Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
saurin dafe saitin zuciyarsa Zaid yayi, wanda yakeji tamkar zatayi tsalle ta fito waje.. Jingina bayansa yayi da bango haɗe da lumshe idanunsa.. Zafi yakeji a ƙirji dakuma zuciyarsa, take wani irin ciwon kai da zazzaɓi me zafi suka sauƙar masa alokaci guda.. Dr.Sadeeq dakansa yasanya Zahrah a mota, wacce har yanzu kuka take, ataƙaice dai tsabar kuka numfashinta har ɗaukewa yake.... Saboda tsabar gudun da Dr.Sadeeq keyi cikin mintuna ƙalilan suka isa gida, kowa acikinsu yana cikin tashin hankali. Inna ce takama Zahrah takaita ɗakinta. Bayan minti kaɗan Inna tafito daga ɗakin Zahrah da sauri. "Likita temaka numfashinta yana shirin ɗaukewa, taƙi daina kukan" Inna tafaɗa a ruɗe. Dr.Sadeeq yana shiga ɗakin yace inna tabasa ruwa, aikuwa mintuna kaɗan Inna takawomasa ruwa, cewa yayi Inna taɗan basu wuri bamusu Inna tafita a ɗakin... ɗago Zahrah Dr.Sadeeq yayi haɗe da kai kofin ruwan bakinta, sosai tasha ruwan, take ta soma sauƙe ajiyar zuciya, amma still hawaye na gangara akan fuskarta.. Idanunta dasukayi luhu luhu saboda kuka ta ɗago dasu takalli Dr.Sadeeq, saikuma tasake fashewa da kuka, haɗi da faɗawa cikin jikinsa tarungumesa ƙam, hanunsa duka biyu yasanya shima ya rungumeta, a hankali ya shiga hura mata kunnen ta, saboda hakan zai sa taɗan samu relief, koba komai kukan nata zai tsagaita. Har tsakiyar kansa yakejin kukanta. Tsawon mintuna 15 yakai yana hura mata kunne, a hankali tasoma rage sautin kukan nata, bayan kamar mintuna 5 yajita shiru, sai sauƙar numfashinta da yake ji akan ƙirjinsa akai akai.. Yana duba fuskarta yaga tayi bacci, hawayene yaji suncika masa idanu, tabbas Zahrah taga ƙaddara a rayuwarta, wani irin tausayinta yakeji me tsanani, tabbas idan ya aureta zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya mantar da ita duk wani damuwa da tshin hankalin da ta tsinci kanta ciki, zai kuma yi iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin yabata farinciki me ɗorewa. A hankali ya kwantar da'ita, haɗe da sanya hanu ya gyara mata dogon gashinta da ya rufe mata fuska. Yajima yana kallonta kafun daga bisani ya tashi yafita daga cikin ɗakin... Zaune yasamu Baffa da Inna a tsakar gidan sunyi jigum. Yana fita suka tsaresa da ido da'alama bakinsu ɗauke yake da tarin tambayoyi.. Ajiyar zuciya ya yi haɗe da cewa "Tasamu bacci, kada ayi wani abu da zai tasheta, ni zan wuce office anjima zandawo" Har bakin motarsa Baffa yarakasa bayan sun tattauna wata magana me mahimmanci.... Zaid ne zaune a cikin falon sa dake guest hause ɗinsa, kallo ɗaya zakai masa kafahimci cewa yana cikin tashin hankali, kwalaben giyane zube a gabansa, guda uku daga cikin kwalaben duk ya shanye giyan dake a cikinsu, ba abun dake gigita masa tunani da ƙwaƙwalwa kamar yanda Zahrah ta nunamasa tsana a fili ƙarara, kallonsa yakai ga hanunsa na dama wanda yake fidda jini, bakomai yajawo hakan ba face ƙarfen da