Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na zuciyarta, tunani take taya zataje ta tunkari ƴar uwarta Hajiya Furaira da wannan maganar, tasan Hajiya Furaira macece mai zafi, bazata taɓa son hakan ba, domin saboda bala'inta da zafin kishin ta, ne ma yasanya mijinta haryau yakasa ƙara aure bawai kuma don baya so ba, to ina kuma da idan taji cewa ƴarta ɗaya tilo zata haɗa miji da wata daban wacce bata da galihu, gaskiya zaiyi wuya ta amince... Haka dai Hajiya tadinga saƙawa da kuncewa daga ƙarshe ta tashi ta wuce ɗakinta.... Cikin matsanancin farinciki Dr S.S ke kallon Baffa Amadu sakamakon jin cewa wai mahaifiyarsa ta amince da aurensa da Zahrah, masha Allah ashe dai mafarkinsa zai zamanto gaskia, sai dai kuma farincikin nasa bai zama cikakke ba, domin kuwa sosai maganar haɗa auren Zahrah da Salima ya daki zuciyarsa, saboda shi a tsarin sa baida burin aje mata biyu acikin gidansa. "Yanaji kayi shiru ne Sadeeq, ko baka amince da sharaɗin mahaifiyartaka bane?" Baffa Amadu yatambayeshi cike da kulawa. Kansa yashiga sosawa yamakasa ce da Baffan nasa komai.. Murmushi Baffa Amadu yayi domin yafahimci halin da Sadeeq ɗin yake ciki. "Kada ka ɗaga hankalinka Sadeeq, atunanina ka kai namiji wanda zai iya riƙe mace sama da biyu, don haka wannan ba abun damuwa bane, kayarda da sharaɗin mahaifiyartaka, addu'anmu shine Allah yatayaka riƙo, yakuma baka dama da ikon yin adalci a tsakaninsu, yanzu yaushe kakeso muje gidansu ita yarinyar?" Gaba ɗaya jiyayi jikinsa yayi sanyi, zuciyarsa kuwa jiyayi tayi masa wani iri. "Zansanarda Baffan yarinyar idan yafaɗamin ranan da zakuzo, saina faɗa maka" inji cewar Dr Sadeeq.. "To shikenan Allah yakaimu" daga haka sukayi sallama, Dr S.S yabaro gidan Baffa Amadu zuciyarsa cike da tarin tunani kala kala, yana farincikin cewa Zahrah zata zamo matarsa, amma kuma ta wani ɓangare na zuciyarsa kwata kwata bayajin daɗi. Zahrah tana buƙatar farinciki da kuma kulawa mai kyau, baikamata ace anraba mata farinciki ita da wata ba, to amma "Miye mafita?" yatambayi kansa, bayan yasan baida amsar tambayan nasa, amma koma dai mene ayau zaije yasamu Baffa yasanar dashi cewa yana neman abashi izini yaturo magabatansa don abasa auren Zahrah, yakuma ƙudurta aransa cewa, dakansa zai bada order a Dubai, na kayan lefen Zahrah, domin kuwa zaiyi rawar gani sosai, wajen ganin komai na Zahrah yafita da ban.... Amatuƙar mamakance Alhaji Ma'aruf ke kallon Zaid wanda yafaɗi maganar daya matuƙar basa mamaki.... "Aure fa kace Zaid, dagaske kake, yanzu kashirya zakayi aure?" "Da gaske nake Dad aure zanyi, kuma inaso kaje da kanka ka tambayamin, banaso auren yawuce nan da sati biyu Dad" Cike da tsananin farinciki Alhaji Ma'aruf yace "Alhmdlh! naji daɗi ƙwarai da gaske, domin zuwa yanzu yakamata ace ka aje iyali, insha Allah, zan je na tambaya maka aurenta, ƴar wayene kuma a ina take?" "Ba ƴar kowa bace Dad, talakawa ne ma, amma ni ahaka naji na aminta ina kuma son na aureta" yafaɗi haka da iyaka