Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuma shi d'in yana da budurwa ne dama bamu ta'ba sani ba"?. "Eh yana da ita man baki sani ba"? Kaita d'aga tana cewa "nikam ban sani ba saifa yau taya zan sani bayan ko fuskar gaida dashi bama samu sosai fad'an sa yafi shirunsa yawa amma koba komai nasan yanzu zamu huta da yayi aure shikenan zai d'auke hankalinsa a kanmu ya mayar kan matarsa" kai prince Hamid ya jinjina a ransa yana hasko daya za'ai ta sani zaman me ake dahar yanzu ba'a fad'a mata ba to sai yaushe ya kamata ace lokaci yayi da zata sani shi kansa Ahmad daya fahimci tasan cewa shi yake sonta zai aureta maybe daga ranar zai daina mata abubuwan da yake mata..................... "Yaya Abdul-Hamid yaufa banyi breakfast ba dama nace sai zaka kawoni ka sai mun wani abu" daina tunanin da yake yayi yana kallon ta yace "ok me kike so"?. "Ina son ice cream da chocolate kawai idan na dawo gida naci abinci". "Amma da kin fad'i wani abu me kyau kyace a siya miki kayan sanyi bakya tsoron mura ta kamaki"? Fad'i wani dai amma Banda wannan a marairaice Baby tace "dan Allah Yaya Abdul-Hamid shi nake so please" parking yai yana cewa "ok jirani" ya fad'a yana fita tana zaune ya sayo mata ya dawo suka karasa school d'in ya sau'keta tai masa godiya sosai cikin jin dad'i saidai tayi mamaki da bataga Ayrah ba kardai bata zo ba meyasa yau tayi fashin school kalle kalle ta fara ganin babu alamarta yasa ta karasa shiga cikin class d'in nasu a zaune taga Ayran da book a gabanta tana karatu sauke numfashi tai tana karasawa ta dafata tana cewa "Ayrah Abdul-Kharim yakike kwana biyu"? D'agowa Ayrah tai ganin Baby yasa tai murmushi tana ri'ke hannunta tace "kai oyoyo Zuhra Ashraf Sharfaddeen ai tun d'azu nake jiran zuwanki naga shiru baki zo ba ya akai"? Zama Baby tai tana aje littafan hannunta da ledar da prince Hamid ya sayo mata kayayyi tace "humm kedai bari kawai Ayrah inacan a gida Ina shirgar barci saboda boss baya nan yabar gari". "Kema yayanki yabar gari Ashraf Sharfa kice hutu kike abinki"?. "Uhm nikam hutu nake wallahi ranar daya tafi kamar sallah har party muka had'a nida Aunty Khairat da Sultan" kai Ayrah ta jinjina tana cewa "nikam nawa Yayan daya tafi ranar wuni nayi ina kuka karshe har zazza'bi nayi gashi 'yar wayar da zamu ri'ka magana ma bani da ita". "Ok ayya yayanki Aiman kema ya tafi ne"? Kai Ayrah ta d'aga Baby taci gaba "wacce qasa ya tafi"?. "Beijing" . "Allah ya dawo dashi lafiya". "Amin Zuhra na gode" ta fad'a jiki a sanyaye bud'e ledar shopping d'in da prince Hamid yai mata l kallon Ayrah tai ganin yadda tai shiru kamar tana cikin damuwa tace "Ayrah meya faru naga fuskarki kamar da matsala"? Murmushi Ayrah ta saki wanda iyakacin sa kan le6enta saboda kartasa Babyn a damuwa tace. "Babu komai Zuhra kawai ina tunanin tafiyar ya Aiman ne shiyasa". "Uhmm 'kwarai kekam har jin kewar yayanki kike banda mu mukam farin cikin fecewarsa muke". "Aini dole nayi kewarsa saboda shine komai nawa shine yake kula dani" tashi Baby tai tana cewa "ok ayya Allah sarki Ayrah karki damu insha Allahu zai dawo ai kamar yaune taho muje waje musha wannan dan haka na taho banci komai ba" mi'kewa Ayrah tai suna