Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 12
nufin ban isa ince kiyi abu kiyi na san kinyi karatun addini kin san hukuncin macen da bata bin Umar nin mijinta amma shine har kike gayamin cewa wai Gwaggo ce ta hanaki zuwa kenan ita take auran ki ?'' "a'ah amma naga ita uwace a guri na idan nayi haka ba-zata ji daɗi ba seta ga kamar dan ba ita ta haife ni ba shi yasa banji maganar ta amma kayi haƙuri'' hannun ta ya kuma riƙe wa yace ''ya na iya tunda ina son ki'' bata san sanda tace ''nima ina sonka''. da sauri ta rufe fuskantar da tafin hannun ta dariya yayi yace ''me kika ce ɗan mai mai ta banji ba'' baki ta turo gaba, kana tace ''wallahi kaji kawai dai kana so na kuma faɗa ne'' ''eh naji amma sekin kuma mai mai tawa'' Ina son ka Ina son ka YAYA SUHAIL har Cikin, zuciya ta tun randa ka dawo daga na ganka naji zuciya ta ta Amin ta da kai,'' '' da gaske MANAL kina so na amma naji daɗi sosai da kema kina ƙauna ta atina nina ni kaɗai nake sonki'' murmushi ta sakar masa wanda ya bayyanar da farin ciki, hancin ta yaja yace ''yanxu ki koma kar Gwaggo ta gane ba kya nan'' miƙe wa tayi ya raka ta har bakin ƙofar yana jin wani son ta na Kuma shigar sa , tana komawa ta ta tarar da MEENA tayi shirin kwanciya ga waya akunnan ta da alama waya take yi itama kwanciyar tayi MEENA ce ta juyo ta kalle ta se wani murmushi take ita kaɗai ''Anty MANAL ina kika je tun ɗazu nake neman ki yanzu kuma kin shigo kina ta murmushi ko dai gurin yaya SUHAIL kika je ?'' harara ta jefa wa MEENA tace ''idan ma gurin sa naje ina ruwan ki naga miji na ne''''' ''iyeeeeeee lallai kema kin zama irin yaya SUHAIL yanzu babu kunya kike cewa mijin ki ne nifa ƙanwar mijin kice tamkar suruka nake awajan ki'' duka MANAL ta kaiwa MEENA ta goce tana mata dariya, kwanciya ta yi tana cewa zaki gane kuran ki.” WASHE GARI ya kama juma'a aranar ne aka kawo lefan MANAL wanda daga ƙasar India aka siyo su zo kuga kaya kamar an buɗe kantin kwari aka kira MANAL tazo taga kayan lefan ta kuka MANAL ta saka wannan kayan ko iyayan ta ne iya kacin abinda su suyi mata ke nan da kyar aka samu tayi shiru se godiya take musu. SARKI yasa aka kirawo ta yayi mata nasiha Sannan yace kar ta kuma yimai godiya in kuwa tayi yasan bata ɗauke shi a matsayin mahaifin ta ba sannan yace idan akwai abinda be mata ba ta faɗa A canza mata Kuma ta zaɓi kalar kayan ɗakin data ke so seta gayawa su Gwaggo Asiya mata ya danƙa mata sadakin ta Wanda bata san iya adadin su ba sannan ga mulkin mota ɗaya SUHAIL ne ya bata ɗaya kuma shi ya bata sannan Kilishi ita ma ta bata Sai kuma Gwaggo wacce ta zama babar amarya MANAL ita kuma ta bata kyautar GIDA dan ƙarere. Yau ne ya kama asabar kuma yau ne ran da aka shirya taron bikin, kowa mamaki yake a ina SUAHAIL ya samo matar aure A'lna ma aka ɗaura auran? dik iyakar me gulma an kasa gane kan zaran duk wanda ya tambayi me martaba se yace ƴar ɗan uwan sa ce daga haka kowa yaja bakin sa ya zuge . Biki yayi biki, bikin da ya haɗa manya manyan sarakuna da ƴan siyasa da masu kuɗi kaɗe kaɗe da bushe-bushe kawai ke tashi faɗar kyan da MANAL tayi ɓata lokacine tayi kyau iya