''Alhamdullih Allah abin godiya SUHAIL ya zama uba cewar Gwaggo sosa kai SUHAIL yayi yana sunne kai wai kunya yake ji bayan an kai MANAL ɗakin hutu suka shiga ga gadanta gana yaran ta wanda aka naɗe su cikin kayan jarirai masu kyau da tsada tunda SUHAIL ya shigo idon sa na kan yaransa inya ɗauki wannan seya ajiye wannan ya kuma ɗaukar dayan har ya bawa MANAL haushi wato ba ta ita yake ba ta ƴaƴan sa yake nan ta cika tayi fammmm, ya kusa 30 minit yana kallon yaran sa, sannan yazo gurin MANAL maganar duniya yayiwa MANAL amma tayi burusss da shi, se cika take tana batsewa Ita dai Gwaggo tana kallan su bata ce ta tafas ba, bare a sauke ''kuka MANAL tasa mai tana cewa shi kenan yanxu ta san baya son ta ƴaƴan sa yake so, shi,kuwa SUHAIL dariya ma, ta bashi, nan dai ya lallaɓa ta suka rabu lafi, kangari ya waye SUHAIL ya ɗora photo yaran a MIDIA anyi masa haihuwa
Kan kace me, ƴan uwa da abokanan arziƙi sun sani kankace kwabo ƴan barka sum a cika acibitin ba masaka tsinke ƙarfe goma na safe aka basu sallama sabida basu da wata matsala daga me jegon har yaran ta kai tsaye sashin Gwaggo aka kai MANAL dan akula da ita da kuma yaran ta, zo kuga yanda ake nannan da MANAL kai ba zaka taɓa cewa bata da iyaye ba, shima SUHAIL yana can gurin abokanan sa sunata yimai tsiya se dare ya samu shigowa cikin gidan ɓangaran su, ya nufa cike da ɗaukin sake ganin yaran sa amma me babu kowa fitowa yayi yanufi sashin Gwaggo dan yafi zaton tana can ilaikuwa ya sameta tana cin tuwan dawa miyar ɗanyar kuɓewa data sha manshanu da yajin daddawa wanda Gwaggo da ta,shiga kicin ta dafa mata shi .
ƙarasa wa inda take yayi se faman Binta da kallo yake kamar ze cinye ta, huremai ido tayi ''kallon fa haka'' dariya yayi yace "gani nai kinyi kyau kuma kin manta dani tunda gashi har kina iya cin abinci batara dani ba, sunkuyar da kanta tayi kana tace ''kayi haƙuri nima dan babu yanda zanyi ne duk duniya na fiso na ganka kusa dani bana so, naga kayi nesa dani dan Allah kada kaga na haihu kace zaka min kishiya wallahi bazan iya sheres ɗin ka da wata na fiso ka zauna dani ni ɗaya takkkk kayimin wannan alƙawarin'' ta faɗa fuskar,ta cike da kishi'' shiru SUHAIL yayi yana mamakin dama MANAL nada irin wannan baƙin kishin haka? tambayar da bashi dame bashi amsar ta ''kayi shiru ko Kanada wata budurwa awaje baka gaya min ba?''' ta tambaye shi idonta fal hawaye da sauri SUHAIL ya girgiza kansa yace ''wallahi kiyar da dani tunda nake ban taɓa ssuraran wata ƴa mace ba hasali ma su, suke cewa suna sona,'' ajiyar zuciya MANAL tayi tace shi kenan na yarda da kai, danna san baza kamin ƙarya ba, dai-dai lokacin yaran suka tashi suna kuka da alama yinwa sukeji ɗakko su, yayi, ya bata HASSAN shi kuma yana jijjiga USAINI bayan tagama bawa Hassan ya miƙa mata usaini ya mutsa fuska tayi ''wallahi na gaji plssssssssssss ka siyo madara a dinga basu ta faɗa tana turo baki'''
Kallan da SUHAIL ya bita da shi ne yasa ta karɓi Usaini tana bashi nono tana gama bashi ta miƙa masa ɗansa ta juya musu baya ya jima a zaune yana yiwa yaran addu'a ya kuma yi musu huɗu ba kwantar da su, yayi yasa hannu ya juyo da MANAL yana kallan cikin ƙwayar idon ta, '' ko bayan raina kika bawa yara na madara ba zan yafe miki ba saboda lafiyar ki ƙalau ki faɗi duk abinda kike so zanyi miki amma kada ki, kuskura ki bawa ƴaƴa na madara'' ya faɗa cikin faɗa da ɗaga murya idanun sa sunyi ja kamar garwashi fita yayi daga ɗakin zuciyar sa, na suya. tun daga nan SUHAIL ya dena shigowa ɗakin idan ma yaxo iya kacin sa farlo yace amiƙo masa yaran sa idan ya gama ganin su ya bada abinda ze bada ya tafi hakan ya ɗagawa MANAL hankali tana ji ze ringa waya da ƴan mata yana dariya kullum cikin kuka take ga kishin mijin ta da yake damun ta ga watsin da yayi da ita.
