dauɗa “to shi kenan idan kazo da ƴan uwan naka ka samu malam RABE shi na wakilta a matsayin wanda ze aurar da ita️”
Jama'a muji tsoron ubanguiji mu ku sani akwai mutuwa akwai kwanciyar kabari akwai hisabi
WANNAN AL-ƘALAMIN MMN HIBBA NE
RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)
WRITER
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN (MMN HIBBA)
07073193332
Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.
littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba.
GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.
NA GODE
17/18
Washe gari misalin sha ɗaya na safe SUNUSI da ƴan uwan sa suka bayyana a gidan su MANAL sun sha yadin su mamar dik ya ya muste kamar an ƙwato su daga bakin kura fuskar nan komai ba su shafa ba takalmin nan dai na jiya shi ne be canza wani ba haka aka ɗaura auran ko sadaki babu, MANAL kuwa tana ɗaki taji anɗaura mata aure da sa'an kakan ta taci kukan ta, ta ƙoshi zazzaɓi me zafi ya rufe ta daddare SUNUSI ya turo wasu dattawa sune ƴan ɗaukar amarya a cikin A daidaita suka zo jakar tsummo karanta ta ɗauka ta fito har lokacin kuka take yi , A farlo ta same su babu nasiha babu komai DADY yace. “gata nan ku tafi da ita ni dai na gama nawa na fita haƙƙin ta tin da na aurar da ita ga wanda ya fi dace wa da ita" se a sannan kukan MANAL ya ƙaru , taje gaban DADY tana roƙon sa da ya yafe mata dik laifin da tayi mai sannan taje gurin MOMY da su NABILA amma babu wanda ya tanka mata illah wani mugun kallo da suke bin ta da shi . tana kuka tana komai dattawan nan suka sata a ɗan sahun da suka zo da shi suka ɗau hanya sun jima suna tafiya sannan taga an ɗauke hanyar cikin gari an shiga cikin wani sur ƙuƙin daji doguwar tafiya kafin suka isa wani gidan jar ƙasa dik da a duhu ne hakan be hana MANAL ta ƙare mai kallo ba irin ginin nan ne na da wanda akeyi da jar ƙasa shi ma ya mutu kana iya hango na cikin gidan ɗaku nan ma ana hango su A taƙaice dai ba shi da maraba da wanda yake waje shiga cikin gidan suka yi caɓal MANAL taji ta tsoma ƙafar ta cikin ruwa wasu zafafan hawaye ne suka sirnano daga idan ta zuwa kuncin ta cikin ranta tace “ inna ilaihi wa inna ilaihi raju'un na shiga uku ni MANAL nan kuma ƙaddara ta jefo ni Allah ya sa nan ɗin ya zame min Alheri ya sa ƙarshen wahala ta ce tazo ya Allah ka ba ni ikon cinye wannan jarabawar ” ɗakin da dattawan suka shiga nan ta nufa taxo shiga ta ƙume ji kake gummm, ashe irin ƙofar nan ce ta ƙauye da seka tsuguna zaka shiga sosai ta bugu sukuwa dattawan se sannu suke rattabo mata kai kawai ta ɗaga musu.
Ƙarfe goma na dare SUNUSI ya shigo da abokanan sa se washe wargajejan bakin sa yake hakan yasa dattawan miƙewa suka yi mata se da safe. nanfa MANAL ta kuma takure wa sabon kuka ya ɓalle mata, kamar famfo yau ne ta ƙara tabbatar da maraice babu daɗi idan iyayan ta suna raye ko rasa mijin aure tayi baza su aura mata wannan tsohon ba sallamar da aka yi ne ta dawo da ita daga tinanin da take kasa amsa sallamar tayi illah miƙewa tsaye da tayi bakin ta na rawa tace. "Dr. JAMAL kai ne? ya akayi kazo nan? waya gaya ma a ɗaura min aure? ya aka yi kasan ina nan?” dariya JAMAL yayi kana yace. “ai nine na ɗaura miki auran.”
“kai ne ka ɗaura min aure ? ta yaya hakan zata faru bacin dazu aka daura min aure da Wannnan bawan Allah kuma kace kai ne ka daura min Aure plsss JAMAL me ke faruwa da ni ne ka gaya min gaskiya ina cikin Rudani ko kai ma cutar da ni zaka yi dan Allah karka min wani abu ka bar ni da tashin hankalin da nake ciki na yi ƙanƙanta da Wannan tashin hankalin.” ta karasa fada tara da zubewa ƙasa tana kuka me tsuma zuciya.
tausayin ta ya kama JAMAL tabbas ba tai ƙarya ba ta yi ƙanƙanta da kalar rayuwar da take ciki ba ko wace mace ce zata iya fuskantar haka ba tare da ta sama wa kanta mafita ba.
