Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
so na tambaye ka tun kwanan baya da dad'ewa lokacin danai kiranka wata budurwa ta d'aga baka nan tace min baka nan amma ita 'kanwarka ce dan Allah wacece ita ya sunanta"? Ahmad baiyi niyyar d'agowa ba saida yaji abinda yace ji yayi ransa ya sake 6aci fiye da d'azu da prince Hamid ya masa magana akansu Babyn tunda yaji yace 'kanwarsa yasan baby ce lokacin data d'aga harya fito ya sameta ya daketa da belt yanzu kuma shi Samir tambayar da yake a kanta me zaiyi mata............... "Ahmad baka fad'a min ba 'kanwarka ce"? A takaice yace masa "eh" cigaba Samir yai da cewa "wow masha Allah fad'uwa tazo daidai da zama mene sunanta sannan zan iya ganin photonta"? Wani kallon 'kasan ido Ahmad yayi masa ji yake kamar ya rufeshi da duka akan tambayar da yake masa amma saboda baya so ya fahimci wani abu sai kawai ya danne yace. "Sunanta Zuhra". "Wai Zuhra nice name daga ji kyakkyawa ce sosai zan iya ganin photonta"? Kai Ahmad ya girgiza da sauri ma kuwa yana cewa "a'a" da mamaki Samir yace "meyasa bakaza nuna min ba"?. "Saboda wani dalili". "Kai dan Allah Ahmad ka nuna min wallahi ina jin muryarta naji na kamu da sonta dama a 'kagare nake ka dawo na tambaye ka idan har zan samu ka shige min gaba na aureta wallahi da gaske nake maka Ahmad ina son 'kanwar nan taka fatan zaka bani ita................ Kusan numfashin Ahmad ne yaso ficewa yabar jikinsa tsabar yadda kalmar ina sonta da Samir ya fad'a ta daki zuciyarsa har saida ya runtse ido saboda jin wani abu kamar mashi ya soki zuciyarsa da sauri ya dafe 'kirji bai iya d'agowa ba duk da kiran sunansa da Samir yake saida aka dad'e kafin da'kyar cikin son danne 6acin ransa ya d'ago idonsa daya sauya kala muryarsa ma a sauye ba kamar yadda Samir ya sanshi ba yace. "Tana da miji". Zaro ido Samir yai yana cewa "dan Allah tana da miji Ahmad is this some kind of joke dan kaga yadda zanyi ne ka zolaye ni right"? Kai Ahmad ya girgiza yana cewa "Samir idan da zanyi maka wasa tun farko dana ja maka rai daka tambaye ni sunanta ina fad'a maka gaskiyar abinda baka sani bane a kanta domin anyi mata miji tana da wanda zata aura tunda dad'ewa lokaci ne bai karaso ba" Ahmad yai maganar da serious face musamman da yaga Samir d'in yana kokarin mayar da abinda ya fad'a masa wasa zazzafan huci Samir ya fitar yana kad'a kai yace. "Ok shikenan na fahimta amma banso wani yai min shigar sauri ba to amma Ahmad bayan ita baka da wata sister dan Allah nidai ina son nai aure a cikin 'kannanka muryar wannan ladyn taja hankalina sosai na shiga halin kamuwa da 'kaunarta please idan kana da wata 'kanwar bayan ita ina so dan Allah" a takaice Ahmad yace "Ina da ita amma itama tana da wanda zata aura". "Haba Ahmad bama haka dakai duk ta inda na 6allo saika zille ka sanni kasan halina sannan idan yaudara ce kasan bazan yaudari 'kanwarka ba dan Allah Ahmad ka taimaka idan kana da 'kanwa ka wacce take free ko Kuma wasa kake min please na had'aka da girman Allah ka fad'a min"? Ya fad'a harda had'e hannu ran Ahmad a dagule yace. "Bayan ita ba wata". Kai Samir ya girgiza yana shirin sake magana ganin bazai ha'kura ba yasa