"Wayyo Allah na, nashiga uku, me zancewa Zaid? kaicona, nakasa haƙuri, gashi yanzu na jawa kaina" abun da Afrah ke faɗa kenan acikin zuciyarta, gaba ɗaya tsoron ma tashi daga kan gadon take, da ƙyar ta iya jan bargo ta rufe jikinta dashi.
Ruwa ne ke dukan kansa, yana tsaye agaban shower kamar wani statue, iyaka ƙololuwar ɓacin rai, yau ya shigesa, baitaɓa tunanin zaiji ciwo acikin zuciyarsa, wai dan yasamu Afrah ba a cikakkiyar virgin ba, sai gashi abun ya juye tunaninsa.
"Ashe dama haka maza sukeji, idan basu samu matarsu a cikakkiyar budurwa ba?" yatambayi kansa.
"ZAHRAH"
itace wacce tafara faɗo masa acikin ransa, take fyaɗen da yayi mata yashiga dawowa cikin kansa filla filla, tamkar alokacin komai ke wakana haka yaji acikin jikinsa, da sauri yasanya hanu ya kama kansa, haɗe da kurma wani uban ihu, yama manta da cewa acikin toilet yake.
Wani irin nadama ne me girma ya ruskesa acikin zuciyarsa, sai yanzu ya tabbatar da cewa bai kyautawa Zahrah ba, yaku ma cutar da ita cutarwa me girma, ya ruguza mata alfaharinta.
"Meyasa yayiwa Zahrah haka? me yasa yarabata da budurcinta? wani irin cutarwa ne yayiwa Zahrah haka?" yatambayi kansa cikin tsananin tsana da ƙyamar kansa.
"I hurt you Zahrah, why do i did this to you? I'am stupid, i dont have sense, meyasa zan aikata haka? kaicona dana cutar da rayuwarki, na gusar miki da farincikin ki, na hanaki mallakawa mijinki budurcinki, na ƙwace budurcinki taƙarfin tsiya, forgive me, i hate my self, because of what i did to you, natsani duk wata rayuwar duniyar nan, rayuwa batamin daɗi Zahrah!!" cikin wani irin murya me haɗe da sautin kuka Zaid ke faɗan haka.
Haƙiƙa yau baida abun da zaice, yasan Allah ba azzalumin kowa bane, sai wanda ya zalunci kansa, gashinan shi ya zalunci kansa, kuma yagani, gashi yanzu Allah ya haɗashi da wata ballagazar mace, wacce ta raba budurcinta ga mutanen titi, yanzu ga abun da Zina ta haifar masa, bayajin son Afrah ko ɗigo acikin zuciyarsa, amma kuma yaji matsanancin ciwon samunta a haka da yayi, to idan dai shi yaji ciwon samunta ahaka, me mijin Zahrah kuma zaice? shida yake so da kuma ƙaunarta.
Jingina kansa yayi da jikin bangon toilet ɗin, yayinda ruwan dake fitowa acikin shower ke dukan bayansa. Rumtse jajayen idanunsa yayi, haɗe da sanya haƙoransa ya danne laɓɓansa, jiyake kamar yata gwara kansa ajikin bango, har sai kan ya rabe gida biyu, koda zaiji salama, acikin zuciyarsa, hanunsa na dafe da saitin zuciyarsa, dake yi masa zafi, yajima a tsaye ruwa na dukansa, har sai da jikinsa yasoma karkarwa kafun ya kashe shower'n....
Buɗe ƙofarsa, yayi dai dai da bugawan zuciyar Afrah, take jikinta yacigaba da karkarwa kamar anjona shocking.
Ko kallon inda take baiyi ba, direct gaban drawer ɗinsa ya nufa, wata farar T-shirt ya ɗauka ya sanya ajikinsa.
Ganin baice da ita komai ba, yasanya ta daɗa firgicewa, batasan me ze mataba nan gaba, cikin muryarta me ɗauke da tarin tsoro, haɗi da fargaba tace.