fita inda suka saba zama anan suka zauna sunaci gaba da hirarsu har lokacin shiga lecture d'insu yayi suka shiga awa uku bayan sun fito Baby taiwa Ayrah sallama driver yazo d'aukarta suka tafi Ayrah itama ta kama hanya da yake kullum a kafa take zuwa ta koma a kafa Hajiya Khubura bata ta'ba bari Daddy ya baiwa Ayrah kud'i wanda zata hau napep koda naira biyar ne bs ada kuma kafin ya sauya driver ya aje mata yake kaita wani lokacin kuma da kansa yake kawota har cikin school lokacin tashi ya baro office d'insa yazo ya d'auketa ya mayar da ita gida tsabar gata baya bari tai tu'ki da kanta amma yanzu ko kallo bata ishe shiba saidai tasan ba laifinsa bane tabbas akwai lauje cikin nad'i shiyasa ta daina damuwa da halin ko in kula d'in da yake nuna mata tasani wata rana sai labari komai zaizo ya wuce kamar ba'ai ba. Baby ta riga Khairat dawowa gida dan ita sai jikin magriba sosai ta dawo direct part d'in Mami ta wuce dan a 6angaren Mamin suke yanzu kafin su koma na Momy tana shiga taga Baby a zaune ita kad'ai a bedroom zama tai cike da gajiya tana cire hijab d'in jikinta ta aje a gefe kafin ta sauke numfashi tana kallon Babyn tace "Baby kinsan wana gani a harabar gida yanzu sun tafi masallaci da yaya Abdul-Hamid kuwa"? Khairat ta fad'a tana zaro ido tare da ri'ke baki" kai Baby ta girgiza tana cewa "a'a waye a wajen dama Yaya Abdul-Hamid d'azu yace min budurwarsa zaije ya d'auko a airport". Gwalo ido waje Khairat tai tana cewa "wacce irin budurwar tasa hum'um to wallahi ya Ahmad ya d'auko ba wata budurwa Yaya Abdul-Hamid d'in ne yake da budurwa boss ne ya dawo"? Zaro ido waje Baby tai itama jin abinda Khairat tace harda zabura tana mi'kewa tsaye tana cewa "Aunty Khairat kikace Ya Ahmad ya dawo kuma dama ba dad'ewa zaiyi ba ko kuwa hukunta ni ya dawo yi"? Ta fad'a tana d'ora hannu aka. "A'a akwai abinda yazo yi inaga karma ki d'orawa kanki wata damuwa ko tsarguwar danke ya dawo ko d'aya ba lallai hakan bane tunda naji Abba suna maganar da Momy dazu bayan tafiyar ki school naji abbanmu yana cewa zai dawo yau akwai abinda zaiyi bazai wuce sati biyu ba zai koma" sauke numfashi Baby tai jin abinda Khairat tace tana cewa "kai Masha Allah har naji dad'i wallahi Allah yasa idan mun had'u karyai min magana akan abinda ya faru". Da sauri Khairat tace "Allah yasa kar yai mana magana dai kin manta Nima harda ni". "Uhmm Aunty Khairat naki me sau'ki ne nifa kinsan abun biyu ya had'e mun yace idan ya dawo saina gane Allah da girma yake nidai na shigesu na da azaba ya Allah ga baiwarka tana cikin matsala ka cireta daga tarkon bawan nan naka" ta fad'a tana bud'e hannu Amin Khairat tace tana dariya ta mi'ke tana shiga toilet zatayo alwala yayin da Baby tai zaman dirshan tana rafka tagumi kafin Khairat d'in ta fito. A ranar basu yarda sunje part d'in Momy ba saboda kowa tsoron had'uwarsa da Ahmad yake musamman Baby a ankare take ta kasa sakewa hatta abinci da Khairat ta fita ta d'ebo musu da'kyar taci baifi spoon biyar ba tasha ruwa kawai ta sakawa kofar bedroom d'insu lock suka kwanta duk da haka saida Khairat ta riga Baby barci saboda yadda ta saka dawowar Ahmad d'in a ranta kasa runtsawa tai data rufe ido take