masa.
“Rashin sani ya fi dare duhu, shi yasa suka yaqi
wannan macen don lokacin ina cikin halwa ta tsafi kuma babu
ikon na tashi amman dana hana ku yin wannan fafatarwa
saboda tana da wani sirri da babu wanda yake da ikon cin
nasara akanta idan ya yaqeta.
Ita kaxai da kake gani zata iya qarar da dakarun
Birnin Hindu ta kuma rushe duka ganuwar garin. Wannan
matar da kake ganinta Macen sirri ce, wani boka daya shahara
a duniyar bokanci shi ne ya qirqireta, kana tsamanin mutum ce
kamar mu? Amman ba haka bane” Wannan maganar ta boka
ba qaramin xaure kan sarki mazwan ta yi ba.
“Kamar ya ya macen sirri?”
“Wannan macen da kake gani kamar yadda na soma
faxa maka kuma ka ganta kyakkyawar gaske, matace ta wani
mashahurin boka wanda ya hardace kalaman sirikan tsafi guda
12
DAN BAIWA
miliyan xari duk duniya babu boka kamarsa. Yana da mace
guda xaya wacce duk duniya babu abinda yake so sama da ita,
sun xauki tsawon lokaci suna soyayya, kwatsam sai aka wayi
gari matar tashi ta kamu da ciwon ajali har ta mutu, ya wanzu
tsawon lokaci yana kukan baqin ciki, haka ya wanzu tsawon
lokaci ba ci ba sha saboda baqin ciki da begen matarsa kullum
yana zaune a gefen kushewarta yana kallon kushewar cikin
tsananin bege na soyayya da qaunarta.
Haka ya wanzu tsawon lokaka yana zaune a gefen
kabarinta. bayan shekara uku yana cikin wannan halin na zama
a gefen kushewar duk yabi ya lalace ya rame ya qanjame ya
koma kamar ba mutum ba saboda idan ka ganshi sai ya baka
tsoro.
A rana daya cika shekara uku yana wannan zama sai
ya tashi daha wajen kabarin nata a wannan lokacin sulasainin
dare ya soma shiga kai tsaye ya shiga cikin xakin tsafinsa ya
zauna akan buzun tsafi zuwa wani lokaci sannan ya tashi daga
wajen da yake ya soma xauko wasu robobi masu kama da qirgi
yana haxasu waje xaya.
Bayan sa’a shida sai gashi ya harhaxa gavai na xan
adam ya ci gaba da haxa roba sashe zuwa sashe kafin wani
lokaci ya haxa sura matarshi da wannan roba baya ya kammala
ya zuba mata idanu yana kallonta, sak matarshi babu abinda ya
rabasu kamar an tsaga kara sai dai wannan bata motsi.
Kuma ta rob ace aka haxata bata da jini taba da
qashi, haka kuma shima yasan