ba tare da sun haxu da wani abu ba sai daya
zamana rana ta faxi magariba ta shiga sannan ne gimbiya zasmin ta
dubi salhim tace masa.
“Abokina ina ganin ya kamata mu sauka anan mu huta zuwa washe gari
muci gaba da tafiya saboda wannan daren babu hasken farin wata ko
kaxan wanda zai zama fitila da dawakan mu za su ga gabansu har su iya
gane hanya” Lokacin da salhim ya ji wannan shawara da gimbiya
zasmin ta kawo sai ya kalleta cikin tsananin mamaki yace mata “Wai ke
shin ya aka yi kike da basira haka gami da hangen nesa? Kuma bah aka
ba ashe kin iya Magana da yarena amma har muka gudo daga birnin
Hindu baki min Magana ba koma kallona kice dani qala baki yi ba?”
49
DAN BAIWA
koda jin wannan maganar sai ta bushe da dariya sannan ta nutsu tace
masa.
“Ai naqi yin Magana da kai ne saboda naga yanda zaka karveni shin
zaka amince ka bini ba tare da tava gani na ba kuma kasan wacece ni ba?
Idan na kuskura na yi maka Magana da yarenaka zaka saki jiki dani ka
bani amanar kanka amma nib a haka nake so ba nafi son na jaraba
imaninka naga shin z aka iya tara abinda ya zo maka ba tare da shakkar
komai ba” Koda jin wannan maganar sai salhim ya jinjina kai cikin
alamun gamsuwa yace mata.
“Tabbas kin cika ma’abociyar hikima” Gimbiya zasmin ta yi dariya
tana jinjina kai tace masa.
“Kai kuma ka cika xan baiwa da har ka samu damar tsalake duk wata
masifa da take binka hark a kawo zuwa wannan lokacin” Gimbiya
zasmin tana gama faxaar haka sai ta hango wani kogon dutse a gabasu
tace masa.
‘Muje ga wani kogon dutse can gabanmu muje mu yada zango a cikinsa
koma samu nutsuwa zuwa washe gari ko kuma akwai wani qorafi akan
haka?” Salhim ya gyaxa kai yace.
“Yaya zanyi qorafi ni da bansan komaoi ba kuma ban isa na iya kare
kaina da komai ba” Ta yi murmushi ta juya ta ci gaba da tunkara
wannan kogon dutse. Shima ya ci gaba da binta a baya suka tunkari
wannan kogon dutse.
Gaskiyar ma su iya Magana da suka ce rashin sani ya fi dare duhu.
Tabbas inda Gimbiya zasmin sun san bala’in da za su riska a cikin
wannan kogon dutsen da ba su yi gaggawar dosar shi ba bare har su kai
ga sun shiga saboda abinda yake cikin kogon na halaka.
50
DAN BAIWA
L
JARUMI XAN BAIWA 4
okacin da Salhim yaga Gimbiya Zasmin ta sunkuyar
da kanta qasa ta yi shiru bata ce komai ba sai ya
kalleta yace.
“Ranki ya daxe kinyi shiru baki ce komai
ba, shin kema kin amince da duka sharuxan da
jarumi Zaiyan ya gindaya mana?” Koda jin wannan sai Gimbiya
Zasmin ta yi murmushi sannan ta dubi Jarumi Zaiyan tace masa.
“Yakai wannan jarumi mai ban al’ajabi ka yi sani cewar ai
tunda ka ceci rayuwar mu ga hannun wannan mugun aljanin wanda ya
zo ya sace mu. Dole ne mu yadda da kai mu kuma karvi yarjejeniyar
daka zo mana da ita tunda ko shakka bana yi ba za mu iya kare kanmu
daga hannun wannan aljanin ba, ko da yake xan uwana yana da wata
baiwa…” Kafin Gimbiya Zasmin ta kammala faxin wannan maganar
dake bakinta sai Salhim ya yi sauri ya tari numfashinta yace.
