nuna namai inda ANNAH take tana sallar asubah. ANNAH na idarwa take tambayar SUHAIL me yake damun. MANAL sosa kai, yayi yace ''dama ba Wani abu bane yake damun ta ba illah ƙaruwar da muka samu MANAL na da ciki'' ya faɗa tara da saurin barin ɗakin saboda kunya dama kuma beyi sallar asubah ba. itama MANAL ji take kamar ƙasa ta tsage ta shige don kunya furar data ke, sha ta ajiye ta koma ta kwanta tana mai jin kunyar ANNAH ita kuwa ANNAH ko a jikinta , se godiya da tayiwa Allah dama tana so taga ƴaƴan SUAHAIL se gashi Allah ya amsa mata.
Gari na waye.wa asibitin ya cika da muta ne hatta dasu LUBABATU da ZAINABA sunxo kowa se nan nan yake da MANAL, se azahar aka sallame su suka dawo gida nan fa aka ɗora daga inda aka tsaya kowa burin sa ya faran tawa MANAL sarki da kansa yazo yayi mata ya jiki kai MANAL taga gata iya gata ko wasshhh, tace se an tambaye ta inane yake mata ciwo ko Akwai abinda ta ke so,
Se dare SUHAIL ya shigo ya same ta Ita da MEENA suna fira gaisawa sukayi da MEENA ta tashi ta basu wuri zama yayi ya kamo hannunta yana kallon idon ta Sannan yace ''ya jikin naki ina fata dai kinci abinci?'' ''eh naci sosai ma kaima kaci ko''? ta faɗa tarada shigewa jikinsa, ''hannu yasa ya ɗaga
ƴar yo loluwar rigar baccin data saka yana shafa cikin ta yace '' in dai mata ta da beby na sunci bani da matsala domin sune farin ciki na'' hannu tasa ta saƙalo wuyansa tace '' indai baka ci abinci ba to muma baxa mu iya ciba kai ɗin katanga ne agare mu taya kake tunanin in baka da wal-wala muma zamuyi" ira Iran wa'inna kalaman suka ringa wa junan su ɗaukar ta yayi suka shige beed room....
Nima dai nace Bara inyi ta kaina domin wannan kalaman soyayya da suke, zayya nowa juna haka kamar ba gobe
MMN HIBBA CE.
RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)
WRITER✍️
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN MMN HIBBA
07073193332
SADAUKARWA
NA
SUDAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA UBAN GIDA NA JAGORA NA A CIKIN DUNIYAR MARUBUTA
ISHAQ NASIR ABDULLAHI (NASSURILLAH)
AL-KAIRIN ALLAH YA ISAR MAKA A DIK INDA KAKE YA KARE GABAN KA DA BAYAN KA YA RABA KA DA SHARRIN MASU SHARRI YA KIYAYE KA DAGA MUGUN JI MUGUN GANI ALLAH YA BAKA ABIN DA KAKE NEMA DUNIYA DA LAHIRA YA RABA KA DA IYAYAN KA LAFIYA.
