zama hoto, aganin iyaye komiye ɗa namiji yayi adone bakamar ƴa mace ba, tabbas hakane duk abun da ɗa namiji yayi adone bakamar mace ba, amma hakan bawai yananufin shi ɗa namiji abarsa sakaka haka bane batare da annuna masa kulawa ba, shi namiji a koda yaushe ana ganin zai iya kula da kansa, amma yana da kyau ana nuna masa kulawa ana kuma jansa ajiki kodan yasamu inda zena faɗan damuwarsa, kowafa yanason yasamu tarbiya me kyau daga Namiji har mace, saboda haka yazama lalle iyaye su tashi tsaye wajen kulawa da ƴaƴansu maza saboda ba mata ne kaɗai suke buƙatan kulawa ba harsuma maza suna buƙata......
Dr.Bilal ne yakatse Dad daga tunanin da yafaɗa me zurfi tahanyar cewa da yayi dashi. "Zaid yana buƙatar hutu saboda haka sai nan da 4 hours kafun su samu ganinsa"
Jiki ba ƙwari haka Dad yafito daga office ɗin yanufo inda su Mom ke tsaye suna sharce hawaye..
"Yaya de Alhaji me likitan yacema?" Mom tatambaya cike da damuwar son sanin wani hali ɗanta yake ciki..
"Kada kidamu, ku kwantar da hankalinku jikinsa da sauƙi zuwa anjima kuma insha Allah zamu samu ganinsa yanzu likita yace yana buƙatar hutu ne, to dole zamu barsa yaɗan huta" Dad yaƙare maganar yana me kamo duka hannayen mom alamun rarrashi..
Hamdala Mom tayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya
Sake kallon Dad tayi cikin yanayi na tuhuma tace "Meyasanya naga fuskarka ɗauke da tashin hankali me tsanani Alhaji?"
Murmushin dole Dad yanemo ya ara akan fuskarsa bayason faɗa mata wan nan maganar yanzu yafiso saisun samu nutsuwa sunkoma gida tukunna, sai de kuma abun da shi besani ba shine tafikowa sanin cewa Zaid yanashan giya, saboda tasha kamasa acikin maye yayi mankas, san nan kuma tajima da sanin cewa yanashan ƙwayoyi, sede abun da bata sani ba shine haɗarin da ƙwayoyin suke ɗauke dashi....
********
Haka Zahrah tawayi gari yau da zazzaɓi sede duk da haka bata nunawa kowa cewa bata da lafiya ba, sede kuma idanunta sun kunbura sakamakon kukan da taci ta ƙoshi a daren jiya..
Haka de tashirya kanta tsab don zuwa makaranta amma kowa yaganta yasan bata da wani isashshen kuzari a tattare da'ita,, ko abun kari bata tsaya taci ba haka ta fice a gidan nasu....
********
"Kuka bazai taɓa yimiki maganin komai ba Zahrah, tabbas nasan kinajin raɗaɗi a cikin zuciyarki amma zuwa yanzu yakamata ace kimanta da baya kifuskanci gaba, aure zakiyi yanzu babu amfani kicigaba da sanya kanki cikin ƙunci!" Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cikin yanayi na tausasawa, kasancewar duk wunin yau ɗin da sukayi amakaranta bata gane kan ƙawarta ta ba...
Hannayen Husnah duka Zahrah takama haɗe da kallonta. Cikin murya me rauni tasoma cewa.....