Gida ne ginin jar ƙasa Irin na da ko albarkacin ƙofa babu se buhun siminti da akasa aka rufe gidan shima duk ya yayyage kana iya ganin wanda yake ciki Ahankali yake magana cikin sarƙewar numfashi yace '' kaico na ni, ABUBAKAR ban riƙe amanar yar ɗan uwana ba gashi yanzu nayi biyu babu ba dukiyar ba lafiya tari ne ya kamashi ya kusa minti 30 yana yi kafin ya lafa masa yaci gaba da cewa '' tabbasss Allah ba azzalumi bane tun aduniya yake hukunci base anje lahira ba BILKISU ZAINAB BABILA ya kira sunan,su. Suka amsa cikin kuka yace '' hakiƙa na kasan ce me son kaina a koda yaushe saɓa nin ɗan uwana da ba haka yake ba, baya taɓa nuna ban-banci duk abinda nake so yana min baya taɓa gajiwa dani amma bana duban haka wata rana naje gidan sa nace ya bani kuɗi zan yi jari yace to amma in yi haƙuri babu kuɗi agurin sa saboda shima yayi odar kaya amma nan da sati inzo in karɓa, alokacin na rufe ido na, nayi mai rashin mutunci wanda shima hakan ya fusata shi, har mukayi musayar yawu na dawo gida na gayawa mahaifiyar ku, itama ta zuga ni nan dai na kuma hawa dokin zuciya cikin daran na fita na haɗa kai da ƴan fashi na basu kuɗi nace su kashe ɗan uwana ALAJI SA'AD ME DALAH nace kar su kashe MANAL saboda idan ba ita bazan samu duka kadarorin dana keso ba Lokacin zuciya ta ƙeƙashe bana ganin komai, cikin dare kuwa ƴan fashin nan suka kashe shi, shi da matar sa wanda daga nan ne MANAL ta dawo gurina da Zama itama ba'aje ko ina ba na amshe dukiyar ta nasa agaba mukai taci ita kuma muka barta cikin wahala da azaba. Wannan shine babban zunubin dana ai kata wanda ban taɓa gayawa kowa ba, wanda na san alhakin ɗan uwana ne yake ta bibiya ta dani daku, babu kuɗi babu gidaje ba motoci ba shaguna komai ya ƙare munsiyar da komai abincin da zamuci ma gagarar mu, yake ƙarshe ga inda muka dawo gidan da bashi da maraba da titi wayyoooooooooo Allah na ina zanga MANAL na roƙe ta gafara ta yafe min ko naji sanyi ta wani ɓangaren na san tawa tazo ƙarshe ba lallai na tashi ba dan haka nake jan hankalin ku, da kuguji duniya domin babu komai Acikin ta se ɓata. NABILA wacce itama ta haihu sedai ɗan nakasashhe ne bashi da ƙafa gashi ita kuma ta gamu da cutar H.I.V wanda mijin da ta aura yasa mata har taci ƙarfin ta tace '' in sha Allahu DADY zamu nemo duk inda MANAL take mune mi, yafiyar ta dan mun azabtar da ita ga mugayan kalamai da muke faɗa akanta wanda kan mu, suka dawo'' ta faɗa cikin kuka me nuna tsantsar nadama Mommy da ZAINAB ma kukan suke "yanxu idan mukace zamu nemo MANAL ina zamu, bamu san inda take ba sannan bamu san gidan wanda aka aura mata ba cewar mommy gaskiya ne mommy amma Ni, aganina mu nemi, RABE me gadi ina ganin ze san gidan tunda shi ne wanda ya nemo mijin da aka aura mata cewar ZAINAB gaba ɗaya sukai na'am da zancanta. Kwana biyu suna neman Rabe wanda da kyar suka Ganshi suka taho dashi,. Shi kanshi RABE seda ya tausaya musu amma daya tuna rashin imanin da sukayi wa MANAL se yaga be Kama tama yaji tausayin su ba,