"Dan Allah kayi haƙur......"
"Get out!!"
yafaɗi haka batare daya bari ta ƙarasa maganar dake cikin bakinta ba.
Cikin kuka takuma cewa
"Dan Allah kayi...."
"I say get out!!!"
yafaɗi haka atsananin tsawace, har sai da Afrah taji ƴaƴan cikinta sun kaɗa.
Gaba ɗaya ta ruɗe ta firgice, yanayin yanda taga idanunsa sunyi jajur dasu, shine abun da yafi komai ɗaga mata hankali, da gudu ta fice daga cikin ɗakin, ko kayanta bata tsaya ɗauka ba, sai blanket ɗin da tayi amfani dashi wajen rufe jikinta.
Kwalbar turaren dake riƙe a hanunsa ya yi wurgi dashi, zuwa wajen wani ƙaton mirror wanda ke kafe ajikin bango, take mirror'n ya fashe, haɗe da tarwatsewa a ƙasan tiles.
Wani irin huci yake fitarwa ta bakinsa, yayinda yasanya duka hannayensa ya kama ƙugunsa, jiyake gaba ɗaya duniyar na juya masa.
"Me ake da irin wannan rayuwa, me ɗauke da takaicin?" yatambayi kansa.
Idanunsa ya sauƙe akan fridge ɗin dake ɗakin, wanda yake a cike da kwalbar wine ɗinsa, a irin wannan halin dayake ciki, wine ce kaɗai zata iya bashi nutsuwa, duk da yasan ba lallaine ta iya ciresa acikin ƙuncin dayake ciki ba, amma tabbas zata iya rage masa damuwa, sai dai kuma bayajin aduniya zai iya ƙara aikata wani abu na saɓon Ubangijinsa, ko a iya nan Allah yaɗauki rayuwarsa, haƙiƙa ya jarabtu, soyayyar Zahrah kaɗai da Allah, yasanya masa, yazamemasa babban jarabawa acikin rayuwarsa.
Zama yayi a bakin gado, haɗe da bin blanket ɗin dake shimfuɗe akan gadon, da kallon takaici, bakomai ne yafaɗo masa arai ba, kamar randa yayiwa Zahrah fyaɗe, haka gaba ɗaya tsakiyar gadon ya ɓaci da jininta, yasamu Zahrah a cikakkiyar budurwa.
"Yayi gaggawa? me yasa bai bari ya amshi budurcinta ta hanyar aure ba?" wasu siraran hawayene suka fito daga cikin idanunsa, suka sauƙa akan ƙuncinsa, sakamakon tunowa da yanda ya farke Zahrah da yayi.
Ahankali ya taka ƙafarsa ya ƙarasa gaban wani tangamemen hotonta, dake liƙe ajikin bangon ɗakin.
Zama yayi agaban hoton haɗe da cewa.
"Kiyafemin Zahrah, a yanzu nayi nadama marar amfani, ni dakaina namiki fyaɗe, nidakaina nasa aka je har ƙofar gidanku aka ya da ke, meye amfanina Zahrah? me yasa nazamo mugu maƙuntaci agareki? nagodewa Allah dayasa baki aureni ba, domin ban cancanci zama miji a gareki ba, ni ban dace dake ba Zahrah, to tayama zan dace dake? ninefa wanda yayi miki fyaɗe, nine azzalumin dana rufe idanuna, na aikata ba dai dai ba akan ki, to taya zaki yarda ki aureni, a'a ko kin yardama ni bazan yarda ba, domin ni dake bamu dace ba, bazan yarda nasake cutar dake akaro na biyu ba, inasonki Zahrah so ba irin wanda kika sani ba, inamiki son da aduniya banayiwa kowa irinsa, sonki ajinina yake, har abada bazan taɓa daina sonki ba, ki hukuntani Zahrah, kimin duk irin hukuncin da kikeso, nacancanci ki hukuntani Zahrah, ko kasheni kikayi bazanga laifinki ba, saboda nasan koda kasheni ɗin kikayi bazaki huce daga abun dana aikata a gareki ba, ki ɗaga hanu ki dakeni Zahrah, kice Zaid natsaneka, banasonka, ki faɗi haka agareni Zahrah dan Allah, ki faɗa ko zanji salama acikin zuciyata!!!"
kuka sosai Zaid keyi kamar wani yaro ƙarami yana me rungume da hoton Zahrah acikin ƙirjinsa.