"Ni kaina inaso naganni cikin farinciki Husnah, amma nasan hakan bazai samu ba matuƙar Zaid yana raye a doron ƙasa, koda ma ace baya raye nasan bazanyi farinciki ba Husnah saboda yariga daya gama lalatamin rayuwa, bana tunanin cewa akwai wani namiji da zaiyi ɗokina idan ya aureni? Shifa budurci wani abune me matuƙar mahaimmanci a rayuwar ƴa mace Husnah, babu wani mutumci dakuma karamci wanda ya wuce mace takai budurcinta ɗakin mijinta, mafi ganganci da kuskure da mace zata aikata kafun aurenta shine ta yarda ta bawa wani kyautar budurcinta, mata irina suna da yawa Husnah wa ƴanda aka mawa fyaɗe aka ƙwaci budurcinsu da ƙarfin tsiya, san nan kuma akwai waƴanda maza suke ruɗansu da kuɗi ko kuma da soyayya harsu yi nasaran rabasu da budurcinsu, san nan akwai kuma wanda dan kansu suke bada kyautar nasu budurcin ga wani daban, rasa budurci abune me matuƙar ciwo Husnah musamman ma ga iri na wanda aka mawa fyaɗe, Yawancin maza suna fatan idan sunyi aure su samu matansu da cikekken mutumcinsu, inde kuwa har a matsayin budurwa suka aureta, haƙiƙa akwai wata soyayya dakuma girmamawa dake shiga tsakanin mace da mijinta matuƙar takawomasa budurcinta ɗakinsa, saɓanin haka kuwa shike hargitsa tunanin namiji, shike jagulawa mace zaman aure'nta, koda ace ya yarda ƙaddarane hakan amma tabbas wani lokaci abun zaina masa ciwo, duk da nasan cewa Dr.Sadeeq yasan komai daya faru dani, amma duk da haka tabbas nasan duk randa yakusanceni saiyaji ciwo acikin ransa, saikuma yaji wani abu saɓanin tunaninsa, shi a yanzu yana ganin cewa hakan bakomai bane, amma kuma hakan komai ne bakuma ze gane hakan ba sai randa ya aureni yakuma nemi dana basa haƙƙinsa na aure,, wan nan ranan nake gujewa kaina Husnah bansan ina zan tsoma kai da zuciyata ba amma nabarwa Allah komai!!" gaba ɗaya hawaye sungama wankewa Zahrah da Husnah fuska, lalle kuwa wan nan itace mummunar ƙaddara wand ba'a taɓa mantawa da'ita,, rungume Zahrah Husnah tayi cike da tsananin tausayin ƙawarta ta,,, tabbas duk abun da Zahrah tafaɗa gaskiya ne kai budurci ɗakin miji yafi komai daɗi a rayuwa saboda ko ba komai zaiƙara muku danƙon soyayya dakuma mutunta juna, duk da cewa Zahrah ba'asonta tarasa budurcinta ba amma kuma tabbas kamar yanda Zahrah ta faɗa hakan yake dolene Dr.Sadeeq zaiji zafin abun sosai aduk ranarda kusantar farko tashiga tsakaninsu, amma kuma babu wanda ya isa ya tsallakewa ƙaddararsa.....
Hawayenta tasanya hanu tashare kafun tashiga sharewa Zahrah ma nata hawayen,,,,
"Ki kwantar da hankalinki Zahrah komai zai zo cikin sauƙi insha Allah taso muje musamu ruwa muwanke fuskarmu ko"
Ba musu Zahrah ta tashi tsaye Husnah takama hanunta suka nufi wajen da sukasan zasu samu ruwa......
***********
Jigum haka su Dad dake tsaye agefen gadon Zaid sukayi, yanzu awa 5 kenan suna irgawa batare daya buɗe idanunsa ba, gashi kuma 4 hours likita yace musu zaiyi....
Babban yatsar ƙafansane tasoma motsawa kafun idanunsa da sukayi nauyi suka soma buɗewa a hankali,, da sauri Dad ɗinsa yaƙaraso jikin gadon yanayi masa sannu...
Ƙoƙarin tashi zaune yasomayi da sauri Dad ɗinsa yamaidasa ya kwanta "Ba sai ka tashi ba Zaid yakamata kabari kaɗan wastsake tukunna kafun kasoma yunƙurin tashi"
Ɗan yamutsa fuska Zaid yayi haɗe dabin ledar ruwan da aka ɗaura masa da kallo.
