gurfane anan naga tun ɗazu muka gama magana daku ko dai wata tsiyar kuka tafka ban sani ba ?" Cewar SARKI.
JAMAL ne ya ƙiftawa SUHAIL ido, dan kar ya ce komai, "kaga shaƙiyyan yara ina magana kunyi shiru kuna magana da ido to kutashi ku bani guri tunda yau shaƙiyan cin naku ne ya motsa" sarki ya faɗa tara da rarumo maficin da yake gefan sa . da gudu suka miƙe suna dariya gami da cewa. "allah ya huci zuciyar, sarkin sarakuna kabari in tayi tsami zamu gaya ma " " kai ku tafi cann ni kun ishe ni da iya shege dikkan su suka sa dariya,
Suna fita SUHAIL ya dubi JAMAL gami da cewa "me yasa ka hana na gaya mai?" "saboda ba yanxu ne lokacin wannan maganar ba kabari seda daddare semu gaya mai ko kuma xuwa gobe da safe yanxu dai muje in kai ka kaganta danna san ka matsu ka ganta" JAMAL ya faɗa tarada kashe mai ido ɗaya, duka SUHAIL ya kai mai yayi saurin gocewa, mota suka shiga suka kama hanaya da isar su magadi ya buɗe musu. MANAL dake kwance kan kujera two sita tana gem awayn ta sam bata ji tsayuwar motarsu ba sallamar su kurum taji da sauri, ta miƙe gamida cewa Dr. kai... bata ƙarasa abinda take son faɗa ba SUHAIL ya shigo ido suka haɗa tayi saurin sunkuyar da kanta jikin ta ya hau rawa kasa tsayuwa tayi da gudu tayi cikin ɗakin ta da ta saka keey tarada jingina bayanta a jikin ƙofar har yanxu ƙamshin tiraransa yana manne a hancin ta ga ƙirjin ta da yake dukan uku uku dama haka yake da kyau kamar shi yayi kansa wannan ai yama fita kyau kuma bama ajinta bane yafi ƙarfin ta gashi ɗan gidan sarauta" se da kallo ɗayan data yi mai taji ta kamu da son shi wannan shi ake kira da kallo ɗaya takk,
Can farlo kuwa JAMAL se ha tintsire da dariya se yi yake shi kuwa SUHAIL yanda kasa an dasa gunki yama kasa cewa komai seda JAMAL yayi me isarsa yace. "gaskiya SUHAIL ka firgita ƴar mutane gashi kasa ta shige ɗaki harda garƙama mukulli seya tsuguna ya ɗauki wayar MANAL data yarda aƙasa ya miƙawa SUHAIL karɓa yayi ya doshi ƙofar ɗakin nata cikin muryarsa me sanyi da daɗin sauraro yace. "MANAAL buɗe ƙofar ko nine baki son gani?" Ahankali ta buɗe ƙofar har yanxu kanta aƙasa yake miƙa mata wayar yayi yace. "wato guduna kikeoyi amma bakya gudun JAMAL saboda ni kama ki zanyi ko cinye ki zanyi ko?" girgixa mai kai tayi alamar a'ah "baki da baki ne ?" cikin shagwaɓa tace. "ina da shi" "to amma bakiyin magana" kayi haƙuri dan Allah zanyi" ta faɗa har yanxu kanta aƙasa. "wai me yasa ba zaki kalle ni ba se rowar fuskar kike min dama bani kika yiwa kalliyan ba?" SUHAIL ya kuma jefo mata wata tambayar baki ta turo gaba kamar zatayi kuka tace. "eh ba kai na yiwa ba" ta faɗa tara da ƙara kawar da kanta shi kuwa SUHAIL gaba ɗaya ya shagala da kallan ta yanda tayi maganr yaji wani abu ya soke shi be san sanda ya kai hannin sa kan fuskar ta ba ya ɗago da haɓar ta suka ƙurawa juna ido gaba ɗayan su suka ji wani abu ya fixge su,, MANAL tai saurin rumtse idon ta tana jin wani irin yana yi da bata taɓa jiba. shima a nasa ɓangaran SUHAIL hakan take dakyar ya saita kansa yace. "se kin gaya min wa kike xumɓuro wa wannan bakin ya faɗa yana jan leɓantea da yasha manleɓe.