Yayi kuka irin wanda bai taɓayin irin saba, yayi kuka wanda har sai da ya haifar masa da ciwon kai, kusan sama da awa ɗaya ya ɗauka yana zaune, agaban hoton Zahrah, da ƙyar ya'iya jaye jikinsa a wajen, ya faɗa bathroom, alwala yayi haɗe da buɗe kofar yafito, idanunsa sunyi luhu luhu dasu, kallo ɗaya zakayi masa kasan ya sha kuka ya ƙoshi.
Blue ɗin jallabiya yasanya, direct ya wuce masallaci, duk da cewa kowa yagansa zai gane cewa yana a cikin damuwa, amma sam baidamu da hakan ba, uban kowa ma yasan yana cikin damuwa, shiba damuwarsa bane, matsalansa ma kaɗai ta ishe sa.
Tunda tashiga cikin ɗakinta take kuka, yau ne karo na farko a rayuwarta, da tayi babban nadamar bada kanta da tayi a waje, yau tayi nadama ƙwarai, yau ta ga sakarci dakuma wautanta, da ta ɗauki kyautar budurcinta sukutum, ta dan ƙawa wani banza, wanda yayi mata ƙaryan zai aureta, me ake da irin wannan rayuwar, wayewar banza, wayewar wofi, taɗauki zugan ƙawayenta, da suke ce mata wai inmace batasan daɗin sex ba bata waye ba, ta biyewa son zuciyarta taje ta bawa wani banza kanta, batare da sadaki ba ya haye kanta, ya karɓi budurcinta, batare da ko da sannu ba, wace irin banzar hallakakkiyar waye wace wannan? wayewar da zata saka kaji kunyar Allah da ta mutanen duniya, kaicon irin wannan wayewar, tir da irinta, bata taɓa manta yanda su Asma ke zugata akan cewa wai yakamata ta bada kanta ga saurayinta Ameer, ta kuma san duniya, duniya ma ta santa, har cewa suke wai ita baƙauyiya ce, saboda kawai bata yarda wani namiji ya taɓa jikinta, haka suke wareta acikinsu, haka suke nuna mata kyara, wai don kawai bata bari maza suna taɓata, tabiye sharrin zuciya data ƙawaye, ta kuma ɗauƙi shawararsu, ta yi watsi da mutuncin kanta, gashi yanzu tun aduniya, ta shiga kunyar mijinta, takuma shiga halin nadama da danasi, ga kuma tozarcin da zata fuskanta daga wajen mijinta.
Zama tayi daɓas aƙasa tashiga rera kukanta, haɗe da tsinewa Asma da ma duk wasu ƙawayenta, da sukayi ruwa da tsaki, wajen tsundumata, cikin halakan data faɗa, shikuwa saurayinta Ameer, wanda shiya fara saninta ƴa mace, ta zuba masa tsinuwa yafi guda ɗari biyu, da ƙyar ta iya lallaɓan kanta tashiga toilet donyin wanka..
Yajima acikin masallacin kafun ya dawo gida, abun dayajima baiyiba kenan, wai yaje masallaci yajima har haka, karatun Al'Qur'ani yayi, kuma da yardan Allah yaɗan samu salama acikin zuciyarsa..
Afrah najin shigowarsa cikin gidan, ƙafafunta yasoma rawa, take taji wani irin ciwon ciki ya kamata, mugun tsoronsa takeji, tun ada ma, balle yanzu kuma da wannan abun yashiga tsakaninsu, ta tabbatar sai yakasheta acikin gidannan, kuma ya kashe banza.