Dai de lokacin Labisat suka shigo ita da Dr.Bilal domin dama Mom naganin Zaid ɗin yabuɗe ido tace da Labisat tayi mata ƙiran Doctor...
Ƴan gwaje gwaje Dr.Bilal yayi masa haɗe dayi masa wasu ƴan tambayoyi, ko motsawa bakin Zaid beyiba balle Dr.Bilal yasa ran samun amsa, ganin haka yasa Dr.Bilal yin murmushi batun yauba yasan Zaid ɗin saboda haka shirun da Zaid ɗin yayi masa bawani abu bane daya kamata ace yadamu ba,, kallon Dad Dr.Bilal yayi haɗe da cewa
"Ko yanzu idan kuna buƙatar sallama se a baku saboda babu wata damuwa, se daifa a kiyaye kamar yanda na faɗa"
Kai Dad yajinjina haɗe da cewa "Shikenan Doctor insha Allah za'a kiyaye, muje sai nakarɓi takardan sallaman ko" Dad da Dr.Bilal suna fita Zaid yatattaro duka wani kuzarinsa dayayi masa saura yamiƙe tsaye, kafaɗun Labisat dake tsaye kusa dashi ya kamo haɗe da ɗaura hanunsa akan kafaɗan nata suka nufi hanyar fita daga ɗakin, domin kuwa koda Dr.Bilal be basu sallama ba tabbas bazai ƙara 1 hour a cikin asibitin ba...
Yana riƙe da kafaɗan Labisat harzuwa cikin mota, shida Labisat mota ɗaya suka shiga, yayinda su Dad da Mom suka shiga wata motar wanda duk su sukazo da ita... Direct gida suka nufa
Idanunsa gaba ɗaya suna a lumshe yayinda yajingina bayansa a jikin kujeran motar wanda yake zaune akai.
Ɗan satan kallonsa Labisat tayi hakanan taji wani irin mugun tausayin ɗan uwan nata ya kamata, tabbas basuyi wani shaƙuwa da yayan nata ba amma tafuskanci cewa yanacikin damuwa, takuma tabbatar da cewa sanadin damuwarne ma har ya kaisa ga kwanciya a asibiti, to wan nan wace irin damuwace yayanta yake ciki haka? tabbas zataso sanin damuwar dake damunsa saboda tana matuƙar son ɗan uwan nata bandashi batada wani ɗan uwa dasuke uwa ɗaya uba ɗaya shikaɗaine yayanta kuma garkuwanta......
Koda suka isa gidama Labisat ce tarakasa har ɓangarensa,, zama yayi akan kujera haɗe da jawo wani ɗan ƙaramin table ɗin dake tsakiyar falon yaɗaura ƙafafunsa akai..
"Yaya mezan kawo maka, yakamata kasa wani abu acikin ka!" cike da ɗar ɗar Labisar tafaɗi maganar saboda tasansa sarai ba'a iyarmasa yanzu saiya saceka..
"Friedrice" yafaɗa a taƙaice batare kuma daya buɗe kyawawan idanunsa dasuke a lumshe ba..
Jiki na mazari haka Labisat ta tafi kawo masa friedrice ɗin dayace, domin kuwa dama agidan nasu ba a rasa friedrice..
Mintuna kaɗan tadawo hanunta ɗauke da ƙaton tire hadda plate ɗin yankakkun kayan marmari akan tire ɗin,, adede gabansa ta ajiye tire ɗin haɗe da ɗaukan plate ta buɗe kulan da friedrice ɗin ke ciki ta zuba masa.
"Yaya gashinan na kawo" tafaɗa tana me tura masa plate ɗin friedrice ɗin gabansa.
Ganin da tayi bece da ita komai ba yasanyata miƙewa sumu sumu tafice daga falon nasa...
