ango kenan, sai ƙyallin amarci kake, gashi kuma kasha kyau"
Ƴar ƙaraman tsuka Zaid yayi, haɗe da wurgawa Abid harara.
"Nifa banason Iskanci, wallahi idan kasake ka kunnani, babu inda zani!" yaƙare maganar aɗan ƙufule.
"Sorry abokina, muje ko" Abid yafaɗi haka yana me tashi tsaye.
A motar Abid suka tafi, Abid ne ke jan motar, sai jan Zaid da hira yake, shi dai Zaid shiru yayi masa, haɗe da lumshe idanunsa, taya zai fassara abun dayakeji akanta?
Suna isa ƙofar katafaren gidan, Abid ya tsai da motarsa, haɗe da juyowa ga Zaid, hanunsa ya ɗaura akan na Zaid, cike da kulawa yace.
"Kamar yanda na faɗama tun a farko, tabbas saika daure, nasan kanajin ciwo, amma dan Allah karka cigaba da sanya, kanka acikin damuwa, basai na faɗa maka ba, nasan kasan cewa, akwai haƙƙi, da kuma alhakin Zahrah, dake bibiyarka, haka kuma idan har ka cutar da Afra, Allah Bazai barkaba, haka kuma haƙƙinta ma dake kanka, bazai barka, kayi rayuwa, me daɗi ba, please Zaid kayi controll ɗin kanka kaji!" cike da lallashi Abid ya faɗi maganar.
Ajiyar zuciya, Zaid ya sauƙe, haɗe da jinjina kansa, alamar yaji, buɗe murfin motar yayi ya fice, saida Abid yaga shigan Zaid gida, kafun ya tada motarsa yabar ƙofar gidan.
Tana zaune a falo, sanye take da riga da sket na kanti, gaba ɗaya tayi wani irin rama, duk da cewa dama tun asalinta, ba ƙiba gareta ba, haƙiƙa tana cikin damuwa, kwananta biyu kenan, bataji koda motsinsa bane, duk da cewa tana mejin tsoronsa, amma kuma tana buƙatar ganinsa, da sallama ɗauke a bakinsa, ya shigo cikin falon, Afrah najin sallamarsa, tayi saurin ɗago da kanta ta kalleshi, kallo ɗaya yayi mata ya kau da kansa.
Ƙarasowa cikin falon yayi, haɗe da zama akan kujera, cike da girmamawa, Afrah ta gaidasa, haɗe dayi masa sannu da zuwa.
Babu yabo ba fallasa, ya amsa mata, shiru ne yashiga tsakaninsu na ƴan sakanni.
Ƙirjinta na bugawa tace "Me za'a kawo maka?"
Kallonta yayi naɗan sakanni, da ƙyar ya iya buɗe bakinsa yace
"Kawomin Ruwa"
Jikin Afrah na tsuma, ta miƙe don kawo masa ruwa, kamar yanda ya buƙata.
Ruwan Faro takawo masa haɗe da ɗan ƙaramin glass cup, har ƙasa ta durƙusa ta aje masa ruwan, a gabansa.
Ɗaukan goran ruwan yayi yakai bakinsa, saida yasha fiye da rabin ruwan, kafun ya aje goran yana shirin miƙewa tsaye ne, yaji Afrah tasanya hanu ta kama ƙafansa, fuskarsa ɗauke da mamaki, ya juyo da kallonsa gareta, gani yayi fuskarta, tayi chaɓa chaɓa da hawaye.
"Dan Allah Kayi haƙuri, kada kajuyamin baya, inason nayi zaman aurena cikin salama, idan baka yafeminba, bazan taɓa jin daɗi ba, wallahi ƙaddarata ce tazo a haka!" kukane yaci ƙarfinta.
Wani irin tausayinta ne yakamashi, "Gwara taki ƙaddaran, tazo miki da sauƙi, akan tawa ƙaddaran" yafaɗi haka acikin zuciyarsa.
Hanunsa yasanya, ya kamo kafaɗunta, ya ta data tsaye.
"Ya isa haka, kidaina kukan nan banaso yana samin headache, kinci abinci ne?"