25 -26
Tin da aka ɗauki amare a motocin da angwaye suka turo domin kai su gidan su, na aure ana cikin tafiya duka motocin da mijin NABILA ya turo suka lalace A hanya gashi kuma babu mutane sosai agurin dan haka yace Bara ya turo wasu motocin a mai da su gida idan yaso ' daga baya sa zo suga gidan hakan kuwa akayi aka kawo wasu motocin aka juya dasu shi kuma ya ɗauki matar sa , awata mota suka tafi seda aka wuce wani ƙungurmin daji sannan akazo gidan shi kaɗai ne agurin babu gida ko ɗaya agurin tunda NABILA take bata taɓa ganin gida me kyan wannan ba kai amma Allah ya kashe ya ba ni irin wannan gida haka se kace wanda aka gina da zinare malam ko ina se walainiya yake ta faɗi hakan cikin ranta, koda suka shiga gidan se taga ashe ɓangare biyu ne ko wanne dana sa kalar fentin wanda yafi tsaruwa suka shiga faɗar dukiyar da aka kashe wa gidan ɓata baki ne kai kace aƙasar waje kake idan ba fitowa kayi ba ba zaka taɓa cewa a Najeriya kake ba, sallah sukayi Sannan ya baje mata nama kala-kala na kaji da na rago da na shanu har da na Raƙumi bayan sun gama yaja ta suka shige ɗaki tun ƙarfe sha biyu na dare ALAJI yake abu ɗaya har seda aka kira sallar asuba sannan ya saurarawa NABILA ta jigata ba kaɗan ba tunda take yawan barikin ta bata taɓa haɗuwa da namiji irin Alhaji daze kwana yana gurzar ta abin mamaki shine tunda tazo gidan sau ɗaya taga yayi Sallah idan tace beyi Sallah ba se yace yayi awaje kafin ya shigo, a haka har aka shafe wata biyu idan aka kai amarya ɗakin miji ƙiba take yi tayi kyau amma banda NABILA Gashi dai zata ci me kyau tasha me kyau ta kwanta ame kyau kai hatta da aikin gidan ba tayi saboda Akwai ƴan aiki agidan amma hakan be sa NABILA ta samu kwanciyar hankali ba saboda jaraba irin ta Alhaji kullum cikin abu ɗaya yake baya taɓa barin ta ta huta wani zubin ma yana gama saduwa da ita idan yaje ya dawo ze kuma komawa ruwa tun abun baya damun ta har ya soma damun ta ga ramar da tayi dik ta koɗe se wasu iyayan ƙasusuwa da sukayi mata sarƙa awuya watan ta biyu agidan tasa mu ciki nan fa abun ya kuma rin caɓe mata gashi ya amshe mata duk wayoyin ta bare ta kirawo wani nata ta gaya mai halinda take ciki, ita ba abokin fira gare ta ba, su, kansu masu aikin gidan basa wani yin doguwar fira da ita, saboda Alhaji yaja musu kunne gashi Allah ya haɗa ta da ciki me laulayi na masifa amma duk da haka ALAJI baya raga mata ka ida ne idan ya fara se asuba kuma yana gama wa ze fice daga gidan bashi ze dawo ba se magrib ta ƙwanja me ta bushe ta. tayi baƙi ta Lalace kamar ƙwaran gwal se uban ciki daya yo mata gaba kamar ba NABILA ba
yau dai NABILA ta shirya tsaf domin zagaye ko ina na gidan sannu a hankali take tafiya har takai ɗaya ɓan garan shiga tayi cikin farlon shi ma dai kamar wancan yake har ma ya fishi tsaruwa zama tayi a ɗaya daga cikin farlon tana hutawa ta kai kusan awa biyu a ɗakin sannan ta tashi zata tafi magan ganun mutane ta juyo ƙasa ƙasa Dama da akwai mutane Acikin gidan nan to amma ai alaji yace min babu kowa aciki mu kaɗai ne ta faɗi hakan cikin ranta tsintar kanta tayi da son shiga ɗakin dan taga suwaye.