gaskiyarsa.. Jinjina kai Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da cewa "Zan sa rana sainaje naga mahaifinta" "To" kawai Zaid yace haɗe da tashi yabar falon Dad ɗinnasa.... Fitowarta amakaranta kenan, tana sauri ta samu abun hawa, don bata son tsayuwa a bakin makarantar, kasancewar Dr Sadeeq aiki yamasa yawa bazai samu daman zuwa ɗauko ta ba... Wani matashin saurayine yanufo wajenta, hanunsa ɗauke da wani babban kwali wanda aka rufesa da wani irin abu mai kyau, aka kuma ƙawatasa da flower mai walwali.. "Ranki ya daɗe barka da yammaci" saurayin yafaɗa. "Yauwa barkan ka dai" itama ta mayarmasa amsa cikin ɗari ɗari dashi.. "Saƙo aka bani nakawomiki" yafaɗi maganar yana me miƙa mata kwalin dake hanunsa.. Cikin mamaki Zahrah ta shiga kallon saurayin nan dake tsaye a gabanta.. Murmushi saurayin yayi mata haɗe da sake miƙo mata kyakkyawan gift ɗin dake hanunsa. "Waye ya aikoka?" tayi masa tambayar cikin dakiya... "amsar tambayarki duka suna cikin nan" yaƙare maganar yana me nuna mata kwalin dake hanunsa. Hakanan taji zuciyarta ta aminta da ta karɓi saƙon.. Hanu biyu tasa ta karɓa, batace dashi komai ba tayi wucewarta dai dai lokacin mai taxi ya ƙaraso tashiga. Tsurawa kyakkyawan kwalin idanu tayi, sosai adon jikinsa yayi kyau haɗe da ɗaukar hankali, gaba ɗaya ta ƙosa, tabuɗe kwalin don ganin ko wanene yake son yin wasa da hankalinta, ta hanyar turo mata da saƙonni, batare da yabari tasan kowaye shiɗin ba. Tana shiga gida direct ta wuce ɗakinta, ko mayafinta bata cire ba, ta zauna haɗe da soma yaye ledan da akayimawa kwalinnan ado dashi, tana buɗe kwalin tayi arba da wani ƙatuwar ta karda wanda aka naɗeta, cikin sauri ta ɗago takardan haɗe da soma warwareta, amatuƙar razane tayi wurgi da takardan sakamakon idanunta da sukayi mata tozali da zanen hoton dake jikin takardan. (🤔Ga Zaid ga Sadeeq ko waye cikinsu zai mallaki Zahrah🤷‍♀) *17/December/2019* *Follow me ...* *Wattpad user name* *@fatymasardauna* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *SHU'UMIN NAMIJI!!* *Written By* *PHATYMASARDAUNA* _(Shalelen Kainuwa)_ *Dedicated To My Brother KHABIER* *🌈Kainuwa Writers Association* {United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers} *https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation* *WATTPAD* @fatymasardauna *Editing is not allowed📵* *CHAPTER 61 to 62* Idanu ta ƙara zarowa domin tabbatar mawa kanta cewa abun da tagani gaskiya ne, ko kuwa, gizo idanunta keyi mata. Tabbas dagaske ne bawai gizo bane, hoton zanen fuskarta ne raɗau ajikin takardan. Hanunta na rawa haka ta durƙusa ƙasa, haɗe da sanya hanu ta sake ware takardan, tabbas itaɗince babu ko kokonto, zanen fuskarta ce kwance ajikin takardan, amma saboda tsananin kyawun da zanen yayi tamkar azahiri haka zaka gani, hanu tasanya ta shafi zanen, cike da fargaba haɗe da ɗaurewar kai. Lallai yazama dole a gareta tanemo wanda yake aikata mata waƴan nan abubuwan, kusan kwana uku yanzu kenan ana turo mata da saƙonni, bata