Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 12
farka ɗin inda sukabar ta nan suka dawo suka same ta kamar gawa kanta ya kumbura kamar ze fashe haka ma idanun ta suka koma kamar lemon zaƙi dan kumburi, bayan sun gama karyawa NABILA taje inda MANAL ke kwance tasa ƙafa ta harbe ta amma kamar ta taɓa dutse shewa ta saki gamida ƙwallawa su Dady da mamy kira suzo su ga MANAL ta mutu burin su ya cika , zasu ci karan su babu babbakaaaaa suma ihuuuuu su kasa suna murna Allah ya rabasu da alaƙakai, dariya ZAINAB tayi gamida cewa "shi kenan Dady dukiya ta zama tamu dik wanda ya tambaya me yasa Meta se muce karuwan ci ta shiga har ta kwaso cutar , H.I.V wato ƙanjamau ita ce ta kashe ta kaga babu wanda ze zarge mu ” “haka za'ayi zee kin kawo shawara me kyau, nan suka bar ta kowa ya shige ɗakin sa acewar su se sunyi wanka sun gama abinda suke sannan zasu gayawa mutane mutuwar MANAL, MANAL kuwa wacca ta mance a'ina take aduniya ko alahira ta dai fi zoton alahira take, cikin azaba da radaɗi ta fara motsawa dishi dishi ta soma gani hakan yasa ta maida idon ta ta rufe , bayan minti tala tin ta sake yin ƙurin sake buɗewa dik hazo hazo take ganin komai ga bakin ta da yake shatatar da jini sakamakon haƙoran ta da suka fita cikin ranta tace “shi kenan na zama me wawulo sun raba ni da haƙora na, Hannun ta da ƙafar ta wa inda suka zama kamar tirmi dan kumburi suma ta kasa motsasu se yanxu ne ta sake tabbatar da rashin iyaye ba ƙaramin musiba bane ashe haka rayuwa take? Ashe dama mutane kowa da kalar zuciyar sa dama in kuka fito ciki ɗaya da mutum halinku ba iri ɗaya bane kowa da nasa ? Allah sarki ABBANA ashe yanda ka. ɗauki ɗan uwanka shi ba haka ya ɗauke ka ba ashe ba sonka yake ba afili yake nuna ma yana sonka a Zuciyarsa kuɗin ka yake so Allah Sarki iyaye na kun tafi kun bar ni alokacin da nake matuƙar buƙatar ku Allah sarki ABBA na kullum kana gaya min cewa ko bayan ranka ƙanin ka shine wanda ze riƙe ni ze bani kulawa kamar kai, se gashi shine yake neman makasa ta baya so ya buɗe ido yaga ina numfashi sabida abin duniya wanda kaima daka tara su kuma kake alkairi dasu ka tafi ka barsu ina ma mutuwa tazo ta ɗauke ni, na huta da wannan uƙubar hawayen azaba ne suka ringa xubo mata kanta ya kuma yi mata nauyi, tamkar dutse Wata ƙara taji an saki wan da ta san NABILA ce nan ta shiga ƙwalwa su mamy kira “Dady mamy kuzo ku ga wannan baƙar mayyar ashe bata mutu ba” sabida sauri dady har neman sulewa yake nan suka tsaya akan ta . wani ƙululun baƙin ciki ne ya kama DADY wannan waca iriyar yarinya ce me baƙin naci dik wannan wahalar da ya bata be sa ta mutu ba tsabar takai ci daya cika shi cewa yayi “ kar wanda ya kuma sauraran ta kuma kar a kuma bata abinci har se yinawa da ƙishiriwa sun kashe ta yana gama faɗar haka ya haye saman be ne yana ta masifa ɗakin sa ya shiga yana ta faman huci se zagaye ɗakin yake ya riga da ya gama tsara komai game da yanda ze yi da dukiyar MANAL idan