kayu ga alkyabba da akasa mata ta fito a matar a saki seta juye ta zama jinin sarauta daloli aka ringa watsawa kai kace shara ce ko takardu ne Se yamma likisss biki ya tashi wajan ƙarfe tara na dare aka raka amarya ɗakin ta wato ɓan garan SUHAIL ƙarfe sha ɗaya abokan ango suka rako shi bayan anyi siyan baki aka ɗora da nasiha Sannan akayi addu'a kowa ya kama gaban sa aka bar amarya da ango sallah sukayi bayan sun idar ya kama goshin ta yayi mata addu'a sannan yayi mata wasu ƴan tambayoyi Game da addinin ta, ta kuma bashi amsa yanda ya kamata kajin da ya shigo dasu ya ɗakko sukaci suka kora da madara kamar kowa na angon da aka kai mai amarya ɗakin sa kuma suke raya sunnar ma aiki (s.a.w) haka suma daran ya kasance a gare su sun nunawa juna kulawa sosai SUHAIL kuwa ya godewa Allah daya mallaka mai MANAL a matsayin mata kuma ya same ta abudurwa. WASHE GARI da safe kamar yanda al-adar masarautar take farin ƙyallan da aka basu aka fito dashi kowa ya gani wannan shine shedar MANAL ta kawo budur cinta gidan miji ''MANAL MANAL MANAAL ki tashi mana gari fa ya waye ki tashi kiyi sallah'' SUHAIL ya faɗa yana yaye bargon data lulluɓa da shi shashsheƙar kukan ta yaji, dafe kansa yayi kana yace '' me kuma aka yi miki MANAL? na ce bazan ƙara ba kiyi haƙuri mana ki tashi kiyi sallah lokaci na ƙurewa '' ''bazan iya tashi ba yaya SUHAIL don Allah ka kiramin Gwaggo wayoo Allah na zan mutu'' se ta fashe da kuka me ɗaga hankali gaba ɗaya tabi ta ruɗa SUHAIL shima ji yake kamar yayi kukan fita yayi cikin hanzari ya nufi sashin Gwaggo kamar an wurgo shi Gwaggo kizo dan Allah MANAL ce bata da lafiya se kuka take kuma ke take kira hankali tashe, Gwaggo tabi bayan shi yanda yabar ta haka suka zo suka sameta se yanzu hankalin Gwaggo ya kwanta dan ita atuna nin ta MANAL ɗin bata lafiya ne ashe ciwon da kowace mace take ji ranr daran ta na farko dan haka Gwaggo tace ya fita ya basu guri da kyar ya fita bayan fitar sa Gwaggo ta shiga bayi ta cika baf ɗin ruwan zafi Sannan tace ta shiga ƙara ta saka tana yarfe hannu ahaka har seda ta sauya mata sau uku sannan ta haɗa mata me tirarakan jiki tawshiga bayan ta gama mata wannan tasa aka kawo mata madara ta haɗa mata da wani magani wanda ze sassauta mata zafin da takeji tace ta kwanta ta huta bayan fitar Gwaggo SUHAIL ya shigo kan gadon ya hau tara da kamo hannun ta yana kallon fuskan ta ''sannu ko ya jikin naki'' tashi tayi zaune ta ɗora kanta a, kafaɗar sa ''da sauƙi'' shafa kanta yayi gamida ''to Allah ya ƙara sauƙi dana san haka zata faru da ban zo inda kike ba ji nake kamar ban kyauta ba” Cikin shagwaɓa tace. ''habaaa yaya SUHAIL kai ɗin fa miji na ne kuma Allah shiya halasta yin hakan tome zesa kace haka wannan ai ba abun damuwa bane kuma haka kowace mace take tsintar kanta ran daranta na farko idan har ta riƙe Mutun cinta ni dai ina alfahari da kai kai ɗin jarumi ne ta ko ina'' ta faɗa tarada rungume shi shima rungume ta yayi nan suka lula duniyar masoya. MMN HIBBA✍️ RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba_ GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE 23/24 GIDAN ALHAJI BUKAR. Tin