Innalillahi wa'inna ilaihi raju'unnn, abinda kunnan ta ya jiye mata ne yasa tayi suman tsaye dama ALAJI ɗan mafiya ne?'' tayiwa kanta tambayar da bata dame bata amsar ta. ''yawwa Gali zuwa yanzu na san cikin matar ka, ya kai wata biyar kuma kasan alƙawarin da aka yiwa dodo idan kayi aure matar ka, ta samu ciki zaka bashi jinin matar da kuma abinda ke cikin ta dan haka lokaci yayi da zaka yi hakan gobe ka kawo mana ita dan DODO yana ƙishiruwar jinin su," buɗar bakin ALAJI se cewa yayi "angama ya. shugaba na ai, dama na gaya maka zan kawo wa DODO Kalar jinin daya ke so shi yasa da naga wannan yarinyar na kuma sa akayi min bincike akan iyayan ta se faɗuwa tazo dai-dai da zama naji labarin suna da san kuɗi se na siye su da kuɗi banza ye wawaye ko bin ciken asalina basu yi ba suka bani auran kai in taƙai ce maka ko sunan basu sani ba, dama ni,ba sonta nake ba na auro tane kawai danna bawa DODO jinin ta Ni kuma na samu dukiya na zarce kowa'' ALAJI ya faɗa cikin ƙwarin guywa da karsashi. Sulalewa NABILA tayi a ƙasa ta ɗora hannu aka zata fasa ihu ta tuna idan tai zasu ji ta dan haka ta toshe bakin ta tana rizgar kuka jin motsin za'a fito yasa tayi saurin barin sashin ta koma nata sashin hankali tashe shi kenan ta mutu ta lalace yanzu bata da wani maceci se Allah gashi babu wanda ya taɓa zuwa inda take, agefe guda kuma ALAJI duk sati seya aika da kayan abinci gidan su NABILA da kuɗaɗe masu tarin yawa Sannan yace NABILA tana gaishe su, in suka samu lokaci zasu zo shi da ita basu samu zama bane saboda suna xuwa ƙasashe yawan cin amae ci, hakan yasa su mommy suka Kuma sakewa da shi se yai kiran su awaya su gaisa busu tambayi NABILA ba a cewar su, me zata musu tunda Allah ya bata miji me kuɗi tana can tana wadaƙa da dukiya suma kuma suna samun rabon su , da haka sha-shan iyayan nata suka sha shance basu ko damu da kiran ta awaya ba, su dai a basu kuɗi kawai, Allah ka tema keni ka fidda ni daga wannan gidan'' cewar NABILA wadda ta miƙa lamurran ta ga Allah, kullum kaga NABILA da unab hijab yanzu sallolin nan biyar basa wuce ta saɓa nin da dase ta share wata da watanni ba tayi ba gashi a kwa nan nan ALAJI ya ƙara matsa mata ta fanni saduwa har yanzu bata faɗa mai ta san ko shi waye ba, Ranar Laraba da misalin karfe Uku na yamma ALAJI ya shigo yasa Meta a zaune ba tarada ya kalle taba yace ''zoki raka ni wancan sashin nawa yau acan nake son kwana kema kina ta ƙorafi baki taɓa shiga cikinsa ba to yau Allah ya nufa seki shirya mu tafi yanzu'' cikin NABILA ne ya bada wani ƙuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu, ƙirjin ta ya shiga duka tara-tara nan da nan jikin ta ya hau rawa kamar ana kaɗa mata gangi hawaye share-share a fuskan '' dan Allah ALAJI kayi min rai kada ka kai ni wajan dodon tsafin ku wallahi ni yanzu kuɗi basa gaba na, na roƙe ka da kabar ni da raina'' ta faɗa cikin shashshekar kuka, "hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh, ALAJI ya bushe da wata wula ƙantacciyar dariya lokaci guda kuma ya maida fuskarsa tamakar ta shanu yace ''ashe ma kin riga da kin san inda zan kai ki , to babu damuwa base nayi miki jagora ba ki wuce muje kawai kuma ki sani kome zaki yi se dai kiyi amma babu fashi sena samu abinda nake so na yiwa dodo alƙawarin bashi ke, da Kuma abinda ke cikin cikin ki, sha-sha kawai, hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh seya kuma fashewa da wata kafirar dariya tunda nake ban taɓa ganin mahaukatan iyaye Irin naki ba, basu san ko ni waye ba suka ɗauke ki, suka bani Saboda kuɗi ya rufe musu ido ki tashi muje ko kuma Ni, na kaiki da kaina nan da sati ɗaya za'a bawa DODO jinin ku, ke da abin da ke cikin ki,'' tashin hankali wanda ba'a samai rana kuka NABILA take tana bashi haƙuri amma ina, wata tsawa da ya daka mata seda abinda ke cikin cikin ta ya juya, da hannu yayi mata nuni da ƙofar bata da zaɓin da yawuce tayi abinda ya Umar ce ta, hankali NABILA be kuma tashi ba seda ta ganta acikin ɗakin matsafa babban ɗaki ne gari guda yara ƙananu da ƴan mata da datti jawa ta gani wasu an musu aski wasu kuma ba'a musu ba sannan kowanne an rubuta