Jawo plate ɗin yayi gabansa yasoma tsakuran abincin yanaci kaɗan kaɗan duk da kuwa bawai buƙatar abincin yakeyi ba adole kawai yakeci... Lomansa huɗu ya aje spoon ɗin dake hanunsa haɗe da jawo plate ɗin yankakkun kayan marmarin dake gabansa yasoma sha, sai alokacin yasoma jin daɗin bakinsa, amma da kwata kwata bayajin ɗanɗanon komai,, fruits ɗinma baiwani sha me yawaba haka yature yakuma maidakansa yajingina da kujera,, idan akwai abun dayake ƙauna dakuma muradin gani yanzu arayuwarsa baiwuce Zahrah ba, dole yaje gidansu ayau ɗin koda kuwa idan yaje zata ɗauki wuƙa ne taluma masa a cikinsa.....
Yauma de kamar kullum Zaune take a tsakar gidan nasu, kwanon abincine aje agabanta tana tsakura da kaɗan kaɗan tana kaiwa bakinta domin kuwa haryanzu bata wani jin daɗin jikinta..
Inna ce zaune daga gefenta tana ta ƙoƙari wajen ganin ta seta tashan radion ta..
Wani yarone yayi sallama yace wai ana ƙiran Zahrah,, "Jekace tanazuwa" Inna tahanzarta faɗa, har yaron yakama hanyar fita daga gidan, Zahrah ta tsaidasa haɗe da cewa "Kace bazata zo ba"
Hangame baki Inna tayi tana kallon Zahrah "Bazakijeba fa kikace?"
"Eh Inna dan Allah kuma kada kitambayeni dalili" tayi maganar tana me langwaɓar da kanta gefe.
Harara Inna ta watsa mata haɗe dayin tsuka baƙin ciki kawai Zahrah'n takeyi mata wayasani ma ko wanda ke ƙiran nata da alkhairi yazo...
"Wai Bazata zoba" yaron nan yafaɗawa wanda ya aikosa.
Waro idanu Zaid yayi maganar ma shi dariya taso basa, amma a irin wan nan yanayin dayake ciki bayatunanin zai iyayin dariya...
"Wayene yacema bazata zo ba?" Zaid yatambayi yaron.
"Ita da kanta" yaron yabasa amsa domin kuwa shiɗin ɗan maƙotansu ne saboda haka yasan Zahrah'n.
Kai Zaid yajinjina haɗe da cije laɓɓansa,, Allah sarki rayuwa babu yanda bata juyawa mutum, amma in banda haka wai yau shine a wata ƙasƙantacciyar unguwa kuma ƙofar gidan su mace yakuma aika tace bazata zo ba, shine fa Zaid ɗin da har gobe ƴan mata suke rushing akan sa, to amma meyasa haka takasance dashi?" ganin da yayi yaron nashirin tafiya ne yasanya yace "Kaje kace injini nace tayi haƙuri tafito" bamusu yaron yakoma yakuma faɗi saƙon da akabasa umarnin yafaɗa..
Tsuka Zahrah taja haɗe da tashi tsaye "Kaje kace wai inji Zahrah kozai mutu a tsaye baza ta zoba" tanakaiwa nan azancenta tayi wucewarta ɗaki..
Abunda Zahrah tafaɗa shi yaron nan yazo ya sanarwa Zaid, kuɗi Zaid yaciro a aljihunsa 1k yabawa yaron dafari yaron yatsorita yaƙi amsa, amma Zaid yatilasta masa saida ya amsa, haka yaron yatafi yana murna...
Motarsa yabuɗe yashiga yayinda yakifa kansa a steering motar meyasa soyayya zata masa haka, idanunsa Zahrah kawai suke son gane masa tabbas yau bazai taɓa iya runtsawaba matuƙar baiga Zahrah ba, yana mawa Zahrah wani irin mugun so me tsananin zafi.. Jan motarsa yayi yakoma ƙarƙashin wata bishiya tayanda bakowa zai lura da cewa yana wajen ba, yaƙudurta aransa cewa koda zai kwana a wajen ne bazai gusa ba harsai idanunsa sun mai tozali da Zahrah....