kuma san daga waye bane. Bata damu da ta duba sauran kayan dake cikin kwalin ba, ta tattara shi ta ɓoye acikin kayanta. Zama tayi dirshan akan katifa tana mai da numfashi akai akai, sosai abun yabata mamaki, tabbas ko ma waye ne wanda yake bibiyarta ta tabbata yayi mata farin sani, amma kuma rainin hankalin yayi yawa, dole zataimawa tufkar hanci. Abun da ta ƙudurta kenan acikin zuciyarta domin iskancin yasoma isarta. Ƙarfe 6:30 na yammaci Dr Sadeeq yayi wa gidansu Zahrah tsinke, bayan yasha adon sa cikin riga da wando na shadda ƴar bugu mai kyau. Zama yayi acikin motarsa yana mai jiran fitowar Zahrah, domin kuwa yamata waya yasanar da'ita cewa gashi nan, a ƙofar gidansu. Kafeta da idanu yayi domin kuwa bakaɗan ba tayi masa kyau, cikin shigar doguwar rigan dake jikinta, lallai Zahrah ƙarshe ce wajen haɗuwa dakuma kyau. Fuskarta ɗauke da murmushi Zahrah ta ƙaraso wajen da motar tasa take fake. Tsayawa tayi ajikin motar, batare da ta buɗe tashiga ba. Ganin haka yasa Dr Sadeeq buɗe murfin motar yafito. "Yau kuma aji ake jamin ne?" ya tambayeta cikin yanayin tsokana. Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da juya idanunta. "Eh mana, ko bankai naja aji bane?" itama ta tambayesa cikin yanayi na shauƙi. "Murmushi yayi haɗe da ɗage giransa sama "Kin isa har kinma wuce, ko bakisan cewa keɗin tamusamman bace?" Hararan wasa Zahrah ta wurgamai haɗe da kawar da kanta gefe, batare da tace dashi komai ba. Haka take al'adar ta ne, bakoda wani lokaci take bada amsar tambaya ba, domin a cewarta shiru ma magana ne. "Kona zagayo na buɗe miki murfin motar ne gimbiyata, saboda naga kamar bazaki iya ba ?" yafaɗi hakan cike da kulawa. "A'a ba buƙatar hakan, ni dakaina ma zan iya" taƙare maganar tana mai buɗe murfin motar, haɗe da shiga tayi mawa kanta mazauni. Shima komawa yayi cikin motar ya zauna. Bayan ya ɗaura duka idanunsa a kanta. "Kinyi kyau sosai, fiye da ko yaushe" yafaɗi haka yanamai kashe idanunsa. Ɗanguntun murmushi Zahrah tayi "Nagode" tace dashi ataƙaice Jinjina kansa yayi azuciyarsa kuwa cewa yayi "Lallai Zahrah tana da aji, duk da ta rasa Virginity ɗinta hakan baisanya ta zama wata sakaka da'ita ba, yanason mace wacce ta'iya takunta, wacce bata sakar baki tayita dariya like mental problem, wasu matan da zaran kace dasu sunyi kyau tofa take zasu wage baki suita ƙyaƙyata dariya, babu wani ɗan jan aji ba komai. nima shaida ce irin su Sister Munubiya idan kace dasu sunyi kyau ae har kyautan kuɗi zasu baka tsabar daɗi🤣" Sake gyara zamansa yayi haɗe da dawo da nutsuwarsa zuwa gareta. "Zaki'iya zama dani a ko wani irin hali Zahrah?" Ya jefomata tambayar da bata tsammaci jinsa ba. Cikin yanayin mamaki Zahrah ta dawo da kallonta garesa, haɗe da cewa "Banfahimci maikake nufi ba" "Inanufin zaki iya rayuwa dani ako wani irin hali na tsinci kaina? sannan zaki iya yarda na haɗaku ku biyu na aura?" yakuma maimaita tambayar tasa. Dummm haka Zahrah taji ƙirjinta ya buga, idan da badon kada yace ta rainasa