mai lamba a jikinsa ƙara ta saka lokacin da idan ta yasauka akan sassan jikin mutanan da aka yanka anyi musu gunduwa gunduwa kuma babu alamar ɗigon jini ko ɗaya agurin kenan an bawa DODO jinin su ya shanye? kenan nima haka za'a bada nawa jinin ta faɗi hakan cikin ranta wasu yara ta gani su biyu daga ganinsu kasan daga makaranta aka ɗakko su saboda yunufom ɗin da yake jikinsu, ''shugaba gata nan na kawo ta Ni, na gama nawa dan yanxu ma haka tafiya zanyi ƙasar Amurika naje na huta ina fatan za'a kulamin da komai'' wanda aka kira da shugaba yace '' karka damu kaje duk inda zaka DODO ze baka kariya adik inda kake'' mai da kallan sa yayi kan NABILA yace ''to NABILA na gode ƙwarai da gaske da irin gudummawar da kika bani wajan ganin na kawowa DODO ke dan haka Allah ya haɗa mu, acan'' daga haka yasa kai ya bar ɗakin hannu ta ɗora a kai ta runtuma îhu tana birgima a ƙasa tun NABILA na kuka har ta dena ta dake kwa nan ta biyu acikin ɗakin a kazo aka ɗauki wata mata shiyar budurwa aka shiga da ita ɗakin da DODON yake dariyar su, suka jiyo alamun dado ya shanye jinin yarinyar kawai se gani sukai an jawo gawarta an warɓar aƙasa wani basa muden mutum yazo da wata wuƙa me mugun kaifi da tsini ya kwakule idon ta da ƙirjin ta da kuma gaban ta sannan ya fita wani ma ya shigo shi da tasa wuƙar har da roba ya cire kan ta da ƙafafunta da kuma hannayan ta shima ya tafi wani ma ya kuma shigowa shima dai kamar sauran da tashi wauƙar ya zauna ya gididdiba sauran sassan jikin ta gaba ɗaya se kace naman kaji yaxu ba a robar ya tafi can kuma suka jiyo wani gur-nani ashe dodan ne yake yin haka dik lokacin da aka ba shi jinin mutum in dai yayi masa to seyayi wannan gurnanin hakan ya nuna yayi farin ciki kuma buƙata zata biya.
*Bara kuma mu wai waya gidan ZAINAB muji ita kuma awana hali take*
ABUJA GARIN GWAMNA
Tunda aka kai ZAINAB gidan bata taɓa jin daɗin zaman gidan ba ashe ƙarya itama saurayin nata ya shirga mata yanada mata har da ƴaƴa zagada zagada kuma matar tashi mugun kishi gare ta dik macan daya aura itace ajali ta gata da bin bokaye ko aure yayi seta gama wahalar dake sannan tasa bokan ta ya miki asiri ki kasa guduwa daga gidan dan haka ya tura su, London wai suje suhuta dan baya son matar tasa tasan yayi aure bugu da ƙari ashe ba ZAINAB kaɗai ya aura ba asabar aka daura mai Aure da wata mai suna KHADIJAH washe gari lahadi aka ɗaura mai da ZAINAB mata biyu a lokaci guda itama waccan ɗin budurwa ce kamar ZAINAB ɗin, a daran da aka kai ta aka fara tar zoma domin kuwa ce mata yayi tsohuwar matar sa ce da ya saka ya dawo da ita KHADIJAH tana ji tana gani ya shirga mata ƙarya itama taci kukan ta ta ƙoshi, ZAINAB kuwa kwana tayi kuka tana ya cuce ta amma da yake namiji ɗan duniya ne seya lallaɓa ta ya samu abinda yake so awurin ta satinsu biyu agidan Uwar gidansya ta dawo ita da ƴaƴan ta nan fa aka shiga ɗauki ba daɗi ita dai KHADIJAH duk abinda suka ce da ita shi take yi shi yasa basa takura mata saɓanin ZAINAB data lashi ta kobin babu macan da zata yiwa biyayya hakan yasa HAULE da yaran ta suka sako ZAINAB a gaba wahalar yau da ban ta gobe da ban kwatsam ZAINAB ta samu ciki HAULE ta ƙra sako ta, a gaba har da cin alawashin seta salwantar da cikin, rayuwa tayiwa ZAINAB zafi gashi ba wata kulawa take samu agurin mijin nata ba raban data ganshi har ta manta watannin sedai ta jiyo Muryar sa, shida matarsa da ƴaƴan sa, zaune take ta rasa abinda yake mata daɗi gashi cikin jikin ta ya dame ta motsi ji tayi an banko ƙofar ɗakin anshigo SUHAIMA ce ta tsaya kanta tace "ZAINAB tashi ki dafa min in domi yanxu ita nake sonci Sannan kiyi