Nan Dady ya kuma faɗawa RABE me gadi Irin aika aikar da yayiwa ɗan uwan sa ya ƙara da cewa ''Rabe ina roƙon ka, daka kai ni gurin MANAL na roƙi gafarar ta kona samu sauƙin ciwon dana keji a jiki na kai kaɗai kasan inda take shi yasa nasa aka nemo min kai kate maka RABE,'' DADY ya faɗa cikin sarƙewar tarin daya kamashi wanda har da jini seda ya lafa sannan Rabe yace '' gaskiya ALAJI bazan ɓoye maka ba wanda na kawo maka bashi MANAL ta aura'' ''wata aura?'' cewar mommy nan RABE ya kwashe duk yanda akayi gurin ɗaurin auren ya gaya musu yaci gaba da cewa ''yanxu haka shekaran jiya na sami labarin MANAL ta haihu kuma ƴan biyu zancan nan da nake muku MANAL matar ɗan Sarkin masarautar ZAKI ce, Gaba ɗaya ɗakin yayi tsittt kamar ruwa ya cinye su, '' DADY kuwa cewa yayi "alhamdullih Allah Nagode maka daka juya wannan lamari RABE na gode da baka aurawa MANAL wanda ka kawo ba ina fata zaka mana, jagora don muje mu nemi yafiyar MANAL” insha Allahu ALAJI duk sanda kuka shirya kuyi min magana zan kai ku Allah ya tsare gaba yasa mufi ƙarfin zuƙatan mu, suka amsa da Amin kowannan su, yana mamakin yadda akayi haka lallai ikon Allah da girma yake,
MASARAUTAR ZAKI
SUHAIL ne zaune a farlon Gwaggo yazo ganin yaran sa Bayan an kawo masa su, ya zauna yana ta ɗaukar su, a photo se zabga murmushi yake MANAL ce ta shigo farlon cikin shiga ta alfarma tayi kyau sosai sallama tayi ya amsa ciki-ciki dan har yanzu fushi yake da ita. Guri ta samu akan kujerar da yake kai ta zauna tara da yi mai sannu da zuwa banza yayi mata duk da haka bata haƙuri ba tace '' kayi haƙuri YAYA wallahi b...'' da sauri ya ɗaga mata hannu yace "ya isa haka MANAL bana son jin komai daga gare ki kin riga da kin nuna min koke wace ban taɓa tina nin zaki yiwa yara na wannan horon ba mena rage ki, da shi me kika nema kika rasa da har zaki ce ba zaki shayar da su ba shi kenan ai bake kaɗai ce mace aduniya ga mata nan birjik aduniya ko nawa nake so zan aura da har zan zauna ina kallo ki ringa yiwa ƴaƴana horan madara '' kuka MANAL ta saka mai har cikin ran sa yake jin kukan nata Amma ya maze dan baya so ko kaɗa nan gaba idan ta kuma haihuwa tace zata bawa ɗan sa madara dan haka yayi banza da ita taƙaraci kukan ta, miƙewa yayi ze tafi ta riƙe rigar sa cikin kuka tace '' saboda bani,da kowa shine kake min duk abinda ka gadama har kake iƙirarin zaka ƙara aure shi kenan SUHAIL ina so ka sani kafin na bar gidan ka seka bani yara na dan sba naka bane da abina ka ganni ko yanzu kace in tafi tafiya zanyi amma da yara na zan tafi" Jikin sa ne yayi sanyi da yaji ta amci bata da kowa se kuma ta basa dariya da tace yaran ta ne cikin son ya ƙular da ita yace '' bazan bayar da yaran ba duk inda zaki kije amma bada yara na ba sannan da kike cewa yaran ki, ai duk wanda yaga yaran nan yasan ƴaƴa na ne saboda kamar da muke yi dasu'' dan takai ci MANAL magana tayi Fuuuuuuuuuuuuu ta bar farlon ranta aɓace shi kuwa SUHAIL dariya yayi yace yarinya se rigimar tsiya wai kaji yaran ta Saboda tsabar rigima Irin Tata,