Ahmad yace "Samir kai aboki nane na ha'ki'ka kasan bana 6oye maka wani abu daya danganci sirri na amma nayi mamaki dana fad'a maka gaskiya ta yau ka kasa fahimta ta why"? Ganin da Samir yayi ran Ahmad ya 6aci sosai sannan yasan abinda ya fad'a masa gaskiya ne da ace 'kanwar tasa bata da miji bazai 6oye masa ba saboda akwai sha'kuwa da yarda mai 'karfi a tsakanin su tuna hakan yasa Samir yayi murmushi yana kallon Ahmad wanda ya gama cika yace. "Ok Ahmad kayi ha'kuri na 6ata maka rai ba a son raina bane nayi hakan ne saboda na nemawa kaina mafita". Kai Ahmad ya girgiza yana cewa "karka damu Samir baka 6ata min rai ba kafin 'karfin komai a guri na da ace ina da 'kanwa zan baka ita kaika san da haka". "Haka ne Ahmad ka fad'i gaskiya nagane ba damuwa Allah yasa gidajen zamansu ne". "Amin kawai shine abinda Ahmad yace daidai an kira wayar Samir ya mi'ke yana cewa "ok bari nazo Mum tana kirana". "Ok". Samir na barin gurin Ahmad ya d'aga waya ransa a 6ace ya kira numbern Khairat dan yasan idan ya kira Momy maybe basa kusa da ita Khairat suna zaune a bedroom jin wayarta na ringtone yasa da sauri ta d'aukota ganin wanda yake kira yasa ta tsaya cak tare da kallon Baby tana cewa "na shiga uku Baby shikenan na kad'e yau" da alamar tambaya Baby tace "meya faru waye ya kiraki" daidai kiran ya katse wani ya shigo a susuce Khairat tace. "Wallahi ya Ahmad ne yake kiran na" zaro ido Baby tai har ruwan data d'auka tasha ya 'kwareta ta kama tari da'kyar tace "ya Ahmad dai"? Kai Khairat ta d'aga tana cewa "ni yanzu bansan yadda zanyi ba kuma kar na'ki d'agawa na sake jawa kaina wani sabon laifin akan na d'azu". "To ki d'aga man tunda ba'a gida yake ba da sau'ki kome zaice tsakanin mu dashi da nisa bazai dake muba saidai fad'a da baki kawai" jin abinda Baby tace yasa Khairat ta jinjina kai a karo na uku da kiran ya shigo cikin azama ta d'aga tun kafin tai magana muryar Ahmad cikin tsawa yace. "Ummul-khairi uban me kikeyi baki daga min kira ba bayan kina gun raini ko"? Kamar yana ganinta da sauri ta girgiza kai tana cewa "dan Allah yaya kayi hakuri wayar tana bedroom tana caji ne mu kuma muna parlor saida muka shigo naga kana kirana kayi hakuri dan Allah" ta fad'a cikin son kare laifinta jin abinda da Khairat d'in tace yasa Ahmad sassauta murya yana cewa. "Okay ina Babyn take"?. Zaro ido baby tai tana rufe baki tare da yarfa hannu tana gwadawa Khairat tace bata gurin ita kuma bata fahimta ba saboda tsoron kar ta sake 'kular dashi tace "gata nan a kusa dani". "Bata wayar". Mi'ka mata Khairat tai da'kyar Baby ta kar'ba tsabar rawa da hannunta ya d'auka tana karawa a kunne tsawar da Ahmad ya daka yasa tai wulli ta wayar tana 'kan'kame jikinta kamar shine a gurin ganin da Khairat tai kiran bai katse ba yasa taje ta dau'ki wayar tana sake mi'ko mata a hankali saboda kar yaji cikin rad'a Khairat tace. "Baby kiyi magana kema kisan 'karyar da zaki masa ki fita kamar yadda nima nayi" Kai Baby ta girgiza zatai magana Ahmad yace "Khairat kina jina"? Da sauri Khairat tace "eh Yaya ina jinka". "Oh kina jina kuma dan ubanki nace ki baiwa Baby wayar kikai banza saboda kinsan bana ne ko"?. "Kayi hakuri Yaya gata