ganinsa saidai ta bud'e da sauri ta kama waige-waige har jikin asuba idonta biyu barci 6arawo shiya d'auke ta batare data sani ba kuma da asuba ta riga Khairat tashi tai sallah bata iya komawa ta kwanta ba taci gaba da zama akan sallaya tana addu'a har Khairat itama ta tashi ta sallar saidai ita tana idarwa ta mi'ke ta koma gado kallonta Baby tai tana cewa "Aunty Khairat kin manta ya Ahmad ya dawo wai barci zaki koma"? D'agowa Khairat tai zatai magana ganin yadda idon Babyn yake yasa tace. "Baby kiga yadda idonki yayi ja baki samu isasshiyan barci bane kome hakan" kai Baby ta jinjina tana cewa "Humm Aunty Khairat kedai bari kawai ban samu na iya barcin ba sai wajen asuba shiyasa kika ganni haka" da mamaki Khairat tace "saboda me"?. "Kin manta ya kashe min warning kuma yace idan ya dawo zamu gauraya tuna hakan yasa na kasa sukuni har karfe uku da rabi bansan sanda barcin ya d'auke ni". Murmushi Khairat tai tana cewa "ai kuma kinsan duk rintsi ya Ahmad bazai shigo mana ba bedroom da dare ba dakamar da safene da yanzu kin ganshi idan yayi niyya Baby ki cire wannan tsoro da damuwar a ranki ki sallama kinsan ya Ahmad idan yai ra'ayin abu sai yayi dan haka ni banga wani abun ki d'aga hankalinki ba tunda kinsan kome zaki idan yaga damar ya hukunta ki zaiyi toni anan banga abinda zaisa ki takurawa kanki ba" sauke numfashi Baby tai tana kallon kofar bedroom d'insu kafin ta d'an girgiza kai tana cewa. "Shikenan Aunty Khairat nagode zanyi kokari naga nayi yadda kikace min da ace abinda kika fad'a min zan iyayi dani kaina na huta amma zan gwada" kallonta Khairat tai tana sakin dariya tace "to indai haka ne tashi muje part d'in Momy nasan yana can ki dake karki nuna wani abu kamar yadda nima zan tsume idan yaga haka ina mai tabbatar miki maybe bazai tada mana wancan zancen had'a partyn da mukai ba. "To Kuma Aunty Khairat kin manta nifa yanzu ba wannan ne a raina ba cewa dayai zan gane ya aje waya na ta'ba masa wannan shine matsala ta". "Ki had'a harda wannan laifin da kikai masa duk ki share muje kawai Khairat ta fad'a tana ri'ke hannunta alamar ta tashi su tafi Baby batako motsa ba sai tambaya data jefo mata "anya kina ganin zan iya kuwa"? Kai Khairat ta d'aga tana cewa "kwarai zaki iya saidai idan bakiga dama ba shimafa mutum ne kamar mu taso kawai kinsan indai Momy ko Yaya Abdul-Hamid wani yana nan bazasu bari ya dakemu ko yasaka mu wani abu me wuya ba" shiru Baby tai kamar zatai kuka tace. "Nidai kawai kije banda ni basai naje ba". "Ban gane basai kinje ba? Please Baby taso muje nayi miki alkawarin koda ace zaiyi tambaya zan bashi amsa kozai dakeni zan shiga cikin zancen ku inyaso ya had'a mu tare yayi mana komai" jin abinda Khairat tace yasa baby d'agowa ta kalleta sosai tana cewa "Aunty Khairat da gaske bazaki barni ni kad'ai ba"?. "Da gaske man Baby taso muje" mi'kewa Baby tai zuciyarta na harbawa tana dar-d'ar suka nufi 6angaren Momy suna shiga kuwa dashi suka fara had'a ido yana zaune kusa Momy suna zance tsaye sukai a kofar shigowa aka rasa wacce zata fara shiga kowa sai raba ido take kamar Ahmad bai gansu ba ya sharesu yaga iya gudun ruwansu aiko kusan awa guda suna tsaye kaiya jinjina a ransa