turo shi ta kuma yi kana tace. "ni bada kai nake ba" "to dawa kike sekin gaya min" "dan Allah kayi haƙuri wallahi bazan kuma ba" ta faɗa cikin shgwaɓaɓɓiyar murya. sakin ta yayi yace. "na haƙura idan kika sake se na hukunta bakin" Hannun ta ya kama suka zauna kan gadon har yanxu Hannun ta na cikin nasa yace. "kee biki iya yiwa mijin ki sannu da xuwa ba? ?" ko irin girkin nan da mata suke wa mazajen su ni biki yi min ba se shagwaɓa da turo baki" "to ai ban san yau xaka dawo ba da nayi maka idan kana so se nayi maka yanxu" "me ze hana in dai baxan takura ki ba " girgixa masa kai tayi tace. babu wani takura" okay muje ki yimin yanxu danna dena cin abin cin kowa sena mata ta" ɗagowa tayi ta kalle sa gira ya ɗaga mata yace. "eh mana koba mata ta bace.?" "itace" ta faɗa tarada rufe fuskar ta data fin Hannun ta . lallai Allah ya kashe ya bani mace mai hankali da nutsuwa ga kunya uwa uba ilimi ga addini ibada ya faɗa cikin ransa
tare suka fito farlon inda suka iske JAMAL zaune hararar wasa ya jefa musu yace. "Sannu romiyo wato shine kuka bar ni anan kamar wani shara ko?" Dariya SUAHAIL yayi kana yace. "haba kai kuwa ai kayi mana uzuri koh daga fitawar mu, ka hau mu da faɗa" harara ya kuma ɓalla mai yace. "Ai gobe ma rana ce sena rakoka zaokamin wannan dogon waulakan cin" nan sukai ta fafatawa....
MANAL kuwa tuni ta shige kicin ta ɗora girki sun ann zaune se ta shin ƙamshi suka ji kallon kallo suka ringa yi Ita kuwa MANAL cikin mintuna ƙalilan ta gama haɗa komai ta zuba a kula sannan ta dakko filet da cokula ta ɗora akai ta kai ta ajiye musu ta juya zata tafi ta jiyo Muryar SUHAIL yana cewa "muza mu zubawa kan mu ?" ya faɗa yana mai kafe ta da maya tattun idanun sa wanda suke ƙara hargitsa ta dawo wa tayi ta zuba musu sannan ta koma daki bayan tafiyar MANAL su SUHAIL suka baje se kwasar girki suke JAMAL kuwa saboda santi harda cire hula ya ajiye a gefe yana kwasar abinci. "A gaskiya SUHAIL ka more mata dan ba kowace maca ce ta iya girki kamar haka" dariya SUAHAIL yayi yace. "Kai dai bari ai wallahi a yanzu ina ji a raina ko me martaba be yarda da aure na da ita ba to akwai matsala " "Allah ko''. ''ƙwarai ma kuwa'' SUHAIL ya bashi amsa. bayan sun gama kwasar girkin SUAHAIL ya shiga ɗakin dan ya faɗa mata zasu tafi kwance yasa Meta ta ƙurawa sili ido, yayi sallama yafi a irga amma bata ji ba seda ya bubbuga gadon sannan tayi firgigit ta tashi ido suka haɗa tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da ƴan tsun ta " mu dai zamu wuce se kuma zuwa gobe in sha Allahu idan muka dawo tara zamu tafi dake" '' To Allah ya kaimu Allah ya tsare hanya" MANAL ta faɗa har lokacin kanta na ƙasa. Murmushin jin daɗi yayi sannan ya fita daga ɗakin da kallo MANAL ta bishi tana kuma mamakin wai yau ita ce matar SUAHAIL mutumin da kowa yake son gani amma babu dama se gashi ita ta gan shi kuma a matsayin mijin ta yake ikon Allah se dai kallo.