Yana shiga cikin ɗakinsa, ya ɗauki magungunansa yasha, tashi yayi yafice daga cikin ɗakin nasa, direct ɗakinta ya nufa.
Tanajin motsin ana buɗe ƙofarta ta miƙe zunbur, take wani irin fitsari ya zubo mata, tsabar tsoro, aikuwa tana jefa idanunta, cikin nasa, taji numfashinta, na shirin ɗaukewa.
Da rinannun idanunsa yake kallonta, ganinta da yayi yasake tuna masa ɓacin ransa, jiyake ya tsaneta, amma kuma yazama dole yayi mata tambayoyin dake cikin ransa..
"Zauna" yafaɗi haka cikin dakiya.
Jikin Afrah na rawa ta zauna aƙasan tiles.
Ƙafansa ɗaya yasanya, yataka kan gado, haɗe da ɗan ranƙwafowa.
"Dama ke karuwa ce?" first tambayar daya fito daga cikin bakinsa kenan.
Ƙirjin Afrah ne ya buga, take hawaye suka ɓalle akan fuskarta, kanta tashiga girgizawa alamar
"A'a"
Laɓɓansa ya cije cike da takaici yace.
"Da bakinki nakeso, ki bani amsa bada kai ba."
"A....a wallahi ni.....ba..ba..ka..ruwa..bace!" murya a sassarƙe tabashi amsa.
"Kinsan me ake ƙira da karuwa?"
Yatambayeta.
Dasauri ta kaɗa kanta, saikuma tatuna da abun dayace mata, baki na rawa tace "Karuwa itace mebin maza, wacce take zaman kanta"
"Good, ashe kinsan mene ake ƙira da karuwa, kenan ke ɗin karuwa ce?"
Da sauri tace "Wallahi niba karuwa bace"
"Idan ke ba karuwa bace, dan ubanki ina kikai budurciki!!!" amatuƙar tsawace yayi maganar, saboda ya matuƙar harzuƙa.
Guntun fitsarin da take ta riƙewane ya silalo, tsabar ta tsorata, ƙyarma tafara tamkar wata mejin sanyi, tsabar tsorata da yanayinsa da tayi, ta makasa ce dashi komai.
"Shirun da kikayi ya nuna alamar cewa eh ke cikakkiyar karuwace, mazinaciya, me kike nema arayuwarki, kina ƴar ƙaramar yarinya dake?" yatambayeta yana me ƙare mata kallo.
Kanta tashiga girgizawa, akaro na barkatai.
"Kayarda dani, wallahi niba karuwa bace, bantaɓa karuwanci ba!" tafaɗi haka tana kuka.
"Okay to tunda dai kince ke ba karuwa bace, ba naci ubanki, wataƙila zaki faɗamin inda kika kai virginity ɗinki" yafaɗi haka yana me ƙoƙarin zare belt ɗin wandon jeans ɗin dake sanye a jikinshi.
Da gudu ta rarrafo ta ƙaraso garesa, zubewa tayi akan ƙafafunsa tana kuka.
"Dan Allah kayi haƙuri, kayafemin, wallahi sharrin shaiɗanne, dakuma na zuciya, amma bantaɓa zaman karuwanci ba!" kuka take wiwi kamar wacce akace uwarta ta mutu.
Tsayawa yayi cak yana me kallonta, kuka take tsakaninta da Allah.
"Mene naka najin haushinta Zaid? mene naka nacewa zaka daketa? idan ita karuwace kai menene?" wata zuciyarsa ta tambayesa.
Rumtse idanunsa yayi haɗe da cije laɓɓansa, da ƙyar ya iya janye ƙafafunsa ya zauna, abakin gado.
Afrah dake duƙe a ƙasa tana kuka ya kalla.
Cikin wata irin murya a cushe yace. "Afrah!"