Kanta ta girgiza alamar "A'a"
"Okay, kinada abun da zakici ne ko kuwa?"
"Eh inadashi, na dafa abinci ɗazu"
"kici abinci!" yafaɗa ataƙaice, yana me nufar hanyar ɗakin sa.
Daɗine yakusa kashe Afra, sam bata tsammaci kulawa, har haka daga gareshi ba.
Zaid kuwa yana shiga cikin ɗaki, ya cire rigar dake jikinsa, ya wurga cikin wani dustbin, ɗin aje kayan wanki, yana shirin cire belt ɗin wandonsa ne, yaji anayi masa knockig ƙofarsa, wani irin haushine ya kamasa, a hasale ya nufi wajen ƙofar don ganin waye.
Yana buɗe ƙofar sukayi ido huɗu da Afrah, sai da taji gabanta ya faɗi, musamman da ta ganshi a tuɓe, amma kuma dolenta zata kau da tsoronta.
"Meye?" yatambaya yana me ƙare mata kallo.
"Ammm... dama abincine nakawo maka" tafaɗa tana me kallon plate ɗin dake riƙe a hanunta.
"Banaci!" yafaɗa ataƙaice yana me yunƙurin rufe ƙofar ɗakin nasa.
Dasauri ta kutsa kanta cikin ɗakin, cike da mamaki yake kallonta.
"Dan Allah kaci, kada kacemin a'a, Dan Allah!" tafaɗi haka tana me langwaɓar da kanta gefe, take idanunta sukayi rau rau dasu, da'alama kuka take son yi.
Ajiye abincin anan, yafaɗa yana me nuna mata kan sofa, cikin jin daɗi ta aje abincin, harta juya zata fita kuma, saita tsaya, haɗe da dawo da kallonta garesa. "Kayi haƙuri, ko badanni ba, kaci abincin" juyawa tayi tacigaba da tafiya, hartakai bakin ƙofar fita Zaid yace
"Afra"
Juyowa tayi garesa, ƙwalla yagani kwance acikin idanunta, da hanunsa yayi mata nuni alamar tazo, kanta aƙasa hartaƙaraso gareshi, domin gaba ɗaya, yacika mata idanu, sosai murɗaɗɗiyar surar jikinsa, ta ƙayatar da ita.
Bata tsammata ba saiji tayi, yasanya hanunsa, ya jawota jikinsa, rungumeta yayi, haɗe da ɗaura kansa akan kafaɗanta, ya lumshe idanunsa, jikinta ne gaba ɗaya yayi sanyi, hanunta duka biyu tasanya itama ta rungumesa, ƙam, haɗi da lumshe idanunta, wani irin shauƙi ke ratsata, ƙamshin sa mai matuƙar daɗi, shi yayi sanadiyar dulmiyata cikin wata duniya....
Yana rungume da ita amma kuma zancen zuci yake.