yana fad'in lallai yaran nan basu sanni ba har yanzu amma zanyi maganin ku d'agowa yai yana kallonsu daidai Momy ta mi'ke ta shiga bedroom sakamakon wayarta da aka kira kusan numfashin sune yaso d'aukewa ganin wacce zata taimakesu tasa baki tabar gurin su juya yaci ubansu su karaso nan yaci ubansu ko'ina basha.................. "Kai tsaiwar me kuke anan ku karaso min kafin sakan daya bana son taku duk wacce ta taka zan take ta" tun bai gama magana ba da gudu suka karaso kowa jiki na 6ari musamman Baby da taga ita yafi kallo tasan yau kam Allah ne kad'ai gatanta........... Saukar muryasa sukaji yace "Baby da Khairat wato saboda na tafi shine kuka had'a party ko harda gabatarwa da DJ nagode gani na dawo ba tafiya nayi har abada ba saidai ku sani yau kun shiga uku sai kun sake had'a min valentine day kamar yadda kuka had'a ranar ku tashi ku nemo cake duk inda yake da balloons sannan ku aro mp dakuka aro nima ina so kuyi min a fili In gani" ya fad'a fuskarsa a had'e yana kallonsu babu ko d'igon murmushi da ganin yanayin sa babu sau'ki tsabar yadda suka rud'e babu wacce fuskarta babu hawaye jiki kuma na rawa ganin halin tashin hankalin da suke ciki yace. "Ko ban kai matsayin da zakuyi min ba"? Duk shiru sukai wanda zai girgiza kai ma a cikinsu rasawa akai sai kuka da yazo musu shima kuma an rasa wacce zata fara fito da nata fili ganin sunyi tsit yasa cikin tsawa yace "ko baza kuyi ba yanzun nan jikin ku yai tsami wallahi yau sai naci ubanku" jin abinda yace yasa Baby kukanta ya fito fili dan tasan duk tsiya kome zaiyi musu saiya fara 'kyale Khairat kafin ita.................... "Ke wato harkin samu bakin kuka ko? Yayi kyau ku tashi ku fara kar'bar hukunci zakuga karshen azabata yau ku fara zaga min parlon nan da frog jump" yana rufe baki da sauri suka tashi kowa ta ri'ke kunne suka fara duk girman parlon da yawan kujerun sai sun zagaye su kuma babu hutu yana kallon su da yadda suka gaji amma yai banza dan yasa a ransa daga yau bazasu sake marmarin koda dariya bane idan ya tafi, suma a nasu 6angaren sun d'auka abun nasa da sau'ki amma sai sukaga baida alamar cewa su tsaya gashi Momy kamar bata part d'in har lokacin bata fito ba tsabar wahala kukan ma sun daina idonsu ya bushe. "Ku tsaya". Yana fad'a da sauri kowa ta tsaya a inda take tare dayin zama da6as suna mayar da numfashi tabbas sun sha wahala ko yanzu ya barsu sun azabtu mi'kewa yai batare daya kalli inda suke ba ya nufi hanyar fita yana cewa. "Ku biyo ni". Zaro ido waje sukai musamman Baby da taji cinyarta kamar ba'a jikinta take ba gashi harya fita mi'kewa Khairat tai da'kyar hajijiya na d'ibanta ta kalli Baby tana cewa "Baby taso mu tafi kinsan ya Ahmad yana da sauri maybe yanzu yaje part d'insu fa karmu jawowa kanmu duka bayan wannan azabar" numfashi Baby ta sau'ke hawaye na zubo mata zurr kafin itama ta rarrafa ta dafe kujera tana runtse ido da'kyar ta samu ta mi'ke kowa tana jan'kafa suka fita yadda suke jin ciwon jikinsu babu me iya sauri a cikin su dole sai a hankali suke tafiya har suka shiga part d'in nasa yana zaune sukaje da suka karasa inda yake kowa kasa dur'kusawa tai. "Bazaku iya zama bane? Ya tambaya yana kallon su "ai bakuji