Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 12
ji yake kamar ya taɓa shiga gidan “INNALILLAHI WA,INNA ILAIHI RAJUN” abin da SUHAIL yake ta nana tawa ke nan afili yace. “wannan ai gidan ALAJI SA'AD ME DALAH ne wanda a shekarun baya ƴan fashi suka shiga suka kashe shi shida matar sa” cikin mamaki JAMAL yace... “ kar dai kace min wanda she karun baya memartaba ya wakilta mu muzo gidan sa saboda walimar da yayiwa ƴar sa lokacin data kammala karatun ta?” “ ƙwarai ma kuwa JAMAL ita ce to amma abin tambayar shine waye yake ruƙon ƴar tasa? kuma su waye a cikin gidan?” “ ba wannan zamu tsaya yi ba gidan ya kamata mu shiga koma me nene zamu gani” cewar JAMAL ƙarasawa suka yi tara da ƙwanƙwasa ƙofar gidan me gadi ne ya buɗe ƙaramar ƙofar suka shiga bayan sun gaisa JAMAL yayi saurin amshe zan can dan baya so SUHAIL yayo musu katoɓara yana so yaji komai abakin me gadin . “dan Allah malam me gidan nan alaji sa,ad muke nema” “Ayya ai ALAJI ya jima da rasuwa hala dai kuba ƴan garin nan bane ko?” “eh gaskiya mu ba mazauna nan bane” me gadi “shi yasa baka samu labarin kisan da aka yiwa alaji ba” JAMAL yace. “wallahi ban sani ba to ina matar sa da ƴar sa suke?” "kayya ai shida matar tasa aka kashe yanzu ƴar sa ce kaɗai ta rage” “ Ko zamu iya sanin inda take kuma su waye acikin gidan?" shiru me gadi yayi yana Nazarin abinda ze ce can ya nisa kana yace “ ai tin ran sadakar uku ƙanin sa ALAJI BUKAR ya dawo gidan da zama ƴar sa kuma tana nan gidan wato MANAL bata jima da fita bara ba yanxu zakuga ta dawo ” “BARAH!!.” SUHAIL da JAMAL suka haɗa baki gurin faɗa “ƙwarai ma kuwa ta tafi bara saboda ƙanin mahaifin nata basa nan shi da iyalan sa sun tafi yawon mema kuke cewa ko yawon zaga gari na dai manta.” INNALILKAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UNA abinda SUHAIL da JAMAL suke ta nana tawa MANAL ce, ta turo ƙaramar ƙofar get ɗin ta shigo har lokacin tana shan lemon ta wanda babu komai aciki se fata se gwaguya take sam bata lura dasu ba ganin tana neman shigewa ciki yasa JAMAL ya ƙwalla, mata kira “MANAL” da sauri ta wai go kasa ƙarasawa tayi sema kafe shi da ido da tayi can kuma tace. “laaaaaaaaaah Dr,. JAMAL kai ne dama zaka kuma zuwa in da nake ina JAMSY ban kuma ganin ta ba” gabaɗaya ta jeromai tambayoyin a lokaci guda kuma cikin murna, “waca tambaya zan amsa miki?" dariya tayi tace. “wallahi dik na ruɗe ne ” se yanxu SAUHAIL ya magantu dace wa. “ ki cire wannan ɓawon lemon daga bakin ki, ” se yanxu ta lura da SUHAIL cire wa tayi cikin jin kunya ta kuma sunkuyar da kanta ƙasa. “ daga ina kike ?” cewar JAMAL in ina tasomayi “uhum uhum naje barane kuma ban samo komai ba se wannan lemon da kuka gani” da suri SUHAIL ya juyar da fuskar sa sabida wasu hawaye da suka taho mai ace yarinya ƴar masu kuɗi wadda batasan wani abu waishi talauciba ita ce take yin bara kai duniya ba matabbata bace.... “me yasa kika fita bara bacin na san da mutane agidan kuma da abinci” JAMAL ya kuma jefo mata wata tambayar. ƙwallace ta silalo daga idon ta tace. ai basa