WASHE GARI......
SUAHAIL da JAMAL ne zaune gaban me martaba , bayan sun gama kora mai dik abin da ya faru kama daga mafarkin da SUHAIL yake yi har zuwa lokacin da suka ɗaura auran MANAL da SUHAIL ba tara da sanin ALAJI BUKAR. shi kanshi me martaba seda ya tausaya wa MANAL, "ƙwarai da gaske na san ALAJI SA'AD ME DALAH abokina na ne kuma mutumin kirki ne sosai bashi da abokin faɗa" cewar me martaba, "yanzu ina ita yarinyar take?" sosa kai SUHAIL yayi gami da cewa "tana gida na a nan na ajiye ta mun yake sharar s sanar da kai idan ka amince se ta dawo nan" "haba ku kuwa yaza ku ajiye ta ita kaɗai acikin wannan gidan lallai lallai gobe kuje ku ɗakkota ku kawo ta nan dan akula da ita'' gaba-daya suka haɗa baki gurin faɗin godiya muke ranka ya dade'' sannan suka fice daga fadar.......
MMN HIBBA
RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)
WRITER
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN (MMN HIBBA)
07073193332
Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.
littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi Shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba.
GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.
NA GODE🤝
21/22
SHIN WANE NE SUHAI?.
SHAMSIDDEN MUHAMMAD shi ne cikakken sunan sa ɗa ne ga Sarkin masarautar zaki, masa rauta ce babba wacce ta jima tana mulki tun iyaye da kakanni MUHAMMAD SHAMSIDDEN shine sunan mahaifin SUHAIL kuma sarki a masarautar zaki ya gaji sarauta agurin mahaifin sa Sarki MUHAMMAD sarki ne me adalci ga al'ummar sa baya zalinci ko kaɗan kuma baya bari ayi zalunci hakan yasa kowa yake son shi ba zaka taɓa ji ance ga aibun sa ba se dia alkairin sa, SARKI MUHAMMAD matansa biyu HAWAU'U wato uwar gida (Kilishi) se HAJARA wacca suke kirada gwaggwo ƴaƴan sa guda biyar ZAINAB ita ce babba se LUBABATU me bi mata se kuma SUAHAIL shine na Uku Kuma shi kaɗai ne namiji hakan yasa duk wani burin sarki ya ɗora shi akan SUHAIL se ƙanwarsa BILKISU se kuma ƴar autar su AMINA wacce ake kira da MEENA, ZAINAB BILKISU LUBABATU anyi musu aure harma da ƴaƴan su, suma ƴaƴan sarakuna suka aura, yanzu sai MEENA kawai tarage wacca daga ita ba'a kuma haihuwa ba. "JAMAL kuma ɗane ga UMAR ABDULLAHI wato ɗan gidan seneto kuma aminin sarki ne hakan yasa JAMAL da SUHAIL suka shaƙu da juna duk da wani zubin SUHAIL yanda miskilan ci.
WANNAN KENAN BARA KUMA MUDORA DAGA INDA MUKA TSAYA.
Da safe SUHAIL da JAMAL suka shirya tsaf suka yiwa gidan da MANAL take dirar mikiya lokacin MANAL ta koma baccin safe bugun ƙofar su ne ya tashe ta addu'a tayi sannan ta miƙe taje ta buɗe musu sam ta manta da rigar bacci ce ajikin ta kunya ce ta kama ta JAMAL kuwa yayi saurin ɗauke kansa shi kuwa SUHAIL wani baƙin ciki ne ya tokare mai xuciya ya za ayi ta fito haka bacin ta san tare suke da JAMAL dik da JAMAL abokin sa ne na ƙwarai kuma ya san koshi waye amma ai be kamata ta fito haka ba dan takai ci be san sanda ya daka mata tsawa, ba MANAL ba hatta da JAMAL se da ya tsorata, nan da nan idon sa ya kaɗa yayi jajir kamar garwashi se huci yake, ita kuwa MANAL saboda firgici, da tsoro ɗaki ta shige jikin ta na rawa tinda take ba'a taɓa yi mata irin wannan tsawar mesa ƴan hanjin mutum su girgiza, rakuɓe wa tayi a ƙuryar gadon jikin ta se rawa yake kamar maxari gani take SUHAIL dukan ta zeyi.