Zahrah ta kwaɗa masa akan hanun,, runtse idanunsa dasuka kaɗa sukai jajur yayi, haɗe da cije laɓɓansa, wani irin zafi yakeji acikin zuciyarsa a duk sanda idanunsa suka hasko masa lokacin da Zahrah taje ta faɗa ƙirjin Dr.Sadeeq, jiyake kamar ya kurma ihu, ko zai samu salama acikin zuciyarsa.... Ahankali yamiƙe tsaye haɗe da nufar ɗakinsa, Da ƙyar yake iya tafiya, saboda abuge yake mankas, kai tsaye ɗan ƙaramin drowern dake kusa da gadonsa yanufa, wani tablet yaɗauko haɗe da ɓarewa kusan guda takwas ya watsa a bakinsa, haɗi da korawa da ruwan swan... Faɗawa kan gado yayi yana me rumtse idanunsa, "Natsaneka" shine kalmar da tafi ɗaga masa hankali aduk cikin kalaman da Zahrah ta faɗa masa. itace kuma kalmar da takeyi masa yawo acikin kansa, cikin wani irin yanayi Zaid yatashi tsaye haɗe da nufar wajen da yake aje kayan shafansa, watsi yashigayi da duk wani abu dake kan dressing mirror ɗin nasa, lokaci ɗaya yayi buji buji da ɗakinsa, yayinda ya fasa gaba ɗaya kwalaben turarensa, har sai da wasu kwalaben suka yankesa a hanu da ƙafarsa, amma don tsabar baƙin kishi ko zafi baiji ba, idanunsa Zahrah kawai suke hangomasa kwance a ƙirjin Dr.Sadeeq. Lokaci ɗaya yaji wani irin juwa ta ɗebesa, harsai da yariƙe bango, a daddafe yaƙa risa kan gadonsa ya kwanta, ji yayi kansa yasoma juyawa, yayinda idanunsa suka soma rufewa, yasoma ganin komai bibbiyu, cikin mintuna ƙalilan idanunsa suka rufe ruf..... *Follow me on Whatsapp and Wattpad* *25/December/2019* *Wattpad user name fatymasardauna* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *SHU'UMIN NAMIJI !!* *Written By* *Phatymasardauna* *Dedicated To My Brother KHABIER* *🌈Kainuwa Writers Association* _{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_ *https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation* *WATTPAD* @fatymasardauna *Editing is not allowed📵* *CHAPTER 68 to 69* Ba'itace ta farka ba sai wajen ƙarfe ɗaya na rana.. A hankali take ware manya manyan idanunta da suka kaɗa suka zama jajur dasu, ba tun yanzu ta farka ba, kawai dai Allah ne be bata daman buɗe idanun nata ba sai yanzu. Tun farkawarta kuwa take cikin tsanani da kuma mamakin mutum mai taurin zuciya irin Zaid, lallai shiɗin yacika ɗan iska kuma shu'umi, duk da irin girman laifin da ya aika ta mata, hakan baisanya yaji ɗar ko kuma shakkan tunkarar ta ba, lallai shiɗin acikin ƴan iska ma daban yake,, haka nan taji gaba ɗaya zuciyarta ta ƙeƙashe takuma bushe, lallai tunda ya nuna mata shiɗin babban ɗan iska ne yakamata ace itama ta nuna masa iyakar iskancinsa, tunda har baiji kunyar tako ƙafa yazo gareta ba, to tabbas itama yakamata tacire kunya, wajen ganin ta koya masa hankali... Sai dai kuma kome zatayi bazata huce ba, saboda iyaka kuma maƙurar cuta Zaid yayi mata, ya mata illa dakuma tabon da bazata taɓa mantawa ba, harta koma ga mahaliccinta kuwa, Zaid ne ya surka mata farincikinta da wani irin mummunan baƙin duhu, ya