Bayan awa ɗaya
Zahrah ce tafito daga cikin gidan nasu sanye da wani siririn mayafi wayarta ce riƙe a hanunta se kuma wani littafi. Zaid dake zaune cikin motarsa yana ganinta ya sake waro idanu haɗe da sauƙe ajiyar zuciya me ƙarfi, jiyakeyi tamkar yaje ya ɗauƙota can caɗak yatafi da ita... Yana kallonta tayi shigewarta wani gida dake kusa da nasu gidan.. Bayan kamar mintuna 8 da shiganta gidan yaga takuma fitowa da sauri yabuɗe murfin motarsa daniyar ƙarasawa gareta sai de kuma ko taku biyu baiyiba tashige cikin gida ko ganinsa ma ita batayi ba, haushine yasanyashi buga tayar motarsa da ƙafarsa, haka yakoma yayiwa motarsa key haɗe dayin reverse yabar unguwar tasu cike da ƙuncin rashin samun daman yi mata magana da be yiba, amma de yaji sanyi sosai a zuciyarsa daya ganta...
*********
Yau tunsafe Zahrah tashiga busy hidama kawai sukeyi ita da Husnah domin kuwa yaune ranar da Dr.Sadeeq yace mata za'a kawo lefenta,, yanzuma daga shopping suke sunje sun sayo kayan drinks da kuma su snacks wanda za'abawa baƙi. Zama sukayi akan tabarma suna me da numfashi saboda sungaji sosai,,, kallon Zahrah Husnah tayi haɗe da sakin murmushi.
"Ƙawata nifa yau daɗi nakeji jinake tamkar ma nice za'a kawowa lefen" dariya Zahrah tayi haɗe dacewa "To aike kince bayanzu zakiyi aure ba saikin gama school gashi Nuruddeen yana tsananin son kuyi aure amma ke kinƙi"
"Hmm ai zan masa maganane yaturo kawai domin ni mafa yanzu dagaske auren nakeso nagaji da rungumar pillow idan nazo bacci" Dariya suka sanya su dukansu hadda tafawa, "Allah yashiryeki Husnah" Zahrah tafaɗa tana dariya.. Haka de sukaci gaba da ƴan hirarrakinsu irin na ƙawaye..........
Ƙarfe biyar dai dai wasu rantsa rantsan motoci suka soma tsayuwa a ƙofar gidan su Zahrah duk macen da tafito acikin motar sai kaga tana yatsuna fuska haɗe da soma ƙarewa wajen gidansu Zahrah kallo, motocine kusan guda goma sha biyu suka kawo kayan lefen ahankali aka shiga fito da akwatuna ana shiga dashi cikin gidan su Zahrah.. Fuska babu yabo ba fallasa haka matan nan suka soma shiga cikin gidansu Zahrah,,,,, da fari'a Inna da tawagarta suka tarɓi mutanen haɗe da basu wajen zama, haka suka zauna wasu daga cikinsu suna yatsuna fuska kamar wanda akace su zauna akan kashi...
"Sannunku da zuwa lale marhaba" Wata mata maƙociyar su Zahrah tafaɗa ga matan da suka kawo lefen. Amma kuma daƙyar aka samu biyu daga cikinsu suka amsa mata..