nan kar'bi baby" ta fad'a tana mi'ka mata kar'ba Baby tai da yake hand free ne tana jinsa sosai yace. "Baby" Muryarta na rawa tace "na'am" jin ta amsa a fusace Ahmad yace "Baby! Baby!! Babby!!! na rantse da Allah duk ranar dana sake aje phone d'ina kika d'auka har kika sake yin magana da wani ban saka kiba saina 6allaki yau kin 6ata min rai sau biyu kenan ke kad'ai ki jira dawowa ta saikin shiga uku a hannuna had'uwar mu bazai miki kyau ba" yana fad'in haka yaja dogon tsuka yana kashe wayar d'ora hannu Baby tai akai tana kallon Khairat tace "na shiga uku Aunty Khairat me nayiwa ya Ahmad kuma ya taso da zancen tun d'aukar wayarsa da nai lokacin da abokinsa ya kira". Zama Khairat tai a bakin gado tana girgiza kai tace "to banace ba tunda kinga ya koma maybe abokin nasa ne daya kira kika d'aga yayi masa maganar ki kinsan dole ne zai tambayeshi wacece ta d'auka masa waya ko 'kanwarsa ce tunda yasan baida mata" jin abinda Khairat ta fad'a yasa Baby dafe kai tana cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah gani gareka kaine gatana ka fidda ni daga wannan damuwa data tunkaro ni". "Insha Allahu zai manta kafin ya dawo kar kisa abun a ranki harya dameki nasan yanzu ransa a mugun 'bace yake dan haka zuwa nan da kwana biyu zan kira miki shi ki bashi ha'kuri sannan ya huce" numfashi Baby ta sauke jiki a sanyaye tace "shikenan zan gwada Allah yasa ya kar'bi ban ha'kurin nawa". "Zai kar'ba kawai yanzu abinda zaki ki dage da addu'a kafin nan da kwana biyun wannan shine mafita" kai Baby ta d'aga tana cewa "bari na fara tun daga yanzu duk da ba'a makara wajen yin abinda ya dace bari nayo alwala" ta fad'a tana wucewa bathroom yayin da tabar Khairat itama tayi shiru ta shiga duniyar tunani............ ✍️MRS ÄL'ÄMËËÑ ÄHMÄD ÇË🌹. TYPING 📲Mon mar17/25 09:45PM YUSRAH 🤞 MUSA 🤞 ABUBAKAR 👑 ROYALTY 👑 💫A*W*A💫 Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta haka taken mu yake tafiyar mu babu rago babu maci amana tsantsan gaskiya muke nunawa. _________________ __________________________ ___________________________________ ALLAH THE MOST HIGH DOESN'T SLEEP ALLAH THE MOST HIGH IS PURE HE ACCEPT ONLY WHAT IS PURE. Ubangiji ka sanya mana tsarkakar zuciya ya Allah kaine mai badawa ubangiji muna ro'konka lafiya a jinmu da ganinmu Allah ka bamu lafiya a duniyar mu da lahirar mu ubangiji ka kyautata makwancin mahaifan mu Amin. YÜSRÄH MÜSÄ ÄBÜBÄKÄR Wrïtër 1~ yarima Abdul-maleek 2~ Rayuwa biyu 3~ Safreeyyah 4~ D'an millionaire 5~ Dama kece 6~ Husnah ko Badiyat 7~ Minah-Umer 8~ Tajuddeen Aryam 9~ Me kamar sarki 10~ Minister Ashraf 11~ Yarima Aryan And now 12~ 👑Royalty👑 Later insha Allah👇 13~ 💘Zuciyar Aliyu ce💘 Yana nan tafe insha Allahu dana gama royalty zan fara shi akan #300 shima babu tsada sai dad'i. Littafai na basu da tsada sai dad'i da ilmantarwa da tunatarwa da kuma koyon darasi da hali masu kyau da d'abi'u na gari sannan ina saida su akan qaramin fara shi saboda masoya na duk mai bu'kata should DM me kayi min magana ta WhatsApp number na. +234 816 098 3083 Chat with me. Farashin book d'ina 01_Me kamar sarki #300 02_Safreeyyah #400 03~Minister Ashraf #300 Free kuma kyauta ne ga mai