ranar suna yara suka ci sunaye HASSAN akasamai sunan me martaba USAINI kuma akasamai sunan mahaifin MANAL wato SA'AD, anyi taron suna me jego da yaran ta suka samu kyautittika da dama har da wani abokin. SUHAIL daya biya mata kujerar maka idan tayi arba'in zata tafi. cikin ikon Allah MANAL tagama wanka yaran ta sunyi kyau sunyi ɓul-ɓul kamar ba haihuwar fari ba randa zata koma sashin su, Gwaggo tasa aka gyara ta da magun gunan mata ga Gara da akayi mata daddare aka rakata ɓangaran ta, washe gari da yamma me martaba yasa aka kira masa SUHAIL da MANAL basu ɓata lokaci ba suka je Gaban MANAL ne ya yanke faɗi lokacin da tayi tozali da su DADY wanda daga ganin sa kasan ba shi da lafiya sabida akwance yake, kasa zama tayi har seda me martaba yace ta zauna sannan ta zauna nasiha me ratsa zuciya SARKI yayi musu sannan yace '' MANAL duk abinda kika ga ya sami mutum to daga Allah ne dama ya riga da ya ƙadar maka haka tun kan kazo duniya na san baki manta da wa'innan mutanen ba to dan haka kiyi haƙuri kiya fe musu duk abinda suka miki saboda manzon Allah (s.a.w) yana son me yafiya'' '' Hakiƙa MANAL munzalin ce ki, ina me roƙon gafara agurin ki, da ki yafe min kona samu Salama a rayuwa ta haƙiƙa ban riƙe zumunci ba na biyewa duniya ina ganin kamar bazan mutuba se gashi tun aduniya Allah ya nuna min iya kata ki yafe min MANAL nina san tawa ta ƙare Allah baxe bar ni ba kodan Abinda nayiwa ɗan uwana Nana ya gaya musu cewa shine yasa aka kashe mahaifin MANAL innalillahi wa'inna ilaihi raju'unnn MANAL ta faɗa tarada miƙewa tsaye cikin kuka tace “ dad da da dama kai ne kasa aka kashe min Abba na momy na?'' ta faɗa cikin kuka se Kuma gani su kai ta sulale ƙasa sumammiya da sauri SUHAIL yayi kanta yana kiran sunan ta ruwa ya ɗakko ya fesa mata ajiyar zuciya tayi kuka take me tsuma zuciya rungume ta SUHAIL yayi ajikin sa yana rarrashin ta, '' bazan taɓa yafe maka ba tunda ka raba ni da iyaye na kuka saka rayuwa ta cikin wahala'' Mommy da ZAINAB da NABILA suka durƙusa gaban MANAL suna neman afuwar ta. ''kinga yanda na koma ko MANAL jibi yanda rayuwa ta juya min baya yanzu haka na kamu da cuta me karya garkuwar jiki ZAINAB Kuma ta gamu da yoyon fitsari mommy kuma Cutar farfaɗiya ce tasa Meta muna roƙon ki da ki yafe mana mun san da wuya ki manta da irin abubuwan da muka yi miki'' cewar NABILA tana kuka kamar ranta ze fita Allah sarki MANAL me zuciyar imani '' Shi kenan na yafe maku Allah ya yafe mana baki ɗaya yasa hakan ya zama IZINA ga yan baya''' gaba ɗaya suka amsa da ameen