“Ni bani da komai dan haka maganar ki ta farko ita ce
haqiqanin gaskiyar” Koda jin wannan sai Jarumi Zaiyan ya yi
murmushi ya dubi Sahim yace.
“Haba abokina ‘yar uwarka tana son sanar da ni cewar kana
da wata baiwa ta musamman ko ba haka bane?” Koda jin wannan
tambayar sai mamaki ya turnuqe Gimbiya Zasmin da Salhim ya kalle
shi yace masa.
“Abokina ya aka yi kasan haka?” Zaiyan ya yi murmushi
yace “Tun farkon shigowar ku cikin dajin nan ina biye da ku a baya
baku sani ba. Ina kallon duk abinda kuke yi ina jin duk abubuwan da
kuke tattaunawa. Inda na fahimci cewar bakwa daga cikin mugaye,
azzaluman mutane wanda hakan shi ya saka na taimake ku. Dana same
ku kuna xaya daga cikin irin waxan nan mutanen da sam ba zan
taimaka muku ba.
Tabbas ko wane bil’adama Allah yana halittarsa da tasa
baiwar. Ba mamaki abubuwan da kake yi na al’ajabi da ban mamaki
sun baiwa ce irin ta sihirin tsafi da iyayenka da kakaninka suka sanya
maka a jikinka tun kana jariri. Koma dai wacce baiwa ce lokaci zai
bambance mana. Yanzu sai ku zo mu ci gaba da tafiya ko?” Koda jin
51
DAN BAIWA
haka sai Gimbiya Zasmin ta dubi Jarumi Zaiyan cikin alamun damuwa
tace masa.
“To yanzu ta yaya tafiyar mu zata zamto xaya da taka alhalin
mu akan dawakai muke kai kuma baka da abin hawa?” Koda jin haka
sai Jarumi Zaiyan ya yi ‘yar guntuwar dariya yace.
“Kada ku damu da yanayin tafiya ta kuyi gaba ni zan riske ku
a yayin da rana ta faxi domin a sannan ne ya kamata mu yada zango”
koda jin haka sai Gimbiya Zasmin ta kalli Salhim ta masa inkiyar su tafi.
Nan take kuwa suka ta shi suka hau dawakan su suka bar Zaiyan a nan
wajen suna waigensa. Kawai sai suka ga ya xauko butar ruwa ya yi
alwala, sannan sai ya fuskanci alqibila ya tayar da sallah koda ganin
haka sai Salhim ya kalli Gimbiya Zasmin cikin damuwa yace mata.
“Wai shin anya kuwa Raiyan mutum ne? ki dubi fa yadda
yake yin wata irin ibada kuma yace mu yi gaba zai same mu a gaba
alhalin shi da qafafunsa yake tafiya mu kuma muna kana abun hawa.
Ke kin sani kafin rana ta faxi mu yada zango sai munyi tafiyar sa’ani
kusan bakwai” Zasmin ta gyaxa kai tace.
“Ni kaina na soma zargin ba mutum bane saboda idan banda
kai dana ga ka kashe muguwar birinyar nan ban tava ganin wanda ya yi
wa aljani kisan galaba sai shi” Sahim ya gyaxa kai yace “Ai dole ne mu
ci gaba da gyada shi sabida mu gano alnahin gaskiyar al’amarinsa shin
kin san abubuwan da za mu lura da su mu gane shi mutum ne ba aljani
ba?” Gimbiya Zasmin tace.
“Kwarai kuwa abu na farko da za mu soma lura dashi shi ne
yanayin cinsa da shansa, shin zai iya rayuwa ta tsawon kwanaki ba ci
bas ha? Aljanu suna rayuwa tsawon kwanaki babu ci ba sha. Suna ma
iya rayuwa tsawon shekara ba ci ba sha. Abu na biyu kuma shima aljani
yana iya rayuwa a cikin akwatin da babu numfashi a cikinta da kuma
qarqashin ruwa. Aljani na iya rikixa ya zama ko wace irin siffa. Batun
shafe dogowar tafiya kuwa a cikin qanqanin lokaci kuwa ba komai
bane a wajen aljani.