sauri karki ɓata min rai kuma karki samin attaruhu da yawa bana so tayi yaji saffa saffa nake so tayi'' shiru ZAINAB tayi ƙwalla na gan garowa daga idon ta Aranta tace ''yanxu wannan ƴar ficiciyar yarinyar ce take sani aiki kuma cikin gadara da izzah. maganar suhaima ce ta katse mata zan can xucin data keyi ta hanyar faɗin ''wai keeeeee ZAINAB ba Magana nake miki ba kikayi banza dani ko kina nufin ba zaki yi abinda nasa ki ba ?" ta faɗa cikin tsawa da ɗaga murya, cikin kuka ZAINAB tace '' dan Allah SUHAIMA kiyi min afuwa wallahi bazan iyayin girki yanxu ba marata ciwo take yi'' ahayeeeeeeeeeeeeeeeeeeee Nana ye to wallahi bari kiji ba ciwan mara ba ko haihuwa zakiyi se kinyi abinda nace'' ''SUHAIMA bazan iya ..'' bata ƙarasa abinda take son faɗa ba SUHAIMA ta wanke fuskarta da wasu lafiyayyun maruka hagu da dama se ganinta da jinta suka ɗauke na wuccin gadi SUHAIMA bata tsaya anan ba ta haye ruwan cikin ta ta ringa kai wa cikin bugu ta ko ina tun ZAINAB na kuka da Neman agaji har ta dena saboda azaba se da SUHAIMA tai mata dukan. fitar hayyaci Sannan ta ɗaga ta tarada barin ɗakin babu wanda ya kuma bi ta kanta bare ya temaka mata SUHAIMA na fita daga ɗakin ta gayawa mahaifiyar ta duk abinda ya faru tace tayi dai-dai gwara da tayi mata haka. Cikin axababban ciwo ZAINAB ta far faɗo daga doguwar suman da tayi cikin ta wanda ya de na motsi ta taɓa taji yana nan a zaton ta babu cikin ajikin ta gaba ɗaya jikin ya kumbura kamar wadda tasha sha kafashe ga jini da yake zuba kamar anbuɗe famfo da kyar ta samu jinin ya tsaya tun daga wannan rana ZAINAB ta shiga taka tsan tsan da dik abinda ta san zesa jikin ta yayi tsami ita kuɗi kawai take so ta samu ta gudu idan ba bata bar gidan ba to sedai a tarar da gwar ta, ga cikin ta Da yayi mata nauyi, ba ko da yaushe yake motsawa ba se yafi kwana da kwanaki be motsa ba ga yinwa da taci ta cinye ta gaba ɗaya ta zama tamkar mahaukaciya ko wanka ba tayi idan ta doso ka kai kace mushe ne. Ita kuwa Khadijah tabi Allah tabi ma aiki tabi HAULE da yaranta se abinda suke so, take yi shi yasa ita bata shan wuya kamar ZAINAB, yau ZAINAB ta tashi da naƙuda ta kai awa ɗaya tana abu ɗaya amma babu sauƙi se gurin Allah da kyar ta rarrafo daga ɗakin ta, ta shiga ɗakin HAULE a bakin ƙofar ɗakin ta dur ƙushe tana kallan su cikin fitar hayyaci tace MUKUTAR ANTY ku temaka min mutuwa zanyi dan Allah kukai ni wajan iyaye na kar na mutu ban gansu ba'' ta faɗa cikin azaba da raɗaɗin naƙuda wannan ne karo na farko da MUKUTAR yaji ze iya tema kawa ZAINAB duk da yana tsoran HAULE amma dole ya ajiye komai agefe ya temaka mata idan ya so daga baya kome ze faru ya faru miƙewa yayi da nufin zuwa inda ZAINAB take adur yaji HAULE ta daka mai wata uwar tsawa ba shiri ya koma ya zauna jikin sa na ɓari , tashi tayi ta ƙarasa inda ZAINAB take tasa hannu ta ɗauke ta da mari ta finciko ta, ta kaiwa cikin ta naushi tasa hannu ta kama gaban rigar ta, ta yaga nan jikin ZAINAB ya bayyana a fili yaran kuwa suka ɗauki shewa suna cewa ''se Mommy wallahi kinyi dai-dai'' cikin bala'i da masifa HAULE tace '' dama na gaya miki duk randa kika kuma shigo min ɗaki sena keta miki mutunci banza ƴar masu son Abin duniya wato ke, kina tina ƙaho kin auri me kuɗi zaki zo ki bararraje ko ai kin ga bararraje wa '' ta ƙarasa faɗa tara da hanka ɗata ta faɗi wata razananniyar ƙara tasaki se kuma ɗif alamar ta suma koma ta mutu se jini daya yanke mata kan kace me jinin ya mamaye gurin da gudu MUKUTAR yayi kanta yana kiran sunan ta amma ina bata ko motsawa be saurari tsawar da HAULE take daka mai ba ya ɗauke ta yasa amota se asibiti.