katse mata jin daɗi da kuma walwalanta, ya lalata mata rayuwa a rana ɗaya, ya ruguza duk wani buri da fatanta, ya gwada mata ƙarfi ya amshi budurcinta cikin yanayi na tozarci, me yafi wan nan ciwo a rayuwar ƴa mace? tasan ƙiyayya amma kuma zafin ƙiyayyar da takeyi mawa Zaid na daban ne, tabbas idan da kisan kai yana da kyau a addinance to haƙiƙa ba abun da zai hanata kashe Zaid san nan kuma itama ta kashe kanta, saboda ƙuncin da ya mamaye zuciyarta ba'irin ƙuncin nan bane da yake fita, lallai ƙuncin zuciyarta dawwa memme ne, sai dai kawai ta roƙi Allah daya sassauta mata..... Hawayen da suka fito daga cikin idanunta suka gangaro ta gefen kumatunta ta sanya hanu ta share haɗe da miƙewa zaune, babu amfanin ɓata hawayenta wajen fiddasu, yanzu lokaci yayi da shine yakamata yayi kuka ba ita ba. Kayan jikinta tashiga cirewa, haɗe da ɗaura zani akan ƙirjinta kana ta sanya lufaya.... Tana fitowa daga cikin ɗakin nata, Inna ta kalleta haɗe da cewa. "Yauwa Zahrah kintashi ko? ya ƙarfin jikin naki de?" alokaci ɗaya Inna tajero mata duka waƴan nan tambayoyin.. "Eh Inna na tashi, ko zan samu ruwan zafi inaso nayi wanka ne, gaba ɗaya banajin daɗin jikina, gashi ina so naje gidan su Husnah" tafaɗi maganar tana me ɗan rumtse idanun ta, saboda wani juwa da taji yana ƙoƙarin ɗibanta.. "Kinkuwa ci sa'a yanzu na ɗaura ruwan abincin rana, gashi can inaga yama tafasa saiki ɗiba, amma idan kin ɗiba ki ƙaramin ruwa acikin tukunyar" Inna tafaɗi haka tana meyi mata nuni da tukunyar abincin dake ɗaure kan murhu... Sosai taji daɗin jikinta sakamakon wanka da ruwan zafi da tayi, bayan ta idar da Sallan Azahar ne, tayi mawa kanta mazauni akan katifarta haɗe da ɗaukan jakar kayan kwalliyanta, mai kawai tashafa sai kwalli da ta zizara a cikin idanunta, ko powder bata shafa ba... Doguwar rigar atamfa irin me sauƙin kuɗin nan tasanya ajikinta, haɗih da ɗaura hijab akan kayan nata mai kalar blue, yakumayi shige da atamfarta saboda shima atamfar kalan blue ne dashi (shuɗi). Me kyau de me kyaune ko a yaya kuwa, duk da batayi kwalliya ba kuma fuskarta a kumbure take saboda kuka, amma hakan bai hana kyawun fuskarta bayyana ba.... Kallon Inna dake ƙoƙarin sauƙe tukunyar abinci Zahrah tayi, tana me gyara zaman lufayar jikinta tace. "Inna ni zan je gidansu Husnah, zuwa yamma zandawo insha Allah" "Wani irin maganar zuwa gidansu Husnah kuma Zahrah? inace ɗazu ɗazun nan muka dawo dake daga asibiti, har kin yi sauƙin da zaki soma fita yawo?" (Su Inna anfara soyayya da Zahrah fans, lol) "Kada ki damu Inna yazama dole ne naje, amma bazan jima ba zandawo, dan Allah kada ki hanani zuwa Inna!" Zahrah ta faɗi haka cikin yanayi na nuna zaƙuwa. "Shikenan tunda kin matsa, ai de kya tsaya kici abinci, idan yaso saiki tafi" "A'a Inna banajin yunwa yanzu, idan nadawo zanci" takai ƙarshen zancen nata tana me nufar hanyar fita daga cikin gidan. Da kallo kawai Inna tabita harta fice daga gidan... Tsayawa