"Tabbas, abun da Abid yafaɗa masa, gaskiyane, Afra itace matar da Allah Ya zaɓa masa kuma daidai dashi, wannan zaɓin Allah Ne, bazaɓinsa ba, kuma zaɓin Allah Yafi zaɓinsa, saboda haka, dole zai karɓi Afra amatsayin matarsa, kuma zai yi ƙoƙari wajen ganin, ya yi mata adalci, bayajin sonta aransa, amma zaiyi iyaka, bakin ƙoƙarinsa wajen ganin, yazauna da ita lafiya , idan ya rabu da ita, baisan wace buɗaɗɗiyar zai kuma samu ba, shidai yasan irin Zahrah ita kaɗaice, kuma yariga daya rasata, saboda haka dole zaiyi haƙuri da Afrah, kodan son kyautata masa daya lura tanayi"
******
Zaune take akan kujera, ta ɗaura ƙafafunta, bisa kan wani table na glass, dake cikin falin, wata ƴar ficikan riga maroon colour ne, sanye ajikinta, saman wuyan rigan net ne, yayinda hanun rigan kuwa, ya kasance na vest, wato siririn hanu, tayi kyau sosai acikin shigar nata, hanunta riƙe yake da kofi, wanda ƙe ɗauke da Banana Smothie aciki, sai kaɗa kanta take da alama, taji daɗin Banana Smothie'n da take sha, duk da cewa, har yanzu bata wani jin daɗin jikinta, amma haka ta daure, take abu kamar me lafiya, miƙewa tayi daga zaunen da take, haɗe da ƙarasawa gaban tangamemen tv plasma'n dake aje cikin falon, remote ta ɗauka, ta ƙara volume ɗin tv, ta aje remote ɗin kenan, wutan nepa ta ɗauke, gashi magriba ta somayi, ɗakin babu wadataccen haske, babu zato ba kuma tsammani, taji an sanya hanu an rufe mata idanunta, wani irin ƙara tasake alokaci guda, sai kuma ta yanki jiki tafaɗi ƙasa, da hanzari Dr.Sadeeq wanda shi yayi mata haka, yasanya hanu ya tarota tafaɗa cikin jikinsa, wayarsa ya laluɓo ya kunna torchlight, daidai lokacin ne kuma wutan nepan ya kuma, dawowa haske ya baibaye ɗakin, amatuƙar razane yashiga girgizata, yana ƙiran sunanta, amma ina ko motsi batayi ba, hanunsa yakai kan hancinta, yaji babu alamar shiga da fitar numfashi, tsorone yakamasa, haɗe da ruɗewa, akiɗime yashiga jijjigata, amma bata motsaba, saboda babu numfashi ajikin ta.....
*13/February/2020*
*✅ote me on Wattpad*
@fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Lovely Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*CHAPTER 110*
A matuƙar ruɗe yake girgizata, yana me ƙiran sunanta, sosai ya tsorita da al'amarinta, gaba ɗaya ya ruɗe, yama manta da cewa shi ɗin likita ne, sungumarta yayi acikin ƙirjinsa, direct sai cikin mota, a gidan baya yasakata, yafigi motar da wani irin gudu, saboda tsabar gudun da yakeyi, mintuna kaɗan, suka kawoshi, cikin asibitinsu, a ruɗe yaje wajan, abokin aikinsa Dr.Salim, yasanar masa abun dake faruwa, emergency aka wuce da ita direct, shikam Dr.Sadeeq kasa shiga cikin emergency room ɗin yayi, suke karɓan emergency patient idan aka kawo, amma kuma sai yau, gashi shine da kansa ya kawo, sai kaikawo yake tayi, aƙofar shiga emergency room ɗin, kwata kwata hankalinsa baya jikinsa..
Bayan Mintuna 30
Yana tsaye ajikin bango, idanunsa a lumshe suke, zuciyarsa kuwa, bugawa takeyi da ƙarfi, tamkar zata faso cikin ƙirjinsa, ta fito.
Dr.Salim da sauran doctors, ɗinne suka fito daga cikin ɗakin, har yanajin tuntuɓe, agarin saurin ƙarasawa inda suke.
"Salim ya ya take? tafarfaɗo ne? Meke damunta dan Allah? Allah Yasa tana lafiya?" Duka waƴannan tambayoyin, Dr.Sadeeq ya jerawa Dr.Salim su.
Murmushi Salim yayi, haɗe da sanya hanunsa, ya dafa kafaɗan Dr.Sadeeq.
"Haba Man, saikace ba doctor ba, duk kabi ka ruɗe, bawata babbar matsala bace bafa, kaida kanka ma zaka iya maganceta, amma duk karuɗa kanka"
Ajiyar zuciya me ƙarfi, Dr.Sadeeq ya sauƙe, sakamakon jin daɗin kalaman da Dr.Salim yayi.
"Masha Allah! kada kaga laifina, wallahi Salim, inasonta sosai ne, banason wani abu, ya sameta shiyasa" Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me lumshe idanunsa.
Murmushi Salim yayi, haɗe da cewa. "Muje office"
Babu musu Dr.Sadeeq yabi bayan Salim, suka wuce office ɗin Salim ɗin.