komai ba kuma bakuyi nadama ba tunda har zanyi tafiya bayan kunsan waye ni dan rainin hankali har ku zauna kuna d'aura balloons da sayo cake kuyi party saboda mugu yabar gida ko? Yau kuwa zakuga mugu zanyi maganin ku" ya karasa maganar yana mi'kewa yace "ku biyo ni" kallon juna sukai a matukar razane yaufa sukam sun shiga uku ina kuma zai kaisu ina zasu sake binsa......................... Sautin bud'e kofa ne ya dawo dasu hayyacinsu ganin ya bud'e ya fita suma suka bi bayansa garden ya shiga yana tsayawa a gurin fountain bai juyo ya kallesu ba yace "Khairat d'auko min boket guda biyu a bathroom d'ina minti d'aya na baki" jin abinda yace yasa Baby sake susucewa mezai saka su badai d'iban ruwa ba Allah yasa Khairat ta had'u da prince Hamid ya tambaye ta me zatai da boket ko Allah zai taimake su................ Ganin Khairat d'in ta dawo da botikan biyu a hannunta yasa Baby ta fahimci basu had'u dashi ba kawowa tai tun kafin ta ajiye yace "dau'ki d'aya ki baiwa Baby d'aya ku fara d'iban ruwa kuna bin flower's d'in nan kuna zuba musu ruwa yau sai kun wuni kuna watering idan tsautsayi yasa na dawo na tarar bakwa sauri ko kun tsaya hummmmnn" yana fad'in haka ya juya yabar gurin kallon juna sukai Khairat data dafe kanta daya sara tace. "Mun shiga uku mune zamuyi watering din flowers yau innalillahi wa inna ilaihi raji'un wallahi a yanxu ma bakiji yadda nake jin jikina ba balle nazo nayita jidon ruwa ina bin flower d'aya bayan daya ina zubawa"? Numfashi Baby kawai ta sauke tana cewa "dan Allah Aunty Khairat mu fara karya dawo ya tararmu a tsaye kinsan halinsa abinda zaiyi mana bazai kyau ba" ta fad'a tana wucewa tasa boket d'in ta d'iba karasowa Khairat tai itama ta d'iba suka fara bi suna zubawa saboda tsoron kar yana kallon su yasa ko iya tsayawa basayi. Ahmad kam kwata-kwata ma baya part d'in ya koma gurin Momy sunci gaba da maganar da suke kamar baisa su Baby komai ba itama Momyn bata tambaye shi inda suke ba duk zatonta ko lokacin data tashi amsa waya su kuma suka fita batasan suna can sun zama masu bayin fulawa ba ya 6ata lokaci sosai a gurinta kafin ya tashi ya koma part d'insu yana shiga ya bud'e kofar da zata kaishi garden ya fita tsaye yayi yana kallon su yadda duk suka bi suka ji'ke da ruwa Allah sarki bayin Allah babu wacce take iya magana a cikinsu kawai aiki suke cike da tsananin gajiya kaiya jinjina yana karasawa inda suke duk da haka basu lura dashi ba saida sukaji gyaran muryarsa a d'ari kowacce ta zabura suka juyo kallon tsaf ya sake yi musu kafin yace. "Tunda na tafi iya abinda kukai kenan baifi guda d'ari kuka zubawa ruwa ba"? Jin abinda yace yasa kowacce mamaki ya kamata badan kar suyi 'karya ba sai suce duk flowers d'in dake garden d'in nan sun bata ruwa saidai wacce bata fito ba amma yace iya aikin da sukai kenan tunda ya tafi babu wanda tai zaman hutun minti d'aya a cikinsu saboda tsoron karya dawo ya same su................... "Ok babu me iya bani amsa a cikinku saboda kun cika ko? Shikenan Kuci gaba da aikin dama aina fad'a muku yau wuni zakuyi kuna kar'bar punishment har dare ku d'ora inda kuka tsaya domin yanzu karfe d'aya da rabi tai" yana rufe baki Baby ta fashe da