tayi tana kallonsa cike da mamaki, yayinda shima kallon nata yake cikin yanayi na mamaki... Giransa ɗaya ya ɗage haɗe dayin murmushi.... "Ashe ma kinyi sauƙi, dana sani da ban bar aikin da nakeyi nazo duba kiba ae" Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me takowa zuwa wajen da take tsaye. Kunyarsa ne taji yakamata, sakamakon abun da yafaru ɗazu a tsakaninsu, wato rungumarsa da tayi, wanda tasan hakan ba abu bane me kyau haramunne, mace ko namiji su taɓa mutumin da ba muharrami'n su ba, duk da cewa ba'acikin hayyacin ta ta rungumeshi ba, amma tabbas hakan bai dace ba... "Yade naga kina wani sunkuyar dakai kamar amaryar da aka kaita ɗakin mijinta" Dr.Sadeeq ƴafaɗi haka cike da zolaya. Sai alokacin ta'iya ɗago kanta ta aika masa da hararan wasa,,,,, " Yaushe kazo? kuma me yasa ka tsaya anan baka shiga cikin gida ba?" "Ummm banjima da zuwa ba, dama inaso amin sallama dake ne, kinga bai dace ace koda yaushe ina shiga cikin gidanku kai tsaye ba, amma sai kuma naga kamar keɗin sauri kike zaki unguwa ko?" Yaƙare maganar yana me leƙa fuskarta wanda ta sunkuyar da ita ƙasa. Wasa da yatsun hanunta tashiga yi, haɗe da sanya haƙorinta na sama taɗan datse leɓenta na ƙasa.. "Yajikin naki?" yatambayeta don yaga bata daniyar basa amsan abun da yatambaya. "Dasauƙi, dama ni lafiyata ƙalau" tabasa amsa a ta ƙaice.. "Eh hakane kuma dama kinsan wani lokacin, idan lafiya tayi mawa mutum yawa, takan iya sawa ya kwanta a gadon asibiti" Saurin kallonsa tayi sakamakon jin abun da yace, "Lafiyan?" ta tambaya cike da mamaki. "Eh itafa lafiyan, to baga example akan ki ba" yanayin yanda yayi maganar kaɗai ya'isa ya tabbatar maka cewa zolaya ne kawai ke damunsa.. "Hmm" kawai Zahrah tace haɗi da ɗan satan kallonsa, aikuwa karab suka haɗa idanu, saurin ɗauke nata idon tayi. Hmm yalura sarai kunyarsa takeji, kuma shiɗin ma kusan hakanne, kawai de dauriya dakuma shariya yafita, shiyasa ya share abun, amma shikansa yasan cewa ya aikata ba dai dai ba, saboda da ta rungumesa baikamata ace yabiye mata ba, kamata yayi ace ya ɓanɓareta daga jikinsa, sai de kuma babu yanda ya'iya saboda alokacin tana cikin halin buƙatar taimako, kum san nan shi be rungumeta don yaji daɗi ba. "Inazakije ne haka, da rana tsaka?" yajefo mata tambaya..... "Gidan su Husnah zani" ta basa amsa a taƙaice, saboda ba da kowani lokaci tacika son dogon magana ba... "Shikenan muje saina kaiki, domin kinsan samun abun hawa zaimiki wahala, saboda rana tayi sosai" Kallonsa tayi naɗan sakanni, kafun ta rausayar da kanta gefe cikin yanayi na shagwaɓa tace "Dama kabarni, koda ƙafana ai zan iya zuwa, idan har bansamu abun hawa ba, balle ma nasan zan samu" "Da gaske zaki iya takawa da ƙafa daga nan har gidansu Husnah? to shikenan tunda zaki iya, zaimafi kyau ki taka da ƙafan, saboda kisamu ki ɗan rage wan nan ƙiban dakika haɗa, gaba ɗaya duk yasa kin yi muni, kin zama wata super mama dake" yafaɗi haka yana me