"haba SUHAIL ya zaka daka mata wannan tsawar? se kace Aradu a haka kake cewa kana sonta to wallahi in dai haka zaka ringa mata zaka sha wahala ka sani cewa su mata abin a lallaɓa ne idan kace zaka mata horan tsawa da hantara tofa zata fanɗare maka idan wata ranka mata tayi shiru wata ran rama wa zata yi kaga kenan zance ya ɓaci mata da kake gani ƙaramar ƙwaƙwalwa gare su tunanin su gajere ne in suka shiga damuwa tofa ba duka bane suke yin tawakkali abinda xuciyar su, ta raya musu shi suke yi”
Ajiyar zuciya SAUHAIL ya sauke kana yace
”kai ma kasan abinda tayi bata kyauta ba inda wani ne ya shigo shike nan ya gama ƙare mata kallo,” dariyar da take cin JAMAL ce tafito fili yayi me isarsa ya gano kishi ne yake ɗawai niya dashi dan haka yace. “kaga yanxu dai ka tashi kaje ka rarrashe ta dan wallahi ta firgita idan yaso daga baya seka kafa mata duk dokar daka gadama JAMAL ya faɗa yana kuma ƙunshe dariya tsaki SUHAIL yayi gami da miƙewa yace “wallahi seta raina kanta dan bazan lamunci haka ba.” “to wai kai an gaya maka haka take wannan ma akasi ne kuma daga bacci ta tashi ya kamata kayi mata uxuri malam me mata ” ya faɗa tarada sakin dariyar ƙeta,
can ƙuryar gado ya hango ta ta cure guri guda, jin an turo ƙofar yasa MANAL ta kuma tsurewa nan da nan hawaye ya wanke fuskar ta ta rufe idanin ta ji tayi an danƙo hannun ta se gata atsaye kamar gunki saboda tsoro saura kaɗan MANAL ta saki fitsari a wando se ma kyar kyata take, kamar me zazzaɓi. “ YAYA dan allah dan annabi kayi haƙuri wallahi ba zan sake ba na tuba wallahi.”
murtike fuska SUHAIL ya kuma yi gami da ƙara matse hannun ta ƙara ta saki tara da yin tsalle ta kuma rintse idanin ta “wallahi na tuba YAYA na tuba bazan kuma ba dan Allah kayi haƙuri ka sakar min hannu karka ɓalla ni,” ta faɗa tana me marai raice murya ga hawaye jage-jage a fuskar ta. sassauta mata ruƙon yayi yana kallan ta kana yace “naji na haƙura wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe muddin kika kuma fitowa a haka sena miki wanda yafi wannan ban yarda ki cire hijabi a wani gurin ba musamman idan da maza agurin kinji ko biki jiba?” “na ji ” maza tashi ki shirya mu tafi gida me martaba yace in zo in tafi dake” tashi tayi da nufin shiga ban ɗaki domin yin wanka se kuma ta tuna yana cikin ɗakin tsayawa tayi tana kallan sa , “ya dai kika tsaya kina kallo na ko wankan ma sena nuna miki yanda zakiyi?” girgiza mai kai tayi alamar a'h. “to meye?.” cikin turo baki tace " ka tashi ka tafi zanyi wanka” kallan ta yayi ya kawar da kansa gefe seda ya gama shan ƙamshin sa, sannan ya fita, da ido ta bishi afili tace "ohhh ni MANAL Allah ya haɗa ni da ƙarfan ƙafa,” wanka tayo tana fitowa, mai kawai ta shafa ta saka doguwarriga tayi rolin da mayafin rigar filet ɗin takalmi ta saka ta fito farlo har ƙasa ta tsuguna ta gaida JAMAL ya amsa cikin sakin fuska shi kuwa hakimin wani kallo yake jifan ta da shi kawai se gani su kai ya tashi ya shiga cikin ɗakin jim kaɗan se gashi ya fito hannin sa riƙe da hijab ruwan ƙasa miƙa mata yayi “oya jeki cire wannan matacin kokwan da kika saka