Suna shiga suka zauna, su dukansu akan kujera ɗaya, murmushi Salim yayi haɗe da maida kallonsa ga Dr.Sadeeq, hanu yasa ya dafa kafaɗan Dr.Sadeeq ɗin, cikin son kwantar masa da hankali yace.
"Kada ka damu Sadeeq, ba wani abu bane, tsananin tsorone kawai, ya sata suma, amma bayan haka babu wani ciwo dake damunta, sai dai naga tana da hawan jini, amma kuma gaskiya abokina, ka iya aiki, wai ma watanku nawa da aure ne yanzu?"
Harara Dr.Sadeeq, ya jefawa Salim. "Wannan wani irin iskanci ne Salim? me ya haɗa ciwonta da tambayan watannin auren mu? yanzu ba lokacin wasa bane, ina tsananin son matata, bana ƙaunar naga wani abu yasameta, idan akwai wani abu bayan wannan, ka sanar dani, idan kuma kaƙi zan bincika da kaina, daɗin abun nima likita ne" Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me ƙoƙarin miƙewa tsaye, sarai yasan iskancin Salim, iya shegensa yayi yawa, gwamma ma yaɗauki Zahrah'nsa, kawai su koma gida, inyaso shida kansa, zaiyi checking ɗinta agida, dama ruɗewan da yayine, yasanya ya kawota asibiti.
Hanunsa Salim ya riƙe haɗe da cewa.
"Meyayi zafi kuma? daga tambayar watannin aure, yanzu duk ba wannan ba, miye tukuicina wanda zaka ban, idan nafaɗama wata magana me daɗi?"
"Tukuici kuma? wace magana me daɗi kenan? nida matata bata da lafiya, har akwai wata magana da za'a faɗamin wacce zatayimini daɗi? nace maka kadaina min wasa ko Salim, yanzu ba lokacin wasa bane." Injicewar Dr.Sadeeq.
"Koma dai menene can maka, kuma tukuicina ne sai ka bani, ina tayaka murna, saboda madam ɗinka, tana ɗauke da ɗan ƙaramin ciki, na wata biyu!" Salim yaƙare maganar yana faɗaɗa fari'ar, dake kan fuskarsa.
Zama daɓas Dr.Sadeeq, yayi akan kujera, haɗe da sanya hanunsa, ya kama duka kafaɗun Salim, cike da tsananin farinciki yace "Dagaske kake Salim? Zahrah na ɗauke da ciki na ajikinta? Kafaɗamin gaskiya, dan Allah karka yaudareni!"
Dariya Salim yayi haɗe da cewa "Wallahi ba wasa nake maka ba Sadeeq, da gaske matarka, kuma Zahrah'n ka, tana ɗauke da ciki, sannan kuma yana da kyau, ka kiyaye ɓacin ranta, dakuma duk wani abu, da kasan zai sanya ta tsorita, saboda yawan tsorita zai iya haifar da zubewan cikin.."
Kafun ma Salim yaƙarisa zancensa tuni, Dr.Sadeeq ya sulale ƙasa yayi sujjada, na tsananin nuna godiyarsa ga ALLAH, Haƙiƙa ya matuƙar jin daɗin, wannan albishir ɗin da Salim yayi masa, rungume Salim yayi cike da farinciki.
"Thank you so much Salim, haƙiƙa yau kasani farinciki sosai, kuma kaima insha Allah, zan saka farinciki, ta hanyar baka tukuici, wanda zakaji matuƙar daɗinsa" yanakaiwa nan a zancensa ya sake Salim, haɗe da ficewa daga cikin office ɗin, direct ɗakin da aka kwantar da ita ya nufa.
Shigowarsa, yayi daidai, da buɗe idanunta, wani irin ƙawataccen murmushine, kwance akan fuskarsa, ƙarasowa yayi, kan gadon ya ɗagota, haɗe da rungumeta, tsam acikin ƙirjinsa, wani irin daɗi yakeji na musamman, kwanciya tayi luf acikin jikinsa, cikin muryan shagwaɓa tace.
"Hubby me mukeyi a asibiti?"
Sake matseta yayi, acikin jikinsa, haɗe da sanya hanunsa, yashiga shafa bayanta, cikin wata irin murya yace.