Akwatuna ne harguda shabiyu aka jibge akan wata tabarma dake shimfuɗe,, su Inna ne suka fara ɗagawa matan da suka kawo lefen gaisuwa ciki ciki suka amsa musu cike da isa,,,,, Aunty Raliya ce ma tayi ƙarfin halin cewa "Ga kayanan munkawo Allah yasa ayi bikin a sa'a, Allah kuma yasa asamu kyakkyawar zuri'a" dagajin yanda tayi maganar kaɗai ya isa ya tabbatarmaka cewa kalaman ba anyi su bane cikin daɗin rai,,, da Ameen kawai su Inna suka amsa musu,,, kuɗi Aunty Raliya taciro acikin jakarta bandir ɗin ƴan dubu dubu har na dubu ɗari ta ɗaura akan wani akwati haɗe da kallon ƴan uwanta tace "Muje ko" dukansu miƙewa sukayi suka nufi hanyar waje,,, yayinda Inna tasa yaran maƙotansu suka kwashi kayan tarban baƙin da suka musu aka kai musu cikin mota, maman Badi'a ɗaya daga cikin maƙotan su Zahrah ita tazari dubu hamsin daga cikin kuɗin da suka aje tabawa ƴarta Badi'a tace takaiwa matan dasuka kawo lefen,,, dawowa da kuɗin Badi'a tayi tace ae sun riga da sun tafi koda tafita ƙurar motarsu kawai tagani,,, "To suko wasu irin mutanene haka ae ba haka akeyi ba, ko fa kayan basu tsaya sun nuna mana ba saikace wanda suke akan ƙaya" Maman Badi'a tafaɗi haka cike da mamakin hali irin na matan da suka kawo lefen,,, washe da baki wata mata daga cikin gayyar Inna tace "Kai amma kuwa Zahrah tayi goshi kuga kayafa kamar wanda za a buɗe kanti" ae kuwa basusan cewa Zahrah tayi goshi ba saida suka soma buɗe akwatunan,, kowanni akwati shaƙe yake da kaya nagani na faɗa,, take Inna tasoma rangaɗa guɗa hadda rawan murna.......
(Team Dr.Sadeeq da Zahrah saiku wanke ƙafa don zuwa gano kayan lefen Zahrah🤗)
*31/December/2019*
*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
*Wattpad user name fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
*Phatymasardauna*
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed: our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
(Kutayani jaje wlh sau biyu kenan typing ɗina yana gogewa😨😨 yanzu saida nayi 2000 words wlh ya kuma gogewa maganan danake wlh yanzu haka ina rubutun nan ina kuka😭😭 wlh abun da ciwo sosai😭😭)
*CHAPTER 74 to 75*
Hayaniya haɗi da guɗan da su Inna keyi shiyayi sanadiyar janyo hankalin Zahrah dakuma Husnah da suke zaune a ɗakin Zahrah sunyi muƙus,,,,
"Ke nifa tashi zanyi naje nabawa idanuna abinci, dan wlh bazan iya zama aɗaki kamar wata sabuwar amarya ba, ke dai da zaman yazamemiki dole saiki ta fama" Husnah tafaɗi haka tana me miƙewa tsaye daga zaunen da take,,, murmushi kawai Zahrah tayi mata haɗe da binta da kallo hartafice daga cikin ɗakin...
Hamdala Husnah tayi haɗe da nunatsantsar farincikinta alokacin da idanunta sukai mata tozali da kayan lefen ƙawartata,,,, lallai Dr.Sadeeq yayi ƙoƙari domin kuwa naira tayi kuka, koda kyawun akwatunan aka barka sun isa sanyaya maka rai, balle kuma aje ga kayan ciki masu kyau da tsadar gaske, wan nan shiyasake tabbatar mata da cewa Zahrah bazatayi kuka ba idan ta auri Dr.Sadeeq, saboda me sonkane kaɗai zai iyayin komai dayasan zai faranta maka rai....