Hatta wannan doguwar tafiyar dake gabanmu zuwa birnin sin
wacce a qallah takai ta watanni uku aljani zai iya shafeta a cikin sa’a
xaya. Yanzu abinda za mu yi shi ne mu sakarwa dawakan mu linzami
mu yi gudu daga nan zuwa faxuwar rana, idan ya so sai muga lokacin
52
DAN BAIWA
da Raiyan zai zo ya riskemu”. Koda jin haka sai salhim ya yi murna
yace.
“Tabbas kin zo mana da shawara mai kyau haka za mu yi”
Nan take suka sakarwa dawakansu linzami suka yi ta gudu babu
sassauci haka dai suka yi ta tsala gudu basa tsayawa face sun gaji sosai
ko qishirwa ta kama su ko dawakan su.
Sai da rana ta faxi,gari ya soma duhu sannan su Salhim suka
yanke shawarar su tsaya su yada zango don haka sai suka ruke
dawakansu suka fara tafiya a hankali suna kokarin su tsaya a bakin wata
qorama. Kwatsam sai suka hango wani hayaqi yana tashi a can bayan
wani dutse. Al’amarin dayai matuqar basu mamaki kenan. Salhim ya
dubi Gimbiya Zasmin yace mata.
“Nifa naga wani bil’adama ya shigo cikin wannan dajin ya
kuna wuta yana jin xumi, alhalin wannan dajin hatta fatake tsoronsa
suke ji” Koda taji wannan maganar sai ta xaga kai tace masa.
“Ni kaina abinda ya bani mamaki kenan amman dai mu
qarasa mu gani sai muga ko waye. Idan mutumin kirkine sai mu rabu da
shi lafiya, idan kuma mugune sai mu yaqe shi” Ba tare da gardamar
komai ba salhim ya bi zasmin a baya suka durfafi wannan dutsen inda
suka hango hayaqin.
Lokacin da salhim da zasmin suka iso gaban dutsen suka
zagayo bayansa sai suka qame kamar gumaka tamkar an zare musu
ruhinsu. Ba komai ne ya haddasa hakan ba face tsananin mamaki bisa
ganin wanda ke zaune a wajen ya banqare wata barewa yana gasawa.
Ashe hayaqin da suka hango na wutar da ake gasa barewar ne. ba wani
bane ba ke gasa wannan barewa ba face Jarumi Raiyan. Koda Raiyan ya
xago kai yaga zasmin da salhim sun iso sai ya miqe cikin murna ya
tarbe su yace.
“Har kun iso sannunku da zuwa. Na yi farin ciki da ganinku
yanzu saboda dama lokacin yin ibadata ya yi. Ku zo kuci gaba da gasa
wannan barewar kafin na hattama ibadar tawa sannan na zo mu ci” koda
gama haka sai jarumi Zaiyan ya nufi wajen da wata qorama take ya
tsuguna a gabanta ya fara yin alwala. A sannna ne zasmin da salhim
suka sauko daga kan dawakansu suka xaure su a jikin bishiya sannan
suka zo gaban wutar suka zauna.
53
DAN BAIWA
Tsawon ‘yan daqiqu suna kallon junan su amman xayan su
baice uffan ba. Daga can sai zasmin ta ja numfashi ta ce “Tabbas zaiyan
aljani ne, idan kuwa bai kasance aljani ba to gagarumin matsafi ne. Ta
yaya za’ace bayan mun baro shi a can baya kuma mun falfala wannan
azababben gudun da dawakanmu amman duk da haka ga shi ya riga mu
zuwa nan”. Salhim ya yi murmushin qarfin hali sannan yace.