Dasauri Afrah taɗago fuskarta ta kalleshi, duk taɓata fuskar ta da majina, ansha kuka anƙoshi.
"Zo" yace da ita ataƙaice.
Babu musu ta ƙaraso gabansa ta durƙusa.
"Meyasa kika zaɓi banzatar da mutuncinki a waje Afrah?" tambayar dayayi mata kenan, sai dai wannan karon, ba acikin tsawa yayi mata tambayar ba.
Cikin kuka Afrah tasoma cewa "Bansan dalili ba, amma nabiyewa son zuciyata ne kawai, nabiyewa zugan shaiɗan da kuma shaiɗanun ƙawaye, najefa rayuwata a halaka, nasan irin wannan ranan zatazo, amma bantaɓa kawo cewa al'amarin zai kai har haka ba, domin wanda ya fara sanina amatsayin ƴa mace, yayimini alƙawarin aure, saboda haka bantaɓa kawowa araina cewa rashin kasancewata ba a budurwa ba zai kawo min wani abu, saboda na ɗauka wanda yafara sanina a cikakkiyar ƴa macena shine wanda zai aureni, ashe shima ƙarya yakemin, ba aurena zaiyi ba, yayi hakane kawai,dan na amince nadinga bashi kaina, aduk sanda ya buƙata!" taƙare maganar tana me tsananta kukanta.
Rumtse idanunsa yayi, haɗe da cije laɓɓansa, akaro na sau babu adadi.
"Banason kuka" yafaɗa ataƙaice yana me kawar dakansa gefe.
Duk da cewa kukan nacinta, amma haka ta haɗiye, tasoma ƙoƙarin yin shiru.
"Kinyi wanka?" yatambayeta still kansa na na kallon wani wajen.
"Eh" tafaɗa murya a raunane.
Miƙewa yayi daga zaunen da yake, haɗe da dubanta.
"Zanshiga na kwanta, banason naji koda motsinkine, ki zauna anan ɗakin, banason damuwa" yanakaiwa nan azancensa, yasakai yafice daga cikin ɗakin.
Afrah kam kan gadonta ta haye taci gaba da rera kukan danasani, ahaka har baccin wahala ya ɗauketa.
Zama yayi akan gado, haɗe da ɗaura idanunsa akan hotonta, hawayene suka zuraro daga cikin idanunsa, abune mawuyaci yadaina sonta, duk da yasan a yanzu ta haramta agareshi, kuma yana gudun ɗaukarwa kansa zunubi, amma kuma akan sonta, baya iya control ɗin zuciyarsa, akullum maganaɗisun ƙaunarta, ƙara fusgarsa take, saidai kuma kamar yanda yaɗaukarwa kansa alƙawari, zai ci gaba da addu'a har Allah yakawo masa sauƙi da sassauci acikin zuciyarsa akan soyayyarta..
*(So ba ƙarya bane, So gaskiyane, amma kuma wanda baitaɓa yiba bazai gane ya yake ba, haka kuma wanda baiyi zurfi acikin saba, bazai taɓa gane ya zafinsa yake ba, ba acire so alokaci guda, a sannu komai yake gushewa, ƙauna acikin jini take, bata taɓa gushewa, watarana a sannu so zai gushe, amma ƙauna tana nan. Ku yiwa Zaid da Zahrah uzuri, wallahi soyayya ta wuce gaban kwatance, idan kanason abu baka ganin laifinsa, shi so hana ganin laifi ne, meyin so shikaɗaine zai gane inda kalamaina suka dosa.)*
*(Yau fejin nasu Zaid ne, bazamu waiwaya gidan Doctor ba, team Doctor da Zahrah i'am sorry)*
*9/february/2020*
*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 108*
Kaikawo take tayi a cikin kitchine ɗin, sauri take ta kammala aikinta, tsaye take acikin kitchine ɗin, tana wanke wani plate dake riƙe a hanunta, sosai nayi mamakin ganinta a haka, rigace irin T-shirt me faɗinnan sanye ajikinta, duka duka tsayin rigar ko rabin cinyanta bai ƙarasa ba, bata kuma sanya wando dan rufe cinyoyinta ba, wani irin slipper ne me kyaun gaske sanye aƙafarta, wanda aka ƙawata samansa da wani kyakkyawan follower,
Irin yanayin shigar nata yasanya tayi kama da irin yaran turawan nan.