bu'kata shima should DM me. 01-Yarima abdul-maleek free book 02- D'an millionaire free book 03- Husnah ko Badiyat free book 04- Rayuwa biyu free book. 7~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Abidinah. @YUSRAHMS CE Page 13 & 14 Tunda Aiman ya tafi da Ayrah gidansu koda wasa bata sake le'ka su Hajiya Khubura ba tana gurin mahaifiyar Aiman tare da 'kannan sa har tayi 'kiba sakamakon d'an hutun data samu dama rashin kwanciyar hankali ne ya hanata sakuni duk kwanakin datai bata gidan Daddy bai ta'ba sani ba tsabar bata gabansa bai damu da ita ba har saida Hajiya Khubura ta gaji da aikin dasu Abidah suke yi saboda rashin Ayran ta samu Daddy ta fad'a masa 'karya da gaskiya sannan tace Aiman ya mayar da ita gidansu yace anan Daddyn bazai iya ri'keta ba bai damu da damuwarta ba kamar ba shine ya haifeta ba jin wannan maganar tai bala'in 6ata ran Daddy a take ya d'aga waya ya kira Aiman cewa yazo yana nemansa humm Hajiya Khubura abinda take so kenan dama ta samu Daddy ya kirashi tayi amfani da wannan damar tasa Daddy yasa Aiman ya dawo da Ayrah gidan ko yana so ko baya so, suna zaune a parlon Daddy ya shigo da sallama yana samun guri ya zauna cikin ladabi ya gaisa Daddy amsa masa yai yana kallonsa murya a nutse yace. "Aiman meyasa ka d'auke Ayrah daga gidan nan ka mayar da ita gidanku batare daka fad'a min ba"? Jin tambayar dayai masa yasa Aiman d'agowa ya kalli Hajiya Khubura wacce ta sakar masa murmushin mugunta tana jinjina kai alamar yasan aikinta ne kafin tai masa magana da ido tana kallon Daddy wanda shi kuma Aiman d'in yake kallo tace. "Ai dama na fad'a maka Alhaji bazai iya baka amsa ba saboda bashi da wata hujja haka kawai ya d'auke yarinyar yabar gidan da ita bayan baka gagara ri'ke iyalinka ba meka rageta dashi harda zaiyi abu batare da ya mayar dakai uba yayi shawara dakai ba" har lokacin idon Daddy yana kan Aiman yace "dashi nake magana kiyi shiru ke kam ina zuwa kanki" ta'be baki Hajiya Khubura tai tana juyar dakai gefe a ranta tace "ku gama ka dawo kaina d'in kome zakai wallahi sai yarinyar nan ta dawo gidan nan zan nuna maka kayi tsararo baka kaiba dani kake zancen ko Zainab bata isa ja dani ba balle wani banza kai data haifa". "Aiman". "Na'am Daddy". "Nace meyasa ka d'auke Ayrah daga gidan nan tsawon lokaci ban sani ba kuma kai baka sameni ka fad'a min ba" idon Aiman na kallon carpet yace "kayi hakuri Daddy nayi hakan ne bisa dole ba'a son raina bane saboda.......... Katse masa magana Hajiya Khubura tai da cewa "bada son ranka bane to waye ya saka ka dole ko Zainab d'in ce tace kazo ka d'auke ta"? D'agowa Aiman yai ya mata wani irin kallo batare daya bata amsa ba yaci gaba "Daddy maganar gaskiya Ayrah bata sakewa a gidan nan rayuwa take kamar tana gidan yari alhali ita da gidan mahaifinta bata da damar data isa zama koda na minti biyar ne a parlor kullum tana zaune guri d'aya daga bedroom sai bedroom sannan Hajiya tana gani 'ya'yanta Abidah da Nadiya suke dukanta su zageta su sakata wanki da wanke toilet gugar kayansu abincin su komai itace take musu sannan abun ba'kin cikin itace zatai komai ta kawo musu amma lomar abinci d'aya bazasu bari tayi