Duk yawan atamfofin dake cikin akwatunan nan saida su Inna suka irgesu kaf, turame hamsin banda su laces haɗi da shaddodi dakuma dangin su materials,, ɓangaren dogin riguna ma akwati guda aka cika dasu, sosai kuma yasaki bakin aljihunsa wajen zaɓo masu kyau da tsada,, haka ɓangaren sarƙokima komai yaji domin kuwa kaf cikin sarƙoƙi da ɗan kunnayenta babu wani mai sauƙin kuɗi acikinsu gwala gwalanta har guda uku,, san nan kuma ɓanagaren jaka da takalma ma yayi ƙoƙari sosai, domin kuwa kusan kowani kaya yanada jaka da takalmi hadda mayafinsa,, wajen kayan shafa ma yayi ƙoƙari sosai wajen fidda naira yasai kayan shafa ƴan yayi masu kyau duk da kuwa yasan cewa ita ba gwanar kwalliyan fuska bace...
"Gaskiya kaya yayi kyau yarinya tayi goshi, ai wan nan kayan ko ɗiyar babban attijiri sai haka" Maman Badi'a tafaɗi haka bayan taƙarewa wani haɗaɗɗen leshi dake riƙe a hanunta kallo wanda a ƙalla kuɗinsa zai kai 50k,,,
"Ƙwarai kuwa yarinya tayi goshi Maman Badi'a ai dama tuntuni nasan fiye da haka ma sai yafaru, ga kaya kan nan harda nasadakarwa!" Inna tafaɗi haka cikin murna...
Wata dake zaune kusa da Inna tace "wan nan haka yake muma dai Allah yabawa namu ƴaƴan mazajen aure masu ƙashin arziki"
Duka matan suka haɗa baki wajen cewa Ameen domin kuwa babu wacce zataƙi ace ƴarta ce tasamu wan nan kayan more rayuwan....
Sai kusan magriba matan dasuka karɓi lefen Zahrah suka soma tafiya, bayan Inna ta yaga musu wani abu daga cikin dubu hamsin ɗin daya rage,, haka suka tafi suna mata godiya suna kuma zuba santin kayan domin kuwa koda maƙiyin Zahrah ne yaga wan nan uban kaya da Dr.Sadeeq yayi mata tabbas dole sai ya jinjina abun.....
Lokacin da Zahrah taga irin yawan kayan lefen da Dr yayi mata kasacewa komai tayi, sosai abun yabata mamaki domin kuwa bata taɓa zaton zai ɓarnata dukiya mai yawa harhaka wajen yi mata lefe ba, bayan kuma yasan cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace,,, sai de taƙudura aranta cewa zata faɗa masa kayan sunyi yawa......
Gidansu Doctor...
"Gaskiya da sake Hajiya, yakamata a dakatar da wan nan batun auren na Sadeeq da yarinyar nan, kinkuwa ga gidansu Hajiya? wlhy ko suminti babu a tsakar gidansu zallan turbuɗin yashine, kallo ɗaya zakai musu kafuskanci cewa suɗin faƙara'une basu da komai, kwata kwata ma Sadeeq baisan inda zaije ya nemo aure ba domin a wan nan gidan bana tunanin akwai wata halitta da zata burge wani ɗa namiji acikinsa, kawai dai ni inaga ma asiri sukayi masa wlhy, amma bacin haka banjin dakansa zaije neman aure wan nan gidan!" Auntie Raliya ce ke faɗan haka cikin ɓacin rai.....
Ajiyar zuciya Hajiya tayi cikin ɗacin rai tace "Hmmm Raliya kenan aeni ban isa hana wan nan auren ba ko kinmanta cewa har ƙarana wajen Baffan ku Sadeeq yakai akan naƙi amincewa da aurensa, ni yanzu baruwana acikin lamarin aurensa ko mai ya jajiɓowa kansa shiya sani"
Ƙwafa Auntie Raliya tayi haɗe da sakai tafice daga cikin ɗakin Hajiyar, harga Allah ita sam batason wan nan auren da Sadeeq zaiyi, yarasa ma wacce zai kwaso musu sai wacce wani ya haiƙewa a waje san nan kuma ƴar talakawa futuk...