Sam bata ji motsin shigowarsa ba, hakan yasa bata kawo cewa akwai wani mahaluƙi dake kallonta ba.
Sake gyara tsayuwarsa yayi, haɗe da jingina bayansa, da jikin ƙofar fita daga kitchine ɗin, sosai tayi masa kyau, babu abun daya fi ɗaukar hankalinsa ajikinta, kamar hips ɗinta, ga santala santalan cinyoyinta, da suka bayyana kansu, gwanin ban sha'awa, gaskiya komai na Zahrah me kyau ne, ta cika mace hundred percent, yajima yana fata da burin samun cikakkiyar mace, me cikar halitta ka marta, a matsayin matar aurensa, sai gashi Allah Ya dubesa ya basa Zahrah.
Ɗan tsayawa tayi, haɗe da sanya hannayenta bisa ƙugunta, tana me sauƙe numfashi, a hankali, da'alama dai akwai gajiya a tattare da'ita.
"Kin gaji ko?"
Cike da mamakin jin muryarsa, acikin kunnuwanta, da tayi ta juyo, tana me fuskantarsa.
Murmushin sa me kyau, ya sakar mata, haɗe da soma takowa zuwa gareta.
"Yaushe kadawo bansani ba?" ta tambayeshi, cike da tsananin mamaki.
"Najima da dawowa, nadai tsaya kallon abar sona ne" yafaɗi haka yana me lumshe gajiyayyun idanunsa, sosai yakejin gajiya ajikinsa, baƙaramin aiki yau yasha a office ba.
"Sannu da dawowa!"
tafaɗa tana sakarmasa murmushi.
Jawota cikin jikinsa yayi, haɗe da rungumeta, kansa ya ɗaura akan wuyanta, wata ajiyar zuciya, me ƙarfi ya sauƙe.
"Nayi kewarki sosai my lovely wife!" cikin murya, me sanyi, ya yi maganar.
Murmushi takuma sakar masa, haɗe da langwaɓar da kanta gefe gudu. "Nima nayi kewarka Hubby na!" cikin salo ta ƙare maganar.
"Dagaske kema kinyi kewata my wife? nifa dukanki nayi kewarki!" yafaɗi haka yana meyi mata wani irin kallo, dake ɗauke da wani tarin ma'anoni masu yawa.
Ganin kallon dayakeyi mata, yasa tasaki murmushi me ɗan sauti, ƙoƙarin janye jikinta daga nashi tasoma yi.
Ƙam ya riƙeta, haɗe da sake mannata acikin chest ɗinsa, da alama dai bayason tacire jikinta acikin nasa jikin.
"Uh dan Allah, Kabarni na ƙarisa aikina, kuma mafa duk ƙauri nake, amma kaketa mannani a jikinka, kaɗan bari nayi wanka kaji!" tayi maganar cikin yanayi na lallashi, tasani sarai, idan dai ba lallashinsa tayi ba, to bazai bari ta kammala aikin data fara ba.
"Nidai naƙi wayon, kuma ni banji wani ƙauri da kike ba, princess nadawo amatuƙar gajiye, gashi kuma ganinki ahaka yasake ɗaura min wani gajiyan, please kiyarda ko 30 minute ne kiban, ina da buƙatarki fa akusa dani...."
Bata bari ya ƙarasa zancen nasaba, tayi saurin toshe masa baki da tafin hanunta, shagwaɓe fuska tayi, haɗe da marerece idanunta, kanta ta girgiza masa akan kada yace komai.