ba, to tabbas da zatace dashi yasake maimaita maganar da yayi. Domin idan kunnuwanta sunjiye mata dai dai, to kuwa bata da amsar da zata basa, domin koda ta basa amsa zata iya faɗuwa, saboda balallai ta bashi amsa dai dai da abun da ya tambaya ba. Idanunsa duka ya tsura mata, amsa kawai yakeson ji daga bakinta. Kasa ce dashi komai tayi, domin kuwa haryanzu bata gama haɗa amsar da zata basa ba. "Nasani dama ba lallaine ki amince ba, Hajiya na ta amince da aurena dake, amma kuma kamar yanda nafaɗamiki a baya, tun tuni akwai zaɓin da tayimin, takuma umarceni da na aureku duka biyu, shin zaki iya aurena a haka, zaki iya zama da wata a matsayin kishiyar ki?" yafaɗi hakan cike da zaƙuwan son jin amsa daga gareta. Jikinta ne gaba ɗaya yayi sanyi, take taji zuciyarta ta karaya, batasan ya'ake zama da kishiya ba, haryanzu ita yarinyace, bakomai tasani na game da al'amarin duniya ba, tanaji a labarai irin illan da kishiyoyi suke mawa junansu saboda kishi, amma ita yanzu ba wannan bane a gabanta, makomarta na gaba take tunawa, shinya zata kasance?" ta tambayi zuciyarta... "Kinyi shiru kice wani abu mana zahrah ko zuciyata zata daina bugawan da takeyi" Dr yafaɗi hakan cikin yanayin damuwa. "Bazan taɓa ƙin aurenka ba, sai dai idan har kaine kace kafasa aurena, sai dai kuma inajin tsoro, bansan mene zai kasance dani gaba ba, dan Allah kada soyayyar matarka ta ruɗeka, ka wulaƙantani, banda wani madogari sai ALLAH sai kuma kai" taƙare maganar cikin rawar murya, yayinda idanunta sukayi rau rau dasu, alamar zasu zubda ƙwalla. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe, haɗe da sakin ɗan taƙaitaccen murmushi. "Har abada kada kitaɓa tunanin zan wulaƙantaki Zahrah, inasonki da gaske bada wasa ba, namiki alƙwari zan kamanta adalci a tsakaninku, bazan juya miki bayaba insha Allah!" Doctor Sadeeq ya faɗi haka cike da lallashi. Tuni idanun Zahrah suncika da ƙwalla, amma idan ta tuno cewa bata da zaɓi sai taji gwamma kawai ta daure zuciyarta, haka ta ta ƙaddaran take. "Kada kiyi kuka kinji My Princess, ina tare dake ako wani lokaci, zankuma share miki dukkanin hawayenki nan bada jimawa ba namiki alƙawari" Saurin maida hawayenta tayi haɗe da ƙaƙalo murmushin dole ta'aza akan fuskarta, wan nan damuwarta ne ita kaɗai, baikamata ace tabari Dr Sadeeq yagane ba, lallai tun yanzu yakamata ta zama mai juriya. "Baffa yana gida kuwa?" Dr. Sadeeq ya tambaya. Wasa da yatsun hanunta tashiga yi, haɗe da kaɗa masa kai alamar "Eh" Kai yajinjina haɗi da cewa "Yanaga duk jikinki yayi sanyi? banace kada kisa damuwa a ranki ba" cikin kulawa yayi maganar. Cike da shagwaɓa Zahrah ta langwaɓar da kanta gefe haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, "Nibansa damuwa a raina ba" tace haka cikin sanyayewar jiki. Wani irin kallo maiɗauke da ma'anoni masu yawa Dr.Sadeeq yashiga yi mata, ji yake tamkar yajawota jikinsa ya rungumeta tsam acikin ƙirjinsa, saboda ako da yaushe idan yana tare da'ita wani irin feeling yakeji a