ta mutu se gashi ta far faɗo tsaki ya kuma yi a fili ya ce“ dole ne ki mutu bazan ci gaba da zama a haka ba tin da mahaifin ki baya doran duniya kuma ke kaɗai ya bari aka mallaka miki dukiyar sa dole ke ma ki mutu ko ta halin ƙaƙa se kin bar dunyar nan ni ma na fanta ma da dukiyar ɗan uwa na! na yi facaka da ita zaki mutu zaki mutu zaki mutu MANAL” ya faɗa yana jefar da hular kansa. KEEEEE DUNIYA INA ZAKI DAMU NE ANYA WA INNAN MUTANAN SUNA JIN TSORAN ALLAH YA ALLAH KASA MU FI ƘARFIN ZUCIYAR MU ALLAHUMMA AMEN IDAN HAR KE MASOYIYA TA TA TSAKANI DA ALLAH KUMA KINA JIN DAƊIN LITTAFIN NAN TO KI TAYA NI TURAWA CIKIN WASU GRP MMN HIBBA TANA GODIYA DA TARIN MASOYA DA ADDU'AR DA KUKE MATA SHAWARA D'AYA ZAN BAWA MASU KARATUN LITTAFIN RAMIN MUGUNTA SISTER BAN CE KARKI KARANTA LITTAFIN NAN BA AMMA IDAN KIN SAN KINA DA RAUNIN ZUCIYA TO KARKI KARANTA DOMIN BA'A FARA KOMAI BA YANZU MANAL ZATA FARA SHAN WUYA WANNAN SHARAR FAGE NE. ƙalamin mmn hibba ne✍️ RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER✍ SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi Shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE 5-6 Kamar yanda DADY ya faɗa hakan ce ta kasance yau kwanan MANAL huɗu ba tara da tasa komai acikin ta ba se dai ta sha ruwa nan da nan ta kuma tsotsewa ta koma kamar ƴar tsana kana iya ganin ƙasusuwan jikin ta , ƙafar ta ta kumbura har ta soma xubar da ruwa amma babu wanda yaji tausayin ta sema abinda ya kuma yin gaba yau ta kama litinin NABILA da ƙawayan ta sun cika gidan se shaye shaye suke abin babu kyan gani maza da mata, ne sunyi wata iriyar shiga wacca da ita gawamma babu kowacce da saurayin ta suna holewar su, gefe guda hakimar tasu uwar gayyar ce jikin wani saurayin ta babu kunya babu tsoran Allah gaba ɗaya gidan ya kauraye da warin wuy wuy da sigari se guntsa suke suna fesarwa. MANAL, ce ta fito tana bin bango dan ko tsayuwar kirki bata iyayi sabida yinwa gaba ɗayan su suka bushe da dariya, kamar mahaukata sabbin kamu MANAL kuwa ko ajikin ta ita bata damu ba dik da tasan da ita suke. ɗaya daga cikin samarin ne yace. “BEBY NABEE ina kuka samo wannan ƙasusuwan jifa ƙashin ta ina iya irgasu zama da irin wannan matsala ne se su goga muku talauci” hhhhhhhhhhhhh, suka kuma sa dariya irin ta gogaggun ƴan duniya tsaki NABILA tayi gami da cewa “kai dai bari Beby wallahi daga ƙauye aka kawo mana ita take mana shara da wanke wanke baku ga yana yin ta kalar na ƴan ƙauye ne ba ?” suka kuma bushewa da wata wula ƙantacciyar dariya, “keeeeee, MANAL baki ga mutane bane zaki wuce baki gaida su ba ?” a san yaye tace “kiyi haƙuri aunty NABILA” se ta juya gurin ƙawayan nata har ƙasa ta tsuguna tace “sannun ku” babu wanda ya amsa a cikin su se ma wani ƙas-ƙantaccan kallo da suka bita da shi. “da halla ni jeki dafa mana shayi ki kawo mana kuma wallahi kika daɗe sena miki bille afuskar ki” ta faɗa cikin ɗaga murya, kicin ɗin ta shiga dafe da cikin ta da yake ƙugin yinwa