bayan barin MANAL daga gidan suka buɗe, sabon shafin rayuwa sun manta da wata MANAL karan su suke ci babu babbaka kuɗi kuwa kamar yayi mosu suke yi an samu dukiyar marainiyar Allah anata ci, NABILA ce ta fito daga cikin gidan tara da wani mutum babba kuma baƙiƙƙirin yake kamar gawayi amma me kuɗi ne na gasken gaske idan ba kuɗi ba babu abinda ze sa NABILA ta bashi fuska wajan da yayi fakin ɗin motar sa suka, nufa wata jib gegiyar mota cd mai numfashi ita kanta NABILA bata taɓa ganin Irin ta ba. Cikin kwar kwasa da yauƙi gami da yin fari da ido tace'' yanzu beby se yaushe zaka dawo kasan bana son kayi nesa dani ji nake kamar bani da lafiya'' ta ƙarasa faɗa cikin shagwaɓa. ''haba swet ki kwantar da hankalin ki, mana sati biyu fa kawai zanyi sannan inna dawo za'ayi maganar auren mu, danna gaji da zama babu aure ''to Shi kenan seka dawo ɗin pls ka kula min da kanka kaji beby'' mota ya shiga ya ɗakko wata ƴar ƙaramar akwati ya miƙa mata yace ''ga wannan kiyi mane ji dasu kafin na dawo'' karɓa tayi ta sunkuyo kanta dai-dai kuma tunsa tayi mai kisss wani jaɓarrrrr yayi a motar yana lumshe ido, wai shi yaji daɗi ''shi yasa nake so ayi maza-maza a bani ke dan kin haɗa komai da nake buƙata ta fannin ƴa mace'' dariya tayi mai shi kuma ya tada motar ya fita suna ɗagawa juna hannu. ''mommy mommy zo kuga Abin arziƙin'' da sauri mommy ta fito tana cewa ''kar dai kice harya tafi Allah yasa dai ya baki kuɗi masu yawa'' ta faɗa sa'ilin data zauna akan kujera buɗe akwatin tayi sega kuɗi fal akwatin kuma ba nera bace daloli ne jikin mommy har rawa yake, saboda murna bandir ɗaya ta dauka tana wul wulasu kana tace ''NABILA yanzu ne kika samu mijin da ya kamata ki aura dama wannan ranar nake jira kuma gashi tazo dan haka ki ce mai ya turo da maga batansa kawai ayi magana babu ruwan mu da koshi waye mu dai kuɗi k muke so kinga se a haɗa dana ZAINAB a yi mun huta dukiyar mu zata kuma haɓaka kina auran me kuɗi ita ma ZAINAB tana auren me kuɗi kai Allah Nagode maka, ƴaƴa na masu farin jini ga ƙashin arziƙi''' hhhhhh suka sa dariya NABILA tace '' mommy shi ma seda yayi min maganar yanzu yace shi baya so aja lokaci'' to mu meya ruwan mu ko yanzu ya fito bashi ke, zamuyi India da wannan ai bamu da matsala ta faɗa tana karkaɗa bandir ɗin dalolin dake hannun ta. Daddare ALAJI BUKAR ya dawo Bayan ya gama cin abinci mommy ta kawo mai kuɗin da saurayin NABILA ya bata ta ɗora da faɗin "kuma yace inya dawo ze aiko da manyan sa ayi maganar bikin su ," washe baki Dady yayi yana ɗaga kuɗin yace '' ko yau yace a ɗau musu aure da ita ai bashi ita zanyi me za mu, tsaya jira muga samu muga rashi" '' nima haka nace kaga faɗuwa tazo dai-dai da zama se ahaɗa dana ZAINAB'' cewar mommy. jin jina, kai Dady yayi alamar gamsuwa da maganar ta, "kaga tunda wannan shegiyar yarinya ta bar gidanna muke, ta samun alkari dama na gaya maka kasan yanda kayi da ita idan ba haka ba wallahi muda ci-gaba se dai muga ana yi yanzu gashi duk yaran mu, sun samu mazajan aure masu kuɗi na kere sa'a''. taɓe baki ALHAJI BUKAR ya yi kana yace ''ni fa wallahi na manta da wannan ƴar iskar yarinyar