ba a gidan nan saidai idan nine na shigo Mata dashi wannan dalilin yasa na d'auketa ta koma can suna zaune tare da Fati da Ashfat lafiya kalau kuma ta sake dasu sosai taji dad'in haka shiyasa nace bazata sake zaman cikin gidan nan ba saidai tazo musu da yawo shima idan kana nan" yana rufe baki Hajiya Khubura tace. "Karya kake munafiki wallahi Alhaji 'karya ya zauna ya shirya maka nice ina sane su Nadiya suke sakata wahala bayan su suke komai a gidan nan aiki kamar zai kashe su amma saboda baka tsoron Allah harda wani itace take mana komai tabd'ijan lallai ma yaron nan ba'a haifi abokin 'karya ka ba". "Ai dama ba dake nake magana ba da mahaifi na nake idan ke kin 'karya tani shi zai gaskata ni". "Shima bazai gaskata kan ba saboda babu gaskiya a cikin abinda ka fad'a sannan dole Ayrah ta dawo gidan ubanta harda wani ba dani kake magana ba da mahaifinka kake dad'in abun ma neman suna kake saidai kace ba dani kake magana ba da mahaifin wata ne ka gani domin a iya sani na 'ya d'aya ya haifa indai ba kalan dangi da son a sani ba ka daina kiransa da mahaifinka ka ri'ka cewa Yaya mahaifinka wannan shine "Bazance yayan mahaifin nawa ba Kinga Hajiya babu ruwanki anan zancen mune tsakani na dashi karki sake saka mana baki Ayrah kuma tunda ba kece kika haife taba dole ki d'auke idonki daga kanta idan kin 'ki akwai ranar nadama tana nan zuwa Ta'be baki Hajiya Khubura tai tana cewa "babu ranar da zata fito wacce a cikinta zanji nadama ta kamani rayuwa kuma yanzu na fara duniya yanzu nake jujjuya ta domin banyi komai ba ka zuba ido ka gani yanzu na fara tara tsinken dazan tsikari duniyar saina baka mamaki zaka yabawa aya za'kinta" Aiman zaiyi magana Daddy da abun ya ishe shi ya d'aga hannu yana cewa. "Ya isa haka ba hayaniya nake nema ba na tambayi Aiman ne inda Ayrah take kuma ya fad'a an wuce gurin tunda ka za'bi ta zauna a gidan ku shikenan hakan yayi zaka iya tafiya" a zabure Hajiya Khubura tace "zai iya tafiya zuwa ina? Gaskiya Alhaji bazata yuwu ba wai so kake a zageka a gari nima a zageni ace 'yarka d'aya ka kasa ri'kewa amma gashi ka ri'ke 'ya'yan ri'ko har mutum biyu". "Duk Wanda bai fasa cewa na kasa ri'ke 'yata na ri'ke d'an aro ba Allah ya tsine masa" Daddy ya fad'a a fusace. Ganin ransa ya 6aci yasa Hajiya Khubura take "A'a nidai Alhaji gaskiya kace ya dawo da ita gidansu ina tuna maka ne meka rasa me babu gidanka daci da sha bai kamata ace 'yarka ta tafi wani gidan can gayyar tsiya a karasa goyata ba dacan lokacin da mahaifiyarta ta rasu basu nuna zasu d'auketa ba sai yanzu data d'ago ta mallaki hankalinta sannan tsabar munafirci da yawan gulmar son a sani zasu wani ce zasu rike ta kace baka so ya dawo maka da ita yanzun nan ka tashi kaje ka dawo da ita". "Ai ba kece kika haife taba saiki bari wanda ya isa da ita yayi magana kuma indai umarnin kine bazan cika ba kin gane"? Kukan 'karya Hajiya Khubura ta saki tana cewa "yanzu tsakani da Allah Alhaji a gabanka yake cimin mutunci yana nuna ni uwar banza ce sai zagina yake yana mayar min da magana kana jinsa yana fad'a min abinda yaga dama? Wayyo Allah na ni Khubura shikenan yau na gamu da gamona" kai Aiman ya jinjina yana