nan sunyi tafiya amma sun kusa dawowa” ta faɗa yayin da ƙwallar data maƙale akwarin idon ta ta samu damar gan garowa. iska me zafi , SUHAIL ya furzar yace. “ka gani ko JAMAL na faɗama nina san ganin ta da nake yi a mafarki ba'a banza ba dan Allah ka duba kaga wannan tanƙameman gidan ace ita kaɗai zata kwana acikin sa dan haka yanzu zamu tafi da ita gida ba zata sake kwana a cikin gidan nan ba ” “A'AH SUHAIL hakan bame yuwa ba ne gwara mu barta anan nina san yanda zamu muɓullowa lamarin dan haka kabar komai a guna ” Seya juya inda MANAL take tsaye ta tsura musu ido cike da tsoro dan gani take kamar cutar zasu yi “kin ga MANAL ki kwantar da hankalinki baxa mu cutar dake ba hasalima ceton ki zamu yi kishiga ciki xamuje mu dawo kin ji ” kai ta ɗaga mai alamar to fita suka yi daga gidan suka shiga motar su SUHAIL ya kalli JAMAL yace. “ina zamu?” “kasuwa zamuje muyi mata siyayyar kaya dana abinci danna lura akwai yinwa atare da ita in yaso gobe se mu dawo kafin nan ta dawo hayyacin ta ” “ eh kuma fa haka ne” cewar SUHAIL. tin daga burosh kilin sabulun wanki dana wanka kayan kwalliya takalmi kayan sawa hijab dogayan riguna pants shimi brxy kai kaya kawai suke jida kamar za'a haɗa lefe shi kuwa SUHAIL komai ya gani ɗauka yake har seda JAMAL yace ya isa ɓan garan kayan abinci suka nufa komai da ake buƙata na girki seda suka siya mata sannan suka se mata da faffe gurin biyan kuɗi suka je suka biya akasa musu amota sannan suka dawo gidan mamaki ne ya kashe MANAL kai ba ita ba hatta dame gadi se da yayi mamaki gainin tulin kayan da suka shigo dasu ɗakinta suka kai suka dire mata tarada gaya mata gove zasu dawo zokuga kukan farinciki gurin MANAL se godiya take musu SUHAIL kuwa se kallon ta yake ji yake kamar ya tafi da ita ya raba ta da wannan wahalalliyar rayuwar amma bara ya jira yaga wana mataki JAMAL xe ɗauka shima megadi ba,a barshi abaya ba seda suka danƙa mai kuɗi masu yawa suka ce yasa musu ido akan MANAL kada ya kuma bari taje ko ina. sannan suka kama hanyar gida..... Cikin dare SUHAIL ya kasa bacci fuskar MANAL kawai yake gani koya rufe idon sa ita yake gani yanda yaga rana haka yaga dare gari na wayewa yayi wanka yaje ya gaida memartaba ya gaida mahaifiyar shi da sauran matan baban shi. ko karin kumallo be tsaya be yi ba ya kama hanyar gidan su JAMAL. “a'ah lale marhabin yau kai ne agidan namu SUHAIL lallai yau za'ayi ruwa da ƙanƙara” cewar wata dattijuwar maga wacca ba-zata wuce shekara hamsin ba. sosa ƙeya SUAHIL yayi yace. “ina kwana” “ MOMY lpy lau ja'iri dole ka sunkuyar da kai dik yanda akai akwai abin da ya kawo ka danna san ruwa baya tsami banza har da zaka dako wannan uban sammakon ka taho seka shiga shima ɗayan mashirir cin ɗan uwan naka yana ciki be ma tashi daga bacci ba”. “to MOMY na barki lafiya” sim sim ya shige ciki yana shiga ɗakin ya ganshi akwance bashi da niyyar tashi duka ya ɗala mai, agigice JAMAL ya tashi har yana bigewa da bango dariya SUHAIL yasa har da riƙe ciki shima JAMAL ya daddage ya ɗala mai dindu tsut SUHAIL ya