kuma banaso a dinga tuna min da ita taje can ta ƙaraci Iskan cin ta,'' kamar yanda saurayin BABILA ya faɗa in ya dawo ze aiko iyayan sa hakance ta kasance suka zo akayi magana saboda tsabar idon su ya rufe basu tsaya binciken ko shi waye ba, daga ina yake suwaye iyayansa. sati biyu aka saka Kuma yace karsuyi komai na kayan ɗaki shi zeyi NABILA kawai yake so akawo masa ko tsinke kar akawo ta dashi murna da farin ciki suka mamaye su, ita ma ZAINAB haka nata saurayin yace shi ze mata komai su ZAINAB da NABILA se gyaran jiki akeyi inka gansu kamar ka sace su, dan kyau tun ranar Laraba aka fara biki kuma duk fita akeyi tunda aka fara bikin ba'a liƙa nera ba Daloli kawai ake amfani dasu mommy kuwa se fan kama take cikin ƙawayan ta tana homa yaran ta sunyi dacen mazaje masu kuɗi se bisha sha akeyi da kuɗi kamar ba'a so Raƙuma da shanu aka yanka na girkin biki Banda naman kaji wanda akakai aikin su wajan masu girkin abincin biki ko suna Yau Lahadi kuma yaune aka ɗaurawa su ZAINAB aure akan sadaki masu tsoka NABILA akan sadaki million hamsin ZAINAB kuma million tala tin bayan ɗaurin aure duk wanda ze tafi se anbashi jaka wanda aka manna hotan amare da angwaye ajiki kayan ƙwalma da ma kulashe ne aciki se kuma tsabar kuɗi nera duba ashirin haka aka ringa rabawa duk wanda suka halarci bikin maza da mata shaɗaya na dare angwaye suka turo moto cin ɗaukar amare domin kai su gida jansu dik cikin motocin babu motar ƙasa da million ashirin se walainiya suke da ɗaukar ido haka akasa kowacce amota domin kaisu gidan jansu... MASARAUTAR ZAKI A ɓan garan amarya MANAL soyayya kawai suke sha ita da mijin ta SUHAIL gaba ɗaya ta miƙa masa kanta se yanda yayi da ita kulawa da soyayya kawai suka sani basu san wani abuba waishi ɓacin rai. MANAL ce a kicin tana ƙoƙarin ɗora grlirki SUHAIL ne ya shigo kicin ɗin bayan ta ya zagaya ya ruƙo kugun ta ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yace ''ni gaskiya ina buƙatar mata ta a kusa dani plsss ki ajiye wannan girkin kiji dani'' ya faɗa yana turo hannunsa cikin rigar ta. Juyowa tayi suka fuskanci juna tace ''wallahi kafiya ta kura fa baka barina na huta ko kaɗan tunda garin Allah ya waye kake abu ɗaya kaƙi bari in ɗora mana abinci rana ko sokake ka maida ni, fanko ne''? ta ƙarasa maganar tana jan hancinsa taɓe baki yayi kamar ƙaramin yaro yace. '' koma me zaki ce se dai kice Ni na san ba daga ni bane daga ke ne ke ɗin ta musamman ce'' hannu ya kai ya kashe gass ɗin data kunna batai aune ba taji yayi sama da ita wutsil-wutsil ta soma yi ''da Allah ka sauke ni babu inda zani mutum se kace doki kai baka gajiya da abu ɗaya'' be ajiye ta ko ina ba se kan gado hararar wasa ta sakar mai shi kuwa dariya ya mai da mata. a haka ya soma sarrafa ta har samu gamsuwa kwanciya ta yi ajikin sa tana ta zuba mai shagwaɓa shi kuma yana aikin rarrashi har suka yi wanka MANAL bata dena kuka ba daya gaji se cewa yayi ''wallahi in biki yi min shiru ba sena ƙara'' wata uwar harara ta banka masa tace ''aikuwa da ni da kai har abada kona gudu wajan Gwaggo'' ta faɗa tana murgu ɗa ɗan ƙaramin bakin ta, hannu ya kawo xye buge bakin