“Ni kuma abin ya xaure min kai, to amman dai za mu ci gaba
da yin nazari akansa”. Zasmin ta numfasa tace “Abinda nake so da kai
shi ne idan zaiyan zai dawo lokacin da za mu ci wannan naman barewar
ina son ka qurawa idanunsa kallo sabida ka gano yadda akai ya riga mu
zuwa nan tunda kana da baiwar hakan. Koda jin haka sai salhim ya yi
murmushi yace.
“Tabbas kin zo da babbar dabara hakan ya kamata na yi”
haka dai Salhim da zasmin suka ci gaba da gasa naman barewa hart a
gasu sosai, har maiqon jikinta na xiga qasa. A daidai wannan lokacin
jarumi Raiyan y agama shafa addu’a sannan ya taso daga inda ya yi
sallah ya dawo wajen su zasmin ya zauna. Ba tare da vata lokaci ba
Zaiyan ya saka wuqa ya na yanko naman yana ajiyewa a gaban zasmin
da salhim suna ci. Sannan shima ya yanko xan kaxan ya saka a bakinsa.
A wannan lokacin salhim ya qurawa cikin idanun zaiyan idanunsa da
nufin gano abinda ya yi xa zu kawai sai yaji kamar an watsa masa
barkono a cikin idanunsa dan haka bai san lokacin daya yi sauri ya
kauda idanunsa daga cikin nasa ba ya sunkuyar da kansa qasa yana
mutsutsuke idanunsa a lokacin idanunsa suka soma zubar da hawaye.
Sai daya sake jarraba kallon idanun zaiyan a karo na biyu
amman ya kasa domin ji ya yi ma kamar idanun nasa za su doxe ya
daina gani.babu shiri ya sunkuyar da kansa qasa. Har suka gama cin
nama bai sake yarda ya qurawa qyayar idanunsa kallo ba. Abinda ya
kuma xaure musu kai game da shi loma uku kawai ya ci ya yi hamdala
ya daina cin abinci. Sai ya miqe ya nufi wajen da jakar guzurinsa take
ya fito da tantuna guda biyu. Nan take ya soma aikin kafa tantuna, a
cikin qanqanin lokaci ya hattama ya koma wajen da suke yace musu.
“Ga tantuna can guda biyu na kafa muku sai kowa ne a cikin
ku ya shiga cikin xaya ya kwanta” Da jin haka sai mamaki ya kama
54
DAN BAIWA
salhim da zasmin suka dubi junansu sannan zasmin ta dube shi tace
masa.
“Saboda me ka rabamu kace kowa ya shiga tantinsa daban?”
Dajin wannan tambayar sai Jarumi Zaiyan ya gyaxa kai yace.
“A Addinina idan har yara sun kai shekara bakwai a duniya to
lallai ana son a raba musu shimfixa. Ni kuwa ko qyaleni zan yi gadinku
da izinin ubangijina kamar yadda na yi muku alqawari. Kusani cewa ni
ban cika yin bacci ba da dare,domin lokacine da nake gabatar da ibadata.
Koda gama faxin hakan sai Jarumi zaiyan ya koma can gefe xaya ya
shimfixa buzu ya zauna a qasa ya kama yin addu’a yana jan carbi. A
sannan ne salhim da zasmin suka sake duban junansu suka gyaxa kai
Salhim yace.
“Nifa na soma ji a jikina Salhim mutum ne kamar mu duk
abinda yake yi na al’ajabi yana yi ne da taimakon ubangijinsa. Yanzu
ne maganar daya faxa min a baya ta faxo min a rai cewar; ni baiwata
tafi qarfin sihirin tsafi. Tabbas na yadda da haka sabida tsafi da sihirin
tsafi basa haxuwa tunda gashi na kasa qura masa idanu naga gaskiyar
al’amarinsa” Koda Salhim ya zo nan a zancen sa sai Gimbiya Zasmin ta
vata rai ta dubeshi a fusace tace.
“Yanzu kana nufin cewar har kayi imani da addininsa kenan?