"Bansan dame zan iya biyanki ba Zahrah, haƙiƙa ke ta musammance, kinkawo min farinciki, na musamman, kinsani acikin wata duniya, me ɗauke da wasu surruka, wanda suke da wuyar mantawa, Inasonki My Wife! ina tsananin ƙaunarki, nagode miki sosai, Allah yayi miki albarka!" "Inaasoonki!!" yakuma faɗa, in a slow sound, yana me sumbatar goshinta.
Mamakinsa ne yacika Zahrah, ita sam bata gane me yake nufi ba, kyawawan fararen idanunta, ta zuba masa da'alamu tanason jin ƙarin bayani daga garesa.
Hanunsa yasa ya shafi gefen kumatunta, idanunsa ɗaya, ya kashe mata, haɗe da cewa.
"Verry soon, ni da ke, zamu zama parents!"
"Parents?" ta maimaita sunan abakinta, da ɗan mamaki.
"Yes, ni dake munkusa zama iyaye, saboda kina ɗauke da, ciki!" yafaɗi haka yana murmushi.
Waro manya manyan idanunta tayi, haɗe da sanya hanu ta shafi kan ɗakalallen cikinta.
"Ciki! inada ciki fa naji kace?"
"Eh kina ɗauke da cikina, yanzu haka ajikinki, saura lokaci ƙanƙani kizama mummy's boy"
Wani irin madaran farinciki ne, taji yana ratsa duk wani ƙofar sadarwa dake jikinta, ko kusa koda wasa bata taɓa, kawo hakan acikin tunaninta ba, rungumeshi ta sakeyi ƙam ƙam, haɗe da sakin wani irin murmushi, gaba ɗaya sai tanemi ciwon jikin nata ma ta rasa, "Ashe itama zata zama Mama? lallai ALLAH Abun godiya ne" tafaɗi haka acikin zuciyarta.
"Babyna mu koma gida ko?" yatambayeta, cike da tarairaya.
Dama ita uwar shagwaɓa ce, aikuwa tuni ta narke masa, haɗe da kaɗa masa kai, alamar
"Eh"
Karɓo musu takardan sallama yayi, haɗe da dawowa cikin ɗakin, ɗagata yayi caɗak, yasanyata acikin ƙirjinsa, haka yanufi ƙofar fita, daga cikin ɗakin, shagwaɓa tasakamai, akan cewa ya sauƙeta ƙasa, zata iya takawa da ƙafafunta, amma fir yaƙi, waishi bayasone ko kyakkyawan motsi tayi, bayaso tasha wahala, haka suka fito cikin asibitin, kowa sai kallonsu yake, abokan aikinsa kuwa, dariya kawai sukeyi masa, sam basuyi mamaki ba, domin kuwa duk wanda yasan Dr.Sadeeq, to yasan,cewa, yana matuƙar ƙaunar Zahrah'n shi, domin ko da yaushe sunanta, nanan raɗau acikin bakinsa.
A hankali yake tuƙa motar, tana manne ajikinsa, ji yake kamar ya maidata cikin jikinsa, wani irin sabon ƙaunarta, yakeji na huda fatarsa, yana shiga cikin jikinsa.
"Me zakici na saya miki my lovely na?" ya tambayeta, cike da kulawa.
Harshe tasanya, ta tanɗe bakinta, haɗe da cewa "Ni gurasa kawai nakeson ci, sai kuma shaka, amma gurasan, nafison wanda, aka yanka masa tomatoes, sosai asamansa" taƙare maganar tana haɗiye yawu.
Dariya sosai tabashi, yanayin yanda tayi maganar kaɗai, ya isa tabbatar maka cewa, cike take da kwaɗayin gurasan.
"Okay kome kikeso ni me samamikine, matuƙar a kwaishi acikin duniyar nan, ni dakaina kikeso nayi miki gurasan ko kuma, nemo miki zanyi a waje?"
Dariya tayi haɗe da dubansa cikin shagwaɓa tace "Kai ka iya gurasa ne?"