Suna isa aka ɗora ta akan gadon marasa lafiya Emergency aka nufa da ita ana bata te makon gaggawa Dr sunyi iya yinsu wajan ganin jinin da yake zuba ya tsaya amma abin ya citura dole tasa aka nemi MUKUTAR yasa hannu domin ayi mata oforeshen nan da nan aka shiga da ita ɗakin tiya ta awa ɗaya da rabi, aka kammala tiya tar sedai ɗan bezo da raiba bayan angama komai aka bawa MUKUTAR gawar ɗan domin yaje ya binne ita kuma suka yi mata allurar bacci sedai inta farka suga yana yin jikin nata, MUKUTAR yayi kuka sosai daya ga ɗan da ZAINAB ta haifa se dai bezo da rai ba tunda ake mai haihuwa be taɓa yiwa ɗa soyayyar da yake yiwa ɗan da ZAINAB ta haifa mai ba ZAINAB ta far faɗo likitoci suka yi mata ƴan gwaje gwaje don a tabbatar da ta samu lafiya sedai ana dubawa aka gano ta gamu da lalurar yoyan fitsari wannan dalili yasa ZAINAB ƙara shiga wata damuwar seya zamana tama dena Magana se dai ta kalleka kawai kwanan ta biyar a asibiti aka sallame ta suka dawo gida ta ci gaba da fuskantar ƙalubalen data saba, babu me raga mata ga yoyan fitsari da ya kuma yin gaba idan ta zauna aguri ta tashi kai kace ruwa kofi ɗaya aka zuba agurin Ranar wata Alhamis HAULE da yaran ta suka fita supar makeet don yin siyayya har da KHADIJAH suka tafi ZAINAB kaɗai aka bari ta shiga tunanin ta yanda zata gudu can ta tuna da wata da Bara ɗakin HAULE ta shiga ta hau bincike lokar mudubi ta janyo idonta yayi tozali da kuɗaɗe masu tarin yawa ɗiba tayi ta mai da lokar cikin sauri ta fito daga ɗakin ta koma nata ɗakin Hijab da takalmi tasaka ta fito sauri take kamar zata kifa tayi Sa'a me gadi baya nan tayi wufff ta fice ɗan sahu ta hau tace ya kaita tashar da ake hawa motar Kano** minti goma ya kai su tasha tayi Sa'a motar Kano ta cika saura gurin mutum ɗaya ta shiga me mota yaja suka ɗau hanya se a sannan ZAINAB ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tarada fashewa da kuka me tsuma zuciya ƙarfe shida na yamma suka iso Kano ɗan sahu ta hau ya kawo ta har ƙofar gida su, kuɗi ta bawa me ɗan sahun bata jira ya bata canji ba ta kwasa da gudu tana zuwa ta ringa dukan gettt ɗin gidan da iya ƙarfin ta me gadi ne yazo yaga waye wannan me bugun tashin Hankali yana buɗewa ZAINAB ta faɗo gidan har tana bangaje me gadi da gudu shima RABE me gadi ya rufa mata baya yana faɗin ''jama'a ku temaka mana mahaukaciya ta shigo gidan nan jama'a ku kawo ɗauki wallahi mahaukaciya ce'' Turusss ZAINAB taja ta tsaya lokacin data shiga cikin farlon se kuma ta sulale ƙasa sumammiya dai-dai Lokacin RABE me gadi ya shigo Mommy ce ta sakko daga saman bene cikin shiga ta Alfarma ''wai kai RABE ihun me kake mana ne haka ka san bana son wannan halin naka , idan kayi wasa yanxu xan kore daga gidan nan'' ' kiyi haƙuri hajiya ina zaune naji ana bugun ƙofar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 12