“ ki yi shiru MANAL ba ni da nufin cutar dake ina me miki albishir da cewa daga yau kin de na hawayen baƙin ciki se dai na farin ciki ki tsaya ki saurari abin da zan gaya miki”.
“ a hankali ta ɗago tana kallan sa kallo me cike da tambayoyi.
ME KARATU BARA KOMA BAYA DON JIN YA AKAI HAKAN TA FARU INYASO SEMU CIGABA
JAMAL yaci gaba dacewa. "malam RABE me gadi ya sanar dani cewa ƙanin mahaifin ki yana shirin aurar dake ga mutumin da yaso kuma wanda bashi da sana'a hakan yasa na samu SUHAIL da maganr bayan mun gama tattauna wa nace mai shiya kamata ya aure ki dan ya ceto ki daga wannan masifar da ake neman jefa ki cikin ta na samu malam RABE na gaya mai halin da ake ciki na kawo mai SUNUSI a matsayin shine wanda ze aure ki in da allah ya temake mu ALAJI BUKAR ya danƙawa malam RABE me gadi ragamar ɗauri auren ki hakan yasa muka yi amfani da wannan damar muka ɗaura auran wanda A zahiri muka cewa alaji BUKAR da SUNUSI aka ɗaura a baɗini kuma da YARIMA SUHAIL aka ɗaura miki aure kinji yanda abin ya kasance ”. “ƙwarai ma kuwa yarinya gaskiya ya gaya miki hatta da wa in nan tsofaffin da kika gani sun taho dake suma haya muka ɗakko su kuma wannan gidan ba gida na bane hayar shi muka yi ko da su alhaji bukarr zasu biyo mu shi yasa kika ga an kawo ki gidan nan wannan shine gaskiyar lamari kuma ba da ni aka ɗaura miki aure wannan kayan da kika gani a jiki na suma aro shi mukayi ba wai kaya na ba ne” cewar SUNUSI, cikin rawar murya MANAL tace.
“yanxu kuna nufin ni matar yarima ce? kuma ɗan sark? ko dai tsokana ta kuke yi don allah ku gaya min gaskiya karku yaudare ni idan da shi aka ɗaura min aure wannan ba damuwa bane danni bana buƙatar wasu kayan more rayuwa na san zan ƙare rayuwa ta acikin baƙin ciki mutuwa ta nake jira danna fison mutuwa akan komai”.
“haba MANAL se kace ba musulma ba biki yarda da ƙaddara bane kiyi gaggawar yin istigifari”cewar JAMAL.
" astagafirillah astagafirillah astagafirillah astagafirillah MANAL ta shiga nanatawa “SUNUSI yace "ƙwarai MANAL kuma ki gode wa allah kina da xuciyar imani da yarda da ƙaddara wallahi da wasune da tuni sun fantsama duniya Allah yana gani ba kowa ba ne ze iya jure wannan uƙubar da kika sha, dan haka ki gode wa Allah ki kuma gode wa, wa innan bayin Allah da suka tsaya kai da fata wajan ganin ba a kuma jefa ki cikin wani tashin hankalin ba daga ƙarahe dai ina miki fatan alkairi kuma insha Allahu daga yau na san kin dena wahala komai yazo ƙarshe bi ixinillahi”. daga haka SUNUSI ya tashi yayi musu se da safe hannu JAMAL ya zura a ajjihu ya ɗebo kuɗi da be san adadin su ba ya miƙa mai godiya yayi mai ya kuma yimusu seda safe.
“muma tafiya zamu yi na kaiki gidan ki kafin angwanki ya dawo ”dariya MANAL tayi dan JAMAL yabata dariya.
gida ne me kyau sosai wanda ya gaji da kyau ba babba bane sosai se dai daga gani kasan an kashe kuɗi ba kaɗan ba, hon yayi me gadi ya buɗe musu JAMAL ya cinna hancin motar ciki,
cikin gidan suka shiga dik da bawani tarkace bane acikin farlon amma yayi kyau matuƙa sosai ya tafi da MANAL ai ko ta ware ido tana kallon ko ina. " to MANAL wannan shi ne gidan ki a ciki zaki zauna har se SUHAIL ya dawo zan ringa xuwa ina duba ki fatan dai baza ki damu ba se yasa hannu a ajjihunsa ya zaro waya babba acikin kwalin ta ya miƙa mata gashi idab kin samu nutsuwa ki duba kiga tayi miki idan ba tayi ba se'a canza miki” karɓa tayi tara da yimai godiya sannan ya zaga da ita gidan ya nuna mata ko ina sannan sukayi sallama ya tafi ita kuma ta dawo ciki ta kulle ƙofa.