"Ko ban iyaba akanki ai zan koya" yafaɗi haka yana murmushi.
"Nidai banaka nakesoba, kawai ka nemomin, kuma ma ni nafison wanda akayi a gida, bawai wanda ake sayarwa a waje ba!" taƙare maganar tana me turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.
"Wannan me sauƙi ne, yanzu kuwa zan kaiki, gidan da za'a miki gurasa" yafaɗi haka yana me karya akalan motar tasa, zuwa wani hanu daban.
(Wallahi nima kwaɗayin gurasan nake😋 batun yauba, ko ta wayane, kuturomin please.😥)
Mamakine yakamata, ganin sun tsaya agaban gidan Hajiya, kallonsa tayi haɗe da zaro idanunta
"Gidan Hajiya fa, ka kawo mu" tafaɗa tana wuƙi wuƙi da idanu.
"Eh mana, kinsan Hajiya, ƙwararriya ce, wajen iya sarrafa abinci, kuma ina databbacin cewa ta iya gurasa, taso mushiga" yafaɗi haka yana me miƙa mata hanunsa, alaman takama.
"A'a gaskiya nidai mukoma gida, yanzu idan ta tambayi, DALILINA nason cin gurasa, muce mata me?"
Murmushi yayi haɗe da cewa "Baza ma tatambaya ba, ai itama tasan watarana, mutum yakan jin son cin irin waƴannan abubuwan" Da haka Zahrah ta yarda suka shiga, cikin gidan.
Suna Sallama a falon, Hajiya dake zaune, tana duba wasu lace's, dake zube a gabanta, ta amsa musu, cike da fari'a, da kuma mamakin ganinsu da tayi, domin kuwa sam bata tsammaci ganinsu, nan kusa ba, saboda basu jima da zuwa ba.
Kan Zahrah a ƙasa, ta ƙaraso cikin falon, cike da ladabi ta durƙusa, akan guiwowinta, ta gaida Hajiya.
Cike da fari'a, Hajiya ta amsa mata, haɗe da kamo hanunta, ta zaunar da ita, akusa da ita.
"Batun yauba na faɗa miki, nima uwace, ki saki jikinki dani, zanfi jin daɗin haka!" Hajiya tafaɗi haka cikin son nunawa Zahrah ƙauna.
"Nidai yanzu agidannan, ba a wani damu dani ba, idan nazo ma ba a wani bani kulawa" abun da Dr.Sadeeq yafaɗa kenan, yanayin yanda yayi maganar kamar wani ƙaramin yaro.
Dariya sosai yabawa Zahrah, ta lura shidai shagwaɓaɓɓene na ƙarshe.
"Ai ni bana yayin tsoho, idan har nasamu sabo, dama ba ɗiya mace ƙarama nake da shiba, to Allah yabani sainace banaso? kariga daka zama goɗo goɗo dakai, me zanyi dakai, ko kinga ya dace na bashi kulawa ne Zahrah?" Hajiya ta tambayi Zahrah.
Kunyarsu ne su duka yakamata, amma kuma yazatayi, Hajiya nason janta ajiki, dole itama ta sake da ita.
"A'a Hajiya, idan kika basa kulawa, zai ƙara shagwaɓewa da yawa!" Zahrah tafaɗi haka, tana me satan kallonsa, ta gefen idanunta, tasakar masa gwalo.
"To kaji abun da matarka ma tace, saboda haka, sai kayi haƙuri" inji cewar Hajiya.
"To ya na'iya, idan banyi haƙuri ba, kuma tunda kikace haka, saina gayawa Hajiya komai" yafaɗi haka yana kallon Zahrah.
Wayyo Allah, Zahrah ina ƙasa ta ɓule tashige ciki, tsabar kunya, tasani, ƙaramin aikinsa ne, ya gayawa Hajiya, cewa ta nada ciki, amma ko daya kunyatata.
Kallon tuhuma, Hajiya tashigayi musu dukansu biyu.
"Me kuke ɓoyewa?" ta tambayesu.
"Hajiya waifa kwaɗayin gurasa take, kuma wai na gida takeso, shine na kawota ki mata" Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me ƙara faɗaɗa fari'arsa.