ƙare mata kallo. Waro idanu Zahrah tayi haɗi da soma kallon kanta, wai tayi ƙiba, takuma zama super mama. Take idanunta suka yi raurau dasu, yayinda ruwan hawaye ya soma cika cikin su, "ashe da gaske tayi ƙiba bata sani ba? gashi harya fara goranta mata, to me yasa ita bataganin ƙibanta?" tatambayi kanta... Dariya Dr.Sadeeq yasanya domin kuwa yalura tayarda da maganarsa, shikuwa wasa yake mata, bawai dagaske tayi ƙiban bane, gashi har tana ƙoƙarin yin kuka, shikam ya lura gaba ɗaya kuka baya bata wahalar yi, hawayenta a maƙale suke, mintuna kaɗan saikaga sun tsiyayo" "Kintsorata ne dan nace kinyi ƙiba? hmmm nan gaba kaɗan zakiyi bindiga ki fashe saboda tsabar ƙiba" Sake waro manya manyan idanunta tayi zuwa yanzu kam har ƙwallan cikin idanunta sun gangaro akan fuskarta.... "Au kinfiso ki kumbura ki fashe ɗin kenan?" yatambayeta yana me danne dariyar da ta taso masa... Kai ta girgiza masa alaman "A'a" "To kinaso na faɗamiki me zakiyi wanda zaisa bazaki fashe ba?" Dasauri ta ƙaɗa kai alamar tanaso yafaɗa mata... "Yauwa ƴar gari ashe de kema bakyaso ki fashe, to abu ɗaya zakiyi wanda shizai hanaki fashewa, kinga de ni likita ne ko? nakumayi zurfi cikin karatun likitanci, saboda tsabar zurfin da nayi ina karatune ma yasanya nagano cewa idan mutum yacika matsantawa kansa da damuwa da kuma yawan koke koke to yakan iya kumbura kamar de yanda kikayi yanzu, daga nan kuma bayan kamar 1 week shikenan sai dai yayi bindiga yafashe fush, shikenan kuma sai de wani bashi ba, kinaso haka ta faru dake?" yafaɗi haka yana me zura mata manya manyan idanunsa. "A'a" tabashi amsa cikin murya me sanyi, domin kuwa a haƙiƙanin gaskiya ta yarda da kalamansa, ko kaɗan bata gano cewa shiya shirya abunsa ba. take fargaba ya ɗarsu a zuciyarta.... Wata irin dariyane takama Dr.Sadeeq amma kuma ba halin yasaki dariyar tasa, dolensa ya danne ta matuƙar yanaso Zahrah ta gamsu da bayanan sa hundred percent,,, lallai yau yaƙara tabbatarwa kansa cewa Zahrah yarinyace kuma yarinta na damunta, amma inbanda haka ta'ina ta taɓa jin ance mutum ya yayi bindiga yakuma fashe da ransa. Gyara tsayuwarsa yayi haɗe da cewa "To yanzu de zaɓi ya rage gareki Yarinya, ko ki daina kuka ko kuma ki fashe, saboda haka zaki biyoni muje ne ko kuwa a'a nayi tafiyata?" "Zanbika" tafaɗa cikin muryar tsoro saboda gaba ɗaya kalaman likita sun rikitata... Murmushin gefen baki Dr.Sadeeq yayi haɗe da juyawa yanufi wajen motarsa, yana me danne dariyarsa... Zahrah kuwa tamkar wacce ƙwai yafashewa haka ta bi bayansa. Saida suka hau titi kafun yajuyo da kallonsa gareta, gani yayi tayi jigum da'ita, da'alama tunani takeyi.... "Amma nace miki yawan sakai a damuwa shike sa mutum ya fashe ko? hala don ba ɓangaren likitanci kike karanta ba shiyasa bakisan da hakan ba" Kallonsa tayi haɗe da ƙwaɓe fuska, cikin murya me sanyi tace "Ni ae yanzu bawai a damuwa nake ba, kawai de ina kallon hanya ne" .... Kansa ya jinjina haɗe