ɗakin da ya nuna mata a matsayin nata nan ta shiga kai tsaye wanka tayo wanda rabon da tayi irin shi har ta manta se da ta wanke lungu da saƙo na jikin ta har gashin kanta se data wanke bayan ta fito gaban mudubi ta zauna ta shafa mayukan data gani masu tsada ga ƙamashi sannan ta fesa ture cover ta buɗe taga kaya himili kuma dukka sababbi ne ɓan garan atamfofi da leshi da ban ɓan garan ƙana nun kaya daban wata rigar bacci me santsi da laushi ta saka tayi matuƙar yi mata kyau kamar dan ita akayi ta. alwala tayo ta gabatar da sallar magarib da isha'i. sannan ta haye luntsumeman gadon me laushi kamar burodi lumshe ido tayi tana jin wani sabon yanayi har ta manata raban data hau katifa wayar da JAMAL ,ya bata ta janyo ta fito da ita daga kwalin sosai wayan ya burge ta komai an sakawa wayar hatta da sim an saka mata kunnawa tayi kamar jira ake ta buɗe massage ya shigo wadda taga anyi sevin ɗin number da SUHAIL shiga cikin massege ɗin tayi ta buɗe ga abinda akace. "slm MANAL ya kike ya gida fatan kina ciki ƙoahin lfy? daga YARIMA SUHAIL.”
bata san sanda murmushi ya suɓuce mata ba se ta tsinci kanta da mayar mai da amsa kamar haka. "lafiya ƙalau fatan kai ma kana cikin ƙoshin lafiya” ta tura mai nan ta tsinnci kan ta da tina nin sa , lallai ta yarda komai lokaci ne bata taɓa tina nin zata kuma yin rayuwar jin daɗi ba bare ta kuma yin dariya da haka bacci me daɗi yayi awan gaba da ita....
MMN HIBBA✍️
RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)
WRITER
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN (MMN HIBBA)
07073193332
Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.
littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba
GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.
NA GODE.
SADAUKARWA
NA
SUDAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA UBAN GIDA NA JAGORA NA A CIKIN DUNIYAR MARUBUTA
ISHAQ NASIR ABDULLAHI (NASSURILLAH)
AL-KAIRIN ALLAH YA ISAR MAKA A DIK INDA KAKE YA KARE GABAN KA DA BAYAN KA YA RABA KA DA SHARRIN MASU SHARRI YA KIYAYE KA DAGA MUGUN JI MUGUN GANI ALLAH YA BAKA ABIN DA KAKE NEMA DUNIYA DA LAHIRA YA RABA KA DA IYAYAN KA LAFIYA.
19/20
Kiraye kirayen sallar asubah da ake yi ne ya farkar da MANAL, daga ni'imtaccan baccin data jima batayi irin shi ba banɗaki ta shiga ta dauro alawala ta gabatar da salla sannan tayi azkar kamar yanda ta saba bayan ta gama ne ta naɗe sallayar ta mai da ta ma'ajin ta ta kuma koma wa bacci se ƙarfe takwas ta tashi ta gyara gidan ko ina yayi fesss se ƙamshi da yake tashi kicin ta koma shima ta gyarashi sannan ta ɗora shayi ƙwai ta soya bayan ta kammala ɗakin ta ta koma wanka tayo ta sauya rigar baccin da take jikin ta zuwa doguwar riga wato A baya green color tayi mata kyau sosai, dik da ba wani kwalliya tayi ba man leɓe kawai ta shafa ta kalmi felet ta saka sannan ta fito farlo ta soma karya wa cikin nutsuwa take cin abincin cikin ranta tana gode wa Allah yanzu ne ta tabbatar da karin maganar gaskiya ne wadda bahaushe yake cewa mai haƙuri ya kan dafa dutse yasha har ma da roman sa sam bata taɓa tina nin zata fita daga ƙangin wahalar data shiga a gidan su se gashi Allah ya yi ikon sa a kanta, a fili tace. “alhamdulillah Allah na gode ma da ka haɗa ni da wa innan bayin naka ko ya su DADY suke? ko suna tinawa da ni? nama san ba zasu damu da ni ba tin da babu wanda ya rako ni gidan miji na ” ƙofar da ake ƙwan ƙwasawa ne ya katse ta daga tuna nin data lula miƙewa tayi taje ta buɗe JAMAL ne ta bashi hanya ya wuce . “Ina kwana Dr. ya kaje gida jiya?” ta faɗa tara da tsugunawa har kasa, murmushi, JAMAL yayi kana yace. “lafiya ƙalau amaryar mu ya baƙunta da Kaɗai ci ?”