jikinsa. "Kije kimin sallama da Baffa inaso zamuyi magana" "To" kawai tace dashi haɗi da buɗe murfin motar tafita. Dakallo kawai ya bita harta shige gida. Tana shiga cikin gida ta iske Baffa yana ƙoƙarin fitowa daga ɗakinsa. "Zahrah har kindawo? badai likitan yatafi ba?" Baffa yajeromata tambayoyi alokaci ɗaya. "A'a baitafi ba Baffa, shine ma yace nace ma yana son magana dakai" Zahrah tafaɗi haka ga Baffa cikin girmamawa. "To Allah yasa lafiya, yanzu kuwa zanje na sa mesa" ya faɗi maganar yana mai nufar hanyar fita daga gidan. Zahrah kuwa ɗakinta takoma. Sosai maganar Dr.Sadeeq yataɓa mata zuciya, bakomai take hangomawa kanta ba, sai yanda makomarta zai kasance acikin gidansa, tabbas ta tabbatar wacce zai aura, ba irin ta bane, tasan tana da galihu, saɓanin ita da take ko oho, sannan kuma dole zata ga banbanci daga ƴan uwansa, haka ma Dr.Sadeeq ɗin dole zai banbantasu, saboda waccar zai sameta a budurwa, saɓanin ita da zai sameta ba'a budurwa ba, kukane yaƙwace mata mai sauti, cusa kanta cikin cinyoyinta tayi tashiga rera kukanta, har abada cutar da Zaid yayi mata bazai taɓa gushewa ba..... "Alhmdlh masha Allah! haƙiƙa naji daɗin wannan magana taka Likita, lallai kacika mutumin kirki kuma mutumin ƙwarai, Allah yasaka ma da gidan Aljanna, kuma idan dai Zahrah ce kada kaji komai natabbatar itama tana ƙaunarka, saboda haka nabaka izini ka turo magabatanka, don mu tsaida magana,kuma maganar bayarwa nabaka Zahrah!" Baffa yafaɗi haka cikin farinciki, duk da kuwa cewa dama tun abaya yasan cewa Dr.Sadeeq yanason Zahrah, amma sake tabbatar masa da Dr. ɗin yayi yanzu, yasanyashi jin daɗi, domin shima yanzu burinsa shine ya inganta farincikin marainiyar Allah wato Zahrah.. Farinciki ne sosai yakama Dr.Sadeeq, yaji daɗin aminta dashi da Baffa yayi. "Nagode da wannan dama da kabani Baffa, Allah yajiƙan magabata" Dr Sadeeq yafaɗa cike da girmamawa. "Mune da godiya Likita, ai mu ba'abun da zamuce maka saidai fatan alkhairi" Baffa yafaɗa shima cikin jin daɗi, domin yasan Zahrah na auren Dr.Sadeeq wahalanta yaƙare da yardan Allah,saboda yana da tabbacin cewa Dr.Sadeeq zai bata kyakkyawan kulawa, duk da kuwa cewa Dr.Sadeeq ɗin yasanar dashi cewa ba Zahrah ita kaɗai zai auraba, yasanar dashi komai, kuma Baffa yayi na'am da hakan, saboda shi baimaga wani aibu acikin hakan ba, ai namiji mijin mace huɗu ne. (Nima nace wannan gaskia ne, sbd haka duk me mace ɗaya ya ƙara😜😂) Cike da farinciki Baffa da Likita sukayi sallama, yayinda Baffa yakoma cikin gida, ya kumace da Dr.Sadeeq zai turo masa Zahrah suyi sallama. Tanajin Muryan Baffa a tsakar gida, tayi saurin share hawayenta, haɗe da miƙewa tsaye, domin har Baffa yafara ƙwaɗa mata ƙira. Fuska cike da fari'a Baffa yace "Likita ke yake jira, zai tafi" Sumi sumi haka Zahrah ta fice yayinda tabar Baffa yana gayamawa Inna abun da ya wakana tsakaninsa da Likita. Tun fitowarta yake ta zabga murmushi, kallo ɗaya zakai mawa fuskarsa ka gane cewa yanacikin farinciki. "Kitayani murna