kukan tsantsan wuya da gajiya tana dur'kusawa a gabansa tare da had'e hannuwanta tace "dan girman Allah Yaya Ahmad Kayi hakuri ka yafe mana mun aikata kuskure wallahi tallahi bazamu sake ba dan Allah kayi ha'kuri" jin abinda tace maimakon ya kar'bi ban ha'kurin ta saiya sake had'e rai yana kallon Khairat wacce ke tsaye tana mayar da numfashi yace. "Wato ke kinfi karfin ki bada ha'kurin ko? Yau kuwa bazaki bar garden d'in nan ba ke kwana zakiyi kina baiwa 'kananun tsirrai ruwa zakisan dani kike wasan............ Da gudu itama Khairat ta dur'kusa tana cewa "a'a wallahi ba haka bane Yaya Ahmad dan Allah kayi mana afuwa kayi ha'kuri wallahi mun dau'ki alkawari bazamu sake ba daga yau". "Kuma sake man ina daidai daku nine maganin ku a gidan nan ku tashi ku 6ace min da gani" yana rufe baki suka mi'ke a susuce kowa tana neman hanyar gudu kamar zasu tashi sama fiiiiiiii haka suka fita da'kyar suka iya kai kansu part d'in Momy badon tsoron karya biyo bayansu ba dasun tsaya sun yiwa driver magana ya kawosu amma gara koda rarrafe ne suje a hakan da muguwar rawa gara 'kin tashi. A gigice suka shiga suna huci kowacce ta zube akan kujera da mamaki Momy take kallonsu ganin babu me cikakkiyar nutsuwa a cikinsu tace ''ku kuma daga Ina kamar wanda kukai wasan ruwa duk kun ji'ke jikinku gashi kunyi wani iri kamar marasa lafiya daga ina kuke yanzun bayan zan shiga amsa waya na ganku kun shigo"?. Kallon kofar shigowa Khairat tai zatai magana kawai saiga hawayen wahala da'kyar tace "Yaya Ahmad ne ya sakamu watering a garden tun d'azu da muka shigo bayan an kiraki a waya kin shiga part d'inki" da sabon mamaki Momy ta sake kallonsu tana cewa "ya sakaku watering kuma na tsawon wannan lokacin me kukai masa haka bayan shigowar ku part d'in kenan"?. "Momy tsohon zance ne akan partyn da muka had'a na tafiyar dayai ne shine yace gaba ma mu sake yana daidai damu dan baki fito da wuri bane anan parlon ya fara saka mu tsallan kwad'o bayan mun gama ya kaimu garden mukai watering d'in". "To Allah me iko akan haka ya sakaku wannan azabar kalli yadda kuka koma aini ban sani ba da yanzu naje na taho daku kuma Abdul-Hamid ma inaga baya nan shiyasa da ace yana nan bazai bari kuyi watering ba tunda kuba gardener bane gashi ya saka min ku shan wahala musamman ma ke Baby kalli yadda kike rawar d'ari ko magana kin kasa gara Khairat d'inma da d'an sauran 'karfinta ku tashi ku shiga bedroom kowa ta cire kayan kuyi wanka da ruwa me zafi sosai saiku fito ku had'a tea kusha zaku samu d'umin jiki sosai tashi kuje" mi'kewa sukai kowa najan kafa suka shiga part d'insu da'kyar sukai wankan amma a cikinsu babu wacce ta samu damar fitowa tasha tea d'in balle suci abinci duk kwanciya sukai ganin shiru basu fito ba yasa Momy tashi tabi bayansu data bud'e kofar bedroom d'insu ganinsu a kwance yasa batai magana ba ta mayar ta rufe flask ta d'auko ta dawo tana had'a musu ta baiwa kowa sannan ta koma ta sake had'o musu abinci ta kawo tasa su gaba saida sukaci Baby kam tuni zazza'bi ya rufeta sosai Khairat d'in ma jikinta yad'au zafi kamar wuta ganin haka yasa ta d'auko musu magani kowa ta 6alla tasha suka tashi sukai sallah a daddafe domin tafiya ma