dena dariyar sabida yaji zafin dukan “ashe babu daɗi ni kayi min ” gabaki ɗayan su sukasa dariya. “kaga malam katashi Ka shirya Mu tafi in yaso ko ahanya ne seka karya danna matsu inji yaya MANAL ta kwana” harara JAMAL ya ɓalla mai yace. “saboda wata MANAL se naƙi karyawa agida na tafi hanya ina cin abinci to bara kaji babu inda zani se na karya kuma anutse Idan zaka jira kajira” tsaki SUHAIL yayi tarada faɗawa kan gadon, shi kuma JAMAL ya shige banɗaki wanka yayi ya shirya sannan suka nufi babban farlon gidan karyawa sukayi sannan suka kama hanya. “kace akwai ta inda zaka ɓullowa lamarin yarinyar nan ta yanda zamu kuɓutar da ita cikin sauƙi" SUHAIL ya faɗa lokacin daya karya kwana.” "eh ƙwarai haka ne a gani na ba shigar sauri zamu yiwa waɗan nan mutanen ba danna lura wannan ALAJI BUKARR ɗin ba ƙaramin mugu bane don haka cikin hikima da bara zamu bi komai zamu sa me gadin gidan yarin ga yi mana si ai din dik abinda yake faruwa da zaran anxo gaɓar daya dace mu tema keta semu te maka mata ammafa shima ba bayyana kan mu zamu yi ba se dai mu tura wasu idan suka gan mu tarada ita tofa zata kuma shiga wani halin Ko suyi mata wani abun kaga kenan lamari ya ɓaci" cike da gamsuwa SUHAIL yace. “haka ne dik abinda ka faɗa yayi Allah yasa mu dace” gaba ɗaya suka amsa da amin. daidai lokacin JAMAL ya cinna hancin motar cikin gidansu MANAL bayan sun gaisa dame gadi sukace yayo musu magana da MANAL.... tin da ta doso su SUHAIL ya saki baki yana kallan ta har seda JAMAL ya xungure sa sannan ya ankare sanye take cikin hijab ruwan ƙasa yayi mata kyau tsakanin jiya da yau ta canza ta fara dawo wa MANAL ɗin asali har ƙasa ta tsuguna ta gaida su suka amsa tace “su Shigo ciki binta suka yi har xuwa ɗakin ta ruwan da suka seyo mata ta kawo musu suka sha gefe ta koma tana wasa da yatsun hannin ta shiru babu wanda yace komai. JAMAL ne yayi gyran murya gamida cewa... “MANAL” ɗagowa tayi ta kalleshi yaci gaba dacewa “sunana JAMILU UMAR ABDULLAHI ɗan gidana seneto UMAR ABDULLAHI amma amfi sani na da JAMAL. wannan abokin nawa sunan shi SHAMSIDDIN ɗa ne ga sarkin masarautar *ZAKI* ana ce mai SUHAIL shine wanda ake sa ran ze hau milki nan ba da jimawa ba kinji daga inda muke dan haka kema munaso musan labarinki.” gefan hijab ɗin ta tasa ta share ƙwallar data xubo mata nan ta shiga basu labarin ratuwar ta tin daga farko har ƙarahe ba itaba su kansu seda suka xubar da hawaye musamman SUHAIL wai dama da gaske ana irin wannan ratuwar ace ɗan uwan mahaifinka ya dinga axabtar dakai har da yi maka mummunan fata ke duniya ina zaki damu rarrashin ta suka yi sannan sukai mata sallama tara da yi mata alƙawarin zasu dinga zuwa suna ganin ta tin daga wannan rana sesu SUHAIL sun xo tarada yo mata siyayyaya nan da nan MANAL ta murmure hasken ta ya dawo kyawun ta ya kuma fitowa tayi ƙiba fatar nan tayi luwai kamar ta Jarirai gwanin sha'awa ta samu kayan more rayuwa uwa uba kwanciyar hankali babu kyara babu tsan gwama bare marin manca hanya. MMN HIBBA RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE 15-16 FILIN SAUKAR JIRAGE NA MALAM AMINU KANO. A hankali jirgin ya sauka ƙasa tara da sakin wata lafiyayyar iska me ratsa zuciya, sannu a hankali fasinjoji ciki suka soma fitowa ɗaya bayan ɗaya canna hango ALAJI BIKAR da iyalan sa sun yi kyau fatar nan see sheƙi take su NABILA da ZAINAB sun koma tamkar ƴan india dan kyau musamman NABILA fatar nan tayi luwai luwai kamar ba ƴar hausawa ba idan ba magana tayi ba zaka taɓa cewa ta san wani abu wai shi hausa DIREBA ne yazo ya ɗauke su dam dam dam gaban MANAL ya yanke ya faɗi lokacin data jiyo maganar su a tazane ta juya ta kalli ɗakin ta wanda yake shaƙe da kayan abincin da su SUHAIL suka kawo mata jiya innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai take ambato hijab ɗin ta ta saka ta fito harabar gidan dan gudin kar ace bata zo tare su ba tin da ta fito suke bin ta da kallo DADY da yake waya kasa ci-gaba da yin wayar yayi ya saki baki galala yana kallonta ita kuwa MANAL tsugunawa tayi har ƙasa tace. “DADY sannun ku da dawo wa ya hanya” babu wanda ya iya tanka mata se na mujiya da suka zuba mata NABILA kasa ɓoye abin da ke ranta tayi tace. “ke muna fuka ƴar iska ƴar tasha mu xaki yiwa daɗin baki gidan ubanwa kika samu kuɗin da har kika ɗinka sutura masu tsada irin wannan se ta juya gurin DADY wai dady baka gani ne baka kayan da suke jikin ta ba? ka duba da kyau komu da muke da gata bamu taɓa sa irin wannan tsadaddun kayan ba dama na faɗa muku in dai taga bama nan se ta kawo kwarton ta gidan nan kuma gashi idan ba maza take biba uban wa ze siya mata kaya masu tsada kamar haka” “kin faɗi gaskiya NABILA don haka DADY muna so ka ɗauki mummunan mataki akan ta ko dai ka kore ta ko kasan yanda zaka yi da ita na gaji da ganin wannan shegiyar yarinyar me kama da aljanu” ceawr ZAINAB. “kuma dai kwa faɗa ƴaƴan nan dana bashi shawarar yanda zeyi da ita ai ƙiyawa yayi gashi nan tana kawo mana ƴan iska cikin gida." cewar MOMY ta faɗa a fusace. DADY kuwa cewa yayi. “komai yazo ƙarshe insha Allahu za'a yita ta ƙare ba dai maza take biba to zan aura mata wanda ya dace da ita kuma kyauta zan bayar da ita ko in ce sadaka” daga haka DADY ya shige ciki suma suka mara mai baya suka bar MANAL tsaye jikin ta dik ya mutu, yanxu ƙiyayyar da suke mata har ta kai a bayar da ita sadaka?. kururuwar, da NABILA take yi ne ya dawo da ita daga duniyar tina nin data lula a ƙofar ɗakin ta, ta gansu NABILA na cikin ɗakin tana fir fito da kayan dasu SUHAIL suka kawo mata se da ta fito da komai hatta da kayan sawa seda NABILA tayi musu filla filla. “magana ta ƙare kuna gani har da kayan abinci hummm ƴar gata wato ruwan roba ma take sha gaskiya ne kin samu sake to wallahi ba zaki kuma amfani da su ba mu zamu ɗauka” gaba ɗaya NABILA ta kwashe kayan bata bar mata ko tsinke ba se kayan jikin ta ɗakin ta ta kai kayan na abinci kuma ta kai su kicin tofa rayuwar MANAL ta kuma koma ruwa tinda suka dawo bata samu zama aiki kawai take kanta gama wannan ance tayi wannan nan da nan ta koma gidan jiya. yau da daddare DADY