Ni har yanzu ban yadda cewar shi mutum bane kuma da sannu zan
tabbatar maka da hakan kai dai kawai ka ci gaba da haquri gami da
zuba idanu”. Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin Gimbiya Zasmin
da Jarumi Xan Baiwa Salhim akan hanyarsu ta zuwa birnin sin domin
tsira da rayuwar su sai gashi sun haxu da wani sabon jarumi wanda ya fi
Salhim Baiwa.
A can birnin Arnan Daji kuwa lokacin da ‘yan majalisar
birnin suka zauna domin su tattauna akan shawarar day a kamata su
yanke akan sarkin yaqi Marnat sai kace nace ya yi yawa. Majalisar ta
rabu gida biyu daidai. Vangare farko sukace su basu yarda da abaiwa
marhat auren Gimbiya Hamrita ba. Kawai a kore shi ya koma garinsu
sabida zaman shi a nan ma zai iya haifar da wani yaqi tsakaninsu da
qasar Hindu kuma dole idan aka yi yaqin ayi asara rayuka da ba a san
adadinsu ba kuma dole ayi asara dukiya mai xumbin yawa. Xaya
55
DAN BAIWA
vangaren kuma sai suka ce su sun yadda a xaura auren Marnat da
Hamrita kuma a karve su hannu biyu shi da sauran ‘yan uwansa tamkar
‘yan gari a kuma koyar da su duk irin al’adarsu da addininsu. A lokacin
da aka ga anyi kunen doki babu vangaren daya yi rinjaye sai aka je aka
sanar da sarki Jamhus abinda ya faru a majalisa.
Lokacin da Sarki Jamhas ya ji wannan batu sai shima ya cika
da mamaki yai shiru yana nazari. Daga baya sai bada umarnin cewar aje
a yi shela ana son ganin kowa a fada. Nan take kuwa masu shela suka
kama yawo a cikin birnin lungu-lungu saqo-saqo suna aikinsu
al’amarin daya baiwa kowa mamaki sabida ba a san dalilin daya saka
sarki ya shirya taro cikin gaggawa ba.
Cikin qanqanin lokaci fada ta cika ta batse, duk inda mutum
ya hanga babu abinda zai gani face kawunan bil’adama. Sai bayan
kamar rabin sa’a da taruwar al’amma sannan aka ga fadawan sarki
jamhas da dattawan garin suna shigowa fadar suna zama.
A can gidan sarauta kuwa tuni sarki jamhas ya saka aka zo da
sarkin yaqi marhat da abokan tafiyarsa suka gurfana a gabansa sannan
ya sake turawa aka kirawo Gimbiya Hamrita. Bayan Hamrita tai so ta
zauna a kusa da sarki, tana hada idanu da Marhat sai ta yi masa
murmushi mai taushi amman kuma idanunta sunyi jawur alamun cewar
tasha kuka ta more. Al’amarin daya dugunzuma zuciyarsa tausayinta ya
malala cikin zuciyarsa ya kuma ji wani sonta ya kuma shiga cikin ransa.
Kawai sai sarki ya yi gyaran murya ya kalli Marhat yace masa.
“Yakai sarkin yaqin qasar Hindu kayi sani cewa yanzu ‘yan
majalisa sun zauna a kanka saboda su yanke hukunci da yafi dacewa
akan ka amman sai duka vangarorin biyu suka yi kunen doki, bisa haka
na saka aka shirya taron gaggawa a nan fada na saka a gayato dattawa
sabida a yanke hukunci na qarshe akan ku sabida ci gaba da zamanku a
cikin birnin nan ba tare da sanin matsayin ku ba ka sani abu ne mai
hatsari ‘yarta Hamrita ta kamu da tsananin sonka kuma kai baka san
cewar jiya kwana tayi tana kuka tana roqona na barta ta aureka. Ka sani
ba zan jefa rayuwar jama’ata a cikin hatsari ba kawai na kyautatawa
‘yarta na samar muku da farin ciki wasu kuma su shiga cikin qunci.