ko d'an kaciya bazai fad'a musu ba haka suke takawa sunayin sallar kuwa suke sake kwanciya kowa idonta biyu amma bamai magana a cikinsu saidai saukar numfashin juna kad'ai suke ji a haka har akai la'asar da magriba da isha duk saidai su tashi suyi sallah kawai su koma kwanciya babu wacce zata moru a cikin su dai a wannan ranar. Ahmad kam bai sake shigowa part d'in Momy ba sai wajen qarfe tara da rabi yana zuwa kuwa ta balbaleshi da fad'a sosai ta nuna masa bai kyauta ba abinda yayi musu da nasan suna part d'insa lokacin daya dawo suke magana wallahi da taje ta taho dasu kashe mata 'yan matan nata yake son yi ko kuma yaya dazai ri'ka basu wahala haka Ahmad dai shuri yayi yana sauraron ta saida takai karshe ya bata hakuri ya nuna bazai sake irin hakan ba kafin ya mi'ke yana fita a part d'in ya koma nasa ya d'auko alluran zazza'bi ya dawo Momy bata parlor direct part d'in su Khairat ya shiga suna kwance kowacce tayi barci kunna fitilar wayarsa yayi yana haskasu ganin barci suke ya yaye bargon da suka lullu'ba yasa hannu ya dafa goshin Khairat yaji jikinta babu zafi site d'in da Baby take kwance ya koma itama ya dafa nata goshin kamar na Khairat d'in itama zazza'bin ya sauka mayar musu da bedsheet d'in yayi yadda yake ya rufesu yana fita a part dama so yake yaji inda me zazza'bi yayi musu allura karsu kwana da zafin jiki amma tunda duk ya sauka shikenan nan..............✍️Mrs Äl'ämëëñ Ahmad ce. TYPING 📲Tue, Apr 1/25 10:00AM YUSRAH MUSA ABUBAKAR 🤘💯. 👑 ROYALTY 👑 ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫 Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai 'ya'yan ta. ••••Dedicated to my blood•••• SALEEM MUSA ABUBAKAR NAJA'AT MUSA ABUBAKAR FATIMA MUSA ABUBAKAR AISHAT MUSA ABUBAKAR ABUBAKAR MUSA ABUBAKAR √Wannan page din naku ne yan uwa rabin jiki Allah ya bamu ha'kurin rashin mahaifin mu ubangiji ya gafarta masa yayi masa rahma ya haskaka kabarinsa. ANNABI SAW Annabi farkon kasantattu wallahi ubangida ba danka ba daba abinda zai wanzu. Da sunan Wanda ke rayuwa me tasiri darai dubba ma'kagin duj abunda baza'a kirashi da rabbi Allah ba nagode ma da sigar dazan banma ko furta uffan ba da kaban iko nake wake wanda kace kadarinsa ya wanzu. 10~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Raki'inah. @YUSRAHMS CE Page 19 & 20 Duk wani shiri da Hajiya Khubura zasuyi na biki sun gama Daddy yana shan kallonsu baice musu komai ba iya abinda ya kamata ace yayi matsayin sa na mijin Hajiya Khubura kuma zatai auren 'ya ya bata gudun mawa me yawa sosai da kud'i da kayayyaki a take ta saka kud'in cikin account d'inta sannan da wayo ta sake fad'a masa cewa abubuwan da zatai bata gamaba kud'in sun qare ya sake mata transfer wasu a take murna kuwa harda rawa. A 6angaren Nadiya masai gyare gyare ake kullum ba zama ita da Abidah suyi nan suyi can khaleel kuma baya gidan kwana biyu yaje gidansu sai daren d'aurin aure zai dawo domin fushi ya d'auka da Hajiya Khubura ya fad'a mata yana son a had'a aurensa da Ayrah dana Nadiya tace a'a shi ba yanzu ba akan haka yai yaji ya tafi ko kiranta a waya bayayi idan ta kirashi baya d'auka karshe dole ta 'kyale shi tasa a ranta duk inda ya tafi

Chapter 11 of 22