. murmushi kwai tayi gami da cewa. “Ina godiya a gare ka dakai da abokin ka Allah ya biya ku ya kai haske cikin rayuwar ku, daku da duk ahalinku Allah ya saka muku da gidan aljannar firdausi.” “Amin Amin ya Allah muma muna matuƙar godiya da wannan addu'a sannan daga yau bana so ki kuma yimin godiya Allah ne ya ƙaddara haɗuwar mu, kuma shine silar komai dan haka shi zamu gode wa ” “ haka ne Dr.” ”Zo ki ci-gaba da karyawar ki ko nine na tare miki guri?” A kunyace ta tashi ta koma kan dainin table ɗin tana shan shayin kamar me koyan sha, “SUHAIL ya kira ki kuwa?.” “A'ah be kira ba ya dai yi min massage” " “amma ya faɗa min yau da safe ya kira ki biki ɗaga ba” "da yake na bar wayar a ɗaki shi yasa daya kira banji ba” "okay idan kin gama abin da kike se ki kira shi ni zan wuce ko kina da buƙatar wani abun?" ''A'ah bana bukatar komai'' sallama yayi mata ya tafi .
yana fita kiran SUHAIL ya shigo tsayawa yayi a bakin motar sannan ya ɗaga wayar gami da karawa a kunnan sa, "wai dan Allah JAMAL me kake jira tin ɗazu baka tafi ba kabar ƴar mutane ba kaje ka duba lafiyar ta kaga a wana hali ta kwana haba meye hakan" SUHAIL ya faɗa cikin ɓacin rai, shi kuwa JAMAL be katse shi ba har se da ya dasa aya kana yace. "to ranka ya daɗe ko kuma nace baba na kagama faɗan naka ko kuma da saura?" JAMAL ya faɗi hakan cikin son ya ƙular da SUHAIL, ai kuwa ya kuma tunxura ta inda yake fita bata nan yake shiga ba, da JAMAL ya gaji faɗan nasa yace. "to tin da dik abinda nake yi maka ban birge kaba seka dawo ka kula da ita ya faɗa tarada gimtse kiran. ko kaɗan JAMAL beji haushin SUHAIL ba dan idan da sabo ya saba dariya ce ta kamashi, daya tuna abinda SUHAIL yace. "wai ya bar ƴar mutane ita kaɗai se kace wani abu ze kama ta ya lura SUHAIL ya kamu da son MANAL ba tun yau ba. “allah yasa ita ma tana son shi” JAMAL yaɗa lokacin da yayi fakin a harabar gidansu.
****
shi kuwa SUHAIL yana can abin duniya ya ishe shi shima ya san abinda yayiwa JAMAL be kyauta ba ko ba komai JAMAL abokin sa ne na haƙiƙa me ƙaunar shi tsakani da Allah amma ya iya da xuciyar sa ita ce ta axal xale shi dan yaji yanda MANAL ta kwana gashi ya kira wayan ta amma bata ɗauka ba faɗawa kan luntsume man gadon yayi wanda ya sha zanin gado na alfarma silin ɗin ɗakin ya ƙurawa ido yana tina nin mafita amma ya gaza samun mafita koɗaya dole dai ya koma wajan JAMAL ɗin iska mezafi ya furxar ya miƙa hannin sa kan allon gadon ya janyo wayarsa kira biyar yayi wa JAMAL be ɗaga ba shi kuwa JAMAL yana kallan kiran amma yaƙi ɗagawa se ana bakwai sannan ya ɗaga
babu Wanda yayi magana a cikinsu sun ɗauki kusan minti tala tin sannan SUHAIL yace. "sorry JAMAL na san ban kyauta ba amma kamin afuwa kai ma kasan ba halina bane" "ni babu abunda kamin SUHAIL kaima kasan ba zanyi fushi da kai ba kawai dai na baka lokaci ne idan ka huce kamin magana" JAMAL ya faɗa yana ƴar dariya daga nan fira ta ɓalle wanda firar tasu akan MANAL sukeyin ta cikin firar tasu ne SUHAIL ya cewa JAMAL. "wallahi ina tsoran ran da zan tunkari ME MARTABA da zan can MANAL wannan shi ne karon farko dana aika ta abu ba tara da sanin sa ba" "gaskiya ne SUHAIL ba kai bama ni kai na ina jin tsoro amma babu yanda muka iya dole mu gaya musu tunda baze yu mu ɓoye wannan maganar ba dole wataran asirin mu xe tonu in ban da abinka ai ME MARTABA yasan mahaifin ta ni A ganina baze ɗauki zafi damu ba " ajiyar xuciya SUHAIL yayi yace. "ba wannan xaka duba ba JAMAL auran da nayi batara da sanin su ba shine matsalar kasan halin me martaba idan ya ɗauki zafi" ƴar dariya JAMAL yayi kana yace. wallahi idan naga hukun cin da'ayi mana me tsauri ne zame wa zanyi in barka ko nace ban san anyi ba gaba ɗayan su suka sa dariya ƙarshe dai sukai sallama kan inya dawo zasu tunkari SARKI da maganar...