bata ce komai ba ta amsa ta shiga ɗakin ta cire mayafin ta saka hijab ɗin daya bata tana fitowa taga b har sun fita amota ta same su dan haka ta buɗe baya ta shiga JAMAL yaja motar suka ɗauki hanya cikin ikon allah suka isa, yau dai ga MANAL acikin masarautar ZAKI gab da zasu shiga fada suka ci karo da MEENA ta fito kallonsu ta tsaya yi idon ta ne ya sauka akan MANAL wacca take gefan JAMAL nan da nan annurin fuskar ta ya ɗauke yanda kasan taga mala ikan mutuwa. kasa jure abinda ke xuciyar ta tayi tace
" YAYA JAMAL wace ce wannan kar dai kace min budurwar ka, ce.” kafin JAMAL yayi magana SUAHAIL yayi caraf yace “eh budurwar sa, ce kuma da ita akasa musu rana ƴar uwar sa ce auren zumunci za'a yi musu” dafe kirji MEENA tayi gami da maimaita kalmar “ auren zumunci” ɗumi taji akan kuncin ta tasa hannu ta taɓa taga hawaye ne juyawa tayi ta cigaba da tafiya hawaye na kuma ɓulɓulowa daga kwarin Idan ta. “MEENA! MEENA!! MEENA!!! JAMAL ya shiga ƙwalla mata, kira amma bata saurare shi ba. se da ya haɗa da gudu sannan ya samu ya sha gaban ta. "Tsaya kiji MEENA, wallahi ba budurwa ta bace matar sa ce ya faɗa ne dan ya haɗa mu rigima plsss ki yarda da ni kin san bazan miki ƙarya ba" "MATAR SA" MEENA ta mai maita dai-dai lokacin su SUHAIL suka ƙarasa inda suke, JAMAL se hararar shi yake, Shi kuwa SUHAIL nunawa yayi kamar be san me yake yi ba ɓan garan mahaifiyar SUHAIL suka yi inda suka iske kafata nin mutan gidan hatta da memarta ba yana gurin guri suka samu suka zauna bayan an gama gaisawa memar taba yayi gyaran, murya ya fara magana kamar haka. "to da farko dai zan gaya muku wata muhimmiyar magana gameda wannan yarinyar yaefaɗa tarada nuna MANAL wadda tunda suka shigo mutanan dake cikin ɗakin suke bin ta da kallon mamaki ya cika su kowa da abinda yake saƙawa a ransa jira kawai suke sarki ya gama magana su tambayi wace ce ita.
ME MARTABA yaci gaba da cewa "ina fatan xaku bani haɗin kai kamar kullum se dai wannan maganar ina so ku ɗauke ta a matsayin ƙaddara da kuma ikon Allah kuyi imani da Allah ku sani kuma buku wuce Allah ya jarabe ku da kowaca irin ƙaddara ba dan haka kuyi haƙuri. ” sai ya nim fasa sannan yaci gaba da cewa "wannan yarinya da kuke gani ƴar aboki na ce kuma kun san shi wato ALAJI SA'AD ME DALA "ehh ƙwarai ranka ya daɗe mun san shi " Allahu akbar ai ranka ya daɗe naji ance ya jima da rasuwa" cewar uwar gida KILISHI. "ƙwarai da gaske ya rasu kuma wannan yarinya ita kaɗai Allah ya bashi se kuma ɗan uwansa nan sarki ya kwashe dik abinda ya faru bayan rasuwar mahaifin MANAL har xuwa lokacin da ya nemi ya ɗaura mata aure da wani ƙarshe auran ya juya kan SUHAIL. ya ɗora da cewa “dan haka yanxu wannan yarinyar MATAR SUHAIL ce se dai idan ita ce tace bata son shi wannan kam batzan mata dole ba"