yasa aka kira mai MANAL gyaran murya yayi yace. “to ƙaramar karuwa tin da kin nuna auare kike so zanyi miki aure zan sa a nemo min faƙiri matsiyaci matalauci wanda bashi da cin yau bare na gobe na aura masa keee, kije can ki ƙawata da iskancin ki zan sa me gadi ya nemo min koma waye dik tsufan sa koda sadaki ko babu haka zan bashi ke tin da baki da galibu” kuka ne ya ƙwace wa MANAL me tsuma zuciya yi take kamar ran ta ze fita dariya su NABILA suka sa gamida tafawa ZAINAB tace. “gaskiya DADY kayi abinda ya dace dama auaran take so magana ta ƙare seta tafi Allah ya raka taki gonaaaaaa.NABILA ta amshe da cewa “ni kam DADY wata alfarma nake so kamin” “faɗi dik abin da kike so ni kuma zan miki shi” “ dama ba wani abu bane face ina so ayi auran cikin satin nan bana so aja lokaci sannan kasa afara yi maka bin ciken wanda ya dace da ita” “an gama ƴar lele ai ko yau kika ce a ɗaura auran yau za'a ɗaura shi” dikkan su suka sa dariya ”kukan MANAL ya kuma tsanan ta yi take kamar zata shiɗe, tsawa DADY, ya daka mata yace. “tashi ki bani guri ƴar iska kawai kukan ubanki kikeyi” Murmushi mugunta NABILA ta yi kana tace “ƙyale ta DADY wai ita muna fuka." Washegari da safe Dady ya samu me gadi ya faɗa mai abin da yake so kan cewa ya nemo mai mutumin da yasan matalauci ne bashi da cinyau bare na gobe. “to Alhaji insha Allahu Zan nemo maka Amma ranka ya daɗe idan an nemo mutumin me zaka yi mai Idan wani aikin ne nima zan iya” "ba aiki bane ba Malam rabe ina so in yiwa MANAL aure ne shi yasa kaji nace ka nemo min matsiya ci faƙiri irin ta sabida ta da cewa da shi ” shiru mai gadi yayi can kuma yace. “kuma fa ALAJI kayi gaskiya dan wallahi auran yafi da cewa da ita ina gaya ma yarinyar nan bata jin magana kaga yanda take kawo ƙartai cikin gidan nan da nayi mata magana seta nemi zagi na shi yasa naja baki na na zuge kuma insha Allahu zan kawo maka irin mutumin da kake so koma wanda ya fishi talauci” “ ai kuwa Malam rabe da nayi maka kayuta me tsoka” baki Rabe ya washe “An gama ranka ya daɗe " ƙofa ya buɗe mai bayan fitar alaji BUKAR me gadi ya koma ɗakin sa gamida turo ƙofa wayar sa ya ɗakko wacca tasha ɗaurin ƙirji da kyauro number JAMAL daya bashi yace idan yaga wata matsala data shafi MANAL yayi gaggawar sanar dashi, “hello ranka ya daɗe malam Rabe ne me gadi ne na gidan su MANAL” daga ɗaya ɓan garan JAMAL yace.“ okay ya kake ya MANAL ɗin tana lafiya dai ko?” cikin rawar baki RABE me gadi yace. “eh tana lafiya se dai akwai abin da yake faruwa wato yanxun nan ALAJI BUKAR ya same ni da wata magana wai na samo mai mutumin da bashi da cin yau bare na gobe nan ya kwashe dik yanda suka yi da ALHAJI BUKAR ya faɗa mai ya ƙara da cewa “ ya bani nan da kwana biyu in nemo mai mutumin shi yasa nace bara na gaya maka .” “to ranka ya daɗe an gama se naji ka, daga haka ya kashe wayar. Afili yace. “ ƙarshan ku yazo mugaye azzalumai marasa imani.” MASARAUTAR ZAKI SUHAIL ne, zaune gaban memartaba gyaran murya yayi yace. “SUHAIL jibi in Allah ya kai mu kan tura Ka London gurin MUHAMMAD