tana addu'ar Allah ya kawo mata ɗauki da gaggawa. wani ragowar abinci ta gani an ajiye da alama bana yau ba ne dan har ya fara yami ALLAHU akubar, haka MANAL tayi zaman dir shan tana ci kwa nan nan abinci da ko dabba baza'a bawa ba ita kuwa murna, take yi ta samu abin da zata sawa cikin ta. ta manta da wani dafa shayi se da taji NABILA na ƙwala mata kira bashiri ta miƙe jiki na ɓari, kamar mazari gass ɗin ta kunna ta haɗa komai da ake buƙata na shayi kan kaceme har ta gama ta juye musu a' filas ɗin shayi ta ɗauki ƙana nun kofuna na shan shayi ta fita kanta aƙasa dan bata son haɗa ido da wa innan ƙartin. gaban NABILA ta kai filet ɗin ta ajiye ta juya zata tafi “ uban waye ze zuba mana shayin da kike ƙoƙarin tafiya ko kinji na ce ki tafi ne?” girgiza kai ta yi gami da dawo wa ta zuba wa kowannen su sannan ta bisu ɗaya bayan ɗaya tana miƙa musu “NABEE dama haka kuke dafa shayi agidan ku?” NANSY ta faɗa gami da furzo, shayin daga bakin ta . nan suma sauran suka kai cup ɗin shayin bakin su ai kuwa suma suka furxo da shi suna ya mutsa fuska, haushi ne ya kama NABILA ta ɗauki cup ɗin shayin ta kai bakin ta ai kwa ita ma ta furzo shi ashe ba siga MANAL tasa acikin shayin ba gishiri ta saka a madadin siga haushi ne , ya kama NABILA yanda MANAL ta kunya ta ta agaban ƙawayanta MANAL kuwa ta rakuɓe jikin ta se kyarma, yake cikin ɓacin rai, NABILA ta cika cup ɗin da yake gaban ta da shayi bata ɓata lokaci ba ta sheƙawa MANAL afuska wata gigitacciyar kara, MANAL ta saki sabida azaba da raɗaɗi NABILA kuwa ko ajikin ta wani cup ɗin ta kuma cika wa ta kuma sheƙa mata, azaba tai azaba Uƙu ba tai Uƙu ba gaba ɗaya fuskar MANAL babu kyan gani domin kuwa ƙunar ta shige ta fatar fuskar ta ta saɓule tin daga wuyan ta da sauran sassan jikin ta hakan bai ishi NABILA ba seda ta haɗa mata da duka tana zagin ta dama iyayan ta da suka rigamu gidan gaskiya. se da aboka nan sha shancin nata suka riƙe ta wai ta bar ta haka Ahakan ma taji jiki . “ NABEE wannan ƙunar da kika yi mata be dace ba idan aka bar ta ahaka fuskar ta ze iya samun matsala kamata yayi mu kaita asibiti tin da wuri” cewar JAMSY. wata uwar harara NABILA ta jefi JAMSY da ita kana tace. “wallahi babu inda zani se dai ta mutu idan ma ta mutu waya damu da ita. fuuuuu, ta wuce kamar zata tashi sama. suma sauran suka fice daga gidan suka kama gaban su akabar JAMSY kaɗai ita kuwa tausayin MANAL ne ya cika ta dan haka ta ƙudiri aniyar ce to rayuwar ta ɗaukar MANAL tayi kamar gawa babu alamar rai atare da ita bayan mota ta saka ta sosai take gudu, tamkar zata tashi sama tin kanta isa asibitin ta yiwa Dr. ɗin waya abinka da ƴaƴan masu kuɗi babu wani bincike ko ace se tazo da ƴan sanda aka shiga da MANAL ɗakin tiya ta jim kaɗan Dr ɗin ya fito yace. "JAMSY ta same shi a office ɗin sa baya nin da Dr JAMAL yayi wa JAMSY ya ɗaga mata hankali, ya tabbatar da cewa. fuskar MANAL tayi dameji In kuwa ana so ta dawo dai-dai to fa se an kashe