My Princess saura ƴan kwanaki ƙalilan na mallake ki!" Dr Sadeeq yafaɗi haka cike da shauƙi. Kunyane yakama Zahrah, don haka ta sanya duka hannayenta biyu ta rufe fuskarta, bayan ta ƙaƙalo murmushi ta aza akan fuskar ta.. "Baffa yabani daman naturo magabatana don asa mana ranan aure, kuma insha Allah, gobe magabatana zasu zo, za'asa ranan aurenmu nan bada jimawa ba, so sai ki shirya domin kin kusa zama amaryata!" yanayin yanda ya ƙare maganar kaɗai ya isa taɓa zuciya.. Kunyane yasake kama Zahrah, har batasan sanda murmushi mai sauti ya kufce mata ba, gaba ɗaya ta lura Dr.Sadeeq ya ƙosa da ayi aurensu bata kumasan dalilinsa nayin hakan ba.. "Kinyi shiru kodai bakya farinciki ne my princess?" yatambaya. Ɗan satan kallonsa tayi haɗe da sakarmasa murmushi mai tsayawa a zuciya. Ƙaran wayarsane ta katsesa daga kallonta da kuma zancen zucin da yakeyi. Ajiyar zuciya ya sauƙe ganin wacce take ƙiran nasa, maida wayar tasa cikin aljihu yayi batare daya ɗaga ƙiran ba. "Dare yayi Zahrah kishiga gida, zamuyi waya, kikulamin da kanki " yafaɗi hakan yana me ƙoƙarin shiga cikin motarsa. Murmushin dole Zahrah tayi haɗe da yi masa saida safe, tajuya ta nufi cikin gida, hakanan taji wani iri a zuciyarta duk da batasan me yasa baiɗaga ƙiran da ake mai ba, amma tana da yaƙinin cewa matar da zai aura tare da itane ta ƙirasa. Saurin kawar da tunanin tayi aranta, domin tuna hakan ma bashida amfani a gareta. Washe Gari.... Kamar yanda Dr.Sadeeq yafaɗa hakanne ya kasance da da dare bayan sallan magriba Baffa Amadu shida amininsa suka zo gidansu Zahrah don tambayan aurenta, balaifi Baffa yayi musu tarba mai kyau, sunkuma ji daɗin hakan, duk da sun lura cewa suɗin basuda wani ƙarfi, ma'ana arziki... Magana ta fahimta akayi tsakanin Baffa da kuma Baffa Amadu, a taƙaice dai Baffa yabasu auren Zahrah, yayinda sukuma suka ɗau alƙawarin cewa a cikin satin za'akawo kayan tambaya dakuma na lefe, daga nan sai asa ranan aure, amma basason auren ya ɗau lokaci, saboda rana ɗaya suke so ayi dana Salima.. Da to kawai Baffa ya amsa musu domin shi baida wani abun cewa banda hakan, sai dai a ƙasan zuciyarsa tunani yake taya zai samu kuɗin da zaiyi mawa Zahrah kayan ɗaki, domin dai bayanda za'ayi ace anyi aure ba kayan ɗaki... Haka dai sukayi sallama cike da mutun ta juna... Baffa ne Zaune akan tabarma ya yi jigum bakomai ke damunsa ba, kamar sha'anin auren Zahrah, Allah yasani ko abincin da za'aci abikin bai tanada ba, balle wata uwa uba kayan ɗakin da za akaita dashi.. "Wai tunanin mekakeyine haka tun ɗazu?" Inna dake zaune gefensa ta jefo masa tambaya. "Ba dole nayi tunani ba Salame, kinga dai yau iyayen yaron nan Sadeeq suka zo, kuma da duk kan alama basa so aja auren nan yakai wani lokaci, kin kuma san halin dai da muke ciki na rashin kuɗi" "Yo dama akan wannan kake ɗaga hankalinka? hmm Malam kenan to ai ni banga abun ɗaga hankali anan ba, ca nake shi Sadeeq ɗin yasan duk halin da muke ciki, kuma shi yakawo kansa yace ya na so, bawai mu