Hanunsa takama, suka fice daga cikin kitchine ɗin, haka yake binta tamkar wani raƙumi da akala, suna shiga cikin bedroom, ta zaunar dashi akan gado, bathroom ta wuce direct, ruwan wanka me ɗan ɗumi, ta haɗa masa acikin bathtub, haɗe da sanya masa turaren wanka, me daɗin ƙamshi, acikin ruwan, take banɗakin ya gauraye da ƙamshi, tana fitowa daga cikin bathroom ɗin, ya kafeta da manyan idanunsa, durƙusawa tayi ta cire masa takalmi, da kuma safar dake ƙafarsa, ita da kanta tacire masa suit ɗin jikinsa, dakuma necktie ɗin dake saƙale a jikin wuyansa, Hanunta ta sanya, ta shiga ɓalle masa aninayen rigar dake jikin sa, ahankali ta zare masa rigar, shi dai haka ya tsaya, yana kallonta, yana me kuma lumshe idanunsa, lokuta zuwa lokuta, murmushine ya bayyana akan fuskarta, lokacin da idanunta, suka sauƙa akan faffaɗan chest ɗinsa, haƙiƙa yanada jiki me kyau, tasan hakan kuma, bazai rasa nasaba, da yawan gym ɗin dayakeyi ba.
Kallonsa tayi haɗe da sake sakarmasa murmushi, hanunsa ta kama daniyar janshi zuwa cikin toilet, da ƙarfi yajawo hanunnata, tafaɗa jikinsa, matseta yayi ajikinsa, haɗe da matso da fuskarsa gaf da tata.
"Ahakane zanje nayi wankan, bayan baki ciremin kaya ba?" yafaɗi maganar ƙasa ƙasa.
Cikin rashin fahimta tace.
"Wani irin kaya kuma, bayan wanda nacirema yanzu?"
Hanunta yakama, ya ɗaura akan belt ɗin dake saƙale jikin wandonsa, tsareta yayi da idanu, da'alama dai har wandon ma, so yake ita tacire masa da kanta.
Kunyan sane ya kamata, amma tasan wayon da zata masa.
"Naji zancirema, muje cikin toilet ɗin" tafaɗi haka tana nufar ƙofar toilet ɗin.
Jin abun da tace, yasanyasa, rufa mata baya, suna shiga cikin toilet ɗin tadawo baya, da sauri tafice daga cikin toilet ɗin, ta rufosa ta baya.
Dariya tashiga ƙyalƙyalawa, tana mejin daɗin wayon da tayi masa.
"I am sorry Hubby, kayi wanka kaji, banaje na kula da girkina, kada ya ƙone!" tafaɗi haka cikin muryar da ta tabbatar cewa zai jiyota.
Jin da tayi yana ƙoƙarin buɗe ƙofar toilet ɗinne, yasanya da sauri ta fice acikin ɗakin gaba ɗaya, tana dariya.
Murmushi me sauti shima yayi, kana ya girgiza kansa, waishi Zahrah zatayiwa wayo, hmmm.
Kwanciya yayi acikin bathtub ɗin , sosai yaji daɗin ruwan wankan data haɗa masa, ga ɗumi ga kuma ƙamshi me daɗi, a hankali gajiyarsa ta soma warwarewa.
Tana kammala girkin, ta zuba acikin manyan food flask, haɗe da jeresu cikin basket's masu hanu, sosai takejin, gajiya ajikinta, amma yazatayi, tunda ita tasanya kanta, duka kwanukan datayi aiki dasu, saida ta wankesu tas, kana ta gyara kitchine ɗin nata, lokaci ɗaya komai na kitchine ɗin, yadawo tsab dashi.
Tana shigowa cikin ɗakin, bata ko kalli inda yake ba, da sauri ta faɗa cikin bathroom, sam bataso ma yaganta a haka, wujiga wujiga da ita, duk ƙamshin kayan girki take, ruwan ɗumi ta tara tayi wankanta, take itama taji rabin gajiyarta, ya kama gabansa, towel ta ɗaura ajikinta, haɗe da buɗe ƙofar bathroom ɗin tafito.