ZAINAB ce tace ''muna godiya MANAL kuma ina ƙara roƙon ki dan Allah dan Annabi kiyi haƙuri ki yafe wa DADY'' share hawaye MANAL tayi kana tace '' na yafe masa seya nemi yafiya gurin Allah, Allah ya tsare gaba'' ''na na nagode sosai MANAL tabbasss ke jinin SA'AD ce na gode Allah yayi miki albarka dake da xuriyan ki, ya kare ku daga mugun ji mugun gani na gode ƙwarai da gaske'' cewar DADY yana kuka ga wani numfashi da yake fitarwa sama-sama me martaba yasa aka kaishi asibiti sannan ya basu abinci da kuɗi masu yawan gaske sannan yace idan wata matsalar ta taso suxo su gaya mai Godiya suka yi mai. Kwanan DADY biyu a asibiti Allah yayi mai rasuwa saka makon tarin daya ci ƙarfin sa wanda likitocin sukayi iya ƙoƙarinsu amma ina rai yayi halin sa . Lokacin da labari ya riski MANAL tayi kuka sosai koba komai shi ma ubane awajan ta rayuwa taci gaba da juyawa yau daɗi gobe akasin haka an samu ci gaba sannan kuma anyi rashe rashe ciki kuwa harda Mutuwar SARKI wato mahaifin SUHAIL mutuwar da tadaki kowa bayan arba'in aka naɗa SUHAIL amatsyin sarki, Wanda kowa yayi na'am da haka kwanciyar hankali ta wanzu ɓangaran su MEENA da JAMAL suma ba'a cewa komai dan kuwa itama MEENA ta haihu ƴa mace wadda taci sunan mahaifiyar JAMAL suna kiran ta da KAISAR NABILA ma tayi aure inda ta sami me irin cutar ta ta amince masa suna zaune cikin rufin asiri ZAINAB ma ta koma gidan tsohon mijin ta MUKUTAR wanda tun bayan tafiyar ZAINAB asirin da HAULE tayi mai ya karye ya danƙara mata saki suna zaman su cikin so da ƙauna ita da yaran HAULE wanda ta fita ta bari MOMMY kuma SUHAIL ya siya mata gida sannan lokaci-lokaci suna xuwa su gaishe ta, MIJIN NABILA da ta aura ƴan sanda sunyi nasarar danƙe su gaba ɗaya su Wanda dama tun lokacin da aka kaisu NABILA wajan su suka sa musu ido yana dirowa garin ƴan sanda sukayi ramm da shi. aka kuma ka masu Gaba ɗaya.
BAYAN SHEKARA TAKWAS.
Wasu kyawawan yara na hanga cikin wani ƙaya taccan farlon suna wasa wasu kuma suna karatu. wata mata ce ta fito cikin shiga ta alfarma gefanta kuyangu ne guda uku hannayen su riƙe da kwani ka, ɗaya kuma tana ɗauke da jariri da alama dai ɗan matar ne lokacin da suka ƙaraso seda na murza ido na danna ƙara tabbatarwa da gaske ne Abinda ido na yake gane min ko kuma gizo ne. Murzawa nayi da kyau na kuma buɗe su fesss akan. Matar da gaske ne MANAL ce agaba na ta zama big Madam komai nata ya sauya ta zama. Babbar mace. Gaba ɗaya yaran suka taso suna mata magana kowa da abinda yake cewa bata saurare su, har seda ta sallami Kunyan gun ta karɓi jaririn gaba ɗaya sun. Cika mata kunne tama rasa yanda zata yi dasu tsawa ta daka musu tsittt suka yi kamar ruwa yaci su '' haba gaba ɗaya kun dame Ni, dame zanji se kace ku kaɗai ne ƴaƴa wallahi duk wanda na sake jin bakin sa sena zane shi'' ta faɗa cikin zare musu ido, USAINI dake zaune kan kujera yana danna computer yace '' kema mommy idan da sabo yaci ace kin saba da hayaniyar wa'inna ɓerayan na ki'' '' ƙyale su, baba na sena ringa zane su tunda basa jin magana musamman kai NAUFAL me taurin kan tsiya irinna baban,ku'' dai-dai lokacin SUAHAIL ya shigo farlon ''naji duk abinda ake cewa ƴaƴa na masu tauri kai irin nawa'' ya faɗa tarada Zama akan kujera gaba ɗaya sukayo kansa kowa yana so ya hau cinyar sa, ɗaukar su yayi ya ɗora su, yana musu wasa cikin so da ƙauna NIHAL da baza ta wuce shekara huɗu ba tace '' DADY gobe ina son ka Kai ni gurin wasa nayi wasa'' '' shi kenan mama na zan kai ki , shi kuwa NAUFAL cewa yayi '' DADY Ni kuma so nake ka saya min kayan wasa mota da jirgi'' an gama kaima Allah ya kai mu duk zan siya muku'' kallan MANAL yayi wadda take bawa SUHAILA nono yace '' shi kenan abinda kuke so?'' Gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin '' yesss DADY'' murmushi yayi kana yace '' to maza ku tashi kuje ku kwanata kuce yaya HASSAN yayi muku addu'ar kwanciya kunji '' to DADY seda safe Mommy seda safe suka faɗa suna barin ɗakin. Tashi SUHAIL yayi ya matsa kusa da MANAL da take ta yamutsa fuska a ranshi yace '' me hali baxe taɓa de nawa ba har yanzu MANAL bata son bawa yaro Nono'' afili kuwa cewa yayi '' maman yara dare fa yayi ya kamata muje ki kwanta nima kuma aji dani'' ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya '' wai dan Allah kai ABBEN WTO YINS baka girma da wannan abun '' ta faɗa kamar zatayi kuka '' kin taɓa ganin wanda ya gaji da raya sunnar ma'aiki nifa so nake yau ɗin nan na baki ajiyar wani BEBYN'' yasa hannu ya ɗauki SUHAILA wadda ta jima da yin Bacci ɗaki ya kaita sannan ya dawo ya ɗauki MANAL da take ta turo baki be dire ta ko ina ba se kan gado yaje ya rufe musu ƙofar sannan ya dawo kan gadon ya hau ya janyo MANAL jikin sa yana shafar bayan,ta cikin tattausar Muryar yake gaya mata kalamai masu sanyaya zuciya daga haka suka lula duniyar ma'aurata bayan komai ya lafa MANAL ta riƙo hannu sa kana tace "alhamdullih Allah Nagode maka da ka bani mijin marainiya me share min hawaye na dama ance me HAƘURI shi ke dafa dutse yasha har da roman ,sa ALHAMDULLILAH ALHAMDULLILAH ALHAMDULLILAH. INA ALFAHARI DA ZAMO WAR KA UBAN YAYA NA.
LEFIN DAƊI ƘARE WA.
Duka duka anan na kawo ƙarshen wannan littafin na RAMIN MUGUNTA ina fatan wannan yazama darasi ga ƴan baya kunga dai yanda ƙarshen Dady ya kasance sanadiyyar biyewa san zuciya da yayi da son Abin duniya harya kaisa ga aurawa ƴaƴan sa wa'inda besan ko suwaye ba bema san asalin su, ba wanda hakan yasa ya kamu da Cutar shanyewar ɓarin jiki NABILA kuma ta gamu da Cutar H.I.V, ZAINAB kuma yoyan fitsari mommy kuma Cutar farfaɗiya wannan kaɗai ya isa yasa mutum yasan cewa duniya ba mattabba bace ALLAH YA TSARE MU DA AIKATA IRIN WANNAN ZALUNCI YASA MUFU ƘARFIN ZUCIYAR MU, YASA DUNIYA TA ZAMO A HANNUN MU, BA'A ZUƘA TANMU BA
GODIYA TA MUSAMMAN A GAREKI KHADIJAH ABDULLAHI UMAR (OUM SHARIFAT) GARKUWA JARUMAI KUMA (BESTY NA🥰🥰) ALLAH UBANGIJI YA BIYA MIKI BUƘATUN KI, NA YAU DA KULLUM
DAGA
MARUBUCIYAR
1 - MATAR YARO
2 - NI DA YAYA OMAR
3 - IZINAH
4 - GANI GA WANE
5 - RAMIN MUGUNTA
6 - ƳAR SHAYE SHAYE
8 - MIJIN BERA
9 - KISHIYAR UWA CE SANADI
️ SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MAMAN HIBBA)
SHA RUBUTU..
nake cewa bissalama
ASSALAMU ALAIKUMA BAYIN ALLAH
SE MUN SAKE KASANCE WA DAKU A CIKIN WANI SABON LITTAFIN NAWA ALLAH YA ƘADDARA SADUWAR MU AMEN.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 12