makai masa dole ba, saboda haka malam ka kwantar da hankalinka, Zahrah ya nema kuma Zahrah'n zamu bashi" Inna tafaɗi haka da'iyaka gaskiyarta... Kallon Inna kawai Baffa yayi haɗe da girgiza kansa, yasan ma koda yayi ƙoƙarin fahimtar da'ita to fa bazata fahimta ba. *** "What? Mom cewa fa kikayi wai bani kaɗai Sadeeq zai aura ba, anya kuwa Mom kinji abun da Hajiya Habiba tafaɗamiki da kyau?" Salima tatambayi mahaifiyarta Hajiya Furaira cike da mamakin jin abun da mahaifiyarta tace da'ita.. "Abun da na faɗa miki shi naji daga bakin Hajiya Habiba, Salima kicire Sadeeq a ranki, domin kuwa aurenki dashi bazai taɓa yiyuwa ba, da raina dakuma hankalina bazan taɓa bari ƴata taje kan kishiya ba!" Hajiya Furaira tafaɗi haka cikin ɓacin rai.. Kuka ne ya ƙwacemawa Salima cikin muryan kuka ta soma cewa "Wani irin cin amana ne wannan mom, sai da maganar aurena dashi ta kankama sannan wata banzar magana zata ɓullo, wallahi bazan haƙura da shi ba, bakuma zan taɓa zama da wata a matsayin kishiyata ba, dole ne Sadeeq ya aureni ni ɗaya batare da wata ba, bazan iya jure rashin saba Mom, dan Allah kiyi wani abu" Salima ta ƙare maganar cikin shaɓe shaɓe da hawaye. "Mekikeso nayi Salima? so kike naje na basu haƙuri akan su sa Sadeeq ya aureki ke kaɗai? ko ko sokike na zubar miki da ƙima daƙuma ƴancinki? Hajiya Habiba ƴar uwatace kuma ƙawata, bantaɓa tunanin haka daga gareta ba, amma bakomai, zanyi maganin abun, kuma ni banzauna da kishiya ba, ƴa tama bazata zuana da kishiya ba, wannan alƙawarine na ɗaukar mawa kaina" still cikin ɓacin rai Hajiya Furaira take maganan... Cikin matsanancin ɓacin rai Salima ta juya ta koma ɗakinta, ji takeyi zuciyarta na tafarfasa, kamar ita ace ta haɗa miji da wata, sam bazai yi wuba, lallai ko da mahaifiyarta bazatayi wani abu ba yakamata ace ita tayi, wayarta da mayafinta ta ɗauka, a fusace ta fice daga ɗakin nata, tana son Sadeeq tun ba yau ba, zata kuma iyayin komai akan sa. Ɓangaren Dr Sadeeq kuwa tuni yasoma haɗa mawa Zahrah kayan lefe, sosai yake iya ƙoƙarin sa wajen ganin yasanya duk wani abu da yasan zai burge Zahrah. Ɓangaren Hajiyarsa da Aunty Raliya kuwa, sam basu wani damu da auren ba, hakanne ma yasa suka tura masa aniyarsa, su dai sunfi bada ƙarfi wajen ganin Salima tasamu abun da take so, yayinda Hajiya Furaira ta kafe kan cewa ƴarta bazata auri Sadeeq ba matuƙar ba'a fasa aurensa da Zahrah ba, ranta bai ƙara ɓaci ba ma, sai da taji labarin cewa Zahrah ƴar talakawa ne, sannan kuma bata da wani galihu, ai take ranta yaƙara ɓaci, tace sam bata amince ba, yayinda Salima kuwa ta kafe akan cewa lallai sai ta ruguza auren da Dr.Sadeeq yake nema bayan nata. Gaba ɗaya Zahrah ta ruɗe, zuwa yanzu wanda yake turo mata saƙo ya uzurawa rayuwarta, a yanda ta fahimta shine duk inda tayi yana biye da'ita, wani babban tashin hankali daya kunnu mata shine, sabbin saƙonnin da yafara turo mata a cikin wayarta, tagama iya hasashenta ko zata gano a ina yasamu number'n ta amma takasa samun daman