da cewa tayi masa kwatancen gidansu Husnah'n domin shi basani yayi ba.... A dai dai ƙofar gidan su Husnah ya tsaida motar tasa, haɗe da dawo da kallonsa ga Zahrah wacce ke ƙoƙarin buɗe murfin motar tayi ficewarta... "Da yaushe zaki koma gida?" Ɗan jim tayi kana tace "Ko zuwa bayan la'asar ma, irin ƙarfe biyar ɗin nan haka" yanayin yanda taƙai ƙarshen zancen nata tana me juya kyawawan idanunta, shi ya shagaltar dashi har ya tsaida idanunsa akan ta, sosai takeyi masa kyau idan tana juya idanunta, ya kuma lura cewa hakan al'adarta ne, idan hartana magana, to takan juya idanunta masu kyawun gani, musamman idan maganar tazo ƙarshe.. "Ya de?" Zahrah ta tambayeshi sakamakon ganin da tayi yakafeta da idanunsa.. "Babu, kikulamin da kanki kinji, zan zo na ɗaukeki idan 5 ɗin tayi, inafata babu wata matsala?" yatambayeta cike da nuna kulawa. Murmushinta me kyau tayi masa haɗe da cewa "Babu wata matsala" Yana kallonta tabuɗe ƙaramar ƙofar dake jikin gate ɗin gidan su Husnah tashige... Yana tabbatar da shigewarta yayiwa motarsa key haɗe dayin reverse yaɗauki hanyar asibitinsu, saboda dama aiki yabaro yazo gareta, to yazaiyi tunda tazama wani ɓangare na jikinsa... Da matuƙar farinciki Husnah ta rungume Zahrah tana mejin daɗin ziyarar bazata da Zahrah'n takawo mata, saboda bata faɗa mata zata zoba. Bayan Zahrah ta gaisa da Momyn Husnah ne, suka rankaya zuwa ɗakin Husna'n,,, ba ɓata lokaci Husnah ta cikawa Zahrah gabanta da kayan ciye ciye dasu drinks. "Naji daɗin zuwanki sosai ƙawata, kamar kuwa kinsan ina kewarki, jiyafa har mafarkin ki nayi, da safe naƙira wayarki kuma najita switch off, ina fata dai kina lafiya?" Hijabin dake jikinta ta cire haɗe da cewa "Lafiya amma ba sosai ba" Da sauri Husnah ta dawo da kallonta ga Zahrah "Meyafaru dear?" Husnah tatambaya cike da kulawa. Kallon Husnah Zahrah tayi na tsawon minti guda.... "Babuƙatar tuna abun da yafaru Husnah, saboda kinsan inada raunin zuciya, tuna abun zai iya sake jefani cikin wani hali" Damuwane ya bayyana ƙarara akan fuskar Husnah haƙiƙa tamkar ƴar uwa ta jini take kallon Zahrah saboda haka duk wata damuwa ta Zahrah damuwar tace itama. "Zaki iya ɓoyewa kowa damuwarki amma bandani Zahrah, sai de kuma babu amfanin takuraki akan cewa lallai sai kin sanar dani, saboda bansan wani hali zaki samu kanki aciki ba bayan kin faɗamin" Dafa kaɗan Husnah Zahrah tayi haɗi da daure zuciyarta... "Nasake haɗuwa da.... da....wanda ya yimin fya......." kasa ƙarasawa tayi saikawai tafashe da kuka. Ko bata ƙarasaba Husnah tafahimci me Zahrah take nufi. Cike da tashin hankali Husnah tasoma salati... Sake jawo Zahrah jikinta tayi haɗi da rungumeta...."Ki daina kuka, yanzu ba lokacin kuka bane Zahrah, kinmaci abinci kuwa ?" Husnah ta tambayi Zahrah cikin kulawa... "Banajin yunwa Husnah!" Zahrah tafaɗi haka cikin shaƙewar murya, wani yunwa zataji ita da take cikin bala'in sake ganin Zaid... "Kinsan de ba kyau zama da yunwa