Auntie Raliya tana fita falo ƙawayenta da ta gaiyato suka kai lefe tare, sukayi caaa akanta kowacce tana ingizata akan cewa tasa afasa auren domin kuwa sam ajin Sadeeq yagirmewa neman aure a wan nan gidan matsiyatan,,, take kuwa Auntie Raliya tahau kan zancen tazauna dabas, takuma ƙuduri aniyar lalata zancen auren abune me sauƙi kuma dakanta zataje ta kwaso kayan lefen ƙanin nata........
Ɓata fuska Zahrah tayi haɗe da tunzuro ɗan ƙaramin bakinta gaba cike da shagwaɓa tace "Dagaske nake faɗa maka kayan lefen nan sunyi yawa, ko ɗazu dawowan Baffa daya gani shima haka yace, kuma kafasan ba kyau yin wasa da dukiya" taƙare maganar tana me langwaɓar da kanta gefe.
Murmushi Dr.Sadeeq yayi haɗe da kwantar da bayansa ajikin kujeran motar dayake zaune akai kana ya lumshe gajiyayyun idanunsa, sautin muryarta nayi masa daɗi sosai...
Shirune yashiga tsakaninsu har na tsawon minti ɗaya.
"Duk abun da mayi miki kin can can ci haka daga gareni ne Zahrah, dan Allah kibar maganar yawan lefen nan, ni banga wani yawa da sukayi ba, naso ma nayi miki wanda yafi wan nan to abubuwane sukai min yawa, amma kin wuce haka a wajena, kuma kinsan ku biyu ne" yafaɗi haka yana me kafeta da idanunsa..
Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da kawar da kanta gefe, sam bataso idan yana kallonta itama ta kalleshi saboda takanjin nauyinsa awasu lokutan,, amma kuma hakanan taji kalmar dayace su biyu ne yaɗan sosa mata rai, wato idan ma ta manta to yatuna mata...
Wani murmushin Dr.Sadeeq yakumayi sakamakon ganin yanda fuskarta ya ɗan sauya lokaci ɗaya yakuma san maganarsa ce batai mata daɗi ba, dama kuma yafaɗi hakanne don yagane cewa tana kishinsa ne ko a'a....
"Bansan wani irin daɗi da kuma farinciki zan tsinci kaina ciki ba aduk sanda wannan ranar taruskeni, amma kuma da zanfi kowa jin daɗi idan har Allah ya gwadamin wannan rana!" yafaɗi haka cikin shauƙi, dason kawar da wancen zancen nasu..
Cike da mamaki Zahrah taɗan saci kallonsa haɗi da cewa "Wace rana ce wan nan?"
"Ranar da zaki zamo mallakina, ranarda za'akawomin ke ɗakina amatsayin matata ta sunna, ranar da zan kwana ina kallon wannan kyakkyawar fuskar taki babuko ƙyafta ido"
Kunyane yakama Zahrah wanda haryakaita ga cusa kanta tsakankanun cinyoyinta, sautari Dr.Sadeeq yakan faɗi abubuwan da suke sanyawa takejin kunyarsa sosai...
Murmushi Dr.Sadeeq yayi haɗe da sake kwantar da jikinsa akan kujeran motar,,,, yana matuƙar son komai na Zahrah ciki kuwa hadda wan nan kunyar nata, tun asalinsa yanason mace me kunya, sai gashi kuma yanzu Allah yabasa, sai de kuma yasan nan gaba kaɗan zaisha fama da'ita saboda idan sunyi aure yasan wan nan halin nata na kunya zatai ta gwadamasa.
Kallon agogon dake ɗaure a hanunsa na dama yayi.
"8:30pm" yafaɗa a bayyane kana yadawo da kallonsa ga Zahrah wacce har yanzu bata ɗago kanta ba.
"Shikenan to tunda dai kunyana kikeji ni zantafi naga dare yasoma yi" yafaɗi haka adai dai lokacin da yake ƙoƙarin ɗaura sit belt ajikinsa..
Sai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 47