Gaba ɗaya ɗakin babu wanda beyi kuka ba saboda tausayin MANAL a gaskiya ba kowa bane ze iya jure wannan uƙubar ba "Allah ya temaki sarki mu bamu da ta cewa dik hukun cin da ka yanke yayi mudai muna musu fatan alakari gaba ɗayan su su kuma wa'in can Allah ya shirye su yasa su gane gaskiya" cewar gwaggo wato babar MEENA. gaba ɗaya suma sauran suka amsa mai da haka "masha Allah alhamdullih Allah ya kara haɗa kanku koda bayan raina ku zamo tsin tsya ɗaya ma ɗauri ɗaya dan haka nan da ƴan kwana ki za'ayi taron bikin a bata sadakin ta tunda dama an ɗaura aure sadaki ne be bayar ba sannan bana so kowa yaji wannan maganar abar ta iya nan ni, zanji da komai Allah ya shige mana gaba" gaba ɗaya suka amsa da Amin. "To MANAL ga baban nin ki, nan duk abinda kike so ki tambaye su nan gidan ku ne ki yi komai kanki tsaye India be saɓa faɗar Allah ba duk Kuma wanda kika ga ze miki ba dai-dai ba to kizo ki gaya min in ɗau mataki kinji ko"? ''insha Allahu ranka ya daɗe nima kuma zaka same ni ame yi muku biyayya har ƙarshen rayuwa ta Na gode sosai Allah ya ƙara maka lafiya'' suka amsa da ameen ameen. "Ni dai ranka ya daɗe ina so a bani ita danna kula da ita'' cewar Gwaggo. Murmushi, me martaba yayi yace. ''an baki ita uwar yara na san zaki kula da ita dan bani da shakku akan ki,''. ''godiya nake ranka ya daɗe Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana'' ''Shike nan nima na samu abokiyar fira kuma a ɗaki na zamu ringa kwana'' cewar MEENA tana dariyar farin ciki, Harara SUHAIL ya banka mata dan haka tayi tsit ne san me martaba yana kallon sa ba seji yayi yace ''sannu baba na da wannan kallon da kake mata me tayi maka? dan kawai tace zasu kwana guri guda shi ne kake hararar ta wato kai me mata ko'' da sauri SUHAIL da JAMAL suka fice daga farlon suna dariya. To rayuwar MANAL a cikin gidan sarauta ta zama tamkar ƴar gold kowa ririta ta yake babu wanda ya taɓa yi mata koda kallon banza duk inda take so zata shiga ko tayi abinda take so duk inda kaga MEENA to zaka ga MANAL sun zama tamkar ƴan biyu.
yau da daddare bayan sallar isha MANAL ce kwance akan gado tana danna waya kiran SUHAIL ya shigo ta ɗauka tara da karawa akunnan ta tayi sallama amsawa yayi ciki ciki ya ɗora da cewa ''wato MANAL dana ce kizo shine kika ƙi zuwa se kace zan cinye ki ko, shikenan Nagode'' ɗifff ya katse kiran da kallo tabi wayar ita ma ta san bata kyauta ba jikin ta ne yayi sanyi ace tun daga yanzu ta fara ɓatawa mijin ta rai amma ai ba lefinta bane gwaggo ce ta hana ta zuwa sakkowa tayi daga kan gadon ta ɗaura hijab akan rigar baccin da take jikin ta, ta ƙofar baya tabi dan kar Gwaggo ta ganta tana zuwa masu gadin shi suka bata hanya ta shiga bata same shi a farlo ba dan haka ta wuce cikin ɗakin kwance ta same shi ya ƙurawa silin ido yana kallo kamar me naza rin wani abu ''YAYA gani'' ko kallan inda take be yi ba bare tasa ran xe bata amsa. Zama tayi abakin gadon ta kamo hannin sa ta haɗa da nata tace ''plsss YAYA SUHAIL dan Allah kayi haƙuri wallahi Gwaggo ce ta hanani zuwa yanzu ma bata san na fito ba.
Zaga yawa tayi inda ya maida fuskar sa ta marai rai ce tana bashi haƙuri ''yanzu kina
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 12