maƙudan kuɗi wanda aƙallah sun kai million goma da dubu ɗari bakwai da hamsin sosai hankalin, JAMSY ya tashi ta san Ko ta gayawa su NABILA ba zasu biya kuɗin ba, dan haka tayi alƙawarin zata ɗauki nauyin aikin tinda tana da kuɗin da suka fi haka a Account ɗin ta nan ta cewa Dr. su fara aikin zata biya na dai ta cike komai da komai aka shiga da MANAL ɗakin tiya ta.... Can gidan kuwa babu wanda ya tambayi inda MANAL take har kokin gaban su kawai suke likafa taci gaba DADY ya mallakawa su ZAINAB da BABILA motoci kowacce uku tara da dan ƙara musu maƙudan kuɗaɗe a account ɗin su haka ita ma MAMY ya ɗauki gida sukutum guda ya bata wanda aƙalla ze kai million hamsin bayan haka ya biya musu kuɗin tafiya ƙasar India dama sauran ƙasashe wai suje su huta duniya sabuwa DADY se wadaƙa yake da dukiyar ƴar ɗan uwan sa ba tara da yasan abinda zeje ya dawo ba. su NABILA da ZAINAB sun samu yanda suke so mahaifinsu ya basu damar su zagi kowa su daki uban kowa kuma su zauna lpy hakan ya ƙara musu girman kai da jin cewa suma ƴaƴan masu kuɗi ne hakan yasa suka kuma dulmiya cikin ƴaƴan masu kuɗi abin dai ba kyan gani sune shaye shaye Kwan a hotel dik wani gidan fati in dai a kano yake to fa sun san shi samari ta ko ina se ɓullu musu suke suna kashe musu kuɗi kamar basa so musamman ma NABILA dan tafi ZAINAB mutane kai in kaga manya manyan masu kuɗin da suke zuwa gurin ta abin se ya baka mamaki hakan be taɓa damun iyayen su ba hasali ma daɗi suke ji ƴaƴan su sun zama man yan yara yau kwanan NABILA huɗu bata gidan abige ta shigo gidan tana tangaɗi gamida layi da surutai bar katai irin na ƴan maye, SUNA WANI LITTAFINA DANA KESON RUBUTAWA MAI SUNA (ƳAR SHAYE SHAYE ) Yaune ake saran kwance tiya tar da aka yiwa MANAL wanda rabin jin yar tata ya ta'allaƙa akan Dr. JAMAL wanda JAMSY ta bashi amana da kuma gayamai irin halinda MANAL ke ciki sabida ita tayi tafiya ƙasar KAMBIRIC dan iyayen ta acan suke da zama shi ne suka bugo mata waya lallai tazo suna son ganin ta hakan yasa ta damƙa amanar MANAL a hannun sa masha Allah aiki yayi kyau sosai su kansu likitocin da suka mata aikin sunyi mamakin aikin basu taɓa tsammanin zeyi kyan haka ba. sosai MANAL ta saba da Dr. JAMAL dan mutum ne me sakin fuska ga kuma faran faran, da mutane ai kuwa MANAL tayi kayu jikin ta da kyan ta da hasken ta suka soma dawowa dik wannan kasusuwan yanzu sun koma. kullum idan MANAL tayi sallah bayan ta yiwa iya yanta addu'a se ta yiwa JAMSY da Dr. JAMAL yau watan ta uku cifff a asibitin Kuma yau ne za'a bata sallama se dai abinda yafi bawa Dr. JAMAL mamaki ya kuma ɗaure mai kai yanda MANAL ta shafe wata uku s asibitin amma babu wanda yazo yace shi ɗan uwan MANAL ne sosai yake mamaki yana so ya tambaye ta se dai baya son shiga hurimin da ba na sa ba dan haka yaja bakinsa ya zuge. MASARAUTAR ZAKI Yau ma kamar kullum yarima SUHAIL ne kwance akan taf keken gadon sa wanda ya sha zanin gado na al-farma. bacci yake sosai amma se