sanin inda yasamu number'nta, gaba ɗaya yanzu salon saƙonnin nasa sun sauya salo, domin kuwa yanzu saƙon kalamai yaƙe turo mata masu daɗi, wanda kuma duk rabin saƙon yaba kyawunta yake, babban abun daya ƙara ruɗata shine irin maƙudan kuɗaɗen dayake turomata ta waya. sannan kuma idan ta gwada ƙiran number'n da yake turo mata saƙo dashi, bata samu domin da zaran taƙira wayan za'ace mata a kashe wayar take, hakan yasa tafara tunanin cewa kodai gamo tayi... Ɗan ƙara wayarta tayi alamar shigowar saƙo, take taji gabanta yafaɗi, zuwa yanzu har tsoro take taji wayarta tayi ƙara, domin kuwa tasan idan har wayanta tayi ƙara to ko ƙiran Dr.Sadeeq ko kuma saƙon mutumin da batasan shiba... Number'n nan ce dai, da aka saba turo mata saƙo dashi, yauma saƙonne aka kuma turowa.. _Tunaninki ya hanani sukuni My Zahrah, ina fatan dai kina lafiya, ina kuma fatan zuwa yanzu kindaina tsoro da kuma mummunan tunanin da kikeyi akaina, kina da kyau My Zahrah, komai naki me kyau da burgewa ne._ Abun da saƙon ya ƙunsa kenan. Zahrah ta karanta saƙon nan yafi sau biyar, kwata kwata ta kasa fahimtar abun da saƙon yake nufi. Saurin yin Deleting saƙon tayi haɗe dayin switch off ɗin wayar tata, bazata taɓa yarda wan nan mai saƙon ya haukata mata tunanin ta ba, yazama dole a gareta ta sanja layi.. Kwanciya tayi lamo tana mai addu'an Allah yasa bacci ya ɗauketa. domin bacci ne kaɗai zai kawo mata sauƙi a zuciyarta. Zaune suke dukansu a ɗan madai dai cin tsakar gidan nasu, domin dama idan dare yayi sukan zauna a tsakar gida su ɗan taɓa hira, haka al'adarsu take.. Wani yarone yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, haɗa baki sukayi wajen amsa masa sallaman. "Wai ana sallama da mai gidan nan" yaron yafaɗa. "To kace inazuwa" Baffa yafaɗi haka yana ƙoƙarin miƙewa tsaye. Kusan tare suka fita shida yaron sai da Baffa yaji wani irin faɗuwar gaba sakamakon wasu irin danƙara danƙaran motoci guda biyu da yagani fake a ƙofar gidansa. Ja Baffa yayi ya tsaya turus yana me mamakin ganin waƴan nan rantsatstsun motocin a ƙofar gidansa, "Allah yasa da alkhairi suka zo" Baffa yafaɗi haka a cikin zuciyarsa. Buɗe murfin motar Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da sako ƙafarsa waje. Sake waro idanu Baffa yayi haɗe da kafe Alhaji Ma'aruf dake ƙoƙarin fitowa daga cikin mota da ido. Fuska cike da annuri Alhaji Ma'aruf ya ƙaraso wajen Baffa, haɗe da miƙa masa hanu alamar su gaisa. Cikin ɗari ɗari Baffa ya ɗago hanunsa haɗe da miƙamawa Alhaji Ma'aruf suka gaisa. "Inafatan kaine ma mallakin wannan gida, kuma Baffa ga Zahrah?" Alhaji Ma'aruf ya tambaya. Saida Baffa yaji zuciyarsa tayi tsalle sakamakon jin an ambaci Zahrah, Allah yasa ba wani abun Zahrah tajawo musu ba. "Eh nine ranka ya daɗe, Allah yasa lafiya?" cikin dar ɗar Baffa yafaɗi hakan. Murmushi irin nasu na manya Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da kallon Baffa..."Nazo da magana mai mahimmanci, inaga zaifi kyautuwa kabiyoni cikin mota

Chapter 20 of 47