Dan haka yanzu nan zamu fita fada gaba xayan mu.
56
DAN BAIWA
Ni kaina ban san hukuncin da dattawa za su yanke akan
wannan al’amarin ba” Yana gama faxin haka sai Sarki Jamhas ya miqe
tsaye ya nufi hanyar fada yana riqe da hannun Gimbiya Hamrita dakaru
suna take masa baya, inda aka tasa qeyar su sarkin yaqi Marnat a baya
inda Hamrita ta yi ta waigensa domin tana ganin cewa ba zata tava
mallakarsa ba a matsayin abokin rayuwarta.
Lokacin da su sarkin jamhas suka iso fada sai jama’a suka
ruxe da yi masa jinjina har said a yaje ya zauna akan kujerar sannan
fadar tayi tsit aka yi shiru ana sauraro don jin dalilin day a saka sarki ya
kirawo wannan taro. Ba tare da vata lokaci ba kowai sai Jamhas ya
miqe tsaye ya fuskanci jama’a yai gaisuwa sannan yace.
“Yaku jama’ar wannan birnin na mu mai albarka gaba
xayanku kowa yasan abinda ya faru lokacin da muka gabatar da gasar
neman auren ‘yarta Gimbiya Hamrita wanda ya zamana ba kowa bane
ya lashe wannan gasar face baqon mu Sarkin yaqin qasar Hindu wato
sadauki Marhat. Dukan su kunsan abinda ya kawo su birnin mu domin
su cika umarnin azzalumin sarkin su na su kamo wasu yara guda biyu.
Tabbas yanzu sarkinsa yana cikin mugun fushi da mu kuma zai iya
kawo mana tayin yaqi sabida mun ba shi masauki shi da abokan
tafiyarsa. Bisa wannan dalilin ya saka na kira kowa da kowa sabida a
yanke hukunci yanzu take sabida ‘yan majilisu sun kasa. A halin yanzu
na miqa wuqa da nama ga dattawanmu saboda sune suke warware
mana wata matsala data gagaremu tsawon shekaru tun daga kafuwar
wannan birnin namu mai albarka” Gama faxin haka ke da wuya sai
sarki jamhas ya dubi wajen da dattawan suke zaune yace.
“Muna sauraren ku” Nan take Dattawa suka shiga yin qusqus
suna tattauna Magana yadda babu mai jin abinda suke faxa sai su isu. A
wannan lokacin cikin Gimbiya Hamrita dana Sadauki Marnat ya xuri
ruwa, hankalinsu ya dugunzuma ainun suka fara tunanin cewar abu ne
mai wuya dattawa su amince da aurensu.
Sai da Dattawa suka shafe kusan sa’a guda suna wannan
tattaunawa sannan suka gama yanke hukunci, kawai sai babban cikin su
wani mutum tsoho tukuf mai farin gashi ya miqe ya tunkari jama’a yace
“Bisa la’akari da sanin hakkin xan adam da kuma sanin darajar soyayya
da kuma ceto rayuwar waxanda ake zalunta mu Dattawa mun amince
57
DAN BAIWA
Sadauki Marhat ya auri Gimbiya Hamrita” Kafin tsoho ya gama rufe
bakinsa tuni fada ta ruxe da ihu da shewa. Ita kuma Hamrita miqewa ta
yi zumbur daga kan kujera da take kusa da Sarki Jamhas ta ruga da
gudu tsakiyar fada wajen da Sadauki Marhat yake tsaye ta rungume shi
cikin matuqar farin ciki suka soma qyalqyala dariya murna.
Kwatsam sai aka ji Sarki Jamhas ya daka tsawa. Take fadar
tayi tsit, Gimbiya Hamrita ta firgita ta janye jikinta daga cikin na
Marhat a wannan lokacin kuma tsohon nan ya ci gaba da bayani.