zaku tattauna kan yanda za'ayi game da harkar kasuwanci daga nan kuma zaka wuce Amerika ka amso min sako gurin aminina LAWAN” cikin girmamawa SAUHAIL yace “ an gama RANKA YADAƊE na barka lafiya .” ɗakin sa ya koma wayar sa ya ɗauka ya kira JAMAL kan yazo suje gidans u MANAL saboda jibi ze bar garin “okay Shi kenan seka zo ɗin” mintina ƙalilan JAMAL ya ƙaraso. “yawa ka ƙara so ai ba seka zauna ba muje kawai” kallansa JAMAL yayi ya kawar da kansa kana yace. “so kake mu janyo mata wata masifar to masu gidan sun dawo dan haka ka saurara min da wannan soki burutsun naka" cikin tashin hankali SAUHAIL ya ce “ kana nufin s ta koma wannan wahalalliyar rayuwar?” ƙwarai ma kuwa amma na samu hanyar da zamu te maka mata nan JAMAL ya kwashe yanda su kayi da RABE me gadi ya gaya mai sosai hankalin SUHAIL ya tashi ,. ganin haka yasa JAMAL cewa. “ka kwantar da hankalin ka a wannan lokacin ne ya kamata ka temaka mata” “ ta waca hanya zan temaka mata ?” “ta hanyar auran ta ” zaro ido SUHAIL yayi yace. "auran ta fa kace kai ma kasan hakan beme yuwa bane memartaba baxe taɓa amince ba” gyara zama JAMAL yayi yaci gaba dacewa. “in dai da gaske kana son ka t temaka mata to ka aure se dai idan ba tausayin ta kake ji ba” shiru SUHAIL yayi tarada furxar da zaxxafar iska kana yace. “shi kenan JAMAL ya kake ganin za'ayi?” " tun da ka amince ka bar min komai a hannu na san yanda zanyi” kamar yanda ALAJI BUKAR ya bawa malam RABE me gadi umarni ya kawo mai mutumin da bashi da cinyau bare na gobe hakance ta kasance wani tsoho ne tukuf har ya ranƙwafa saboda tsufa ƙafafunsa dik gidan memery wato faso takalmin ƙafarsa kuwa silifa ne lamba gomasha ɗaya yadin jikin sa kuwa irin ya din nan ne da ake cewa ishirinka maraya shima dik ya fefe har ya fara fashewa cikin gidan suka shiga inda suka iske dika mutanan gidan har MANAL bayan sun gaisa RABE yayi wa alaji bukar baya nin mutumin da yace a samo mai. washe baki DADY yayi gamida cewa. “ƙwarai kuwa yayi yanda nake so ”MOMY ma cewa tayi “gaskiya kam yayi ga dikkan alamu talauci yayi mai kanta kuma ya dace da ita se dai bamu san kenan shi ba?” “suna na SUNUSI kuma ni almajiri ne ina da mata uku ƴaƴa na sha takwass sannan banida sana'a ruwa nake siyar wato garuwa” “masha Allah haka ake so”cewar ZAINAB. “gaskiya kam dady yayi se taje ta riga tuƙa tuwo a lamaba talatin ina ga shima ba kullum ake cin tuwon ba” inji NABILA kenan. “kin faɗi gaskiya yarinya se muyi sati bamu ɗora tukunya ba se dai na basu ashirin ashirin su se garin kwaki su jiƙa su sha” inji SUNUSI kenan, “shi kenan malam SUNUSI dama wannan yarinyar zan aura maka kuma kyauta na baka da idan har ka amince to gobe ka turo magaba tanka a ɗaura kuma na gaya maka bana son komai daga gare ka ko sadaki bance ka kawo ba” “haba ALAJI wa za'a yiwa wannan kyautar yace baya so ai se dai in bashi da hankali wannan kykkyawar yarinya san kowa ƙin wanda ya rasa in sha allahu gobe zan turo” SUNUSI ya faɗa yana washe bakin sa me ɗan karan wari haƙoran nan kamar jar dawa dan

Chapter 5 of 12