Tsayawa tayi tana kallonsa, Tsaye yake agaban dressing mirror, yayi matuƙar kyau, cikin sky blue ɗin, shaddan dake jikinsa, agogo yake ƙoƙarin ɗaurawa a tsintsiyar hanunsa, yayinda tulin gashin kansa ke ta faƙan ƙyalli, da'alama dai yasha gyara, da man gashi, na musamman, akan fuskarsa kuwa, ƙawataccen sajensa ne, ya samu waje, ya kwanta luf akan ƙuncinsa.
"Wallahi duk wanda yace Dr.Sadeeq, bai haɗu ba yayi ƙarya" Zahrah tafaɗi haka acikin zuciyarta.
Dawo da kallonsa yayi gareta, fuskarsa ɗauke da murmushi yace. "Sannu da fitowa, Hajiyar wayo"
Itama murmushin tayi masa, haɗe da takowa zuwa garesa, hakanan ta tsinci kanta, da matuƙar son rungumesa, lokaci ɗaya ta faɗa jikinsa, haɗe da ɗaura kanta akan ƙirjinsa, shima dama nema yake, sosai ya matseta acikin jikinsa, tare da sanya hanunsa, akan bayanta, yana shafawa, a hankali, lumshe idanunsu, sukayi su duka, suna masu, sauƙe ajiyar zuciya.
"Kayi kyau sosai Hubby!" Zahrah tafaɗa cikin murya me sanyi.
"Nagode my princess!"
yabata amsa, yana me faɗaɗa, murmushin dake, kan fuskarsa, yanason Zahrah har acikin ɓargonsa, so sosai yakeyi mata, ko kaɗan baya fata Allah, Ya nuna masa, ranan dazai ɓata mata, alƙawari ya ɗaukarwa kansa, cewa Insha Allah, Bazai taɓa wulaƙanta Zahrah ba, koba komai itaɗin farincikinsa ce, sannan kuma tana da, wani irin girma, na musamman, acikin idanunsa, itace mace ta farko, daya fara sani, acikin rayuwarsa, itace macen data fara, jiyar dashi wani daɗi, wanda bai taɓa sanin akwai irin shi, acikin wannan, duniyar ba, Zahrah ta shayar dashi zumanta, wanda ɗanɗanonsa, keda wahalan mantawa, duk da cewa bai sameta, amatsayin cikakkiyar budurwa ba, amma haƙiƙa tanada wani, matsayi na musamman agareshi.
"Hubby!!"
taƙira sunansa cikin wani irin cool voice.
"Ummm princess ɗina, ya akayi ne?" yayi maganar yana me duban fuskarta.
Murmushin dake ƙara mata kyau, ako da yaushe idan tayishi, tasakar masa, haɗe da zare jikinta daga nasa, body lotion ɗinta tajawo tasoma shafawa, batare da tace da shi, komai ba.
"Na lura tunda nace miki, yau zamu fita, kike ta ɓare ɓare, kodai ma nace na fasa ne" yafaɗi haka yana me jingina kansa da bango, alamar nazari.
Da sauri ta juyo ta kalleshi.
"Dan Allah, Hubby karkace ka fasa, kaga fa har na kammala abincin!" tafaɗi haka a shagwaɓe.
Murmushi yayi haɗe da cewa "Cigaba da abun da kikeyi, wasa nake miki"
Murmushin jin daɗi tayi, haɗe da ɗaukan powder, tasoma shafawa akan fuskarta.
Batayi wani kwalliya sosai ba, janbaki da kwalli kawai ta saka, saikuma mascara, wanda sakasa yazamemata sabo, dazaran ta goga akan eye lashes ɗinta, sai kaga kamar eye lashes ɗin kanti tasanya, sosai kuma tayi kyau.
Wata haɗaɗɗiyar abaya gown, wanda aka sanya mata, acikin kayan aure, taciro ta sanya, sosai rigan ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 47