juyi yake yi kamar wanda yake ganin wani abu cikin baccin nasa frigigit ya tashi yana salati se gumi yake kamar wanda yayiwa sarki ƙarya ƙafafunsa ya xuro ƙasa yasa wani tattausan ta kalmi mafarki da ya saba yi kullum yau ma shi yayi se dai be taɓa ganin fuskar ta ba kawai abinda ya sani shine tana yawan zuwar mai a mafarki tana kuka tana neman tema konsa kuma wai acikin wata rijiya me zurfi da duhu take ga macizai da kunamu suna ta saranta shi kuma yazo wuce wa ta gurin ya ganta cikin wannan halin da zarar yaje gurin domin ya temaka mata se rijiyar ta dinga matsawa ahaka ahaka har ta yi mai nisa “wace ce ke a ina kike wana irin temako kike so na yi miki” me yasa ba zaki bayyana min kanki ba?” yayi wa kansa tamabayar da bashi da me ba shi amsar ta. tashi yayi jikin sa babu ƙwari kamar anyi mai duka toilet ya shiga yayi wanka gaban mudubi ya wuce wasu tsadaddun mayuka masu ƙamshi kamar tirare ya shafa a jikinsa wasu kaya masu taushi da santsi kamar Auduga kuma farare yasa sosai suka yi mai kyau jikinsa ya feshe da turare me ƙamshi da daɗin ji al-kyabba ya ya ɗora akai sosai ta ƙara mai kyau waje ya nufa cikin takun sa na ƙasai ta irin na sarakuna gaba ɗaya bodi gad ɗin sa da dogarawa da suke bakin ƙofar suka zube suna kwasar gaisuwa kai kawai ya gyaɗa musu. Bodi gahd ɗin suka take mai baya su kuma dogarawan suka zauna gadin sashin nasa dik inda ya gifta bayi da ƙwarori sai sun tsugunna sun kwashi gaisuwa kai kawai yake gyaɗa musu kun san masu mulki busu fiya son magana ba domin tana yi musu wuya. Kai tsaye FADA suka nufa. “An gaishe ka yarima ɗan sarki jikan sarki wanda yagaji sarauta gaba da baya taka lafiya yarima mejiran gado kaga ɗan Sarkin sarakuna kaga ɗan Sarkin daya san sarauta gaba SALAMUN baya SALAMUN ɗan sarki jikan sarki wanda suka gaji sarauta kaga masu abu da abun gado ba taka haye ba”. Abin da dogarawan suke ta faɗa kenan har yarima ya shiga fada yayin da mutanan dake ciki suka fito suka basu guri wannan Umar nine daga sarki muddin yarima zezo fada dik wanda yake cikin fadar ya fito ya basu guri sun gana in yaso bayan ya tafi se su dawo yana shiga ya rungume Mahaifin nasa yana dariya kamar wani ƙaramin yaro bayan sun gaisa memartaba yake tambayar sa yau she ne ze gudanar da bikin buɗe asibitin sa da ya gina Sosa kai yayi yace, “ehh to ranaka ya daɗe ban tsaida rana ba amma zan kira JAMAL se mu tsaida rana” "to toto shike nan yarima Allah ya bada Sa'a nima in an tashi taron asanar da ni da wuri dan ina so in halarci taron kuma nima ina son na bada tawa gudummawar” “to memartaba” In sha Allahu muna godiya Allah ya ƙara girma da buɗi ya baka lafiya me ɗorewa gaba ɗayan su suka amsa da Amin. ɗakin mahaifiyar sa ya shiga wato uwar gidan sarki bayan sun gaisa ya shiga sashin kilishi itama suka gaisa sannan ya shiga sashin gwaggo wato ƙaramar matar sarki acan yayi karin kumallo dan dama yafi sabawa da ita kome zeyi in dai yana neman shawara to ita yake