ta goce tana turo baki shi ''wallahi yau se nayi maganin bakin nan mara kunya sena hukunta shi ya faɗa tarada miƙewa yana binta da gudu, MANAL tayi farlo aikuwa ya biyo ta suka ringa zagaye ɗakin ganin da gaske so yake ya kamata seta fita waje tayi sashin KILISHI wato mahaifiyar sa, shima kuwa ya bita duk inda sukai se an bisu da kallo kowa yana sha'awar su, wasu ma dariya sukeyi wai yau SUHAIL ne yake gudu yana bin matar sa ?.kamar anjefo ta ta faɗa dakin bayan ANNAH ta ɓuya se haki take '' a'ah MANAL Lafiya kike wannan uban gudu haka ke dawa ?" Kafin MANAL tayi magana SUHAIL ya shigo ɗakin shima yana haki, ''wayyoooooo Allah ANNAH kiyi mai magana don Allah karya duke ni,'' se ta ƙanƙame ANNAH. yarinya gwara ma ki fito dan babu abinda ze hanani dukan ki ba dai junin ki rashin kunya ba to daga yau baza ki kuma murguɗa wa kowa wannan bakin ba'' ya faɗa yana ƙoƙarin zagayawa bayan ANNAH ''kai SUHAIL kafita idona na rufe kai Yanzu ko kunya bakaji ba ka biyo ta kuka keto gidannan kuna gudu to naga ka taɓa ta ɗin'' ''haba ANNAH ya zaki goyi da bayan ta bacin itace bata da gaskiya'' ya faɗa kamar xeyi kuka ita kuwa MANAL se xuro kai take tana masa gwalo. tsaki yayi sannan ya fita yana gun guni bayan fitarsa ANNAH ta dubi MANAL kana tace '' Idan kika kuma tsokano shi bazan hana shi dukan ki, ba dan SUHAIL baya kunyar dukan ki ze yi ba, shi kamar ƙaramin yaro haka yake'' baki MANAL ta turo gaba tace ''ni wallahi babu abinda nayi mai kawai dai muguntar sa, ce ta motsa'' na dai gaya miki dan haka fito min daga baya duk kinbi kin yamutsa min kaya. MANAL bata bi takan ANNAH ba ta ɗauki furar data gani kusa da ita tasha nono se ƙamshi take nan MANAL ta gyra zama ta fara antawa Cikin ta tana yi tana lumshe ido, ''hummmmmm wannan yarinya da fi'ili kike naga ca kika yi baki shan fura yanzu kuma me ya haɗa ki,da ita har kike zalama haka?'' "uhum uhum ''nima ban san ya aka yi ba naji ina son sha kuma in ban sha ba ba zan iya sukuni ba'' taɓe baki ANNAH tayi tace ''kya ji da shi uwar tsugudidi'' To, rayuwar MANAL acikin gidan mijin ta rayuwa ce me tsaf ta gaskiya da ruƙon amana duk abinda take so se an mata tayi kyau tayi ɓul-ɓul da ita tayi ƙiba tayi fari fatar nan kamar ta jarirai SUHAIL na iya ƙoƙarin sa Wajan faranta mata yanda ya kamata. Cikin dare MANAL zazzaɓi me zafi ya rufe ta wanda dama tun jiya yake nuƙur ƙasar ta daurewa kawai take yi can Kuma ta ringa kyalaya amai hankalin SUAHAIL ya tashi kan kace me har ta gala ɓaita bata ma san wanda yake kanta gashi duk ta ɓata ɗakin da amai SUAHAIL ya rasa ya zeyi fita yayi harya doshi ɗkin Gwaggo seya tuna yau itace da girki ɗakin ANNAH ya shiga ya tarar tana bacci tashin ta yayi ya gaya mata abinda yake faruwa tara suka taho suka tarar da MANAL kwance kamar gawa bata ko motsi ''innalillahi wa'inna ilaihi raju'unnn MANAL MANAL me ya sameki dan Allah ki tashi karki tafi kibar ni wallahi bazan iya rayuwa da wata mace ba idan ba ke ba'' cewar SUHAIL yana share ƙwalla ruwa ANNAH ta ɗakko a firixa ta juye mata shi ajikin ta, ajiyar zuciya, tayi wata robar ruwan ta ɗakko ta miƙawa SUHAIL tace "ungo