shirin magana Daddy yace "Aiman gobe idan Allah ya tashe mu cikin basu rai ina so ka dawo da Ayrah kamar yadda ka d'auketa" takaici ne ya kama Aiman musamman ganin irin kallon da Hajiya Khuburan take masa lokacin da Daddy yace haka kamar bazai tanka ba sai kuma yace. "Daddy ka bar Ayrah ta zauna acan bata jin dad'in nan gidan ko kad'an". "Haka tace maka bata jin dad'in zaman gidan nan ko kaine ka fad'a"?. "Bani na fad'a Daddy idona ne suka gane min". "A'a Aiman ka dawo da ita gobe da safe na gama magana tashi kaje" jin abinda Daddy yace yasa Aiman ya mi'ke ransa a 6ace ya fice daga parlon kamar jira Hajiya Khubura take yana fita ta sake matsawa kusa da Daddy tana kashe murya tace "nikam Alhaji ya maganar tafiyar Aiman makaranta ko ka fasa ne naji kayi shiru da zancen"? Kai Daddy ya girgiza yana cewa " a'a ba mantawa nai ba kuma ba fasawa nayi ba na gama komai lokacin tafiyar tasa ne baiyi ba saboda akwai wani mutum abokina ne da mukai magana tare dashi zasu tafi shi akwai abinda xanyi acan daya gama zai dawo Aiman kuma sai nan da shekara biyu idan ya kammala sannan zai dawo gida insha Allahu" Daddy na rufe baki Hajiya Khubura ta sauke wani daddad'an sansanyan numfashi tana sakin murmushin tsantsan farin ciki tare da jinjina a fili kuma sai tace. "To ikon Allah, Allah yasa ayi mai amfani nima dai Khaleel ya kirani a waya yau kusan kwana biyar yana fad'a min ya kusa dawowa gida kwanan nan" "kai Daddy ya d'aga yana cewa "ok Allah ya dawo dashi lafiya". "Amin Alhaji bari na duba su Abidah ko sun bar parlon nasan yanzu haka suna nan suna kallo ba hankali ne dasu ba idan na barsu zasu iya kaiwa asuba gara naje na korasu Ina dawowa" ta fad'a tana mi'kewa ta fita dama already tasan basa parlon kawai gulma ce take ciciyarta so take ta fad'a musu cewa Aiman zai bar gari ta huta dan bazata iya barci ba yau indai bata fad'a musu ba bedroom d'insu ta shiga suna zaune kowa da waya a hannunta tana chat tsaye Hajiya Khubura tai daga bakin kofar shiga bedroom d'in tana kallon su tace. "Albishirin ku kuce min goro" duk aje waya sukai suna kallonta tace "kuce goro idan ba haka ba bazan fad'a ba" d'an ta'be baki Nadiya tai tana mayar da hankalinta kan wayarta tace "dama dai Umma baki niyyar fad'a ba indai sai munce miki goro ne" ta fad'a tana sake gyara kwanciyarta Abidah ce kad'ai tace "albishirin mu goro manya farare tas 'kwalla 'kwalla masu girma fad'a mana meya faru na ganki cikin farin ciki haka Umma"? Murmushi Hajiya Khubura tai tana cewa. "Humm ba dole nayi farin ciki ba idan ta kama harda rawa zanyi yanzun nan nake magana da Alhaji sai na tambaye shi ya maganar tafiyar Aiman makaranta koya fasa yace a'a ya gama komai wai abokinsa yake jira su tafi tare fad'in haka shine ya saka ni murna annoba zai tafi ya barmu musha iska muyi abinda ranmu yake so batare da fargaba ba shiyasa daya d'auke Ayrah nasan yadda zanyi na zuga Alhaji yanxu yace lallai yana so gobe da safe ya dawo masa da ita" jin abinda ta fad'a yasa ba iya Abidah ba harda Nadiya wani tsalle sukai suna cewa "da gaske Umma"?. "Da gaske man saiku sake shiri kafin tsinanniyar ta dawo ni na koma kar Alhaji yaga na dad'e" tana