Kallon Zahrah, Hajiya tashiga yi, na ƴan wasu sakanni, tsab tafahimci abun da take son fahimta, take wani irin farinciki, ya ɗarsu acikin zuciyarta, hakanan taji ƙaunar Zahrah, ta sake shiga zuciyarta.
"Alhamdulillah! Masha Allah!! aikuwa yanzu zakici gurasa, da kaina ma zanyi miki" Hajiya tafaɗi haka cike da tsananin jin daɗi. " Ashe dai akwai, tsananin rabo, dake tsakanin Dr.Sadeeq, da kuma Zahrah, yanzu da ace ta dage, ta kafe kai da fata, ta hanasu aure, shikenan kuma da wannan cikin, alayi za'a sameshi, daga nan kuma, ta ɓata sunan zuri'arta, domin kuwa aje azo yaro ko yarinyar da aka haifa wajensu zai dawo, tunda Sadeeq shine uban sa" Hajiya tafaɗi haka acikin zuciyarta.
Zama Zahrah tayi, acikin falon, tana me hararan Dr.Sadeeq ƙasa ƙasa, Allah ma yasota da bai ce ciki ne da ita ba, da itakam yagama kasheta, sam bata fahimci cewa Hajiya, ta gane hakan ba.
Bayan mintunan da basu da wani yawa sai ga Hajiya, hanunta ɗauke da plate, wanda ke shaƙe da gurasa, sosai yaji ƙuli, da kuma mangyaɗa, gashi an ƙawata samansa, da dangin su albasa da kuma tumatur, hadda kabeji, ga kuma cocumber, wayyo wannan gurasar fa tayi, tuni yawun Zahrah ya tsinke, haka ta shiga lasan bakinta, kamar wata mayya, ai Hajiya na aje plate ɗin gurasan, Zahrah ta jawo shi gabanta, sam tama manta da cewa Hajiya surukarta ce, hanu baka hanu ƙwarya, haka Zahrah kecin gurasan, abun daya yi matuƙar bawa, Dr.Sadeeq mamaki kenan, shidai yasanta, ita ba mutum bace, me cin abinci da yawa, hasalima idan zataci abinci, aɗan ƙaramin kwano take ɗebowa, amma yau gashi tana cin gurasa, tana wani lumshe idanunta, kamar bata taɓa, cin abinciba, haka takeyi, idanu kawai, ya zuba mata, aduk ko wani minti ɗaya ƙaunarta sake cika zuciyarsa take.
Sosai Zahrah, taci gurasan nan, sai da tajita ta ƙoshi nak, kamar tunbinta, zaiyi bindiga, kafun ta ɗauki, goran ruwan faro, takai bakinta, ajiyar zuciya tashiga sauƙewa, akai akai, kamar wacce tayi tsere.
"Sannu" Dr.Sadeeq, yafaɗa mata haka, cike da kulawa.
Murmushi tasakar masa haɗe da ɗan matsowa kusa dashi, dayake Hajiya bata falon.
"Naci gurasa saura shaka" taƙare maganar tana tanɗe ɗan ƙaramin bakinta.
Idanunsa ya zuba mata, haɗe da cewa.
"Wani irin baby ne haka na samiki, me masifar ci, da kuma kwaɗayi?"
Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da cewa.
"Wallahi inaji, idan bansha shaka ba, akwai matsala, batun yauba nake jin kwaɗayi matsananci, amma na yau ɗin dai yayi over, har inajin idan bansamu, abun da nakeso ba, bazan iya koda yin bacci ba " taƙare maganar tana me shagwaɓe fuska.
Murmushi yayi, haɗe da sanya hanu, yashafi kan kumatunta, cike da kulawa yace.
"Allah Yasauƙeki lafiya, My Acici na!"
Dariya suka saka, su dukansu biyun.
Hajiya dake tsaye, tana kallonsu, batare da saninsu ba, itama ta saki murmushi.
"Ashe da tahana Sadeeq auren Zahrah, ƙwarai da ta tauye, musu haƙƙinsu, Allah sarki, ashe suna son junansu har haka?"