wannan idan kaga tayi irin haka ka zuba mata ni zan koma na ɗakko ta kalmi se mutafi asibiti'' karɓar robar ruwan yayi ita kuma ta fita ƙura mata ido yayi baya ko ɗif tawa gani yake idan ya ɗauke idonsa ze iya rasa MANAL ɗin sa, Kafin ANNAH ta dawo ai harya cicciɓo MANAL a bakin ƙofa suka ci karo kawai se ta juya suka shiga mota da kanshi yake tuƙin ga masu gadinsa na biye dasu awata motar Lokaci-lokaci ya kan waigo yaga yana yin jikinta sosai yake gudu kafin su isa ya kira JAMAL awaya kuma akayi Sa'a yau aikin dare JAMAL yake yi suna zuwa aka kaita Emergency aka fara bata agajin gaggawa dirip a kasa mata domin ta jigata sosai gashi tayi amai yafi a'irga wajan rabin awa JAMAL da sauran Dr. cin suke kanta bayan gwaje-gwaje da akayi aka tabbatar da MANAL tana ɗauke da juna biyu na tsahon sati huɗu wanda hakan yayi dai-dai cikar satin bikin su huɗu a ranar da aka kaita tasamu Cikin. Bayan sun gama komai kuma har ta dawo hayya cinta suka fito inda suka tarar da ANNAH da SUAHAIL a inda aka ta nada cikin hanzari SUAHAIL ya nufo inda JAMAL yake itama ANNAH ta biyo bayan shi dan san sanin awana hali MANAL take ciki '' JAMAL me ya ke damun ta? ina fatan dai yanzu ta dawo hayya cinta?'' cewar SUHAIL yana kallon JAMAL dan jin mexe ce ''ka kwantar da hankali ka, SUAHAIL babu abinda yasa meta kuma taji sauƙi sosai yanzu ANNAH ki shiga ki zauna agurin ta kai, kuma ka biyo ni Office zamu yi magana ɗakin ANNAH ta shiga su, kuma suka tafi Office ''zauna mana SUHAIL muyi magana seka ce wanda ake min tsini'' ''kaga JAMAL ba zama bane ya kawo ni ka gaya min abinda yake damun mata ta'' dariya JAMAL yayi, kana yace ''idan kuma naƙi faɗa maka fa me zaka yi kaga SUHAIL in zaka zauna muyi magana ka zauna dan wallahi bazan gaya maka ba kana tsaye se kace wanda ya haɗiyi muciya'' tsaki SUHAIL yayi sannan ya zauna shi kuwa JAMAL zama ya gyra kana yace ''albishirin ka, ''goro'' ya bashi amsa ata kai ce. JAMAL ya kuma cewa ''fari ko jah'' wayyo Allah SUHAIL ji yayi kamar ya rufe JAMAL da duka amma ya daure dan yasan halin JAMAL idan zasu shekara to seya amsa masa tambayoyi Sannan ze gaya mai abinda ke damun MANAL dan haka yace ''fari kal-kal'' murmushi JAMAL ya kuma yi kana yace ''MANAL ɗinka tana da juna biyu'' kamar wani dolo haka SUAHAIL ya ringa bin Jamal da kallo bakin sa har rawa yake wajan faɗin ''da da dan Allah JAMAL da gaske kake MANAL na da ciki'' ''ƙwarai ma kuwa SUHAIL matar ka nada juna biyu na tsahon sati huɗu ina taya ka, murna aboki na Allah yara bata da shi lafiya'' SUHAIL sauka yayi Daga kan kujerar da yake ya kai goshin sa , ƙasa yanawa Allah godiya sannan ya tashi ko sallama be yiwa JAMAL ba ya fita ɗakin da aka kwantar da MANAL ya shiga lokacin tana zaune tana shan furar da ANNAH tasa aka kawo mata sabida bata son komai idab ba fura ba. tunda ya shigo ya kafe ta da ido baya ko ƙif tawa ƙarasawa yayi ya zauna akan gadon yana kallon furar data kesha kanta ya shafa kana, yace ''beby na ina godiya agare ki, da irin wannan kyautar da ki ka min naji daɗin haɗuwa dake seya shafa fuskar ta zuwa wuyanta. Ture hannun sa tayi, ta

Chapter 8 of 12