gayawa in dai bata gidan bace. ko Sarki da suka fi shaƙuwa da shi fiya da kowa be fiya gaya mai wasu matsalolin nasa ba A cewarsa girma ya kamashi be kamata yaringa ɗaga mai hankali da nasa matsalolin ba ya maji da mulkin da yake kai, jefi jefi suna taɓa fira da gwaggo damma yarima be fiya son magana ba. (Kunji fa masu karatu ya tsallake ɗakin mahaifiyar sa yazo yana ci aɗakin kishiyar ta shin me yakawo hakan??????) miƙewa yayi yace. “Gwaggo se anjima” “to se ka dawo Allah ya tsare ” “amen gwaggo se na dawo har ya kai bakin ƙofa yaji ankira suna shi . “YAYA SUHAIL,” ta faɗa lokacin da take ƙoƙarin sakkowa daga saman be ne tana zuwa ta ware hannunta alamar ya ɗauke ta ɗaukar ta yayi ya shiga jijjuya ta kamar wata ƴar tsana ita kuwa se dariya take. Sauke ta yayi ya lakace kumatun ta yace. “ ƴar lukutar gwaggo ya akayi ne na san wannan kiran da akamin Akwai magana” baki taturo tace. “ba kai bane jiya kace inka fita zaka sayomin dogayan riguna kuma baka siyamin ba” ta faɗa cikin muryar shagwaɓa “sorry MEENA mantawa nayi ungo ATM ɗina kisa Direba ya kaiki kuma kice sikiruti suraka ku kinji” tsalle tayi, gamida cewa “yawwa YAYA na nagode amma fa se wani satin zani sabida akwai abinda zanyi” “wannan kuma ya rage naki ga dai A.T.M nan na baki” Gwaggo na zaune tana kallansu se yanxu tasa musu baki da cewa. “A'A tin da ba yau zata je ba karɓi A.T.M ɗinka kar ta wullar maka ka san ta da shirirta” “a'ah gwaggo kibar mata kawai idan ma ta ɓatar se na sake yin wani ko autr mu?")” “Eh yaya na” “to Shi kenan ni zan wuce” “to seka dawo Allah ya tsare” da “Amin” ya amsa “kai tsaye sashin sa ya koma wayarsa ya ɗauka ya kunna wadda tin jiya ya kashe saƙwani nine suke ta shigowa cikin wayar na abokansa dama na ƴan matan da suke son sa shi kuma baya son su , saƙwan JAMAL kawai ya duba dariya yayi afili yace. “kai JAMAL se abarka ba dai tsokana ba” number sa ya kira . dai-dai lokacin da JAMAL yayi fakin a'kofar gidansu MANAL Wanda ya koma na su Dady ɗaukar wayar yayi yana dariya yace. “Se yanxu ka ga damar kira na wallahi SUHAIL idan kayi aure se dai mu dinga zuwa inda kake danna san mantawa zaka yi damu” kome yace mai Seya kwashe da dariya yace. “Ina xuwa zan kiraka naje wata unguwa ne oky sena kira ɗin” ya faɗa tara da sauke wayar daga kunnen sa ya dawo da duban sa gurin MANAL wacca dik tabi ta fiegice ta gigice. Maganar sa ce ta dawo da ita daga tina nin da take . “kiyi haƙuri MANAL dik da ban sanki ba amma na fuskanci kina cikin damuwa da alama ke marainiya ce ki cigaba da haƙuri da kai wa Allah kukan ki haƙiƙa Allah maji roƙon bayinsa ne ba zaki taɓa dana sani ba muddin kika riƙe sallah da addu'a zaman wannan gidan yafi miki alkairi idan kika ce zaki bar gidan nan zaki tsinci kanki a yana yinda ba aso addu'a itace makamin mumini zaki ga ribar haƙuri ga wannan kuɗin ni ne na baki kisiyi kayan sawa dana kwalliya” girgiza mai kai tayi tace “A'ah kabar su Na gode

Chapter 2 of 12