ko, kinga yau ni namayi abincin dakaina, bana zuba mana muci tare, kuma dan Allah kada kicemin a'a" Babu yanda Zahrah ta'iya dole tabiyewa Husnah taci abinci, gaba ɗaya Husnah se zuba take tamkar kurna, takasa yin shiru koda na minti biyu ne, tayi hakanne kuma saboda ta gusarwa da Zahrah da muwarta, daga ƙarshe de har game, Husnah ta jona musu a tv suka buga, sosai kuma hakan ya ɗebewa Zahrah kewa.... Tare sukayi sallan la'asar daga nan kuma Husnah ta ɗebi Zahrah, suka tafi shoprite, dangin su ice cream da chocolate suka jida, daga nan sukayo gida. Kamar yanda yafaɗa ƙarfe biyar da minti ɗaya dai dai ya ƙaraso ƙofar gidansu Husnah.. Ƙiran Zahrah yayi a waya ya tabbatar mata cewa yana ƙofar gidan su Husnah.... Zahrah na ajiye wayarta Husnah ta kalleta haɗe da kashe mata ido ɗaya. "Ƙawata tazama ƴar soyayya, sosai yanayin soyayyarku da Man ɗin nan yake kasheni, kinfasan gayen naki ya haɗu over, da badan ke bace danayi snatching ɗin sa!" cike da zolaya Husnah ta faɗi maganar... Dariya suka sanya su dukansu, haɗe da rungume juna. Har bakin motar Dr.Sadeeq Husnah ta raka Zahrah, bayan Momyn Husnah ta cikawa Zahrah leda da dangin su turare dakuma kayan shafa hadda kyautar wani haɗaɗɗen leshi, sosai Zahrah tayi godia, hakan kuma yana ɗaya daga cikin abubuwan daya sanya bata son zuwa gidansu Husnah, saboda idan dai tazo tofa sai mahaifiyar Husnah tayi ɗawainiya da'ita wajen bata kyautan kayayyaki masu kyau da tsada... Harsaida Husnah taga tashin motar su Zahrah kafun takoma cikin gida... "Kinsamo abun daɗi shine kokimin tayi ko?" Dr.Sadeeq yafaɗi haka ga Zahrah wacce ta ɗaura ledan sayayyar da sukayi a shoprite ita da Husnah akan cinyarta... "Murmushi me sauti tayi haɗe da cewa "Ba'abun daɗi bane, kayan shafa ne" "Um um ni banyarda ba, kitaimaka kiban ko chocolate ɗaya ne, naci yunwa nakeji, yau duk banci abinci ba" yaƙare maganar yana me shagwaɓe fuska, sai kace wani ƙaramin yaro... Dariya Zahrah tayi haɗe da satar kallonsa "wai ma ya'akayi yasan cewa acikin ledar hanunta akwai chocolate?" ta tambayi kanta. "Kina mamakin ya'akayi nasan cewa a ledarki akwai chocolate ko?, ai ba abun mamaki bane, tunda nasan shiɗin favorite ɗin ki ne" yafaɗi haka cikin yanayin shauƙi, amma still idanunsa naga titi.. Buɗe ledar tayi taciro wani chocolate mai kyau da daɗi kusan yafi kowanne ma daɗi acikin sauran chocolate ɗin da ta saya, ta miƙa masa haɗi da cewa "Ga wan nan amma bazan iya baka kyautarsa duka ba, saboda haka kaci rabi kabarmin rabi" Saurin kallonta yayi fuskar sa ɗauke da murmushi... " Naƙi wayon, idan har kinaso na karɓa saide kibani kyautansa duka" Turo ɗan ƙaramin bakinta tayi gaba, haɗe da noƙe kai alamar hakan bazai yiwuba, kallon bakin nata yayi, harsai da yaji tsikar jikinsa ƴa zuba, hmmm lallai idan ya auri Zahrah, zai tsotse wan nan ɗan ƙaramin bakin nata ne yanda ya kamata🙈... "Kici chocolate ɗinki ke kaɗai nikam na gode" yafaɗi haka a taƙaice