"Kwanciyar hankali da hutu yasa MANAL ta fara komawa MANAL ɗin asali kyawunta ya kuma fitowa fatar nan kamar ta jatirai dan laushi da santsi tayi ƙiba abinta ɓul ɓul kamar ba itava dirin ta da surar ta da baiwar da Allah yayi mata ta cikar ƙirji sun kuma fitowa kai hatta da gashin kan ta daya ƙuƙƙulle saboda wahala ya ware dik na mijin daya kalle ta se ya kuma kallanta kai bama na miji ba mace ma, seta kuma wai wayawa ta dube ta kullum se JAMAL yaxo ya duba MANAL tarada tambayar ta ko akwai abinda take so ga kuma wayar ta wacca take ɗebe mata kewa akai-akai SUHAIL yake kiran ta dik da bawani fira suke yi ba daga gaisuwa se ya kake,
Daga banɗaki ta fito jikin ta ɗaure da tawul ga kuma wani ahannunta tana goge jikin ta , da alama wanka tayo abinda bata taɓayi ba yau shi tayi wato kwalliya haka kurum ta tsinci kanta da tsarawa fuskar ta kwalliya ita kanta seda ta kuma duban kanta saboda kyan da tayi cover ta buɗe tana duba kalar kayan da xata sa ta jima tana xaro kayan dik wanda ta ɗakko se taga be mata ba a haka har hannun ta ya kai kan wani farin leshi me ratsin golden ajiki doguwar riga ce bubu sosai ɗin kin ya mata kyau sauran kayan data janyo ta mayar sannan ta saka kai tubarkallah masha allah kyau iya kyau gashi ɗin kin yayi mata ciff kamar dan ita akayi ɗaurin dan kwali tayi gamida feshe jikinta da turaruka masu ƙamshi wayar ta ɗauka ta koma farlo tana gemm lokaci lokaci takan ɗagowa ta kalli agogo kamar wacca take jiran wani.
Filin saukar jirage na malam aminu kano JAMAL ne tarada dogarawan masarautar zaki suna jiran fitowar SUHAIL sun jima sannan suka hango shi yana sakkowa daga sitef ɗin jirgin cike da takun ƙasaita kai daga gani sa kasan babu ƙarya ya haɗa iri da jinin sarauta yana ƙarasowa suka rungume juna shi da JAMAL sannan suka shiga mota tun a hanya SUHAIL yake tambayar JAMAL ya faɗawa MANAL yau xe dawo?" "a'ah ban gaya mata ba saboda ina so in shammace ta naga ya zata yi idan ta ganka" dariya suka sa gami da tafawa SUHAIL yace. "wallahi JAMAL baka da dama wato kaga yanda zata yi tome zata yi idan ta ganni bacin ba yau ta saba gani na ba," "dik da bayau ta taɓa ganin ka ba amma wannan shine karan farko da zaku kalli juna amtsayin miji da mataaaa" dai dai lokacin suka fito daga cikin mota bayi da ƙwarori se kwasar gaisuwa suke gami da yi mai sannu daxuwa gefe guda kuma algaita na tashi inda ake ta yimai kirari tara da yi mai barka da dawowa, kai tsaye ɗakin sa suka nufa wanka SUHAIL yayo ya sauya kayan jikin sa sannan suka tafi fada kamar yanda fadawan suka saba tashi sukayi suka basu guri JAMAL ne ya fara gaishe da me martaba sannan SUHAIL se sunne kai suke daga gani kasan basu da gaskiya, " lafiyar ku kuka zo kuka min
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 12