“Mun yadda da wannan abun bisa sharaxin dole ne Sadauki
Marhat da abokan shi su yi yaqi da mayaqan mu waxanda babu kamar
su a filin yaqi su kai su qas. Sharaxi na biyu dole ne su yi rantsuwa
cewar za su zauna da mu da gaskiya da amana kuma za su kare qasar
mu kamar yadda za ku kare wacan da kuka baro taku ta haihuwa.
Sharaxi na uku dole ne ku ajiye waccan naku addinin na qasar Hindu
ku amshi na mu. Sharaxi na huxu wanda shi ne na qarshe dole ne
Sadauki Marhat ya iya yaren mu a cikin sati guda kuma dole shi da
yaransa su ajiye na su yaren su riqe na mu” Lokacin da Tsoho ya zo nan
a jawabinsa sai hankalin kowa ya tashi a cikin fadar saboda an san cewa
ba abu ne mai yiwuwa ace su Marhat sun tsallake duka waxan nan
sharuxan.Nan fa aka sake yin tsit a lokacin da jikin kowa ya yi sanyi
tamkar ana zaman makoki. Abokan tafiyar Marhat kuwa durqushewa
qasa suka yi suka dafe kawunan su cikin alamun baqin ciki kamar su
fashe da kuka. Ita kuma Gimbiya Hamrita sake rungume Marhat ta yi ta
fashe da matsananci kuka mai tattare da baqin ciki. Sautin kukan nata
kawai ake ji a fadar yayin da kowa ya yi jigum-jigum. Kawai sai aka ga
Sadauki Marhat ya janye jikinsa daga cikin nata ya dubeta cikin
murmushi a lokacin da ya sanya hannunsa ya share mata hawaye
sannan yace.
“Abar qaunata idan har qaunata a gare ki ta gaskiya ce na
miki alqawarin ni da abokan tafiyata duk za mu tsalake wannan
sharuxxa da aka gindaya mana” Da jin haka sai farin ciki ya lulluve
Gimbiya Hamrita ta sumbaci goshin Marhat tace.
“Zan zuba ido na gani idan soyayyarka a gare ni ta gaske ce
babu algus a cikinta” Dajin haka sai Marhat ya taka ya zo gaban karagar
Sarki Jamhas ya risina a gabanshi sannan yace “Ya shugabana yaushene
58
DAN BAIWA
za mu fafata mu da manya dakarun naku abin dogaronku?” Sarki
Jamhas ya yi murmushi cikin jin izza gami gami da yadda da kai yace
masa.
“Nan da cikar kwanaki bakwai kuma a wannan ranar ne za ku
iya yaren mu kuma ku cika sauran sharuxan da muka saka muku” koda
gama wannan maganar sai sarki jamhas ya miqe tsaye ya yafito
Gimbiya Hamrita ta taho gare shi ya kama hannunta ya jata suka fice
daga cikin fadar. Nan dai fatar ta waste kowa ya kama gabansa.
Lokacin da sadauki Marhat tare da abokan tafiyarsa suka
dawo masaukinsu sai suka zauna sukayi tagumi cikin sanyi jiki gami da
tsananin damuwa tsawon ‘yan daqiqa xayansu bai ce qala ba. Daga can
sai mafi girma da iya yaqi daga cikin dakarun ya dubi Marhat yace “Ya
shugabana ta yaya kake ganin za mu iya haye waxan nan sharuxan da
aka gindaya mana? Na yarda cewar zamu iya karva ad’adunsu da
addininsu amman ta yaya zamu iya samun nasara akan zakwakuran
dakarunsu? Ta kuma yaya zaka iya koyon yaren su a cikin sati xaya?
Kuma mu ina batun iyalin mu da muka baro a can qasar Hindu? Shin
baka tunanin cewar a yanzu haka sarki ya saka an halaka su? ” Koda jin
waxan nan tambayoyyin sai sarkin yaqi ya ja gwauron numfashi ya yi
shiru kamar ba zai ce wani abu ba can ya miqe ya yi tafiya taku uku
yana mai juya musu baya yace.