Da wannan zancen zucin taƙaraso cikin falon.
"A'a Hajiyar gurasa, kin ƙoshine kodai a ƙaro miki?" Hajiya tatambayi Zahrah.
Ƙasa tayi da kanta, haɗe da cewa "Naƙoshi Hajiya, saidai zan tafi da sauran gida, saboda inaso naci kafun na kwanta"
"Wannan ai me sauƙi ne, na aje miki wani ma a kula, idan kin tashi saiki tafi dashi" Inji cewar Hajiya.
"Hajiya bakida Shaka acikin gidan nan ne? kinsanfa mutumiyar taki, kwaɗayi ta koya, yanzu kuma wai shaka take son sha" Dr.Sadeeq, ya tambayi Hajiyarsa.
"Ai kuwa akwai shaka, acikin fridge, domin kuwa jiya da dare, banajin daɗin bakina, shine na haɗa nasha, to akwai ragowan, yayi sanyi ma sosai, ae inaga" Hajiya tafaɗi haka tana me nufar wajen da fridge ɗinta ke aje.
Shaka'n ta ɗauko, ta kawowa Zahrah, wayyo Zahrah tasamu abun da takeso, gyara zama tayi daɓas, tashiga zuƙan shakanta abunta, daɗi kamar kunnenta zai fita haka takeji.
Hmmm Zahrah, dai basu bar gidan Hajiya ba, saida tayi ƙat, har guzuri, na gurasa, da kuma, kayan ƙwalama, Hajiya tayi mata, tatafi dashi, koda sukazo tafiya, Dr.Sadeeq ya keɓe da mahaifiyarsa, inda ya gayamata cewa, Zahrah na ɗauke da ciki, duk da tagane hakan, tun kafun ya faɗa mata, amma sai jin datayi daga bakinsa, yasanya taƙara jin daɗi, sosai, takuma ƙarfafa masa guiwa, akan cewa kome Zahrah takeso, yayi mata waya, ya sanar da ita, zatayi mata shi ko menene, ta bawa driver, yakai mata har gida, sosai yaji daɗin hakan...
Suna komawa gida, ta faɗa toilet, wanka tayi, kana ta ɗauro wani ɗan ƙaramin towel, wanda ya tsaya iyaka cinyarta, tafito, yana zaune akan gado, yana danna laptop ɗinsa, sanye yake da dogon wando, da kuma wata farar riga me shara shara, tana fitowa daga cikin toilet ɗin, ya sauƙe idanunsa akanta, murmushinsa dake, ƙarawa fuskarsa kyau, yayi mata, itama ta mayar masa da martani, duka hannayensa, ya buɗe mata, alamar ta taho garesa, da gangan ta yada towel ɗin, dake ɗaure ajikinta, tashiga takowa zuwa garesa, wani irin abu yaji yashiga cikinsa, take yaji wani irin sha'awarta, me tsanani ta kamasa, tana zuwa tafaɗa jikinsa, haɗe da haɗe ƙirjinsu waje guda, atare suka sauƙe ajiyar zuciya, rungumeshi tayi ƙam, haɗe da cusa kanta acikin ƙirjinsa, sosai ƙamshin turarensa, keyi mata daɗi fiye da da.
Bakinsa ya ɗaura akan wuyanta, haɗe da manna mata wani irin hot kiss, hanunsa yasanya duka biyu, yana shafa bayanta, cikin wata irin murya yace.
"Idan naganki da kaya, nakan rasa nutsuwata wani lokacin, yanzu kuma da kikazomin a haka, so kike na haukace miki ko Baby?" yaƙare maganar yana me sake cusa, kansa acikin wuyanta. Hanunta ta nutsa acikin gashin kansa, yayinda take ya mutsa gashin nasa a hankali, kansa ya maida kan ƙirjinta, inda ya sauƙe bakinsa atsakiyan ƙirjinta, wato tsakankanun breast ɗinta kenan, lasan wajen yakeyi a hankali, yana me shafa kan mararta, lumshe idanunta tayi haɗe
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 41 Chapter of 47