domin dama wasa yake mata baci zaiyi ba, shi da yake fama da ciwon ciki idan yaci chocolate kuma yake nan? Lokacin da suka iso gida biyar da rabi har ta gota... kallon Zahrah Dr.Sadeeq yayi haɗe da ɗan nisawa. "Nagama haɗa miki kayan lefe da kuma sauran abun da suka dace, wace rana kikeso a kawo?" Saurin ɗaga idanu tayi ta kallesa jin abun da yace. Idanunsa ɗaya ya kashe mata, wanda yasanya taji gabanta yafaɗi, saboda a wajen mutum ɗaya ta saba ganin irin wan nan kashe idon, kuma shi hakan yazame masa al'adarsa ne, bakowa bane kuma face ZAID. "Zamuyi waya" Zahrah tafaɗi haka don son kawar da tambayar tasa, saboda a yanzu bata da amsar da zata basa.. Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da dafa steering motar da duka hannayensa biyu. "Shikenan idan kin nutsu zan ƙiraki" yafaɗi haka cikin sanyin murya.. Murmushi tayi masa irin me tsayawa a rai ɗin nan, kana tabuɗe murfin motar tayi ficewarta, sai de batare da yasani ba, ta aje masa wan nan chocolate ɗin... Bayan kamar 2 minute da shiganta cikin gida yaja motarsa shima yayi tafiyarsa... *ZAID* Tunda yasha wan nan ƙwayoyin baisan inda kansa yake ba harsai ƙarfe uku na yammaci,, ko da ya buɗe idanunsa ji yayi duniyar na juya masa, amma haka adaddafe ya shiga bathroom yayi wanka haɗe da ɗauro alwala, sai yanzu zaiyi sallan Azahar don tsabar asara, gashi har la'asar ma takawo kai.... Yana idar da sallan azahar ya miƙe daga kan sallaya haɗe da zura slipper ɗinsa yafice daga ɗakin... Kai tsaye masallacin jikin gidansu yanufa don gudanar da sallan la'asar wanda ake ƙira yanzu.. Ko a cikin masallacin mutane sai mamakin ganinsa suke saboda abune mawuyaci ka gansa a masallacin da wan nan time ɗin, yafi yawan zuwa sallan isha ko asuba, amma banda azahar da la'asar saboda a wan nan lokacin ma kwata kwata baya gida, sai de yayi sallah a wani wajen. Baidamu da kallon da mutane suke masa ba, yana idar da sallan sa yatashi yayi shigewarsa cikin gida... Tsab yagama shirya kansa cikin ƙananan kaya, riga da wando na blue jeans wanda suka matuƙar amsar jikinsa. Ba abun da yake sai tashin ƙamshi. Zama yayi abakin gadonsa haɗe da sanya hanunsa duka biyu ya dafe kansa dake yi masa ciwo kaɗan kaɗan,, wani irin sabon al'amari yakeji a cikin zuciyarsa, baisan da wani suna ze ƙira abun ba, amma tabbas jiyake zuciyarsa na azalzalarsa akan Zahrah, san nan yanajin cewa itace muradinsa, saurin buɗe idanunsa da ke lumshe yayi sakamakon hasko masa marukan da Zahrah ta sharara masa akan fuskarsa da sukayi, hanunsa yakai kan ƙuncinsa ya shafa haɗe da sakin murmushi, tunda yake a a rayuwarsa wata mace banda mahaifiyarsa bata taɓa kai hanunta jikinsa da sunan duka ba ballan tana har akai ga mari, sai gashi yau, Zahrah ta shararamasa lafiyayyun maruka harguda biyu akan fuskarsa, takuma haɗa masa hadda duka, amma ko kaɗan baiji zafin abun ba, anya kuwa shine? kodai an musanyashine bai sani ba? meke damun

Chapter 23 of 47