“Nasan halin sarkinmu bazai kashe iyalinmu ba face ya
kamomu a raye domin ya yi musu kisan gilla a gabansu. Sannan muma
ya yi mana kisan wulaqanci. Ina son ku saka a cikin ranku cewar babu
wani abu da ba zai yuwu ba a wannan duniyar face ba’a jarraba shi ba.
Bisa wannan dalilin nake son mu zage matse muyi qoqari wajen ganin
mun tsallake duk waxan nan sharuxan da Sarki Jamhas ya shimfixa
mana kada ku damu da nawa sharaxin kudai ku yi naku daga yau zamu
soma baiwa kanmu horon yaqi har zuwa cikar kwana ki bakwai da za
mu yi wannan gumurzun. Ku sani akwai sababin hanyoyi danayi tunani
akai wajen tunkara waxan nan zaqaquran mayaqan na birnin nan ina
mai tabbatar muku idan har kuka dage kuka karvi horon da zan baku
tabbas za mu samu nasara akan su dan haka ina son ko wanen ku ya
zauna cikin shirin fara karva horo a yau idan dare ya raba” koda ya zo
59
DAN BAIWA
nan a cikin zancen sa sai shugaban dakarun ya kalli sauran su takwas
xin sannan ya dubi Marhat yace.
“Ya shugabana komai tsanani da irin wahalar da zaka bamu
zamu jure koda kuwa za mu rasa rayukan mu sabida wannan ne kaxai
abinda za mu yi mu ceto iyalinmu daga sarki mazwan kuma mu kwato
‘yancin talakawan qasar tamu daga hannun azzalumin sarki.
Amman ni abinda nake shakka kai ta yaya zaka iya yaren su a
cikin kwana bakwai alhalin yaren nasu yana da wahala? Su kuma gashi
sun iya namu yaren”.
Sa’adda sarkin yaqi marhat ya ji wannan batun sai ya buxe
baki da nufin bashi amsa amma sai ga wata kuyanga ta shigo cikin
masaukin nasu xauke da wani abu a qunshe a cikin mayafi, kuyangar ta
zube qasa a gaban marhat ta kwashi gaisuwa sannan tace.
“Ya kai sarkin yaqin birnin Hindu ina son na yi magana da
kai a sirance” Cikin mamaki marhat ya dubi kuyangar yace.
“Wacece ke kuma wane ya aiko ki zuwa gare ni?” Kuyangar
tace.
“Duk bazan iya baka wannan amsar ba face mun kaxaita”
Kawai sai marhat ya dubi gaba xaya dakarun nasa kawai sai suka miqe
tsaye suka fice daga cikin xakin fitarsu ked a wuya sai kuyangar ta
miqawa marhat wannan abun dake hannunta ta ce,
“Gimbiya Hamrita ce ta aikota ni na kawo maka wannan
saqon,littafi ne wanda babu komai a cikinsa face dukkan kalmomin
yarenmu waxanda aka fassara su cikin yaren ku na Hindu, wannan
littafin na sarki ne kuma a sirrance Gimbiya tasa aka sato mata shi aka
kawo maka domin ka sami damar iya yarenmu a cikin kwanakin nan
bakwai.
Gimbiya tace na gaya maka cewa kada ka kuskura ka bari
wani yaga wannan littafin a hannunka” Koda jin wannan batun sai
Marhat ya dubi kuyangar cikin alamun tsoro yace.
“To yanzu idan sarki ya duba baiga littafin nasa ba fa?”
Kuyangar tayi murmushi tace.
‘Kada ka damu ya shugabana tuni Gimbiya ta xauki
tsatstsauran mataki aka hakan domin tasa Bokanta ya qirqiri wani
littafin irin wannan sak an ajiye shi a inda