fad'in haka ta fita kai Nadiya ta jinjina tana cewa "humm idan muka samu wannan takurar yabar gidan shikenan komai zai dawo mana sabo zamuyi abinda ranmu yake so babu fargabar komai tunda shima Daddyn ba zaman gida yake ba". "Uhm nikam bazan ce komai ba saita dawo bautar da zatai min bazai fad'u ba azaba zata sha iri iri wacce ta sani da wacce bata sani ba" Abidah ta fad'a tana d'aukar tata wayar itama taci gaba da chatting d'inta.......... Fitar Aiman gidansu ya nufa ransa a 6ace da yake ba sosai dare yayi ba yana shiga ganin babu kowa a parlor ya wuce part d'in mahaifinsa yana zaune ya shiga ganin yadda fuskarsa take yasa yace "Aiman lafiyarka kalau meya faru"? Zama zuciyarsa na 'kuna yace "Abba daga gurin Daddy nake yanzu akan na taho da Ayrah ran nan shine matarsa ta zugashi wai saita koma idan bahaka ba mutane zasu ri'ka masa kallon wanda ya kasa ri'ke 'yarsa ya ri'ke 'ya'yan ri'ko shine yace min dole saina mayar da ita gobe dan Allah Abba da safe kaje kace masa basai ta koma ba kaga ni 'kasar zan bari ga shegun yaranta bansan wanne hali zata tsinci kanta ba a gidan nan a haka ma suna ganin wulgina basu daina azabtar da ita ba balle akace sun tabbata bana gari abinda zasuyi mata bazai kyau banaso wani abu ya samu yarinyar nan" duk abinda Aiman ke mata Abba yana sauraron sa har yakai karshe kaiya jinjina yana cewa. "Shi Yayan ne yace ka mayar da ita gidansa daga nan kar ace ya kasa ri'keta? Kenan mu kasa ri'keka mukai shiyasa muka bar masa kai tun bakasan waye kaina harka taso har zuwa yau mun ta'ba cewa wani abu kodan ba laifin sabane mace ya aura gur6atacciya saidai muyi hakuri da komai amma ina mamakin yadda gabadaya ya canza rayuwarsa kamar wanda aka asirce? Allah ya rufa asiri karka damu Aiman zanje nayi magana dashi tashi kaje duk yadda za'ai Ayrah bazata koma can ba amma idan naga ya matsa lamba sosai zata koma tunda har ya nuna 'yarsa ce babu kara shikenan jeka" mi'kewa Aiman yai yana fita amma yasa a ransa Ayrah bazata koma gidan nan ba kome Daddy zaiyi tunda ba ra'ayin kansa bane sawar Hajiya Khubura ce zai nuna mata tayi kad'an. 👑 Palace 👑 Yau su Khairat basu wuni a sashin Momy ko Mami ba tun safe suka shiga fada gurin mai martaba Sultan Sharfaddeen tun safe har la'asar suna can sun saka su a gaba sai tsokana suke wannan yace wannan wancan yace wannan har saida mai martaba Sultan ya gaji ya kallesu yana cewa "kunga idan baku daina sakani magana haka ba zan kira muku Ahmad a waya na fad'a masa nace tunda ya tafi kullum sai kunzo kun dame ni" kallon juna sukai suna murmushi Baby data dau'ki wayarsa dake aje a kusa dashi tace "wow ya Ahmad zaka kira mana nikam waye ma Ahmad ne Aunty Khairat"? D'aga kai sama Khairat tai kamar gaske tace "bari na tuna nimafa ga dukkan alamu na manta shi kamar Ahmad sunan anguwa ko Sultan"? Ta fad'a tana kallon mai martaba Sultan tare da rufe baki ta soma dariya kai Sultan Sharfaddeen ya d'aga yana cewa "eh sunan anguwa ne anan tunda kun manta Ahmad amma baku manta Shadad ba ko shima bakusan shiba". "Eh to nidai kamar na san Shadad sunan wani lemo ne nima na ta'ba sha" Baby ta fad'a tana dariya "au da gaske sunan

Chapter 8 of 22